Share this page
    **** Misalin ƙarfe biyu saura na rana, Mamansu Fakiha na zaune tana zuba musu girkin da ta sauke kawai sai Jafaru ya yi sallama ya shigo gidan. Ajiye serving spoon ɗinda yake hannunta ta yi cike da tashin hankali ta dafe ƙirji ta ce. "Jafaru! Lafiya? Miye yasa ka dawo? Miye ya faru?" Ɗan guntun tsaki ya ja tare da janyo kujerar tsugunno ya zauna akai yana mai yasar da ƙaramar school bag ɗinsa wacce ke ɗauke kala uku ta kayansa gefe ya kalle ta ya ce. "Ba bu abinda ya faru... Kawai dai na zo ne inji dalilin da yasa wannan Ashirun ya sayawa Beenafah waya.." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Jafaru! Kana da hankali kuwa?" Yana gunguni ƙasa-ƙasa ya ce. "To ai hakan ba daidai bane,fisabilillahi Mama kuma ace kuna gani ku bari wani ƙaton banza ya siya mata waya ya bata, wannan hanyar lalacewa ce aka biɗar mata, idan ba shi ba dan Allah Mama Ina Beenafah ina Way..." Kafin ma ya iyarda rufe bakin sa tuni ta rotsa masa Cokalin miyar da yake Cikin tukunyar gabanta a hasale tana faɗin. "Ka ci ubanka da kai da dalilin naka.." Saurin Miƙewa ya yi ya matsa gaba can nesa da ita domin Cokalin ya sauka a daidai, hakan ne ya haddasa masa jin zafi a gefen bakin shi shiyasa ya tashi ba shiri. Cikin nuna tsantsar ɓacin rai ta kalle shi taci gaba da faɗa tana cewa. " Yanzu Jafaru saboda baka san ciwon kanka ba, Alhaji ya kashe kuɗi ya saka ka a makaranta amma shi ne zaka wani ɗebo ƙafa sati ɗaya ka dawo gida akan wani dalilinka na banza na wofi? Ina ruwanka don Ashiru ya saya mata waya? Na ce ina ruwanka? Can wan can lokacin baya da ta taɓa yin wayar don ubanka kasan ma da zancen? Inda tana da niyyar lalacewa da tun can bata lalace ba... " Miƙewa tayi tare da nuna shi da yatsa ta ce. " To wallahi bari kaji in yi maka rantsuwar Musulmi.. Wallahi tallahi kar in ji kar in gani wai ka yi musu zancen wayar nan da sunan ɓacin rai,ban amince ba ka ji na faɗa maka, kuma wallahi yanda ka ɗauko ƙafa a yau ɗinnan ka zo a yau ɗin nan zaka koma ba sai gobe ba. Sannan mags Garin nan kuma; idan har ba hutu aka yi ba ban amince da ka zo shi ba. Domin baka isa ka zubar mini da mutuncina ba a wurin Alhaji ka ji na faɗa maka.. " Daga haka ta ƙwala kiran Fakiha akan ta zo taci gaba da raba abincin ita kuma ta shige ɗaki rai a matuƙar ɓace. Tsaye ya yi kawai yana mai jin wani irin tashin hankalin da bai san ma yanda zai fasalta shi ba. Wai Mama ko tasan miye yake ji akan Beenafah? Jiya sam bai samu ya runtsa ba tunda ta yi nasarar shaida masa wannan mummunar maganar.Wallahi tallahi zai iya ɗaukar mummunan mataki akan koma waye akan Beenafah. Shi kenan kawai don ya taɓa taimaka musu sai a bar shi da ita yayi ta abin da ya ga dama. Idan ba iskancin banza ba akan me zai saya mata waya to? Ya jima a tsaye tsawon lokaci yana karanta wasiƙar Jaki. Ya saƙa ya warware ya saƙa ya warware ya rasa ma tudun dafawa. Yana nan a haka sai ga babansu ya yi sallama ya shigo. Daga ganin irin