an ce Beenafah to an kai ƙarshen magana. Ammie bukin ne aka fito? To Allah ya tsare...."
Ina murmushi na ce.
"Na yi kyau dai kenan ko Ya Jafaru?"
"Haba!...."
A hankali muka ga mota ta iso ta parker inda muke tsaye kowa ɗauke da mamaki a fuskarsa.
Wani irin mugun haɗe rai Ya Jafaru yayi ganin Yaya Ashiru ya fito a hankali daga motar yana murmushi ya ce.
"Ammie ina wuni?"
Itama da murmushin ta ce.
"Lafiya lau Ashiru. Ya hidima kuma? Allah yasa alheri?"
"Amin Ammie. Daman cewa na yi bari na zo na tafi daku tunda baku san wuri ba kada kuje kuyi ta wahala."
"Amma Ashiru baka ɗaurawa kanka wata wahala ba? Ai da ka bar shi munzo a Napep.."
Hannu ya miƙawa Ya Jafaru yana murmushi yayin da Ya Jafarun ya gimtse sosai suka gaisa.
Ƙofar motar ya buɗe wanda Bahrain har ya jima ciki tunda ya buɗe ya fito ya shige ciki yace mana.
" Ku shiga Ammie mu tafi yamma na ƙara yi. "
Cikin motar Ammie tashiga, sannan Farisa, sai kuma ni da na kasa ce masa komai sai murmushi nake na shiga sannan ya rufe.
Ya Jafaru dake tsaye ji yayi wani baƙin ciki ya taso ya tokare masa maƙogwaro...wata zuciyar na ingiza shi akan ya shiga motar shima ya bimu, wata kuma zuciyar na ce masa a'a Jafaru! Kai dai yi zaman ka, kana nan zaune zaka ga sun dawo.
Da haka na yi ta ɗaga mishi hannu har muka wuce. Bakin bishiya ya kama ya zauna yana jin a zuciyar shi ba zai iya ɗagawa ko'ina ba sai idan ya ga mun dawo.
Shi wallahi a yanzu yama rasa wane kalar tunani ya kamata ya yi. Ko Makaho ya lalaba tsakanin Beenafah da Ashirun nan yasan cewa Ashiru sonta yake... Wata irin zabura ya yi da ƙarfi ya furta.
"Kai! Inaaaa! Wallahi tallahi wannan Ƙarya ce ma."
Daga haka ya sake komawa ya zauna yana mai ɗora hannayensa akan gwiwoyinsa ya buga wani uban tagumi yana tunani.
Duk irin labarin da take bashi akan Ashiru bai taɓa hasko abin ta haka ba, tun ranar farko da Ashiru ya zo suka tsaya suna wannan firar tun a ranar ya tsinci kansa cikin matsanin baƙin cikin da har bacci sai da ya hana shi. Ya hana mai walwala, babu abin da yake gani da ji idan ba firar su ba ta ranar.
Ya kasa zuwa makaranta, tun ranar Kawunsa ke kiran sa amma ya kasa ɗagawa domin bai ga ta tafiya yabar gari ba domin wallahi ba zai taɓa yarda ya yi sake ayi mishi sakkiya ba.
To amma kuma ina mafita? Mafita ɗaya ce mafitar da bai san ya ma zai iya fuskantar ta ba a yanzu amma kuma dole ya yi wani abu idan ba haka ba wallahi yana nan tsaye yana kallon ruwa kwaɗo zai masa ƙafa.
****
Yaya Ashiru bai tsaya ko'ina damu ba sai ƙofar gidansu inda muka tarar mutane da yawa sai kai kawo ake masha Allah ana ta hidima.
Cikin farin ciki da wani alfahari yake nunawa duk wanda muka haɗu da shi ni yana faɗin ga Beenafah su gaisa.
Ƙofar Umma aka yi mana shimfiɗa muka zauna wanda ni sam na kasa ganewa, domin mutane sai watsewa suke a hankali suna barinmu a zaune. Ummar ce ta fito daga cikin ɗaki ta zauna a gefena, fuska cike da murmushi ta ce mana.
