Share this page
To! Ni dai gaskiya na so ya Auri Sabila tun da dai ita ce wacce muka sani, amma kuma ɗan yau nasan baka isa ka shiga gaba da al'amarin shi ba,saboda haka nima na amince amma dai ba don raina ya so ba." Babu wanda bai dara ba a wannan amsar ta ƙarshe da Ayya ta bada, sannan daga ƙarshe Yaya Nura ya ce. " To abu yayi kyau, kuma In Sha Allahu zan tattauna da su Alhaji Nasiru suma (cewa da sauran yuyyunsu da kuma en uwan su) nan da sati biyu zamu kai ƙarshe, gabaɗaya zuwa wata ɗaya, sai mu zo muje gidan wurin nema masa ita. Saboda haka gobe a tare zamu koma da kai ƙafata ƙafarka, ina so zan tafi ɗauko kaya, dole za ka tsaya a Shago.... " Wata Hararar Umma ta sake jefa mishi sannan ta ce. " To yanzu sai na gani kuma idan haƙurin wata ɗaya ne ba za ka iya ba, tunda har an yi wannan maganar ina so ka tsaya ka fuskanci kasuwancinka." Tamkar wanda aka zarewa lakka haka ya gyaɗa mata kai a hankali ya tashi ya bar ɗakin. Can wajen ƙofar gidan ya fice gabaɗaya yana nazari. Shifa wallahi notukan kanshi ma sun kwance a halin yanzu, ya kasa rarrabe cewa shin a yanzu farin ciki yake ciki ko kuwa. Auren Beenafah fa akace za'a nema masa amma kuma bai taɓa furta mata cewa yana sonta ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Abin da ya shiga nanatawa kenan yana mai samun wani ɓaragurbin tunane daga wani ɓangare na zuciyarsa cewa to idan ta ce ita bata son shi da aure fa?? Tambayar kan shi ya fara na cewa to shi ɗin yana sonta kuwa? Duk da tsoro ne fal a cikin zuciyar sa amma hakan bai hana mishi murmusawa ba a lokacinda ya tsinci kanshi da yiwa kansa tambayar.    Tabbas yana sonta yana yi mata wani son da baki ma ba zai fasalta shi ba. Wayarshi ya zaro daga Aljihu ya duba agogo. Ƙarfe goma sha ɗaya saura na dare, saboda haka lokacin kiranta ya wuce a gareshi amma kuma magana ta gaskiya ba zai iya kai wa Magribar gobe ba tare da ya bayyana mata halin da ake ciki ba. Hakan yasa ya tura mata text da cewa dan Allah gobe ta yi haƙuri ta tafi da wayar wurin aikinta yana so ya yi wata magana da ita mai matuƙar muhimmanci.                          ***** Tun a daren jiya, da mamakin rashin kiran Yaya Ashiru na kwana a raina har gari ya waye. Ina yin sallah na janyo wayar da sunan yin azkhar ɗinda nake yi wanda yake Application ne mai zaman ƙanshi a wayar kwatsam sai ga text ɗin Yaya Ashiru na gani. Na daɗe tsawon lokaci ina jujjuya maganar a ƙwaƙwalwata sannan daga ƙarshe kawai na yi murmushi na tashi na yi duk abin da zan yi sannan da zan tafi na maƙale wayar a hijabina abin da ban taɓa yi ba. Wato yi wa Ammie rashin gaskiya da kuma saɓa maganarta, wanda ni har ga Allah ban yi hakan da wata manufa ba, kawai dai na ƙosa ne in ji shin wacce magana ce yake so ya furta a gare ni,domin ba zan iya jira har Magrib ɗinba. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus.... *PAGE 25*   Ina isowa ko zaunawa ban yi ba na wuce na yi duk aikinda ya kamata na yi, daman kuma gashi Hajiya bata nan ta tafi Dubai kamar yanda ta saba tafiya wasu lokutan sannan Aunty Ziza ma bata ƙasar kamar yanda Su Munira suka faɗa mini, shiyasa muke zaune muna cin karenmu babu babbaka,musamman saboda babu wasu ayyuka akanmu masu yawa. Muna zaune a ɗaki bayan mun kambala karin kumallo suna firar su ni kuma ina zaune a gefe riƙe da wayata ina game Ina murmushi, musamman da na ji irin firar da suke wacce a yanzu ita suka sakawa gaba tunda Haula ta yi saurayi, wani ne ya zo har gidan yace yana sonta shi ne fa Hajiya ta bashi dama akan ya riƙa zuwa tun da daman iyayenta sun yi magana. Na yi nisa sosai a tunani wanda har yasa na daina fahimtar abin da suke faɗi na ji Munira ta daki cinyar ƙafata tana dariya ta ce. "Ga masu yi nan ba'a magana...." Tayi maganar tana mai fashewa da dariya sannan ta sake kallon Haula sai kuma ta kalleni ta ce. "Beenafah ta raina mana wayau Haula, duk ana zancen soyayya sai da tayi shiru alhali tafi kowa ƙwarewa..." Ɗan zaro ido na yi ina mai nuna kaina da yatsa na ce. "Ni wai? Gaskiya a'a.." Jinjina kanta ta yi idonta still a cikin nawa ta ce. "ƙwarai kuwa.... Shin kina lura da kanki kuwa musamman a 'ƴan kwanakin nan Beenafah ?" Cikin rashin fahimta na girgiza kaina na ce. "A'a! Miye ya sameni Munira? Ko na rame ne dan Allah?" Wata dariyar suka kwashe da ita har sai da suka sakani murmusawa nima sannan Munirar ta ce. "Ki ci gaba da rainawa kanki hankali wai ke kina rai na mana..." "Wallahi da gaske nake miki Munira..." "To naji, ba zancen rama nake miki ba, zance ne na kin zurma sosai a cikin soyyaya wacce a yanzu har baki iya ɓoyewa ko a gabanmu ne musamman a 'ƴan kwanakin nan." Saurin girgiza kaina na yi na ce. "A'a wallahi ni kam...to mima yasa kika ce haka? Soyayya fa! Ni bana soyayya da kowa..." Dariya Haula ta yi ta ce. "A taki haukar kenan? Amma ko makaho ya shafa rayuwar da kike ciki a yanzu yasan cewa kina cikin shauƙi da begen soyayya." Itama Munira murmushi ta saki tare da ɗan ƙara matsowa kusa dani tana faɗin. "A gabanki fa saurayinki Ashiru ya so ya mareni amma kuma ba ki nuna kin damu ba, haka kuka riƙa rawar jiki tamkar za ku haɗiye juna a wannan ranar wanda babu komai a cikin idanun ku sai zallar soyayya..." Still cikin rashin yarda na sake girgiza mata kaina ina mai jin wani iri na ce. " Yaya Ashiru ba saurayina ba ne Munira, shi ɗin tamkar yaya yake a wurina... " Saurin katseni ta yi tana wani jinjina kai ta ce. " Oh! Haka ne.. To bari in gaya miki Beenafah, ita Soyayya ba lallai sai an faɗa miki da baki ba. Akwai abubuwan da zuciya ke yi da kanta wanda idan kika fara jin su, to ki sani kin faɗa a cikin soyyaya." Sake gyara zamanta ta yi da kyau ganin da gaske na bata dukkan nutsuwata ta ci gaba da cewa. " A duk lokacin da aka kira sunan wanda kike so to tabbas sai zuciyarki amsa fiye da yadda kike ji idan an ambaci wani daban, ko kuma idan kinji sautin muryar sa koda a waya ne za ki ji numfashinki ya ɗan