✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM*
*OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 59*
Da su Suhaib na yi shirin komai wanda sai daga baya ne Emraan ya kawo mini jadawalin bayanai daga Golden Pathways cewa ai a wannan shekarar ne Company ɗin zai cika shekaru ashirin da biyar da kafuwa.
Hakan ba ƙaramin farin ciki ya ƙara mini ba wanda na ci gaba da shirye-shiryena ba tare da ya sani ba.
A cikin kwanakin na yi coordinating da event planners SANTORINI,Wanda Grace Blue Dome Luxury Resort Shi ne suka bani shawara akai domin sun ce yafi da cancanta, na yi booking ɗakuna Hamsin na VIP sannan na tura Invitation cards da taimakon su Raihab zuwa ga 'ƴan uwa da abokanan arxiki da kuma abokanansa da na kasuwancinsa da kuma abokan kasuwancin kamfanoninmu wanda a yanzu nake da babban matsayi zuwa nan Dubai ɗin, Sudan, Riyadh Qatar, UK, Canada, Yemen da kuma Nigeria.
Duk wani abinci, abin sha, masu bada nishaɗi da komai na gama da su lokaci kawai muke jira idan Allah yasa muna cikin masu rai da lafiya.
Duk shige da ficen da nake kawai ya zuba ido yana kallona sai da ya tabbatar cewa bani da niyyar sanar da shi duk zirga-zirgan da nake yasa da dare bayan na ajiye masa Coffee a inda yake zaune tare da su Aryaan suna duba karatu waɗanda suka kasance manyan abokansa yanzu na kusa da shi ya kalleni yana murmushi yace.
"Bibi.."
Kallonsa na yi na ce.
"Na'am Daddyn Abdallah.."
"Wai miye kike ta yi ma up and down ne? Haƙuri na fa ya ƙare..."
Ban san lokacin da na fashe da dariya ba, domin ba ƙaramin dariya maganar tasa ta bani ba.
Juyawa na yi na fice kawai ba tare da na amsa ba.
Kallon su Arhaam ɗin ya yi, cikin sigar rarrashi da nuna wayon manya ya ce.
" Abokanaina....ni fa ban gane ba, Naga Maami sai ta yi ta buga waya, tana yawan fita ba damu ba, mts! Bakwa tunanin akwai abinda take shiryawa?"
A hankali Aryaan ya ɗaga ido ya kalli Arhaam ɗin sannan sai suka girgiza kai a tare kowa ya ce.
"A'a.."
Girgiza kansa ya yi ya dawo yana ta rarrashi amma suka ce su ma ba su sani ba. Daman sai da na musu gargaɗin cewa duk wanda ya sake ya faɗa masa abinda nake shiryawa to fa ba inda zan je da shi a nan zan bar shi. Daman shi bawan Allah Abdallah na ko 2yrs bai iyarda cikawa ballantana yasan miyar da ake sha.
Daga ƙarshe miƙewa ya yi yace su je an tashi daga wannan class ɗin sai kuma gobe idan Allah ya yarda.
A ɗaki ya sameni na gama shirin kwanciya bacci ya zauna a kusa dani tare da rungumoni jikinsa ya ƙara yin ƙasa da murya ya ce.
"Ba za ki faɗamin abin da yake faruwa ba? Ni fa hankalina ya ɗan ɗaga..."
Ɗan waro ido na yi alamar mamaki na ce.
"Miyasa to hankalinka zai ɗaga?"
"Because tun da nake dake baki taɓa ɓoye mini komai ba. Amma a 'ƴan kwanakin nan na kasa gane kanki."
Juyowa na yi na ɗane jikinsa tare da saƙala hannayena a wuyansa muna facing juna na yi kissing lips ɗin Shi Sannan na yi masa murmushi na ce.
