magana ɗaya ce kuma ita ce ta gaskiya, ban shigar da iyayen ki kowace ƙara ba."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!"
Abin da ta maimaita kenan har sau biyu sannan daga ƙarshe ta yanke kiran ta lalubo numbern Beenafah ta kira. Bayan sun gaisa ne Daga can ɓangaren Beenafah ta ce.
"Aunty Aysha Lafiya kuwa? Na ji muryarki ta yi wani iri.."
"Beenafah ba lafiya ba..."
Nan ta yi min bayani kamar yanda ta yiwa Ammie sannan daga ƙarshe ta ce.
"Beenafah dan Allah ki dubi Allah ki yafe musu.."
Girgiza kaina nayi cikin rashin sanin abin da take magana a kai na ce.
"Wallahy Aunty ban san komai a wannan maganar ba. Ba ni bace..."
"Ko mijin ki ne Beenafah??"
Shiru na yi na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe na girgiza kaina na ce.
"Kai...gaskiya a'a. Dayaa ba shi da lokacin wannan. Ba shi ba ne gaskiya."
Kashe kiran ta yi ta sake kiran Ammie wai don ta ji ko Dr. Basheer ne ya shigar da ƙarar amma kuma nan ma ba shi ba ne. Wasa-wasa sun nemi kowa da suka san yana da mu'amala da su amma kuma kowa ya ce ba shi ba ne. Kallonta Daddy ya yi a rauna ne ya ce.
"Aysha ashe daman kina magana da Mulaifa tsawon lokacin nan kika ce min baki san a ina take ba??"
Tana wani irin kuka ta shiga ɗaga murya tana faɗin.
"Eh Daddy! To amma akan me zan sanar maka inda suke bayan ka riga ka gama da rayuwarsu? Ita ɗin da ace irin zuciyarku ke gareta da ko kallon inda nake tana yi? Allah ne wanda ya haɗani da su ba zato ba tsammani. Kuma sai da muka yi sharaɗi da ita akan bata son kusan inda take kuma na amince....to akanmi zan sanar muku inda take. Babu irin nasihar da ban muku ba, babu irin faɗa muku gaskiyar da ban yi ba. Amma haka kuka zo ku ka share maganata ku ka yi ta yin abin da ranku yake so kuka manta da cewa akwai Allah wanda baya bacci baya angaje....inda nake iya neman alfarma na roƙo, sunce ba hannun su a ciki, saboda haka sai ku shirya zaman gidan yari tun da haka kuka zaɓarwa kanku.."
Daga haka ta shige ɗaki ta faɗa kan katifa ta fashe da wani irin kuka na takaici da baƙin ciki.
Suna nan inda ta barsu su Mummy ana ta kukan nadama Sai ga Hafiz ya iso. Daman da ƙyar Uncle Isma'ila ya amince akan ya riƙa zuwa shagon sa yana masa tsaro duk wata yana biyansa.
"Daddy!"
Ya ambata cike da karyewar zuciya.
"Daddy Allah ya yi mana maganin wannan masifar da muka siyo da kuɗinmu...wallahy munci amana Daddy..mun cutar da Ammie, da Daddy Bello.."
Ganin kawai suka yi a hankali ya sulale daga inda yake tsaye ya zube ƙasa numfashinsa ya lokaci ɗaya yanke. Da gudu suka yo kansa suna faɗin.
" Daddy...Daddy.."
Aysha bata batasan lokacin da ta fito da gudu ba, hankali a matuƙar tashe tana faɗin.
" Miye abun da ya samu Daddyn kuma?"
Da gudu Hafiz ya bar gidan ya fita neman mai Napep ɗinda za su ɗauke shi zuwa asibiti.
Suna nan ba jimawa sai gashi ya dawo suka tattala shi da ƙyar suka nufi asibiti da shi cike da tashin hankali.
