gabas ke ɗauke da babban madafar abincin gidan baki ɗaya. Ƙasa ce turɓaya ke malale a farfajiyar gidan wacce tayi fes sakamakon sharar da ta samu, ko'ina ya yi zanen tsintsiya ya yi kyau ga wata iskar da ke kaɗawa tare da babban Iccen Mangwaron da ke farfajiyar filin gidan.
Kwance yake ya kinshigiɗa da jikin bishiyar Mangwaron tare da lumshe idanunsa da alama bacci yake yi.
Umma ce ta zo ta tsaya a kan shi cike da mamaki a fuskarta ta ce.
"ASHIRU... Ashiru..kai Ashiru!"
Da sauri ya zabura yana mai share hawayen idanunsa ya kalle ta murya a sanyaye ya ce.
"Na'am Umma.."
Haɓa Umma ta riƙe tana ƙara girmama wannan al'amari na Ashiru ta ce.
"Au! Wai Kuka kake? Lallai Ashiru! Kai shikenan ba za ka haƙura ba kenan? Sai kace ba musulmi ba..."
Bokiti Ayya ta ajiye dai-dai inda suke tsaye suna maganar itama ta ce.
"Hmm! Ni wallahi tun da na yi tozali da su zuciyata ta cika da tababar cewa anya waɗan nan mutanen bil'adama ne kuwa? Sai ga shi a dare ɗaya zargina ya tabbata, labarin su ya zama tamkar an yi ruwa an ɗauke."
Cike da jin wani irin zafi a ƙoƙon ransa ya kalli Ayya ya ce.
" Ni dai dan Allah Ayya ku daina irin waɗan nan maganganun, wallahi bana jin daɗinsu sam! Beenafah yarinya ce ƙarama,kuma ita take ɗauke da nauyin kula da mahaifiyarta da ƙanenta, sannan su ɗin Mutane ne kamar kowa..."
Jinjina kai Ayya ta yi ta ce.
" To naji! Yanzu sai ka faɗa mini ina suke?....Ka tafi neman su an ce ba bu ma wasu masu kama da su da suka taɓa zama gidan, har su Fa'iza sun tafi amma kuma dai maganar ɗaya ce ba'a san wasu masu kama da sunan ba. Wata ƙila kuma sun koma garin su tun da dai kace su kaɗai ne su uku ƙwallin-ƙwal..."
Cikin nuna ɓacin rai Umma ta ce.
"Ai sai ya zauna nan ya yi ta ɓatawa kansa lokaci! Tun da dai ba ya jin shawara. Tun da ka kasa samun su ka haƙura mana! Ka tashi ka shirya ka wuce Kano, yan da ka ɗebo ƙarfar nan ba tare da neman izinin sa ba ka tashi ka shirya ka koma. Tun ranar da ka iso garin nan ya kirani ya sanar mini cewa bada izininsa ka taho ba, saboda haka ka tashi ka koma ka ji na faɗa maka...abu tun ana na marmari har an dawo na ɓacin rai, haba!"
Ta shi ya yi kawai ya ɗauke ledar da ke gaban sa ya nufi ɗakinsa dake ƙofar gida ya bar su Ayya nan suna halaƙoƙo.
Tun ranar da wayarsa ta lalace ya kaita gyara akace gyaranta kusan dubu talatin ne, hakan yasa ya kira Babban Yayansa dake Kano, Yaya Nura akan cewa ya turo masa da kuɗi wayarsa ta lalace, shi kuma Yaya Nuran sosai ya hau shi da faɗa yana faɗin bai ga amfanin Keke-napep ɗinda ya saya masa ba, tun da in dai lalura ta wuce dubu goma baya iya magancewa kansa ita ko kuma wani na cikin gidan to ya tattara ya dawo kusa da shi ya shiga shago shima, idan admission ɗin ya tashi daga can ya riƙa tafiya. Daman tun da ya gama N.C.E yake zaune zaman jiran Admission na zuwa jami'a, ganin yana zaune a banza yasa yayan nasa ya siya masa Napep domin ya dogara da kansa kuma ya riƙa taimakawa iyayen su da 'ƴan wasu lalurori na yau da kullum. Jin babansu da ma sauran mutanen gidan sun goya baya, hakan yasa dolensa ya shirya ya washegarin daren da ya kira Beenafah a waya. Bai ƙara shiga tashin hankali ba sai da ya yi ta kiranta bata shiga abu kamar wasa.