kallon da yake bin shi dashi kasan cewa labari ya riga da ya gama kai masa. Cikin nuna ɓacin ransa ƙarara shima yace. "Mutumin banza mutumin ɗan magori!" Cike da fatan Allah yasa baban ya Fahimce shi a wannan maganar ya yi ƙasa da murya ya ce. "Yanzu kai ma Baba laifina za ka gani kenan? Beenafah fa amana ce a garemu bai kamata mu bar ta tana rayuwa kara zube ba a duk yanda taga dama..." "Beenafahr ce take rayuwar kara zube?? Miye ka taɓa gani ko ka taɓa ji ance tana yi wanda ba daidai ba? Ka faɗa mini shi ni kuma na yi maka alƙawarin ɗaukar mata mataki da kaina" Ƙasa ya yi da kansa ya na wani turo baki yace. "To amma dai ai wannan wayar bata kamata ba, idan ma magana yake so yayi da ita ya kira ta wayar Mama man..." "Kai.. Kai.. Dan Allah banson shirme ka ji ko! Ɗauki jakarka ja juya yanzu-yanzu ba sai anjima ba ka koma..." Wani irin shock ne ya ji ya ziyarcesa a lokaci ɗaya wanda har bai san sanda ya ɗago ya kalle shi ba yana faɗin. "Haba Baba! Dan Allah ku bari zuwa gobe..." "Wallahi yau za ka juyi ka koma Jafaru ka ji na faɗa maka. Idan kuma karatun ne baka so sai ka faɗawa Alhaji Usman ɗin ya daina asarar kuɗinsa a kanka.." "To ai ni yanzu bani da isassun kuɗinda zan iya komawa yau ɗin..." "Au! Yanzu ashe ma ba kada isassun kuɗi amma ka yi ƙunar baƙin Wake ka wanko ƙafa ka zo?" Fitowa Mama tayi daga can varender ta watso mishi dubu biyar tana faɗin. "Ga su nan ka ɗauka maza da zafi ka juya ka koma ka ji na faɗa maka....Hmm!" Ta faɗa daga ƙarshe tana mai riƙo daga cikin ƙarfen turakunda suka riƙe verander ɗin ta ci gaba da faɗin. "Aikin banza aikin wofi! Wannan ai isar baka isa bace kake nunawa. Idan har so kake ka nuna isa to ka je ka fara zama wata tsiya tukunna." Tsince kuɗin ya yi ransa na yi masa wata irin suya tamkar ya fashe haka ya ke ji. Yana gama tattare kuɗin ya ɗauki jakar sa ya fice. Hanya ya kama wanda sai da ya yi nisa sannan ya juyo kuma ya dawo, ya so ya yi zuciya ya tafi amma kuma ba zai juyawa ya koma bai ganta ba. Yana dawowa sai gani ni kuma na iso ƙofar gidan...wani irin mamaki ne ya ziyarce ni a lokaci ɗaya na wani hangame baki ina zare ido na ce. "Ya Jafaru??" Fuska ba yabo ba fallasa ya kalle ni ya ce. "Beenafah! Kin dawo?" "Miye ya dawo da kai kuma? Ba kace sai kun yi jarabawa ba?" Ga dai bikin zuwa amma babu Zanen ɗaurawa. Ga dai Beenafah yana gani amma kuma bai isa ya yi mata zancen waya ba tunda Mama ta hana, sannan uwa uba ga maganganun da Mamar ta yi masa na ƙarshe sun yi matuƙar ƙona masa zuciya. Wato ga mari ga tsinka jaka! Tuna wannan yasa ya ɗan ƙirƙiro wani murmushin dole ya ɗaura akan fuskar sa ya ce. "Wani ɗan abu ne ya kawo ni kuma ma na kambala yanzu zan juya in koma..." "To amma ko shigowa ba za ka yi ba Ya Jafaru??" Girgiza kansa ya yi ya ce. "A'a. Ni na wuce sai an jima." Tsaye nake yayin da fuskata ta cika da maɗaukakin mamaki ina kallon sa har ya ɓacewa ganina. Ajiyar zuciya na sauke tare da girgiza kaina kawai na juya na