Share this page
ta daban na ɗauke ki zuwa ƙasar Yemen na ƙwanƙwasa gidansa na bashi ke...." Kuka ne mai tsananin ƙarfi ya sarƙesa tsabar yanda yake jin abin na dukan zuciyar sa. Tsawon shekaru ya kasa mantawa, ya kasa manta ranar da ta saka ƙafa ta baro shi. Ya kasa manta ranar da ya ɗauketa da hannun sa ya kaita gidan sheikh.. Cikin wani irin kukan tausayinsu na kalle shi na ce. "To amma miyasa ka ɓadda kama Kaka? Miyasa sai a shigar mahaukata kake bayyana a gareta? Shin idan ka bayyanawa Sheikh kanka kana gani ba zai karɓeta ba? Kasan yanda mahaifiyata ta cutu kuwa? Kasan tsayin darare da ranakun da ta ɗauka tana kukan rashin iyaye? wanda kullum take cikin waswasi da ƙuncin cewa shin ta ma wace hanya aka same ta?" Hannayen shi ya haɗe wuri ɗaya yana mai kallona alamar roƙo ya ce. " Ban san mafita a wannan lokacin. Ni ɗin na kasance sannannen mutum a faɗin Qatar, abun kunya ne a gare ni abun da Sumaiha ta aikata mini sannan ace hatta dangina sun kasa riƙe mini 'ƴata. Sannan zan yi matuƙar baƙin ciki da takaici idan har watarana Sumaiha ta ji labarin inda Nana Hauwa take, domin idan taje ta ɗauketa ba tare da sani na ba, idan hakan ta kasance yana nuna cewa na faɗi, kuma hakan ya tabbata cewa tayi nasara a kaina. Har na koma ga Allah ba zan daina nadamar auren Sumaiha ba, domin ta nakasa min rayuwa da ta 'ƴa' ƴana...bata rasa komai ba,domin koda ta aureni ni ɗin ina da aiki kuma ina kasuwanci. Babu abinda ta nema ta rasa, lokuta dama na so ace mun samu fahimtar juna ta fahimci wane irin mutum ne ni. Amma ba ta yi hakan ba, ita fa a rayuwa...ba dole sai ka samu abinda kake so ba ɗari bisa ɗari. Rayuwar wannan namiji daban ta wannan daban. Abinda mijin ki zai jure ba lallai  mijin wata ya jure shi ba, ɗabi'unki da wasu bururruka naki na rayuwa, idan sun sha bamban da ra'ayin mijinki ya ce baya so, matuƙar ba Allah yace ki saɓawa ba to ki yi haƙuri ki yi biyayya. Tun a wancan lokacin na faɗa miki cewa ni banga wani abu mai wahala a nan ba, zamu iya haɗa kai mu cim ma duk wani mafarki naki ba tare da kin saɓa ra'ayi na ba, amma ba ki saurareni ba Sumaiha, kin rusa farin ciki na, kin mayarda mahaifiyata ba kowa ba. kin raba kan 'ƴa' ƴana. Kalli idanuwana ki gani....akan baƙin ciki da takaicin halin da kika saka ni da kuma abinda na aikatawa Nana Hauwa sai da suka kusa makancewa tsabar kuka da..." Sai yanzu Nana Maryam wato mahaifiyar Noura ta jinjina kai cike da al'ajabi tana kallon mahaifiyar ta su tana kuka ta ce. " Daman abin da kike ta ɓoye mini kenan tsawon shekaru Ammah? Kema Jadda ko?" Sai kuma ta juya gun mahaifin na su shima ta shiga kallon shi da hawaye a idonta ta ce. "Kai ma Abiyh abunda ka ɓoye mini kenan duk roƙonka da nake ta yi tsawon shekaru??" Kallonta Ammie ta yi ta ce. "To amma ke taya kika koma gare shi? Bayan kuma dake ta wuto Sudan ɗin." "Bayan nayi nasarar haddace Alƙur'ani. Na kambala secondary school, wata ƙawata ta taɓa yi mini gorin mahaifi...da wannan dalilin na turke Ammah na ce sai