jikin sa,shi ne na yi ta bashi haƙuri, shi ne yanzu ya tsaya yana faɗamin baƙar magana cewa wai akwai nutsuwa da hankali. To nufin ka kenan bani da hankalin da nutsuwa ko? tun da na kusa kifa maka abu a jiki."
Lokaci ɗaya ran Jadda da Uncle Mu'aƙƙib ya ɓaci suka rufe shi da faɗa musamman Jadda wacce bata iya ɓacin rai ba idan an taɓa ta, sai faɗin take.
" Yarinya baƙuwa wacce zuwan ta kenan ka ke so ka ɗaga mata hankali da shegen zafin zuciya da fushin da ka saba! Waye ba ya kuskure da har za ka dinga faɗa mata baƙaƙen maganganu daga zuwan ka? Tun da ta zo garin nan take farin ciki sai yanxu da ka zo kai kaga sarkin en rashin haƙuri za ka matsawa rayuwar ta. Kai duk laifin da kake idan an ce za'a riƙa tsaurara maka za ka ji daɗi ne??"
Ai fa yau ya shiga uku. Daman mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Laifin da ya yi mata ne tun wan can zuwan da ya yi shi ne kenan ba ta huce ba, akan wannan ɗan abun take neman hawaye masa kai.
Da sauri ya harɗe hannayensa alamar roƙo yana murmushi ya ce.
"Dan Allah Jadda ayi haƙuri...ni wallahy wasa nake mata, Ita ce dai ta ɗauka da zafi. Amma kuyi haƙuri..."
Kallonsa ya mayar gun Hairin wacce ke tsaye tana wani cika tana batsewa yana murmushi ya ce.
"I'm Sorry please...I'm sorry!"
Jikin Jadda ta koma ta lafe tare da lumshe idanun ta tana mai jin yanda zuciyarta ta sanyaya. Tabbas da ba ta fitar da wannan abin daga zuciyarta ta yi magana ba, da wata ƙila ko bacci ba za ta iya yi ba a yau. How comes zai kalle ta bayan duk irin haƙurin da ta bashi ya zo cikin mutane yana faɗa mata baƙar magana?.
Murmushi Ya mohaa ya yi bayan mun gama kallon dramar ya ce.
"Ba komai Suhaib. Ka yi haƙuri. Ita ɗin yarinya ce ƙarama.."
"No...Ba komai Yallaɓai. Ai ita ce da gaskiya, duk abin da ta faɗa haka akayi ba ta yi Ƙarya ba. Saboda haka ta yi haƙuri..."
Firar su suka koma yi yayin da muma muke tamu har kusan 1am Sannan muka yiwa kowa sai da safe. Ganin zan wuce yasa Ya Mohaa kiran sunana ya ce.
" Bibi.."
Waigowa na yi a darare na ce.
" Na'am."
"Ki je, ina zuwa yanzu kin ji ko."
Kallon kallo muka shiga yi ni da su Hairiyyah wanda shi kam tunda ya yi maganar ya juya suka ci gaba da magana da su Suhaib kamar ba shi ne ya yi maganar ba. Wucewa na yi daga ƙarshe ina mai ɗaure fuskata domin ko tsayawa ce musu sai da safe ban yi ba na je na shige na yi wanka na yi kwanciyata.
A hankali ɗaya bayan ɗaya suka shiga watsewa wanda wurin ya rage daga Jaddi sai Ya Mohaa.
Kallon Hammodin ya yi wanda a duk lokacin da ya yi ido biyu da shi sai ya ƙara jin wata irin sabuwar ƙaunarsa na ƙara kama shi. Cikin sanyin murya Jaddin ya fara masa magana da cewa.
"Gabaɗaya kanmu a haɗe yake. And kuma muna zaune lafiya ƙalau. Mi zai hana kaci gaba da zaman ka a nan kawai da kai da matarka? Mun rayu tsayin shekaru ba tare da kai ba, a yanzu ina so na ci gaba da ganin ka a kusa dani. Ka yi tunani, ina so ka dawo nan ka shiga cikin shuwagabanni ka ci gaba da tafiyar da siyasa ta tare da iyayenka da en uwanka tun da Kaga ni ƙarfina ƙara tafiya yake."
