Share this page
wurin da aka tanadar mana na musamman Jaddi ya miƙe yazo ya riƙo Hannun Ya Mohaa suka tsaya akan stage da aka tanada domin yin magana ya fara magana cike da alfahari cikin harshen larabci da cewa. "A matsayina na minister of foreign affairs...na haɗa wannan special dinner ce domin gabatar muku da Jikana MUHAMMAD ATTAHIRU ARAAM wanda ya kasance Jika na farko a gare ni wanda Rania ce ta haife shi. Ya dawo garemu bayan shafe tsawon shekaru ba tare da ya taɓa haɗuwa damu ba. Wannan abun alfahari ne da farin ciki wanda ya same mu, wannan dalilin ne yasa na gayyato ku na musamman domin ku tayamu murna. Shi ɗin ba ɓoyayyen mutum ba ne domin na san da yawa daga cikin ku kusan shi ko don hulɗar kasuwancin sa. Gashi a gabanku ina ƙara gabatar muku da shi cike da alfaharin kasancewarsa jininmu... " Mayar da kallonsa ya yi wurin Ya Mohaa yana murmushi ya ce. " Tonight...is your day Hammodi...Sudan is happy to have you back..waɗannan mutanen duk sun taru ne saboda kai..Ina so ka gaishe su kuma ka miƙa musu kalaman godiyarka" Cikin jin wani irin yanayin farin ciki ya yi masa murmushi tare da jinjina kansa ya ce. " Thank you Jaddi...Thank you all...haƙiƙa nima na yi farin cikin kasancewata a nan. Na kuma yi farin ciki da Allah yasa na kasance ɗaya daga cikin Ahlin SAMI Allah. Ina godiya sosai." Hannayensa ya ɗaga sama yana jinjinawa alamar yana musu godiya sannan ya koma ya zauna. Bayan ya kambala aka gabatar da manyan baƙi suka gabatar da bayanai. Daga nan aka dawo kiran dangin nasa ɗaya bayan ɗaya suka gabatar da jawabi na nuna zallar farin cikin da suke ciki dangane da zuwan sa. Bayan an kambala aka shiga hidimar ci da sha komai gashi nan gwanin burgewa sai nishaɗi ake musamman mu da su Taimiyyah wacce kusan Ita da Suwara ne ke fassara mana duk abin ake gabatarwa wanda bamu san shi ba. Bayan an kambala aka dawo sannan aka shiga bada tarihin sa da gwagwarmayarsa tun daga tasowar shi har zuwa karatunsa da kasuwancinsa wanda ni sai a yau ma nake ƙara sanin wasu abubuwan dangane da rayuwarsa. Bayan an kambala Uncle Mu'aƙƙib ya kira Ya mohaa ya je ya tsaya a gabansa. Wani ne daga cikin baƙin ya taso ya karɓi microphone ya yi bayani sannan daga ƙarshe ya kalli Ya Mohaa ya ce. "Danginka mutane ne masu matuƙar karamci da daraja, sun iya mu'amala da mutane yanda ya kamata kuma sun ji ma suna hidimtawa wannan ƙasa tamu wanda har da mahaifiyarka, domin bamu manta wa da ita ba kuma har abada ba zamu manta da ita ba domin ta kawo mana alkairai da dama a wannan ƙasa tamu. A yanzu...Kai ɗin ka kasance ɗaya daga cikinmu, saboda haka, mun naɗaka a matsayin Special International Cultural Ambassador Domin kawo haɗin kai a tsakanin ƙasashenmu guda biyu....In Sha Allah, za'a zartar da wannan gobe idan Allah ya kai mu." Tafi Hall ɗin ya ɗauka ko'ina cike da farin ciki. Takowa ya yi yazo har inda nake zaune ya kama hannuna muka koma saman stage ɗin a hankali ya ce. "Ni da Matata...dama sauran en uwana. Muna matuƙar godiya da wannan karamci da garin Sudan da kuma mutanen cikinsa da suka nuna