Share this page
ce. " Amin Ya Allahu.... Ai da yake lokacin tun da wayata ta lalace shikenan na koma Kano, bayan na dawo na yi ta neman ku amma kuma babu labari." "Allah sarki! Ai bayan mun dawo daga jinyar ne sai kuma muka dawo nan gidan." "Allah sarki! Allah ya ƙara bi da lafiya. Su Umma ma duk suna gaishe da ku. Ko yanzu auren Zulfa ake yi shiyasa ba su biyoni ba. Amma dai daga zaran an kambala in sha Allahu za su zo.." "Allah sarki. Muna godiya sosai, Allah ya sanya alheri da albarka yasa a gama lafiya.....yaushe ne auren?" "Juma'ar nan mai zuwa in sha Allahu." "Allah ya nuna mana lafiya. Mun gode, mun gode, Allah ya yi albarka." "Amin.." Daga haka ya miƙe cike da nutsuwa ya ajiye ledarda ke hannun sa ya juya yana faɗin. "Sai an jima, Allah ya ƙara afuwa." Cikin sauri nabi bayan sa muna ta jiyo muryar Ammie tana ta yi mishi addu'a har muka iso inda mashin ɗin yake. Jinginawa ya yi ya ɗan zauna jikin Mashin ɗin tare da harɗe hannayensa akan ƙirjinsa yana kallona ya ce. " Kin canza mini sosai Beenafah.." Ba tare da kawo komai a raina ba na fashe da dariya na ce. "Kai ma ai ka canza sosai.." "Ina wayarki?" "uhm! Tun da simcard ɗin ya lalace na kai ta na ajiye, sai daga baya kuma wani abu ya taso na saidata, Ya Jafaru ma na bai wa ya kaita ya siyar...." "Kin taɓa jin kina kewa ta duk tsawon lokacin nan da bama tare Beenafah?" Dariya na yi ina jinjina kaina na ce. "Sosai kuwa, wani lokacin dana tuno da kai irin yawon da muka riƙa yi a asibiti a tare, da kuma firar da kake mini a waya san da muna Sokoto har kuka nake yi, ko kuma idan wani abu ya ta so wanda nake buƙatar support person mai bani shawara da makamancin hakan sai na ji ka zo mini a raina." Cikin farin cikin jin daɗin maganata ya ce. " Tun da na koma Kano ban sake samun kwanciyar hankali ba Beenafah, na za ta ma kin manta da ni..." "Haba! Ai har abada ba zan iya mantawa da kai ba Ya Ashiru. Da ba dan Allah ya jeho mana kai ba, da Ammie ta rasa ranta a wannan ranar. Kana da kirki, matuƙar matuƙar kirki, kana da wani matsayi da girma a zuciyata wanda har abada ba zai canza ba." "Za ku zo auren Zulfa?" Ɗan Jim na yi ina nazari na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe na ce. "Uhmm! To sai na tambayi Ammie na ji..." "Idan kuka zo zan yi farin ciki da hakan." "Tau! In sha Allah zan mata magana, Allah yasa ta amince..." Idona ne ya sauka akan Ya Jafaru da ya fito daga cikin gidan su yanzu. Cikin sauri na ce masa. "Ya Jafaru zo ga Yaya Ashiru ku gaisa." Ƙarasowa ya yi ya bashi hannu suka gaisa sannan ya kalli Yaya Ashirun ya ce. "Ai Beenafah tana yawan bani labarinka, mun gode sosai da taimakawa Allah ya saka da alheri." Murmushi ya yi masa yana jinjina kai ya ce. "Ai ba komai, yiwa kai ne." Daga haka ya shige gidan ya cim ma Ammie zaune ta yi shiru tana tunani. Kallon ledar da Yaya Ashiru ya ajiye ya yi sannan ya kalli Ammie ya ce. "Ammie lafiya kuwa?" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta yi murmushi ta ce. "Wallahi ba komai Jafaru. Kaga Ashiru yau Allah ya bayyana mana shi ko?" Jinjina kai ya yi ya ce. "Na gan shi, Masha Allahu. Allah ya ƙara zumunci." "Amin amin.. Ai wallahi Ashiru yaron kirki ne, ya taimaka mana a lokacin da muke cikin tsananin buƙatar taimako..." Miƙewa ya yi yana wani murmushin ya ce. "Allah sarki! Ai haka rayuwar take.. Ammie bari in je in karɓo kayana kin san gobe da wuri zan fita, Kawu yace yana so in isa Zariar da wuri." "To ba laifi, Allah ya kai muna rai amin." Fitowa ya yi ya wuce mu ba tare da ya ce komai ba, amma kuma sai kallonmu yake a kaikaice har ya miƙa hanya ya wuce. Ni kuma wallahi hankalina ya ɗauku sai fira muke ina dariya gabaɗaya ban ma lura da shi ba. Baifi minti goma ba, sai gashi ya dawo ya shiga gida, iyaka minti biyar ya sake fitowa, ya shiga gidanmu ya fito ya sake Miƙewa. Ƙarshe dai sai gashi ya dawo ya zo ya tsaya yana faɗin. "Wai miyasa za ku wani tsaya a nan ƙofar gida kamar wasu saurayi da budurwa. Ku shiga cikin gida mana kamar zai fi. Ko kuwa? Amma nan kun tsaya a waje duk wanda ya biyo sai ya kalle ku ai bai yi ba." Kallon Yaya Ashiru na yi ba tare da nace komai ba, shi kuma sai ya kalli Ya Jafarun ya yi murmushi sai kuma ya jinjina kai ya ce. "Kar ka samu damuwa, ai yanzu ma zan tafi." Jinjina kai Ya Jafaru ya yi yace OK kawai ya yi gaba ya koma gidansu Bayan ya shige still muka ci gaba wanda sai daga baya bayan yaga Ya Jafaru ya fito ya zauna gindin bishiyar ƙofar gidansu yana yi yana kallonmu sannan  Ya Ashiru ya ce mini. "Bari na zo na tafi, ai fira tayi fira ko? Kinga muna da baƙi sosai, musamman ni na jima bana nan,amma in sha Allahu gobe zan dawo..." Gyaɗa kaina na yi na ce. "To gaskiya kam, dan Allah gobe ka dawo, amma ka bari sai six domin zanje Islamiyya." "To ba damuwa." Daga haka ya hau mashin ɗinsa ya kunna duk ina tsaye ina ta masa murmushi. Sai da ya yo corner sannan ya ce mini. "Kada ki sauke Layin, an jima In Sha Allahu idan na samu sarari zan kiraki." Jinjina kaina na yi na ce. "In sha Allahu, na gode sai goben." Daga haka na shige gida abina domin wallahi sam na manta da wani Ya  Jafaru kamar dai yanda akace zuciya ke gani ba ido ba.   Ina shiga na janyo ƙatuwar ledar da ya ajiye ina dubawa, ashe kayan chocolate ne da kuma kayan shafe-shafe da turaruka masu matuƙar daɗi da ƙamshi. Ɗagowa na yi na kalli Ammie wacce ta yi shiru na ce. "Ammie kin yi shiru, lafiya?" "Hmm! Ba komai Beenafah. Allah ubangiji ya shige mana gaba." "To,amin. Duba ki gani abin alherin da ya kawo mana? Wai ashe Kano ya koma gabaɗaya." "Haka fa yace mini nima." "Wallahi kuwa, wai Yayansa ne ya mayar da shi can ya buɗa masa shagon atamfofi da kayan yara... Yace min dai komai suna siyarwa, sannan kuma ya koma makaranta yana degree amma only weekend yake zuwa..." Duk labarin da ya bani da irin wahalar nemanmu da ya sha sai da na bai wa Ammie labari, har yanda yace ya yi kewata