Share this page
Juyin duniya ta yi, amma ta kasa samun ko kalma ɗaya daga gare ni, duk da haka ba ta sare ba, domin kwantar da murya ta ƙara yi sosai tana mai ƙara jimƙe hannuna a nata ta ce. "Kin san dai duk duniya daga ni sai mijinki ne wanda baki da kamar su a yanzu ko? To ba zan tilas miki ba, domin ke ɗin ba jaririya bace. Idan har ba zaki faɗa mini ba, to ki faɗawa mijinki, domin shine wanda yafi kusanci dake da kowa a yanzu, shi ne abokinki, amininki, garkuwanki kuma shugabanki. Ki bashi muhimmanci da damar da zai riƙa jin damuwowinki domin nema miki mafita idan har akwai buƙatar hakan, idan kuma na taya addu'a ne sai ya taya ki addu'a,ki riƙe ibada sosai, kuma ki yi ta gayawa Allah dukkan wata matsalar ki, a hakan za ki samu nutsuwa da kwanciyar hankali. Idan kuma matsala ce a tsakaninku..to ki zama mai haƙuri da kuma lissafin rayuwa, domin duk wanda yace zo mu zauna to fa lallai yace zo mu saɓa, gidan miji haƙuri ake yi, kowa da kika gani haƙuri yake muddin yana son aurensa ya ɗore ya yi ƙarko, sai ya yi haƙuri, ya yi ibada, sannan kuma ya yi biyayyar aure..." "To Ammie idan wanda kake yin komai domin sa watarana ya juya maka baya fa? Idan ya samu wata wadda ta fi ka komai...shin ba aurar ta zai yi ba? Tsoro na ke ji Ammie...ina jin tsoro sosai kada ya juya mini baya watarana, ganin cewa ni ɗin ban cancanta da na zamo matarsa ba. Ammie kinfi kowa sanin cewa bani da wani zurfin ilmi sosai, shi kuma matsayinsa da komai nasa sun wuce nawa nesa ba kusa ba, Ammie shin bakya tunanin watarana zai iya butulce mini? Ammie ni ji nake komai ya fita a kaina....ji nake kamar ba na son ci gaba da rayuwa da shi..domin duk abinda yake yi a kaina duk Ƙarya ce, bab.." Cike da tsantsar tashin hankali ta saka hannu ta toshe mini baki tana faɗin. " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Na shiga uku ni Mulaifa! Beenafah a ina kika ji yo wannan masifar kuma?" Murya cike da kuka na ce. " Wata ƙawata ta faɗa mini haka...!" "Wacce ƙawar ce wannan? Faɗa mini a ina take? Dan Allah ki faɗa mini kinji Beenafah!" Girgiza kaina na yi ina mai jin mummunan faɗuwar gaba na ce. "Ammie ba'a nan take ba.." Da sauri ta girgiza kanta ta ce. "Koda yake sanin ta ba shi ne ma mai muhimmancin ba...gubar da ta shayar da ke ce ya kamata na fara baki maganin ta....kina jina Beenafah? Mijinki mutumin kirki ne sosai, bai jima da muka san shi ba, amma dai duniya da mutanen cikinta da dama sun yi mishi kyakkyawan yabo da shaida ta gari. Har abada ba zai taɓa iya juya miki baya ba Beenafah. Shi ɗan halak ne kuma yasan halacci....Kada ki sake saurarar irin waɗan nan gurbataccin ƙawayen domin babu alheri a cikin tarayya da su. Ciki ne da ke, idan kika ce zaki riƙa damuwa, to tabbas damuwa ce za ta maye miki ƙarshe matsala ta biyo baya, ki dogara ga Allah kuma ki yarda cewa dukkan wani abun da zai same ki, to ikon sa ne kuma yinsa ne ba wani mutum ba. Ki kwantar da hankalinki, ki zauna da mijinki lafiya dan Allah Beenafah ina roƙon ki. Ki daina wannan tunanin