*******
Gefen Ya Mohaa kuwa, sosai abin da yake ganin kamar ba komai ba yake neman yafi ƙarfin tunanin sa. Da ba don kada ya zamto mai butulci a wurin Allah ba, shi kam da yace ya yi dana sanin gano dangin mahaifiyar sa da ya yi a wannan karon. Domin bai haddasa masa komai ba sai rashin kwanciyar hankali da dagulewar lissafi.
Ubaid da ya shigo Office ɗin nasa a yanzu ne ya ɗan daki table ɗinda ke gaban sa ko Allah zai sa ya farka daga duniyar tunanin da ya abka.
Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya buɗe su sannan ya kalle sa murya a ƙasa sosai ya ce.
"I don't know what to do right now..."
"Akwai abin da za ka yi mana..."
Ubaid ɗin ya faɗa yana mai samun wuri kan kujerar da ke facing ɗinsa ya zauna ya ce.
"Use your brain as you always do...za ka samu mafita."
Girgiza kai ya yi cike da karaya ya ce.
"Ban da mafita Ubaid...na auna yafi sau dubu amma na kasa samun mafita, domin ba zan taɓa iya yin wani aure ba a yanzu...idan na Kalleta tausayi take bani....rayuwarta da dukkan wani fatanta yana a kaina ne..ko shekara ɗaya bamu yi spending a tare ba. Ta ya ya zan je mata da zancen wani aure? Daga ni har su Jaddan ta kallemu ya ya? Ma su son kan su da manta alheri??"
Girgiza kansa ya yi yana mai ƙure kallon Mohaa ɗin ya ce.
" Ko ɗaya! Ai ita ɗin yarinya ce kamar yanda ka ce tun farko. Tana sonka sosai, bana tunanin idan har kaje mata da magana musamman akan umarnin Jadda za ta ɗaga hankalinta..."
Da sauri ya girgiza kansa ya ce.
"Ubaid! Ita ɗin fa ba tsana ba ce. Mutum ce kamar kowa wacce ke da zuciya a ƙirjinta. Duniya ta daga ni sai Beenafah nake son kasancewa a Cikinta. Ka manta da cewa za ta damu ko ba za ta damu ba, I want only her in my life..."
"Su kuma iyayenka da abin da zaka saka musu kenan bayan shekarun da kuka kwashe baka tare da su? Kasan irin yanda suka cutu tsawon shekaru akan rashin ka? Yanzu da ka same su ashe basu cancanci ace ka yi duk abinda suka ce ba muddin dai zai saka su farin ciki?....Engineer! A Rayuwar nan ko? ɗan Adam matuƙar dai ya yarda da ƙaddara to dole ya shirya amsarta a duk yanda ta zo masa....ba dole sai fa ka samu abinda kake so 100% ba, Ka yi duba daga inda ka faro...kada ka tsaurara abubuwa. Idan har kana son duniyar ka ta yalwata da farin ciki da kwanciyar hankali, to ka amince da auren Noura,tunda har sun nace ka yi haƙuri ka bai wa zuciyar ka magana. Ka duba ka gani tun da ka dawo tsohuwar nan ta ƙi amincewa ta amsar wayarka. Ba don bata sonka take maka haka ba, ta yi ne saboda ƙarfafa zumunci. Kuma shin ka lura da wani abu kuwa? Ganin ƙanin ka zai auri Suwara, Ƙanwar ka za ta auri Suhaib ne ta ji cewa hakan ya burgeta idan Kaima za ka ɗauka daga cikin dangin abin sai yafi daɗi sosai da kuma armashi. Ka daure ka amsa tayinsu, hakan shi ne zai ba Ƙwaƙwalwarka hutu daga mugayen mafarkai dare da rana. Sannan matarka za ta daina damuwa akan damuwar ka, sannan za ka saka iyayenka a farin ciki.....ya kamata fa kayi tunani, domin da kunya sosai ace tun karon farko sun nemi alfarma ka kasa cika musu."