shige gida ina faɗawa Ammie cewa yanzu naga Ya Jafaru ashe ya zo har ya juya ya koma kuma. Itama da mamaki a fuskarta ta kalleni ta ce. "Jafarun?" "Ƙwarai kuwa Ammie. Wallahi na ganshi yanzu. Amma kuma har ya koma." Ɗan Jim tayi kaɗan tana nazari, sai daga baya kuma ta jinjina kai ta ce. "To wata ƙila akwai abin da ya dawo da shi, amma zan shiga gidan na ji." Da ta je gidan ta tambayi Mama, ce mata tayi wasu takardun makarantarsa ne ya manta wanda dole ana da buƙatarsu shi ne ya zo ya ɗauka ya koma.                           ****   Gefen su Hassana kuwa;Tun  bayan da su Ammar suka zo suka gansu da wata uku aka kawo kayan gaisuwa tamkar za'a buɗe wani super market. Mummy wacce ta ji kamar ta yi hauka akan tsananin farin cikin da take ciki, babu abinda take in ba alfahari ba tana ɗaga shoulder musamman da taga an ɗora kuɗi sama har 5M. Wai kuɗin gaisuwa kawai. Hakan yasa ta ƙara jaddadawa su Hassana cewa gwanda ma ta bada kai bori ya hau, domin kuwa wallahi tallahi aure tsakanin su da 'ƴa'ƴan Alhaji Mansur Anka babu fashi sai idan mutuwa ce ta shiga tsakani. Hassana tasan Mummy ta san me take iya yi hakan yasa dole ta shafawa kanta ruwa, duk cewa Aunty Aysha sa saurin en uwa sun yi lallashin duk a banza, domin kuwa ba don ta haƙura ba. Yau ma a makaranta tun da suka fito morning lecture take tare da sabon saurayinta Salman a school cafeteria. Suna zaune Husaina ta iso wurin a hankali ta yi musu sallama sannan ta tsaya akan Hassana ta ce. "What you are doing is not right Hassana..." Miƙewa ta yi cikin azama ta janyo hannunta da ƙarfi suka bar wurin, cikin nuna ɓacin ranta ta ce. "Hussy miye haka? A gaban Salman ɗin za ki fara yi mini maganganun haukar na ki??" Girgiza kai ta yi itama ranta a ɓacen tana mai nuna ta da yatsa ta ce. "Ke ce kike abin da bai kamata ba Hassana... Akan me za ki zo da maganar wani akanki amma kuma ki fara soyayya da wani! Ina jiye miki abin da ke bakya hangowa Hassana..." "Ina ruwan ki? Na ce miye abin da ya shafeki da abin da nake yi? Salman shi nake so kuma shi zan aura...Wallahi tallahi ni babu wani Ameer ɗinda zan aura..." Hannunta Husaina ta kama hankalinta a tashe ta girgiza kanta ta ce. " Please listen to me Hassy... Ka da ki bari hakan ya girmama. Mummy ba za ta amince ba... " " Dole sai ta amince? Ko kuma ita ce za ta zauna mini a gidan aurena?" Girgiza kanta Husaina ta yi still ta ce. "Hassy ina jiye miki kada..." Hanya ta nuna mata cike da hargagi tana wani girgiza mata kai alamar bata ma son maganar ta ce. "Kinga Malama dan Allah, ki wuce kije wurin abin da ya shafeki.." "Hassy! Gabaɗaya yinin yau only morning lecture kika yi attending...Tun da aka tsaida maganarki da Ameer ko sau ɗaya baki taɓa bashi lokacin ki ba, haka zai zo ya zauna ƙarshe ya kakkaɓe rigar sa ya tashi ba tare da kin kula sa ba, sannan yanzu gabaɗaya karatunki ya fara samun matsala duk ta dalilin Salman... Ina shawartar ki da kuma gargaɗin ki; kada ki bari Mummy ta gano