*OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM*
*OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 41*
ƙaramar jakarsa ya buɗe ya ciro wasu katin hotuna guda biyu irin na da ɗinnan marar colour ya miƙa masa.
Hannu na rawa ya karɓa ya ƙura ido yana Kallo, wasu irin hawaye na bin fuskarsa tsabar yanda ya ji zuciyarsa ta ƙara raunata.
Wannan ɗin mahaifinsa ne tabbas Alhaji Attahiru, wannan kuma...itace kenan mahaifiyar tasa wacce Baba Ustaz ya kira da RANIA. Sanye take cikin shigar alfarma da manyan gwala-gwalai a wuya da kuma hannuwanta, yayin da Alhaji Attahiru ke sanye cikin shigar manyan kaya na er ciki da babbar riga, cikin style na irin hoton da ɗinnan da akeyi sun zauna akan kujera ɗaɗɗaya. Sai ɗayan hoton kuma, Baba Ustaz ɗin ne, Baban sa da kuma kakansa Malam Araam sai wasu guda biyu waɗanda bai shaida su ba.
Jinjina kai Baba Ustaz ya yi ya ce.
"Wannan ita ce Mahaifiyarka, ita ɗin 'ƴar babban gida ce domin iyayenta sun kasance manyan en kasuwa masu hannun Jari da yawa a fannin Zaren auduga, kayan ado, da kayayyakin ƙasashen Larabawa da ake shigowa da su daga ƙasar Masar da Saudiyya, sannan kuma sun mallaki rukunin manyan gonaki na sesame (Gyaɗa) Gishiri da kuma Goro da ake fitarwa zuwa ƙasashen Habasha da Chadi. Mahaifiyarka ta kasance babbar 'ƴa ta farko a wurin mahaifinta Alhaji Musdhapha Sami wanda mutum ne mai daraja da ya shahara ya yi suna a cikin manyan attajiran Sudan. Hakan yasa koda ta taso ta tsayu akan kasuwanci kamar yanda taga iyayenta na yi wanda tun tana yi a cikin gida har ta shahara, ita ce mace ta farko a yankinsu da ta buɗe kasuwa mai suna Suq Rania da taimakon mahaifinta wanda a hankali ta bunƙasata da shaguna ta zuba kayayyakin kasuwanci na kayan gida da kuma wanda ake shigowa da su daga waje. A hankali ta fara bunƙasa har mutane suka riƙa zuwa suna sayen wuri suna buga rumfuna suma suna kasa nasu kayayyaki wanda ita a lokacin ta shahara sosai. A hankali kasuwar tana ƙara suna tana ƙara Faɗaɗa har ta yi shura a Sudan wanda har yanzu akwai kasuwar ta nan a Oumdurman ana ci gaba da kasuwanci a cikinta."
"Shi kuma Mahaifinka a wannan lokacin, shima mutum ne mai jimirin neman na kansa, ƙasashe yake zuwa a wannan lokacin yana saro kaya idan ya saida a Kasuwar Kano, sai ya dawo gida yaga iyayensa ya yi mana sayayya sannan ya juya ya koma a haka har Allah ya jefa shi Sudan inda ya sayi kayan abinci, yaji da sauran abubuwan da basu da shi ya tafi dasu Suq Rania. Yana zuwa aka kaishi Ofishin tattaunawa kan musayar kaya wanda suka ce ba za'a yi komai ba sai dai idan ya ga shugabar su. Sai da ya kwana uku cikin na huɗu sannan ya samu ganinta."
"Ya yi mamaki ganinta Mace budurwa kuma mai ƙananun shekaru ace ita ce ke da wannan Kasuwar. Bayan ya gama gabatar mata da abinda ya kawo shi ba ɓata lokaci ta amince ta bashi rukunin kaya masu yawa daga cikin kowane nau'inda ya buƙata. Bayan an gama suka ƙulla yarjejeniya akan cewa idan ya sayar zai dawo mata da kuɗinda tayi masa ƙarin kaya da kuma ribar ta da zai bata domin kayanta da ta bashi sun ninka waɗanɗa ya zo da su da yawa."