Ido ya ƙura sosai yana kallon kakansa wanda ya zo masa da wata iriyar maganar da bai san ma ta ina zai fara ba. Jin ya yi shiru yasa Jaddi ya ɗan ƙara matsowa gaba kaɗan yana mai ƙara fuskantarsa da kyau yaci gaba da cewa.
" Ka na ji ko Hammodi...Ba wai ina nufin yau ko gobe ba. A'a, ka bari sai lokacin da ka shirya,lokacin da ka ji zuciyarka ta aminta sannan. Idan kuma baka da ra'ayi, still I won't force you, Kawai a yanzu, I want feel your presence a duk lokacin da na bukata."
Murmushi ya yi yana mai jinjina masa kansa ya ce.
" Jaddi! I respect your opinion, Saboda nima ina jin yanda ka ke ji a ranka...I also respect politics domin a yanzu ina ciki tsumbul tunda har ku ahlina kuna ciki gabaɗaya. But ka yi haƙuri amma ba zan iya siyasa ba. Ba Layina ba ne ba ra'ayi na ba ne. Ni ɗin Engineer ne kawai wanda bai san komai ba sai aikin gine-gine da yin tituna. Yanzu ne na fara rayuwar aure Jaddi...Things will become more harder on me Idan na ce zan ƙara ɗorawa kaina wani nauyin. Ka yi haƙuri ba don na bijire wa umarninka ba. Amma ka barni na ci gaba da rayuwa a Dubai kamar yanda na saba, In Sha Allahu zan riƙa zuwa time to time ina duba ku domin a yanzu kun zamto nauyina kuna da haƙƙi a kai na, har abada ba zan taɓa barin ku ba, na yi alƙawari. I will always stay connected."
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu na en wasu daƙiƙu sannan daga ƙarshe Mohaa ya ɗan ƙara matsawa kusa da shi tare da kamo hannayensa ya jimƙe a nasa yana mai ƙara kwantar da muryarsa sosai ya ce.
" kun shafe tsawon shekaru ba tare da kun san cewa ina raye ba. Haka nima na shafe tsawon shekaru ba tare da na san cewa ina da ku ba. To miyasa kake tunanin yanzu da na sameku zan iya ɗaukar dogon lokaci ba tare da na zo na ganku ba? Ina da kamfani wanda yake da rassa daban-daban kuma dole ni ne ke tafiyar da shi. sannan su kan su ƙannaina suna da buƙata dani a kusa da su domin su ɗin Amana ce a wurina. Barin duk waɗannan abubuwan kai tsaye ba abu mai sauƙi ba ne Jaddi. Ina fata za ka fahimce ni dan Allah!!"
Murmushi Jaddi yayi yana mai jinjina masa kansa ya ce.
" Ba komai Hammodi! Daman tun farko na faɗa maka cewa I won't force you. Waɗannan kalaman naka kaɗai sun gamsar da ni cewa hasashena Sam ba gaskiya ba ne, na cewa za ka iya barinmu. Allah ya yi maka albarka. Allah ya baku zaman lafiya da Zuriya ɗayyaba."
"Amin Jaddi. Na gode da fahimta. Allah ya ƙara maka tsawon rai da lafiya mai amfani da albarka."
"Amin. Ta shi ka tafi wurin matarka, dare ya yi sosai. Allah ya tashemu lafiya. Gobe ka fito da wuri zamu zaga inda na faɗa maka ka dubo ka gani"
Murmushi kawai ya yi domin kalmar "tashi ka tafi wurin matarka" ba ƙaramin dariya ta bashi ba. Miƙewa ya yi yana ƙara yi masa sai da safe sannan ya juya ya wuce.