mana. Haƙiƙa har abada ba zan taɓa manta wannan ba. A yanzu rayuwa ta ƙara koyar dani wani abu. Ba lallai saika san mutum tsayin shekaru ne za ka samu farin ciki ba...haɗuwa ta ɗan ƙanƙanin lokaci, idan har akwai kyakkyawar zuciya to tabbas ta wadatar. " Haka aka kambala ƙayataccen taron cike da farin ciki kowa ya watse wanda har dare ya lila sosai ba tare da mun sani ba. A jere motocinmu suke tafiya tare da juna har sai da muka kusa isa gida ne ya cewa drivern motar tamu ya dakata. A yanda nake kwance a ƙirjinsa ina nan a haka ban motsa ba, domin ban san dalilinsa na cewa a tsaya ba, wata ƙila akwai abin da yake so ya yi. Pressing waya kuwa da gaske naga yana yi da alama shi ne uzurin. Ƙara lumshe idanuwana na yi waɗanda ke cike da bacci na yi shiru ina mai ƙara gyara kwanciya ta a jikinsa. Sai da suka miƙa sosai kusan 15mnt haka sannan muka ci gaba da tafiya a slow sosai wanda koda muka shiga gidan har kowa ya shige mahutarsa. Muna saukowa na ji ya riƙo hannuna ya ce. "We are going to our room Bibi..." Waro idanuwana na yi na kalle sa jin wata iriyar magana. "Miye kike wani kallona haka kamar wanda ya kauce hanya?" Still bance komai ba na bisa muka fara takawa. Sai da muka kusa shigewa na kalle sa na ce. "To ai babu kayana ko ɗaya a nan. Bari na je na ɗauko." Jinjina kansa ya yi alamar gamsuwa da maganata sannan ya ce. "Do quick please, nasan kina jin bacci sosai." Tun da na juya bai ɗauke kallon sa a kaina ba sai da na ɓacewa ganin sa. Har cikin xuciyata na yi niyyan ɗauko kayana na dawo kamar yanda ya ce. Sai dai kuma, ina shiga ɗakin tunanina ya canza, domin gabaɗayan su suna nan a zaune sun cika ɗakin tab yau hadda Khairum da wasu guda biyu. Duk da cewa ba'a nan za su kwanta ba na san cewa zaman fira suke. Kallona suka yi suna min sannu sannan Suwara ta ce. "Aunty Beenafah sai yanzu?" Wani irin wiƙi-wiƙi na ƙara yi da ido jin kalar tambayarta,ni duk sai ma naji na shige gashi. Aunty Labiba ce da murmushi a fuskarta ta kalli Suwara sannan ta kalle ni ta ce. "Suwara wannan wace iriyar kalar tambayace Mace da Mijinta?" Dariya ta yi ta ce. "Haka ne kuma Aunty Labiba. To a gafarce ni, kin san mu tuzurai sai muga kamar kowa haka yake kamar yanda muke, sai mu riƙa mantawa muna da bambanci da masu aure." Dariya suka fashe da ita suna faɗin. "To Allah ya aurar da ke." Wuri na samu akan kyakkyawan gadona wanda bai cika faɗi sosai ba na zauna a gefe na yi shiruna ina sauraren firar su. Tunanin Dayaa ne ya tsaya cak a ƙwaƙwalwata, na san cewa yana can a tsaye yana jirana. Amma kuma sai dai ya yi haƙuri domin ba zan iya wai ɗaukar kaya na ce zan fita na je wurin sa ba. Ai abun da kunya na tsallakesu na ɗauko kaya da sunan zuwa ɗakin da mijina yake. Muryar Hairi na ji bayan ta taso daga gadonta ta dawo nawa tana faɗin. "Mummy dole daddy ya riƙe ki a hannunsa yau don wallahy ba ƙaramin wankuwa kika yi ba...kinga ko a hall ɗinnan yanda yake wani kallon ki yana rirriƙe ki kamar wanda akace za'a ƙwace masa ke. Duk wani motsinki ina gani fa akan idonsa, da kin yi zai ce Bibina lafiya. Kai...Wallahy