Share this page
ta yi tana faɗin. "A'a Mummy! Tun da yace ki je dan Allah ki je, ba gamu ba...ga mutane ko'ina. Ki je ki saurare shi." Jin maganar da Hairiyya ta yi ne yasa na taka tamkar zan haɗiye zuciyata na mutu saboda baƙin ciki. Ina zuwa na tsaya tare da kallon shi a sheƙeƙe na ce. " Ga ni..." Ƙasa ya yi da murya kamar da gaske ya ce. " Zuwa na yi in faɗa miki wallahy tallahy har abada ba zan taɓa haƙura da ke ba. Na san cewa kina so na Beenafah, kawai dai ƙaddara ce ta yi mana rigaye a tsakaninmu. Saboda haka na ba ki lokaci ki je ki yi nazari. Dan Allah Beenafah ki dawo gareni...Ya Jafarun ki ne fa! Ban san komai ba idan ba son ki da ƙaunar ki ba. Ba zan iya rayuwa ba idan babu ke Beenafah..Na san cewa fushin zuciya ne ya sanyaki aikata abin da kika aikata kamar yanda nima fushin zuciyar ne. To amma ki sani ni babu wata mace a raina har abada sai ke. Ko shekara ɗari za ki yi zan iya zaunawa na jira k... " " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Jikina na rawa na furta masa hakan ina mai Girgixa kaina,sannan daga ƙarshe na ce. " Ubangiji Allah ya shirye ka." Daga haka na juya na je na shige mota ina mai yiwa su Fakiha yaƙen ƙarfin hali domin kaɗan ya rage zuciyata ta tarwatse tsabar baƙin ciki. A yau tabbas yaci darajar su Hairi ne,domin hana so in yi wani move ɗinda za su gane cewa akwai matsala, amma da ba dan haka ba wallahy tallahy da sai na yi masa abin da yafi na ranar ma. Wai anya Ya Jafaru bai haukace ba kuwa? An ya bai fara shaye-shaye ba? Idan ba shi ba wane irin ƙarfin hali ne haka ɓarawo da sallama? Shi yanzu ashe har yana da guts ɗin biyoni cikin taron jama'a yana faɗamin maganganun banza? Wallahy darajar Su Mama na ke dubawa amma Kada ya bari ya kai ni maƙura. Ji yanda Mama ta dinga magiyar bani haƙura dan Allah? Amma saboda Jakki ne shi shi ne yau ya sake dawowa. Ya Hamza ma ko ɗazu sai da ya kirani da safe muka gaisa lafiya lau ya yi mini ya jiki. Amma da yake ƙwaƙwalwar kifi ne da shi ya kasa gane kawaicin da nake masa. Shi ne fa dalilin da yasa na cire son zuwa gidan su Yaya Ashiru a raina da nake ta ɗoki,domin ban san shi ma ta ya ya zai karɓeni ba daga har iyayensa. Ina jin kewar sa a raina, kuma na so zuwa gidan su kamar me, to amma hakan ba zai samu ba, domin kada ya gaza fahimta ta kamar yanda wannan shashashan yake. Koda muka isa gidan na tarar wai Aunty Ziza ta kawo min Ɗinkin da zan sanya gobe wanda sun yi kyau ba kaɗan ba. Amma kuma ni dai ban yanke saka su ba, domin Aunty Labiba ta kawo mini ɗinkunan da Ya Mohaa ya biya domin a ɗinkamin tun daga Kaduna wurin Aunty Nadeeyah. Kuma kayan Mijina sun zan saka gaskiya, sai daga baya watarana can na saka idan ina ra'ayi, amma ban nuna mata ba, domin sosai na yi ta zuba mata godiya tare da yaba yanda Ɗinkunan suka tsaru. Washe gari da wuri aka gama tsara komai. SOS event aka gayyato na musamman suka ƙawata harabar gate na ɗaya da decoration wanda ya haɗu sosai. Wani abun burgewa da farin ciki shi ne, RANIA (Mima) shi ne sunan da Emraan ya raɗawa Babyn. Hakan ba ƙaramin farin ciki ya sanya Ya Mohaa ba, domin daga yanda yake ta nanata min maganar cike da jindaɗi shi ne ya tabbatar min da cewa ya yi farin ciki sosai da wannan karamcin da Emraan ya yi masa. Nan aka sha Hidima wanda ni ina wuri ɗaya domin ban yi wani zirga-zirga ba kada na wahala da yawa. An ci an sha Alhamdulillah! an sha hotuna kamar ba gobe ga kayayyakin rabawa nan