Allah ya raya su ya yi musu albarka."
Ammie ce ta amsa da amin sannan ta ce.
"Ina Ashiru yake Maman Fa'iza?"
"Ashiru yana Kano. Tun da ya tabbatar cewa da gaske an yi auren Beenafah ya wuce bai dawo garin nan ba har yau ɗin nan. Yana can ya na ta kasuwancinsa."
"Allah sarki! Allah ya ci gaba da dafa masa ya zaɓa mishi mafi alheri."
Ayya ce ta karɓe zancen tace.
"Amin ya Allah. Ai auren sa da Sabila ma sati biyu ne suka rage in sha Allahu. Ai tuni ya cire Beenafah a rai tare da yi mata fatan alheri."
Duk firar da suke ina nan zaune na yi shiru tare da saukar da kaina a ƙasa ina chart da Abbansu Arhaam. Yayinda kuma can ƙasan raina nake tanyasa farin cikin auren da aka ce zai yi. Hmm! Allah sarki rayuwa! Yanda nake farin ciki da mijinda na aura ina masa Addu'a shima ya samu farin ciki da kwanciyar hankali da matar da zai aura. Allah ya basu zuria ɗayyaba ya ƙara yalwata masa arzikinsa.
Cikin farin ciki Ammie ta ce.
"Kai Alhamdulillah! Wallahy na yi farin ciki da jin wannan labarin. Daman aure ɗaya ne zai tsayar da ni zuwa wani satin. Amma yanzu kam dole na tsaya domin shi ma Ashiru ɗa na ne, ina farin ciki da wannan labarin, Allah ya nuna mana lokaci lafiya ya sanya alheri."
Bayan sun ɗan ƙara taɓa fira nace Ya Hamza ya shigo musu da siyayyar da nayo musu sannan ba su kuɗi dubu ɗari biyar sannan itama Ammie ta basu kuɗi wanda ban san ko nawa ba ne sannan muka musu sallama muka fito.
Bayan mun koma gida muka shiga tattara kayanmu wanda komai Ammie ta sake gyara mana. Sannan ta zauna ta ƙara mini nasiha da jan kunne, muka yi ta tattauna har kusan ɗaya na dare sannan muka kwanta bacci.
*******
Washe gari tun misalin ƙarfe shida na yamma Su Aunty Labiba suka iso gidanmu tare da Aunty Ziza da Suwara wacce ke ɗauke da yaron ciki a jikinta.
Daman koda suka iso mun riga mun gama shiryawa ni da su Aryaan, sai kuma en rakiyarmu wato, Su Aunty Hassana da kuma Maman Fakiha waɗanda su ne mutanen da muke da su a faɗin Gusau.
Bayan an gama gaggaisawa an yi fira kaɗan muka fito. Hamshaƙan Motoci ne jere guda uku na gani a ƙofar gate ɗin namu.
Kallon Aunty Labiba na yi na ce.
"Aunty Labiba sai ka ce za'a kai Amarya? Ni wallahy dama bari ku ka yi Mijina ya zo ya tafi dani duk ya fiye mini wanna..."
Wata irin shewa sukayi sannan suka fashe da dariya Aunty Ziza ta ce.
"Lallai ma matar nan! To idan kika yi haƙuri yanzu mintuna kaɗan ne za su sadaki da Mijin naki.."
Hannu na saka na toshe bakina ina dariya na ce.
"Auh! Shin duk Auntyies ɗina ne a nan ko? Na ɗauka Su Fakiha ne kuyi haƙuri.."
Dariya sukayi sannan Aunty Labiba ta ce.
"Yi abun ki ƙanwata kuma Auntyna, lokacin ne kuma damar ki ce. Wallahy banga laifin ki ba."
"Shin wai sai an kira sallar magrib sannan za ku shiga ko yaya? Mts! Ku da yake in dai mata ne tseguminku ba ƙarewa yake yi ba."