ta kai ni gun mahaifina, idan kuma ya mutu ta faɗa mini in san halin da nake ciki. Bayan na kwana na wuni ina mata bori ita da su Jadda...nan ta shirya mini suka mini visa da komai ta ɗorani a jirgi da address...ta hakan na isa gun mahaifina wanda ya kwana yana kuka da ya ganni. Sam ban samu karɓuwa daga danginsa ba sai kaɗan daga cikin su ne suka karɓeni. Ban sha wata wahalar su ba wanda ban sani ba ko don na je da girmana ne oho! Mahaifina ya nuna mini soyayyar da naji cewa na yi nadamar rashin kasancewata tare da shi tun farkon fari. daman na ɗauke har takardun wanda Ammah ba ta sani ba,hakan yasa ba jimawa ya nema mini makaranta na fara, iyaka idan na ƙarasa semester ɗaya ya mini aure da wani yaron abokinsa, mai suna Abdulmajeed. Na yi mamaki da babu wani labari ko ta mafarki akan Ammah tunda naje, idan na tambayeshi sai yace za ta dawo itama watarana. Sai da na haifi Noura sannan na zo Oumdurman da ƙyar wanda bai amince na zo nika ɗai ba sai tare da mijina, ya ce kuma ya zauna a nan na gama duk kwanakin da zan yi mu koma a tare..Abiyh baya bari ko 'ƴa' ƴana su zo Oumdurman su zauna sam bai amince ba. Na bi duk hanyar da zan bi domin na kamo kan matsalar daga shi har Ammah babu wanda ya bani haɗin kai...yanzu ina amfanin hakan? Na ce ina amfanin hakan da kuka salwantar da rayuwarmu akan ra'ayoyinku na son zuciya musamman ma ke Ammah..!!!" A hankali na je na rungume mahaifiyar Noura domin yanda take kuka na tashin hankali ba ƙaramin tausayi ta bani ba...kai dukkan su babu wanda ba abin tausayi ba musamman Abiyh wanda shi ne ma wanda ya fi kowa cutuwa. Maimakon Ammie taga laifin Mahaifinta? Sam ba hakan ta faru ba, laifin gabaɗaya ta ɗauka ta ɗora akan mahaifiyarta da dangin ta ne wanda ta yi mata wani kallon tana faɗin. "Ke ce wacce kika haifeni...sam shekaruna da tunanina ba su kai na ki ba. Amma dai na san cewa, muddin dai uwa ta amsa sunanta na uwa! To tabbas rayuwar 'ƴa' ƴanta musamman idan suka kasance mata, rayuwar 'ƴa' ƴanta ya kamata ace ta fara ɗauka a matsayin babbar matsalar rayuwarta, wacce za ta iya haƙura da komai matuƙar ba kaucewa Allah ba ne aka ce za'a ɗora ta a kai. Kin zaɓi ra'ayin ki, kin zaɓi kasuwancinki akan mijinki da 'ƴa' ƴanki, bayan Allah da kansa ya kai darajar miji ƙololuwa da har yace da zai ce wani ɗan Adam ya yi Sujada wa wani...da tabbas ya umurci Mataye da su yi wa mazajensu Sujada....Aljannar mace tana tafin ƙafar Mijinta...da roƙo da komai ya dinga roƙonki, amma haka kika saka ƙafa kika bar shi. Sannan yanxu har kike iƙirarin cewa ya ci amanar ki? Anya kinsan wane matsayi mutum idan ya taka ake kiransa uwa kuwa?? Mahaifinmu bai aikata kowane irin kuskure ba...ke ce kika bar ƙofar da wannan ɓaraka ta samu gindin zama Ammah. Hmmm! Koda yake ba zan yi mamaki ba,domin son zuciya da nuna son kai a jinin ku yake...domin a gabana er uwarki ta faɗawa 'ƴata muna nan kalamai akan Mijinta wanda ko condition ɗinta bata duba ba..." "Ammie please..." Na ambata da sauri ina mai