Tunda ya tafi da ƙyar ya ga wucewar wata ɗaya lafiya, haka ya roƙi Yaya Nuran alfarma akan ya barshi ya zo gida yana da uzuri. Tun da ya sauka Gusau ya dire jakarsa ko minti ɗaya bai ƙara cikin gidan ba ya fita zuwa gidan su Beenafah. Sai dai kuma! Bai san cewa allon ƙaddara ne zai juya da shi zuwa wani bigire ba bayan ya sauka a ƙofar gidan na su.
Haka ya dawo tamkar wani mutum mutumi jin cewa wai babu ma wasu masu kama da wannan sunan a cikin gidan. Tamkar wani mai taɓin hankali haka ya dinga musu da mai gadi yana neman kai masa duka. Haka ya ɗauki tsawon lokaci suna dragging ƙarshe dole dai ya bai wa kansa magana ya juya ya koma gida da tunanin cewa wata ƙila suna asibiti har yanzu ba'a ba su sallama ba. Daman tun farko da za su tafi yaso ya bi su Sokoton Babansa da Umma suka ce ba su amince ba.
Haka ya share kusan sati yana zarya gidan su amma magana ɗaya ce dai cewa babu wasu mutane a gidan ma su suna Beenafah.
Haka ya tattara ya koma garin Kano zuciyarsa cunkushe da baƙin ciki da damuwar rashin samun su Beenafah. Kullum kwanan duniya sai ya kira Su Ayya cike da jaje suyi ta aikin ba shi magana mai tausasa zuciya. Sannan kullum su Fa'iza cikin zarya suke wurin neman su amma babu wani labari.
Haka ya rayu tsawon wata huɗu cikin damuwa na rashin su Beenafah, daga ƙarshe shi ne ya sake biyo hanya ya dawo ɗaɗɗake da kayayyakin siyayyar da ya jima yana yi musu musamman Beenafah, ba tare da ma Yaya Nuran ya sani ba.
Shi dai waɗan nan mutane sun zame masa ƙaddara a rayuwar sa, da yana zaune hankalinsa kwance babu abin da yake damunsa, a lokacin da ya same su sai ya ji duniyar sa ta ƙara faɗaɗa, ta yalwata da wani wadataccen farin cikin da shi kaɗai yasan mi yake ji dangane da Beenafah da ahlinta. Sai dai kuma! Daga lokacin da ya rasa su shikenan ya gigice ya ɗimauce, rayuwa ta yi masa ɗaurin kazar kuku. Yarinya ƙarama! Mai ƙaramin tunani; duk da cewa bai san komai dangane da rayuwar su ba, yasan tabbas daga action ɗinta tana da buƙatar matallafi....Tausayinta yake ji, matuƙar-matuƙar tausayinta yake ji har ma Ammien da Bahrain. Kuma in sha Allah muddin ba numfashinsa ne ya yanke daga gangar jikinsa ba, har abada ba zai daina neman su ba.
Bayan Umma ta hasa mishi wuta, dole uwar naƙi ce zaɓi, haka ya tattara ya sake komawa Kano.
****
Tun da muka shiga azumi, tare muke aiki ni da Aunty Hajjo a kitchen bayan kowa ya kambala aikinsa da zai yi na yau da kullum.
Ƙarfe biyu muke farawa wanda watarana zuwa biyar mun gama kambala komai. Kuma tun da aka fara azumi komai na ci da sha idan mukayi sai Aunty Labiba ta bamu shi, wanda kayan amfanin da ta bamu iyaka ga Suhr muke amfani da su domin komai tana bamu.
