Share this page
ta fafutukar haɗa abincin tarbar Ya mohaa. Sam ni ban ji wani ɗoki ba, duk yanda Hairi ke ta surutunta wanda mafi yawa duk akan zancen aurenta ne da Suhaib gabaɗaya ni hankalina baya wurin. Tunanin Ya Jafaru ne ya yi mini kane-kane a zuciyata, ji nake tabbas ina so in ji minene abin da yake so ya sake sanar mini. Kenan bibiyata yake ko me? Ta ya ya yasan cewa na je gidan Aunty Labiba? ******* Jafaru kuwa, tun daga ranar da suka baro gidan su Hafsa ya shiga bibiyarta ba dare ba rana. Ko kaɗan ya hana kansa sukuni. Tunda ya lashi takobin sai ya ga bayan wannan auren na Beenafah ya rasa nutsuwarsa. Tunda ya kira ta ya ji cewa tabbas kalamansa sun yi tasiri a kanta yake cikin tsananin farin ciki. Take ya fara sabon lissafi domin ya ƙiyasta ba jimawa za ta fito ta bar gidan Mohaa, shi kuma daga zaran ta fito a wannan lokacin...zai tayar da ƙayar baya kamar yanda Baba Kali ya bashi shawara wanda dole su Baba su goya mishi baya kuma su bar shi ya aureta. Koda ta je gidan Ammie akan idonsa har ta gama wuninta ta koma gida. Hankalinsa ne ya tashi sosai jin cewa wai tafiya za ta yi ta koma Dubai. Haka yasa ya biyo ta har gidan Labiba, da hope ɗin cewa zai haɗu da ita ya ƙara jaddada mata kalamansa, sai dai kuma, haƙar sa ba ta cim ma ruwa ba,domin taƙi ba da haɗin kai. Hakan yasa ya biyo ta gida, wani irin farin ciki ya ji ganin ta dawo gidanta, kuma ya tabbatar cewa mijin na ta bai dawo ba, domin da ace ya dawo tabbas ba zai taɓa bari wani driver ya tuƙata ita kaɗai ba tare da shi ba. Sai da ya bari aka gama sallar magriba sannan ya je kai tsaye zai shiga gidan. Masu gadi na tare shi yace shi ɗin ɗan uwanta ne ya zo ne yi mata sallama domin ya ji ance gobe za ta koma. Ganin ɗaya daga cikin security ɗin ya gane shi domin a tare suka zo har da zu Ammie a ranar, sai bai sha wata wahala ba suka bar shi ya shige. Yana shiga ya tsaya nesa da gidan tare da tunanin abin da ya kamata ya yi. Idan ya shiga gidan mi zai ce mata? An ya ma za ta saurare shi kuwa? Yana nan yana shawara kawai ya ji ƙarar motoci, na'urori sai amsawa suke har aka gama wangale gate ɗin. A gigice ya faɗa tsakankanin flowers ya kwanta tsabar yanda ya gigice lokaci ɗaya. Bai ƙara ruɗewa ba sai da ya hango sa ya fito daga mota cikin nutsuwarsa, ga shigar nan ta manyan kaya wacce ke ƙara masa ƙima da ƙwarjini...Kishi ne kawai ke sa yana kiran sa da tsoho, amma ko makaho ya shafa yasan cewa wan can sam bai kai a kira shi da wannan kalmar ta tsoho ba duk da cewa shekaru sun ja, domin jikin sa ƙyanƙyan yake tamkar wani ɗan 35yrs. Ga sajen nan baƙi wulik wanda yake ƙara fito masa da kyaunsa uwa uba ga hutu da jindaɗi. Bai ƙara ruɗewa ba sai da ya hango yanda securities ɗinsa wanda suke da kusan kalar Kaki uku suka ɗauki saiti tare da samun kowane lungu da saƙon da ke gidan suka ƙame domin bada kariya da gidan da kuma lafiyar mutanen gidan. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Wannan ita ce kalmar da ya shiga furtawa ba ƙaƙƙautawa yana mai ƙara lafewa cikin flowers ɗin ganin irin bala'in da yake gabansa. Shi yanzu ya zai yi kenan? Ya zai yi ya fice daga gidan nan? Dama ace tun farko da suka shigo ya wuce direct cikin gidan wata ƙila ya samu mafita idan ya ce bankwana ya zo mata. To amma wannan wace haukar ce ta hau kan shi da har zai ɓoye haka kamar wani ɓarawo? ******* Ya mohaa kuwa, yana shigowa Hairi da ke zaune tare da Biba ta maƙalƙaleshi tana mishi sannu da zuwa. Bayan sun gama gaisawa Biba ta gaishe shi sannan ya wuto direct ɗakinda nake. Zaune nake akan Sallaya wacce tunda na kambala sallar magrib ɗin na kasa matsawa ko'ina, sabon aikin da Ya Jafaru ya samar mini shi na zauna ina yi wato tunani wanda ko cikakken Azhkhar ban samu na yi ba. Ina ganin ya shigo na miƙe tsaye da sauri ina kallon sa. Wani irin kallo ya bi ni da shi mai cike da zallar karaya kamar yanda nima nake yi, mun shafe kusan minti biyu a haka sannan daga ƙarshe ya ware hannayensa cikin sagewar gwiwa, alamar na zo. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* *PAGE 52* Yau da zuciyata take cikin mugun yanayi, sai naga ya koma min wani mutum na daban. Ƙwarjininsa da kuma nauyinsa da nake ji, sai na ji sun ƙara nauyi sosai a Idona. Ban sani ba ko don akan shi kaɗai na fara sanin mine ne soyayya, maimakon na ji haushinsa na ji cewa ya fice mini a rai, sai na ji ma tamkar wata sabuwar soyayyar ce aka sake dunƙulawa aka naɗe ƙirjina da ita, tsananin kishin sa sai na ji na ninku a raina fiye da yanda na ke a 'ƴan kwanakin nan. Wata zuciyar ingi zani take da cewa na tafi garesa yayin da wani ɓangaren ke bina da mugun gargaɗin cewa kada na yarda na yi wannan gangancin, domin idan har komai da yake mini duk na ƙarya ne ba da gaske yake ba...mi zai sa nima na riƙa mutuwa akansa ina jin tamkar shi ne ɗan autan Maza? 'He's just using you and He's just pretending...Har abada ba zai taɓa son ki ba saboda matsayinsa da na ki ba ɗaya...lokaci kaɗai yake jira, da ya samu yanda yake so zai auro wata wadda tafi komai, ke kuma a lokacin saki zai biyo na wulaƙanci. Waɗannan su ne kalmomin Ya Jafaru da na tuna wanda lokaci ɗaya na juya masa baya ina mai jin wani irin raɗaɗi a zuciyata na shiga girgiza kaina alamar ba zan iya zuwa gare shi ba, kawai sai na fashe da kuka. Mohaa ya shiga cikin wani tsananin tashin hankali da gigitar da bai san ma lokacin da ya watsar da duk abin da yake hannun sa ba, wata irin super ya yi ya iso gareni tare da janyoni jikin sa tamkar zai fashe da kuka ya ɗago fuskata tare da zuba mini idanu kawai yana kallona, ban kalle sa ba, domin ban san ta ya ya zan fara kallon idonsa ba, duk da cewa ban kallesa ɗin ba, na lura da yadda duk ilahirin jikinsa ya ɗauki ƙyarma tamkar wanda ake wa azabar ƙanƙara. A wasu ɗabi'unsa da na laƙanta;yana da wahala idan wani abu ya faru na rashin daɗi ya iya buɗe bakin sa ya yi magana kai tsaye, a duk lokacin da wani abu zai zo mana, sai da ya sanyani cikin jikinsa ya rungumeni na tsawon lokaci, sannan daga baya ya nemi jin abin