"Labiba!"
Cike da nutsuwarta ta amsa.
"Na'am Barrister."
"Ina so ki faɗa min miye abin da ya faru a gidan nan har Hajiya Marwa ke kai yara Islamiyya da boko da kanta."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta kai hannunta ta ɗora akan na shi ta fara magana.
"Barrister! Ka san halina sarai. Wallahi ban san abin da ya faru ba. Na dai san ranar na kira ka kana gidanta na faɗa maka cewa munyi late saboda Hajjo bata da lafiya idan tafiya za su yi su tafi idan ya dawo sai ya ajiye su,Idan kuma bai dawo ba ni sai na ajiye su da kaina, to ban san miye ya faru ba."
" Shi kenan. Sai magana ta gaba, amma tashi ki fara saka mini system ɗinnan a caji please..."
"Ok to. Daga nan zan duba yaran can har su shiga bacci, ina dawowa yanzu."
****
Tun da na raka Ammie asibiti na dawo, kullum bana fashin zuwa, kuma idan na tafi sai biyar na yamma nake komawa gida. Hakan sai ya ƙara mana kusanci sosai da Aunty Labiba da kuma yaranta. Mace ce mai matuƙar mutunci da kirki...kai ba ita ba, duk wani wanda zai zo daga gefen ta to da wahala ka ganshi ace ba shi da kirki. Ina jin daɗinta kuma har abada bana danasanin haɗuwata da ita domin ita ɗin ta kasance fitila a cikin rayuwarmu. Sati biyu cikin na uku na share idan na zo sai five nike tafiya sannan Aunty Hajjo ta dawo, bayan ta murmure.
Aunty Labiba ta so na ci gaba da kaiwa ƙarfe biyar na yamma ɗin amma na ƙi amincewa domin duk inda nake Ammie tana cikin tunanina, ko kwanakin baya daurewa ce kawai nake don bani da yanda zan yi amma yanzu tun da Aunty Hajjo ta dawo kawai na ce tayi haƙuri.
Sai dai, a yanzu mun ɗan ƙara sake wa juna ba kamar farko ba, musamman yanzu da Adeel ke yawan saka ni a gaba wurin yin assignment ɗinsa idan ya zo da shi daga makaranta.
Muna kitchen tare da Aunty Hajjo, tun ina shara har na kambala na yi duk goge-gogen da zan yi tana nan maƙale da waya a kunnenta tana magana.
Kallonta na yi na ce.
"Wai Aunty Hajjo da wa kike ta magana haka a waya tun ɗazu?"
Kashe wayar tayi tana dariya ta ce.
"Soyayya nake yi mana."
Ƙureta na yi da kallo bakin gaskiyata na ce.
"Soyayya? Kamar ya kenan?"
Wani kallon uku saura kwata ta yi mini sannan ta ce.
"Ban son renin hankali fa Beenafah."
Murmushi na yi mata ina faɗin.
"To Allah ya baki haƙuri."
Daga haka na wuce na wanke Uniform ɗin su Hanan sannan na fito zuwa gida.
Ina zuwa ƙofar gida na tarar da Yaya Jafaru yana zaune. Gaishe shi na yi ya amsa sannan ya kalleni ya ce.
"Beenafah ko za ki ɗan sammin abincin nan ne, wallahi ina jin yunwa."
Da murmushina na ce.
"Ƙwarai kuwa Yaya Jafaru mi zai hana. Bari yanzu na shiga na ɗebo maka, jirani kaɗan."
Koda na fito daga gida na tarar Yaya Jafarun ya ci kwalar abokinsa da na tarar da su zaune a tare kafin na shiga gida mutane sun taru da yawa sai faman rabasu ake. Gefe na ja na tsaya ina jiyo duk abin da ke faruwa wai ashe akanmu ne Yaya Jafaru yake faɗa.
Ina nan tsaye a gefe har aka ci aka suɗe, mutane suka watse sannan na zo inda yake zaune na ajiye masa abincin na juya bance masa komai ba na shige gida.
****
Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare.
Daddy ne zaune a gefen gadonsa yayin da Mummy ke tsaye tana shiryarwa cikin kayan baccin ta.
"Hajiya ke fa nake jira ina so zamuyi magana."
Ɗan ƙara gaggautawa ta yi ta kambala sannan ta zo dab da shi ta zauna tana faɗin.
"Alhaji Allah dai yasa lafiya?"
Jinjina kai ya yi ya ce.
"Lafiya ƙalau, magana ce akan Aysha..."
Lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɓace, cikin kaushi ta ce.
"Miye ya faru?"
Ƙara sassauta muryarsa ya yi sosai ya ce.