Azumi na goma sha biyar ta kiramu ta bamu Atamfa bibbiyu da shadda ɗaɗɗaya da kuɗi naira dubu talatin-talatin ta ce kowa ya je ya yi ɗin ki ya sai takalmi.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM*
*OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*
*FREE-BOOK*
*PAGE 14*
Rabon da muyi sabuwar sutura har mun manta, tun lokacinda mahaifinmu na raye da kuma lokacinda Daddy yake ƙaunarmu. Amma kam rabonmu da sabon ɗinki anyi shekara uku, shiyasa kayan da muke dasu duk sun yi mana kaɗan bama kamar ni da na kasance da tsawo tamkar bishiyar zogale wacce ga tsayi amma ba jiki.
Cikin nuna tsantsar farin ciki na isa gida tamkar zan kife akan murna na zube kayan gaban Ammie ina faɗin.
"Ammie duba ki gani daga Aunty Labibata..."
Ɗaga kayan Ammie ta yi tana ta yabawa tana sakawa Aunty Labiba albarka.
Bayan ta gama duba kayan na kalleta na ce.
"Ammie, kinga sai a ɗinkewa Bahrain wannan shaddar ayi mai har da babbar riga ke kuma a ɗinke miki ɗaya nima in ɗinke ɗaya mu saka muje Idi idan Allah ya yarda..."
Hawayen da suka silalo mata ne suka ɗaga mini hankali lokaci ɗaya. Cikin ruɗewa na ce.
"Ammie lafiya? Miye ya faru?"
Girgiza kanta ta yi a hankali ta ce.
"Ba komai. Kawai dai idan ina tunawa da wasu abubuwan sai in ji zuciyata ta yi mini nauyi sosai..."
Ni ma ban san lokacinda hawaye suka wanke mini fuskata ba, ina kallonta idanuwana cike da rauni na ce.
"Ammie kina tunawa da Abbie ko? Ni ma haka! Ina jin wannan raɗaɗin da zafi a zuciyata. Shin Ammie dole Daddy ne kaɗai danginmu? Na ga wasu suna da dangi da yawa, to mu fa?"
Jinjina kanta ta yi a hankali ta lumshe idanunta ta buɗesu a kaina ba tare da hawayenta sun tsahirta ba ta ce.
" Dr. Bello da Alhaji Mudassir, Yaya guda suke da ita tallin tal wacce suke uwa ɗaya uba ɗaya da ita. Ita ce ta zamto uwa agaresu domin ita ta rainesu su biyu har suka girma wanda aurenmu bai fi shekara biyu ba ta rasu. Shiyasa Alhaji Mudassir ya zamto shi ne komai na mahaifinku..."
Sallamar Yaya Hamza ita ce ta katse mana wannan muhimmiyar firar da na yiwa babbar Register a masarrafar tunanina.
Wuri ya samu ya zauna yana mai kallon Ammie yace.
" Subhanallah! Ammie..ya naga fuskarki ta yi wani iri? Akwai wata damuwa ne?"
Murmushi ta yi tana mai share hawayenta ta ce.
"Ba komai Hamza, an dawo daga shagon?"
"Mts! Wallahi tserowa na yi Ammie na ɗan sarara idan an sha ruwa na koma. Ɗinki ya yi mana yawa kamar zan yi hauka nake ji wllhy..."
"To ina ka baro shi Jafarun?"
"Yana can Shagon, ai ya ce in faɗawa Beenafah ta haɗomai abinci idan kun rage, tuwo yau Mama tayi kuma ba zai ci ba na sani...."
Ya ƙarashe maganar yana kallona.
Nima kallonsa na yi na ce.
"To Yaya Hamza kaima gaka ka zo kuma nasan nan kake so kasha ruwan?"
"Sosai ma! Miƙo mini buta na yi alwala kinga ma lokaci ya ƙarato..." Kallon kayan da ke gaban Ammie ya yi ya ce.
"Ammie wannan ɗinka muku za'a yi?"
Ɗan murmusawa ta yi ta ce.
"Kayan ɗinkinmu ne da aka bamu sadaka a gidan aikin Beenafah."