"I love you Dayaa na. I so much love you with all my heart, body and soul...hankalinka ya daina ɗaguwa a kaina, domin ba zan taɓa yin abin da zai cutar da mu ba, babu abin da nake yi kawai ɗan wani ƙaramin abu ne, ka ga ne. A koda yaushe kai ne kake yin komai, a wannan karon kuma....na shirya mana tafiya zuwa santorini nan da kwana uku In Sha Allahu. Tun birthdayn Su Aryaan da muka fita bamu ƙara fita ba...and I need fresh air with you, tunda har na kambala karatuna, let's see the world for some weeks.."
Murmushi ya yi mini mai sanyi sannan ya ce.
" Yanzu na ji hankalina ya kwanta...ahm! Golden Pathways fa ya yi 25yrs da kafuwa..."
Sauka na yi daga jikinsa ina faɗin.
" mu bar zancen sa tukun sai mun dawo daga hutunmu."
Hasken fitilar ɗakin na kashe sannan muka kwanta ina ta jinjina wayon da na yi masa a raina ina ta murmushi.
A cikin kwanaki ukun muka gama shirya shirye, har da Biba domin kulamin da masoyina Abdallah.
Ƙarfe 6:45 na yamma jirginmu ya yi landing a Santorini kamar yanda na tsara. Wata farar limousine ce Sabuwa dal muka shiga zuwa masauki mu wanda bai san cewa duk su Jadda da kowa da kowa ba suna wurin.
Ɗakunanmu muka shige muka ci abinci muka huta sannan muka yi sallah, bayan mun kambala na ce mi shi ya zauna a nan kada ya fito sai idan na bashi umarni.
Wajen su Ammie na je muka gaiggaisa sannan na yi Magana da su Emraan cewa su kula da baƙin kafin mu fito zuwa 11:55pm.
Bayan na gama ganawa da su na je muka gana da ma'aikatan da duk na biya, bayan na tabbatar komai ya ɗauki sai ti na koma da kayan da suka shirya mana da ni da shi da Yara wanda suka da ce da bukin.
Kallonsa na yi da mamaki na ce.
"au! Wai bacci kake?"
Miƙewa ya yi ya zauna yana wani ɓata rai yana faɗin.
"To Bibi idan ban yi baccin ba mi zan yi? Kin ce kada na fita, kin kama wayoyina kin kashe,...."
Waigawa ya yi wurin su Arhaam da suke ta buga game da ya ce.
"Su dai kam gasu nan idon su biyu, wanda ni har yanxu ban yarda cewa bakinku ba'a haɗe yake ba..."
Dariya na yi sosai har ina kwantawa jikinsa tsabar yanda ya yi kamar wani yaro ƙarami. Bayan na gama dariya na ce masa ya je ya fara yin wanka.
Tashi ya yi ya shiga wankan sai muka hau shiryawa sai da lokacin ya cika sannan na ce Su Aryaan su yi gaba kaɗan muna fitowa yanzu. Kallon sa na yi ina murmushi na ce.
"Zamu iya tafiya?"
Murmushi ya yi yace.
"Kin yi kyau sosai...and the dress too."
"Thank you."
A hankali muka shiga takawa muka fito inda a nan bakin wani room ɗin na tsaya na karɓi Abdallah wanda shi ma yana tafiya da ƙafafunsa sannan muka jera tare da su Aryaan muka fice.
A bakin resort ɗin ne muna isowa aka buɗe wutar fireworks,sai ga manyan rubutu suna ta tartsatsi da wuta gwanin burgewa tamkar taurari, daga nan sai kuma ya ji ƙarar speakers ciki wani amo mai daɗi na faɗin.
"Welcome to the 5TH weeding anniversary,...Mrs Araam Family...Happy 52 Birthday to the amazing beloved Husband and the best Daddy of the world....And 25Years Of Golden Pathway Company?!!!"
Maganar na tsayawa, wani irin haske ya mamaye ko'ina na filin ya dawo tamkar safiya. A hankali sai ga kowa ya bayyana da abubuwan taya murna a hannun sa cike da farin ciki.
Tsayawa ya yi cak yana kallon su ɗaya bayan ɗaya da wani irin maɗaukakin mamaki a fuskar sa. Sannan sai kuma ya waigo ya kalleni still harshensa ya kasa bashi haɗin kai wurin ganin ya furxo da abinda yake zuciyarsa.