duk wannan abubuwan da kike a bayan idonta. " Daga haka ta juya ta koma class. Mamaki take ta rasa mike damun Hassana, duk abubuwan nan da take tsawon lokaci Hussaina ba ta taɓa yi mata magana akai ba sai yau. Kuma da ace ita ce take wannan da yanzu ta daɗe da kaiwa Mummy labari. Tun da ta haɗu da Salman shikenan komai na ta ya ƙara komawa baya, bata ji bata gani idan ba Salman ba. Ita kuma tana jiye mata masifar da za ta janyowa kanta domin tasan Mummy ba ƙyale ta za ta yi ba.                        **** Tun da Hajiya ta yiwa Aunty Ziza gargaɗi akaina tun daga wannan lokacin na samu sassauci. Ba ruwanta da ni irin haka muddin dai ba wani aikin take so ba, kuma shima ba na irin takurawar nan ba kamar na da. Sai da ta cika wata uku da haihuwa a gidan cif sannan ta shirya ta koma gidanta. Hakan ya ƙara bani wata damar samun kwanciyar hankali wanda bani da wata matsala a yanzu. Shi ma Mijinta ni dai tun bayan sunan da na ganshi sau ɗaya ban sake ganin shi ba har yau. A duk lokacin da ta zo gidan ta ganni a zaune bana aikin komai, hakan ba ƙaramin baƙin ciki yake bata ba. Da wannan ta yi nasarar shawo kan Hajiya akan dole ya kamata ace na koyi girki ko don yau da gobe. Ta hakan tayi amfani da ƙarfin ikonta tasa Oga Sule ya ɗaukeni ya kai ni Ziza Eatry and more inda na duƙufa koyon girke-girke ba kama hannun yaro. Babban wurin abinci ne dake titin bypass mai sassa daban-daban da ake gabatar da abubuwa a ciki, wanda aka ƙawata shi da kayan girke-girke na zamani wanda babu abun da babu. Manyan hotunan ta ne kakkafe a babban reception ɗin, sai hoton wani daban wanda ban san wanene shi ba sannan hoton mijinta yana sanye da kaki. Ma'aikatan dake wurin kuwa, ganin Oga Sule ke kawoni akodayaushe yasa suka saki jiki dani sosai muna harakar mutunci da su yayinda na ƙara kwantar da kai ina ƙara samun ilmi. A wurin wata Aunty Subai'a ce na tambaya cewa wace ce Ziza wai? Domin ganin irin yanda take hulɗa da mutane daban-daban a wurin yana matuƙar bani mamaki. Cike da alfahari ta fara mini bayanin ta da cewa; ita ɗin ta yi karatu a ƙasar France inda ta karanci Culinary Arts a Le Cordon Bleu University. A nan ta yi degree ɗinta a fannin girke-girke, ta koyi abincin ƙasashe daban-daban tare da samun gogewa daga manyan chefs na duniya. Ziza ta kasance Mace mai baiwa ta musamman wadda Allah ya horewa hikima da fasaha a harakar girki. Bayan ta dawo ƙasarta Nigeria da taimakon Daddy Ashraf shaharren ɗan kasuwa wanda ya kasance zaman mahafinta domin tun tana 'ƴar ƙarama ya ɗauko ta ya dawo da ita hannun shi a nan Potarcourt inda a nan ne bayan ta dawo ta samu damar cike mafarkinta na buɗe babban gidan girke-girke na Ziza Eatry. A hankali ta fara suna har ta zama cikin manyan gwanayen da ake ji da su a duniyar girke-girke a Nigeria. Sannan daga baya a hankali tana ƙara girma har ta fara samun gayyata daga ƙasashen waje, Dubai, Turkey, France da Kuma Saudi Arabia inda take yawan halarta domin