"Allah sarki! Allah ya saka musu da alheri. Na kun sai a bai wa Yaya Jafaru domin shi ne ke yin ɗinkin Mata ni kuma sai na ɗinka na Bahrain."
Ina dariya na ce.
"Ai kuwa shikenan ta kwana gidan sauƙi...amma dan Allah ka faɗa masa ya yi mini mai kyau na zamani."
Butar da na ajiye masa zuwa gabansa yaja yana faɗin.
"To ki faɗa masa da kanki mana."
"Tau shikenan in sha Allahu zan faɗa masa Yaya Hamza. Daman Fakiha ta taɓa faɗa mini cewa Yaya Jafaru yana ɗin ki ashe kuwa da gaske ne."
Babbar tabarmarmu na ɗauko na baza sannan na ɗauko plate da sauran kayan amfani na ajiye sannan ɗauko mana kayan zuwa masallaci na ajiye a gefe.
****
Washe gari Ammie ta kira Yaya Jafaru ta bashi kayan tare da naira dubu biyar amma ya ce ba zai karɓi kuɗi ba. Babu yanda bata yi ba amma yace shi sam! ba zai karɓa ba ai yanzu an riga an zama ɗaya.
Ina kan hanya sai ga Yaya Jafaru ya cim mini wai in faɗa masa wane kalar ɗinki zai mini.
Kallonsa na yi na ce.
"Ni kam Yaya Jafaru ina nasan ɗinkin da za ka yi mini? Duk wanda ka yi mini ina so..."
"To ni ina nasan wanda kike so."
Haka dai muka yi ta janiniya har muka yi kusan kai gidan Aunty Labiba, kallonsa na yi na ce.
"Yaya Jafaru!"
"Na'am Beenafah."
"Please ka daina bi na haka bana so. Idan kana da wata magana dani to ka cim mini a gida kamar yanda ka saba, Ammie ta faɗa mini bata son hakan please daga yau ka daina."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"In Sha Allah ba za'a koma ba. Kinga ma na tsaya daga nan....Allah ya tsare hanya."
"Amin. Sai na dawo."
Ina zuwa na tarar da Adeel da ƙur'ani a gabansa yana karantawa. Dariya ce ta suɓuce mini ƙasa-ƙasa na ce.
"Adeel hala har da yau ɗinma azumi kake?"
Jinjina kan shi ya yi ba tare da ma ya kalleni ba, alamar irin boss ɗin nan wanda mai kashe shi sai ya shirya.
Jinjina kaina na yi na ce.
"Masha Allah. Allah ya nuna mana..."
"uhm! Kafin an jima ka fara mana kuka ba."
Cewar Aunty Hajjo tana mai ƙarasowa cikin parlourn.
Dariya na yi muka gaisa sannan kowa yaje ya kama aikinsa. Bayan munyi sallar azahar muna kitchen misalin ƙarfe uku saura sai ga Adeel ya shigo fuskar nan a turbune ya ce.
" Ni fa wallahi Aunty Beenafah cikina zafi yake mini.."
Taɓe baki nayi ina mai ɓoye dariya ta na ce.
"Allah ko!"
"Shikenan kawai an kai Hanan gidansu Hajiya ni an barni a nan kuma ita can ɗin bata azumi..."
Ruwan zafi na ɗebo na haɗa masa Tea nan take na miƙa masa sai gashi ya karɓa. Jinjina kaina na yi na ce.
" Amma dai kam ya kamata ka riƙa yin lissafi Adeel. Bahrain fa azuminsa goma sha uku, kai kuma shida kawai, haba! Bana son mutum ya zama mai raki da yawa. Kana namiji ya kamata ka riƙa zama mai juriya."
"To kiyi haƙuri,in sha Allahu gobe zan yi..."
"Ai kullum haka kake cewa.."
"Ki yi haƙuri zan yi gobe. Amma dan Allah za ki kawo mini Bahrain in gan shi?"
"Eh..."
"Yaushe kenan?"
Kallon shi Aunty Hajjo ta yi ta ce.
"Dan Allah kada ka ishemu da tambayoyin nan naka na 'ƴan Jarida, a bikin Sallah In Sha Allahu za ta kawo maka shi."