soyayya ta yi a rayuwa." Hannuna na kai da sauri na toshe mata baki ina mai ƙara zaro ido waje murya a ƙasa sosai na ce. " Hairi kina cikin saitin ki kuwa? Ba kiga mutane ba?" Miƙewa tayi tana dariya ta ce. " To ai bani kaɗai ba...duk wanda yake wurin nan kowa ya lura da ku, shiyasa tun ɗazu muke firar ku." Ya Allah! Abin da na furta kenan a raina tare da juyawa na kwanta ina mai basu baya domin ni dai ba zan iya da wannan kayan kunyar ba. Ya Mohaa kuwa, tun yana tsaye yana jiran fitowar ta har sai da yakai ga jinginawa jikin bango yana ta baza ido yana zaman jiran gawon shanu. Mamaki ne fal a ransa ganin har yanzu daga zuwa ɗauko kaya ace bata dawo ba. Ga wayar ta a hannunsa kuma ballantana ya kira. Cikin Seconds ya kamo sabon layin Aunty Labiba ya kira wanda aka sayawa kowa a jiya domin amfani. Tana ganin kiran ranta ya bata cewa Beenafah yake nema. Tana receiving bai ko tsaya ya ji maganarta ba ya ce. "Ki bai wa Bibi waya.." Kallon inda nake kwance ta yi ta ce. "Mummyn Adeel ungo ga Daddy yana son Magana da ke." Ƙara lafewa na yi ina mai yin baccin ƙarya kamar bana jinta, kiran duniya tayi min amma ban nuna alamun naji ba. Hakan yasa ta ce. "Daddy ta fa yi bacci." Katse kiran ya yi a hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe su kamar ya ɗauke wuta ya rarrafa ya shige building ɗin. Toilet ya shige kai tsaye ya kunna shower ya sakarwa kansa ruwan sanyi tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ya yi wanka yayo alwala kamar ko yaushe ya zo ya tsayu amma bai tsayu da nisa ba kamar sauran darare ba ya kambala yaje ya Kwanta. Koda ya farka haka ya tashi kaca-kaca wanda dole ba shiri ya fara zuwa yayi wanka sannan ya shirya ya fi ce masallaci. Ni kam koda na farka na yi lattin tashi sosai domin har sun gama haɗa abin kari duk tare da su Aunty Nadeeyah a kitchen wanda tun jiya muka ce yau damu za'a yi aikin tare da su Taimiyyah da sauran masu aikin su don muga yanda ake yi. Sai yanzu na cire kayan jikina dana kwanta da su bayan na yi wanka. Ina gama shiryawa na fita na shige ɗakin Jadda. Turus na yi na tsaya ganin Ya Mohaa a kwance, ya ɗora kansa akan ƙafar Jadda suna murmushi a tare yayin da naga laɓɓanta suna motsawa da alama akwai firar da take mishi. Sallama na yi musu tare da zuwa gabanta na duƙa na gaisheta cike da ladabi. Ƙara Faɗaɗa murmushinta ta yi sannan ta miƙo hannu ta shafi gefen kumatuna ta ce. "Kin ɗebo gajiya daren jiya kam, shiyasa kika jima kina bacci. Da fatan kin tashi lafiya?" "Lafiya lau Alhamdulillah!" "To masha Allah...Daman jira nake ki taso..." Shigowar ɗaya daga cikin mai aikinta ce ta katse mata numfashi, bayan tayi sallama ta ce ana nemanta a waje. Kallona tayi tace in jira ta tana zuwa. Lokaci ɗaya na ji gabaɗaya na nemi nutsuwata na rasa, domin Ya Mohaa Sam yaƙi ma ya kalli inda nake zaune ballantana nasan a irin yanayin da yake da ni. Na dai ga shi da Jadda suna dariya da juna to amma tun da yaji cewa na shigo ban ƙara ganin kyakkyawan annuri a fuskar tasa ba. Cikin rashin kuzari daga inda nake zaune na ce. "Daddy barka da