Ganin haka yasa na kama hannun sa na sumbata ina murmushi na jinjina masa kaina na ce.
"This is true love...this is your legacy and you deserve everything Mijina..Happy birthday to you, ina maka addu'ar Allah ƙara bulbulawa rayuwarka albarka, ya ƙara maka lafiya da tsawon rai mai amfani, ya shiryar maka da 'ƴa'ƴanka yasa ka yi kyakkyawan ƙarshe. You are the best Husband, domin kai ne rayuwa ta. Ina maka fatan alheri....Happy 5th years Anniversary of happiness...And a matsayin jajirtaccen ɗan kasuwa wanda ya yi aiki tuƙuru ya gina kansa da en uwansa da ma mutanen duniya da dama ya zamto kafaɗar dogaronsu...Happy 25Yeras of Golden pathways."
Muryar su Aryaan Ya ji suma suna faɗin.
" Happy Birthday to our super hero Daddy...we love you Daddy."
Hawaye ne masu sanyi suka ƙwace masa, domin sam ko a mafarkin sa bai taɓa kawo wannan ranar za ta zo masa irin haka ba. Yasan cewa kamfaninsa ya cika shekaru ashirin da biyar and yasan cewa anniversary ɗinmu na cika 5yrs ya zo amma bai taɓa tunaninsa ta wannan hanyar ba.
Hugging ɗina ya yi a hankali ya ce.
"Thank you so much Bibi...thank you for everything. Haƙiƙa yau kin sanyani farin ciki wanda bai san ta ya zan misalta miki shi ba. Allah ya saka miki da alheri ya ƙara zaman lafiya da farin ciki."
Tafi wurin ya ɗauka kowa ya shiga tayamu murna sannan daga ƙarshe aka shimfiɗa mana blue carpet mai tsawo muka shiga takawa cikin manyan flowers masu kyau sosai har zuwa cikin babban Hall ɗin resort ɗin.
Muna shiga aka saki wani sassayan kiɗan mai ɗauke da English song na weeding anniversary har muka je inda table ɗinmu yake muma tsaya.
Muryar MC ɗin ce ta karaɗe wurin da cewa.
"please Welcome....the king and Queen of tonight...Mr. And Mrs. Mohaa."
Bayan mun zauna aka shiga Family Parade inda kowane dangi suka faro isowa inda muke domin taya murna da fatan alheri.
Su Jadda ne suka fara zuwa wanda har suka tsaya a gabanmu bai daina mamakin ganin su ba. Wai to ta ya ma suka san da duk wannan har suka shirya suka zo. Tsofaffi da su sai neman rigima.
"Hammodi....Ina muku addu'a da fatan alheri...Beenafah, babu abin da zan ce miki sai dai mun gode miki da kika dawo da farin ciki cikin rayuwarsa wanda muke fata ya ci gaba da ɗorewa har abada.."
Dariyarsa da farin cikin sa sun kasa ɓoyuwa a wannan lokacin. Babu abinda yake idan ba dariya da murmushi ba.
Jaddi kuwa, hannunsa ya kama yana faɗin.
" Kai ɗin na musamman ne a wurin kowa Hammodi, har a wurin matarka kai ɗin na musamman ne. Fatana ɗaya ne, watarana ka zo ka ci gaba da rayuwa a kusa dani, ko da ba za ka yi siyasa ba."
Yanzu kam sai da ya ji hawaye a idonsa, jinjina kansa ya yi ya ce masa.
" In sha Allah, watarana tabbas zan cika wannan mafarkin naka Grandpa. Na gode sosai."
Daga nan sai su Abiyh wanda har da Sanda yake ɗan dogarawa suma suka zo suka mana addu'a sannan Annie wacce take ta murmushi ta ce masa.
"You took care of our daughter like a queen...a ko'ina nuna ta kake yi da kuma yin alfahari da ita. Allah ya ƙara muku shekaru masu albarka ya ji ƙan iyayenku ya albarka wannan zumuncin."