gabatar da gasanni da kuma shirye-shirye a fannin girki. Ta samu awards na African Female Chef Wanda aka gudanar a ƙasar Ghana, sannan ta samu award na Best traditional Cuisine Innovator a Dubai food Expo Sannan kuma da award na Taste of Excellence a Paris International food festival. A Kaduna suka haɗu da Emraan, bayan sun yi aure aka kawo ta Gusau, inda Emraan ya cika mata alƙawarinta na buɗe mata reshen ta na Ziza Eatry a nan bayan wancan dake gudana a portacourt ɗin. Har laƙani gareta akan ƙwazonta wanda ake kiranta da shi wato Queen Ziza the Flavour Master, wannan Sunan ya samo asali ne ta dalilin yadda ta iya haɗa aroma, texture da Kuma presentation na abinci gwanin burgewa akodayaushe. Suna yawan yabon halayenta na kirki da kuma son mutanen da take da shi amma kuma ni Sam ban gani ba, domin ko sau ɗaya bata nuna mini kirkinta ba sai baƙin hali da mummunar fuska wacce a duk sanda na kalle ta, to bana hango komai sai tsantsar tsanata wanda har yau na rasa dalili. Haka na ci gaba, kullum idan gari ya waye Oga Sule ko Lawan har ƙofar gidanmu suke zuwa su ɗaukeni su kaini, idan ƙarfe uku ta buga na rana su dawo dani har na tsawon wata uku. Wanda ban sani ba ko ita gani take kamar mugunta ce ta mini,bayan bata san cewa wannan abun da ta yi mini ba tayi matuƙar taimaka min  kuma har abada ba zan daina gode mata ba domin ta ƙara inganta mini rayuwata. A haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar damu yau daɗi gobe akasinta,inda yanzu na doshi tsawon shekara ta biyu ina aiki a gidan Hajiyar. A gefe ɗaya kuma ina nan ina zuwa Islamiyya, Alhamdulillah na samu na kambala sauke Al-Kur'ani kuma ina ci gaba da litattafaina. Ina nan ina ta ƙara samun gogewa a rayuwa ta gefen ƙawayena su Hafsa da kuma su Munira. Gefen Ya Jafaru kuma;yana nan sannu a hankali ya kambala aji ɗaya ya shiga aji na biyu. A kullum kwanan duniya sai ya kirani a wayar Mama sau ɗaya ya ce a kirani yana so mu gaisa,baya dawowa sai ƙarshen Semester idan ya kambala exam ko kuma idan wani wani uzuri ya ta so. Wani abun da yake ɗauremin kai kuma ya tsaya a raina shi ne, yanzu kwata-kwata ya daina matse mini kamar yanda yake yi ada. Kuma tun ranar na kira shi da wayar nan bai taɓa kirana da ita ba, idan ma na kira shi baya ɗagawa sai dai ya kirani ta wayar Mama muyi magana wanda a yanzu na daina kiran sa ma da ita, kuma ko ya zo bai taɓa cewa yana so ya ga wayar ba. Sai dai maganarsa guda ce kullum, na kula da kaina kamar yanda yake kulawa da kansa. Gefen Yaya Ashiru shima yana Kano abinsa, amma dai shi baya shafe cikakken wata ɗaya bai zo ba, sai dai kuma, baya wuce kwana ɗaya ko biyu yake juyawa ya koma, shiyasa na ƙara samun kusanci da kuma shaƙuwa da shi sosai. Dokar Ammie tana nan wacce ta sanya mini akan waya, bana fita ko'ina da wayar nan, amfaninta a gareni kawai sai idan ina gida, wanda shima daga zaran Yaya Ashiru ya kirani sau ɗaya da magariba, baya ƙara kirana sai kuma wata goben amma kuma