"Hajiya! Sannu da zuwa."
"Yauwa Maman Ashiru sannu, ya gida ya bayan rabuwa kuma?"
Umma ta ce.
"Alhamdulillah! Sai godiya. Ya kuma jiki?"
"Jiki Alhamdulillah! Sai godiyar ubangiji. Ana ta hidima ashe? Allah ya sanya alheri ya bada zaman lafiya."
"To amin amin ya Allah. Mun gode sosai Allah ya saka da alheri..."
Muryar Ashiru muka ji yana ta ƙwala kiran Ayya amma kuma babu ita babu labarinta. Da kanshi ya dinga kiran mutanen gidan muna gaisawa, sai wani kallona suke tamkar sunga wata sabuwar halitta har sai da naji har cikin raina na tsargu.
Abinci aka kawo mana da ruwa wanda gabaɗayanmu babu wanda ya taɓa sai Bahrain ne ma ya ɗauki lemu ɗaɗaɗaya da shi da Farisa suka fasa suna sha.
Kallon Ammie na yi ganin kowa ya kama wata sabgar domin har Umma an kira ta wani wuri, ganin hakan yasa murya a ƙasa-ƙasa na ce.
"Ammie ta shi mu tafi gida."
Gyaɗa kanta ta yi sai muka miƙe a tare muna kiran zamu tafi. Fitowa Yaya Ashiru ya yi daga can cikin wani ɗakin da ya shiga tunɗazu ya ce mu shigo mu gaisa da Ayya.
Ɗakin cinjim yake da mutane wanda ashe har Amaryar tana ciki. Nan muka sake shiga wani babin gaishe-gaishe,daga can ƙuryar ɗaki ƙarshen gado Ayya take yi mana magana ciki-ciki kamar ba ita ce ta taɓa zuwa gidanmu tana surutu tamkar an kunna redio FM ba.
Dubu uku Ammie ta miƙawa Ayya tace a sai wa Amarya tsintsiya Allah yasa albarka ya bada zaman lafiya.
Har waje wasu daga cikin su suka rakomu suna mana godiya yayin da wasu kuma suke ta baya-baya damu.
Da kanshi ya sake ɗaukarmu ya maishe mu har ƙofar gida wanda har lokacin ashe Ya Jafaru yana nan inda muka bar shi yana zaune.
Yana ganin mun fito motar ya zo yana mai karɓar ledar da take hannuna ya ce.
"Sai yanzu?"
Murmushi na yi na ce.
"Mun daɗe ne Ya Jafaru?"
Jinjina kansa ya yi ya ce.
"Gaskiya dai kam."
Gida Ammie ta shige tabarni ina magana da Ya Jafaru wanda bamu ankare ba muka ji horn ɗin Ya Ashiru.
Juyawa na yi na koma gefen driver na tsaya jikin window na ce.
"Yaya Ashiru mun gode sosai."
Jinjina kan shi yayi da murmushi ya ce.
"Ba komai Beenafah ai ni ke da godiya, na gode sosai. Sai na dawo.."
"Yaushe kenan?"
"Uhm! Ni ko gobe kika ce na dawo zan dawo...beside yau an riga an gama komai kinga na zama free."
"Eyyah ni kuma Kaga Alhamis da juma'a ne kaɗai nake gida domin sauran ranaku ina makaranta."
"To yanzu sai Alhamis kenan?"
Gyaɗa kaina na yi na ce.
"Eh, zai fi."
"To Allah ya kaimu."
"Amin, sai anjima na gode."
Idon Ya Jafaru ƙyar a kaina koda na juyo, gashi ya wani haɗe rai sosai kamar ba shi ne yanzu yake mini murmushi ba.
"Beenafah!"
"Na am"
Na amsa ina kallon shi kamar yanda shi ma ni yake kallo ya ce.
"Wane ne wannan a wurin ki?"
"Uhmmm! Wai Yaya Ashiru kake nufi?"
"Eh"
Ya bani amsa kai tsaye.