sam ba shi da wani amfani. Akan hanya kuke, bai kamata ace na zaunar da ke sosai a nan ba, amma in Sha Allahu zamu tattauna a waya idan kin huta. Allah ya tsare ya ƙara miki lafiya." "Amin. Na gode sosai." Daga haka muka fito suka rakoni gabaɗaya har mota sannan suka koma gida. ****** Tunda muka dawo tsawon kwanaki biyar kenan na daina ganinsa a idona,daga ni sai Hairi ne muke budurinmu, to itama a yau ɗin ta koma school. da farko na ɗauka tafiya ya yi. Sai daga baya na gane cewa ashe sai dare ya yi sosai yake shigowa gidan, idan gari ya waye kuma, da wuri yake shiryawa ya fita. Yanzu kenan yana nufin fushi yake dani kome? Ni ya zan yi da raina? Ya Jafaru ya riga ya cutar dani, ban gane cewa na yi kuskure ba sai da Ammie ta farkar dani daga mummunan baccin da ya ɗauke ni.....kunyar kaina nake ji a yanxu, ina jin kunyar sa shima, ban san ta yanda zan fara kallon sa ba... Damshin da na ji akan kumatuna shi ya tabbatar mini da cewa ashe kuka nake da gaske. Dole na yi kuka, domin na riga na ɓata rawa ta da tsalle. Yanzu ta ina zan fara.? Ta ina zan fara ni Beenafah? Dole na gyara kuskure na...dole na gyara komai zai faru. Ina da buƙatar mijina,ina jin kewarsa. Wayata na janyo na duba, tunda muka dawo ko sau ɗaya bai kirani ba, bai turo mini text ba. Dole na gyara kuskurena. Da wannan tunanin na zauna a raina, bayan na gama sallar Isha naje na yi wanka na shirya cikin kayan baccin da yafi so ya ganni a ciki na koma parlour na zauna. Tun ina zaman daɗi har na dawo jin na ga ji, gashi har 11pm ta gota amma bai dawo ba. Duk da cewa zaman ya gundureni...ko kaɗan ban ji a zuciyata cewa zan iya matsawa ko nan da can ba muddin ba dawowa ya yi ba. Ina nan a haka har bacci ya fara kama idona sai ga shi ya shigo. Mamakina ne ya kamasa ganina zaune akan kujera na takure tamkar wata marainiya. Cikin shakka-shakka ya kira sunana a hankali, wanda can ƙasan ransa ji yake tamkar ba gaske bane mafarki ne ko kuma gizau. "Bibi..." Tasowa na yi gudu na shige cikin jikin sa ina mai ƙanƙameshi na fashe da kuka ina faɗin. "I'm Sorry...I'm sorry please..." Cikin wani jin wani sabon yanayi ya saka hannayensa ya rungumeni a hankali yakai fuskarsa ya binne a cikin gefen wuyana yana na tsawon mintuna, sannan daga ƙarshe ya ɗago yana mai ƙara ƙanƙameni sosai ya ce. "Ki daina Kukan nan Bibi...Ƙona mini zuciya yake bana so...ki yi haƙuri kin ji?" Ɗago kaina na yi ba tare da janye jikina daga nasa ba na kalle shi ina kuka mai cike da zallar magiya na ce. "Ka yi haƙuri...cewa akayi ba da gaske kake so na ba, komai kake mini duk ba na gaskiya ba ne...you are just using me, kana zaune dani ne kawai akan dole saboda na taimakeka, amma daga zaran an kwana biyu zaka samu wata wadda ta fini komai mai babban matsayi irin naka ka aura, a lokacin ne za ka sakeni...da gaske za ka iya yin aure watarana? Da gaske wacce ta fini ilimi, wayewa, da komai ma za ka auro? " Luu! Haka ya tafi suka zube akan kujera wacce ita ce ta zamto ginshiƙi a gare su, ba don haka ba, da tuni sun rabke