*****
Washe gari kam lafiya ƙalau na farka ba tare da wata damuwa ba, domin jiya ban san ma lokacin da ya shigo ɗakin ba sai da na farka da asuba na ji ni a cikin jikin sa, kuma yana dawowa daga masallaci ya shirya suka fita tare da su Uncle Mu'aƙƙib wanda ban san inda suka nufa ba.
Bayan na shirya ni kuma na fito Kitchen muka ci gaba da yin aiki tare da su Suwara. Muna nan muna fira cike da nishaɗi Suhaib ya leƙo wanda da alama daga wurin motsa jiki ya fito sanadiyyar wata irin zufar da yake tsiyayarwa ga kuma kayan motsa jiki a jikin nasa.
Gaisawa muka yi da shi cike da mutuntawa ɗaya bayan wanda Hairi ce kaɗai wacce ta ɗauke kai tare da ƙara yin fuskar shanu tamkar bata taɓa sanin yan da ake dariya ba.
"Ke! so dangi..."
Ya faɗa yana mai kallon fuskar Hairi.
Ɗage kafaɗarsa ya yi tare da ware hannayensa alamar ko a jikin sa sannan ya kakkallemu ya ce.
"Ita ce ta min laifi, kuma ita ce ta tara min jama'a ta saka Jadda neman tono laifina na kusan watanni huɗu, sannan kuma still ita ke fushi...Taimiyyah!"
Ya ambata sunan ta daga ƙarshe yana mai kallonta ya ce.
"A bata breakfast ta kawo min ɗakina kafin na gama wanka."
Bayan ya wuce muka ɗauko firar muna ta tsokanar ta da ita muna dariya wanda ko kaɗan bata buɗe baki ta yi mana magana ba.
Bayan Taimiyyah ta gama haɗa abincin ta miƙa mata tana faɗin.
"Idan kika fita ta wannan ƙofar, ɗakin da ke kallon wancan garden ɗin can ne ɗakin sa.."
Wani irin ƙara ɓata rai ta yi kai tsaye ta ce.
"Ni fa ba zan je ba. Ku bai wa mai cikakkiyar nutsuwa da hankali ta kai mas.."
"Haba Hairi! Ki yi haƙuri mana. Kina ga fa har zubar da kansa ya yi gaban kowa jiya ya baki haƙuri. Shi ma ɗinfa Yaya ne a gare ki kamar su Emraan."
Cewar Aunty Labiba tana mai ɗan Kausasa Muryarta kaɗan ko Allah zai sa ta sauko daga Dokin zuciyar da ta hau.
Jin irin yan da Aunty Labibar ke magana yasa ta karɓi trayn ta tafi tamkar za ta kifa ta tura ƙofar ɗakin ta shiga kai tsaye. Within seconds ta gama ƙare masa kallo da ɗakin nasa wanda ya kai maƙura wurin haɗuwa sannan ta ajiye trayn a kan wani glass table tana wani Harararsa a kaikaice daga can inda yake tsaye jikin window yana Waya.
Ganin yaƙi ya tsinke kiran ballantana har ya yi noticing ɗin cewa ya ganta yasa ta Juya ta nufi ƙofa domin ficewa.
"Jira na ne ba za ki Iya ba?"
Tsayawa ta yi cak ba tare da ta waigo ba ta ce.
"To ai ga shi nan na riga na ajiye maka.."
"I LOVE YOU..."
A ruɗe ta waigo tana mai zuba idanuwanta ta kalle shi da kyau domin ƙara tantance mi ya ce a bayan idon ta.
Ta kowa ya yi ya tsaya a gabanta yana mata murmushin da tun a daren jiya idan ta kalleshi taga yana yin sa yake burgeta ya ce.
"Daman jiya har da haushin zancen ƙin auren da na yi ne yasa Jadda ƙara harzuƙa kuma ke ce kika janyo hakan. Saboda haka ina son ki, ina son ki, ina son ki. Yanzu sai ki san yanda za ki yi dani ki aureni."
Ƙirjinta na wani irin tsalle jin ta a wani irin yanayi, Muryarta har tana sarƙewa ta ce.
