Share this page
zo su shiga ciki. Yana shigar da shi ya juya ya tafi abinsa. A zaune ya tarar da ita cikin shigar Abaya baƙa tayi rolling da gyalen ta so masha Allah. Kafin yakai ga dire mazaunansa har ya ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa daga inda take zaune. Wanda shi in dai ganawa ne da yarinya irin haka to shi kam sai ya ce ba baƙon abu bane a wurinsa, domin an yi haka yafi a ƙirga wanda har sai da takai idan an ce mishi ga yarinya sai dai ya ce kawai ba sai ya ganta ba, kawai idan ta amince a ci gaba kawai da hidimar buki, daga ƙarshe haka za'a ƙare cikin rashin nasara wanda shi ne ciwon sa da baƙin cikinsa har aka ka zo kan Beenafah, lokacin da Labiba ta zo masa da zancen kwata-kwata bai saka shi a kansa ba har sai da ya ji cewa an ɗaura musu auren da gaske. Cikin nutsuwarta ta furxo kalaman maraba a gare sa ba tare da ta ɗago ta kallesa ba. Ba ta jira amsar sa ba ta ɗora da cewa. "Zan amsa auren ka ne kawai ba don raina yana so ba...domin bayan mijina da ya rasu bana jin akwai wani namiji a duniya da ya yi saura wanda zai iya bani farin cikin da na rasa. Zan yi ne don biyayyar iyaye..." Take ya ji wani irin ɓacin ran da bai san ma daga ina yake ba ya yi masa dirar mikiya ya cake masa zuciyarsa, wani irin shegen kallo ne ya mata a hargitse ya ce. " Ohh! Wai ke a ta wannan fuskar kika ɗauki abun? Waye ya ce miki na zo nan ne saboda ina son ki?" A razane ta ɗago ido ta kalle shi domin kalamansa sun yi matuƙar zo mata a ba zata. "Kallon me kike min? Kamar yanda kike tunanin babu namijin da zai iya baki farin ciki bayan mijin ki da ya mutu, haka nima bana tunanin akwai wata mace a duniyar nan da za ta bani farin cikin da matata take bani...wai miyasa ku wasu mata kuke abu tamkar babu ƙwaƙwalwa a cikin kan ku ne? Da aka ce na zo nan ɗin kin ɗauka shashasha ne ni marar aikinyi ko me? Da kin san yanda akayi har na zo nan ɗin da ba ki buɗe baki kin fara tarba ta da wannan banzar maganar ba... " Kuka ta fashe masa da shi tana mai girgiza kanta ta ce. "Matsalarka kawai kasani, shiyasa kake furta waɗannan kalaman a gareni..." "Matsala? Ai ni Allah ya rabani da matsala tsawon lokaci, Alhamdulillah! Amma dai sai ke yanzu sabuwar matsalar da na samu ta haye kaina ta yi bake-bake. Da kike ma wani zancen matsala ke har matsala kike da ita? Saboda mijin ki ya mutu shi ne matsala? Zaman Auren shekara bakwai kaɗai har yasa kin iya kinibibin ƙin maza ko? To su waɗanda suke rayuwa tsawon shekaru talatin, arba'in, hamsin...ɗaya ya mutu ya tafi ya bar ɗaya su ce ya ya? Kowa fa a rayuwar nan ba shi da ikon zaɓarwa kansa Ƙaddara. Sannan kamar yadda farin ciki bai zama har abada haka ma baƙin ciki ba ya zama har abada. Kin rayu tsawon shekaru kina farin ciki, don yanzu wannan ƙaddarar ta same ki sai ki yiwa Allah butulci? ki ce duk ni'imominsa a gareki baki gode da ko ɗaya ba? akan mutuwar mijinki za ki yanke ƙauna daga gare sa? Tsawon shekaru uku bakya farin ciki to su 'ƴa' ƴan