muna ɗaukar lokaci akan wayar muna magana wacce duk yawanci hirarrakin duniya ne. Gefen Daddy kuwa, babu wani labari tsakaninmu da su, bamu da nasu haka zalika suma ba su da namu labarin. Komai tamkar a mafarki haka yake tafiya tsakaninmu da su Daddy tamkar bamu rayu da su ba. Alhamdulillah! Ubangiji duk inda yake so yaga bawansa a nan zai barshi, duk abinda ya rubuta maka ya nufeka za ka samu to tabbas babu wanda ya isa ya hana hakan faruwa. Ga shi dai muna raye kuma cikin rayuwa mai daɗi ba tare da su ba. Idan ka dogara ga Allah haƙiƙa ya isar maka da komai. Uncle Isma'ila sau biyu ya taɓa zuwa gidanmu, ganin gidan yana nan tsab hakan yasa ya ɗauke ƙafarsa, kuma ni duk zuwa biyun da yayi ban taɓa haɗuwa da shi ba, sai dai daga baya Ammie ta bani labari. Rayuwa tayi mana komai Alhamdulillah, muci mai kyau musha kyau sannan mu gabatar da sauran buƙatocin rayuwa duk a cikin inuwar Aunty Labiba da kuma Ahlinta wanda babu komai tsakaninmu da su sai fatan alheri.                           ****   Misalin ƙarfe biyar na yammar ranar Talata. Ashiru yana zaune a bakin ƙofar ɗakin Ayya suna magana kwatsam sai ga Yaya Nura ya shigo. Wata irin zabura Ashirun ya yi ya miƙe tsaye yana wani rarraba ido alamun rashin gaskiya. Kallon shi Yaya Nuran ya yi calmly yana girgiza kai ya ce. "A'a! Zauna abin ka, ni indon ganina ma bari wata razana." Wuri ya samu ya zauna yayinda har yanzu Ashirun yake a tsaye. kallon Ayya ya yi suka gaisa sannan ya tambayeta Umma ta ce ta fita anguwa. Ɗaya daga cikin ƙannen na su ne wata ta zo ta ɗauki jakar Yaya Nuran ta shigar masa da ita ɗakin Umma daga nan shi kuma ya miƙe ya ce idan sun yi sallar Isha yana so su zo a zauna yana da maganar da yake so su tattauna akai. Tun da Ashiru yaga shigowar Yaya Nura bai sake samun nutsuwa ba, musamman idan Umma ta dawo ya faɗa mata cewa sai da yace masa kar yazo amma ya ƙetare maganar sa ya yi tahowar sa. Sannan yanzu bai san wane kalar hukuncin Yaya Nuran zai yanke masa ba, domin abin da har ya ɗauko shi a wannan lokacin daga Kano ya kawo shi Gusau to tabbas abin nan ba ƙara mi ne ba. Da wannan tunane-tunanen ne ya samu jiki sanyaye ya gabatar da sallar Magriba da Isha sannan ya tattaro ya dawo gidan. Bai ƙara shiga tashin hankali ba sai da yaga Yaya Kamal da kuma Aunties ɗinsa guda biyu, Nasma da kuma Nusaiba. A bakin ƙofar ɗakin Ummar ya tsaya ya togace domin ya kasa ƙarasowa ciki. Wani kallon Umma ta jefa mishi sannan ta ce. "Ai sai ka ƙara so ciki kai ake jira mutumin banza kawai!" A hankali ya saɗaɗo ya zauna a gefen Nusaiba tare da faɗin ina wuninku. Babu wanda ya amsa daga cikinsu tsawon lokaci sannan daga ƙarshe Yaya Nura ya sauke wata ajiyar zuciya ya ce. "To! Alhamdulillah! Ni dai maƙasudin tara ku a nan shi ne; Ashiru dai ƙanina ne kamar yanda yake a gare ku kuma, bani da wani buri a raina face inga na gina shi kamar yanda nima na ginu. Shiyasa na tsaya na ɓata lokacina da kuma kuɗina wurin ganin ya samu