"To bayan ya dawo Nigeria sai da ya shafe shekara ɗaya cif sannan ya juya ya koma mata da kuɗin ta da kuma ɗimbin alherin da aka samu. Jindaɗin gaskiyarsa da amanar da ya nuna yasa ta kai shi wurin iyayenta suka gaisa tasa aka bashi wurin kwana ya kwana biyu sannan ta sake bashi wasu kayan wanda a wannan karon bai fi wata biyar ba ya koma mata cike da alfaharin yin nasara. A hankali suka ƙulla soyyaya da kasuwanci wanda har mahaifinmu a lokacin ya so ya nuna rashin amincewarsa sai daga baya ya samu aka shawo kansa ya yarda ya shirya da wasu en uwa aka tafi aka nema masa aurenta....Wannan hoton guda da kake gani...ranar ɗaurin auren ne, gani nan a ciki, ga mahaifinmu ga Mahaifinka sannan wannan da kake gani na gefen Malam shi ne mahaifinta wato kakan ka na wurin uwa sai ƙaninta Mu'aƙƙib ga shi nan a gefena. Auren ya kasance na alfarma wanda aka haɗa al'adar ƙasar Sudan da kuma tamu ta Hausawa. Bayan an gama bukin muka tattaro harda ita muka dawo Nigeria inda suka ci gaba da gudanar harkokin kasuwancinta ta hanyar wakilinta, wato mahaifinka da saƙonni daga uwayenta da en uwanta."
" Hajiya Rania ta rayu da mahaifinka tsawon shekaru biyar wanda sai a shekara ta shida ne aka haife ka kuma a ranar da ka zo duniya, a ranar ta amsa kiran Mahaliccinta..."
Yana wani irin kuka tamkar wani ƙaramin yaro ya kalli Baba Ustaz ɗin a raunane ya ce.
"A lokacin da ta rasu ɗin...iyayenta ba su zo ba ne?? Miyasa na rayu ba tare da na san su ba?"
Jinjina kai Baba Ustaz ya yi yana kallon sa ya ce.
"Sun zo mana! Sai dai koda suka iso an riga an kawar da ita, bayan an gama gaisuwa an gama jimami sai mahaifiyarta da ƙanwarta suka ce suna so a ba su kai su tafi da kai amma sai Tsohuwar mu da mahaifinka suka tsaya kai da fata suka ce lallai sune waɗanda za su riƙeka. Hakan yasa dole ba su da yanda za su yi suka barka. To a wannan lokacin renonka sai ya dawo hannun mahaifiyar ta mu wanda sai daga baya ne ya auro Hajiya Batula, daga nan kuma ka koma hannunta. Haƙiƙa ta nuna maka so, son da ko mahaifiyarda ta haife ka iya ƙaunar da za ta nuna maka kenan, a hannunta kayi wayau ka girma, a hannun ta ka samu tarbiyya, domin tunda ta auri mahaifinka kai kaɗai ne ke gaban su basu samu wata haihuwar ba sai da ka shekara goma sha biyu a duniya sannan suka haifi Labiba....a yanda ta nuna maka so babu wanda ya kawo cewa za ta iya cutar da kai Muhammad, kuma sanin cewa suna zuwa da kai Sudan babu wanda ya taɓa kawowa cewa wai basu taɓa sanar da kai dangin mahaifiyarka ba. Sai yanzu ne da abu yazo a haka take sanar min da bakinta cewa ai ita ce ta ƙulla makircin da ta sanar wa dangin mahaifiyar taka cewa ka mutu kaima baka duniyar...."
Wani irin nauyi ne ya ji ya ƙara tasowa ya danne masa ƙahon zuciyarsa akan mamaki da al'ajabin hali irin na Hajiyarsu. Hannayensa ya kai ya dafe kansa da ke masa wata irin barazana kamar zai rabu gida biyu tsabar yanda ya ji saukar wannan mummunar maganar da ko a mafarkin sa bai taɓa kawo wa cewa Hajiya za ta iya yi masa haka ba.
Daman gabaɗaya jikin sa baya masa daɗi tun daren jiya yanzu kuma ga wannan mugun labari da ya riskesa bagatatan.