Daga nan sai su Hajiya da su Aunty Labiba suka yo ƙungiya guda suna ta farin ciki suna tayamu murna sannan daga ƙarshe Aunty Labiba ta ce.
"Listen everyone..Beenafah is literally the best thing that ever happened to our brother, and to our super Daddy...muna muku fatan alheri, muna ƙaunar ki sosai a cikin rayuwarmu, har abada ba zamu manta alherinki a garemu ba."
Hannuna Hairi ta jimƙe tana murmushi ta ce.
" Happy Anniversary Mummy...Haƙiƙa ke da Aunty Labiba...Ku ne allon kwaikwayona..har abada ina alfahari da ku. Fatan farin ciki."
"Na gode favorate...na ji Jadda na sanar mini ranar kin ƙara buɗe wani shagon a Suq Rania.."
Dariya ta yi tace.
"Mafarkina ya cika Aunty Beenafah, har abada ba zan daina godewa Daddy da IG Suhaib ba da kuma su Jaddi."
"Masha Allahu, Allah ya taimaka yasa albarka."
"Amin."
Ammie itama bayan kowa ya koma ya zauna ne ta zo ita da Abbu da Bahrain ta bani wata sarƙa sannan ta bai wa Dayaa Agogo, sai kuma Bahrain da ya yi presenting ma su Aryaan wasu manyan toys waɗanda na ji yana cewa wata ƙasa yaje na musamman ya siyo su.
"Ina tayaku murna, Allah ya ƙara albarka a cikin rayuwar auren ku."
Cewar Abbu sannan itama Ammie ta yi mana addu'a tare da Bahrain suka wuce.
Bayan nan kuma abokan arziki da abokan kasuwanci suka shiga tayamu sannan daga ƙarshe aka shiga gudanar da wasannin yara kamar yanda na tsara daga nan aka kuma aka juya zuwa ga wani bango mai ɗauke da hotunanmu waɗanda wasu ma bai san da su ba, domin tun farko-farkon aurenmu nake ajiyar su, dana haihuwar Su Aryaan ga su kala-, kala. Wasu a jirgi, wasu a gida, wasu a Sudan wasu nigeria, da sauran su.
Daga haka na saka gasar fassara hotuna da videon da ke yawo a majigin. Haka aka yi ta nishadi da farin ciki kowa sai faɗin albarkacin bakinsa yake yi. Bayan an gama muka wuce bakin teku domin yin dinner ta ban mamaki wacce kowa sai da ya yaba. Wata banner ce ta musamman wacce akayi hoton kamfanin da kuma Hotonsa a jiki wanda aka yi rubutu da fitilu masu ɗaukar hankali. The CEO Golden pathway company.
Bayan an gama cin abincin ya hau saman stage ɗin wurin ya kalle ni ya jinjina kansa sannan ya kira kowa yake wurin ya yi godiya sannan ya ce.
"Tonight...it's not about me only...it's about the woman who rebuilt my heart. It's about a wife who gave me peace. Ita ɗin garkuwa ta ce, Mafarkina da Allah ya cika min,I love you more than the life itself. En Uwa da abokanan arziki. Ina godiya sosai da kuka haɗa kai wurin bani wannan bazata da bazan taɓa mantawa da ita ba. Haƙiƙa yau na yi farin ciki, kuma na tabbatar cewa ina da mata wacce ke matuƙar ƙaunata da yin alfahari da ni. Allah ya mayar da kowa gidansa lafiya, mun gode sosai."
Daga nan na hau stage ɗin muka yanke cake ɗin tare da su Aryaan. Aka yi hotuna cike da nishaɗi sannan kowa ya koma gefe da wanda yake so aka yi ta fira wanda ni ina tare da Ammiena wacce ke ɗauke da 'ƴar ta Kausar wacce ta haifa a gidan Dr. Basheer shekara biyu da suka wuce, yarinyar da nake matuƙar ƙaunar ta a raina. A duk lokacin da na kalleta, hoton fuskar Sajjad ke dawo mini. Bahrain dake saɓe da Abdallah ne ya ce.