"Yaya na mana, wanda ya taimaka mana."
"Bayan wannan dalilin fa Beenafah?"
Ba tare da sanin inda maganar sa ta dosa ba na ce.
"Ba wani dalili."
"Kin tabbata Beenafah?"
Gyaɗa kaina na yi na ce.
"Na tabbata."
Cikin jin wani irin sanyin da ya jima bai ji irin sa a zuciyarsa ba ya lumshe idanunsa a hankali sannan ya buɗe su a kaina yana mai kwantar da murya sosai cikin yanayinda ban taɓa jin muryar sa a haka ba yace.
"Bani da wani zaɓi Beenafah, ya zama dole gobe in tafi Zaria, Kawu har ya yi fushi sosai akan rashin zuwana...."
"To wai ni abinda ya hana ka tafiyar ne ya bani mamaki Ya Jafaru..."
Wani guntun Murmushin ya saki yana girgiza kansa ya ce.
"Ko na faɗa miki dalilina yanzu ba za ki fahimta ba Beenafah... Zo.. Zo mu zauna a nan."
Ya ƙarashe maganar yana mai samun bakin bishiya ya zauna nima ya nuna mini gefen sa yace in zauna.
Wani irin rikitaccen kallo ne ya bini da shi har sai da na ji zuciyata ta tsinke domin a tunanina wani laifin na aikata masa.
" Beenafah ki yi mini alƙawarin cewa daga gidan aikin ki sai Islamiyyar ki kaɗai za ki riƙa bai wa muhimmanci, duk wani mutum ko waye shi ba za ki tsaya kina ɓata lokacinki wurin tsayawa magana da shi ba..."
"Haba! Ka sanni ai Ya Jafaru, ni bani da wannan rayuwar, ko mazan da suke ajinmu a islamiyya babu wanda nake magana da shi in dai ba ta kama ba. Sannan gidan aikina ma su kansu suna da doka,babu wacce ta isa ta tsaya da namiji suna fira koda a wajen gidan ne."
Cikin jindaɗin fahimtar sa da nayi yasa shi sakin murmushi ya ce.
"To na gode Beenafah, zan riƙa kira da wayar Mama sai ta baki muyi magana a duk sanda na tashi, kema kuma idan kina so ki yi magana dani za ki iya ɗaukar wayar ki yi mini plashing kai tsaye kinji ko."
"In sha Allahu Lauyanmu na gobe, Allah ya taimaka ya bada sa'ar abinda aka je nema.."
"Amin. To amma ke baki da wani alƙawarin da kike so na riƙe miki ne Beenafah??"
Cikin seconds na ɗan wawwara ido nayi nazarin maganar sannan na jinjina kaina ina murmushi na ce.
"Alƙawari ɗaya Ya Jafaru, kada ka biyewa abokan banza, kamar yanda Ammie ke yawan gaya mini, abokan banza sune babban jigon da ke taka rawa wurin taɓarɓarewar tarbiyyar yaro duk yanda kuwa ya samu training a gida. ka mayarda hankali akan karatunka kamar yanda kake faɗa mini nima."
Wani abu yake ji yana ƙara girmama a zuciyarsa fiye da yadda yake tunani musamman wannan firar da mukayi, ta tsaya a cikin ranshi tare da sake haska mi shi wata sabuwar hanyar da bai san tana existing ba a cikin duniyar sa.
Muna nan zaune muna ta fira har sai da aka fara kiran Magrib sannan ya ce na tashi na shiga gida.
Washegari koda na fito na shiga gidan wai har yayi sammako ya wuce zuwa Zaria. Fatan alheri na yi musu sannan na sa kai na wuce.
Ko bayan da aka gama sunan Muhammad (Abeer) sai da muka kwashe tsawon sati muna aiki sosai sannan daga baya muka samu sassauci bayan mutanen da suka zo kowa ya watse sai en tsirarrun da suka rage ne ba su tafi ba.