kamar banza komai an yi shi Masha Allah. Su Ammie na wuce nima na tattara ni da Hairi muka shige ciki. Bayan na kambala sallar Isha na miƙe daga parlourn da muke zaune na ce musu zan shiga na yi wanka na kwanta domin na gaji sosai. Na gama cire kaya kenan na ɗora towel na ga wata sabuwar number tana kira na. Ba tare da kawo komai a raina ba na yi picking domin na san cewa na baiwa en ajinmu numbernta da yawa, to wata ƙila daga cikin su ne wata ta kira. Sai dai kuma, muryar da na ji ita ce ta kusa Sumar da ni tsabar mamaki da al'ajabi. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* *PAGE 51* Cikin wata irin magiyar da ba za ta mishi amfani ba kamar yanda ni ma har abadan abada ba za ta taɓa yin tasiri a kaina ba ya ce. "Dan Allah Beenafah ko sau ɗaya ne ki tsaya ki saurareni!..." Shiru na yi ba tare da na yi magana ba kamar yanda shima daga can ɓangaren ya ɗan janye wayar daga kunnen sa ya kai idanunsa akan ta ya duba kyau domin tabbatarwa cewa na yanke kiran ko ban yanke ba. Wani irin sanyi ne ya ji ya ratsa shi har da lumshe idanunsa sannan ya mayar a kunnensa ya ce. "Beenafah! So ɗaya ne, kuma shi nake miki. Kada ki manta su irin masu kuɗin nan babu abin da suka sani idan ba son kansu ba. Ina so ki auna da kaifin hankalinki ki gani, ke fa ƙaramar yarinya ce wacce ba ta yi wani zurfin ilmi ba. Ke ɗin ba kowa bace idan aka kwatanta da Engineer domin yafi ƙarfin ki ta ko'ina, Babban mutum ne wanda duniya ta san da zamansa, yana da kuɗi, yana da ilmin da ke ko kan akaifar ƙafarsa ba ki kamo ba,da za ki zauna ki nutsu ki yi nazari, sam! Ke da shi baku dace ba, kawai yana amfani dake ne na ɗan wani lokaci domin biyan wata buƙatar sa. Daman wata mummunar ƙaddara ce ta yi masa hijabi da samun matar da ta dace da shi, tunda kuma a yanzu dama ta samu, ba jimawa zai aure Macen ta waye, ta goge, ta yi ilmi mai zurfi da ta fiki komai ta kowace fuska, a wannan lokacin ne za ki dawo bola shara marar amfani, daga ƙarshe saki ne zai biyo baya na wulaƙanci ma...Beenafah! Ba wai ina faɗa miki shaci faɗi ba ne, abun da zai faru kenan nan da ɗan wani lokaci domin har abada mutum kamar Engineer Mohaa ba zai zauna da ke a matsayin matarsa wacce zai iya nuna ta a duniya ba..." A gigice na fashe da wani kuka ina mai ɗaga murya ina girgiza kaina jin wasu sababbin abubuwan da suka shiga yawo a kai na ina neman ƙaryata shi na ce. "Ƙarya ka ke!!! Ƙarya ka ke Ya Jafaru. Dayaa har abada ba zai taɓa yi mini haka ba, duk inda muka shiga bai taɓa ƙin nuna ni ba, da alfahari yake nuna ni a ko'ina..." "Ƙarya ne! He's just pretending. Muhammad ba zai taɓa son ki ba, har abada Beenafah ba zai so ki ba. Komai yake miki yana yi ne kawai domin kara akan sadaukarwa da ya yi miki. Sadaukarwa ki ce a gare shi Beenafah yasa yake miki duk waɗannan abubuwan, amma sam ba zai iya ɗaukar ki a matsayin matarsa ba ta dindindin har abada..." Ƙara kwantar da muryarsa ya yi jin kamar kalamansa sun fara kamani sun kuma soma yin tasiri a kaina ya ce. "Beenafah! Ke da shi Sam baku dace ba. A GANIN IDON ki ne kike ganin kamar yana son ki amma sam ba haka ba ne. A lokacin da za ki kai ganiyarki ta cika Mace cikakkiya...shi a lokacin ya riga ya gama amfani domin ya tsofe sosai. Da ni kaɗai kika dace Beenafah, saurayine ni mai jini a jiki, tazarar da ke tsakaninmu ba ta yi nisan da za ta hana mana zama mata da miji ba har abada. Ni ka ɗai na san irin son da nake miki