safiya.." Lumshe idanunsa ya yi ya buɗe sannan ya miƙe zaune cikin nutsuwar nan tasa mai ƙara masa ƙwarjini ya ce. "Zo nan Bibi.." Tashi na yi jiki sanyaye naje kamar yanda yace. Janyoni ya yi ya zaunar dani akan cinyarsa yana kallon fuskata ya ce. "Miyasa jiya kika barni Bibi? Kin san a irin mummunan yanayin da na kasance kuwa?" Girgiza kaina na yi lokaci ɗaya naji hawaye sun ciko ido na na ce. "Ka yi haƙuri...koda naje ɗakin kowa yana ciki kuma ni ban san yanda zan iya ɗauko kayana ba suna kallona.." Tun da na fara maganar yake kallon laɓɓan bakina har na dasa aya. Wato duk mai auren yarinya dai ya shiga uku dole ya yi haƙuri da ƙurciyarta da kuma wautar ta. Domin ita a nata tunanin komai tayi daidai ne,Idan ba shi ba, ke da kike matar aure ina ruwanki da cewa wai za'a kalle ki don za ki je gun mijin ki. Jinjina kansa ya yi yana mai yin murmushi kawai ya ce. "Shi ke nan, na haƙura." Hannuna ya kama yana mai bin jan ƙunshin da ke yatsuna da kallo ya ce. "Ya yi kyau sosai...kin ci abinci?" Girgiza kai na yi na ce. "A'a. Ai yanzu na fito.." Aunty Nadeeyah ce ta fara shigowa da sunan kirana muci abinci amma ba shiri ta koma tana faɗin "afwan" Duk wanda ya shigo sai dai ya Juya ya koma amma shi sam ya ƙi ya sauke ni daga kan ƙafarsa, hankalinsa kwance kamar wanda yake cikin gidansa shi kaɗai. "Bibi.." "na'am" Na amsa masa ina mai ƙure kyakkyawar fuskar sa da kallo. "Idan har na nemi ki kasance tare dani, please ki tsaya kada ki sake barina ni ɗaya, Idan dai ba so kike wani mummunan abu ya faru dani ba...Miji kike da shi ba saurayi ba. Ki daina damuwa da mutane ki fara damuwa da mijin ki" Da sauri na jinjina masa kai na ba tare da na fahimci inda maganar tasa ta dosa ba na ce. "In Sha Allahu ba zan sake ba. Ka yi haƙuri..." Aunty Labiba ya kira yace tasa a kawo mana abincin a nan dani dashi zamu ci. Cikin mintunan da basu gaza ashirin ba aka kawo mana tangamemen trayn abinci muka zauna a ƙasa muka ci. Bayan mun kambala ne Jadda ta dawo ɗakin ɗauke da wasu gwala-gwalai a hannunta da wasu kayan al'adarsu na alfarma ta miƙamin tace na je su Suwara su tayani shiryawa shima Ya Mohaa ya je ya shirya. A bakin gangar shiga parlour na tarar da Suwara Ita da Ya Emraan suna tsaye suna magana wanda alamu ya nuna dukkan su suna cikin nishaɗi ne. Wani mamakin ne ya ƙara sarƙafe mini zuciya ganin yanda suka tsaya kusa da kusa sosai tamkar za su shige cikin juna. Saukar da idona na yi ba tare da nace komai ba na kama hanya na shige ciki a raina ina tambayar kaina cewa 'kenan soyayya suke ko me?' lokaci ɗaya Aunty Ziza ta zo mini a raina, tuna irin wutar kishin Mijinta da ke balbala a cikin jini da ɓargon jikinta kamar yanda naji su Munira suna faɗa. A yanda suke faɗamin yanda take kishi har suna bani misalai da tsananin kishi tabbas idan har Ya Emraan ta tabbata son Suwara yake akwai gagarumar matsala. Ni ɗin nan ta nuna tsantsar kishin ta a kaina ni da ba kowa ba,ina ga Suwara Babbar Mace er kasuwa, mai tarin ilmi na zamani dana addini, a labarinta da ta bamu ita ɗin jagora ce a cikin gwamnatin