Maimakon Aunty Ziza ta canja daga halin da take nuna mini tunda Hajiya ta yi magana, ko ɗaya ba ta sauya ba wanda sai ma ƙaro sabbin wulaƙancin da ta ƙirƙiro, hatta kofi idan za ta sha ruwa sai ta saka an kirani na zo na ɗauko mata. Ni kuma abin da bata gane ba, ko kaɗan yanzu na daina shakkarta tunda na gano abin ta bana arziki bane, duk tayi abu don ta ɓata mini rai ko kaɗan hakan baya damuna wanda ita shi ne abinda yake ƙara ƙonata dangane da ni, aiki kuwa, idan za ta kwana tana saka ni aiki bana taɓa nuna mata komai, kuma ita ko a gaban waye bata shakkar yi mini haka idan ka cire Aunty Labiba da Emraan. Waɗan nan mutum biyun sune kaɗai idan suna a wuri bata nuna alamun musgunawa a gare ni.
Yauma ina zaune bakin kitchen tare da Haula sai gashi ta kira Haula a waya wai in zo tana nemana. Tashi na yi kai tsaye na shige na ce mata gani.
Flask ta nuna mini tana faɗin.
"Ɗauki ki dafo mini ruwan zafi ki kawo ina jiran ki yanzu."
Ɗauka na yi ina faɗin to,babban kitchen na dawo na buɗe wata babbar tukunyar ruwan zafi ina ta wani mitsitstsika ido akan hayaƙi su Munira sunata mini dariya na cika flask ɗin na ɗauka naje na kai mata na ce ga shi.
Wani kallon sama ƙasa ta mini ta ce.
"kina nufin yanzun nan har kin dafo ruwa?"
Girgiza kaina na yi kai tsaye na ce.
"A'a, a Kitchen na ɗebo wurin su Inna Kuluwa..."
"Did I asked you to go there and fetch?? Cewa na yi kije ki kunna wuta ki ɗora ki dafasu su tafasa sannan ki juye ki kawo mini."
Ɗauka na yi kurum na fice naje waje na juyesu a bakin famfo cikin wani bucket duk su Munira suna zaune suna kallona fuskokinsu cike da alamar tambaya.
Kitchen ɗin ciki na koma naje na kunna Gas kamar yanda Haula ta koya mini na ɗora tukunya na tsaya nan jikin ƙofa har sai da ruwan suka tafasa na juye na kashe sannan na fito naje na kai mata.
"Ɗauki Abeer kije ki cire masa diaper ki kawo mini shi."
Ta ƙarashe maganar tana mai nuna mini toilet.
Ɗaukar shi na yi na je toilet ɗin na tsabta ce shi tas cikin lokaci na dawo na miƙa mata shi. Wai ita ƙila a tunaninta zan rikice ne na ce bansan yanda akeyi ba,don ta samu damar ci mini mutunci son ranta. Bata san cewa In Sha Allahu ko ita bata fini sanin yanda ake kulawa da jariri ba, domin lokacin da Ammie ta haifi Sajjad, ni ce na dawo uwar sa ta dalilin halin da Ammie ta tsinci kanta a ciki wanda hatta wanka, bacci, da cin abincinsa duk ni ce, sai da ya bar duniyar sannan na daina kulawa da shi. Saboda haka ni kula da yaro sam baya bani wahala, kuma zan iya jure ƙiriniyar yaro ko yaya yake ko.
Yana da fa Nannynsa ta musamman da aka kawo mata ita kwana uku da suka wuce. Amma don neman fitina ita dole sai ta san yanda ta nemi hanyar musguna mini.
"Ɗauko ga cup can Ki haɗa mini Tea Ki zauna ki fifita mini har sai ya sha iska sannan."
Ina zaune a ƙasa ina fifita mata na ji sautin muryar ta tana faɗin.
"Wai har ke Hairi za ta dinga wani zuzutawa! Ina abin zuzutawa a nan? Mai aiki ana biyan ta har wani abin burgewa ke gareta? Hmm! Wai Pretty! Pretty na inda take ke kam sai dai Pretto..."