duk sai da na sanar mata,ƙarshe na tashi na kwashe kayan na kai ɗaki na fito na shiga wata sabgar. Da dare ana dawo daga masallacin Isha, Ya Hamza na gidanmu shi da Fakiha munata firar duniyar da muka saba na fita naje gidansu neman Ya Jafaru domin tun da yamman nan ban sake sanya shi a idona ba. Na yi mamaki da akace wai har yanzu bai dawo ba, wanda da zaran an gama Sallar Isha duk inda yake ya dawo gida, in dai ba wani aiki ba ko kuma sallah da suke ɗunke-ɗunke. Abu kamar wasa har goma tayi na dare Ya Jafaru bai dawo gida ba. Dole na haƙura naje na kwanta. Washe gari ina tashi da asuba na yi aikace-aikace na kamar yanda na saba sannan na fito tun 6:30 kamar ko yaushe na wuce gidan su Hajiya. Yau ma na za ci Munira za ta yi mini magana ne akan abinda ya faru jiya amma bata mini ba, har na kambala wanda sai kusan ƙarfe uku na rana na dawo gida sanadiyyar aikace-aikacen da suka yi yawa. Bayan na iso gidan na shiga na yi shirin islamiyya na fito na wuce. Bayan mun gama karatu mun taso da ƙarfe shida, ina zuwa ƙofar gida na tarar da Ya Jafaru yana zaune a bakin bishiya. Cike da maɗaukakin mamaki a fuskata na ce. "Wai daman Ya Jafaru baka wuce ba?" Fuskar nan a turbune, yanayin da ban saba ganin sa a ciki ba ya ɗago ya kalleni sai kuma ya kauda kansa gefe ya ce. "Eh, ban wuce ba." Jinjina kaina na yi na ce. "Miye yasa to?" "Wani uzuri." Ya bani amsa kai tsaye. "To jiya ma baka dawo gida da wuri ba Ya Jafaru, kuma ji fuskarka duk ta yi wani iri, miye yake damunka? Ko ba kada lafiya?" Maimakon ya amsa mini tambayata, bai yi hakan ba sai na ji ya sauya magana da cewa. "An ce jiya kin zo nemana, Miye yasa?" Ɗan Jim na yi sannan na ce. "Daman Yaya Ashiru ne ya ce zai kirani shiyasa na zo ka bani aron wayarka." Jinjina kansa ya yi ya ce. "Ok. Na ɗan je wani wurin ne." "Allah sarki. To bari in je, yama ce mini zai zo yanzu. Bari na shiga gida." Kallona ya yi kamar zai yi magana, sai kuma ya fasa kawai ya miƙe ya shige gida. Ni kuma ina shiga ban fi minti ashirin ba sai gashi ya zo, yau ma cikin wata shigar yake ta ƙananun kaya wanda ya mini kyau sosai, still a ƙofar gida muka fito muka yi ta fira har sai da aka fara kiran magariba sannan ya ce mini suna da baƙi ko yau, don auren ya rage saura kwana biyu. Washe gari ina zuwa gidan aikina na tarar gidan ya ƙara kacamewa sosai da yawan mutane, musamman sashen baƙin nan. Kayayyaki ne aka zube bakin babban store wanda da alama duk na budurin bukin ne Haula ta kiramu ta ce an ce mu gyarasu mu jera su can ciki. Muna tsaka da aikin ne sai ga Aunty Labiba ta shigo ita da wata wacce ke sanye da wani half quarter na jeans wanda yasha kyau har ya gaji, sai wata ƙamar riga fara mai adon wasu stones sai walwali take, ga Kanta an yi mata Kalaba ta tubke a gefe da wani kyakkyawan farin glasses da yake idonta yayin da kunnuwanta ke maƙale da Earbud ta yi kyau sosai, kana ganin ta kasan hutu ya zauna jikinta gaba da baya. Gaishe da