daga shi har ita zuwa ƙasa. Wannan wace iriyar mummunar magana ce? A ina ta jiyo wannan maganar? Wane maƙiyin Allah ne masoyin shaiɗan mai warin bakin da ya faɗa mata wannan maganar? Ga shi har yanzu bai gama farfaɗowa daga shock ɗin Jadda ba da ta ce wai an kai kuɗin aure da komai yanzu lokaci kaɗai ake jira. Ga shi ta matsa masa lamba akan dole sai ya sanarwa Beenafahr tun yanzu domin kada tace an yi mata rashin adalci gashi lokacin sai ƙaratowa yake ta yi. Damuwa da firgici sune suka hana masa tunkararta tsawon kwanakin nan domin har ga Allah bai san ta ina zai fara ba. Kunyar ta yake ji, da nauyin ta. Yanxu kuma ga mummunar maganar ta ta riske shi wacce kwata-kwata bai tsamma ce ta ba. Yanzu ta ina zai fara yi mata bayani kenan? Wane munafukin ne wannan ɗan ƙasa ga wuta? Wanne azzalumi ne mai haɗa gurmi tsakanin mata da miji wanda Allah da manzon sa suka yi hani akan hakan domin mummunan ɗabi'a ce wacce bata da kyau. Yanxu da ta zo masa da wannan zancen...tabbas ko kwana zai yi yana mata bayani ba za ta yarda cewa auren Noura ba'a son ransa za'a yi sa ba. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* *PAGE 53* Waye wannan munafukin da ya faɗa mata wannan maganar? Sam bai shirya ba...bai shirya sanar mata..bai san ta ina zai fara ba...ashe duk fushin nan da take akan wannan dalilin ne..sannan kowane ne don kawai ya ƙara ɓata tsakaninsu ya ƙarawa maganar magi da gishiri yace mata zai yi aure don ita ba ta cancanta ba..kowane ne wannan bai masa adalci ba..sam bai masa adalci ba. Ɗagowa nayi na kallesa cike da karyewar zuciya na ce. "Haka ne ba? Zancen haka yake ko? Ni ɗin ban cancanta ba..." Gabaɗaya ya yi resting bayansa jikin kujerar ya jingina tare da zuba mata idanu yana kallon fuskarta, yanda idanunta suka kumbura saboda kuka,karan hancinta ya yi ja, fuskar nan ta yi fayau wanda hakan ba ƙaramin dukan zuciyarsa ya yi ba. Kowane ne wannan bai kyauta masa ba, sam bai kyauta masa ba. Ya zalunce shi ya cutar da shi cuta mai girma..and now...since ta riga ta ji komai...ya zama dole ya fayyace mata komai, duk da cewa yana jin tsoron yanda za ta ɗauki maganar, ga shi an riga an ɓata komai. Ta hakan ya yanke faɗamata gaskiya wanda shi a tunanin shi zancen auren ne kai tsaye aka samu wani munafukin ya sanar mata, bai san cewa jirwayene ta yi masa mai kamar wanka ba, sai gashi ta yi sara akan gaɓa. A yanzu jin shirunsa ya gama ruguza mini zuciya, shirunsa ya bani amsar da nake nema ba tare da na sha wahala ba. Ashe Ya Jafaru ya yi gaskiya, shi ɗin fuska biyu ne da shi. Shi ɗin ashe da gaske bai amshe ni ba, shi ɗin bai aminta har cikin ransa cewa mun zamo ɗaya ba kamar yanda ni na gama sakankacewa...da gaske kenan komai da yake mini yana yin sa ne don kawai sadaukarwar da na masa. Komai yana yin sa ne don GANIN IDO na amma akwai abinda yake nufi a zuciyarsa. Yunƙurawa na yi da ƙyar tamkar wata wacce aka daddane na miƙe ina mai yi masa wani kallon mai ɗauke da abubuwa masu tsaya na ce. "You break my trust...amma ba komai, Allah