Share this page
haka ka nuna bani da wata daraja ko wata ƙima kenan..... " " No..no..please Ziza,wallahi that's not what I meant...ko kaɗan ban faɗi haka wai don in tozarta ki ba ko kuma wulaƙanci... I love you... I love you so much Ziza kuma hakan ba zai taɓa canza wa ba, ke ɗin matar rufin asiri na ce kuma ina matuƙar alfahari da hakan domin tsawon zamanmu ban ga wani babban kuskurenki da zan ce Allah wadai ba...please try to understand me Ko kaɗan ban da nufin wuƙalanci a gare ki.. In fact gidanki daban na ta daban...Babu wacce zan wulaƙanta kuma ba zan bari wata ta wulaƙanta wata ba a cikinku,... And kasancewar ki babba, dan Allah let's peace and harmony reigns between us...... " Cike da jin wani irin sabon baƙin cikin ta girgiza kanta ta katse shi da faɗin. " Emraan ko a ƙarƙashin ƙasa za ka sakata wannan duk a banza domin ba'a canzawa tuwo suna, muddin ka aureta ta riga ta zama kishiya ta kuma wallahi tallahi na rantse da Allah hakan ba zai faru ba domin baka isa ba wallahi!!!" Jinjina kansa ya yi yana mai jin wani irin ɓacin rai ya ce. " Haka ki ka ce ko?" " Eh haka na ce Emraan!" Miƙewa ya yi tsaye kamar yanda ta tsaya a kansa suna fuskantar juna ya ce. " To bari ki ji Aziza...Tun da har na biki da lalama kuma baki saurare ni ba, shikenan! Zan yi aure, kuma zan auri Beenafah, dan Allah idan kin isa ki hana. Zaman lafiya akace ya fi zama ɗan sarki... Da wannan yasa nake so mu yi komai cikin ilmi da wayewa..." Wani irin matsanancin kuka ne ta sake fashewa da shi tana faɗin. " Haka ka ce? Haka ka ce ko? Wallahi tallahi za ka gani! Matuƙar dai na amsa sunana ni Ziza Ashraf wallahi tallahi ba za ka aureta ba... " Zaunawa ya yi a hankali ya janyo glass cup ɗinda ta kawo masa ya tsiyaya lemu da nufin sha amma cikin zafin nama ta saka hannu ta ture kayan gabaɗaya suka watse a ƙasa suka tarwatse. Miƙewa ya yi kurum ba tare ya ce mata komai ba yasa kai ya fice daga gidan gabaɗaya. Wayarta ta ɗauko hankali a tashe ta kira wayar Mummy Raliya. Tana jin ta ɗauka a gigice ta ce. "Mummy na shiga uku na lalace Mummy.... Wai Emraan kishiya zai mini kuma kishiyarma 'ƴar aiki..." Daga can ɓangaren Mummy Raliyar ta ce. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!....Please cool your mind...Samu wuri ki zauna ki kurɓa ruwan sanyi sannan ki yi wannan addu'ar; ki ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Allahumma ajirni fiy-musibati-Wa Akhlufni khairan minha...please ki yi yanda na ce miki yanzu, idan kin kambala sai ki kirawo ni muyi magana. " A gaggauce ta aikata duk abinda ta ce mata exactly sannan ta sake ɗaukar wayar ta kira ta ta ce. " Mummy na yi duk abin da kika ce...." A hankali ta jinjina kanta ta ce. " Masha Allah, In Sha Allahu ko mine ne zai zo miki da sauƙi... " " Mummy kishiya fa na ce miki Emraan zai mini kuma da mai aiki..." "Duk na ji! Amma ki sani, tashin hankali ko wani barazanar ki ba zai sa ya sauya ba, in dai ma namiji ne sai da ya ƙara miki baƙin ciki akan baƙin ciki muddin kika ce ba za ki shafawa