tsaya, sai ki yi ta murmushi ba tare da wani dalili ba. Idan kika yi fushi da shi sai ki ji gaba ɗaya duniyarki ta ƙuntata, da zaran kuma ya furta miki kalmar ban haƙuri, sai ki ji zuciyar ki ta huce tamkar ruwan sanyi. Idan kika ga yana magana da wata ko kuma shi  yaga wani wanda ba shi ba yana magana dake, sai ya ji wani abu ya motsa a ƙirjinsa na tsananin ki shi tamkar ana hura masa huta,amma kuma da zaran ya kalli kyakkyawar fuskarki mai lallausan murmushi sai ya ji ya wuce." Shiru na yi ina mai ƙure ta da idanuwana yayin da ƙwaƙwalwata ta shiga cikin tsananin ruɗani da neman ƙarin haske, domin babu abinda nake hange da tunanowa sai Yaya Ashiru, idan haka ne tabbas ina cikin ruɗani. hakan yasa ban yi nauyin baki ba tambayeta cewa. " Munira yanzu kina nufin waɗannan abubuwan duk alamomin soyayya ne?" Jinjina kanta ta yi ta ce. "Eh Beenafah. Wannan shi ne so wanda ba dole sai an furta shi da baki ba. A kullum za ki ga yana neman abubuwan da zai yi don kawai ya ganki a farin ciki, kullum yana so ya ji muryar ki, da supporting ɗinki ga dukkan abin da kika sakawa gaba." Hannu na saka a gefen zuciyata na ɗan lokaci sannan na sake kallonta na ce. "To idan haka ne, miyasa mutum baya  iya fitowa ya furta kenan?" "Saboda soyayya ba ta neman izini Beenafah! Ita ɗin tamkar iska ce mai shigowa sannu a hankali har tayi nasarar mamaye zuciya daga ƙarshe,ta gama nannaɗeki da farin ciki,baƙin ciki, damuwa, kewa, kishi ba tare da kin fahimta ba." Kaina na sunkuyar ƙasa ina mai wasa da yatsun hannuna lokaci ɗaya kuma ina jin wani abu na daban a ƙirji na ce mata. "To idan har ni waɗannan abubuwan sun nuna alamar na kamu da soyayya to shi kuma fa?" Miƙewa ta yi tsaye tare da jinginawa jikin wardrobe idanunta cikin nawa  ta ce. "Sun ma fiki kamuwa Beenafah. Ashiru da Jafaru dukkan su suna tsananin ƙaunar ki. Na jima wannan al'amarin yana dukan zuciyata, sannan kuma, ban san mi zai faru zuwa gaba,amma dai ki kula, domin soyayya kamar wuta ce wadda idan har kika kuskure, to tabbas za ta ƙone ki ƙurmus, idan kuma kika yi nasara a cikinta;tana iya zama hasken da zai haskaka maki hanyar rayuwa har ƙarshen numfashinki......" Mun jima Munira na mini wankin ƙwaƙwalwa wanda na kwashe tsawon lokaci ban ɗauki haske akai ba sannan daga ƙarshe suka fice wurin aiki suka barni nan. Kwantawa na yi a ƙasa na yi lamo! tamkar ruwa sun cinye ni domin na kasa yin wani kataɓus. Babu abinda nake ji da gani idan ba mutum biyu ba. Mutum biyun da suka tsaya mini matsayin inuwa da garkuwa. su ɗin mutane ne masu matuƙar muhimmanci da nake tunanin su ɗin yayyune a gare ni, ashe duk wannan soyayya ce.?? Wani irin zabura na ƙara yi na miƙe zaune ina wani girgiza kaina jin yanda wasu hirarrakinmu da kuma wasu actions ɗin su both Ya Jafaru da kuma Yaya Ashiru suka shiga dawo mini beat by beat waɗanda a yanzu suke alamta mini cewa tabbas suna nufin soyayya a gare ni. Zuciyata ce ta ƙara tsinkewa har ban san lokacin da