Ɗan wara ido na yi ina kallon mutumin da ya leƙo kansa daga cikin mazaunin driver yana magana.
Dariya Aunty Labiba ta yi ta ce.
" leƙa fuskar sa da kyau ki gani. Barrister ne da kansa. Daman ya ce shi ne yau wanda zai mayar dake sannan ya baki haƙuri akan korar ki da ya taɓa yi daga gidansa, wanda yanzu abin ya dame sa..."
Dariya na yi na ce.
"Lah! Ai ba shi ne da godiya ba Aunty Labiba ni ce. Wallahy ni ce da godiya, domin da ace bai koreni ba a ranar, da yanzu ban je gidanku har na haɗu da Abbansu Arhaam ba,dan Allah ki tayani godiya."
Sai da muka gama dariya sannan muka shiga motocin muka tafi. Koda na shiga na tarar da Biba da wasu mata masu aiki guda biyu.
Basu wani jima ba suka tattara suka fece wanda Fakiha ce kaɗai wacce ta tsaya akan cewa sai na bata alƙawarinta domin ba lallai wannan zumuɗin da nake ya bari ta ƙara ganina ba. Daman na faɗamata ba zan tsaya bukinta ba tun jiya da muka yi waya da dare.
Kwalayen kayan ƙamshin na buɗe na zazzaɓa mata sannan na kira Biba na bata na ce ta samu kwali ta jera mata su.
Ina cikin rufe kayan ta kalle ni don bata da kunya ta ce.
"Sauran kayan matan ko?"
Wani kallon banzan na yi mata sannan na ce.
"Nima da za'a kai ni gidana sanda aka mini auren ba'a bani kayan matan ba, kayan ƙamshi kaɗai aka bani...tashi ki wuce dan Allah. Kinga yanxu an gama sallar magariba, daga zaran an yi Isha dawowa zai yi. Dan Allah ki wuce ki barni na shirya masa. Ke wallahy gidan Haya ce da ba'a kwashewa lafiya da ke."
Wata uwar dariyar ta sheƙe da ita sannan ta ce.
" Allah ya baki haƙuri to, na tafi sai da safe."
"Yauwa! Allah ya bamu alheri."
Har bakin Main door ɗin na rakota Sannan ta karɓi kwalin daga Hannun Biba ta wuce.
Kallon Bibar na yi na ce.
"Kin gama shiryawa su Arhaam ɗin?"
"Eh! Na gama tun ɗazu."
"Ok tau, ki ci gaba da kulawa da su,ina zuwa yanzu."
Sai da na gama duba abincin da suka shirya sannan na wuce na yi sallar Isha na shiga na tsala wanka na fito na kashe lokaci sosai na shirya cikin wani musulmin Lace na kashe ɗauri na fito sak Amarya ta. Sai murmushi na ke yi wanda ni kaina farin da zuciyata take ciki ban san yanda zan misalta shi ba.
*******
Ya Mohaa kuwa, sai da ya gama sallar Isha sannan ya fito daga masallacin zuwa gida.
Ɗan tsayawa ya yi daga nesa yana kallon mutumin da ke tsaye ɗan nesa da gidan kaɗan.
Sai da ya gama ƙare masa kallo sannan ya ƙarasa inda yake tsaye ya ce.
"Malam ya dai?"
Tun da ya iso garin ko minti goma bai ƙara cikakke ba ya fito ya zo gidanta bayan Fakiha ta tabbatar masa da cewa Beenafah tana garin bayan ya tambayeta.
Sai da ya iso ƙofar gidan sannan ya shiga tunanin yanda zai yi ya shiga gidan. Gabaɗaya basirarsa ta ɓace. Dama ya sani ya ɗauko Hamza ko Bahrain sun zo ko zai samu ya yi nasarar aiwatar da aikinsa. Ga shi tsawon wata huɗu da ya je gidansu ya kasa cika aikin nasa, kuma yau wannan damar ita ce kaɗai yake sa wacce daga ita muddin dai bai yi nasara ba to yasan faɗuwa ta tabbata gare sa ta har abada.