kakanta mai babban matsayi, sannan tana da kasuwanci na musamman kuma tana da muƙami a SUQ RANIA mai zaman kansa...Uwa uba gata kyakkyawace ajin farko. Hmm! Lallai akwai case kuwa. Tunanina ya yanke ganin Hairi ta fito cikin kyakkyawar shiga tasha uwayen gwala-gwalai tayi kyau sosai. Jinjina kai na yi ganin su Aunty Nadeeyah su ma sun shirya kowa cikin kalar laffayarsa mai kyau sosai. "Mummyn Adeel wai baki shirya ba?" Cewar Aunty Nadeeyah tana mai kusanto inda nake tsaye. Jinjina kai na nayi alamar eh, sannan na ce. "Yau kuma ina muka nufa da safen nan Aunty Nadeeyah? An faɗa muku inda zamu tafi yau?" Baki ta sake tana min wani kallon mamakin ta ce. "Wai dan Allah ban ce ki daina kirana da Aunty ba? Daddy fa ba zai ji daɗi ba, dan Allah ki daina." Dariya na yi na ce. "Ni wallahy na riga na saba amma ki yi haƙuri Maman Dija." "To shi ke nan. Kasuwa aka ce zamu tafi daga nan mu shiga gari. Kasuwar da Mama ta kafa (Cewa da Mahaifiyar Ya Mohaa Suq Rania)" Cike da zumuɗi na ce. "Gaskiya I'm excited...yanda ake ta bamu labarin kasuwar nan idan muka je nasan ba ƙaramin burgemu za ta yi ba." Taimiyyah ce ta shigo a shirye ta kama mini na shirya ta ƙara gyaramin gashin kaina sannan muka fito a tare cike da farin ciki muna tafe muna nishaɗi har bakin mota. Kallon Dayaa na yi wanda yake shirye cikin shigar jalabiya fara irin tasu yasha rawani fari ya yi kyau sosai. Kamar yanda nake kallon shi ina murmushi haka naga Suwara tana kallon Ya Emraan dake cikin shiga irin ta ɗan uwansa tana masa murmushi itama tana jinjina kanta. Yatsar ta babba ta hannuna dama ta ɗaga masa tayi masa thumb up alamar ya yi kyau sosai. Kallonta su Aunty Labiba naga sun yi suna murmushi kamar yanda nake yi nima wanda ban sani ba ko sun fahimci abinda na gani ko kuwa ni ce dai nake shirme na. A tare muka shiga motocin wanda hannuna na cikin nasa har muka isa babbar ƙofar kasuwar. Masu kiɗi da bushe-bushe muka tarar na al'ada suna ta aikin su, yayin da wurin yayi cinjim da mutane Manya, yara da ƙanana suna ta mana maraba. Jami'an tsaron da ke wurin ne suka kewayemu suka sanya mu a tsakiya yayin da wasu mutane guda biyu da aka turo daga Office ɗin ministan kasuwanci na ƙasar suka shiga gabanmu domin kasancewa a tare damu mu kuma muna binsu a baya. Hannaye kawai muke ɗaga musu alamar mun amsa gaisuwa muma muna miƙa tamu gaisuwar zuwa gare su kamar yanda Jadda ta ce muyi wanda wannan shi ne yaren da suke amfani dashi, domin ba za su iya game kowa a kasuwar su gaisa da shi ba. SUQ RANIA (THE WOMEN'S HEART OF OUMDURMAN) Abin da aka rubuta da kenan da yaren larabci da kuma turanci a saman babbar ƙofar shiga Kasuwar. Kallon Dayaa na yi wanda fuskarsa ta cika ta da murmushi da alama yanayin ya yi masa daɗi sosai a rai nima ina murmushin na ce. "Dayaa...it's seem like the whole city breaths her name a wannan kasuwar.." Jinjina kansa ya yi yana mai ƙara Faɗaɗa murmushinsa baki har kunne yana kallona ya ce. "She became the air of this Land Bibi..wanda har abadan abada ba za'a taɓa iya shafe tarihin ta ba har sai idan an wayi gari