rufe mata baki da hannuna tare da girgiza mata kaina alamar ta daina. "Beenafah ki barta...ki barta ta sauke duk wani abin da take jin ya tokare mata zuciya! Tabbas ni ɗin na ruguza kaina a matsayina na uwa, na kasa sauke nauyin da ya rataya a kaina. Na rabu da mahaifinku ba tare da ya yi mini laifin komai ba. Tabbas ya yi iya abinda zai iya wurin ganin cewa ban nemi wani abu na rasa ba. Ni kuma na yi nisa sosai, wani abu nake hange mai nisan gaske....to amma na cim ma wannan abun kuwa? A'a! Ita ce amsar, domin daga lokacin da na watsar da gidana tun a wannan lokacin rayuwata ta samu giɓi. Hatta iyayena da dangina ban faɗa musu gaskiyar rabuwarmu ba. Tun ina saka rai da tsammanin cewa watarana zai dawo gare ni, har ta kai ga na cire rai,domin ya yi fushi mai tsanani. bayan wannan zunubin da na aikata, hakan bai ishe ni ba, da naga cewa tabbas ba zai dawo ba, naji SAMI na gama da iyayena akan cewa zai je Qatar nemansa...a lokacin ne na buɗe baki na juye maganar da cewa shi ne wanda ya wulaƙantani ya koreni yace na tafi ya sakeni,kuma har abada baya so ya ƙara ganina, Nana Hauwa Ita ya ɗauka yace na tafi da Nana Maryam ya yafeta har abad..." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Kalmar da kowa ya ɗauka a ɗakin kenan jin wani irin labari na ban mamaki wanda Hatta Jadda sai da ta girgiza. Haƙiƙa biri yay kama da mutum. Sumaiha bata da wani aiki sai kuka, ta ƙaratar da tsawon rayuwarta da sadaka da kuma ciyar da marayu, aikinta kawai shi ne ibada. Maganarta ɗaya ce, kullum a roƙa mata ubangiji ya yafe mata kuskurenta. Ashe shi ne wannan kuskuren? Taƙi ta yi aure tsawon lokaci tun rabuwarsu har tsufa ya kamata, duk tsawon shekarun nan cewa take ta gama aure a duniya. Sosai maganar ta girgiza duk wanda yake ɗakin. Sai a yanzu ne Jaddi ya iya kallonta rai babu daɗi ya ce. "Ashe kece da laifi Sumaiha? Ki ka rabani da abokina aminina tsawon lokaci? Ina ribar da kika samu a yanzu?" Ba tare da ta Ƙarya ta ba tace. "Ni ce SAMI! Dan Allah ku yafe mini. Na tsufa, har na kai ga jikoki amma ciwon da yake raina ko kaɗan bai ragu ba tsawon shekaru. Daga lokacin da mutum ya ɗora rayuwarsa akan wani burin da yake ƙoƙarin cim mawa, musamman ga 'ƴa Mace....to tabbas yana da buƙatar goyon bayan mijinta ko iyayensa akan wannan al'amari, idan ya bijire yace shi lallai sai ya cika wannan mafarkin ta kowace fuska to tabbas zai ƙare a danasani. Kamar dai ni ɗin nan. Na nuna taurin kai da hawa dokin fushi dokin zuciya, wanda nake ganin ko da mijina ko babu shi zan iya cika mafarkina, ba tare da la'akari da irin ƙoƙarin da yake a kaina ba. Ya jure sosai akan irin tsananin da mahaifiyarsa da danginsa suke masa a kaina, a kullum cikin bani haƙuri yake akan cewa in yi haƙuri watarana komai zai wuce. Sai na ɗauka kamar labarin tatsuniya ne domin hakan har abada ba zai samu ba, hakan yasa ganin sun uzzura mini ni ma na yanke rabuwa da shi domin ba za su taɓa sona ba, sannan tunda har ya kai ga cewa na zaɓa ko shi ko kasuwancina to