Yana cikin neman mafita kuma sai ga mai gidan ya rutsa sa yana tambayar sa wai ya dai?
"Tambayar ka nake, lafiya? Waye kake jira a nan?"
A rikice ya fara ƙyafta murya yana faɗin.
"Daman...Daman...ahm daman.."
Wani murmushin gefen baki ya yi sannan ya ƙara ɗaure fuska tamkar bai taɓa sanin yanda ake dariya ba ya jinjina kansa ya ce.
"Kasan wani abu? Tun ina da ƙurciyata wallahy tallahy ban taɓa sha'awar Zina ba. Duk irin jarabawar da na shiga ban taɓa jin cewa ina sha'awar bin wata macen ba ballantana in riƙa bibiyar matar aure. Ba wai ina alfahari ba ko wani abu, domin na san cewa ban fi ƙarfin jarabawa ba. Amma tambaya ta ɗaya ce a gare ka...Miyasa kake bibiyar Matata? Laifin me ta yi maka ko kuma ni wane laifin na yi maka da cancanci wannan hukunci da har yasa kake bibiyarta tsawon lokaci?"
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM*
*OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 58*
Wani irin matsanancin tsoro ne ya dabaibaye masa zuciya a lokaci ɗaya, domin yanda yaga wani irin ɓacin rai da ya bayyana ƙarara akan fuskar Ya Mohaa ɗin ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba.
Wato a irin wannan mugun yanayin da ake ciki, ko wuƙa a ka ɗora masa akan maƙogoransa yasan cewa ba zai iya faɗar wai dalilin da yasa yake bibiyarta ba.
Cewa zai yi don yana sonta yake bibiyar ta ko me? Ko kuma cewa zai yi yaga shi ɗin bai cancanceta ba sai ga shi? Hmm! Wai aka ce wuya makarantar Kare.
Da ya buga ya buga yaga cewar dai he has no way to escape yasa ya zube akan gwiwoyinsa murya cike da zallar magiya ya ce.
"Sharrin shai ɗan ne kawai...wallahy sharrin shaɗain ne. Dan Allah ka yi haƙuri,wallahy daga yau ba zan sake ba."
Girgiza kansa ya yi yana faɗin.
"A'a kam! Duk tsawon lokacin da ka kwashe kana bibiyar ta, taya ya rana ɗaya za ka ce mini ka daina kawai in yarda da kai. Yan da ka jure ka ke ta wahala haka na zaman bibiyarta dole dai kana da wani dalilin da yasa kake bibiyantan."
"Wallahy tallahy, na rantse da Allah, billahillazy ba komai, kawai sharrin shai ɗan ne..."
"Shi ne wanda yake ƙawata maka matar tawa ko? Hmm! Ka kuwa san rayuwar waye kake bibiya? Duk da da cewa a wannan lokacin ka samu ka kuɓuta da ƙyar wato ashe bai ishe darasi ba. Mata ta itace komai ta wa, duk wanda yace zai raɓeta da wani sharri kuma! To tabbas mutuwa za ta fiye masa alheri a cikin rayuwarsa."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Dan Allah yallaɓai ka yi haƙuri..."
Bai san ya akayi ba, cikin en daƙiƙu kaɗan yaga sojojin sa sun zagaye da bindiga suna jiran umarni.
Cikin gidan ya wuce direct ya bar su a nan ba tare da yi musu wani bayani ba.
Ni kuwa, ina nan na zauna parlour tare da twins ɗina inda muka ci uban gayu sai farin ciki muke. Suna nan na zaunar da su duk da cewa zaman bai gama nuna ba da kayan wasan su wanda Bahrain da Ya Hamza basa gajiya da zuwa kasuwa wurin siyowa, wata haukar ma sai ta baka dariya, yi ni suke wasa da su matuƙar dai suna gida ba su fita ba. Shiyasa Ammie ke cewa da a nan za su ci gaba da zama har su yi wayau da tabbas su Ya Hamza sun haukatar da su.