zai mini sakayya..." Takawa na yi zuwa bakin ƙofa sannan na tsaya tare da juyowa na sake kallonsa na ce. "Kafin gobe...ina so ka rubutamin takardar saki na ka bani..." Tamkar wanda aka shaƙewa wuya, haka ya furxo kalmomin sunana a gigice ya ce. "Da...Dan Allah Bibi!! Dan Allah ki tsaya ki saurare ni...Dan Allah!" Wasu sabbin hawayene masu tsananin zafi na ji sun gangaro mini, a raunane na ce. "Ka daina kirana a haka..domin kana mini illa sosai..wallahy zuciyata ji nake tamkar za ta fashe...na yarda da kai...yarda mai girma..na ɗauka na samu madogara, na ɗauka na riga na samu shingen da sai mutuwa ce za ta fitar dani daga ciki..." "Bibi..is not like that! Is not what you think and is not what you have heard...please I beg you for the sake of Allah akan ki tsaya ki saurare ni da kunnen basira ki kuma kalleni da ido na fahimta...." "Me zan ji daban bayan wannan ɗin? Tabbas kai ɗin babban mutum ne mai babban matsayi, ga kuɗi ga kyakkyawar nasaba ta dangi wanda ni duk bani da su kuma ban kai ka ba..." Lumshe idanunsa ya yi yana mai jin zuciyarsa na masa nauyi sosai. Wannan wace irin mummunan rana ce? Miye duk wannan yake faruwa tsakaninsa da abar sonsa? Ciki ne da ita fa...jaririn ciki! Ya zai yi da ransa idan wani abu ya same waɗannan mutum biyun da ba shi da tamkar su a duniya. Su ne farin cikinsa, uwa da ɗan cikinta su ne walwalarsa, dariyar sa da kuma rayuwarsa baki ɗaya. Dole ya yi wani abu...tabbas dole ya taɓuka kada ya rasata da gaske. "Bibi!" Ya furta kalmomin sunana yana mai tasowa a hankali ya ɗan matso inda nake tsaye kaɗan. "Wallahy ban taɓa tunanin rayuwata da wata macen ba idan bake ba..da gaske nake faɗa miki wannan..wannan auren ma da ake ta ƙoƙarin ƙullawa wallahy tallahy ba'a son raina ba ne. JADDA ta riƙe wuta Bibi..., bana cikin komai duk su ne suke ƙullawa....i told them a millions times Cewa ke kaɗai kin isheni rayuwa.." "Auaaaurree? Jadddda?" Na furxo kalmomin tamkar Wata sabuwar mahaukaciya wacce cutar Echolalia ta kamata, haka na shiga maimaitawa. Runtse idanuna na yi da ƙarfi sai kuma na buɗe..sai kuma na yi gaba sai kuma na dawo baya tare da using hannuna alamar ban gane miyake nufi ba domin na ruɗe na gigice na ɗimauce. Ganin kamar na daina fahimtar komai yasa a ruɗe ya kamoni tare da neman sanya ni jikinsa. Wata irin zillewa na yi na fara ja da baya ina mai binsa da wani irin kallo na ce. "Jadda? Aure? Aure za su maka? Ban cancanta ba? Kenan a family group da aka sanya ni ta what'sapp ana ta zuzuta auren Noura da Engineer kai ne ake nufi kenan?..." Jikina na wata irin ciccira komai ya shiga dawo mini, beat by beat. Wannan ɗin ita ce za'a aura masa suka mayar dani shashasha marar lissafi? " Bibi...no Bibi please..." Wani irin mummunan kallo na jefa masa ina mai jin wani irin azababben tashin hankali na ce. "Ka amsa mini Ya Mohaa!! Kai ne Engineer ɗin Noura kenan???" Jin ya yi shiru yasa na sake matsawa baya sosai ina mai dafe jikin gini domin jirin da nake ji na saki wani murmushin da yafi kuka ciwo ina