"Ubaid! I know, you are all telling me this Saboda kawai ka dace da matan ka basa faɗa da juna...but kada ka manta, don ka samu hakan ba lallai ace nima na samu ba...gidan Abdul-qadeer kullum cikin tashin hankali suke ba jituwa sam, Kaga dai duk da cewa ba'a gida ɗaya suke ba. Kullum cikin tashin hankali yake da rashin nutsuwa..."
Murmushi Ubaid ɗin ya yi tare da girgiza kansa ya ce.
" Ya kamata ka kyautatawa Allah za to Engineer. Lokacin da ka faro, tsawon shekaru ka shafe ko mata ɗaya baka da ita, lokaci ƙanƙani Allah ya azurtaka da samun Beenafah, wanda ba wayonka ko dabarar ka ba ne suka baka ita ba Ikon sa ne...ba ina faɗa maka haka bane don in turaka ƙarshen rame...ni kawai ina nema maka maslaha ne. Kai ne za ka tsara yanda kake so. Ba lallai sai ka ajiye su a gida ɗaya ba, ba lallai sai ka ajiye su a unguwa ɗaya ba, in fact! Ko cewa ka yi ba a Ƙasa ɗaya zaka ajiye su ba, no body will judge you. Kawai dai za ka sha azabar yawo, don jikinka ma sai ya faɗa maka ba. Idan har kana gudun matsala ka ajiye Noura a Nigeria ko a Sudan ɗin. Kaga babu wacce za ta san a wanne hali er uwar ta take, sai idan kai ne kaso su haɗu...."
Da sauri ya wani runtse idanunsa yana girgiza kai ya ce.
" Ita kaɗai nake so Ubaid...ina tsoro kada Allah ya kamani da laifin rashin yin adalci... "
" To ai baka zauna da Noura ɗin itama ka gani ba. In Sha Allahu za ka iya. Kai dai kawai ka roƙi Allah mafi alheri. Idan har kaga an yi auren, to tabbas ita ce mafi alheri. Yanzu tun da har ta kafe akan sai ka je ka ganta, to ina baka shawara akan ka shirya ka je ɗin, don ka ganta ai ba shi ne auren ba, ka dai tafi shi ne muradinta."
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali yana mai jinjina kansa ya ce.
" In Sha Allahu zan je. Amma ba don na amsa da zancen auren ba, zan je domin zumunci. Thank you so much for the advice."
Daga haka suka yi sallama da Engineer Ubaid ɗin ya wuce. Yana fita bai ma jira 6pm ɗin ta yi clocking ba ya tattara ya kama hanyar gida. Tabbas ya yarda da maganar Ubaid cewa ganin ta da zai je ya yi ai ba shi ne auren ba. Zai ma iya faruwa ita kanta tun da ba yarinya ba ce ta ji bai yi mata ba, kuma babu wanda zai tilasta mata. Allah ma yasa hakan ta kasance. Da sai ya fi kowa farin ciki.
Bayan ya dawo sosai ya saki jikinsa wanda ni abun har mamaki ya ɗan bani. Bayan mun gama shirin kwanciya bacci ya zaunar dani akan ƙafarsa yana murmushi ya ce.
" Zan je ziyarar dangin su Jadda, but I will spend only two days I promise..."
Langaɓar da kai na yi cike da shagwaɓewa na ce.
"To zan je mana...dan Allah ka je dani ka ji.."
Wani irin bugawa ƙirjinsa yayi wanda cikin seconds yanayinsa ya nuna Kamar akwai wata damuwa. Hannuna ya kama cikin fargaba ya ce.
"Kina ji ko Bibina...daga zaran na dawo da kwana ɗaya zamu wuce Kaduna a tare wurin yin wannan aikin da na faɗa miki.."
Cikin jin daɗi na wani ƙanƙame wuyansa na sumbaci gefen kumatunsa na ce.
"Thank youuuu!!"
Janyewa na yi ina kallonsa da murmushi na ce.