" Ka taɓa ji inda akace an kamu da soyayya daga dare zuwa safe?"
Jikin ƙofar ya jingina tare da tallafe hannayensa a ƙirjinsa yana kallon fuskarta wacce duk ta nuna rashin nutsuwa ya ce.
"Ana yi mana! Sau nawa ma akayi? Wa su ma ko ganin juna basayi kuma a ɗaura musu aure su zauna lafiya ballantana mu da tun a daren jiya son ki ya hana zuciyata sukuni..."
"To idan ni kuma bana son ka fa?"
"Ba zai ma faru ba....Tun jiya da kika ɗauko min Tag ɗina kika ruɗe kina ta bani haƙuri da kuma irin yanda kike ta satar kallona a Rooftop kina magana ta da Taimiyyah na gane cewa kema kin kamu da So na..."
Zuciyarta na wani irin pumping ta gimtse idanunta da ƙarfi tace.
" Ni dai ka matsa mini a hanya na wuce."
Janyewa ya yi ya koma gefe yana murmushi har ta fice da gudu tamkar za ta kifa tsabar yanda ta ruɗe take neman ficewa daga hayyacinta.
Har suka kambala breakfast ɗin gabaɗaya hankalinta baya jikinta, idan sau dubu ta rufe idonta babu abin da take gani yana mata gizau idan ba shi ba. 'IG SUHAIB' sunanda ke ta mata yawo kenan a brain ɗinta tsawon lokaci.
*******
A ranar Juma'ar da muka cika sati, a ranar muka shirya domin komawa gida, inda aka ajiye maganar Suwara da Ya Emraan daga zaran ya koma gida ya shaidawa sauran iyayensa. Sannan Ig Suhaib da Hairiyyah shima kamar da wasa sai ga shi ya kai maganar gaban su Jadda wacce daman ta jima da damuwar rashin aurensa, hakan yasa suka yi matuƙar farin ciki musamman da ya kasance Hairi ce zaɓinsa duk da cewa mahaifiyarsa ta so ta ɗan yi tirjiya sakamakon kasancewar Hairi ɗin 'ƴa a wurin Hajiya Batula. Sai da su Jadda suka tsawatar sosai sannan ta saki ranta ta amince itama.
Mun yi nishaɗi, munyi zumunci mai ma'ana a ƙasar Sudan wanda za mu jima wannan tarihin bai shafe a zukatanmu ba.
Tunda aka saka kayanmu a mota Suka fara koke-koke musamman Jadda. Bayan mun fito na riƙa hannun Suwara ina murmushi na ce.
"Zo ki rakani na hau Rooftop ɗin nan na bankwana. Wallahy wurin nan yana matuƙar bani nishaɗi."
Jinjina kanta ta yi tana murmushi ta ce.
"To shi kenan Aunty Beenafah. Muje daga nan sai na miki hotuna, kinga idan kin koma gida duk randa kika ji ina jin kewar Rooftop ɗin sai ki kamo ki yi ta kalla."
Sama muka haura har da Hairiyyah muna ta hotuna muna nishaɗi.
Kallon Ya Mohaa Jadda ta yi tana ta wani kuka ta riƙe masa hannu ta ce.
" Hammodi dan Allah karka barni.. "
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali sannan ya ɗago hannun da ta riƙe shi da shi ya sumbata. cikin sigar rarrashi ya kwantar da murya ya ce.
" Ba zan taɓa barin ki ba Jadda...nan ɗin a yanzu shima ya zama gidana. Ba zan taɓa barin ku ba sai idan mutuwa na yi..."
"To ai kana iya jimawa baka waiwayemu ba Hammodi...I'm afraid.."
"Ba zan yi hakan ba Jadda. Da lokacin da kika so gani na, da lokacinda ma ba kya buƙata dani duk za ki riƙa ganina In Sha Allahu..."
Kallon Jaddi ta yi wanda shima duk ya yi wani iri ta ce.
"Alhaji miyasa ba zamu aura masa Noura ba??"