wani girgiza kaina na ce. "HUhmm! Lallai ɗan Adam! Wato sakayyar da su Jadda za su mini kenan? Bayan na gama dawo da kai mutum...bayan na cire ka daga ƙangin da ka yanke ƙauna...akan jindaɗin ka dawo gare su bayan tsawon shekaru...basu ga dami za su saka mini ba sai aura maka er uwar ka ko? Tabbas Ya Jafaru ya yi gaskiya....kai ɗin sam ban cancance ka ba, Noura ce wacce tafi da cewa da kai, mai cikakkiyar nasaba da ilmi...Sai yanzu na yarda da gaske cewa kai ɗin you are just using me, sai yanzu na yarda cewa you are just pretending na kasancewarmu miji da mata but as temporary Ko Mr. Engineer??" Haukace masa na yi tuburan wanda sai da ya yi nadamar zuwan wannan ranar a rayuwarsa. Duk inda ya taro ni sai na zille, na bushe idona bana ji bana gani tamkar ba ni ba. Bai san cewa haka nake ba sai yau, bai san ina da wata kalar fuskar ba sai yau domin ya rasa gane kai ne. Sai kuka nake ina masa hauka. Daƙyar da taimakomin ubangiji ya samu na tsaya na nutsu bayan ya yi ta magiya akan cewa na tsaya na saurari uzurin sa wanda idan har bai mini ba sai na ɗauki duk wani hukuncinda naga cewa ya fi cancanta. Wasu irin hawaye ne suka wanke masa fuska domin kalamaina kama suke da saukar ruwan dalma akan dukkan wata gaɓa ta sasssan jikin sa. Ya shiga tashin hankali domin gani yake ma kamar har ya rasa ɗin da gaske. Girgiza kai kawai yake tamkar wani zararre yana ƙoƙarin furta mini kalamai amma ya kasa yin hakan, kalmomi biyu ne zuwa uku yake ta nanatawa domin ya rasa makama. "No Bibi..Please Bibi...dan Allah ki saurare ni..." "Na san cewa da ka aure ta, everything will become over between us. Domin ta fini ilmi, wacce take da class, wacce English ɗinta very fluent, ita ce za ka iya zaga duniya da ita ka nuna ta a ko'ina ba tare da jin kunya ba, ita za ka iya hawa jirgi da ita, ita za ka iya kaiwa Office ka nuna ta a gaban kowa,familynka ita ce za su dawo suna so ni kuma na dawo banza, kai ma haka za ka dawo yi mini riƙon sakainar kashi, ƙarshe ka sake ni saki na wulaƙanci..." " Stop it! Stop it please!" Ya furta a tsawace yana mai kakkafeni da ido. Haƙiƙa kalmomina sun soke shi ba kaɗan ba. Ya jima shiru wanda bai san mi yake nazari akai ba sannan daga ƙarshe ya jinjina kansa tare da haɗiye wani abu daƙyar a maƙogoronsa sannan ya ce. " Okay! Zan faɗa miki gaskiya ɗaya Bibi...ba zan ɓoye miki komai ba., Eh, da gaske Su Jadda sun matsa akan sai na auri Noura, sun ce dole sai na aure ta, amma ba don..." Ban san lokacin da na runtse idanuna ba ina wani girgiza kaina ina ci gaba da zubo da ruwan hawaye, a karye na ce. " To ka ji fa dan Allah! Kenan duk sadaukarwar da na yi musu na yi ta a banza kenan? A idon su sam ban yi darajar da za su ɗaga mini ƙafa ba su bari na rayu da kai ni kaɗai koda na tsawon shekaru uku ne kacal ba, a misali kenan? Ashe ban cancanci hakan ba? A GANIN IDO na ne ashe suke nuna suna so na amma daga zaran na juya baya ni ce babbar maƙiyayarsu abokiyar gabar su? Sakayyar su a gare ni kenan bayan na ƙwato musu kai a bakin Kura? Za