"To gaskiya na haƙura, domin na fi son zuwa Nigeria, ina kewar Ammiena da Bahrain sosai...ai za ka kai ni na gansu ko?"
Da sauri ya jinjina kansa ya ce.
"Sosai ma kuwa. Duk inda kike so na kaiki zan kaiki In Sha Allahu."
"To na gode...bari na fara ƙirgen days ɗin. Amma kai ma fa a gidanmu za ka zauna har mu dawo tunda nima na zauna a gidanku da muka je Sudan...bari na kira su Aunty Labiba na sanar musu zuwana...har Jadda ma sai na faɗa mata"
Wayata na ɗauko na dawo saman jikin sa na kwanta ina ta kiraye-kirayen mutanen da na ce.
Murmushi kawai yake tare da tsuramin idanu yana ta kallona. Duk abin da nake a duniya burgesa yake kamar yanda yake faɗamin koda yaushe.
Tun ina wayar yake ta shinshinar ƙamshina yana shafa fatar jikina, wanda na san tunda har gobe zai tafi, to babu abin da zai hana masa shanye daɗina a wannan daren. Haka na biyesa har muka kambala sannan muka yi wanka muka kwanta.
******
Washe gari da wuri ya shirya na rakashi mota sannan na dawo gida cike da jin kewar sa.
Bacci na koma nasha son raina sannan na ta shi na yi sallar Azahar na ɗauko wayata na zauna na fara sana'a. Wato kiran waya wacce idan baya nan aikin da nake yi kenan sai kuma charting. Hairi na fara kira muka gaisa na yi mata ya exams sannan na kira Jadda muka sha fira har da su Taimiyya. Daga nan na kira Ammie wanda a nan ne muka ƙara tattauna maganar Daddy domin gano waye wanda ya shirgar da shi ƙara amma bamu gane ba. Gashi ta ce min yanzu haka yana gadon asibiti ciwon shanyewar ɓarin jiki ya kama shi. Nan na yi mata alƙawarin cewa zan kira Aunty Aysha in mata ya mai jiki kamar yanda ta umurce ni. Sannan daga nan na kira Aunty Labiba. Bayan na gama naje na ci abinci na dawo na zauna na yi ta shiriritar kallo da charting.
Misalin ƙarfe shida na yamma, ina zaune a garden muna chart da Aunty Nadeeyah kiran wayar shi ya shigo. Cike da jin daɗin ganin kiran nasa na yi saurin ɗagawa, daman tun da ya fita yau bamu yi magana ba.
Ina ɗagawa na ce.
"Na yi kewar ka tun ba'a kwana ba...da fatan ka sauka lafiya?"
"Uhm! Ni ma haka Bibina...kina ji?"
Gyaɗa kaina na yi tamkar ina a gabansa na ce.
"Uhm! I'm all ears sweetie.."
"Did your Mum get twin sis?? Ina nufin ita ɗin 'ƴan biyu ne??"
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM*
*OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus....
*PAGE 47*
Tunani na ne ya juye lokaci ɗaya jin irin abin da yazo min da shi. Twin sis? Yana nufin kenan mai kama da Ammie ya gani ko me? A ina ne to? Sannan ita ɗin wacece?
"Bibi..."
Ambatar sunana da ya yi, shi ne abin da ya dawo dani daga duniyar tunanin da na shiga ina mai amsa masa na ce.
"Na'am!"
"Ita ɗin tana da en biyu ne?"
Tambayar da ke cikin zuciyata ce na fara jefa masa na ce.
"A ina ne Kaga mai kama da Ammiena?"
Kai tsaye ya ce.
"Qatar."
Girgiza kaina na yi na ce.
"A a. Gaskiya Ammiena ba 'ƴan biyu ba ne, ita kaɗai ce, sannan dama a Yemen ne zan iya ce maka zai iya faruwa domin can ne gidan iyayenta yake. To amma miye haɗinta da Qatar kuma? Kasan fa ance mutum irin sa guda bakwai ne a duniya. Ta yi yu kama ce kawai, amma ba ta da wasu dangi a Qatar gaskiya. Duk da cewar bata san daga ina mahaifinta yake ba, bana nan yana da wani haɗi da Qatar gasjiya. But zan kira ta na tambayeta mu ji."