ki taya za ki iya ƙarfafasu?" Hankali tashe ta haɗiye sauran kukan ta domin wannan mutumin ba ƙaramin mamaki ya bata ba. Ta ɗauka cewa zai zauna ne ya rarrasheta ya bata haƙuri akan irin yanda ta ke ji kamar yanda Maza da yawa suke mata idan sun zo gareta, amma sai ta ji yau kawai ta haɗu da wani mutum na daban wanda ra'ayi da rayuwarsa sun bambanta da na sauran mazajen. Miƙewa ya yi sannan ya kalle ta ya ce. "Ba nuna ƙiyayyarki a gare ni bane abin da yamin zafi...magana ta gaskiya ko! ni hakan taimakona ma kika yi,domin matata Allah ya sani bana da burin haɗata da kowace mace, saboda haka ki faɗa musu da bakin ki cewa har ki mutu ba za ki iya son wani mutum ba domin mijinki kawai kike so, idan kuma suna so suga farin cikin ki to lallai su dawo miki da shi. amma yanda kika tarbeni da munana nan kalamai ne abin ya mini zafi. Ni ba yaro ba ne, at least ya kamata ki tauna kafin ki furzo.." "Ka yi haƙuri!" "Kema haka! And....Idan har na sa ki jin ba daɗi ki yi haƙuri, amma dai kin san cewa ni ɗin ɗan uwanki ne ,yayanki. Ina da dama da ikon da zan yi miki faɗa idan har kika yi ba daidai ba." Daga haka ya fito ya cewa Raihab ya yi masa sallama da Hajiya domin a wannan daren ya ke son komawa gida, ba zai iya kwana a wannan garin ba. A tare ta fito da wasu kyawawan yara guda uku wanda tana tafe suna biye da ita har ta zo ta samu wuri ta zauna. Da murmushi a fuskarta ta kalle shi ta ce. "Ban san wace irin tattaunawa ku ka yi da Noura ba. Amma dai ina baka haƙuri da irin ɗabi'unta. Mutuwar Mijinta ne har yanzu ta kasa barin jikinta. In Sha Allahu komai zai yi daidai." Cike da girmamawa ya jinjina kansa ya ce. "Ba komai. Amma dai ina neman wata alfarma guda ɗaya;kada ku ce za ku tilasta mata, ta faɗamin Cewa ba ta da ra'ayi, Sam bana son ta sanadina ace rayuwar mace ta ƙuntata. Ita ɗin bazawara ce, tana da haƙƙin zaɓarwa kanta mijin da ya dace da ita. Ku ƙara mata lokaci ta ƙara fahimtar matsalarta domin neman mafita..." Hannu ya miƙawa yaran yana murmushi, sai gashi sun zo gare sa gabaɗayansu suna masa murmushi. Babbar ce wacce za ta yi 7years ta gaishe da shi sannan mai bi mata da za ta yi 5yrs jin yayar ta ta gaishe itama sai ta gaishe da shi. Hannu yasa ya ɗauko ɗan ƙaramin ƙanin su wanda zai iya yin 3yrs ya ɗora shi akan ƙafarsa  yana ta yi masa wasa yaran na gefensa suna masa surutu tsawon lokaci wanda har sai da ya ji cewa ya gaji sannan ya ajiye shi ya ce. "Ni zan koma Hajiya..." Lokaci ɗaya Hajiyar ta ji cewa ya kwanta a ranta tana son ya kasance mijin 'ƴar ta. Kalli yanda yake yi da yaranta wanda da alama yana matuƙar son yara sosai. Ko ba komai zai barta ta zauna tare da su a hannun ta ko don saboda zumuncin da ke tsakaninsu. Kallon shi ta yi ta ce. "Dan Allah ka zauna zuwa gobe mana, kafin nan mahaifin su ya dawo sai ku tattauna da shi. Ko ba da auren ba ai nan ɗin gidanku ne kai ma..." Jinjina kansa ya yi ta ce. "Haka ne gaskiya. Na gode sosai da karamci. Amma ba zan iya