kan ki ruwa ba.....Hajiyarsa ta sani?" Ido cike da ruwan hawaye ta ce. " Hajiya bata sani ba, na tabbata bai isa ya faɗa mata wannan abun kunyar ba...." "To Labiba fa?" Cikin jin wata irin tsanar Labibar a lokaci ɗaya ta ce. "Ya sanar mata, dole ita zai sanarwa tunda ita ce babbar munafukar da ta kawo yarinyar gidan na su wai da sunan mai aiki, wallahi tallahi wannan munafukar yarinya daman ba ta yi kama da mai aiki ba kawai dai munafurci suka shirya wanda tun farko ban gane ba ma sai yanzu... " " Duk da haka dai, ki bari abi komai a sannu Ziza, tashin hankali babu abinda zai haifar idan ba ƙarin matsala da ɓacin rai ba... " Cikin wani irin kuka ta shiga girgiza kanta tana faɗin. " Ai na san haka za ki ce Mummy....daman nasan haka za ki ceee... " Daga haka ta yanke wayar tare da jifa da ita a ɗayan kujerar da take zaune. ******** Sai da Mummy ta share kusan kwana uku a asibiti, ta suma ta farfaɗo ta suma ta farfaɗo haka ta dinga yi sai daga ƙarshe suka samu aka samo kanta da ƙyar sannan suka tattara suka dawo gida. Gabaɗaya ta susuce ta gigice ta fita hayyacinta, ko kaɗan ko a mafarkinta bata taɓa zaton cewa wai Hassana za ta iya bijire mata ba har da haɗa kayanta ta tsere. Wannan wane irin tozarci ne da abun kunya? Tana zaune Aysha na ta aikin ba ta baki ta ɗago idanuwanta da suka rine sosai suka yi sasul akan kuka ta kalli Ayshar ta ce. "Aysha duk an bincika ko'ina ba'a ga Hassanar ba har yanzu? Ko ba'a je neman ta ba ne? Ina Alhajin yake?" Cikin tausasawa Aysha ta ce. "Mummy ki kwantar hankalinki In Sha Allahu za a ganta..." Hannu ta saka da ƙarfi ta ture kofin shayin da Husaina take bata tamkar wata mai taɓin ƙwaƙwalwa ta shiga kallon su tana faɗin. "In kwantar da hankalina kike cewa Aysha?? Miyasa kike yin wasu abubuwan da yasa nake jin kamar bakya ƙaunata? Kin san irin kalar alƙawarurrukan da ke tsakaninmu da gidan Alhaji Mansur ɗin idan har wannan auren ya tabbata? Ni karan kaina akwai wani kamfaninsa da ya yi alƙawarin mallakamin, suma su Hassana akwai abubuwa da dama da za su mallaka na manyan kadarori,...waccan jibgegiyar motar da kika gani fa sabuwa tare da lefen nan aka kawo Alhaji ita kyauta, an ce ta amaren da tawa suna hanya...sannan har cikin shares ɗinsa ya yi alƙawarin mallakawa Alhajin da kuma Hafiz wasu daga ciki da zaran an yi auren kafin nan kuma Hafiz ya iyarda kambala karatun sa ya dawo..." "To Mummy idan ban ce ki yi haƙuri ba mi zan ce? tun fa ranar Daddy ya aika har garin su Salman ɗin amma ba'a samu labarinta ba, har kulle Salman ɗin akayi sai jiya aka sake sa amma kuma shi kan shi an yi duk binciken da za'a yi amma bai san inda take ba. Gida ma duk su Alhaji Baba su Uncle Isma'il kowa ya ce bata je wurin sa ba... " Girgiza kanta take tamkar wata mahaukaciya tana faɗin. " A'a, wallahi tallahi wannan ƙarye ne... Wayyo Allah na! Wayyo ni Zaliha! Hassana ta tona mini asiri, na shiga uku na lalace..." "Innalillahi! Dan Allah mummy ki yi haƙuri. In sha Allahu za a gano inda take..." "Ina Alhaji