su aura maka wata, watan ma Noura, wacce suke ganin tafi da cewa da kai, domin ta haɗa komai na rayuwa ni kuma ban cancanta ba...ko secondary school ban kambala ba, a islamiyya ma ban yi nisa sosai ba..." Yanzu kam sosai yake kuka kamar yanda nake yi. Tamkar wani ɗan maye haka ya ƙara kusanto inda nake yana faɗin. " Stop saying that about me...you know that I will never do that for you...domin ni ɗin ɗan halak ne...a yanzu sai Ince kin fi sanina fiye da kowa, ba zan taɓa aikata miki hakan ba. Idan ma na yi hakan kuma...Allah ma ba zai barni ba, domin na ci amanar marainiyar yarinyar da ta yarda dani.. " Numfashi ya ja a hankali sannan ya sauke yana mai ƙara matsoni sosai ya ƙara kwantar da murya ya ce. " Bibi! Yes! Su Jadda sun matsa sun kuma tsaya kai da fata..sun ce idan na aure ta zamu yi farin ciki a tare mu uku...but ba hakan ba ne!" Bakin gaskiyata har cikin zuciyata na girgiza kaina ina mai jin wani iri game da su na ce. "Ba zan ɓoye maka ba...sam ban ji daɗin yanda su Jadda suka juya mini baya ba." Hannuna ya yi nasarar ruƙowa yana mai matso da fuskar sa dab da tawa sosai ya ce. "ki yi haƙuri dan Allah. Abin da nake ta gudu kenan...but ni kece farin ciki na, ban san kowace mace ba idan bake ba. I'm not a boy, I'm a man...and as a man...i choose only you." Buɗe idanuna na yi sosai na kallesa ina jin wani iri a zuciyata na ce. " Idan har ni kaɗai ka zaɓa to me yasa ka yarda da zancen su? Idan har su basu ga cancanta ta ba ai kai ka gani ko ba haka ba?" Ɗan taune lips ɗinsa ya yi kaɗan yana mai shafa bayan ƙeyar kansa ya ce. "Saboda sometimes...bin umarnin iyaye shi ne maslaha Bibi..na rasa su na tsawon shekaru, ina jin tsoron bijirewa maganarsu kada su ce don mahaifiyata bata raye ne naƙi yi musu biyayya..amma ki yarda dani cewa tun farko har zuwa yau ban amince ba..bazan iya saka mace biyu a zuciyata ba, domin wurin ki ne ke ɗaya, ina jin tsoron rasa ki Bibina, shiyasa na kasa sanar miki, ina jin tsoro da fargabar aikata wani abun da zai karya miki zuciya.... " Sama ya yo da hannuna ya ɗora akan saitin zuciyarsa yana faɗin. " Feel my heart...Does it feel like someone that's wants to hurt you? Har abada ba zan iya cutar da ke ba Bibi, har na mutu...." Sosai na ji gaɓoɓin jikina sun saki, maganganunsa sun hudani, na ji gabaɗaya kamar na yarda da duk abinda yake faɗa mini. Tabbas a tsorace yake, kuma duk ya birkice kamar ba shi ba. Yanda nake ƙonewa shima haka ya ke ji a ransa. To amma muddin aka ce auren sa zai tabbata da Noura to ni kuma sai dai na haƙura da shi gabaɗaya, saboda ba zan yarda na rayu da dangin mijin da basa so na ba kamar yanda ya faru da Ammiena. Silar hakan ne yasa ta ƙare a matsala. Hannunsa na janyo nima na saka na share hawayena, amma ba don sun daina kwarara ba. wani kallon na shiga bin sa da shi ina girgiza kaina na ce. " Dayaa! Ina son ka sosai kamar yanda ka ke ji kaima...zan iya cewa ma na fi ka zurmawa da yawa domin ni da kai kaɗai na fara so, saɓanin da kai da ka taɓa son wasu a baya Allah ne bai