Jinjina kai ya yi tare da saurin kawar da tunanin a ransa yana wani murmushi hannun sa bayan ƙeyarsa yana shafawa ya ce.
" Haka ne kuma maganar ki. Wata ƙila ma na zare ne akan mahaukacin son da nake miki Bibi..wanda yasa har nake ganin fuskarki da ta danginki a duk inda na tafi. Mai yiyuwa kamar ce na gani, musamman daman ga shi ba wani saninta na yi irin sosai ɗinnan ba."
Daga ƙarshe sai ya canja topic ɗin da cewa.
" Da fatan kin wuni lafiya?"
Jinjina kaina na yi na ce.
" Lafiya lau, da fatan ka sauka lafiya? Suma mutanen ina fata suna lafiya?"
"Alhamdulillah! Lafiya ƙalau suke. Ya gidan na ki? Da fatan komai da kowa lafiya?"
"Lafiya gida yake da mutanen cikin sa, sai dai daga mai gidan har gidan da mutanen gidan duk muna kewar ka."
"Ni ma haka daɗina..."
"Oup!"
Abinda na ambata kenan da sauri ina mai saka hannuna na rufe bakina tamkar nice na faɗi maganar tsabar jin kunya.
"Ba haka ba ne?"
Shagwaɓe murya na yi na ce.
"Ka fara ko? Ni dai ka daina, idan kai ba ka jin kunya to ni ina ji..."
"Da gaske?...faɗamin ya ake jin kunyar to? Kinga sai na fara ji daga yau..."
"Ni dai ka je wurin danginka ka ci gaba da zumuncinka ni ka ƙyaleni.."
Ina gama faɗar haka na yanke kiran ba tare da na jira amsar shi ba.
Numbern Ammie na kamo kai tsaye na kira ta, bayan ta ɗauka muka gaisa cike da mamaki na ce.
"Ammie ya nake jin hayaniya kuma? Kamar ana kiɗan Ƙwarya?"
Dariya ta yi ta ce.
"Muna Bunza tun jiya."
Ina murmushi na ce.
"Bunza Ammie? Mi kuka je yi kuma?"
"Wallahy wata ɗiyar Hajiyarsu Dr. Ce ake yi wa aure shi ne muka zo."
Cike da jin kewa na ce.
"Allah sarki! Kuna can kuna ta bukinku ni kuma kun barni nan ni ɗaya, sai da na baro ake ta nishaɗi..."
"In ji waye? Kema ai kina nishaɗi tun da kina tare da mijin ki kuna zaune lafiya. Ko akwai wani abu Beenafah?"
Kai na tsaye na girgiza mata kai na ce.
"A'a, ba komai. Lafiya ƙalau muke zau.."
Kitt! Haka na ji ta yanke kiran lokaci ɗaya. Haka na riƙe wayar a hannuna ina ta murmushi, jin cewa Ammiena ta na zaune lafiya da dangin Mijinta waɗanda suka girmama ta suka ba ta matsayi ba tare da nuna mata wariya ba. Ina ji fa aka kira sunan ta, maimakon ta bari mu kambala sai kuma ta yanke kiran taje ta amsa musu.
Ina nan tsaye kusan mintuna goma sai ga shi ta kirani back. Ina ɗagawa ta ce.
"I'm sorry, Hajiya ce ta kirani."
Jinjina kaina na yi na ce.
"Uhm! Na ji kuwa lokacin da aka kira ki.....ahm! daman...Daman.."
"Miye kike wani ƙyafta murya Beenafah? Miye kike so ki faɗamin? Kar ki komai kin ji ko. Ki je kai tsaye ga maganarki."