Ina ganin shigowarsa sai da na ji wani abu mai sanyi ya ratsa cikin xuciyata wanda ya saka na lumshe idanuna sannan na buɗe su a hankali na taka na je na rungume shi na ce.
"Welcome home my LOVE. Na saba yi maka barka da zuwa a duk lokacin da ka dawo gida....yau kuma da ni da yaranmu muke maka barka da zuwa...Welcome home DADDY."
Tun da ya ɗaura ƙwayar idonsa a kanmu, sai da ya ji wani sanyi ya ratsa duk wata gaɓa da jijiyar jikin sa. Wai shi ne a yau ya dawo gidansa ya tarar da matarsa da 'ƴa'ƴansa? Ashe akwai irin wannan lokacin da zai zo a gareshi watarana. Tabbas komai yana da lokaci muddin ka yi haƙuri ka saka Allah a cikin al'amarinka...
"Why are you quite?"
Saukar ɗumin hawayensa na ji a gefen wuyana. Sannan ya ɗago fuskata a hankali ya kalli ƙwayar idanuwana sai kuma ya kalli su Arhaam sannan ya sake kallona cikin wani irin yanayi ya ce.
"farin ciki ne Ya hanani Magana Bibi. Wani irin yanayin farin ciki na ke ji na a ciki wanda ban san ma abin da zance ba...Kin haskaka rayuwata kin sauya mini duniya. You are different Bibi!"
Murmushi na yi masa na ce.
"Alhamdulillah Ala kulli-hal!"
Maimaita kalmar ya yi sannan ya kalle ni a nutse ya ce.
"Bibi...na san Jafaru, nasan irin alaƙarku ta maƙotaka da kuma irin zumuncin da ya ƙulli har yanzu a tsakaninku. Amma ina so ki faɗa mini da bakin ki gaskiyar abin da yasa yake bibiyar ki daga baya....bai kamata Sam ace zancen sa ya shigo a cikin rayuwarmu a irin wannan lokacin da muke tsaka da farin ciki ba. Amma kamawa ta yi ki yi haƙuri. "
Ban san lokacin da wasu hawayen baƙin ciki suka wanke mini fuska ba. Cike da takaicin sa na yi masa bayanin komai da ya wakana tun wancan zuwan har ranar da akace ya zo nemana a daren suna.
Hmm! Wato wani irin mummunan yanayi ne ya bayyana akan fuskarsa wanda sai da ya saka na ji a raina dama ban faɗa masa ba.
Wani irin zafi ne ya ji yana ratsa ƙirjinsa har zuwa fatar jikinsa tsabar yanda ya ji kalaman masu kama da feshin wuta a cikin kunnuwansa.
Wayarsa naga ya ciro yana faɗin.
"Ku yi masa mugun dukan da sai kamanninsa sun sauya sannan ku rufe mini shi..."
Wayar na karɓe jikina na wata irin ciccira na ce.
"Ku harbe min shi! Ku saka bindiga a tsakiyar kansa ku harbesa, kafin ku aiwatar ku faɗa masa cewa saƙo ne daga Beenafah..."
Da sauri ya fisge wayar yana mai mini wani kallon mamaki ya yi sauri ya ce.
"No, don't kill him. Kui masa duka sannan ku rufe mini shi..."
Wasu zafafan hawayene suka biyo saman kumatuna domin sam ni wannan decision ɗin bai mini ba, na so ace an kasheshi domin sam na san har abada ba zai daina bibiyata ba tunda shi ɗin jahili ne, munafuki mai fuska biyu. Jin da gaske ya sauya hukuncina yasa na karye wuyana still da hawaye a fuskata na ce.
"To don Allah kada a bar mini shi a cikin gidannan, domin idan har ya kwana a nan to burinsa ya cika na kwana a inuwa ɗaya da ni. A yi nesa da shi dan Allah."