"Ina ƙara tayaki murna Aunty Beena....kalli yanda Daddy ke farin ciki. Raayuwa kenan.."
Murmushi na yi na ce.
"Na gode Bahrain..To kai wai yaushe zaka yi auren?"
Dariya ya yi ya kalli Ammie sai kuma ya kalleni ya ce.
"Idan na cika miki mafarkinki, na zamo jagoran WazeerMed, in sha Allah zan yi aure..."
"Kana da budurwa?"
Wata uwar dariya ya yi sannan ya ce.
"Budurwa kuma Aunty Beena? Noo! Not yet. 3years ya rage na haɗa Degree na, ko bayan na kambala, zan yi service na shekara ɗaya, sannan in fara aiki a Matsayin CEO, sai na yi kamar 2years haka, sannan na nemi budurwar. Kinga idan na fara tun yanzu, na rantse miki da Allah kuɗina kawai za ta riƙa sheƙewa tana cin duniyarta da tsinke..."
Da gani har Ammie da Abbu bamu san lokacin da muka fashe da dariya ba sannan daga ƙarshe na ce.
"To ai ita ce rayuwar..."
"No..ban yarda ba. Misali da ke. Koda kuka yi aure da Daddy bai ma taɓa ganin ki ba kema kuma haka, and ki kalla yanda kuke farin ciki rayuwarku na ta albarka. Ya Hamza haka Nimrah ta dinga tatsarshi in gaya miki ta dinga wanke shi, to wallahy bai samu sukuni ba sai da akayi auren nan. Amma kinga Ya Jafaru babu budurwarda take cin kuɗinsa. Tun da ya koma makaranta bayan wannan rigimar bai ƙara kula mace ba har yau. Yanzu haka ya zama barristernsa aikin sa kawai yake yi sai kula da su Mama."
Jinjina kaina na yi na ce.
"uhmm! Ya zaɓa abu mai kyau.."
Wani kallon ya mini da cewa.
"Aunty Beena cewa fa kika yi ya zaɓa abu abu mai kyau? Zaɓar yin rayuwa kai kaɗai shi ne abu mai kyau? Oh no! This is a very bad idea. Da iyalin dai...rayuwar za ta fi cika daidai."
"Bahrain...aure sunna ce mai ƙarfi, amma kuma ba dole ba ne matuƙar za ka kiyaye dokokin Allah. Tunda har yaga hakan ya fi masa fine! Let him be. Rayuwarsa ce, nobody will force him."
Girgiza kai Ammie ta yi cike da takaici ta ce.
"Jafaru ya ɓata rayuwar shi, sam bai kyautawa kansa da iyayen sa ba. Hatta ni ɗin nan ya daina magana da ni, yana da wata irin zuciya wacce ni dai ban taɓa ganin ɗan Adam kwatankwacinsa ba a duniyar nan. Iyayen sun yi sun yi, sai dai yace musu idan lokaci ya yi zai yi. To abinda bai gane ba shi ne, shi fa Allah duk abinda ya ga dama shi ne zai tabbata a cikin rayuwarka, idan kayi farin ciki a kowane yanayi ka gode masa...To sai ya ƙara maka kamar yanda ya yi alƙawari. Amma idan ka butulce...to tabbas za ka yi ta ganin ba daidai ba a rayuwarka. Amma kinga Ashiru! Ashiru ya kai ɗa wallahy, ya riƙemu har yanzu tamkar komai bai faru ba, yakan zo har Sokoto tare da matarsa idan dama ta samu muyi zumunci su koma. Ni da wannan ma na yi shawara da Dr. Cewa zamu ɗora shi a FruitWave wanda suka sakar mana, kinsan tun da ya dawo mallakinmu gabaɗaya, har yanzu ba'a yi wani yunƙuri ba. To In Sha Allahu zamu tattauna yanda ya kamata sai mu gani."
Cikin farin ciki na ce.
" Gaskiya na ji daɗin hakan sosai. Yaya Ashiru ya cancanta Ammie. Allah ya taimaka ya bada sa'a yasa ace gwamma da akayi."