yake??" "Daddy tun safe ya hau jirgi zuwa Australia an yi mishi kiran gaggawa daga makarantar su Hafiz." Komawa ta yi luf ta kwanta jikin kujera kamar wata marainiya tana mai share hawaye akai-akai abin duniya duk ya bi ya isheta. ******* Tun da Daddy ya karɓi saƙon gayyata ta gaggawa through Email ɗinsa daga makarantar su Hafiz hankalinsa ya tashi, gabaɗaya ko baccin kirki ya kasa yi akan wannan dalilin, kwana ya yi yana tambayar kansa miye ya faru da har ta kai aka aiko masa da official letter of misconduct? Miye Hafiz ɗin zai aikata haka da zafi? Yaron kirki mai matuƙar basira miye zai faru haka? Tambayoyinda ya yi ta jerawa kansa kenan daga cikin zuciyarsa waɗanda yasan tabbas ba shi da amsar su sai dai idan ya isa makarantar ya gani ya kuma jiye ma kunnen sa. A hankali ya taka ya shiga Main Admin block ɗinsu Wanda daga nan reception aka dangana shi da office ɗin vice Chancellor Mai suna Professor Dean Michael inda a nan ya tarar da Head of academic, Register, Discipline committee, sauran head of department da kuma sauran lecturers wanda daga cikin su akwai Mr. Collins. Gefe ɗaya kuwa, Hafiz ne tare da sauran ɗalibai en uwansa su takwas. A hankali Daddy ta taka ya je ya samu ɓangaren inda sauran iyayen yaran suka zauna shima ya zauna riƙe da file ɗinda aka bashi tun daga Reception ɗin. Vice Chancellor ɗin ne ya fara magana cikin harshen turanci cike da girmamawa ya ce. " Good afternoon all, muna yi muku barka da zuwa kuma mun gode muku sosai da har kuka iya amsa gayyatarmu akan lokaci kuka halarta daga sasassa daban-daban na faɗin duniya. Muna fata kuma za ku bamu haɗin kai domin gudanar da abin da ya tara mu a nan cikin girmamawa da mutuntuwa....." Bayan sun gama gudanar da duk wasu bayanai da tsare-tsaren su sannan Mr. Anderson daga Discipline committee ya janyo file ɗinda ke gaban sa ya buɗe shi ya fara bayani da cewa. " Mun kira ku nan ne akan manyan laifukan da aka kama yaranku sun aikata, waɗannan laifuka ne da suka shafi both academic and moral standards na wannan makarantar." Tsit ɗakin ya yi tamkar ba kowa a ciki tsabar yanda daga yaran har iyayensu suka sha jinin jikinsu, ba ma kamar Hafiz ɗin. A hankali ya ci gaba da cewa. "Waɗan nan laifukan su ne waɗanda muka same su da su bayan yin ƙwaƙwƙwaran bincike yanda ya kamata tare da tuhumar yaranku akan laifin kuma suka amsa ba tare da sun musa mana ba, Hafiz Mudassir Wazeer; Laifinsa na farko akwai academic fraud. Hafiz ya haɗa baki da Mr. Collins ya biya sa kuɗi masu yawa ya shirya masa false academic records na fake result ɗin semesters shida, wanda ya nuna yana da high scores amma kuma bayan biyar diddiƙi na ainahin result ɗinsa mun gano ko wace semester GPA ɗinsa is below 1.50 GPA. Laifi na biyu kuma shine;Bribery and corruption. Ma'ana mun samu ƙwararan shaidu da suka nuna cewa Hafiz yana turawa Mr. Collins maƙudan kuɗaɗe akan ya riƙa canja masa result ɗinsa a kowace semester. Sai kuma na uku, wanda dukkan su ne ta shafa har da sauran waɗan nan ɗaliban na