tabbas watarana shi ma ɗin zai iya juya mini baya. A lokacin ƙuruciyata, ni sam ban yarda da yin shawara da kowa ba, domin ra'ayina daban da na wani, abinda zuciyata ke so da hasashe,...ba lallai sun yi daidai da ra'ayin wani ba. Na taso da wata irin rayuwa ta daban wanda sam daga ƙarshe bata amfane ni ba. Babu wata rana da za ta zo ta wuce ba tare da naji kewar mijina da 'ƴa' ƴana ba, na yi ta saka rai da burin watarana ya dawo gare ni, amma bai dawo ba. Nana Maryam ma da nake gani in ji sanyi....tunda taje garesa bai sake bari ta zo gareni ba. Ni ce na ɓata komai, na yarda ni ce. Dan Allah ina neman yafiyarku da gafararku, dan Allah Abubakar ka yafe mini. En biyu na dan Allah ku yafe mini..." Kamar wani haɗin baki dani da Noura muka yi saurin isa gareta muka rungumeta. Ɗagowa na yi ina share mata hawayenta nima ina kukan na ce. " Haba Ammah dan Allah! Kada ki tsaurarawa kanki da yawa, a matakin shekarunki, idan kika ci gaba da kuka haka, wani abu zai iya faruwa dake. Na san ai za su yafe miki...tabbas za su yafe miki. Duk wanda ya aikata kuskure kuma ya nemi afuwa ya kamata a duba masa a manta da komai. Da ace abubuwa ba sa wucewa a rayuwa to da har abada zamu ci gaba da kasancewa a tsagin da rayuwa ta zaɓa mana kenan, wanda walau na farin ciki ko kuma na baƙin ciki. Da ke da Abiyh dukkan ku kowa yana da laifi, ke kin nuna taurin kai shi kuma ya nuna tsananin fushi, wanda da ace baki nuna taurin kai da nuna isa ba, da yanxu rayuwarku ba ta ƙare a haka ba, shi kuma da ace bai nuna zafin fushi da rashin yafiya ba, da yanxu kuna nan a tare, domin da ace ya haƙura ya biyo sawunki, tabbas a yanda zuciyoyinmu suke da taushi mu mata, da tabbas na san za ki iya ajiye ƙudurinki ki bisa ku koma. Rayuwar nan idan har bama fahimtar mazajenmu, bama ɗaukar matsayinsu da girman da Allah ya basu da muhimmanci, to fa tabbas suma za su fito mana da wata fuskarda bamu taɓa sani cewa suna da ita ba watarana. Abu na ƙarshe ni dai da zan faɗa a matsayina na ƙarama sosai a cikin wannan wurin,mu riƙa uzuri wa juna muna yafiya, sai wani abun ya faru a rayuwarmu muke samun damar wani abin. Ban rayu da mahaifina lokaci mai tsawo ba. sannan ɗan uwansa jinin sa ya cutar damu ni da mahaifiyata da ɗan uwana. Mun ɗauka a wannan lokacin cewa wata ƙila a hakan ƙaddararmu ta zo kuma a hakan zamu ƙare...but da ubangiji ya tashi sauya mana rayuwa..sai ya juya mana tamkar wani ciwo bai taɓa samuwar rayuwar tamu ba..." Cikin jin wata irin ƙuna Sheikh ya kalli Ammie yana zubar da hawaye ya ce. " Mulaifa halin da kika kasance a ciki kenan? Kai co na! Kai Co na! Sai da na ji a raina kamar ban amince da wannan mutumin ba a lokacin da kika kawo shi gareni...sai dai yanda kika nuna ƙauna a garesa sai na haƙura na kuma yi addu'a, ashe duk da haka ban damƙa ki a hannun da ya dace ba. Ki gafarce ni dan Allah..." Jinjina kanta tayi a hankali tana kallon fuskar sa ta ce. " Kada ka taɓa jin cewa wai baka yi daidai ba don ka aura ni ga DR. Bello Sheikh. Tabbas