Lokaci ɗaya kuma na ji hankalina ya tashi. Anya idan na tunkareta da wannan maganar na yi mata adalci kuwa? Yanzu ne fa ta samu farin ciki bayan dogon lokacin da ta kwashe tana fama da ƙunci da baƙin cikin rayuwa. In tambayeta cewa ita 'ƴan biyu ce ko kuma in tambayeta ko suna da wasu dangi a Qatar? Ita ɗin fa a Aden ta tashi sannan iya tsawon rayuwarta wannan mutumin shi ne wanda ta sani kuma ko shi ba ta da sahihiyar magana guda a kansa. To ina zan fara? ina zan fara tunkarar ta da wannan magana? Dayaa bai wani santa sosai ba. Ta yi yu kama ce kawai irin ta 'yan Adam. Idan na bata wannan labarin hankalinta ta shi zai yi sosai, za ta shiga wani sabon tashin hankali da ruɗani, mai yiyuwa ma in fama mata ciwon da muka sha baƙar wahala a kansa muna jinya tsawon lokaci...kai! Gaskiya Beenafah da muguwar rawa gwamma ƙin tashi.
"Beenafah wai lafiyarki kuwa?"
"Uhm! Ba komai. Daman so nake in ce dan Allah nima idan na zo zamu iya tafiya Bunza a tare? Ni ma sai na gano garin, yana burgeni.."
Dariya ta yi ta ce.
"Af! Kin ji ki da wani shirmen kuma. To miye a ciki da za ki tsaya yin 'ƴar murya! Matuƙar dai mijin ki zai amince babu abin da zai hana, Allah ya kawo ku lafiya."
"Amin. Bari na barki ku ci gaba da hidimarku. Ina gaishe da Hajiya."
"Za ta ji In Sha Allahu. Sai da safe, Allah ya tashemu lafiya."
Ciki na koma tare da samun bakin kujera na zauna na dafe kaina ina ci gaba da tunani. Har yanzu lissafina ya ƙi tafiya daidai. Da ace fa Ammie tana da wasu dangin to da tabbas Sheikh zai faɗa mata. To amma bai san daga ina mahaifinta ya fito ba, sannan shin muna mada tabbacin cewa shi ɗin mahaifinta ne da gaske? Mahaukaci ne fa! Sannan ma idan har tana da dangi miyasa shi da take kallo a matsayin Baban ta zai zo ya hannun ta ta a wurin Sheik? Idan har yana da dangi mi zai sa a matsayinsa na mahaukaci su bar shi da ita? Idan har tana da dangi miyasa bai kai ta gare su ba tsawon lokaci? Mts! Kai! Gaskiya Wannan kama ce kawai. Ba ma zan gwada wannan katoɓarar ba, domin kada na je wurin gyaran gira a rasa ido, maganin kar a yi to kar ma a fara. A yanda ta samu farin ciki yanzu...ko kaɗan bana son na zama silar komawarta turkenta mai caɓo. To ko dai na bari idan ta dawo gida ta nutsu ɗin sai in kira ta?, ko kuma dai na bari sai na tafi munyi fuska da fuska sannan na faɗa mata?
Wannan tunanin shi ne abinda ya shiga zaga ƙwaƙwalwata ya hana min sukuni har na kwanta bacci da shi a cikin raina.
********
Tower 14, Porto Arabia,
The Pearl,
Doha, Qatar.
Sai da ya sauka a gidan sannan ya kira Suhaib ya ce ya kira Jadda ya faɗa mata cewa ya na gidansu Noura.
Bayan gama wayar sa ba'a rufa minti biyar ba sai ga shi ta kira shi da kanta saɓanin shi da ya shafe tsawon lokaci tunda ya dawo idan ya kira ta bata amsawa, sai dai idan da wayar Jaddi ko kuma wani a gidan, ko shi daga yanayin ta yanda take amsa kiran kasan ba don ranta ya so ba. Shiyasa har yau ya kasa daina al'ajabinta, at least ai dai ko na marmari ne ya ci ace ta yi masa ta ɗaga masa ƙafa ko don tsawon shekarun da ya yi ba tare da su ba. Yarinyar nan idan da tunani ya ci ace sun ɗaga mata ƙafa sun nuna mata kara. Sai dai ya fahimci ita ɗin mace ce mai tsattsauran ra'ayi da kuma tsayawa akan maganar ta.