Repeated misconduct, An sha kama su ana kawo mana ƙarar su daga security campus a wuraren da bai kamata ba, suna shaye-shaye,lalata da yaran mutane, da kuma gurbata rayuwar salihan ɗalibai zuwa mutanen banza. Sun kasance suna yawan shirya abubuwa waɗanda suke taka mana dokar makaranta,sannan ga rashin girmama malamai da yi musu rashin ɗa a. Na huɗu kuma;Akwai poor academic performances Wanda for the past four semesters Kowanne daga cikin su ya yi failing Registered courses da Kuma missing five official exams without any genuine reasons. Sai abu na ƙarshe kuma;Forgery of official document. Ma'ana, an gano cewa Hafiz yana printing fakes progress reports yana aikawa gida Nigeria yana yaudarar iyayensa da sunan shi ɗin mai ƙoƙari ne alhali ba haka bane." Cikin tashin hankali kowa ya hau faɗin albarkacin bakin sa, cike da baƙin cikin abin da yaran na su suka aikata musu bayan sun jima suna kashe musu maƙudan kuɗaɗe. Wasu irin hawayene masu matuƙar ɗaci da ƙuna suka gangarowa Daddy wanda ya ƙura ido kawai yana kallon Hafiz. Wata envelope ce Head of academic ya bi dukkan iyayen na su ya rarraba musu bayan an ba su dama cewa idan akwai mai wani ƙorafi ya yi. Bayan ya gama miƙa musu a hankali ya ce. "Wannan ita ce takardar official expulsion, ma'ana;an kore su daga wannan makaranta. Muna fata za ku yafe mana domin dole ce ta sa muka aikata hakan." Waje suka dawo wanda har yanzu ya kasa buɗe baki ya furta masa wata magana kamar yanda shi ma Hafiz ɗin ya yi tsamo-tsamo tamkar an tsoma kaza a ruwan zafi. Kwata-kwata Hafiz bai tsammaci zuwan wannan ranar ba a rayuwar sa. Ya ɗauka cewa salin asalin zai gama baza life ɗinsa ya amshi fake result ɗinsa ya koma gida, ashe-ashe rana dubu ce ta ɓarawo rana ɗaya ta mai kaya. Yanzu ga shi son zuciya da ganin kuɗi yasa ya rushe rayuwar sa, bama kamar yanda Mr. Collins ya dinga kuka bayan shi ma an kore sa shi ne abinda ya tsaya masa a rai. Duk irin yanda Mr. Collins ɗin ke ta baya-baya gashi sai da ya jefa shi a matsalar da yake gudu. Suna nan tsaye sunyi cirko-cirko sai ga motar jami'ai ta iso wurin, a gaban iyayen na su aka ɗauke su zuwa office ɗin immigration domin a fitar da su daga ƙasar Australia cikin kwanaki uku da kuma izinin cewa kada su sake dawowa ƙasar har abada kamar yanda dokar ta su ta tanada. ******* Jafaru kuwa, yana Zaria ƙaninsa Hamza ya kira shi yana ƙyanƙyasa masa halin da ake ciki na cewa, idan bai dawo ba wallahi sai an aurar da Beenafah ga Ashiru domin har sun zo shi da iyayensa wurin neman auren na ta. A gigice ya baro Lectures ya juyo ya dawo gida. Ita dai Mama tana zaune ita da Bahrain da Farisa suna ƙulla guggurun da ta gama yi yanzu taga mutum ya shigo mata hankali ta she yana faɗin. "Yanzu Mama Beenafahr tawa ce ake zancen a aurawa wani ita? Mama wai ko don ban taɓa faɗa muku bane ina sonta?Wallahi tallahi ina son ta, babu wacce nake so a cikin raina idan ba ita ba, dan Allah Mama ki faɗawa Baba wallahi ita nake so na aura..." Hannu Mama ta miƙa masa hankalinta kwance ta