ba kowa a ƙasar Sudan ɗin nan gabaɗaya...every breath they take here...whispers her story." Takawa muka yi muka shiga kasuwar mai cike da ɗimbin tarihi wacce ta tara jama'a daban-daban na ƙasashen duniya masu kasuwanci bayan mutanen cikinta. Yanayin Kasuwar ya kasance tamkar wani ɗan ƙwarya-ƙwaryar gari ne mai zaman kansa. An tsara ta cikin tsarin zamani amma dai tana nan a sifar ta tun wanda aka kafata da shi. Wasu manyan benaye ne muka tsaya ta gabansu wanda suka saka billboard na dindindin mai hotonta da kuma sunanta. shagu na ne kawai na kayan ado da kwalliya na mata da yara ƙanana a bene na ɗaya. Bene na biyu kuma, cibiyar horar da matasa mata ce a harakar kasuwanci, ƙirƙirar kaya da sana'o'in hannu. Sai bene na uku wanda ke ɗauke da Office ɗin Rania foundation inda ake bayar da tallafi da shawarwari ga 'ƴan kasuwa mata domin dogaro da kai. Wasu dattijai ne mata guda biyu suka ƙaraso suka gaishe da Jadda sannan suka tsaya a gaban ya Mohaa suna faɗin. "Allah ya ji ƙan mahaifiyarka ya gafarta mata, Haƙiƙa ta kasance mace mafi daraja da girma wacce ta kawo mana ci gaba da sauye-sauye a cikin rayuwarmu da ma ta 'ƴa' ƴanmu mata baki ɗaya. Allah ya albarkace ka. Allah ya shirya maka zuri'a yasa ka gama da duniya lafiya da kai ahlin ka gabaɗaya." Wani ɗan ƙaramin kwano wata daga cikinsu ta ɗauko ta miƙa masa, fuskarta cike da murmushi ta ce. " Kasha wannan madarar daga hannuna Hammodi...Rania ita ɗin ta koyar dani dabarun kasuwanci da hannayen ta da kuma dukiyarta...ita ce wacce ta koyar damu cewa, kasuwanci ba abokin gaba ba ne shi ne abokin rayuwa. Duk wacce ke son ta rayu cikin farin ciki to ta koyi kasuwanci domin ta taimaki kanta da Iyalinta." Karɓar kwanon ya yi ya kafa a bakinsa ba tare da nuna ƙyama ko tsantseni ba ya sha sannan ya miƙa min nima na karɓa na sha. Kallon su ya yi yana mai jin wani iri a ransa ya kalle ni yana jinjina kansa ya ce. " Ita ɗin mata ta ce, suruka ce a gare ku..waɗannan kuma ƙannai na ne." Wasu irin hawaye ne na ji sun cicciko idona, tabbas a duk lokacin da ya furta wannan kalmar da baya shayin faɗinta ko a gaban kowa yake ta cewa 'Ita ɗin matata ce' tana sanyaya min zuciya na ji na ƙara zurfafa da jinsa sosai a cikin raina. Hannayenmu muka ɗaga sama alamar jinjina a gare su sannan yayi musu godiya da kuma basu tallafin kuɗaɗe domin ƙara jarin kasuwancin su da kuma kashe wasu matsolalin su na rayuwa. Haka muka shiga zagaya kasuwar kowane lungu da saƙo sannan daga ƙarshe muka dawo Office ɗin shugaban kasuwar mai ci a yanzu wanda wani ƙanin Jaddi ne a wurin da sauran danginsu. Manyan hotunan ta ne aka kakkafe har da na Mahaifinsa Alhaji Attahiru da ma sauran waɗanda suka cancanta ace akwai hoton su a wurin. Bayan mun gaisa ne wani daga cikin office ɗin ya shiga nuna mana abubuwan tarihinta na gwagwarmayarta dake office ɗin wanda a ciki har da litattafan da ta rubuta da Kanta ta wallafa guda uku wanda na ɗaya shi ne; The journey of a market woman, na biyu kuma;women and wealth in Africa, sai na uku kuma; A letter to a young Lady. Hannu muka miƙa kowa