nufa ba. Ni kuwa, kai ne kaɗai wanda na fara so, kai ne wanda ya koyar dani komai, ban san wata kalar soyayyar ba idan ba taka ba. Dalilin hakan yasa nake jin tsananin kishin ka wanda nake ji zan iya mutuwa idan kace za ka haɗani da wata macen, zan daina moruwa in daina gane komai idan ta tabbata cewa da gaske kai ɗin ba so na kake yi ba kuma za ka iya rabuwa dani watarana...idan har aurenka ya tabbata da Noura...to tabbas zan haƙura da kai har abada..." Hannayensa ya saka ya janyoni sosai tare da ɗora kaina akan ƙirjinsa ya rungumeni. Wani irin riƙo ne ya yi mini tamkar wanda akace za'a ƙwace masa ni. Sosai hankalinsa ya tashi da jin irin furucina, tunani ya shiga da kuma neman mafita wa rayuwar aurensa, Bibi itace rayuwar sa da kuma abin da yake cikinta, saboda haka dole ya ɗauki action ɗinda zai ceci aurensa ya hana masa samun tangarɗa. Haɓata ya ɗago tare da sanya hannunsa ya share mini hawayena sannan ya saita narkakkun idanunsa cikin nawa murya a ƙasa sosai ya ce. "I love you Bibi...i love you in a way that I can not explain in one language... Saboda babu wani harshen da ya isa ya kwatanta irin yadda kike a zuciyata. Ni mijin ki ne Bibi, da ni kaɗai ya kamata ace kin yarda. Babu wani zancen cewa wai zan auri wata na wulaƙantaki, babu wani abu makamancin cewa wai ke ɗin ba class ɗina ba ce, ke ce Mace mafi daraja da girman da tafi dacewa da Engineer Muhammad Attahiru Araam..kece rayuwata, kece nutsuwata, kece abokiyar tafiyata a duk inda zan sanya gaba, kece addu'ata cikon mafarkina. Ba ki yi zurfi ilmin boko ba...so what? Ke irin ilmin ki, wayonki,hankalinki, basirarki da kuma kaifin tunaninki ya zarta na dubban mata. A haka nake son ki, a haka nake so da burin ƙare rayuwata dake Bibi..wanene yafi dacewa dake idan ba ni ba?" Kallon sa nake kallon da babu ƙyaftawa a ciki...zuciyata sosai na ji ta ɗauki sanyi a hankali tana samun sarari saɓanin kasancewarta a cunkushe tsawon lokaci. Hannunsa ya sanya a nawa ya yi twisting sannan ya ɗago sama ya sumbaci bayan hannun nawa yana mai jinjina kansa ya ce. "Ni Mijin Beenafah...Daddyn babynmu da yake ciki...na yi alƙawari  a yau, ina kuma yi wa Bibina Alƙawarin cewa...I will never replace you in my heart, I will not marry another wife...tunda har bakya so..mi zai sa na aikata? I don't care about duk wani abun da za su ce...farin cikin ki..shi ne kaɗai abinda na sani....yes! I choose your smile, I choose your peace and I choose our Marriage over their talks....ina neman gafararki akan barin zancen nan da na yi har yakai kunnenki ya dami zuciyar ki ya hana mata sukuni, maganata ta ƙarshe da zanyi shi ne, ba zan aure ta ba muddin hakan shi ne ci gaban dariyarki da walwalarki..." A ɗan razane na jinjina kai na na ce. "Da gaske kake ba za ka aure ta ba?" "You have my word Bibi...Ba zan yi ba. Komai za su ce, ko wane irin hukunci za su ɗauka, ba zan aure ta ba. Ki yarda dani." Rungumesa na yi ina mai jin wata nutsuwa da sanyin rahama na ratsani.  Wani abu na ke ji mai kama

Chapter 53 of 67