Zaune yake kurum yana kallon mutanen gidan da ɗabi'unsu tun da ya shigo. Abu ɗaya ne zai ce ya ɗan ƙara mishi armashi dangane da zuwansa gidan shi ne zuwan Raihab wanda shi ɗin ƙanin Noura ne kamar yanda ya faɗa masa.
Sun jima a zaune babu wanda ya fito daga cikin su wanda har ya fara tunanin ta shi ya tafi sai ga mahaifiyarsu ta fito.
Farkon fara ɗora idonsa a kanta bai wani kawo komai ba, sai dai yanayin fuskar ta ya yi mishi kama da wata fuskar da ya haɗu da ita nan kusa. Bayan ta zauna sun gaisa ne ya ƙara jin abin a ransa, domin har muryar ta yi mishi sak ta fuskar da ya tuna cewa ya haɗu da ita sau biyu a rayuwar sa.
Hakan yasa bayan ta fita ya fito balcony ɗinsu ya kira Beenafah wata ƙila su ɗin suna da alaƙa da su. Bayan ya ji cewa ba su da dangi a Qatar ɗin ne ya yarda cewa tabbas wannan kama ce kawai. Idan ma ba shi ba, mutumin da yake ɗan Sudan miye haɗin sa da Yemen? Tabbas wannan kama ce kawai kamar yanda ta ce. Hakan yasa bayan sun gama wayar ya koma inda Raihab yake zaune yana mai shashatarda zancen ya kalle shi ya ce.
"Yayar taka ba ta nan ne na tafi har wani lokacin? Ina da ayyuka sosai a gabana and...Matata ma tana jirana a gida. Bana son na ɓata lokaci sosai a nan ba tare da na gabatar da abinda ya kawoni ba."
Cike da kwantar da kai Raihab ɗin ya ce.
"Ka yi haƙuri Yallaɓai, koda ka iso ta riga ta fita amma tana kan hanyar dawowa.."
Wayar shi da ta shiga ɓurarin neman agaji ne ya kai hannu ya ɗauka daga inda ya ajiye ya kara a kunnensa ya na mai yi mata sallama.
Murmushi ta yi daga can ɓangaren wanda har yana iya jiyo sautinta ta ce.
" Ka yi haƙuri Hammodina kada ka ji kamar na dameka...kai ɗin ne baka sanar wa kowa cewa zaka je gidan a yau ba, shiyasa ta fita, amma dai an yi mata waya yanzu ta ce tana kan hanya..Kana ji ko Hammodi? Noura nitsatstsiyar yarinya ce, sam ba ta da karauniya, kamar matarka haka take..."
Kai tsaye ya girgiza kansa ya katse ta da faɗin.
" Jadda Matata daban wannan daban..."
"Duk da haka, tana da halin nutsuwa da hankali kamar ita. Dan Allah ka sassauta mata ka ji hammodi? Ka bada haɗin kai yanda ya kamata."
"Hmhm"
Abin da ya furta mata kenan tare da jinjina kansa tamkar yana a gabanta.
Jin bai ƙara jin sautinta ba yasa ya ajiye wayar kawai tare da lumshe idanunsa yana jin wani irin takaici da haushin maganganunta. Akan me za ta riƙa haɗa ta da Bibinsa? Ta san kuwa wacece ita a cikin rayuwar sa?.
Bayan ya ƙara jira na kusan hour ɗaya wanda har ya gama yanke tashi ya tafiyar sa, sai ga Raihab ya miƙe bayan ya gama amsa kira ya ce masa ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 46 Chapter of 67