Tamkar tana magana da iska haka na yi mata kamar ban san dani take ba. Ina nan zaune Haula ta shigo mata da Lunch cikin wani babban tray mai ɗauke da dishes sun kai kala biyar ta ajiye mata a gefe tana faɗin ga abincin ta nan, kallona tayi ta yi mini murmushi nima kuma sai na mayar mata.. Aiko ina wuta ta ka ɗani, kawai ta hau bakinta tana faɗin wai na raina ta ina kallonta ina yi mata dariya, ita sai na nuna mata abinda na gani a jikinta da yake sakani dariya.
Maimakon in ji tsoro in daina, yanda take ɗin sai ya ƙara sakani dariya wanda har bansan lokacin da wata dariyar ta sake suɓuce mini ba.
Aikuwa jiki na rawa ta miƙe ta nufo inda nake, kallonta nake da mamaki ina jira inga shin dukana za ta yi ko kuma me. Ganin ta juyo gareni yasa Haula sakin dariyarta a hankali tana yi tana toshe baki wanda shi ne abu na uku da ya sake bani dariya.
Ficewa tayi fuu! Sai inda Hajiya tana wani huci ta ce.
"Hajiya! Shin ina so in san wani abu. Waccan 'ƴar aikin bata san matsayina ba ne a gidannan ko kuwa?"
Ajiye remote ɗinda ke hannunta Hajiyar ta yi sannan ta kalle ta ta ce.
"Ziza wacce mai aiki kike nufi?"
"Marar kunyar yarinyar da Aunty Labiba ta kawo mana."
"Beenafah kike nufi?"
Da sauri ta gyaɗa kanta ta ce.
"Eh, ita. Hajiya dariya fa ta dinga mini, sai ta kalleni ta tuntsire da dariya..."
Hankali kwance Hajiya ta girgiza kanta ta ce.
"Ba dai Beenafah ba Ziza, ko Munira da nasan tana iya aikata makamancin haka ba za ta yi miki dariya ba ballantana Beenafah da ba ruwanta...."
"Wallahi Haji..."
"Ziza! Samu wuri ki zauna mu yi magana."
Haɗiye sauran maganar ta tayi tare da samun kujera wacce ke fecing Hajiyar ta zauna tana kallonta.
"Ki daina shigewa gaban yarinyar nan Ziza, Hairiyyah ta faɗa mini irin abin da kika mata ranar wanda Munira ce ta faɗa mata kuma hakan sam bai kamata ba,ko ni ranar a gabana ki ka dinga yi mata kuma kin san ni bana son haka, ni da na ajiye su ban uzurra musu ba kema banga dalilin da zai sa ki riƙa uzurra musu ba. Tunda kika yi aure gidan nan ban sanki da haka ba, saboda haka dan Allah ki bari, idan ma akan kuskuren da Emraan ya yi ne kema kin san ya faɗa ne kawai, domin kinfi kowa sanin wane ne mijin ki, ko ɗaura mishi ita aka yi a ƙafa ba zai ja ta ba. Ki kama girmanki ki daina shiga harkar yaran nan bana son hakan. Ban hana ki saka su aiki ba, duk abin da kike so suyi miki dole za su yi shi ko basa so domin matsayinki da na su Nadeeyah duk ɗaya ne a gidan nan, to amma ki tsaya matsayin ki dan Allah."
Murya a raunane ta kalli Hajiyar ta ce.
" Ki yi haƙuri Hajiya."
Jinjina kanta ta yi ta ce.
" Ba komai. Kina iya tafiya."
Fitowa tayi jiki sanyaye ta dawo ɗakin wanda har a lokacin ina nan inda ta barni ina fifita mata shayinta. Wani kallon ta yi mini a yatsine ta ce.
"Ki haɗa da kofin ki wuce da shi ki bani wuri."
Cikin sauri na fito riƙe da Tea cup ɗin na cikawa rigata iska. Ɗaki na dawo wurin su Munira. Sai da na shanye lafiyayyen Shayi na wanda ya ji komai yayi zam sannan muka dawo muna cin abinci ina ƙara ba su labarin abin da ya faru sai dariya muke har muka kambala na ta shi na haɗa kayana na yi gida.