da yake faruwa, wanda ya yi imani da cewa, a duk lokacin da wanda kake ƙauna ya shiga wani hali to abun na farko shi ne ka fara bashi kulawa ta hanyar musayar saƙon zuciya da kuma body language, matuƙar kuɗin masoyane na haƙiƙa...to tabbas kaso casa'in na daga cikin azabar da kake ji da nauyi a ƙirjinka za su ragu. Ganin da gaske na ƙi bashi haɗin kai yasa ya nemi ya rungumeni domin ya bani lokaci,sai dai kuma, yanda na ture shi ne ya ƙara mugun ɗaga masa hankali a gigice ya ce. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Beenafah! Mine ne yake faruwa haka? Mi nai miki da zafi haka?....kinga..Dan Allah kada..." Cikin wasu irin zafafan hawaye na ɗago idona na kalle shi, sosai na ji wani irin tsoro ya kamani ganin yanda idanunsa suka kaɗa sosai suka canja launi tsabar tashin hankali da damuwar da suka cim mi shi a lokacin da bai yi aune ba. A hankali na shiga ja baya ina faɗin. "Kada ka zo kusa dani,..domin.." Maganar tawa ce ta maƙale, ganin irin kallon ya kafeni da shi wanda ko ƙyaftawa babu shi ne ya sanyani haɗiye sauran maganata...Zan iya rantsewa cewa tun da nake da tsawon lokaci ban taɓa karo da shi a irin wannan yanayin da yake ciki ba, kuma ko a mafarki akace zan gansa da irin wannan ɓacin ran da damuwa tabbas zan ƙaryata. Gabaɗaya cikin kalmomin da na tana da zan furta masa ni karan kaina na tabbatar babu ɗaya wacce za ta kasance alheri daga ciki... A raunane ya buɗe bakinsa zai yi magana kwatsam sai muka ji wata ƙara daga kusuwar ɗakin ta shiga amsawa alamar security alert. Wata ƙaramar hologram security device ce ta fito tamkar an yi amfani remote control wurin fito da ita, a hankali red light ta shiga ɓillawa tare da sakin wata murya irinta robot tana faɗin. "Intruder detected...i repeat intruder detected! We have discovered an unknown thief inside the house, can we proceed with immediate action or await further instructions.? I repeat intruder detected." Cike da rashin kuzari ya juya ya fita still hankalinsa tashe, a ransa faɗi yake Wane irin ɓarawo daga magaribar fari haka? Da ace cikin dare ne da tabbas ko waje ba zai leƙo ba zai ba su umarnin yin maganin sa yanda ya dace, to amma shigowarsa kenan ace ɓarawo? Sai dai idan akwai wani abin. Sulalewa na yi zuwa ƙasa abin duniya duk ya bi ya isheni, wannan wace irin rayuwa ce. Ni yanzu dan Allah mi ya kamata na yi? Shi ɗin fa ba yaro ba ne, at least ya kamata duk abinda zanyi na kwatanta ko? Miƙewa na yi a zafafe jin wani irin mugun tunani da ya ɗarsu a ƙwaƙwalwata lokaci ɗaya, tunawa da sanarwar security alert. "To idan Ya Jafaru ne ya yi haukar shigowa gidan nan fa? Innalillahi wa inna ilaihi!" Na furta da ƙarfi ina mai jin yanda kai na ke wani irin sarawa, lokaci ɗaya na ji kamar kaina na juyawa, tamkar na kife haka na ke ji...duk da haka ban sare ba, hakan yasa da gudu na runtoma na yo waje. Duk wani haske da ke gidan ya canja launi zuwa Red alamar danger mode Daga inda nake tsaye bana iya hango komai da kyau kasancewar naga yanda securities