Fira muka yi ta yi har misalin ƙarfe huɗu na asuba, sannan a hankali kowa ya watse muka yi sallama wanda da gari ya waye kowa zai koma gida inda ya fito. Nan na ce Ammie ta wuce da su Aryaan da Abdallah domin daman na yi plan ɗin ciresa daga Nono idan ta zo ta wuce da su, su yi mata ko one month ne sannan su dawo.
Washegari sai da na tabbatar kowa ya watse sannan na ce mishi ya shirya akwai surprise na gaba.
Sai da muka fito ya ga ba kowa daga ni shi ne muka rage.
"Ina su Arhaam Bibi.?"
Hannun shi na kama ina murmusawa na ce.
"Sun tafi gidan Ammie mu ɗan shaƙata..."
"Har da Abdallah?"
"Eh, a lissafinmu na cire a nono ai yau ne ya kama.."
Shiru ya yi alamar nazari sannan daga ƙarshe ya jinjina kansa yana kallona ya ce.
"Ke ɗin ta musamman ce. Tabbas yau ne date ɗin. Kin yi manipulating ɗina kinsa na manta komai....five years in marriage, and I still choose you everyday, over and over Bibina."
"And I will always choose you for ever Mijina."
Sai da muka yi sati biyu muka ɗai a nan muka shaƙata sannan muka koma gida.
Watarana ina zaune ina yanka masa fresh fruit ya kalleni yana ta murmushi ya ce.
"Har yau na kasa manta bukin bazatan da kika shirya mini Bibina. Na mutu da matuƙar mamaki domin komai ya tafi a sai ti..."
Wata irin dariya na yi sannan na ce.
"Oh! Wato ka za ta kai kaɗai ne mai kuɗi ko kuma kai kaɗai ne mai watau ko?"
"Wane ni! Ai ke ɗin kuwa ke ce mai kuɗi Bibi, domin an narka dukiya ba kaɗan ba. Kuma na san ba kuɗi ba ne..."
Dariyar na ƙara yi na ce.
"Ai zan zare su ne na dawo da kayana a hankali."
Dariyar ya yi shima sannan ya ce.
"ba komai. Ai komai nawa mallakin ki ne. Amma ina faɗa miki na ji daɗi sosai a raina. Ina son ki"
"Ni ma haka Dayaa na."
Bayan wata ɗaya muka je Qatar auren Shuraih daga nan muka dawo da su Aryaan muka ci gaba da tafiyar da rayuwa kamar yanda ubangiji ya tsara mana.
********
15years later....
A shekara sha biyar....abubuwa da yawa sun faru na daɗi da kuma akasin sa. Rayuwarmu ta canza sosai inda muka samu ci gaban da sai dai muce Alhamdulillah! Kamar yanda ya yi wa Jaddi alƙawari kafin rasuwarsa...ya dawo Oumdurman da alhalinsa wanda ya gina mana katafaren gida muke rayuwa Muda 'ƴan' ƴan mu. A yanzu shi ɗin shugaba ne kuma jagora kamar yanda Jaddin yake mafarki a koda yaushe inda yake a matsayin Minister kamar yanda Jaddi ya kasance a baya.
Ya kasance mutum mafi daraja da girma da ake ji da shi a faɗin Sudan ɗin, domin ya zamto abin dogaro, ƙashin bayan al'umma wanda baya gajiya da tallafa musu da kuma jin kokensu a koda yaushe.
Aryaan da Arhaam sun girma sosai wanda a yanzu suke aji ɗaya a jami'a yayin da Abdallah yake a SS2. Sai Aliyu Haidar da ke Jss1 sannan autata Zarah da ke primary 3.
Rayuwar dai, duk da tana cike da ƙalubale da jarabawowi, Alhamdulillah a kowane irin yanayi, duk da cewa kakan nasa baya raye, sosai suka ci gaba da haɗe kansu tare da su Uncle Mu'aƙƙib wanda a yanzu daga shi sai Ya Mohaan ke jagorantar iyalin na su da sauran yara da jikoki.