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Idan kuka gama dukansa..take him to police station, ayi masa azaba mai tsanani."
Yana kashe kiran ya je ya ɗauki Arhaam wanda yake wasa da kuka a lokaci ɗaya alamar ya gaji da zaman, Aryaan na ɗauka nima na fashe da dariya ganin da yake ta wani diri yana dariya na kalli Arhaam na ce.
" Kaga Aryaan yafi ka wayau, domin dariya yake yana welcoming Daddy kai kuma sai wani taɓe baki kake kana kuka.."
Dariya ya yi tare da ware ɗayan hannun sa muka shige ya zagayemu yana faɗin.
"Shi ma ai haka ne a wurinsa. Alhamdulillah! Da sabuwar rayuwar da zamu shiga. Allah ya amintar damu ya bamu zaman lafiya."
"Amin yah ubangiji."
Haɗa masa su na yi sannan na je na kawo mana kayan abincin na baje su a nan,muka zauna muka ci. Bayan na dawo ne ina haɗa musu madara yana ta kallona na yi murmushi na ce.
"Ya dai?"
Jinjina kansa ya yi yace.
"Kin yi kyau sosai. Ban ga wata mace mai kyaunki ba a duniya Bibina.."
Dariya nayi sannan na ce.
"Duk Mazan duniya haka kuke cewa..."
"And every man Idan kika ji ya faɗi haka, to ki yarda cewa shi abinda yake hannun sa, yake zuciyar sa kaɗai ne ya yarda da shi."
"Uhmm! To na gode. Kai ma ka yi kyau sosai..."
"Yanda kika ce kenan."
Bowl ɗin na miƙo ina faɗin.
"Na baka ka ciyar da su.."
Zaro ido ya yi sannan ya yi dariya ya ce.
"What! No...kada na shaƙa musu a hanci."
Dariya na yi ina jinjina kaina na ce.
"Hardai Aryaan, wallahy idan ba ka yi da gaske ba, sai ka shaƙa masa a hanci saboda gadauniya da rashin zama wuri ɗaya."
Matsowa ya yi a kusa damu ya taimaka mini ina basu yana ta dariya ganin yanda muke ta drama, Idan na yi da wannan kafin in waigo wannan ya kama wani abun na daban, a haka dai har muka gama sannan na gyara musu muka wuce ɗaki domin yi shigar da su bacci.
Dariya na yi tuna abinda na faɗawa Suwara ɗazu na ce mata maganin bacci zan ba su domin kada su shiga rayuwata da ni da mijina a yau. Da haka na yi ta addu'a a raina ina roƙon Allah yasa idan suka yi baccin nan kada su farka a yanzu sai na gama bai wa mijina farin ciki da na ƙudurta da shirya masa a wannan daren.
Shi dai yana tsaye tun ɗazu yana kallona ganin yanda nake ta lallaɓa su suna shan Nono har na samu Allah ya taimakeni suka yi baccin.
Bayan na gama tofesu da addu'a na taso ne na ji ya rungumeni a hankali ya ce.
"Thank you for everything Bibi...you are the best mother ever. Allah ya baki lada akan duk wata hidimarki akan su da kuma ni..."
Murmushi na yi tare da saƙalo hannuna cikin wuyansa ina kallon idonsa na ce.
"And thank you for being the best Husband and Super Daddy. Allah ya ci gaba da kare min kai a duk inda ka shiga a faɗin duniyar nan. Allah ya ci gaba da baka halal ɗinka komai ƙanƙantarta ya kuma kare daga sharrin haram komai yawanta..."
"Amin.."
Saukar da hannuna na yi na saƙala a cikin nasa ina masa wani kallon na ce.
"Can we?"
"Anything special?"
Lips ɗina na kai a hankali na goga a nasa sannan na janye tare da kashe masa ido na ce.
"We are gonna burn in fire today..."
Cikin wani irin yanayi ya jinjina kansa yana mai riƙo kwankwasona ya ce.