su mukayi dukkan mu, sannan Aunty Labiba ta kalli Munira ta ce. "Don Allah Munira waɗan can masu aikin da suka zo ɗinnan ki nuna musu wancan sashen baƙin na gefen hagu su je su gyara mana shi please..." Cike da shagwaɓewa ta ce. "Eyyah Aunty Labi tun ranar da na zo fa ba'a sake gyara mini room ɗina ba, har bedsheets ina so a canja mini..." Aunty Labiba na dariya ta ce. "Ba Naji ɗa zu Dija na cewa ta gyara miki ba.." Waro ido tayi sannan kuma ta fashe da dariya ta ce. "Rabani da zancen kuka dan Allah Aunty Labi, wannan gyaran ko ni nan idan na tashi abun kirki ina iya wanda ya fi shi nesa ba kusa...Dan Allah please talk to them,yanzu Idan na yi Magana Munira ko kunyar idanuna bata ji za ta ce mini aiki take yi..." Dariya Munira ta yi ta ce. " Haba Hajiya Hairi, da kince na yi ai da dole duk abinda na ke yi na ajiye shi na je na miki... " "Ba wani daɗin baki da za ki mini, tun da na dawo ai baku zo ɗakina kun tayani fira ba, kullum haka nake yin bacci.." Girgiza kai Aunty Labiba ta yi tana dariya ta ce. " Yanzu dai shikenan, Beenafah kije ki gyara mata." Juyowa na yi ina faɗin to na nufo bakin ƙofar inda suke tsaye. " Ya Allah! What a beautiful soul..! Aunty Labi is she the girl that you are telling me about??" Jinjina kai Aunty Labiba ta yi ta ce. " Yeah, she's the one... " Wani kallon ƙurulla ta bini da shi wanda har sai da naji na ɗan tsargu sannan ta ce. "She's just beautiful...Very very beautiful Aunty Labi. Rabbi yasa yanda fuskarki take haka yasa zuciyarki itama haka take kyakkyawa.." Juyawa suka yi a tare ina kallon su Munira waɗanda suma ɗin ni suke kallo sai kuma na bi su a baya, sai da muka shiga ciki ta kai ni har ɗakinta wanda na taɓa shiga tace mini nan ne, na je na ɗauko kaya na zo na gyara mata, sannan akwai bedsheet a wardrobe na ɗauko na canza mata. Bayan ta fita ne na ware ido ina kallon ɗakin wanda ya cika da daddaɗan ƙamshi wanda ya gauraya da sanyin Ac kamar karka fita. Ni dai wallahi ban ga abun sharewa a nan ba, komai tsab yake, sannan wannan bedsheet ɗinma shi karan kanshi tamkar ba'a taɓa kwantawa akan shi ba. Kai! masu kuɗi sun ji daɗin su. Sai da na gama zagaye ɗakin fes na gama bai wa idona abinci sannan na yi aikin hankali kwance na kambala na fito. Cikin rashin sa'a na ci karo da Aunty Ziza wacce ta ci uban ado da wani Lace abin da ake kira Lace, tana zaune ita da wa su mutane waɗanda ba zance ga mutum guda a ciki dana sani ba. "Ke!" Tsayawa na yi cak inda nake, duk da cewa ban juyo ba, nasan dole dani take magana. "Ba za ki waigo ba kina ji ina kiran ki?" Waigowa nayi riƙe da kayan da na gamo gyaran ɗakin Hairi na ce. "Na'am." "Kije kitchen ki haɗa mini simple snacks haka, ina da baƙi suna hanya." Ina kallonta kamar yanda take Kallona na ce. "Ban iya wannan aikin ba, kuma ma ba aikina ba ne bari na kira miki Haula...." Cike da tsantsar mamaki ta ce. "Iyyehhh! Ni za ki kalli tsabar idona ki ce mini wai ba aikin ki ba n..." Muryar