wasu zafafan hawaye suka silalo mini ba musamman dana tuna cewa wai Yaya Ashiru yace yana so ya sanar dani wata magana. To wace magana ce wannan yake so ya faɗa mini wacce ba zai iya jira har zuwa dare ba?? Ina nan kwance tsawon lokaci sannan daga baya Haula ta shigo ta kalleni ta ce. "Beenafah! Ko kinyi bacci ne?" A hankali na yunƙura na miƙe zaune ina ma kallonta da idanuna waɗanda suka canza launi tsabar ruɗanin da nake ciki murya a ƙasa na girgiza kaina na ce. "Ba bacci nake ba. Ya akayi?" "Yanzu Aunty Labiba ta kirani tace akwai baƙin da za su zo yau ɗinnan, saboda haka dole muna da buƙatar yin girke-girke kamar yanda ta buƙata. Sannan kuma ta ce Uncle Ishaq wai shima yana hanya ya ta so daga Sokoto, yace dan Allah a yi masa girki shaf-shaf domin yau yake so ya wuce Katsina. To shine nake so ki je ki yi na Uncle Ishaq ɗin tunda ba mai yawa ba ne mu kuma sai muji da wannan ɗin na baƙin Hajiya." "Waye Uncle Ishaq??" Maimakon ta bani amsa kai tsaye, ba ta yi hakan ba, kawai dariya na ji ta sheƙe da ita sannan daga baya ta tsahirta ta ce. "Hajiyar gidan nan, to ƙaninta ne ɗan autan su. Mugun ɗan renin hankali ne na ƙarshe." Jinjina kaina na yi sannan na ce. "To mi zan dafa masa?" Juyawa ta yi ta nufi ƙofa tana faɗin. "Duk abin da kika ji za ki iya tunda shaf-shaf ya ce." Ko bayan fitar ta, na kusa minti biyar sannan daga baya na tashi na shiga toilet na yi fitsari sannan na wanko fuskata na fito na ɗauki wayar na wuce kitchen na fara aiki. Karon farko tsumayi nake na jiran kiran Yaya Ashiru, amma kuma a yanzu; fargaba nake ji ta rashin sanin dalilin kiran. ****** Lieutenant Commander Emraan Attahiru Araam. Shi ɗin Naval Officer ne (Sojan Ruwa). Yana aiki ne a Nigerian Navy Logistics Command, Kaduna state Nigeria. Yana daga cikin masu jagorantar rukunin sojoji, kula da kayayyaki, tsaro da kuma gudanar da ayyuka na musamman. Tun da ya fara aiki, a nan Kadunar yake tsawon shekaru, sai yanzu da ya samu transfer zuwa jihar Rivers State a kudancin Nigeria. Bayan ya samu takardar transfer sai kuma a ka haɗa mishi da takardar hutu na wata ɗaya domin samun lokaci da iyalin shi sannan kuma ya samu damar shirye-shirye na komawa sabon wurin aikinsa. Da wannan ya tattaro a daren jiya ya dawo Gusau, sai dai kuma; ta wata fuskar bai ga amfanin hutun da ya samu ba, domin Hajiya bata nan haka zalika Ziza itama bata ƙasar. Shiyasa ya ji abin yayi masa wani iri, duk da cewar Ziza ta tabbatar masa da cewa nan da sati biyu za ta dawo In Sha Allahu. Yana sauka gidan sa ko wanka bai tsaya ya yi ba, yana gama ajiye kayayyakinsa ya tattaro kawai ya dawo gidan Hajiyarsa wanda bai shigo gidan ba sai kusan sha biyu na dare. Hakan yasa babu wanda yasan cewa yana gidan har su Munira. Tun da ya dawo masallacin asuba ya koma bacci bai sake farkawa ba sai misalin sha biyu saura na rana. Yana tashi ya janyo wayarsa inda a nan yaga kiran Ziza kusan 5miss calls,sannan kiran Blood sis (Aunty Labiba) 