"And Dayaa is ready to burn in fire..."
"Let's go..."
Tun a wurin wanka ya tabbatar da kalamaina domin na bashi mamakin da sai dinga kallona yana jin na koma masa wata Bibin ta daban a yau. Bayan mun fito muka shirya inda a gabansa na ɗauko wata fitinanniyar Nighty wacce tun ɗazu na gama jiƙeta da sihirtaccen ƙamshin da na shirya masa. Bayan na saka na zare ribom ɗin kaina na zubo gashina kamar yanda na san yana burgesa.
Kallona yake yana mai jin duk wata gaɓar da ke jikin sa tana amsar saƙona yanda ya kamata.
Rigar da ke jikina da ita da rashin ta duk ɗaya, maimakon shi da ya saba fara kawo mini far miki, ni ce nan yau na nemi na zautar da shi da wata kalar zazzafar soyayyata wacce ya ji ta a yau har can cikin ƙololuwar birnin ransa.
Zallar madarar ƙauna muka zuba mai matuƙar daɗi da sanyaya zuciya. Bayan mun kambala mun yi wanka ne na je na ƙara duba su Arhaam wanda duk tsawon lokacin nan suna nan suna bacci abin su sannan na juya na koma a hankali na kwanta a jikinsa tare da ɗora kaina a ƙirjinsa.
Ji na yi ya rungumeni tare da kissing lips ɗina a hankali ya ce.
"Thank you for the Love we made today...kin bar ni wani tarihin da har abada ba zai goge mini ba kamar yanda farkon tarayyarmu ta kasance a tunanina...you promise us to burn...and we burn Happily...thank you."
Shiru na yi tare da ƙara narke masa ba tare da na ce komai ba. Sai dai kalamansa sun yi tasiri a zuciyata sosai, da wannan farin cikin na yi ta murmushi a raina har na yi bacci.
Shi kuwa, gabaɗaya baccin neman sa ya yi ya rasa a wannan daren tsabar yanda ya ji duniyar ta yi masa daɗi.
Bayan ya tabbatar ta yi baccin da gaske, nan ya lallaɓa ya zame ta gefe tare da lulluɓa mata Duvet ya saka pillow ya tare da kada ta ji ta ita kaɗai.
Sai da ya jima yana kallon fuskar twins ɗinsa yana ta zubo da hawayen farin ciki sannan ya tashi daga ƙarshe ya je ya yi alwala ya zo ya duƙufa yana ta nafila yana godiya ga Allah da kuma neman albarka da fatan cika da kyau da imani.
Yana nan zaune yana karatun Qur'an ya ji motsawarsu. Koda ya duba agogo ƙarfe huɗu saura ne na dare.
A hankali yaje ya tasheta taje wurin ta ji da su wanda sai da ya dawo masallaci yaje ya tarar ina ɓingire a nan na ci gaba da baccina tare da su.
Murmushi ya yi sannan ya tashe ni a hankali yace.
"Kin yi sallah ne?"
"A'a! An yi ne?"
"Ƙarfe shida da rabi fa..."
Dirowa na yi a raina ina faɗin ai yanzu salla ta daman sai wuraren ƙarfe shida zuwa bakwai nake yinta, duk yanda Ammie ke tashina sai na yi da gaske sannan nake iya miƙewar tsabar yanda bacci ke dagula lissafina.
Bayan na yi sallahr na kambala na kira Bibi domin ta yi musu wanka ta shirya su, sannan na wuce kitchen na duba mai girki, wacce ɗaya daga cikin chefs ɗin Ziza ne na Eatery ɗinta. Ɗayar kuma ita ce mai share-share.
Wanka na yi na shirya cikin wasu English wears na riga da skirt da hula sannan na je na gyara mana table muka je muka karya.
Haka muka yi ta mu huɗu muna ta rayuwarmu inda a nan muke ta ƙara sanin wasu abubuwan dangane da juna tsawon kwanaki uku.