jira zuwa gobe ba, ku ɗin m en uwa ne, ko ba don Ita ba zan iya dawowa watarana." "To ba damuwa. Allah ya tsare, a gaida mutanen gidan." Tun da ya baro gidan har suka isa Airport bai ji ya daina jin haushinta ba a ransa duk da cewa ta ce bata son sa, hakan ba ƙaramin faranta masa rai ya yi ba. Wayarsa ya ɗauko ya lalubo numbern Labiba ya kira ta. Tana ɗagawa bayan ta gaishe shi ya ce. " Ni ɗin mutum ne mai takurawa Labiba? Ina nufin na cika zafi ko?" Da sauri ta girgiza kanta tamkar tana a gaban sa ta ce. "A a Daddy, waye ya faɗa maka haka? Kai ɗin nan fa kafi ruwa sanyi da son zaman lafiya" Jinjina kansa ya yi ya ce. "Uhm! Yanayina ne ya canza, sai na yi mata faɗa sosai bayan ta faɗi wasu kalamanda ba su kamata ba..." Hankali a tashe ta ce. "Wace ce wannan?" "Noura da Jadda ta ce sai na aure ta. But...Alhamdulillah! Ta ce bata yi, yanzu hankalina ya kwanta. Ina fata za ta yafe min ko ba komai mu ɗin 'ƴa uwa ne. sannan ina fata ta canja tunanin da take watarana, ko zai sa ta samu wani mijin ta yi aure. Ya yi wuri da yawa a cikin rayuwarta ta ce ba za ta sake wani auren ba." Cikin farin ciki Labibar ta ce. " Kai! Amma gaskiya na ji daɗi sosai, domin magana ta gaskiya ni dai ba son auren nake ba Allah ya gani. Don kawai bani da iko ne yasa na yi shiru. Allah ya ji ƙan mijinta ya bata haƙuri ya sanyaya mata zuciya." "Amin. Zamu shigo cikin satin nan idan Allah ya nufa." "Allah ya nuna, ai Mummyn Adeel ta faɗa mana." "Amin." ********* Emraan kuwa, shiryawa ya yi ya wuce wurin aikinsa wanda bai dawo ba sai da ya yi sati biyu cif. Yana shiga gidan bai ko bi ta kan Ziza ba ya ajiye kayansa ya shiga ya yi wanka sannan ya fito ya tafi gidan Labiba. Koda ya je gidan bata nan bata dawo daga wurin aiki ba. Hakan yasa ya shiga gidan Hajiya Marwa wacce tunda ya shiga suka gaisa ta shige ciki bata ƙara Fitowa ba sai da Labiba ta kira shi ta ce ta dawo. Yana shiga suna haɗa ido da ita ta yi murmushi ta ce. "Sarakan en Zuciya Allah ya yi ka sauko?" Ɗan sosa bayan kansa ya yi yana murmushi ya ce. "Hajiya Labiba, Ziza ce idan ba haukace mata na yi ba ba za ta barni na zauna lafiya ba. Ki duba fa tun da na tafi nake ta kiranta amma taƙi ta yi magana da ni, sai dai ta ba wa Abeer Waya idan na gaji na kashe. Yau ma tana gani nan na dawo ko dai ta ɗago idonta koda da munafurci ne ta ce min na dawo lafiya. To tunda har ba bakin Uwa ne da ni ba ai dole na yi mata kishiya koda ko za ta mutu..." "Innalillahi! Emraan wai kana cikin hayyacinka kuwa? Ƙarin aure hauka ne aka faɗa maka....kaga..! Kabi a hankali! Kabi a hankali wallahy kada ka je kallon ruwa kwaɗo ya maka ƙafa. Ka natsar da zuciyarka ka tsaya ka rarrashi matarka ku shirya tukun. Ƙwarya ƙwarya ce amma kuma kowacce da gurbinta. A iya zamanka da Ziza ba ta da wata matsala idan ba wannan makahon kishin ba, kuma son ka take,shiyasa take duk wannan...." "Saboda tana So na sai ta hanani son wata, nima ai ina son ta..." "Kishi fa gaskiya ne Lieutenant