Wani irin waro ido ya yi a gigice ya ce.
"What!!"
Suma su Aunty Labiba a mamakance suka zuba ido suna kallonta, jin wata iriyar yasassar maganar da sam ba su tsammata ba.
Murya a karye ta ce.
"Ita ɗin er uwar ka ce Hammodi...ya kamata muyi hakan ko don ƙarfafar zumuncinka da en uwanka..."
Wani irin girgiza kai ya yi da ƙarfi tare da faɗin.
"This is a very bad Idea Jadda...ban shirya aure ba ni. Matata wacce nike da ita ta isheni komai...i can't do this to her."
"Hammodi!..babu wanda ya isa ya shiga tsakaninka da matarka. Duk kowa da yake nan yana sonta...amma dan Allah ka auri Noura..Alhaji! Mu'aƙƙib... Razia! Dan Allah kuyi masa magana mana! Ina so ya auri Noura. baiwar Allah ce mai matuƙar kirki da son ibada. Tun da Mijinta ya mutu yau kusan shekara uku kenan ta kasa samun farin ciki, ga marayun yara gareta. Ita ɗin 'ƴar uwar ka ce..."
Lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa ta shiga tsaka mai wuya domin har abada ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zai iya haɗa Bibinsa da wata macen ba. Wato a tare suka kitsa komai kenan? Tun da gashi babu wanda ya buɗe baki ya faɗa mata cewa wannan maganar da tayi ba akan daidaita take ba, Sam ba ta dace ba. Miyasa ma duk tsawon zamansa a gidan ba su kawo masa wannan zancen ba sai yau da ta kasance ranar rabuwar shi da su?
"Hammodi!!"
Uncle Mu'aƙƙib ya ambata sunansa a hankali sannan ya ci gaba da cewa.
"Tsawon shekaru baka tare da su. Alfarma Ƙwaya ɗaya! Ka daure ka cika musu ita dan Allah.."
Wai miye haka ne? Ya tambayi kansa ya yin da yaji ƙwaƙwalwarsa na neman zaucewa.
Daga irin kallon da Labiba ke musu kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa sam ba ta yi na'am da wannan maganar ba. Idan har zancen xumunci suke ai an gama ƙulla shi tunda ga shi kowa ya bayar da mutum biyu daga ɓangarensa. Gaskiya su Jadda ba su so gaskiya ba kuma muddin za ta faɗa masa ya ji to ba zai auri wata Noura ba.
Muryar Jaddi ya ji a tsakiyar kansa yana faɗin.
"Please kada ku matsa masa, idan ba ya so dan Allah kar ku matsa..."
Yana hango su Beenafah suna saukowa ya ƙara jin zuciyarsa ta sarƙafe da wani irin sabon ruɗani wanda ba shiri ya ɗagawa Jaddi Hannu da sauri ya ce.
"Please dan Allah ku bar wannan maganar, ga ta tana tahowa. Ku daina na roƙe ku....."
Da sauri na nufi mota da gudu ganin ya wuce kai tsaye ba tare da ya kira ni ba. Wata ƙila kuma fushi ya yi ganin na jima a sama ban sauko ba ya gaji da jira.
Ɗaga musu hannu na shiga yi ina murmushi kamar yanda suma suke min har muka fice daga gidan a raina ina jin wata irin kewar su tun ban bar garin na su ba.
Muna isa muka sauka wanda daman su Aunty Labiba daga nan Nigeria za su wuce, yayin da, ni, Ya Mohaa da kuma Hairi ne zamu wuce mu koma Dubai daga can ta wuce makarantar da take a Jami'ar Madina.
Hannuna Aunty Labiba ta riƙo idanunta cike da hawaye ta kalleni tana mai jinjina kanta ta ce.
"Ke ɗin Jaruma ce ta gaske Beenafah. Na yi imani daga inda kika faro da manyan jarabawowi har kika kawo nan to babu wani abu da zai tari gabanki wanda zai ba ki tsoro. Na gode da duk irin sadaukarwa da kika yi a gare ni Beenafah. Ina roƙon Ubangiji ya ƙara muku zaman lafiya da fahimtar juna ya ƙara muku danƙon soyayya a tsakaninku sannan ya ba ku zuria ɗayyaba."