ce. " Bani kuɗin sadakin ka, lefe, sannan ka nuna mini gidanda zaka ajiye ta...." Shiru ya yi tare da ƙura mata ido domin ya rasa bakin magana. Kwata-kwata shi bai tsammaci wannan magana daga bakin ta ba. "Ka yi shiru! Bani sadaki da lefe na ce, sannan ka nuna mini gidan da za ka sakata a ciki, da kuma sana'ar da kake wacce za ka iya riƙe ta sannan kuma ka ci gaba da ɗaukar nauyin karatun ka...." Gunguni ya fara ƙasa-ƙasa yana faɗin. "To amma ai Mama komai na duniya ɗan a hankali ne..." Jinjina kanta ta yi tare da ƙara tamke fuska ta ce. "Allah ko! To ai tun kafin a haifeka na san cewa komai na duniya ɗan a hankali ne.... Tabbas da ace kana da waɗannan abubuwan da na lissafa da dani da Malam ko sama da ƙasa za ta haɗe sai mun tsaya akan dugaduganmu mun tabbatar cewa ka same ta....amma yanzu Jafaru magana ta gaskiya ka yi tsaga da faɗi. Da ma ace itama karatu take kamar kai, da na san tabbas za ku iya yin daidai... " " To Mama dan Allah a sakata makarantar mana, sai mu jira juna ni da ita... " " Jafaru! Jafaru! Ka wuce ka mayarda hankali akan karatunka ko dan goben ka, ka sakawa kanka salama domin ba za ka taɓa samun Beenafah ba... " Cike da wani irin ƙunci da damuwa ya ce. " Dan Allah Mama ki fahimtar da su cewa su mayarda ita a makaranta wallahi na san zamu yi daidai.. " Jinjina kai ta yi ta ce. " To je ka ka fahimtar da su Jafaru." A nan ya yasar da jakar sa da yazo da ita ya fito afujajan ya nufi gidan Ammie ransa na masa wata irin suya. Ammie na tsaye tana shanya kayan Bahrain a igiya ya yi sallama ya shiga. Kallo ɗaya Ammie ta yi masa ta fahimci kwanan zancen, daman ta san tabbas za'a rina wai an saci zanin mahaukaciya. Ido a rufe ya fara masifa da faɗin. "Ammie miyasa za a nemi bayar da Beenafah alhali ni ɗin ina sonta?? Wannan ba adalci ba ne, babu wanda zai aure ta ya kula da ita fiye dani,..." Jinjina kai tayi cikin tausasa murya ta ce. "Na sani Jafaru....amma samu wuri ka zauna mu yi magana." A nan inda yake tsaye a nan ya darɓe zaune yana mai ƙure ta da kallo alamar yana jira ya ji mi za ta faɗa masa. Kujera ta janyo ta zauna suna fuskantar juna cikin ƙara tausasa maganarta ta ce. "Na san cewa kana son Beenafah, na fi kowa sanin yanda kake sonta,kuma idan har Allah ya rubuta cewa Beenafah matar ka ce, to babu wani mahaluƙinda ya isa ya hana, idan kuma Allah ya rubuta cewa ba matarka ba ce duk yanda aka so ba za ka aure ta ba. Abubuwan sun juye fiye ma da yanda muka tsammata Jafaru. Kuma ina neman alfarma a gareka....kamar yadda ka ji tana cewa tana da matsayi a gareka na soyayya, to ina so ka sake bata wani ɓangaren a zuciyarka na zamto wa ƙanwa a gareka, ka ɗauketa tamkar Fakiha wacce duk rintsi za ka tsaya mata a matsayin Yayanta mai kare mata mutuncin ta. Idan har Allah ya nufe ka da aurenta ba ni da ja da hakan, idan kuma ya ƙaddaro cewa wani daban ne za ta aura to za ka yafe mata ku ci gaba da zumunci. " A hankali kukan da yake riƙewa ya kubce masa da ƙarfin gaske tamkar wata Macce. Tashi ta yi taci gaba da