wanda har abada babu wani mahaluƙin da zai so ki kamar ni Beenafah. Idan har na rasa ki ban san a wanne hali zan faɗa ba. Ki tausayi min ki zo gareni dan Allah. Ba zan matsa miki ba, ki je ki yi tunani Beenafah, duk abin da na faɗa miki haka yake." Sulalewa na yi na zube akan ƙafafuna tare da janye wayar daga kunnena. Sosai Kukana ya tsananta domin notukan kaina gabaɗaya sun kwance a halin yanzu. Da gaske ne waɗannan kalaman da yake faɗa mini ko kuma yaudarata yake yi? Kamar yanda nake ƙoƙarin auna maganganunsa...haka wasu tunanuka barkatai suka shiga bijiro mini. Da gaske Ya Mohaa amfani kawai yake dani? Da gaske zai yi wani aure har ya auro wacce ta Fini komai? Tabbas ni da shi ajinmu ya yi nesa da juna, sam idan ana zancen sa ban isa na nuna kai na ba domin ya yi mini ratar da ta ko'ina ba zan iya kamo shi ba har abada. To amma wanne rashin adalci ne zai sa ya ji cewar ni ban cancanta ba? Na san tabbas ni ɗin ban yi karatu ba, ko secondary school ban kambala ba, shi ɗin kuma babban mutum ne sannan mai kakkaifan ilmin zamani da na addini wanda duniya ta san da zamansa. Idan ya ce ya ɗauko mai aji irin sa har abada na sani ba zan kai labari ba. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Wayyo Allah na wayyo ni kai na...!! Mi yasa zai nuna a GABAN IDO na cewa yana so na amma kuma can cikin zuciyarsa ba haka ba ne? Yanzu ni da na sadaukar masa da kaina da rayuwata ba tare da sanin mi zai zo gabana ba har yana iya tunanin butulce mini? Idan kuwa hakane sam bai mini adalci ba. Ƙarshe girgiza kaina nayi ina mai jin tunani na neman haukatani gabaɗaya. Idan har Ya Mohaa zai iya yin haka a gareni to mi zai rage min a duniyar nan? Shi ne wanda na fara jin soyayya a kansa kuma na yarda da ita. Rayuwata da fata na duk na ɗora su a kansa. Idan ya ce zai juya mini baya in yi ya da rayuwata kenan? Haka dai na kwashe tsawon lokaci ina ta saƙawa ina warwarewa wanda ban samu komai ba sai ƙarin tarin damuwowi da ruɗanin da ban san ma yanda zan misalta shi. Lokaci ɗaya na dawo tamkar wata er maye domin na rasa ma wane kalar tunani zan yi. Da ƙyar na samu na rarrafa na haura kan gado na kwanta ina mai jin yanda wani irin ciwon kai ya yi mini dirar mikiya, kafin ka ce mi...jikina ya ɗauki wani irin zafi tsabar yanda nake cikin tsananin ruɗani da damuwa. Ina jin alamar buɗe ƙofa na yi saurin rufe idanuna tare da jan duvet na lulluɓe har saman kaina. ko ba'a faɗa ba nasan cewa aikowa ya yi a dubani domin tun ɗazu yake kiran wayata amma na kasa ɗauka wanda ban san dalilin hakan ba. Muryar Hairi na ji tana faɗin. "Mummy...mummy! Aunty Beenafah.." Juyawa ta yi tare da faɗin. "Halo Daddy kana jina? I told you cewa ta yi bacci,because tun around 9pm ta baro mu tace za ta yi wanka ta kwanta domin tana jin gajiya, har warning ɗina ta yi tace kada na zo ɗakinta domin ba za ta saurare ni ba ita bacci za ta yi." "Favourite kin tabbata Bibi tana lafiya?" Dariya ta yi tana mai gyaɗa kanta tamkar yana a gabanta ta ce. "I'm 100% sure Daddy! Ka kwantar da hankalinka Bacci take yi...bari ma na rage mata gudun ACn nan because na ji kamar ya yi yawa...kada mura ta je ta kama mana babynmu a banza tun yana ciki in shiga uku in lalace..." Remote ta ɗauka ina hangota da maƙalallen idona ta rage gudun sannan ta kashe mini fitila ta fice tare da ja mini ƙofa. Ina ganin ta fice na miƙe zaune ina mai tattaɓa jikina domin in tabbatar cewa da gaske sanyi ya yi yawa? Sam ban ji wani abu makamancin hakan ba domin zufa nake ta ko'ina. Hannuna na kai ina shafa cikina tare da lumshe idanuna na zubo da wasu irin zafafan hawaye a rai na ina faɗin. 