ɗin suka zagaye wuri ɗaya da bindigogi a hannunsu, sai Ya Mohaa da Hairi waɗanda ke tsaye dab da su da alama magana yake musu. Da gudu na ƙara so wurin domin na ƙara tabbatarwa da mike faruwa. Durƙushe yake akan ƙafafunsa, securities ɗin sun kewaye shi an rufe masa fuska an kuma ɗaure hannayensa ta baya. Duk da cewa banga fuskarsa ba, jikina ya gama bani cewa Ya Jafaru ne...tabbas shi ne domin na san shi farin sani da wannan rigar ta en ƙwallo. Wani irin bugawa zuciyata ta yi tsabar yanda na tsorata, bakina na rawa na ce. "Kuk..ku cire masa wannan ƙyallen na fuskarsa yanzu!" Ganin yanda hankalina ya tashi sosai yasa Hairi matsowa inda nake ta kama hannuna a tsorace tace. "Please Mummy calm down...kin san condition ɗin ki dan Allah ki yi a hankali." Da sauri suka cire masa ƙyallin. Da gaske kuwa Ya Jafarun ne. Da sauri na soma juya idanuna alamar tsantsar mamaki na ce. “JAFARU!!!” Ganin yanda wani daga cikin securities ɗin ya zage ya zabga masa mari ne ya sake ɗaga hankalina a gigice na ɗaga masa hannu na ce. “Ka daina dukansa! Ku sake shi yanzu-yanzu!” Cike da mamaki suke kallona sannan wani ya ce. "Ma'am...this man..." "I said you should let him go...matuƙar kuna son aikinku ya ɗore, to lallai ku sake shi ya tafi. Shi ɗin ba ɓarowa ba ne, Yayana ne." Na ƙarasa maganar cike da faɗa yayin da idanuna ke cike da hawaye tsabar tashin hankali. Jinjina kai Ya mohaa ya yi yana kallona, cikin wani irin sabon mamakina murya a ƙasa sosai ya ce. " Bibi...ki bari abi komai a hankali..." Duk da cewa a tsorace nake, hakan bai hanani ɗaga murya ba ina faɗin. "Tell them to let him go please...Kada ka bari su yi masa illa, wallahy shi ɗin ba ɓarawo ba ne." Umarni ya yi musu da cewa su sake shi tunda hakan na zaɓa. Ina nan tsaye har sai da suka kwance shi ya tashi kai tsaye ya fice daga gidan. Ina ganin ficewarsa na sauke wata irin ɓoyayyiyar ajiyar zuciya sannan kai tsaye na saka kai na shige ba tare da na ƙara kallon inda suke tsaye ba. Na jima a kwance akan gado shiru ina ta nazari akan wannan abun da ya faru. Ban san lokacin da na miƙe zaune ba jin wani sabon tunanin again da ya nemi ya zautar da ƙwaƙwalwata. "Tabbas Hairi ta taɓa ganin Ya Jafaru, domin a gabanta shekaranjiya yace yana son magana dani a keɓance....so what of Idan ta sanarwa Ya Mohaa fa? Ko kuma ita kanta dame za ta fassara abun? Ya zo ranar, sannan yauma ga shi ya biyoni gida...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Da gudu na diro daga kan gado wanda hatta Ƙasan marata sai da naji ya amsa ba daɗi. Tamkar wata taɓaɓɓiya haka na fito ina rarraba idona ko Allah zai sa in gan su suna tattauna maganar. Wayyo Allah na ni Beenafah! Wallahy haukacewa zan yi! Ni na ma rasa miye abin da yake damuna a yanzu. Tabbas dole na bayyana mata komai domin gudun zargi, to idan ta faɗawa Ya Mohaa ta wace fuska zai kalleni kenan? Cewa ina tare da wani a waje? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wayyo Allah ni Beenafah mi na aikata haka? Ya shigo gida tamkar ɓarawo kuma na tsaya kai da fata na ce dole sai an sake sa ya tafi? Miyasa zan kare sa? Wace hujja nake da ita akan hakan? Gaskiya da za'a auna BP na a halin yanzu...tabbas za'a cim masa ya haura ɗari biyu tsabar yanda na ke cikin tashin hankali da ruɗani. Ganin bangansu a ko'ina ba, yasa na wuce direct ɗakin da take na shige kai tsaye domin sanar da ita gaskiya. Murmushi ta yi mini tamkar wani abu bai faru ba ta ce. "Aunty Beena...Yanzu Suhaib ya gama sanar dani cewa su Aunt Fattoom za su zo kawo kayan aure na...yace za'a yi komai kamar yanda muke yi a nan." Wani irin murmushi na ƙirƙiro wanda dai iyakacin shi kan leɓe na ce. "Ai kuwa, ya kyauta. Allah ya nuna mana..." "To wai Aunty Labiba sai tambayata take wai mi nake so. Ni dai na ce ta bari zan yi shawara...kema mi kika gani?" Jinjina kaina na yi kawai sannan na ce. "Gaskiya nima dai a yanzu ban sani ba Hairi...ko za ki bari zuwa idan muka koma gida muka nutsu sai muyi tunani a kai...ko ya kika ce?" Dariya ta yi sannan ta gyaɗa kanta ta ce. "Haka ne kuma Aunty Beenafah, and again ga Daddy ya dawo yau. Ni sai yanxu na gano cewa na tabka shirme...please ta shi kada ya dawo bakya nan.." Miƙewa na yi tamkar tasan abun da nafi buƙata kenan na wuce da sauri na koma ɗakina. Ganin irin yanda ta tarbeni ba tare da nuna alamar wata tuhuma ba, hakan yasa na fasa ƙudurina na faɗa mata abinda yake faruwa. To amma shi fa idan ya tambaye ni? Na jima a zaune inda na kambala sallar Isha ba tare da sanin abin yi ba. Ina kallon sa ta ƙasan idona har ya wuce toilet ya yi wanka ya fito. Koda ya fito ni har na koma na zauna a bakin Gadon yayin da na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsun hannuna. Lallen da aka mini kawai na tsurawa ido ina kallon yanda ya yi maroon ya yi kyau sosai. Tun da ya gama shiryawa ya tsaya wuri ɗaya tare da resting jikin gini ya harɗe hannayensa yana kallona. Duk da cewa ni bana kallon sa, jikina ya bani cewa kallona yake. Sosai na ƙara jin wata irin sabuwar karaya ta sake sarƙafe mini zuciyata. Cikin rashin sanin abin yi yasa kawai na fashe masa da kuka. Wani lallausan murmushi ya saki cike da nutsuwa, yana mai jin wata irin sabuwar ƙaunar da duk abin da zata yi baya tunanin zai iya ganin laifinta ko na second ɗaya,yasan cewa duk abin da zata yi tabbas tana da dalilin yinsa. Macen da take da basirar bin diddigin zance ta kuma jajirce wurin ganin ta tsamo shi daga cikin matsalar da yake cikinta tsawon lokaci tabbas ita ɗin Mace ce ta daban a cikin dubban mata. Ita ce Macen da ta fito da rayuwarshi daga cikin tsananin duhu zuwa haske. Ta sanadinta komai ya daidaita a rayuwar shi. A hankali suka saba, a hankali suka fara samun kusanci, a hankali shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, a hankali soyayya mai sanyi da musulmin daɗi ta shiga tsakanin su..Shi ne kaɗai wanda take so, har kuka fa take yi don zai tafi ya barta, farin ciki ne ya kamata a lokacin da labarin Cikin da ke jikinta ya riske ta....Da waɗan nan