2miss calls da kuma kiran Hajiyarsa shima 2miss calls. Ajiye wayar ya yi ya sauka daga kan lallausan gadonsa wanda tun na samartakarsa ne ya shige toilet ya wanke bakinsa da fuskarsa sannan ya fito ya saka wasu simple nic and shirt ya fito zuwa kitchen. Idan zai iya tunawa tun abincin da yaci a gidansa na Kaduna bai ƙara cin wani ba,saboda haka he need something to eat kafin Ziza ta ji ya zauna da yunwa ta fara mishi kuka. Tun da ya ƙara so ƙofar Kitchen ɗin ya ji sautin Muryarta mai cike da nutsuwa a hankali tana magana da alama akwai maganar da take mai muhimmanci. Ɗan ƙara stepping ya yi gaba kaɗan ya tsaya jikin ƙofar ba tare da ta sani ba ya harɗe hannayensa a ƙirjinsa ya tsurawa bayanta kallo wanda ita gaba ɗaya hankalinta ya ɗauku ga aiki da kuma magana a waya. Tun da na shigo Kitchen ɗin na fara aiki Yaya Ashiru bai kirani ba sai gab da ina batun kambala aikina. Sai da ya kira kusan sau uku sannan a na huɗu na yi picking a darare ina mai sakata a amsa kuwwa domin kada maganar ta hanani ƙarasa aikina cikin lokaci daman ga Haula sai zanzamata take wai Aunty Labiba ta ƙara kira. A yanda ya ji yanayina, sai hakan ya sage mishi gwiwa tare da zare mishi duk wani kuzarin da ya zo da shi domin bai taɓa ji na a haka ba. Juyin duniya ya yi dani akan in faɗa masa miye abin da yake damuna na ce mishi ba komai. Jin na kafe kai da fata ina faɗin ba komai yasa shi sauke ajiyar zuciya ya ce. "Ko in bar ki zuwa an jima idan kin shirya sai muyi maganar?" Girgiza kaina na yi tamkar yana a gabana na ce. "A'a! Kawai ni dai dan Allah idan ka yi niyyar faɗa mini kawai ka faɗa bana son jan rai, ba zan iya jira har daren ya yi ba." Jin irin amsata ya sa shi sadaƙarwa ya ce. "Ko na yi niyyar faɗa miki Beenafah sai inji gabana yana faɗuwa...dan Allah kada ki yi mini mummunar fahimta.." "In sha Allahu matuƙar dai ba ka kauce hanya ba ba zan yi maka mummunar fahimta ba, ballantana ma nasan halin ka nasan abin da za ka iya da wanda ba za ka iya ba.." Wani murmushi ya saki mai sauti wanda har ina iya jiyosa sannan ya ce. "Kin taɓa jin wani abu akaina kamar yanda ni ma nake ji Bee..." Da shigowarsa Kitchen ɗin da fisgo wayar daga inda na ajiye ta ya rotsa a ƙasa duk ba'a yi second talatin ba. Tamkar wacce ta yi mummunan gamo, haka na shiga ja baya hankalina a matuƙar tashe, jikina sai wani ciccira yake domin ban san da wanzuwarsa ba a wurin. Shi kuma cikin wani irin hargagin da bai san ya iya shi ba ya watso mini idanunsa waɗanda suka kaɗa lokaci ɗaya suka canja launi ya ce. "Daman abin da kike yi kenan? I... I were thought cewa you are too small for all this that's why na nisanta kaina da ke har zuwa lokacin da ya kamata....I thought yanda kike baya-baya kina yin kamar kina tsoron mutane lokaci kike buƙata domin ki gama sanin miye rayuwa?.....but ashe ni kika mayar sauna ko!!!" Ban san lokacin da na fashe da wani irin kuka ba, a firgice na faɗa jikin gini tare da runtse idanuwana domin tsawar da ya daka mini ba ƙaramin tsoratani ya yi ba..... Ban ƙara tsorata ba, sai da ya jimƙo tsintsiyar hannuna ya wani fisgoni gab da gab ya ce. "Buɗe idanunki ki kalleni... Buɗe idanunki ki kalleni na ce!!!" Cikin tsananin tsoro da ruɗani na yi saurin buɗe idanun nawa ina kallon shi still ina kuka na ce. "Nannn....na kalle ka! Ka yi haƙuri wallahi na kalle kaaa!" Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya sake buɗesu a cikin nawa ya ce. "Ni Emraan! Tun a ranar farko ban yi kuskuren kiran ki da mata ta ba, domin ni ne nan wanda zan aure ki. Ban ja baya don Labiba ta shata mini layi ba... Na yi baya ne don jiran lokacin da ya da ce." Yana gama faɗin haka ya yarfar da hannuna kawai ya juya ya yi tafiyar sa. Ganin da gaske ɗin ya tafi, yasa a gigice na ruga na koma ɗakinmu tare da duƙunƙunewa sosai na shiga raira wani sabon kuka. Ƙwaƙwalwata ta rikirkice a halin yanzu. Tambayar kaina na fara, cewa; Shin wannan ɗinma da gaske ne yake faruwa ko kuma ƙwaƙwalwata ce ta fara samun matsala? Emraan! Emraan ni Beenafah zai ce wai ni zai aura? To ta ya ya ma??? Yah Allah ina roƙon ka, idan ma bacci nake ka farkar dani daga wannan mummunan mafarki da na tsinci kaina a ciki. Wace ce ni da har Emraan zai yi wannan furuci a gare ni? Aunty Zi...Ziza!!!    Ji na yi hankalina ya sake yin wani irin ƙololuwar tashi tunawa da Aunty Ziza da na yi. Ya ilahiy! Rabbi kasa wannan ya zamto mafarki a gare ni, domin haƙiƙa na fahimci so yake ya katse mini hanyar neman abinci na wanda wallahi sam ban shirya ma hakan ba. Ina nan a kwance na ji shigowar Su Munira suna faɗin in tashi in shirya abincin a table Idan na kambala, sai dai kuma;shiru ba amsa domin ba zan iya kallon su ina cikin wannan yanayin ba.   Haula, ganin yan da Aunty Labiba ta matsa mata da kira, dole hakan yasa ta nufi kitchen ɗin da kanta yayinda Munira ta tsaya a kaina tana tuhuma wai ko akan firarmu ta ɗazu ce yasa na shiga damuwa wanda ni dai ƙala ban ce mata ba. Haulatu na shiga Kitchen ɗin turus ta ja ta tsaya ganin waya tarwatse a ƙasa ta yi ɗai-ɗai-ɗai. Duƙawa ta yi da sauri ta ɗauko wayar ta shiga dubawa. "Tabbas wannan wayar Beenafah ce da ta zo da ita. To ya akayi haka ta faɗo ta tarwatse? Gaskiya kam dole ta yi kuka, ashe abinda ya faru kenan. Ko ya akayi har ta yi wannan irin mummunar faɗuwa?" Daga haka ta tattara ta ajiye a gefen drawer sannan ta yi sauri ta shirya abincin tunda daman already na kambala kaɗan ne ya rage. Bayan ta kai abinci sai ta koma kitchen ɗin ta ɗauko wayar ta dawo ɗaki cike da alhini tana nunawa Munira. A tare suka shiga janjantamin tare da bakin cewa in yi haƙuri ƙaddarori ne. Ni dai ƙara lafewa na yi kawai ina mai yin godiya ga Allah wanda yasa fashewar wayar ta zama dalili a tsakanina da su, domin kuwa, ko kwana za su yi suna tambayata wallahi ba zan iya faɗa musu wannan abun da ya faru ba. Da ƙyar na samu na rarrafa na yi sallah sanadiyyar wani irin tsananin ciwon da kaina ke