Emraan! Sai dai na wata yafi na wata, wata na hankali take wata kuma na hauka ta ke yi. Kuma mafi yawa suna nan zaune tare da mazajensu ana ta gurgurawa. Misali....Idan ka dubi Hajiya Marwa ,gata nan ai kishiyata ce. Tunda nake tare da ita tunda Barrister ya auro ni ko sau ɗaya bata taɓa jin tana sona ba, da ni da duk wani wanda zai fito daga waje na bata son sa, ta faɗamin haka ya fi cikon carbi. Sannan babu tashin hankalin da ba ta yiwa Barrister, amma bai taɓa sakinta ba wai don saboda ni, dalili...a tare na iskosu. Ina alfahari da mijina, domin yana kamantawa Emraan, yana iya ƙoƙarinsa wurin kamanta adalci a tsakaninmu da kuma haƙuri damu. To ina so kai ma ka koyi amfani da tracks ɗinsa, In Sha Allahu za ka yi nasara. Ka lallaɓa ta, ka kwantar mata da hankali, na san da ace bamu tattauna wasu maganganun da ita ba da yanzu abin da za ta yi maka sai yafi haka muni. Ba don ba'a son uwayen gida ko sun gaza ba ne ake ƙara musu abokan zama, aure zuwa yake. Ka lallasheta ku kai ƙarshen wannan. Idan har wani abu ya ƙara tasowa makamancin wannan kuma na bincika kai ne baka da gaskiya, to magana ta Allah zan haɗaka da Daddy, Baba Ustaz da su Kawu Ɗan Ladi...idan ya so sai su hana ka auren in ga yanda za ka yi." Wani murmushi ne ya suɓuce masa tare da girgiza kansa ya ce. " Ki yi haƙuri. In Sha Allahu za'a gyara ranki ya daɗe." "Ai kai ne ranka ya daɗe, Allah sabbinane, mai laifi kuma ya yi fushi." Nan dai suka ƙara taɓa fira sannan ya tashi ya tafi gida. ******* Alarm ɗinda ya buga shi ne abin da ya tasheni yasa na motsa a hankali domin miƙa hannu na daƙilesa kasancewar bana jin zan iya tashi a yanxu. Jina kamar a cikin jikin mutum yasani saurin buɗe idanuwana a razane ina mai neman ƙwallara ihu. "Shihh! Bibi! ni ne mana. Cikin dare na iso, kuma kina bacci, shiyasa na yi wanka na kwanta..." A zabure na miƙe zaune ina ƙara murza idanuna domin ji nake kamar kunnuwa gizau suke min ba gaskiya ba ne kawai dai kewar sa yasa zuciyata da ƙwaƙwalwata jin cewa kamar shi ne a kusa dani... "Ke ni ne fa. Taɓani ki ji.." Ya faɗa yana mai kamo duka hannayena ya ɗora su akan fuskarsa yana mini murmushi. "Wallahy kuwa kai ɗin ne da gaske...to amma miyasa ka dawowa kamar ana korar ka?" "Saboda na riga na gama ganin duk wanda ya kamata ace na gani..." Jinjina kai na na yi ina ta wani irin murmushin farin cikin ganin sa, lokaci ɗaya na ji na nemi baccinda na ke jin yana ƙoƙarin danneni na rasa. "Are you Happy?" Cikin jikinsa na koma na kwanta ina dariya na ce. "Sosai ma kuwa. Welcome!" Shiryawa ya yi ya fita masallaci nima na yi wanka sannan na yo alwala na zo nayi sallah bayan ya dawo ne muka koma muka kwanta na ce. "Good morning!" "Did you miss me?" Dariya na yi kawai ina jinjina masa kaina alamar eh. "Kamar ya kenan?" "Kamar dai haka....Kamar haka...Kamar kuma haka." Na faɗa ina mai kissing gefen wuyansa har zuwa fuskarsa kamar yanda yake min... "Iyyehh! Ki ce an ƙara sabon course bana kusa..." Dariya