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu wanda babu abinda suke idan ba kuka ba. A hankali Emraan ya sauko ya dafa ƙafar Yayan na su wanda ya kife kai a tafin hannunsa yana tsiyayar da ruwan hawayen baƙin ciki. Cikin rashin kuzari murya a raunane ya ce.
"Yaya! A faɗin duniyar nan bani da wata kalma guda wacce zan iya amfani da ita wajen furtawa da har ta isa ta zamomin tsani ko yin nasarar tausasa zuciyarka akan wannan kuskuren da Hajiya ta aikata maka...amma ina so ka sani, mu ɗin nan mun rayu mun kuma ta so a matsayin tsintsiya mai maɗauri guda ɗaya...Wanda idan har abin dariya ya zo mana to tare zamu dara, idan kuma abin kuka ya zo mana still a tare zamu koka. Saboda haka, dan Allah kada ka riƙe abinda bamu muka aikata ba, ƙwarin gwiwarka ita ce tamu, idan ka shiga damuwa sai mun fi ka shiga damuwar sau dubu. Ita ɗin da ta zaɓi ta cutar damu wace ribar ta samu? Babu! I'm very sure cewa duk irin halin da muke ciki a yanzu na baƙin ciki da damuwa ta fi mu domin kunyar duniyar nan kaɗai ta isa ta hana mata sukuni...akan abun duniya...Wanda babu abin da ta nema ta rasa za ta zaɓi ta cutar da maraya..."
" Shihhh!"
Abun da ya faɗa kenan tare da kai hannu ya ɗora yatsarsa akan lips ɗin shi alamar yayi shiru.
Bayan ya haɗiye sauran maganar sa ya jinjina masa kai tare da ƙuresa da idanuwansa da suka canja launi sosai, murya cike da nuna mazantaka, ya ce.
" Kai! Kada fa ka manta...ita ɗin Uwa ce Mahaifiya mai daraja...akan kuskurenta ɗaya...ba shi zai sa ka nemi tsallake iyakar ka ba...dukkanmu ajizai ne wanda babu wanda yafi ƙarfin aikata kuskure a cikinmu. Saboda haka kowa ya hutar da zuciyarsa komai ya wuce dan Allah...Ni ta yiwa, kuma na yafe mata...Allah ya yafe mana baki ɗaya.."
Girgiza kai Baba ya yi cike da jin wani sabon tausayinsa ya ce.
" Allah sarki! Allah ya ƙara maka albarka, Allah ya ji ƙan iyayenka ya gafarta musu kusakuransu..."
"Amin Baba...."
Daga haka ya waiga ya kalle su ɗaya bayan ɗaya da wani murmushin ƙarfin halin da ya ƙirƙiro ya ɗora akan fuskarsa ya ce.
"My Peace...Nadeen Connel...Hairin Daddy..."
Tasowa Hairi ta yi ta zauna a gefen sa tare da ɗora kanta akan shoulder ɗinsa cike da kewa ta ce.
"I miss you so much Daddy...Zuciyata ta karye fiye da zato..."
A hankali ya kai hannunsa yana share mata hawayenta cike da nuna kulawa ya ce.
"I miss you too Uwar alheri...in sha Allah komai ya wuce."
Ɗagowa Labiba ta yi fuska cike da murmushin da ta jima bata yi kalar sa ba ta ce.
"Yayanmu ina Beenafah.?"
Waigowa ya yi ya kalle ta kai tsaye yace.
"Tana ciki tana bacci."
Sanin cewa safiya ce yanzu, hakan sai baisa suka kawo komai a ransu ba.
Kallon Baba ya yi ya ce.
"Baba yaushe ne kaga ya kamata mu tafi Oumdurman?"
Miƙewa Baba ya yi tare da faɗin.
"Duk san da ka shirya MUHAMMAD, ni a shirye nake....yanzu bari na shiga na ɗan huta."
Baba na wucewa suka ci gaba da tattaunawa. Fira sosai suka yi har kusan sha biyu saura na rana sannan ya miƙe yace su je su huta su ci abinci.
Koda ya dawo ɗakin still baccina kawai nake shaƙa hankali kwance domin tsayin daren ranar ba wani baccin kirki na yi ba, ina nan ba tare da na san budirin da suke sha ba.