Hajiya muka ji wacce ke shigowa ɗauke da Muhammad a shoulder ɗinta ta ce. "Lafiya kike ɗaga murya Ziza?" Cike da jin wani ƙololon baƙin ciki ta ce. "Wai Hajiya Imagine mai aikin nan in ce taje Kitchen ta yi mini aiki wai amma ta kalleni cikin taron mutane ta ce mini wai bata iya ba, kuma ma ba aikinta ba ne..." Kallona Hajiyar ta yi, sai kuma ta kalli Aunty Ziza ta ce. "Gaskiya ta faɗa ai,bata iya ba don ba a kitchen take aiki ba..." "To ai ya kamata ace ta koya Hajiya, ba ta iya ba amma ai tasan yanda ake ci, ko ko su masu shiga kitchen ɗin bayinta ne? Kullum sai dai ta shigo nan tana raba ido tana gulma da sunan aiki amma shi Kitchen bata san yanda ake aiki a cikin sa ba, wato ita ga 'ƴar gold Ko!" Cike da mamaki Hajiya ta kalle ta ta ce. " Ziza What's your problem wai? Daga wannan' ƴar maganar sai ki yi ta faɗa abun da ba halinki ba. Ki aika Eatry ɗin ki mana sai a kawo miki, suma kan su ma'aikatan kinga aiki ya yi musu yawa. Sannan da kike zancen snacks ai na ma tuna akwai shi yana nan, ki aika a ɗebo miki daidai yawan da kike so.." "Duk da haka Hajiya she needs to be taught yanda ake shiga kitchen ɗin. I will take her to Ziza Eatry classes taje ta koya Yanda ake shiga kitchen tun da sauran ba bayin gidansu ba ne."               ✍️  *OUM-AMEER*  ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM*      *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus.... *PAGE 23*   A hankali Hajiya ta taka ta miƙawa ɗaya daga cin baƙin nata babyn kawai ta juya cike da jin ɓacin rai ta koma gefenta. Ni kuma tsaye kawai nake tare da sadda kaina ƙasa, a irin yanda na ji na muzanta da ace lokacin da ne da yanzu na fara kuka, amma kuma tunawa da irin gargaɗin da Haula ta yi mini sai yasa na dake kawai na haɗe raina ina jiran in ga ƙarshen gudun ruwanta. Ɗorawa ta yi da faɗin. "Kuma ana ta aiki ke shafaffa da mai kullum da kinzo ki yi wani sharar gulma sai ki kama ki koma gida, da ƙarfe biyu ki bar en wahalar ki su ci gaba da yi miki wahala ko? To wallahi tun da ba zane kika fi su ba, dole ki riƙa tsayawa har dare sannan ki tafi kinji umarnina daga.... " Hannun Hairiyyah maƙale dana Emraan suka shigo cikin Parlourn, hakan yasa Ziza saurin haɗiye sauran maganar ta tana mai fuskantar Emraan da murmushi ta ce. "Emraan! Ga su Safinar ku gaisa." Shima ɗin ita yake kallo da mamaki sai kuma ya kalleni ya kalli mutanen da ke ɗakin ya sake mayar da kallonsa gare ta ya ce. "And what's going on here na Ji Kamar kina Ihu Ziza?" Waskewa tayi tana wani murmushi ta ce. "No! Ni wai? Ba komai.." Kallona Hairi ta yi ta ce. "Pretty, miye kike a nan? Kin kambala mini gyaran ɗakin ne?" Ban san dani take magana ba, domin ban sanni da wani suna wai shi Pretty ba, amma kuma jin ta ambaci kin kambala mini gyaran ɗakin ne yasa na ɗago na kalle ta ina mai jinjina kaina alamar eh. "To miyasa kika tsaya a nan?" Kallon Aunty Ziza na yi na ce. "Aunty Ziza ce ke magana dani..." "No... You