na yi ina faɗin. "Yau za ka fita wurin aiki ne?" "eh, zan fita yau. Gobe sai na tsaya mu yi shirin tafiya, jibi sai mu wuce." "Uhm." "Allah ya nuna mana." "Amin." Ƙarfe takwas na rakashi ya tafi na dawo gidan wanda ni tun a yau ma na fara shirina, ji nake kamar na buɗe idanuwana na ganni a gaban Ammie haka nake ji. Washe gari muna ɗaki ina zaɓa mana kaya wanda a wannan karon ni na ce zan haɗa kayan tafiyar kawai ya zauna ya yi kallo. Ina cikin aikin yana zaune shima yana aikin da ya saba aka kira shi akace mun yi baƙi. Da mamaki muka fito domin ganin su waye waɗannan. Jadda, Suhaib da kuma Taimiyya, su ne muka gani. Cikin tsananin farin ciki na je da gudu na rungume Jadda ina mata sannu da zuwa, bayan mun gama gaisawa ne, na tashi na je Kitchen wurin Madam Amima na sa suka shirya musu abinci nan take na ji da gani sannan na shiga ciki tare da Taimiyya domin na basu wuri su gana naga kamar Jadda na buƙatar hakan. Bai gama farfaɗowa da mamakin ganinta ba ta kalle shi tana murmushi ta ce. "Beenafah mutuniyar kirki ce Hammodi! Ina alfahari da ita." Murmushi ya yi tare da jinjina kansa ya ce. "Haka take. Ba ta da matsala." "Na gani. Kuma In Sha Allahu za su zauna lafiya da Noura..." Cikin zallar mamaki ya kalle ta ya ce. "Jadda! Ina tunanin ai an kai ƙarshen wannan maganar domin ita kanta ba ta da ra'ayi." "Waye ya faɗa maka?" "Jadda ita fa yanzu tana da right ɗin zaɓarwa kanta miji. Dan Allah kada ku tilasta ta..." "Hammodi...Noura har yanzu ita ɗin yarinya ce. Tana da ikon zaɓarwa kanta miji na yarda da wannan, to amma idan iyayenta suka ga wani zaɓin da ya dace da rayuwarta shi ma ɗin ba laifi ba ne. Da farko ta yi kuskure...shi ne ma abun da ya taso na ji ba zan iya jira har sai ka zo ba, na zo da kai na. Saboda haka a yanzu ita da iyayenta sun amince muma haka..." Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!!! Abin da ya furta kenan a ransa yana mai jin duniyar na wani irin kewayawa da shi, tamkar zai kifa haka yake ji. Jin alamun kamar tahowar ta yasa ya yi saurin ɗaga mata Hannu ya ce. " Dan Allah Jadda mu bar wannan maganar a yanzu. Beenafah bata san da wannan zancen ba har yanzu.." "To ka faɗa mata mana! Idan kuma ba za ka iya ba ni sai na faɗa mata...kana ji ko? Gwanda ka sanar mata tun wuri domin ka sauke wannan nauyin a kanka, kada sai lokaci ya ƙure taga cewar kamar ba'a yi mata adalci ba." Da sauri ya girgiza kansa ya ce. "A a dan Allah! Ki bari I will find the right time ɗinda ya kamata na faɗa mata idan ma akwai buƙatar haka." Ƙara kwantar da murya ta yi ta ce. "Hammodi,... Za ka ɗauki duk wannan a matsayin takurawa, amma watarana sai ka gode mini In Sha Allahu. Su a yanzu sun riga sun amsa, kai ne ake jira daga ɓangarenka..." "Idan na amsa na ce sai nan gaba....shin za ku iya jira?" Cikin farin ciki ta ce. "Nan gaba? Kamar yaushe kenan?" Girgiza kansa ya yi kai tsaye ya ce. "Ban sani ba, amma dai idan na gama yankewa zan sanar." "To ba laifi...amma dai