Ya jima a zaune yana kallon fuskata sannan daga ƙarshe ya janyo ƙafata a hankali ya saka yatsansa yana shafa tafin ƙafar tawa.
A hankali na shiga buɗe idanuna lokaci ɗaya kuma ina janye ƙafata na kallesa a lumshe na yi murmushi kamar yanda naga shima ya yi min.
"Bibi...jikin ne har yanzu?"
Girgiza kaina na yi ina ƙara lumshe idanuwana na ce.
"Alhamdulillah. Zafin ya rage sosai..."
Hannu ya kai ya shafo fuskata zuwa idanuna ya ce.
"Still idanun nan sunƙi su rage kumburin da suka yi...Gaskiya zuciyata ta karye..."
"Hmm!"
Abin da kawai nace kenan tare da kawar da kaina gefe.
"Tashi muje muyi wanka.."
'ƴar dariya ce ta suɓuce min ba tare da na shirya ba, a raina ko faɗin nike ba da ni ba sa lallen Kaza. Ni ɗin zan shiga Wanka da kai? To mu kalli juna yaya kenan..?
"Bibi.."
Ya ambata yana mai kawo fuskarsa saitin tawa, jin hakan yasa na ƙara ƙudundunewa na ce.
"Uh uhm! Ni dai ka je ka fito ba zan iya ba..."
Wucewa ya yi yaje yayo wankan ya fito sannan na sauko da ƙyar na lallaɓa na shige toilet ɗin a daddafe.
Ba na wani jin alamar zazzaɓi ko wani abu, kawai dai ƙafafuna ne suka min nauyi da kuma zafin da ƙasa na ke min wanda shima ba sosai ɗinnan ba amma kuma bana iya haɗe ƙafafuna da kyau idan zan yi tafiya.
Tun da na sauko har na shige toilet ɗin kallona yake yana ƙara jin abin a ransa yan da nake tafiya da kuma yanayin fuskata da ta koɗe fes tsabar yan da nasha kuka.
Ko yanxu sai da na jima a toilet ɗin, domin sai da na ƙara gasa wurin da ruwan ɗumi wanda na ji daɗin hakan ba kaɗan ba, because na ƙara samun salama ba kamar yanda na shigo ba.
Koda na fito na tarar ya kawo mana abinci da kansa bayan ya shirya cikin wani 3quater da Tshirt wanda suka ƙara fito min da tsantsar kyaunsa da nake ƙara gani.
Tare ya tayani na shirya, bayan na gama gyara gashin kaina da kanshi ya karɓi ribbons ɗin yace na faɗi yanda zai min domin ya cika mini alƙawarinsa da ya ɗauka. Ina dariya na nuna masa ya yi sannan daga ƙarshe na kwance na sake kamawa da kyau na naɗiɗiyeshi wuri ɗaya.
Kallonsa na yi ta cikin mirror na ce.
"Yau ba za ka fita ba ne.??"
Hannayensa yakai ya zagayeni yana murmushi yace.
"Mi kika gani Bibina..."
"Uhm! Naga ka yi wannan shigar ne.."
"Da me kuma?"
Ina wani murmushi na jinjina kaina tare da ƙara Kallonsa ta mudubin na ce.
"And ka yi kyau sosai..."
Juyoni ya yi muna fuskantar juna ya saƙala hannun sa da kyau ya riƙo kwankwasona ya kai lips ɗinsa a hankali akan nawa ya fara kissing ɗina...
Jin abin na neman zauce tunanina yasa a tsorace na ɗan tura shi baya na ce.
"Uh uhm! Dan Allah ka bari..."
Murmushi ya yi yana ƙara kawo fuskarsa saitin ta wa yace.
"Kin tsorata ne?? Is just a kiss fa!"
Hannunsa na ja ina faɗin.
"Muje muci abinci, gwanda ni nasha Tea kai kuwa tun daren jiya bakaci komai ba.."
Abincin muke ci amma gabaɗaya yau yanayin tsokana yake ji har muka gama. Bayan mun gama muka yi sallar azahar sannan ya zaɓomin kaya na musamman yace min na shirya mu sauka ƙasa.