A yanda na lura ba su cika shiri da Aunty Hajjo ba, domin ita bata cika shiga al'amarin yara ba, ban sani ba ko su Adeel ɗin ne bata doguwar alaƙa da su ko kuma haka dai take a rayuwa.
Madara ya buɗe ya ƙara sannan ya ɗauki gorar ruwa ɗaya ya fice kawai ba tare da ya ƙara cewa komai ba.
Tsaki ta ja tana mai ci gaba da mita tana faɗin.
"Allah Beenafah na tsani rashin sanin ciwon kai a rayuwa. Mafi yawan yaran masu kuɗin nan sai a hankali, sakuwa da shiririta ya yi musu yawa, kana zaune 24 hours a A.C baka aikin fari baka na baƙi amma azumi ya gagareka....wai nan har don ma Mummyn ta su tana yi masa jan ido, shiyasa Hanan ta fishi daɗin sha'ani, ga shegen surutun tsiya, idan ya fara maka tambaya tamkar wani jikan Aku.."
Ni dai ƙala bance ba kawai na ci gaba da dariya, in dai fagen tambaya ne ni dai ina da Oga Bahrain saboda haka ba zance komai ba.
****
Tun ana sallah saura kwana uku muka fara aikace-aikace masu matuƙar yawa da kuma wahala, idan akayi wannan ayi wannan, sannan ga Aunty Labiba ba ta son tarkacen mutane, mu ɗin dai mu kaɗai ne sai ita cikon ta uku. Na ga wasu en mata su biyu sun zo da alama Sallah suka zo, amma kullum suna ɗaki ban taɓa ganin sun zo kitchen ba. Ana saura kwana biyu salla ta kiramu bayan mun kambala aiki, ta bani kaji guda biyu na turawa da aka gyara ta bai wa Aunty Hajjo biyar, magi, shinkafa, Mai, komai haka ta raba mana shi wanda komai na Aunty Hajjo yafi nawa yawa wata ƙila kam sun fi mu yawa ne shiyasa ko kuma don ta fini daɗewa da ita.
Wani ƙarin farin cikin ma Leshi ɗan ubansu ta ƙara mana da Atamfa tace mana daga gidan iyayenta aka raba shi ne ta karɓo mana namu.
Wallahi Allah ya sani ina ƙaunar Aunty Labiba domin tasan girma da darajar ɗan adam. Duk abin da Biba ta faɗa mini dangane da ita ashe somin taɓi ne sai yanzu da na zauna da ita na ƙara sanin haƙiƙanin wacece ita.
Cike da uzuri na gama shirya kayana na ɗauka nabi ta ƙofar baya na kai bakin gate sannan na dawo parlournta ana yi mata zanen lalle mai kyau na ce.
"Aunty Labiba na tafi sai da safe..."
"A'a! Ba inda zaki je sai an miki lalle Beenafah."
Ɗan gwalo idona na yi ina mai dubin agogon bangon parlourn na ta na ce.
"Aunty Labiba biyar ta gota sosai..."
Gyaɗa kanta ta yi ta ce.
"Na sani. Yau ɗin already dare ya yi, gobe kuma daren sallah sannan kuma sai kin zo nan ɗin still, to idan ba'a miki yau ba shikenan a haka za ki yi sallar?"
"Aunty Labiba..."
"Sai fa an miki lalle Beenafah. Ki gayawa Maman taku cewa ni ce na tsayar dake."
Zaunawa na yi daman already an gama mata za'a farawa cikin baƙinta ne ta ce su yi mini alfarma a mini.
Da ƙyar na lallaba ta yarda aka mini kaɗan wanda daga yatsu sai bayan hannu da tafi shima ɗan mitsini, maganin dai ba'a yi ba. Ƙafar ma haka, ba wani mai yawa ba amma yayi matuƙar yin kyau kamar ka lashe.