tarin dalilan...,Har abada yasan ba za ta taɓa yin fushi da shi haka kawai ba domin jin daɗi. Har abada ba za ta so baƙin cikin sa idan dai ba kamawa ta yi ba. Yasan Bibinsa farin sani...ita ɗin ta yarda da shi sosai domin komai na ta bata ɓoye masa, wannan ma dole akwai wani...Tabbas akwai wani abin da yake tafiya ba daidai ba. Daga can inda yake tsaye na ji sautin muryarsa mai nakasa duk wani kuzari na jikina yana faɗin. "Bibina...har yanzu muna cikin faɗan ne? Why are you avoiding my gaze? Saɓani tsakanin miji da mata, is not something new....tabbas zamu saba, kuma zamu shirya matuƙar mun yarda da junanmu..amma kada ki bar fushi ya zama abin da zai ratattake soyayyar da muka gina ta bisa gaskiya da amana. " Yana gama faɗar haka ya tako a hankali ya zauna a gefena tare da kamo hannuna a hankali na sarƙafe a cikin nasa yana mai ƙara kwantar da murya sosai cike da nutsuwa ya ce. " Kin san wani abu Bibina.? Idan muka ci gaba da yi wa juna shiru a lokacin da wata matsala ta faru...soyayyarmu tabbas za ta samu mummunan giɓi..kuma ni har bada ba zan so hakan ta faru ba koda kuwa a mafarki ne. Bibi ina miki ƙaunar da ko ni ban yiwa kaina ita. Ina miki sonda baki ba zai iya misalta miki ko kwatanta yanda nake ji a kanki ba. Idan har wani abu mummuna ya shafi alaƙar mu, to tabbas har abada ba zan ƙara moruwa ba. Wata sassanyar ɓoyayyar ajiyar zuciya na sauke, har can cikin ƙasan zuciyata kalamansa suka taɓo tsabar yanda ya dulmiyani lokaci ɗaya, sosai tunanina ya karkata ya koma only him nake ji da gani. "Rayuwa dole akwai uzuri wa juna Bibi...amma duk abinda muke mu Riƙa lissafi muna duba haƙƙin abokan zamanmu da ya rataya akan wuyanmu. Ban san laifin da na miki, amma ina nema da roƙon ki alfarma dan Allah ki yi haƙuri ki yafe min. Ina son ki, ina son ki sosai..." Kwantawa na yi lamo cikin jikin sa ina mai rera wani sabon kukan a hankali ba tare da na yi magana ba. Ina jin rashin kyautawa ta wani ɓangaren amma kuma har yanzu na kasa sauka akan maganganunda zuciyata ta gama aminta da yanke hukunci akan su. Duk yanda na ke jin sonsa a raina dole na haƙura da shi kuma na ja baya, koda zancen Ya Jafaru ya tabbata da gaske..kaɗan zan ji na cutu domin na riga na gama ɗaukar haske kuma na sanya a raina cewa, from today henceforth...komai zai iya faruwa a tsakaninmu idan har ya ci karo da matar da ta dace da tsarinsa da kuma rayuwarsa. Janyeni ya yi a hankali ya miƙe ya fice mintuna kaɗan sai ga shi ya dawo da tray a hannunsa. Tamkar wasu kurame haka ya ciyar dani abincin ba tare da munyi magana da juna ba. Bayan ya fitar da kayan ya dawo, ina jin sa yana magana da Emraan a waya yana ce masa kada su zo domin baya gidan kuma ba zai dawo da wuri ba. Ni dai ina nan na lafe kamar mai bacci da gaske, amma kuma sam ba baccin nake ba. Bayan ya kambala bai jira komai ba ya kashe muna fitila ya hauro kan gadon tare da janyoni jikin sa ya rungumeni a ƙirjinsa. Bai damu da saina canja kaya ba domin yana gudun yayi wata magana cibi ya zama