ko kaɗan ba ka yi kuskure ba, domin ka aura mini mutumin da ya dace. Wallahy ya so ni ya kuma riƙeni cikin aminci, wanda ina fata da addu'ar A koda yaushe Allah ya tasheni tare dani da shi a Aljanna. Domin shi ɗin miji ne kuma shi ɗin uba ne. Mutuwa ce wacce tayi mana tsakani, ita ce tayi mana gaggawa a tsakaninmu.....Hmm! na ga lokacin sallar magariba ya ƙarato, ya kamata muyi sallah sannan na ɗora muku yanda na rayu." Daga haka kowa ya tattara jiki sanyaye aka watse. Nana Maryam, Ammie na ta bi zuwa masaukinsu cike da kewar juna suna ta labari suna farin ciki gwanin tausayi. Gidana na nufa tare da Aunty Nadeeyah, ina ta bata labarin abinda Jadda ta mini kafin zuwansu, muna nan bayan na yo alwala, ina fitowa na taradda Noura ta shigo. Kallonta na yi kamar yanda itama take kallona sannan daga ƙarshe ta yi mini murmushi ta zo ta rungumeni tana faɗin. "I'm sorry sis...I'm really really sorry. Dan Allah kada ki riƙeni da komai, wallahy sam bani da ra'ayin auren mijin ki, su Jadda su ne waɗanda suka ga cancantar hakan. Sai ga kuma wani al'amari na ubangiji ya sake bayyana mana cewa, bayan auren ki da ɗan uwana....mu ɗin ashe en uwa ne na jini...please I'm sorry..." Murmushi na yi mata ina mai share hawayen farin cikin da suka silalo mini na ce. " Ba komai. Abu mafi muhimmanci shi ne....mu ɗin en uwa ne. Na kasance a da idan naga mutane suna hulɗa da en uwan su, sai inji suna burgeni, a raina nakan ce nima inama ace ina da dangi haka kamar su....sai ga shi ashe nima ina da kyakkyawan family ba tare da na sani ba. Na yi matuƙar farin cikin da wannan. Ubangiji ya ci gaba da ɗaurar mana zumuncinmu har Aljanna." "Amin ya Allah." "Mu yi sallah?" Wuri ta samu akan kujera tana mini kyakkyawan murmushinta ta ce. "Zan jira a nan." Zaunawa tayi har muka kambala sallar dani da Aunty Nadeeyah, sai ga wata daga cikin masu aiki ta shigo mana da tray shaƙe da kayayyakin Ci da Sha masu matuƙar daɗi da garɗi a baki tace wai daga Jadda ta ce a kawo mini ko akwai abinda nake son ci a ciki. Hmmm! Ni ce shugabar cewa idan an maka laifi ka zama mai yafiya. Amma wallahy sam na kasa jin cewa wai zan iya yafe mata duk da kasancewarta Kaka a gareni nima. Duk tsawon kwana biyun nan da take ta wani rawar ƙafa a kaina sam bana jin tana burgeni, daga zaran na kalle ta sai in ji abinda tayi mini yana ƙara dawomin sabo a raina. A duk lokacin da na ɗora idona a kanta sai na riƙa tambayar kaina cewa, wai ashe haka take matar nan, kamar ta kirki. Ko daga sama na faɗo ai yaci ace darajar so da ƙaunar da jikanta ke mini da kuma cikin da yake jikina yaci ace ta tausaya mini. Amma haka ta bushe idanun ta musamman ranar da na iso, ga gajiya ga ciki amma bata yi tunani mai kyau a kaina ba. Allah dai ka haɗamu da mutane na gari, shi kaɗai zamu iya cewa. Bayan mun kambala sallar Isha ne muka koma parlourn wanda a lokacin har da su Suhaib, Raihab da kuma ƙaramin ƙanin Noura ɗin, Shuraih suka yi joining na mu. A nan Ammie ta basu tarihin rayuwar da