Koda na koma na tarar da Ya Ashiru cikin gida zaune da shi da Ammie suna fira.
Ɗaki na shige na ajiye kayan na fito muka gaisa da shi.
A nan gaban Ammie ya ciro waya a kwalinta ya ajiye yana faɗin.
"Ammie Waya ce na kawo muku domin zan koma Kano gobe,kuma ina so idan na koma in riƙa ji daga gareku kada a maimaita er gidan jiya."
Ɗan Jim tayi sannan ta ce.
"Waya Ashiru? Kuma Wayar ma irin wannan babba haka?"
Ɗan ƙara sadda kan shi ya yi ƙasa yana faɗin.
"Ba komai Ammie... Ai ba wani abu bane, kunfi ƙarfin haka a wurina."
Daga haka ya miƙe yana mana sallama ya wuce waje. A hankali cikin jin ba daɗi a raina na biyo bayan shi har bakin Mashin ɗinda ya saba zuwa da shi muka tsaya, muryata a sanyaye ba tare da sanin mi nake ji ba na ce.
" Yanzu Yaya Ashiru idan ka tafi sai yaushe kenan?"
Murmushi ya yi ya ce.
"Ban sani ba Beenafah, amma dai ni na san ba zan iya jure nisa dake ba, tabbas dole zan dawo..."
"Allah ya kai ka lafiya yasa a dawo lafiya.."
"Amin. Ina Layina da na baki?"
Zaro idona na yi ina mai jin wani irin ba daɗi a raina na ce.
"Yana Wayar Ya Jafaru kuma ya tafi Zaria."
Wani murmushin gefen baki ya yi yana kallona ya ce.
"Wane ne wannan Ya Jafarun? Ku en uwa ne?"
"Eh to, haka zan ce dai, su ɗin maƙotanmu ne, ga gidan su nan..."
Na faɗa ina mai nuna mai gidan su sannan na ce.
"Tun da muka dawo unguwar nan da su muka fara haɗuwa, kuma suna da kirki sosai, hakan yasa sai muka zama kamar en uwa."
Jinjina kansa ya yi yana wani kalar murmushi ya ce.
"OK. Ba damuwa, akwai layi a ciki na yi mata caji na yi komai, zan riƙa kiran ku ina jin halin da kuke ciki."
"To Allah ya tsare hanya, ina gaida su Ayya."
Daga haka ya haye Mashin ɗinsa yana yi yana kallon gidan su Jafaru tare da tariyo duk abinda ya riƙa yi masa a cikin ƙwaƙwalwarsa. Tun ranar da ya fara zuwa gidan tun daren ranar ya cire Layin ya yasar daga wayarsa, domin duk ya kira ce masa ake a kashe take har yau kuwa.
Ni dai ina nan a tsaye har sai da ya ɓacewa ganina sannan na koma cikin gida.
Cike da zumuɗi na ja wayar na buɗeta,Infinix ce touching screen mai kyau sabuwa dal da ita.
Kunnawa na yi ina ta latsawa cike da farin ciki. En ajinmu a islamiyya kawai nake tunawa su Hafsa waɗanda mafi yawancinsu suna da Waya, sai kuma su Munira. Camera na shiga na fara Selfie ina yi ina dariya kamar wata taɓaɓɓiya.
"Beenafah!"
Waigowa na yi na kalli Ammie jin ta kira Sunana na ce.
"Na'am."
"kina ganin karɓar wayar nan ya yi Beenafah?"
Ɗan jim na yi sannan na kalle ta fuska cike da neman ƙarin bayani na ce.
"mi kika gani Ammie?"
"Ba komai, kawai dai wani abu nake dubawa..."
"Ammie fa kinji cewa ya yi so yake ya riƙa ji idan muna lafiya."
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta jinjina kanta ta ce.
"Haka ne kuma. Allah ubangiji yasa mu dace."
"Amin. Tashi na yi na shirya tsab cike da zumuɗi na fito da jakar Islamiyyata na ɗauko wayar na saka a jaka domin tafiya da ita.