ilmi ya kuma samu hanyar dogaro da kansa. Mutumin kirki ne, domin gaskiya idan na ce ga kuskurensa da ya taɓa yi wurin saɓa mini to na shiga haƙƙinsa. Yana nan yana karatunsa lafiya lau ba wata matsala kasuwancinsa ma haka, komai na tafiya yanda ya kamata kuma ana kan samun alheri babu laifi,to amma yanzu matsala ɗaya ce wacce ku kanku nasan kun san da ita kawai dai kun yi shiru kun zuba masa ido ne bama kamar ke Umma da Ayya. Tun da yarinyar nan ta dawo rayuwar sa shikenan ya rasa sukunin rayuwa, bai da wani aiki sai nata bai da wata magana sai tata, yanzu a wata sai ya zo Gusau sau biyu ko sau uku kullum cikin zarya yake akan ƙarfe, Maman Nabil har da magana ta yi masa kwanaki akan ya sararawa hanya amma bai saurareta ba, sannan ni kaina a wannan karon sai da na faɗa masa cewa kada ya zo, amma haka ya shure maganata ya ɗauko ƙafa ya dawo... " Cike da jin haushi Yaya Kamal ya maka masa wata uwar harara ya ce. " To tun da har ya nuna ba'a isa da shi ba ai shikenan, sai yaje ya yi ta abunda ya ga ya fiye mish... " Girgiza kai Yaya Nura ya yi ya ce. " A'a, duk batun hakan bai taso ba. Ku kanku kun sani, an yi faɗan an yi mi amma kuma bata sauya zani ba..." Kallon sa Umma ta yi ta ce. " Nura ka daina cewa wai ba zai canza ba! shi ne ya haifi kansa ko kuma haifar sa akayi da zai ce yafi ƙarfin mutane... " " To ai ni Umma ina da wata shawara wacce nake tunani da kuma ganin ita ce maslaha a wannan al'amarin. Kawai aje a nema masa aurenta. Idan akayi auren sai ya tattara ta su dawo Kano gabaɗaya kinga shikenan an huta an yi maganin abun... " Wata irin zabura Ayya ta yi ta ce. " Kai Ina! Gaskiya Nura wannan magana ba za ta yiyu ba, mutanen nan fa ni har yanzu ban yarda da su ba, hatta kuɗin da Uwar ta ta kawo wai a siyawa Zulfa Tsintsiya suna nan na maƙale su a kusurwar ɗakina... " Girgiza Kai Nasmatu ta yi tana faɗin. "Haba Ayya! Dan Allah ki daina wannan maganar. Hasashen fa da kike akan mutanen nan sam ba gaskiya ba ne, tashi suka yi daga gidan da suke suka canza wuri ba tare da kowa yasan inda ɗan uwansa yake ba. Sannan tun da ya samo inda suke har yau kin ƙara jin cewa sun ɓata?.....Ni dai Yaya Nura Ina goyon bayan wannan maganar kawai a nema masa aurenta kowa ma ya huta, domin zaryar hanyar nan da yake ta yi yawa..." Jinjina kai Yaya Kamal Ya yi, ya ce. " Tabbas nima na goyi da baya, tsawon lokacin nan da aka share yana bibiyarta, komai za'a yi ba zai daina ba, saboda haka a saka lokaci kawai mu shirya muje a nema masa aurenta." Nusaiba itama ta ce. " Ni ma na amince da wannan shawarar, kuma wallahi Beenafah yarinya ce mai nutsuwa da hankali, daga ita har mahaifiyarta suna da kirki sosai, ko haihuwar nan da na yi kwanakin baya sai da suka zo mini barka." Ido ya juya ya kalli Umma ya ce. "Umma ke baki ce komai ba??" Girgiza kai ta yi ta ce. "Bani da matsala domin ba ni ce zan zauna masa zaman auren sa ba, Allah yasa alheri yasa albarka." "Ke fa Ayya?" "Hmm!

Chapter 19 of 67