abin da take ba tare da ta yi yunƙurin hana sa kukan ba. Sai da ya yi sosai wanda har sai da ya ji zuciyarsa ta ɗan sanyaya sannan ya sassauta tare da miƙewa a tsaye ya kalle ta murya a dusashe ya ce. "Na gode Ammie, idan Beenafah rabona ce ina fata Allah ya mallaka mini ita, idan kuma ba rabona ba ce ina yi mata fatan alheri da fatan farin ciki mai ɗorewa har zuwa ƙarshen rayuwarta." Daga haka ya juya ya fice ba tare da ya jira amsar ta ba. Jikin gini ta tsaya shiruu! Tana jujjuya al'amarin a zuciyarta, wallahi tallahi ta yi matuƙar tausaya masa a yau kamar yanda take tausayawa Ashiru. Duk irin amsar da shima ta bashi ya ce sam ba zai haƙura ba, ƙarshe ma cewa ya yi ta bashi numbern Daddy da address ɗinsa shi zai je har Abuja ya same shi. Jin ya matsa ya dage akan dole sai ta bashi yasa ta ce yaje tsohon gidanda suka taso wurin Uncle Isma'il ya bashi numbern Daddyn da address ɗinsa. ********* Ziza kuwa, tun da Emraan ya sa ƙafa ya bar gidan bata sake sanya shi a idonta ba, kiran duniya ta yi kuma ya ƙi ya ɗaga wayar ta. Gashi bata ma son haɗa fuska da Labiba ballantana taje ta koka mata halin da take ciki. Sannan ta yi tsammanin Hajiya za ta zo gidan ta sameta idan ta ganshi a gidan amma kuma ba ta yi hakan ba wanda shi ne abin da ya ƙara tunzura ta. Shawara take na ta kira Baba Ustaz Ƙanin Mahaifin Emraan ɗin ko kuwa ta ɗan ƙara jira ta gani. Ƙarshe dai haka ta miƙe ido cike da ruwan hawaye ta ɗauki Abeer ta je ta shiga motarta ta wuce gidan Hajiya. Tana shiga gidan ta wuce har bedroom ɗinta ta zauna a sofa ko gaisawa bata jira sun yi ba kawai ta fashe mata da kuka. A hankali Hajiyar ta ajiye turarukan da take gyarawa ta zo ta zauna a edge ɗin gadonta suna fuskantar juna ta ce. "Subhanallah! Ziza Lafiya kuwa?..." Cike da damuwa ta ce. "Hajiya yanzu abin da Emraan zai mini kenan? Ga mari ga tsinka Jaka! Sannan Hajiya ace kina ganin sa amma ba za ki masa magana ba..." "Bayani za ki yi mini yanda zan fahimta Ziza, go straight to the point please." "Hajiya Emraan ne ya sameni da zancen wai zai ƙara aure, kuma auren ma da Beenafah wanda na san bai faɗa miki ba, to wai don saboda na nuna rashin amincewa ta shi ne ya baro gidan ya dawo nan yau tsawon kwana biyu cikin na uku. Yanzu Hajiya dan Allah hakan adalci ne?" Girgiza kai Hajiya ta yi tana mai kallon ƙwayar idanunta ta ce. " Magana ta gaskiya, na san da zancen auren amma kuma ban san cewa yana gidan nan ya yi miki ya ji ba tsawon kwanaki... " Wani iri dummm! Ta ji a ƙirjinta tamkar an soka mata Mashi jin furucin Hajiya a gareta...Yanzu kenan tasan da zancen auren na shi kuma shi ne take zaune hankalinta kwance? " Ki yi haƙuri, In Sha Allahu zan mi shi magana... " Wata irin zabura ta yi ta miƙe tsaye ranta na mata wata irin suya a gigice tana kallon Hajiyar ta ce. "Yanzu Hajiya abin da ma za ki ce kenan, duk irin ƙuntatamin da ya yi ya bar ni tsawon kwana biyu sannan ga zancen auren da ya yi duk baki ga wani laifin sa ba, abin da zaki ce kawai shi ne in yi haƙuri za ki masa