kamar zai fi idan akayi Lokaci ɗaya. Sannan ko akan Beenafah da Noura ina ga gwanda a yi tun yanzu domin a samu su haɗe kansu komai ya tafi daidai,hakan zai yi matuƙar faranta maka ranka.kaga ga auren Su Suwara...ana ma iya yin sa lokaci ɗaya.." "Uhm! Nan da wata uku? Hakan ba zai samu ba Jadda, magana ta gaskiya. Bana son na ɗauki alƙawarin da ba zan iya cikawa ba, amma ba zan aure ta nan da wata uku ba, ba zan yi alƙawarin wannan ba." Shiru tayi tana kallon sa na ɗan lokaci sannan daga ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya ta ce. "Haba Hammodi!! Shin idan aka haɗa auren nan lokaci ɗaya bai fi ba? Kaga za'a sauƙaƙawa mutane wahala, sannan Kaga a lokacin kowa yana nan, amma idan akayi auren su Suhaib ba lallai wasu su dawo daga baya ba domin mun jima bamu aurar ba. Dan Allah ka bari ayi shi lokaci ɗaya komai sai yafi tafiya daidai..." Cikin jin wani dan irin ɗaci a ransa ya girgiza kai tamkar zai fashe da kuka Ya ce. "Jadda zan yi nazari a kai.." "A'a, ba fa wani nazarin da za ka tsaya yi Hammodi, ka je kawai ka fara shiri. Allah ya sanya alheri da albarka yasa ace gwamma da akayi.." Daƙyar ya yi nasarar jinjina mata kansa amma wallahy ba don yasan abin da yake masa daɗi ba. Babu abinda yake masa yawo a kai da zuciyar sa sai maganganunsa da Engineer Ubaid. Shawararsa da ya bi babu abin da ta ƙara masa sai cakwakiya. Shiru ya yi tare da zuba ido yana kallonta yana mamaki da irin yanda take ta wani farin ciki kamar ba ita ba. Tunaninsa da damuwar sa miyasa za ta dage akan dole sai ya Auri Noura a irin wannan lokacin alhali matarsa bata ragesa da komai ba. An ya akwai adalci kuwa? Idan Beenafah ta zo tasan wannan bi ta da ƙullin da suke mata mi zai faru daga baya? Shi fa farin cikin matar sa yafiye masa komai a duniyar nan. Bayan sun gama tattaunawa ya kirani na fito ina murmushi na miƙa mata waya na ce. "Jadda ga Ammie na za ta miki barka da zuwa." Karɓa ta yi suka gaisa wanda a nan ne nake jin cewa wai gobe za ta koma. Suna kambalawa na karyarda wuya ina kallonta na ce. "Ni dai gaskiya ba za ki tafi gobe ba.." Dariya ta yi ta ce. "Haba Beenafah! Kwana ɗaya ai dai mun ga juna, uzuri ne dama ya kawo ni kuma na kambala, sannan gashi kuma gobe zaku tafi..." "To ai ko yanzu akwai kwana biyar kafin fara aikin nasa, kawai dai muna so mu isa da wuri ne.." "Beenaf..!" Hannu na ɗaga ina dariya na ce. "Jadda bafa zan yarda ba sai kin mana kwana biyu. Na gama magana, indan akan tsohon mijin ki kike son ki tafi ki bari ni zan kira sa na lallasar masa zuciyar sa....ta shi mu shiga ciki." Na ƙarashe maganar ina mai riƙe ta hannun ta muka tashi a tare. Kallon sa na yi tare da yi masa magana da ido alamar miye ya faru da ya ke ta kallona haka? Murmushi ya yi tare da lumshe idanunsa a hankali ya buɗe yana mai girgiza mini kansa alamar ba komai. Haka muka yi kwana biyu cike da farin ciki, duk abin da take so dama wanda bata ce ba jiki na rawa nake yi mata shi har muka rabu cike da