Wani irin freezing nayi naja na tsaya ganin su Aunty Labiba zaune a parlour a lokacin da banyi tsammani ba. Hairi na wani irin blushing ta rugo da gudu ta rungumeni tana faɗin.
"Mummyn Daddy.."
********
Gefen su Mummy kuwa, Aunty Aysha da ƙyar ta yi nasarar shawo kan Alhaji Baba da Uncle Isma'ila suka ce za su zo washe gari.
Suna nan har sai da aka fito da ita zuwa wani ɗakin sannan suka ɗunguma zuwa can amma har yanzu bata farfaɗo ba.
Kallon Husaina Mummy ta yi jiki a sanyaye ta ce.
"Husaina ki je gida ki dafa mana abinci da ruwan zafi kafin ta farfaɗo, idan kin kambala sai ki fara biyawa ki kaiwa su Humaida sannan ki kawo mana nan, zuwa dare ke Aysha sai ki wuce can wurin Alhajin ki kwana tare da ita...."
Zumbur ta miƙe hankalinta a tashe tana faɗin.
" Innalillahi! Mota! Mommota tana can hannun wani.. "
Daga haka ta fito da gudu tayo harabar gate ɗin asibitin a gigice tana addu'ar Allah yasa bai mayaudari bane ta haɗu da shi.
Yana hangota ya fito motar sa ransa a matuƙar ɓace, tana isowa ya jefa mata mukullin motar a masife ya ce.
"Ke! An faɗa miki bana da aikin yi ne da zan zauna yi miki gadin mota ko me? Ni za ki mayar shashasha ki shige ki bar ni nan kamar wani kayan wanki. Kin san wanene ni?"
Jin yanda yake masifa yasa ta sulalowa da ruwan hawaye ta ce.
"Dan Allah ka yi haƙuri..."
Wani guntun tsaki yaja tare da juyawa ya shige motar sa yace Miftab yaja su tafi.
Jiki sanyaye ta shiga motar ta zauna tare da kifa kanta a kan starring motar tana jin taratsin da yayi mata yana yawo a ƙwaƙwalwarta. Bayan ta ɗauki tsawon lokaci tana tunani ƙarshe ta kunna motar ta wuce ganin wankin hula na neman ya kaita dare.
Washegari sai wuraren ƙarfe biyu na rana su Alhaji Baba suka iso wanda a lokacin Salman ya jima da isowa.
Bayan Alhaji Baba ya ƙara natsawa ya zauna ya saurari bayanin komai da kyau wanda Asyha da Husaina suka feɗe masa biri har wutsiya sannan daga baya ya kalli Mummy wacce ke ta keta uban kuka yace.
"Ni duk wannan kukan naki ko kaɗan ban kawo shi a kaina ba Zaliha...haƙƙin marayu! Matar da ba ta ji ba bata gani ba kuka cutar da Ita miye ribar ku? Wallahi tunda har kuka ce wannan hanyar kuka zaɓa to fa masifu yanzu kuka fara gani..."
Cikin gunjin kuka ta ƙara marairaice murya ta ce.
" wallahi na tuba Baba...wannan masifar da muka janyowa kanmu tafi ƙarfinmu...dan Allah ka taimaka..."
"Wallahi darajar waɗannan 'ƴa' ƴan naki kawai kika ci,amma da ba dan su ba da ko dafaki ɗanye nama za'a yi sai dai a dafaki.."
Nan suka ƙara tattaunawa da kuma yanke shawarar tafiya Lagos wurin belin Hafiz.
Bayan su Baba sun fito ta biyo baya su domin ta ƙaro musu ruwa kwatsam ta hangosa tsaye ya jingina jikin motar sa yana Kallonta.
Ɗan ƙara ware idonta tayi tare da murza su a hankali tunanin ko dai gizo ne yake mata ba shi ɗin bane.
"Miye kika tsaya kallo? ko na koma ne?"
matso wa tayi tare da dire carton ɗin ruwan gorar da ta ɗauko cike da jin daɗin sake ganin sa da tayi tacce.
"Welcome!"
Jinjina kansa ya yi yana mai ƙure Kallonta ya ce.
"Ya mai jikin?"