Gidan yana sa ka ji ba daɗi idan ka tuna da Jaddi wanda shi ne haske kuma annurin gidan na su. To amma a rayuwa, mutuwa ba ta da gwani, sannan bata barin wani don wani. A duk lokacin da Allah ya yi za ka bar duniyar to lallai ba makawa sai ka tafi.
Ko a Qatar Abiyh ne kaɗai ya rage wanda ya tsufa sosai, lokacin da masoyiyarsa Ammah ta rasu, ya yi kuka wanda sai da ya baiwa kowa tausayi. A hannunsa ta rasu a gadon asibiti, ashe duk ihun da ake, ɗan lokaci ne kaɗan a tsakaninsu wanda shekara goma kaɗai suka yi a tare ta rasu ta bar shi.
A yanxu na kasance Uwa, shugaba, jagorar Al'umma kamar yanda mijina ya kasance. Kuka da farin cikin iyalina shi ne kan gaba da komai nawa. A duk lokacin da zan kalle su suna farin ciki, sai na riƙa tunawa shekarun baya, wanda babu abu ɗaya da muka saka cewa zai faru irin haka, musamman Ya Mohaa da ya cire rai da farin ciki da kuma Mafarkin samun iyali.
Shi ne yau yake da manyan 'ƴa'ƴa. Masu nutsuwa da cikar kamala. Shi ne kullum za'a ce masa Daddy kaza, Daddy ya kamata ayi kaza, Daddy ya kamata ace kaza kaza ne. Daddy a biya mini kuɗin registeration, Daddy ni yaushe za'a yi walima ta,Daddy ni kuɗi kaza za'a bani domin zamu yi get together a school, Daddy we love you.
Waɗannan sune kalmomin da yake yawan faɗamin cewa suna saka shi farin ciki kuma suna saka shi jin cewa shi ɗin yanzu mutum ne, uba kamar yanda ya yi mafarki.
Siyasar sa...bata hana masa lokacinmu, domin ba don kuɗi yake yi ba, yana yi ne domin cika alƙawarin kakansa wanda ya mutu da farin cikin cewa burinsa ya cika domin Hammodinsa ya dawo ya kuma ɗauka daga inda ya tsaya wurin taimakon jama'a. kamar yanda ya saba cewa, shi ka ɗai ba zai iya ba sai da taimakon su Uncle Mu'aƙƙib, to haka ma ya tabbatar cewa ko bayan ya mutu Uncle Mu'aƙƙib ba zai iya shi kaɗai ba dole taimakon Ya mohaa.
Da wannan yake yawan tafiye-tafiye. Duk da cewa muna shirye-shiryen yin 20years anniversary a cikin watan nan, hakan bai hana shi shirya tafiyar da suka tsara ba, tafiyar ta ministoci ce da za su yi taro a Nigeria wanda ya ce mu shirya har mu zamu tafi.
Yau ma tun ƙarfe huɗu ya dawo gidan ba tare da na sani ba. A parlournsa na tarar da su suna cin abinci har da Aliyu wanda dawowarsa kenan daga school shi da Zarah.
Kallonsu na yi ina mai dire musu tray ɗinda yake hannuna na ce.
"Ai sai ku sanar mini cewa kun dawo,.."
"Mami mun ga kina da baƙi ne shiyasa."
Cewar Abdallah yana mai kai hannu ya ɗauki glass cup ya tsiyaya lemu. Duƙawa na yi na ɗauki cup ɗin na zubawa babansu ina miƙa masa na ce.
"To kai miye ya hana ka kirani a waya?.."
Kallona ya yi sannan ya ce.
"Na fa aika har sau biyu aka ce kina da baƙi.."
Jinjina kaina na yi sannan na ce.
" Uhm! To sannu da dawowa...tukunna wai ina ma ka tsaya tun ɗazu bayan ya kamata ace kana gidan nan tun 2pm?"
Kallon su Aryaan ya yi sai kuma ya kalli gefen su Abdallah sannan ya dawo da kallon guna yana murmushi ya ce.
"Har na kamo hanya, sai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 63 Chapter of 67