Murmushi na yi mata yayin da nima ɗin na ji wasu irin hawaye sun ciko mini idona na ce.
" Amin yah Allah Aunty Labiba. Ina gaishe da Adeel da Hanan da su Hajiya....Aunty Nadeeyah. Ki barni na kiraki da shi na yau kawai. Allah ya kaiku lafiya ya sake sa da mu da alherinsa. Ina gaishe da su Dija."
Huggig ɗina Aunty Nadeeyah tayi itama da ruwan hawaye tab a kwarmin idonta muka yi bankwana. Duk budurin nan da muke yi Hairi na can tare da Suhaib suna ƙara zantawa yayin da Ya Mohaa da Emraan da kuma su Jaddi ke can suna wata maganar ta daban.
Su suka fara tashi sannan mu. Kallon Ya Mohaa na yi wanda duk ya yi wani iri wanda nasan bai rasa nasaba da kewarsu da yake ji a ransa. Tabbas ko ni nan wallahy rai na cike yake da kewarsu ballantana shi da ya kasance jinin su da ya shafe shekaru ba ya tare da su.
Hannu na kai na shafa gefen fuskarsa, cikin nuna kulawa na ce.
" Kana jin kewa ko? Uhm! Daman haka rayuwar take. Muna son masoyanmu muke rabuwa da su ba don hakan yana mana daɗi ba sai dai don wani dalili mai ƙarfi. Kamar dai yanda ka rabo ni da Ammie na wacce nake matuƙar ƙaunarta ba don na gaji da ita ba ba. To haka abun yake, Amma kuma a ko'ina suke masoyan namu suna zuciyoyinmu, ga kuma waya. Sannan idan an samu rarar lokaci, sai a yi ziyarci juna, in ma dai mu je, ko kuma su su zo gare mu..."
Ji ya yi lokaci ɗaya zuciyarsa na neman tarwatsewa tamkar gilashin da aka rotsawa falalen dutse. Hannayensa ya saka ya wani rungumoni har sai da na ji faɗuwar gaba ya riskeni jin wannan irin cakuma haka.
Shiru muka yi dukkanmu yayin da nake iya jiyo yanda zuciyarsa ke bugawa domin kunnena a daidai saitin ƙirjinsa yake.
Girgiza kansa ya fara a hankali tare da runtse idanuwansa tamkar mai tsoron kallon wani abu ya shiga tambayar kansa cewa. Miye yasa haka? Mi zai sa su yi masa haka? Sun san kuwa Wacece Beenafah a wurin sa? Akan me za su nemi su ƙirƙiri auren da wacce suke fighting akanta ma bata ƙasar? Auren nasa kwata-kwata kwana nawa ne? Miyasa wai mutane basa son a zauna lafiya ne...to ya ce mata me? Su Jadda sun bani mata don kawai su ƙara ƙarfafa zumuncinmu ko me? Ita ɗin fa yarinya ce ƙarama wacce bata san komai ba sai son a bata kulawa. Ta ya ya zai fara furta mata zancen wani aure alhali auren su ko shekara bai rufa ba? Impossible? Har abada abin da ba zai faru ba kenan? Da dai ya ɓatawa Bibi..to gwanda ya ɓata da kowa har abada....
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM*
*OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671*
*FREE-BOOK*
*PAGE 46*
Tun da muka dawo tsawon sati biyu kenan amma na rasa gane miye abin da yake damun mijina. Ko kaɗan bai canja min daga irin yan da yake kulawa dani da kuma nuna min soyayya ba, hasalima ƙaunarsa da kulawarsa a gareni ƙaruwa suka yi wanda nike jin yanzu a duniya kamar nafi kowace irin mace sa'a. Duk yan da zai jima a wurin aiki ƙarfe shidda na yamma a gida take masa komai yawan ayyukan da yake da su kuwa. Idan kuma ya dawo, zamu kasance a tare wanda sallah kaɗai ke rabamu, sannan idan ƙarfe takwas ta yi na dare, to zai taɓa aiki na hour ɗaya kacal sannan ya ajiye sai kuma gobe.