mukayi a lokacin da Abbie ya rasu ya barmu, da kuma irin riƙon sakainar kashin da Daddy ya yi mini da cutar damu da ya yi har sauyinda muka samu da kuma auren ta da Dr. Basheer da kuma yanda aka yi aure na. Ba ƙaramin al'ajabi suka yi ba jin tarihin aurena da Ya Mohaa. Wanda sun jinjina mini ba kaɗan ba. Kowa sai albarka yake saka mini da fatan kasancewarmu da ni da shi har mutuwa. Sosai idon Jadda ya raina fata domin ko a yanda suke ta zuzuta cancantarmu da irin yaba masa a yanda ya nuna mini ƙauna yasa ta sa jinin jikinta kuma taji har cikin ranta cewa ta yi kuskure. Cikin wata irin magiya Abiyh ya kalli Ammie yana ta roƙonta shi da Ammah akan ta yafe musu domin su ne sila. Nan aka hau yafe-yafe ana ta koke-koke. Gefe na koma na amsa kiran masoyina ina ta bashi hint da abinda ke faruwa in brief. Mai karatu ka kwatanta irin farin cikin da mutum ke shiga idan ya rasa danginsa tsawon lokaci sai kuma dare ɗaya ace ya same su. Alhamdulillah shi kaɗai zamu ce. Amma kowa yana cikin farin cikin da baki ba zai iya misalta shi ba. Addu'ar kambala taron akayi wanda Sheikh ne wanda ya jagoranta sannan daga ƙarshe na ce kowa ya dakata ina da magana. Shiru suka yi suna masu kasa kunne domin jin abinda yake raina. Muryar Annie na ji (Nana Maryam) tana faɗin. "Akwai hikima sosai a kalaman ki Beenafah. Haka nake ganin rayuwarki kamar ta Raihab. Nutsuwarku da baiwar kalamanku iri ɗaya." Murmushi na yi tare da kallon inda Raihab ɗin yake zaune na ce. "Daga yau kuwa, kai ne babban abokina, domin duk shawarar da za ka bani in sha Allah na san mai amfani ce." Dariya ya yi yana jinjina kansa ya ce. "Tau shikenan Aminiyata, Allah bar mana zumuncinmu har mutuwa." Da amin duk muka amsa sannan na kalli Sheik na ce. "Sheikh...dan Allah ina so ka yi wa Ammah da Abiyh nasiha, akan su dawo da auren su su yi haƙuri su manta baya..." Wani irin kallon suka bini da shi wanda sai da na ji kamar na karaya, amma sai na ƙara dagewa tare da roƙon Allah ya bani sa'a yasa na yi nasara. Da Ammah na fara na wani kalle ta na ce. "kin wani ƙuro ido kina kallona. Taurin kai ne kawai kika nuna amma a yanda kike ta kuka kina neman sa gafara dole akwai sauran soyayyar nan a zuciyarki. Kuma ma da ace baya cikin tunanin ki tsawon shekarun nan da yanxu kin auri wani kin manta da shi. Saboda haka, sanadiyyar ki ne ya nemi ya rasa idanunsa, dole ki koma gidansa domin kulawa da shi." Sai kuma na waiga wurin Abiyh na ce. "Kai ma sai wani kallo kake mini, da ba ta cikin ranka da ba za ka yi kuka har ka nemi rasa idanun ka ba, sannan da ba ta cikin ranka da yanzu ka yi wani auren ka manta da ita....kuna ji ko? Kun biye wa zuciya kun cutar da junanku. Shawarata a nan ita ce, ɗan lokacin nan da ya saura muku a duniya yana da matuƙar muhimmanci ku ƙarasa shi a tare. Sannan abu na ƙarshe...dan Allah ku dawo da auren ku ko don farin cikin waɗan nan 'ƴa'ƴan naku da kuka ruguza farin cikin su tsawon shekaru." Nan ɗakin ya ɗauka, kowa ya bayar da goyon baya akan cewa