magana! Ba za ki kira sa a gabana gani ga shi ki yi mana hukunci ba? Ya rasa wacce zai aura sai Mai aiki? Wallahi tallahi ba zan yarda ba! Wallahi ba zan yarda ba... " Daga haka ta juya ta bar gidan gabaɗaya ta koma gida ta shiga haɗa kayan ta. Hajiya kuwa, Wayarta ta janyo cike da al'ajabi ta shiga kiran Emraan ɗin amma kuma bai ɗaga ba. Mamaki take wai ace Emraan yana gidan tsawon kwana biyu ba tare da ta sani ba, jiya ya shigo da yamma, shekaranjiya ma ya shigo da dare amma kuma duk bai wani jima ba ya tafi. Bayan ta yi ta kiran wayarsa bai ɗaga ba, ƙarshe ta fito da kanta ta je ɗakinsa amma kuma baya nan babu wata alama da ta nuna mata ma cewar yana gidan. To ko dai wani wurin ya je ba nan ba? Da haka ta sake juyawa ta koma ciki ta ci gaba da ayyukanta. Tunani take a ranta cewa tun da har taji hatta Hairiyya bata kira ta akan wannan maganar ba to ta tabbata babu wacce ya sanarwa daga cikin su, daga Labiba har Nadeeya babu wacce ya sanar wa. Saboda haka so take sai ta fara magana da shi sannan ta san irin hukuncin da ya kamata ta yanke. Ta na nan dai Misalin ƙarfe biyu da rabi na rana, ganin har yanzu bata samu magana da Emraan ba kuma shi bai zo ba yasa ta ɗaga waya ta kira Haula ta ce mata ta faɗa mini cewa tana son ganina yanzu. Ina zaune bayan na kambala sallah na yi shiru ina nazari. Baccin da na yi ne mai nauyi har yasa na makara wurin gabatar da sallar Zuhr ɗin. Suna zaune a gefe suna cin abinci Hajiya ta kira ta ina ji ta ce tana son ganina. Kallona Haula ta yi ta ce. "To tunda kin ƙi kici abinci ta shi kije Hajiya tana neman ki." Miƙewa kawai na yi na fito waje na samu wuri na zauna tsawon lokaci, sannan daga ƙarshe na tashi na shige cikin gidan ba tare da sanin dalilin kiran ba, sai dai kuma ban kawo komai a raina ba domin tun ina jin ɗar-ɗar na cewa za ta yi mini magana akan Emraan, ko ita ko Aunty Labiba har na zo na daina damuwa domin a tunanina shi ka ɗai ne yake shirmensa ba tare da kowa ya sani ba. Sannan kuma sanin cewa Daddy ya ce zai aurar dani ga Ilyas yasa na daina damuwa da al'amarin Emraan ɗin domin nasan Ihu ne kawai yake bayan hari, domin tun da Daddy ya furta, to kuwa nasan tabbas zai cika. A hankali na tura ƙofar tare da yin sallama na shiga na zauna a ƙasa ina faɗin gani. Sai dai kuma, ganin mutanen da ke zaune a ɗakin ne ya yi matuƙar ɗaga mini hankali ganin babu mutum ƙwaya ɗaya da na sani a cikin su sai Hajiyar. Wayarta dake gefe ce ta shiga ɓurari ba ƙaƙƙautawa. Sai da tayi kamar ba za ta ɗauka ba sannan kuma daga ƙarshe ta janyo ta duba,ganin sunan babbar ƙawarta Hajiya Samira dake zaune a Lagos, yasa ta yi saurin ɗaga wayar tana faɗin. "Ziza ta kawo ƙara ko?" Dariya matar ta yi daga can ɓangaren ta ce. "Kamar ko kin sani! Yanzu ta kirani tana shaida mini shi ne na ce ta jira zan kira ki yanzu..." Miƙewa tayi tare da ɗaukar excuse a wurinsa ta fice daga parlourn domin amsa kira. Suna ganin ta fice suka juye baki suka yi ta magana da turanci wanda na san hakan ba ya rasa

Chapter 23 of 67