Sai dai kuma, Komai da yake yi sam babu walwala a ciki tunda muka dawo, idan na tambayesa abin da yake damunsa sai dai ya yi murmushi ya kalallameni yace min ba komai har sai na yarda a raina da cewa ba komai ɗin.
Yau ma koda na farka har ya gama shirin fita. A gaggauce na diro daga kan gadon cikin nuna rashin jindaɗi na ce.
"Eyyah! Please I'm sorry...bacci ne ya kwasheni sosai har ban san cewa ka gama shiryawa ba.."
Da sauri ya riƙo tsintsiyar hannuna a hankali ya tura ni cikin jikin sa ya rungumeni na ɗan lokaci sannan ya sumbaci gefen Wuyana wanda na tabbar hakan yana matuƙar yi masa daɗi sannan ya janye yana mai kallon cikin ƙwayar idanuna ya yi mini murmushin nan nasa mai sanyi ya ce.
"Tun da yanzu Bibina ta rage yin raki ai ni kam komai ya yi daidai. Kwalliya ta biya kuɗin sabulu..."
Cikin ƙirjinsa na mayar da fuskata domin ni dai ba zan iya kallon sa da wannan abin kunyar da yake faɗa ba. Mutum duk yan da ake nema a faranta masa kuma sai ya nemi yanda zai mayar da shi abin tsokana.
"Madam Amima ta riga ta gabatar min da breakfast na ci kada ki damu...ɗauko Hijab ɗin ki ki rakani mota."
Juyawa na yi na ɗauko na sanya muka fito hannu na a cikin nasa har wurin jerin gwanon motocinsa. Su Sharath na ganina suka shiga gaishe ni kamar yanda suka saba inda sun yi tozali dani.
Bayan ya shiga nima sai na shiga tare da zaunawa na riƙo hannunsa ina murmusawa ba tare da nace komai ba.
"Tare zamu tafi office ɗin ne?"
Girgiza kaina na yi alamar a a, sannan ya sake cewa.
"To ko na fasa fitar ne?"
Nan ma girgixa kaina na sake yi tare da ɗagowa na kallesa ina mai karyar da muryata ba tare da na saki hannun nasa ba, na ce.
"Abincin da madam Amima ta ajiye ko kaɗan baka taɓa ba, na fahimci hakan ne daga yanda aka saba jera kayan komai ba'a taɓa ba a ciki. A 'ƴan kwanakin nan kwana kake a zaune,inma kana sallah ko kuma kana kwance idanuwanka a buɗe,hakan yasa baka samun ishashshen bacci wanda hatta idanuwanka idan na kalla ina gane hakan, kuma sam hakan baya min daɗi. Yana sakani a damuwa nima. Dan Allah idan har ni ce nake maka wani abun wanda baya maka daɗi dan Allah ka gayamin, idan ma wani ne can a waje, ko kuma a wurin aikin ka ka sanar dani. Idan na bayar da shawara ne sai na baka, idan kuma ba hurumina ba ne sai na taya ka da addu'a, duk da cewa kana cikin addu'a ta....."
Lumshe idanunsa ya yi a hankali ya buɗe su a kaina yana mai jin yanda zuciyarsa ke masa wani irin sanyi tamkar ana zuba masa ruwan ƙanƙara akan yanda kalamai na ke shiga kunnuwansa suna yin tasiri...yarinya ƙarama, amma idan ta yi magana tamkar wata babbar mace. Hankali da baiwar magana ba lallai dole sai mai tsagwaron shekaru ba. Idan Allah ya datar da kai mata ta gari ka huta da duk wata damuwar duniya, domin daga lokacin da ka samu mata ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 44 Chapter of 67