wannan shawarar tawa ta yi daidai. Kawai a mayar da auren tare da na Emraan da za'a yi jibi. Nan sheikh ya ƙara yi mana jan hankali akan girman haƙuri a gidan aure da kuma lura da haƙƙoƙa da muhimmancin haɗin kan miji da mata a kowane irin abu da zai zo a cikin rayuwar su. Domin da ace akwai haƙuri da biyayya da auren Ammah bai ƙare a haka ba, sannan shi ma Abiyh da ya zama mai haƙuri da rashin biye wa mata da yanzu auren su bai ƙare a haka ba. Da wannan ya samu ya janyo hankalinsu har suka amince wanda a nan Abiyh ya ce zai kira danginsa ya sanar musu, daman daga cikin su sun yi ta bashi shawara tun a lokutan baya akan ya zo ya dawo da ita ya ce baya buƙata. Hatta mahaifiyarsa kafin ta rasu sai da tace ya dawo ita yace baya buƙata. Kallon Jadda Ammie ta yi murya a tausashe ta ce. "Jadda! Roƙona ɗaya ne. Mu dai a yanzu family ɗaya ne, Alhamdulillah! Shawarata da roƙona shi ne;tun da har kun ga cewa Noura ta fi da cewa da Hammodi....to gwanda ta bar mata shi domin namiji bai isa ya ruguza mana zumunci ba. A ranar da na iso ƙasar nan naga irin abinda kika mata a gabana, ya sosa raina sosai, domin bani da kamar Beenafah a duniya, zan iya yin komai domin ta, da ba dan wannan zumuncin ba wallahy tallahy har na gama yankewa a raina cewa Beenafah ta gama auren shi har abada, komai zai faru ko. Domin ba zan bar 'ƴata ta rayu a dangin Mijinda basa son ta ba kamar yanda ya faru dani. Har abada ba zan lamunta ba....to amma tunda har abun ya zo a haka, za ta iya bar mata sh..." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku ni Samaahat" Jadda ta furta a gigice tana mai ɗora hannu a kai tamkar za ta zubo fitsari tsabar yanda ta ruɗe. Sai faɗin take. "Sharrin shaiɗan ne wallahy NANA Hauwa! Dan Allah ki yi mini gafara. Sam ban kyauta ba,damuwar Noura ta dameni..." Cikin wani irin takaicinta Aunty Nadeeyah ta ce. "Gaskiya Jadda kin bani mamaki. A yanda kika mana farkon zuwanmu ko a mafarki akace za ki iya Cutar da Beenafah zan ƙaryata. Amma dan Allah ji kalaman ƙasƙancin da kika mata ko arzikin cikin da ke jikinta baki duba ba. Ai a tunani ko ke ce kike son auren Hammodin za ki ɗaga mata ƙafa... " Tsawa Baba Ustaz ya daka mata sannan ya ce. " Wannan wane irin shirmen magana ne? Ina ce an yi komai ya wuce an nemi yafiya kuma komai ya wuce? Miyasa za ku nemi dawo da hannun agogo baya? Kowa ya yi haƙuri wannan magana ta wuce. Hajiya Nana Hauwa sam wannan magana ba ta kama ta ba, duk da cewa nasan ɓacin rai ne. " Girgixa kai Jaddi ya yi cike da tai ci yace. " Duk tsuntsun da ya ja ruwa ai dole su yi masa mugun duka Alhaji Ustaz! Wato da na ce miki kibar wannan maganar ta wuce ashe baki barta ba Samaahat??" Tamkar za ta yi dungure wurin bashi haƙuri haka ta yi, sai kuka take harda wani juyowa tana nemana gafara. Nikam ta shi na yi ina faɗin ba komai ya wuce, sannan na wuce ƙofata, daman ga wani uban fitsari da ya cika mini mara ta sannan ga kiran Dayaa sai shigowa yake, da yaga naƙi na yi picking ne yasa

Chapter 57 of 67