ƙari. Duk da cewa ina cikin halin damuwa, hakan bai hanani yin bacci ba domin da gaske nayi kewar wannan yanayin. Shi kuma, bayan ya tabbatar na yi bacci, a hankali ya janye ya tashi bayan dare ya raba sosai yaje ya ɗoro alwala ya fara ibada. Sam bai samu bacci ya ɗauke sa ko na second ɗaya ba. Tunanin abinda ya saka ta wannan fushin yake yi. Iya saninsa lafiya ƙalau suka rabu kuma lafiya ƙalau suke waya suke chart. To amma mine ne abin da ya faru a tsakanin kwana biyun nan? Komi ne ne yana fata Allah ya daidaita tsakaninsu domin idan aka ci gaba a haka, har abada ba zai samu nutsuwar zuciya ba. ******* Jafaru kuwa, wani abu ne ya ji ya ɗalla masa cizo wanda bai san ko mine ne ba, hakan yasa ba shiri ya zabura ya miƙe tsabar azaba ya shiga yarfe hannu a gigice. Kafin kace mi, tuni security alert ya ɗauki saiti bayan wasu mutum biyu sun yi ram da shi. A yanda suka nuna masa rashin imani har ya riga ya sadaƙar da cewa mutuwar sa ce ta zo,domin ya tsorata ba kaɗan ba. Fitowar Beenafah da yanda ta haƙiƙance ta nuna tsantsar damuwar ta da alfarmar da ta nema masa shi ya tabbatar masa da cewa har yanzu tana ƙaunarsa, kuma da zai ci gaba pushing In Sha Allahu ba jimawa zai cim ma nasara. Yasan cewa da ya riƙe wuta dole za ta matsa ya sake ta saboda ta dawo gare shi. Kuma ba zai sare ba, yana nan akan bakarsa har sai ya samu nasarar ta dawo gareshi. ****** Washe gari, da sassafe Su Emraan suka zo gidan wanda ban san mi suka tattauna akai ba tsawon lokaci. Bayan sun kambala sun wuce muma ba jimawa muka fito. Da ni da shi da Hairi, Biba ce daman yace sai bayan kwana biyu idan an gama shirya mata za'a aika mini da ita daga baya. Ban yi tsammanin cewa wai zai biya dani ta gidan Ammie ba, domin rabona da magana da shi tun a daren jiya, yanda nake haka ya shiga bi da ni don kawai a zauna lafiya. Muna isa na sauka na shige ciki. Da su Aunty Husaina na ci karo suna zaune a parlour tare da su Bahrain wai suna buga game ɗin PS. "Aunty Hussaina! Yanzu dan Allah harda ke a wannan?" Dariya ta fashe da ita sannan ta ce. "Beenafah. Ashe za ku biyo ta nan?" "Eh, wallahy Ina su Ammie da Aunty Aysha?" "Ammie tana ciki, amma Aunty Aysha ta yi gidan wata ƙawarta." Ciki na wuce bayan su Bahrain sun gaishe dani na cim mata a ɗaki tana zaune tana waya. Yanke wayar tayi tare da maido da hankalinta wurina ta ce. "Kun fito kenan?" Gyaɗa kaina na yi tare da ƙarasowa a hankali na zauna a gefenta na ce. "Ni zan tafi Ammie..." Kallona take babu ko ƙyaftawa ta kira sunana a hankali. "Beenafah!" Ɗagowa na yi na kalleta ina ƙoƙarin danne hawayena na amsa ta na ce. "Na'am Ammiena.." "Miye abinda yake damun ki?" Hawayenda nake ta ƙoƙarin dannewa ne suka ƙwace mini tamkar an kunna famfo. Kaina na ɗora akan kafaɗarta na ci gaba da kuka. Ganin cewa bani da niyyar buɗe bakina na yi magana yasa ta ci gaba da cewa. "Idan har ba buɗe baki kika yi ba, ba zan san abinda yake damun ki. Ki buɗe baki ki mini magana kinji? Miye abin da yake damun ki?"

Chapter 52 of 67