Ina nan sai da aka fara kiran sallar Isha bayan ya bushe naje na wanke sannan na fito a gaggauce ina ta mata godiya. Ni da baƙinta dai ido ne, bayan gaisuwa babu abinda yake haɗamu da su, to ko zaman lallen nan sai dai in ɗago in ga suna kallona daga zaran mun haɗa ido sai su kauce.
Ina isowa inda na ajiye kayana muka yi kiciɓis da Muhsin da kuma Adeel wanda da alama masallaci za su tafi. kallon inda na ɗaga ledar naman Muhsin ya yi yaga ruwan naman duk sun ɓata floor ɗin ya wani buga tsaki ya ce.
"Dan Allah ƙazamar banza ki zo ki wankewa mutane wuri kin ji ko..."
Cikin shakku Adeel ya waro ido ya kalleni sannan ya kalle shi ya ce.
"Ya Muhsin Aunty Beenafah ce fa..."
"And so! Miye ruwana da kowace banza ce ita. Ki wuce ki ɗebo ruwa ki zo ki wankewa mutane wuri....kuma kai idan na ji ka ƙara kiranta da Aunty wallahi sai na fasa maka baki..."
Lumshe idanuwana na yi jin yanda kalamansa suka dakar mini zuciya har ban san lokacin da wa su zafafan hawaye suka wanke mini fuskata ba.
Wai wannan yaron! Idan har ban girmeshi ba shima ba zai girme mini ba, sai dai kuma idan mu zo ɗaya da shi ne a shekarun amma shi ne ya tsaya a gabana yana ci mana fuska son ran sa. Hmm!
Duƙawa na yi na kwashe ledojina domin wallahi ba zan goge wurin ba, duk abin da zai yi ya daɗe bai yi ba ina jiransa. Ban yi aune ba kawai na ji an ja hijabina baya da ƙarfi har saida ya yage. Jikina na wani irin mazari na waigo tare da yi masa wani mugun kallo na ce.
"Sake mini hijabita Muhsin!"
"Idan ba'a sake ba mi za ki yi?"
"Ya Muhsin ka sake mata hijabinta...ka daina Ya Muhsin.."
Cewar Adeel hankalinsa a matuƙar tashe.
Hannayena guda biyu na saka na fisge da ƙarfi sannan na sake duƙawa na ɗauki kayana na kama hanyar gate na fice zuwa gida.
Ina shiga na tarar da Ammie, Bahrain da kuma Fakiha. Bahrain ɗin yana fifita wa Fakiha lallenta ga hasken Nepa fal ko'ina ya haska tamkar farin wata. Tuni na ji duk wani ɓacin ran da na zo da shi ya tafiyar sa.
Cike da jin zallar farin ciki na ce.
"Wayyo Allah Nepa! Ammie Nepa? Waye ya saka mana Nepa?"
Dukkan su dariya suka shiga yi ganin yanda duk na ruɗe na cika da farin ciki.
Kallona Bahrain ya yi ya ce.
"Ya Jafaru ne ɗa zu yazo da wani abokinsa ɗin nan mai aikin Nepa ya saka mana..."
"Innalillahi! Wayyo Allah Nepa, shikenan mun huta da duhu...Mun gode mun gode Allah ya saka masa da alheri."
Daga haka na fito da gudu daga gidanmu na shige na su gidan sai ga shi kuwa na ci sa'a yana zaune a saman benci yana cin abinci.
"Ya Jafaru mun gode sosai, mun gode Allah ya saka da alheri, Allah ya biya maka buƙatocinka na alheri duniya da lahira."
Cikin nuna jindaɗin addu'a ta yace.
"Amin Beenafah. Kin dawo?"
"Eh na dawo, Ina zuwa naga gidanmu ko ina haske,wallahi na ji daɗi sosai....miye kake ci haka?"
Kallon cikin plate ɗin ya yi sannan ya kalleni ya ce.
"Indomie ce na sa Fakiha ta soyamini..."
Kafin ya iyarda rufe bakin sa har na zauna na kaɗa hannuna muka ci gaba da ci.
Kallon lallen hannuna ya yi ya ce.
"Kai! Amma dai wannan lallen ya yi kyau."
Dariya na yi na ce.