ya amshi copy yana dubawa wanda ni da Ya Mohaa ne muka buɗe letter to a young Lady muka fara dubawa. Murmushi ya yi ganin babu komai a ciki sai tarin baiwa, hanyoyi da kuma dabarun kasuwanci ga yara matasa mata. Yatsan shi ya ɗora akan wani muhimmin sentence da ta ce. "Dear Young Lady...never be afraid of carrying your dreams everywhere you go around the world.." Idanunsa ne naga sun cika da hawaye. A hankali Ya rufe littafin ya rungume sa a ƙirjinsa ya kalle ni yace. "Her dreams did not dies Bibi...it lives here....in every smile, in every woman selling her hope. Duba Ki gani, kamar yau ne ta rubuta wannan littafin.." Jinjina kai na nayi cike da ƙwarin gwiwa na ce. "Ita ɗin jarumar Uwa ce, domin ta bar baya mai kyau. Kowa a kasuwar nan da ma mutanen gari kowa sai faɗin alherinta yake. Yeah! She built a home for every woman..." Hannuna ya jimƙe a nasa sosai ya ce. "And now...it's my turn to keep it alive. In Sha Allahu abubuwa za su ƙara sauyawa da sabon ci gaba." "Allah ya taimaka ya dafa maka ya kuma sanya albarka ga duk abunda ka sanya wa gaba amin." Bayan mun kambala a nan muka yi sallar Zuhr sannan suka yi ta gabatar mana da kyaututtukan abun da suke siyarwa da yawa, daga ƙarshe muka yi sallama muka wuce Old Oumdurman Heritage Quarters inda manyan gidaje na tarihi suke. Muna nan muna ta ɗaukar hotuna ana ci gaba da bamu tarihin wurin Sai ga Jaddi ya iso. Murmushi ya yi mana ya ce. "Kun ganni shiru sai yanzu ko? Ina can ina ji da wasu baƙi da nayi sai yanzu na samu na lallaɓa suka tafi....kunga gidan tarihin gwagwarmaya mazan jiya?" Dariya muka yi muna jinjina kai kowa na yabawa da abin da ya burgesa a wurin sannan Hairi ta ce. "To ni ya zan yi na zama Jaruma kamar Mama Rania da ma sauran mata Jaddi?" Dariya ya yi yana kallonta ya ce. "Abin ba mai wahala ba ne Hairiyya. Kawai daga zuciya ne, ki saka a ranki cewa za ki yi aiki tuƙuru domin cika wani mafarki na ki, sai ki saka aikin a gaba ki kuma riƙe Allah, da taimakon en uwan ki da mijinki ko iyayen ki tabbas za ki zamo kamar su watarana." Kallonta Ya Mohaa ya yi ya ce. " ki kasance komai kike so iyaka ki ganshi a gabanki, abinci, sutura, karatu da kuma kayayyakin more rayuwa....anya za ki iya kuwa favorites...duk fa wanda kika gani a wani matsayi duniya ba haka kawai ya same shi ba, sai da yayi aiki tuƙuru.." Hannun shi ta riƙe cike da sangarta ta ce. " Dan Allah Daddy ka goya min baya, wallahi yau an zubarar da tunani dangane da rayuwa, da gaske nake ina so in fara kasuwanci...and I want become like them." " To shi kenan. Bari mu nutsu sai muga abin da ya kamata." Bayan mun gama kewaya wurin muka ranƙaya zuwa bakin ruwan teku masu gudana gwanin sha'awa. Murmushi na yi yayin da kowa ke tofa albarkacin bakin sa na kalli Jadda na ce. " Yanzu na ƙara fahimtar dalilin da yasa kika ce Mama tana ƙaunar bakin ruwan nan a lokacin da take raye. Wuri ne mai cike da sanyi da sanya nutsuwa, babu hayaniya ba komai sai tarin ni'imomi..." Jinjina kanta ta yi ta ce. "Ta kan zo nan a duk lokacin da take bincike akan wani

Chapter 42 of 67