Ina ɗaki da Arhaam a bayana ina duba wasu ayyukan Daddynsu Arhaam da ya nuna mini yace an kawo musu talla na duba na gani kafin ya mini bayanin yanda abun yake sai ga kiran Ammie ya shigo.
Hankali a tashe ba ta ko bari muka gaisa ba ta ce.
"Beenafah Jafaru ya ɓata, tun ranar da ya iso ya ajiye jakarsa ba'a ƙara sanin ina yake ba. Wayarsa kuma a kashe."
Kai tsaye na ce.
"Ni da Mijina ne muka kulle shi a police station...ni tun a ranar ma na so a kashe shi amma Daddynsu Aryaan ya hana...."
Cikin wani irin tashin hankali ta ce.
"Mi kika ce Beenafah? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Miye ya yi muku haka da zafi..."
"Ammie Jafaru bai da mutunci....kuma a can zai ƙare rayuwarsa har ya mutu."
"Dan Allah Beenafah ki yi haƙuri ki rufamin asiri,...kinga...ina shi Hammodin yake??"
Daga haka na ji ta kashe wayar wanda daga nan ban san mi ya faru ba, sai gashi ya shigo saɓe da Aryaan a kafaɗarsa ya kalleni ya ce.
"Ki shirya mu tafi police station ɗin. Ba dole sai na je ba, amma zan tafi domin wani dalili."
Sauke shi na yi na shirya cikin wani Lace da mayafinshi sannan na sauya musu kaya, sai da na gama duk shiririta ta sannan muka fito a tare muka shiga mota. Na yi mamakin ganin Convoy ɗinsa domin in dai a cikin gari ne daga ni sai shi muke fita a mota. Sai dai idan garin ne zamu bari zamu fita a irin wannan yanayin.
Koda muka isa mun tarar da su Ammie har sun Iso da su Maman Fakiha da Baba.
Tuni duk mutanen da ke wurin suka ɗauki saiti sai ya yi musu umarni da a fito da shi.
Ganin yanayinsa kaɗai sai da ya sanya su Ammie fashewa da kuka mai tsanani. Domin baka ma gane fuskarsa muddin ba ka yi masa kyakkyawan sani ba.
"Jafaru! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wai miye yake faruwa ne??"
Cewar Ammie tana mai kallona da ni da Daddynsu Arhaam.
"Kowane irin laifi ya aikata muku ai bai cancanci wannan hukuncin ba. Shi fa tamkar ɗan uwa yake a wurinku..."
Wani kallon ya yi masa sannan ya ce.
"Wannan dalilin ne yasa har kika iya ganinsa a nan Hajiya. Ba don hakan ba da yanzu wani zancen ake na daban....Kai! Ka buɗe baki ka faɗa musu laifin da ka yi, komai da ka aikata bana so ka rage musu, idan ba haka ba, zan saka ka a motana na tafi da kai wata duniyar da har abada ba za ka taɓa mantawa dani ba."
A somaye ya buɗe bakin sa tsabar yanda ya sha baƙar wahala ya ce.
" Zan faɗa! wallahy zan faɗa dan Allah ka yi haƙuri na tuba."
Yawuna na tofa masa ina mai yi masa kallon tsana na ce.
" Ashe kai ɗin marar kunyar ƙarya ne matsoraci. Ba ka ce a shirye kake domin akan son da kake mini ba koda za ka mutu ba? Miyasa kake magiya kana bada haƙuri a yanxu?"
Hannu Mama ta ɗora a ƙirji tana mai doka wata irin taslima sannan ta ce.
"Yanzu ashe duk tsawon lokacin nan ba ka ji maganata ba Jafaru? Duk yanda na tsawatar maka akan wannan shashancin baka saurare ni ba ashe?..."
Kallon Police ɗin ta yi ranta a ɓace tace.
"Yallaɓai! Ni ce nan mahaifiyarsa, wannan kuma mahaifin sa. Ku ɗauke shi ku mayar da shi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 61 Chapter of 67