'Wanne Babyn Hairi? Babyn da nasan ko shi amfani ne kawai yake dani domin ya samu cikar burinsa na zamo wa uba a karon farko na rayuwar sa, tabbas na san da ba don wannan ba banga wani dalili da zai sa ya yi ɗokin haihuwa da ni ba, ni ɗin nan da ba kowan kowa ba...da sauri na sake ɗora ɗayan hannun nawa na dafe cikin baki ɗaya ina mai girgiza kai cike da jin wata irin matsananciyar ƙuna a raina na furta a fili na ce. "Ka yi haƙuri Babyna..amma idan har ta tabbata cewa zargina akan mahaifinka ya tabbata....i won't regret for doing my second thought..." Daga haka na komar da kaina kan Pillow ina mai jin yanda zuciyata ke wani irin zafi tamkar an kunna mini wuta a cikinta. Miyasa ma tun farko zan aikata? Idan har hakan da gaske ta kasance ya Ammiena za ta yi kenan? Sosai hankalin ta ya kwanta ganin yanda nake zaune lafiya ina farin ciki...to idan wani abu ya bijiro sabo daga sama mi zai faru da ita? Kada sanadiyyar hakan ta sake rasa tunaninta. "...Ke ɗin ba kowa bace idan aka kwatanta da Engineer domin yafi ƙarfin ki ta ko'ina, Babban mutum ne wanda duniya ta san da zamansa, yana da kuɗi, yana da ilmin da ke ko kan akaifar ƙafarsa ba ki kamo ba,da za ki zauna ki nutsu ki yi nazari, sam! Ke da shi baku dace ba, kawai yana amfani dake ne na ɗan wani lokaci domin biyan wata buƙatar kansa..." "....amma sam ba zai iya ɗaukar ki a matsayin matarsa ba ta dindindin har abada..." ".....Daman wata mummunar ƙaddara ce ta yi masa hijabi da samun matar da ta dace da shi, tunda kuma a yanzu dama ta samu, ba jimawa zai aure Macen ta waye, ta goge, ta yi ilmi mai zurfi da ta fiki komai ta kowace fuska, a wannan lokacin ne za ki dawo bola shara marar amfani, daga ƙarshe saki ne zai biyo baya na wulaƙanci ma..." Waɗannan su ne maganganun da suka shiga dukan ƙwaƙwalwata ba tare da bata sarari kona Second ɗaya ba. Waɗannan kalaman sun yi mini illar da ko ruwan guba nasha bana tunanin za ta iya cutar dani ta lahantani kamar yanda suka yi ba. Na ɗimauta na gigita. Sam tunanina bai kai can ba. Sai yanxu na tabbatar da cewa ni mahaukaciya ce domin ban taɓa yin irin wannan tunanin ba. Kwata-kwata hangena bai yi nisan wannan ba sai yanxu. Haka na kwana ba tare da runtsa ba, domin sam bacci bai yi gigin kawo mini farmaki ba, sanin irin mummunan yanayin da nake ciki a wannan daren. Daƙyar na iya lallaɓawa na watso ruwa sannan na zo na yi sallah na sake komawa na ƙudundune. Wani irin amai ne na ji ya taso mini lokaci ɗaya, ba shiri na diro ina mai faɗawa toilet na shiga kakari tamkar zan amaye hanjin cikina. A gigice Hairi ta shigo har toilet ɗin ta kamani tana ta faman yi mini sannu. Sai da ta tabbatar cewa na gama sannan ta bani ruwa na kuskure bakina muka fito. Kallona ta yi cikin tausayawa tamkr za ta fashe da kuka ta ce. "Sannu Aunty Beenafah! Daman baki da lafiya ne? Na harda jikin ki ya yi zafi..." Murmushin ƙarfin hali na yi mata domin na kwantar mata da hankalinta na ce. "Lafiya ƙalau nake, kawai dai yanayin ne bana jin daɗinsa..." "Allah sarki! Kewar Daddy kike ko? Shima na san duk inda yake yana can hankalin sa a kanki..wallahy ko jiya ba ki ji yanda duk ya ruɗe ba jin ya yi ta kiran ki ba ki ɗaga ba. Ko bayan na kwanta sai da ya sake kirana domin ya ƙara