can go ai, shikenan." Kallona ya yi cike da kulawa yace. "And why are you sad?..." Ganin yanda na yi masa wani kallon yasa ya girgiza kansa ya ce. "I mean.... Miyasa kike cikin damuwa?" Muryar Hairi na ji tana faɗin. "And da fushin nan bakya yin kyau pretty. Je abinki Kawai...Ya Emraan kasan wani lokacin rayuwar farin ciki wani lokacin kuma akasin haka." Tamkar an kwance mayunwacin Zaki daga sarƙa, haka na saka ƙafa kamar walkiya na fice daga ɗakin. Gaisawa ya yi da baƙin da suka dawo tamkar hoto a zaune suna kallon mu tunɗazu tana ta tijara tamkar ba mai haihuwa ba. Bayan sun gama yi masa barka ya juya ya koma still riƙe da hannun Hairi, daman saboda ya gaisa da baƙin ne yasa ta kira shi a waya ya zo. Suna fitowa ya kalli Hairiyyar yana murmushi ya ce. "And why did you give her the name?" "huh! Kana nufin wai Beenafah?" Jinjina kansa ya yi ba tare da yayi magana. Itama dai jinjina kan nata ta yi sannan ta ɗan ɗage shoulder tare da ware hannayenta ta ce. "Nothing, kawai dai she deserves to be call pretty,because ita ɗin mai kyau ce da gaske, and beside...Aunty Labiba ta bani labarinta tana da kirki sosai kamar dai sauran ma'aikatan gidan nan." "And wai ita kowa sai ta bashi labarin wannan yarinyar ne? Miye yasa haka?" Dariya Hairi ta fashe da ita tana jinjina kanta ta ce. "Tun ina UK ake bani labarin Beenafah har na dawo, Aunty Nadee ma naji jiya tana ta mata mita wai ita bata san miye yake damun Aunty Labiba ba wanda bata da wani zance saina mai aiki, shi ne fa Aunty Labibar tana dariya tace wallahi babu abinda yake tsakanin su sai alheri, kawai dai yarinyar ta burgeta ne da kuma darajar Biba..." "Biba....kina nufin Yarinyar Inna Ramatu?" "Eh, ita fa. Wai ita ce ta kawo mata ita." Jinjina kai ya yi sannan ya kalle ta ya ce. "Ki koma Aminiya, ina da wasu baƙin da dole zan yi attending na su." A nan ta tsaya tana ɗaga mishi hannu ta ce. "OK amini, Bye." Ni kuwa, A ɗaki na samu Haula ita kaɗai tana bubbuɗe ɗinkuna masu kyau na Leshi. Kallona ta yi ta ce. "Sai yanzu? Kinga kayanmu in ji Hajiya, yanzu Lawan ya kawo su." Murmushi kawai na yi amma ba don ina jin daɗi ba,domin na ji haushin abin da Aunty Ziza ta mini ba kaɗan ba. "Miye kuma? Na san dai Hairiyyah ba ta da matsala..." Ina kallonta na ce. "Itama 'ƴar Hajiya ce?" Jinjina kai ta yi ta ce. "Auta Jaja manya kenan, ɗiyarta ce, ita ce auta. Ga taɓara ga kirki ga kuma shagwaɓa. Suna matuƙar matuƙar ji da ita sosai musamman Ya Emraan cewa yake ita ce babbar ƙawarsa Aminiyar sa, kinga yanda take damu? Kamar wa su abokan wasanta,musamman Munira, haka za ta kiramu ɗakin ta muyita fira, sai taga dare ya yi sosai ta ce wallahi babu inda zamu sai mun gyara mata ɗakinta zamu fito......" "Wannan matar ta jiya fa da ta ce in zo in goge ruwa ya zube?" "Au! Mummy Na'ima kike nufi wai? Matar Baba Ustazu ce shi ne ƙanin Alhaji marigayin gidannan." Wucewa na yi na shige na yo alwala na zo na tayar da Sallah.                             **** Haka muka yi ta aiki wanda dolena na dinga tsayawa sai Magrib sannan in koma gida domin sai da ta ƙara jaddadawa Su Munira amma bana tunanin su Hajiya sun san da wannan. Gidan ya cika sosai, mutane babu kalar da babu da masu kirki da marasa kirki, wata idan ta saka ki aiki tamkar ta samu Engine ba bu abunda ya dame ta. Wannan dalilin ne yasa dole bazan iya zuwa bukin gidansu Yaya Ashiru ba domin rana ɗaya ake yi dana Aunty Ziza. Daren da nake yowa yasa bana samun ganawa da Yaya Ashiru, sannan shi ma Ya Jafaru ya canza mini sosai wanda har abin ya fara damuna. Ko wayarsa na ce ya ara mini sai yace mini bata da caji ko kuma yace wani abokinsa ya ara. Bayan na faɗawa Ammie cewa ba zan samu zuwa gidan su Yaya Ashiru ba, shi ne ta ce ita dole sai ta tafi ita da Bahrain, ni kuma hakan yasa dole ba zan iya barinta ta hau ƙarfe taje wani wurin ba tare da ni ba, hakan yasa na ce mata yau daga zaran naje sunan duk yanda zan yi zuwa ƙarfe biyar ta jirani zan dawo mu tafi. Koda na je gidan ya ilahiy! Ya cika maƙil ana ta hidima, wai bahaushe yace masu abu da abun su, ɗan fari a wurin Emraan Attahiru Araam. Su kansu mutanen gidan shaida ne akan yanda Hajiya take tsananin ƙaunar Emraan,da kuma aka zo aka haifo mata jika daga tsatsonshi sai taji ƙaunar da take yiwa jairirin har ta zarce misali, sannan kuma uwa uba ga shi Muhammad. Su Aunty Labiba da yaransu, dangin Aunty Ziza da kuma dangin Hajiya sun taru sai farin ciki suke suna taya murna. Tunda nake da su, yau ne rana ta farko da na taɓa tuɓe kayana nayi wanka a gidan muka shirya a tare cikin ɗinkin da aka yi mana mai kyau. Muna nan dai a ɗakinmu sai zuba uwar fira wanda sai idan za'a yi wani abinne muke ta shi mu fita. Ni daman yau na yi alƙawari na kuma roƙe su alfarma na cewa dan Allah kada su ce na shiga cikin gidan nan domin ba zan shiga ba In Sha Allahu har na koma gida. Ina nan ma sai ga Adeel ya shigo nemana, nan muka lalace dani da shi yana ta bani labari ina dariya. Sai da huɗu tayi na yi sallah sannan  na kamkanta kayana, duk wani abin da Haula ta kawo mini da sunan nawa ne na tattara gudan kaya na ce musu na wuce gida. Munira sai tsiya take mini wai sai ta faɗawa Aunty Ziza tace na wuce tun ba'a gama bukin sunan ɗan gold ba. Hijabi na Sanyo na hawo mashin daga can zuwa gida, ina zuwa na cire na sanya gyalen Lace ɗin na ƙara gyara fuskata wacce ba komai sai farar powder da lipstick muka fito mu huɗu da niyyan zuwa mu hau Napep har da Farisa da tace tana zuwa. Wani irin girgiza Zuciyar Ya Jafaru tayi a lokacin da idanuwansa suka yi tozali dani. Tunda nake bai taɓa ganina da gyale ba sai yau, sannan kuma gashi daman na ɗan ƙara samun gogewa a abubuwa da dama ba kamar da ba. Take yaji duk wani ɓacin randa na sanya masa ya gafarta mini. Baki kamar gonar auduga ya kalleni wanda da alama ya manta cewa har da Ammie muke yace. "Masha Allahu! Beenafah ƙarshen kyau kenan...da

Chapter 17 of 67