yi ta dalilin wannan kwamacalar da na tsinci kaina a ciki. Bayan na gama na sake komawa na kwanta ban farka ba sai kusan ƙarfe huɗu saura. Da wani irin zazzaɓi mai zafi na farka har sai da su Munira suka bani magani na sha sannan na samu na lallaɓa na tafi gida cikin wata kalar sabuwar fargabar da ban san mi zan cewa Ammie ba game da wayar. ******    Gidan Daddy ya kacame da farin ciki da guɗa na mashahurin lefen da aka kawo na su Hassana, lefe ne abin da ake kira lefe. Farin cikin Mummy ya kasa ɓoyuwa domin yau ne ta ƙara tabbatarwa cewa lallai auren nan yinsa za'a yi because an riga an saka date nan da wata biyu. Kuma an riga an tsara cewa Idan auren ya rage saura sati biyu to za su ɗunguma su koma gida Zamfara both familyn Daddy da na Alhaji Mansur Anka duk da cewa ita Mummyn ba haka ta so ba, domin ta ci burin yin bukin ta anan Abuja, buki wanda sai guda-guda ne suka taɓa gudanar da irinsa kaf a faɗin ƙasar. Sai dai kuma wannan burin nata ba zai cika ba domin Alhaji Mansur ya nuna musu yin hidima a gida tafi sauƙi da kuma ƙarfafa zumunci, hakan shi ne ke bayar da duk wata dama ga danginka su samu halarta da kuma yin participating yanda ya kamata. Idan kuma suka ce su za su bukin su a Abuja su kuma suna Zamfara abun ba zai yi daɗi ba. A wannan matsayar suka amince dukkan su wanda Mummy ta shiga yin shirye-shirye babu kama hannun yaro. Kuɗi ta shiga narkawa ba ƙanana ba tun daga kan kayan ɗaki, kayan buki da komai da komai. Duk budurin nan da ake Hassana Sam bata cikin farin ciki domin a yanzu ne ma take ƙara jin tsanar Ameer fiye da can baya. Tun suna yin abin su tsakanin ta da 'ƴar uwar ta har Husaina ta kai ga sanar da Aunty Aysha domin su samu su shawo kan Hassana ta yarda ta amince. A yanda su ka ga Mummy ta ɗauki al'amarin auren nan na su da girma tabbas idan Hassana ta ce ba za ta amince ba komai na iya faruwa da Mummy. Hakan yasa suka tsaya a kanta ba dare ba rana amma kuma fir! Ta shafawa idonta toka ba ta ji bata gani. Bata ƙara shiga tsananin tashin hankali ba sai da taga jiya an kawo lefen nan an saka rana. Hakan yasa ko abinci ta kasa ci, babu abinda take idan ba kuka ba. Tana kwance akan gadonta Biba ta shigo ɗauke da kayan Breakfast ta ajiye a saman wani glass table ta ce. "Hassana ga abincin nan Husaina ta ce na kawo mik..." Wani irin ihu ta daka mata tare da miƙewa zaune tana mai ƙara fashewa da kuka ta ce. "Ba zanci ba Biba!......Ki ɗauke ki fitar da shi yanzu.." Da sauri Biba ta ɗauke trayn ta juya ta koma kitchen inda ta tarar da Husaina ta faɗa mata yanda suka yi da ita. Da kanta ta amso abincin ta dawo ɗakin ta ajiye sannan ta zaune gefenta a hankali ta dafa kafaɗarta ta ce. " Ki yi haƙuri mana dan Allah Hassy, rabon ki fa da abinci tun jiya..." Cikin wani gunjin kuka ta wai go ta kalleta cike da karyewar zuciya ta ce. "Hussy na rantse miki da Allah idan har ban auri Salman ba komai zai iya faruwa dani.... Sannan matuƙar aka

Chapter 20 of 67