tabbatarwa na ce masa kina nan lafiya ƙalau.." " Lafiya lau nake, kema ki kwantar da hankalinki. Kira mini Biba in faɗa mata abinda za ta dafa mini.. " Har ta kai ƙofa na kirata ta waigo na ce. " Dan Allah kada ki faɗawa Yayanku, kinga kada a ɗaga masa hankali." Jinjina kanta ta yi tana faɗin. "In Sha Allah ba zan faɗa masa ba. Daman ai yau ne zai dawo.." Daga haka ta jiya ta wuce. Tea Kawai na iya sha ko shi don na ji kamar na fara jin juwa because kamar na faɗi haka nake ji. Daman a 'ƴan kwanakin nan duk na yi lattin cin abinci sai na ji yanayina na neman sauyawa. Duk wanda yake gidan ya fahimci cewa sam bana cikin yanayin walwala ta, domin maganganun Ya Jafaru sun kasa barin ƙwaƙwalwata , ko kaɗan na kasa samun sukuni. Ina gama shan Tea ɗin na shirya na cewa Hairi ta faɗawa Oga Sule cewa zan ta fi gida wurin Ammie na ya shirya ta kai ni. A tare muka tafi mu biyu dani da Hairi. Muna shiga gidan muka tarar an yi Uwar siyayya komai da komai gashi nan da alama ma yanzu aka gama sauke kayan. Bayan mun gama gaisawa ne na kalli Ammie na ce. "Ammie wannan kayan fa?" Kallon kayan ta yi sannan ta kalleni ta ce. "Siyayya ce na yiwa Hassana, Mijinta ya zo, gobe za su koma gida." "Ok. Allah ya tsare hanya." "Amin. Yau fa suka ce za su wurin ki tunda kema tafiya za ki yi, amma tunda kin zo bari na kira su na faɗa musu sai su zo nan ɗin..." Ƙara juyowa ta yi tana fuskantata da kyau cike da kulawa ta ce. "Beenafah!" Buɗe Idanuwana na yi waɗanda suke a rufe tunɗazu na kalle ta na ce. "Na'am Ammie.." "Miye abin da yake damunki?" Gabana ne ya faɗi jin wata tambayarda kwata-kwata ban tsammace ta a yanzu ba. Murmushi na yi ina ƙoƙarin sai ta kaina na ce. "Lafiya Lau Ammie..mi kika gani?" Cikin rashin yarda da maganata ta ce. "Naga fuskar ki tayi fayau, kuma duk kin susuce bakya cikin yanayin ki....ga idanunki ma duk sun zurma..." Murmushi Hairi ta yi ta ce. "Da wani irin Amai mai tsanani ta farka, kuma ba ta ci wani abinci ba, Tea Kawai ta sha muka fito...." A ruɗe ta ce. "Subhanallah! To kin je wurin likita kuwa?" A tausashe na ce. "Ammie ki kwantar da hankalinki please...ba wani abun da ke damuna, kawai kwana biyun nan ina jin yanayin amai ne, musamman idan naji wani kalar ƙamshin da bai gamshe ni ba." Jinjina kai ta yi tana faɗin. "OK! Allah ya ba ki lafiya." Wayarta ta ɗauko ta kira Su Aunty Aysha da kuma su Maman Fakiha ta faɗa musu cewa tafiya zan yi. Na san ta faɗa musu haka ne domin idan na koma gida ba lallai su samu ganina muyi sallama ba, duk da cewa tafiyar ina jinta tana mini wani iri a zuciyata tamkar na fasa haka nake ji. A yanda na ke ji a yanzu...tabbas komai na iya faruwa. A nan muka wuni har magriba, bayan mun sha fira da su Aunty Aysha su Fakiha sannan muka koma gida. Muna shiga na shige ɗakin Aunty Ziza domin na samu damuwata ta ɗan ƙara ragewa wanda na lura idan ina ni kaɗai abun yafi damuna sosai. Bayan mun gama fira sai misalin sha ɗaya muka koma ɗakina ni da Hairi. A yau kam ban isa na hanata kwana a nan ba domin na san ko nace ta tafi ba tafiya za ta yi ba. Ina nan naga text ɗin Ya Mohaa ya shigo kamar haka. "Salam Bibina...na rasa laifin da na yi haka da har kika ɗauki wannan tsattsauran hukunci a kaina...please ki sasauta min domin ya yi mini nauyi da yawa,... Sam ko Ruwa na kasa haɗiyewa, duk da cewa ban san laifina ba, please ina fata da ki sauko da wuri dan Allah...Duk yanda na so na kasa isowa yau, ina Abuja