"Da gaske?"
"Da gaske nake, waye ya yi?"
"Gidan aikina. Aunty Labiba ta saka aka mini."
"Gaskiya ta kyauta. Mun gode, Allah ya biya."
"hmm! Ya Jafaru Aunty Labiba tana da kirki. Ta fa ƙara mana kala biyu ni da Aunty Hajjo, sannan har da hijabai guda biyu da kayan kwalliya da gyale..."
Nan na yi ta bashi labari Maman su na ta aikinta tana saurarenmu har muka kambala na fita na wuce gida.
Kallona Fakiha ta yi ta ce.
" Wai ke kin wani je kin yi zamanki. Mai lalle tunɗazu tana ta can tana jiran ki.. "
Hannayena da ƙafata kawai na nuna mata ba tare da na ce komai ba sai aikin murmushi.
"Au! Ashe ma kin yo lallenki daga can? To an huta, daman Ya Jafaru ne ya bamu dubu huɗu kowa dubu biyu ya ce muyi lalle da kitso..."
"Kitso tun kwana biyar da suka wuce Aunty Hajjo ta dunƙule mini abina...saboda haka a bani kuɗina."
Wata uwar harara Fakihar ta maka mini sannan ta ce.
"Wai ma! Nikam wallahi na riga na sayi kayan lalle da nau da naki na kai mata, har kuɗi na biya ta don ban san cewa daga can zaki yo ba...."
"To ta yiwa wata da su sai ta bata kuɗinta mana."
Cewar Yaya Hamza dake shigowa gidan yanzu.
Jinjina kaina na yi na ce.
"Ah to! Kina karɓowa ki mayar masa da kuɗin sa tunda an samu sauƙi. Ya Hamza ka goge mana kayanmu mana dan Allah..."
"Ba zan yi ba..."
"Kai Ya Hamza dan Allah?"
"Gaskiya aiki ya yi mini yawa ba zan iya ba..."
"Eh, amma idan kana son wani abu ka iya sakani wahala, shi ne nasiha ɗaya ba zaka mini ba. Da Ya Jafaru ne da yanzu ya amsa. Wallahi Ya Jafaru da abinda na ce da ma wanda bance ba komai yi mini yake."
Dariya ya yi ya ce.
"To Ya Jafaru kika ce Beenafah. Ya Jafaru daban Ya Hamza daban..."
"Beenafah!"
Ammie dake ɗaki na ji ta kira sunana, hakan yasa na shige ɗakin na bar su a nan.
****
Washe gari ma ban dawo gida ba sai tara na dare. Cikin daren nan bayan na dawo na shiga haɗa mana Miyar stew da sauran aika-aikacen da ke jirana wanda ban kwanta ba har asuba.
Muna cikin shiryawa zuwa filin Idi Ya Jafaru ya shigo mini da ɗunkunan da Ammie ta bashi shekarajinya wai har ya ɗinke su.
Daman na riga su shiryawa cikin Atamfa ta sabuwa da sabon hijabina da takalmi. Ina jin sallamarsa na fito ina murmushi na ce.
"Kai Ya Jafaru gaskiya ka wanku...ka yi kyau, wannan shaddar ta maka kyau."
Murmushi ya sakar mini yana jinjina kansa ya ce.
"Ke ma kin yi kyau sosai... Zo mu yi hoto."
Matsowa na yi muka yi ta ɗaukar hoto da wayarsa da ni da shi. Bayan mun gama ya yi ta ɗaukata ni ka ɗai har sai da Ammie suka fito ita da Bahrain ɗin sannan muka fito muka nufi babban masallacin Idi tare da su Fakiha da maman su,cike da farin ciki.
Bayan an kambala muka dawo gida muka zauna zaman cin abin ci da sha muna ta yiwa juna barka da shan ruwa.
Muna nan zaune a gida munata firarmu, sai misalin sha biyu na rana na na cewa Ammie.
"Ammie bari na tashi naje gidan Aunty Labiba, tace mana yau ne kaɗai take gida daga gobe gidan su za ta riƙa tafiya sai dare
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 67