kewa ina mai yi mata lissafin watannin da suka rage na sake dawowa Sudan. Bayan sun tafi washe gari muka shirya sai Kaduna. Tun da muka sauka kwana ɗaya muka yi ya fara aikinda ya kai sa ba dare ba rana wanda sai da muka yi sati uku cikin na huɗu sannan ya kambala muka yi shirin wucewa Sokoto. Muna zaune a daren da washe gari zamu tafi Sokoto muna cin abincin dare sai ga kiran Ammie. Ina ɗagawa lokaci ɗaya ƙirjina ya buga jin muryar Bahrain cikin wani irin yanayin da ko bai furta ba nasan akwai wata damuwa. Cikin gigita na yasar da spoon ɗin hannuna na ce. "Bahrain! Ina Ammie.?lafiya? Miye ya faru da ita?" Kukan da yake riƙewa ne ya kubce masa yana faɗin. "Aunty Beena...Daddy...Daddyn gidansu Humaida ya rasu.." "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" Na faɗa a gigice tare da miƙewa tsaye na ɗora hannuna a kai ina mai fashewa da kuka... ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* Kuyi sharing, ku yi comment fisabilillahi! Channel ɗinmu na tafe in sha Allahu zamu riƙa yi muku posting gaba ɗaya free books ɗinmu waɗanda babu algus.... *PAGE 48* Ƙarar faɗowar spoon ɗin hannunsa ne na ji ta karaɗe kunnuwana, da gudu ya yo kaina ya tallafoni wanda kaɗan ne ya rage ban kai ƙasa ba, tsabar yanda maganar ta shiga kaina a lokacin da ban tsammata ba. Janyoni ya yi zuwa cikin jikinsa tare da saka hannayensa ya rungumeni yana mai bubbuga bayana a hankali cikin nutsuwa ba tare da ya yi magana ba. Sai da ya ji kukan na wa ya yi ƙasa sosai sannan a hankali ya kawo bakin sa saitin kunnena ya raɗamin cewa. "Ki ce Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!" A hankali na shiga furtawa tamkar wata yarinya ƙarama mai koyon magana na yi ta maimaitawa har sau uku sannan a hankali ya ce. "Miye ya faru?" "Dad.. Ddyy wai ya rasu!" Wayata da ta yi ƙara ne yasa ya janye jikinsa kaɗan ya ɗauko ta, still sunan Ammiena shi ne abin da ya ƙara appearing gaban screen ɗin. Receiving ya yi a hankali tare da ɗosana Wayar a gefen kunnena. "Beenafah.." Murya a ƙasa sosai na ce. "Na'am Ammie." Sosai ta sassauta murya ta ce. "Ki bar zancen Bahrain kin ji ko? Ta wayar Dr. Ne aka kira ya ji muna magana bai ji da kyau ba ne shi ne ya ɗauki waya ya kiraki ba tare da mun sani ba..." "Bai rasu ba kenan Ammie?" "Bai rasu ba, yana dai gadon asibiti." Bansan lokacin da na sauke wata irin sassanyar ajiyar zuciya ba ina mai saka hannu na kashe wayar sannan na ɗago idanuna na kallesa a hankali na ce. "Ka ji wai ba rasuwa ya yi ba." Jinjina kansa ya yi ya ce. "OK..Allah Ubangiji ya bashi lafiya." A sanyaye na ce. "Amin ya Allah." Har muka shiga bacci na kasa daina mamakin kaina wai don ance Daddy ya rasu na gigice ina ta uban kuka wanda a can baya ni ɗin nan babu abin da nake masa a koda yaushe idan ba mummunan fata ba, akan girman zaluncin da ya mana. Amma wai yau ni ce nake ta kukan rashinsa. Washe gari da wuri muka shirya, sai da muka biya wani Company a tare ya shiga ya ɓata

Chapter 47 of 67