dole sai gobe zan iso. Ina ƙaunarki sosai...ina kuma jin tsananin kewar ki tamkar zan yi hauka haka na ke ji..." Taɓe baki na yi ina mai kawar da wayar a gefe, duk da cewa nima ina jin kewarsa kamar yanda yace shi ma yana kewata. To amma ni Sam ban wani jisa har can ƙololuwar kai na domin yanxu na gane cewa duk abin da yake faɗa mini na yaudara ne kawai ba don yakai har zuciyarsa ba. Washegari ma, ganin mun samu rarar lokaci muna gama karyawa na cewa Hairi mu tafi gidan Aunty Labiba domin na yi mata bankwana, idan har na koma ban je gidanta ba hakan ba zai mata daɗi ba ko da kuwa bata faɗamin ba. A bakin gate muka ci karo da kishiyarta Hajiya Marwa tana tsaye tare da driver da kaya a gaban shi da alama saƙo ne take so ta aike shi da shi. "Ina wuni?" Kusan iya kalmomin da muka furta a gareta kenan, wanda a wurin Hairi ko arzikin kallo ba ta samu ba. A mamakance ta wani kalle ni tamkar idanun ta za su zazzago ta ce. "Wace ce wannan kamar Beenafah?" Sai yanzu Hairi ta waigo ta yi mata wani kallon sannan ta ja ta togace ta ce. "Ita ce! Ya aka yi?..." Aunty Labiba da fitowarta kenan muka ji tana faɗin. "Ya kuka tsaya a can? Ku shigo mana." Kamar yanda take neman ƙarin haske haka itama Hairi ta ke ta tarin maganganu a cikin bakinta wanda ta so baje mata su kamar me, sai ga Aunty Labibar ta fito hakan yasa muka yi gaba muka shige ciki. Muna man misalin karfe uku na rana sai ga text ɗin unsave number ya shigo wayata. Da sauri na ɗauka, hannayena har wani shaking suke tsabar yanda na ruɗe ganin numbern Ya Jafaru. "Na ji ance gobe ne za ki tafi, kuma bamu samu mun ƙara tattaunawa ba, na san cewa kina cikin gidan Labiba a yanzu, please idan ba damuwa za ki iya fitowa mu haɗu mu tattauna, ina nan waje ina jiran ki..." Ajiye wayar na yi ina mai jin wani iri a raina, na jima ina ta saƙawa da warwarewa tsawon lokaci wanda daga ƙarshe na bi shawarar zuciyata da ƙwaƙwalwata cewa kada na tafi wurin sa, domin har yanzu ban gama farfaɗowa daga shock ɗinda ya bani ba, har yanxu ban gama fayyace maganganunsa ba na shekaranjiya ba, bitarsu na ke daki-daki wanda har yanzu ban kai ko rabin shafi na maganganun nasa ba, so nake na baje su da kyau na yi musu fassara ta fahimta domin neman mafita. Idan na ce yanxu na sake saurarensa tabbas kaina da zuciyata tarwatsewa za su yi. Haka muka ci gaba da fira sukuku dani tamkar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki. Muna nan misalin ƙarfe huɗu na yamma muna shirin tafiya gida sai wayar Hajiya ta kira tana shaida mana cewa wai daga nan gidana zamu wuce domin Ya Mohaa ya faɗawa Emraan cewa na wuce gida yana gab da isowa. Addu'a ta biyoni da ita har bakin gate, bayan mun shiga mota ta kamo hannuna cike da soyayya ta ce. "Beenafah! A kullum son ki ƙara ninkuwa yake a zuciyata, kin zame mana alheri Beenafah bayan kin shigo rayuwarmu. Kin sanya Daddy farin ciki wanda shi ne silar sauyawar ƙaddararsa. Ina alfahari da ke. Allah ubangiji ya ba ki lafiya, ya kuma sauke ki lafiya. Ki kula sosai, kuma ki riƙe duk shawarwarin da na baki kin ji ko? Allah ya kai ku lafiya." Murmushi na yi ina mai jin wani sanyi a raina na ce. " Amin yah Allah. Na gode sosai Aunty Labiba,Allah ya saka da alheri." Muna fita na fara waige-waigen inda zan gansa tamkar wata Mahaukaciya, sai dai, har muka isa gidan ko alamar sa babu. Muna shiga na tarar har Biba ta dawo ta shige kitchen baiwar Allah tana

Chapter 51 of 67