Ammie dake fitowa daga ɗaki ne ta kalleni ta ce.
" Beenafah ina wayar nan take?"
Kallon jakata na yi sai kuma na kalle ta na ce.
"Gata nan a Jakata."
"Ciro ta ki ajiye a ɗaki, daga Islamiyya har gidan aikin ki ban amince kije da ita ba."
A hankali na juya na shige ɗakin na ajiye ta akan Katifa na fito na wuce.
Da dare bayan na yi sallar Isha Ya Hamza na shigowa na ɗauko wayar na nuna masa sannan na ce ya saka mini numbern Ya Jafaru.
Jujjuya wayar ya yi a hannunsa ya jinjina kai yana ƙara kallon wayar ya ce.
"Iyyeh! Infinix! Lallai yarinya kice kin Faso garin..."
Cike da jin ya wani fasa mini kai na fashe da dariya na ce.
"Yaya Ashiru ne ya siyo mini ita."
"Gaskiya ya yi ƙoƙari..."
"Yi sauri ka saka mini Numbern Ya Jafaru dan Allah na kira shi kada kaje ka rigani faɗa masa nasan halinka."
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM*
*OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
*PAGE 24*
Yana saka mini numbern ba ɓata lokaci na kira Ya Jafaru cike da farin ciki na kara a kunnena.
Ina jin ya ɗaga na buga wani irin ihu tamkar zan fasa masa dodon kunne na ce.
"Ya Jafaru na yi Wayaaa! Yaya Ashiru ya siya mini waya"
Zaune yake akan gadon sa a hostel da tarin Handout a gabansa, daman kuma already an wuce shi a lectures na tsawon sati biyu sannan ya yi joining na su.
Lokaci ɗaya ya miƙe tsaye tamkar wanda aka tsikara da allura jin wata irin mummunar magana...
"Hallo! Ya Jafaru kana jina??"
Cikin wani irin ɓacin ran da har yasa ya kasa controlling kansa ya buga mini tsawa da faɗin.
"Akan me to zai saya miki Waya? Ban ce kada ki tsaya saurarar kowane shashasha ba Beenafah?"
Cike da mamaki na ce.
"Ya Jafaru Yaya Ashiru fa na ce maka..."
"And so! Akan mi zai saya miki Waya? Akan wane dalili?"
"Ya Jafaru ba fa wani abu ba ne, Kano zai wuce shiyasa ya siya mini..."
"Uhm! To na ji!"
Daga haka ya katse kiran wanda ni a tunanina network ne, hakan yasa na sake gwada kiran numbern tasa amma kuma sai aka ce mini wayar a kashe take.
Kallon Ya Hamza na yi sai kuma na kalli Ammie wacce gabaɗaya hankalinta ya ɗauku yana kan Bahrain da Farisa suna magana. Ganin hakan yasa na kalli Ya Hamza na ce.
"Ya Jafaru fa faɗa yake akan Wayar nan. Daga jin yanda yake magana bai ji daɗin ta ba. Ko kuma dai akwai abin da yake damuna? Saboda ba haka yake ba."
Miƙewa ya yi bayan ya gama cin abincinsa ya jinjina kansa yana faɗin.
"Wata ƙila akwai abin da yake damunsa dai kam.....Ni na wuce sai da safe."
Game muka shiga bugawa a wayar ni da Bahrain, bayan kuma wani ɓangaren na zuciyata cike yake da tunanin abin da ya Jafaru ya yi. Muna nan daga nan na ɗan yi wasu aikace-aikace sai muka je muka kwanta domin Yaya Ashiru bai kirani ba, nima kuma ɗin ban yi tunanin kiran sa ba. Washe gari ina tashi na yi Sallah na ɗauko wayar na yi ɗan latse-latsena wanda ko Azhkar ban samu na yi ba akan ɗoki saboda dannar wayar, bayan na ga lokaci ya tafi na ajiye na je wurin shirin tafiyata bayan na kambala duk aikinda ya kamata na fice zuwa gidan aikina.
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 67