"Alhamdulillah! Ta samu sauƙi."
"I...I'm sorry for yesterday...abun ne ya bani haushi that's why I react that way...suna na Fahil Kabeer Abba.."
Jinjina kanta ta yi tana murmushi tace.
"Husaina Mudassir Wazeer..."
Da ɗan alamun mamaki ya kalle ta ya ce.
"Thesame family with Late Dr. Bello Wazeer?
Da sauri ta jinjina kanta tana ƙara Faɗaɗa murmushinta ta ce.
" Eh."
Wayarsa ƙarama ya miƙa mata yace ta saka mishi Numbernta. Bayan ta saka ya Kalleta yana jinjina kai ya ce.
" Ƙila nafi shekara biyar ban taka ƙafata asibiti ba. Amma ta dalilin ki lokaci ɗaya yasa na zo har sau biyu. Allah ya ƙara mata lafiya."
"Amin. Thank you."
Murmushi ya yi mata tare da jinjina kansa sannan ya juya ya shige motar sa ya wuce.
Ta jima tsaye tana Kallonsa tana ta wani blushing har sai da ya ɓacewa ganinta sannan Daga ƙarshe ta duƙa ta ɗauki ruwanta ta shige.
Duk yanda su Mummy ke ɗaukar al'amarin Hafiz ya wuce nan domin wani ne wanda ya fisu ƙarfin iko ya riƙe wuta a wannan maganar. Kuɗinda aka tana da don fitar da Daddy ƙasar Waje wurin nema masa magani ƙarshe su aka ɗauka har da ciko sannan da ƙyar aka samu aka kashe case ɗin Hafiz ɗin.
Daga baya aka sake ɗaga babban gidan su na gusau aka sayar da wasu filayen Mummyn guda uku aka samu aka haɗa kan kuɗaɗe sannan sukayi nasarar fitar da shi.
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM*
*OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 42*
"Hey! Are you sick? Naga fuskanki tayi wani iri."
Cewar Aunty Labiba tana mai ƙara tsatstsareni da ido. Murmushi na yi tare da gyaɗa mata kaina ina ƙara lafewa jikinta na ce.
"Na kwana da zazzaɓi ne Aunty Labiba, but Alhamdulillah na ji sauƙi...and ni idan ina ciwo na rasa mi yake damuna sai na yi ta kuka..."
Cike da tausayawa ta ce.
"Allah sarki! To ya jikin?"
"Alhamdulillah. Nasha magani na ji sauƙi...Yah Emraan ina wuni."
Na ambata ina mai bin sa da ido ganin yanda yake ta kallon mu muna magana.
Jinjina kai yayi ba yabo ba fallasa ya ce.
"Lafiya lau. Ya jiki?"
"Alhamdulillah. Ina Aunty Ziza?"
"She's fine."
Haka na bisu ɗaya bayan ɗaya muka gaisa dasu cike da mutuntawa wanda na lura dai tun da na zuro ƙafa na shigo suke min wani kallo tamkar waɗanda suka ga wata sabuwar halitta, hakan sai da ya saka na ji na tsargu. Shi ma Ya Mohaa ɗin tun da muka shigo ya samu wuri ya zauna babu abin da yake sai aikin murmushi musamman da yaga irin yanda suka tarbeni suna nuna min kulawa.
Hairi kam kasa daurewa tayi, hakan yasa ta taso ta kama hannuna tana wani irin murmushi tana kallon ƙwayar idona ta ce.
"Kinga muna ta kallon ki ko Preety? Wallahi ba komai bane tsabar farin ciki ne. Ashe wai akwai watarana irin wannan da za'a wayi gari ya kasance matar Daddy za ta zo cikin gidannan ta tsaya a gaban mu haka..Alhamdulillah ya Rabb! Shi ne ka ɗai abinda zamu ce. Ki sani,wallahy Kina da wata ƙima da girma a idon mu Beenafah. Yanda kika taimaki Yayanmu kika zama sanadin yaye duhu da damuwa da kuma ƙuncin da yake tare da shi tsawon lokaci, kema muna miki addu'ar Allah ya ninka miki alherin da yafi wanda kika masa..."
Hawaye Aunty Labiba ta share tare da jinjina kanta tana wani murmushi tace.
" Bari kawai Hairi! Komai a duniya yana da dalili yana da kuma sanadi. A duk lokacin da Allah ya baka aron dama da lokaci, to kayi aiki da ita da kyau yanda ya dace kada ka tsaya shirme da shiririta ka bar wannan damar ta tafi a banza. A lokacin da Beenafah ta zo gareni ban taɓa kawo komai a raina ba, kawai ji nayi har cikin zuciyata ina so in taimaketa saboda Allah...."
Nadeeyah ta gyaɗa kanta alamar gamsuwa da kalaman Labibar ta ce.
" Mafi girman kuskure da ɗan Adam zai tabka a rayuwarsa idan har ya samu aron dama da lokaci shi ne wulaƙanta wanda yake ƙasa dashi. Wallahi daga lokacin da ka ɗauki girman kai da jiji da kai ka shiga rigar wulaƙanta mutane wai don ka na da wani arziki ko mulki to ka shiga uku kuma ka nemi hanyar halakar da kanka da kanka domin Allah ma da kansa yace baya son mai girman kai mai alfahari..."
"A lokacin da na yi buri da nufin aurenta ko kaɗan ban yi nufin ja baya ba, domin gani ɗaya da nayi mata sai naji cewa ta cancanta. Daga baya kuma Girmanta a idona da kuma matsayin ta sun ninku ne daga lokacin da ta tsayu a gabana a matsayin wacce ta sadaukar da kanta da rayuwarta domin ceton ɗan uwana. She make a great Woman wacce ta kai ƙololuwar girma da nagartacciyar haiba. Allah ya sanyawa wannan auren naku albarka ya baku zuri'a ɗayyaba."
Cewar Emraan yana mai kallon ɗan uwansa cike da nuna ƙwarin gwiwa.
Cikin wani irin yanayin farin ciki Yayan nasu ya jinjina kansa yana wani irin murmushi yana kallona yace.
" Amin.. Amin yah Allah."
Daga nan ya riƙo hannuna a gaban su wanda har sai da naji kunya ta kamani yana murmushi ya ce.
" Shiyasa komai a rayuwa yana da sanadi...ga shi sanadin Labiba na samu canjin rayuwa. Allah ubangiji ya ƙara ƙarfafa mana zumuncinmu ya ƙara mana haƙuri da juna."
Nan muka wuni har dare muna fira muna ta nishaɗi tamkar wani abu bai faru ba, musamman Hairiyya wacce ta zage take ta bani labarin rayuwarsu iri-iri wanda sallah ce kaɗai ke ta da mu. Bayan mun kambala sallar isha, a tare muka yi dinner har Baba Ustaz Wanda Emraan ne kawai baya wurin ya fita wurin wata sabgar gaban sa, a wani gefen kuma sai nake tunanin kamar dai baya so yana ganina kamar hakan yana masa ba daɗi. Domin duk zaman firar da mukayi maganar sa ɗaɗɗaya ce a ciki kuma gabaɗaya ya ɗauke kallon sa daga gare ni.
Suna miƙewa nima na miƙe ina kallon Aunty Labiba na ce.
"Aunty Labiba zan kwana tare daku muci gaba da fira.."
Zaro ido tayi da sauri ta kalli direction ɗinda Yayan nasu ke zaune domin taga reaction ɗinsa, sai dai ga mamakinta koma alamar ya ji zancen da muke bai nuna ba. Ganin ta kalle shin sai nima na waiga na kalle shi amma har yanzu idonsa na kan wayarsa da alama akwai abin da yake mai muhimmanci.
"Kar ki damu, ai muna nan tare tsawon sati ɗaya har sai kin gaji damu.."
Girgiza mata kaina nayi ina dariya nace.
"Gaskiya ba zan taɓa gajiya daku ba."
"To kiyi haƙuri kije sai da safe kin ji, again kinga daman bakya jin daɗi. Allah ya bamu alheri. ."
Bayan sun shige ne na ɗan kalle sa kaɗan, har yanzu bai ɗago daga abin da yake ba, hakan yasa na wuce ciki abina tare da cire kayan jikina na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 67