"Hajiya Zaliha! Dole lokaci ya yi da ya kamata ki saurareni. Na sani cewa Aysha ta aikata kuskure, kuma na ɗauke shi cikin rashin wayau da kuma sharrin shaiɗan. Saboda haka ki yi haƙuri ki yafe mata...."
"Haba Alhaji! Ayshar ce ba ta da wayau? Shekara ashirin da bakwai a duniya! Ɗauke da igiyoyin aure a kanta! ta haihu tasan zafin haihuwa sannan ka ce mini rashin wayau...komai rashin wayaunta ai ta san cewa ni ce mahaifiyarta kuma ko mahaukaci yasan uwar sa...Ni Aysha za ta nunawa karenta ya kai tsaiko!..."
"Duk na ji Hajiya Zaliha, ki yi haƙuri..Allah ma muna masa laifi kuma ya yafe mana ballantana tsananinmu mu 'ƴan Adam. Ki yi haƙuri ai ta riga ta gane kuskuren ta sai dai a haƙi gaba,kuma In Sha Allahu ba za ta sake ba. Ke fa mahaifiyarta ce ba ta da wata uwa a duniyar nan bayan yake, wannan hukuncin ya isa haka, ina so daga yau ki janye furucinki itama ta dawo cikin sauran en uwanta taci gaba da mu'amala da su da kuma mu, ki bar komai ya wuce."
Ta ɗauki tsawon lokaci tana nazari sannan daga ƙarshe ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
" Shikenan! Allah ya yafe mana baki ɗaya."
"Ameeeen! Uwargidan Mudassir Wazeer. Na gode miki, Allah ya ƙara bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali."
"Amin. Ina so zan kwanta."
Ta faɗa tana wani yatsina fuska tamkar wadda taga kashi.
Ɗan janyewa ya yi kaɗan shi kuma yana faɗin.
"Ba matsala, yi kwanciyarki ki huta. Allah ya tashemu lafiya."
Tashi ya yi ya rage mata hasken fitilar ɗakin sannan ya fice ya kira en biyu suka fito parlour suka samesa.
"Daddy lafiya?"
Cewar Hassana tana mai samun wuri ta zauna ido cike da bacci.
Shi kuma cikin farin ciki ya ce.
"Albishir na zo na muku; Mummynku ta yafe wa Auntynku yanzu za ta iya tahowa gida..."
Wani Uban Ihu Husaina ta buga tana laƙe daddy cike da farin ciki ta ce.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah! Alhamdulillah! Yah Allah. Thank you so much Daddy, ubangiji Allah ya ƙara girma, Allah ya ƙarawa wannan family namu zaman lafiya mai ɗorewa da ci gaban rayuwa."
"Amin Yah Allah. Yanzu kam kuka ya ƙare ko?"
Murmushi ta yi tana mai gyaɗa masa kanta. A ranta kuma, addu'a take 'Allah yanda ya juya al'amarin dake tsakanin Mummy da Aunty Aysha a dare ɗaya, to ko yanzu al'amarin Su Beenafah tana addu'a Allah ya canza zuciyoyin iyayenta yasa su gane gaskiya su dawo da su cikinsu su ci gaba da rayuwa kamar yanda suke a baya'
Tsintar Muryar Hassana suka yi wacce ta ɗauki hanyar komawa ɗakin su tana faɗin.
"Ni dai bacci nake ji, sai dai da safe idan na fito.."
Kallon Husaina Daddy ya yi ya ce.
"To kema ki je ki kwanta ki bar shi sai gobe..."
Cikin sauri ta girgiza kanta tare da duba agogon wayar ta ta ce.
"A'a Daddy! Ba zan iya jira ba,....A wannan yanayin, tazarar hour ɗaya ce tsakaninmu da London kamar yanda Aunty Ayshar ta faɗa mini, saboda haka yanzu muna ƙarfe goma sha biyu saura na dare, kenan su a wurin su ƙarfe ɗaya ne saura, amma gaskiya ba zan iya jira ba dole na kira ta a yanzu na sanar mata."
Girgiza kan shi ya yi yana murmushi kawai ya juya ya koma ciki.
Ringing ɗaya zuwa na biyu ta ji muryar Ayshar ta ɗaga, sauti can ƙasa sosai ta ce.
" Hussy, lafiya kuwa? Ko wani abin ne ya sake faruwa?"
Cike da farin ciki ta ce.
" Aunty Aysha you freed congratulations!"
Daram! Haka ta ji ƙirjinta ya buga, da sauri ta ce.
"Are you serious?"
"Yes... Yes.. Aunty Aysha, wallahi da gaske nake miki. Mummy ta yafe miki, tace you can come home anytime you want. And za ki iya magana da duk wanda kike so a cikinmu"
Wa su hawayen farin ciki ta ji sun wanke mata fuska lokaci ɗaya ta shiga furta kalaman godiya zuwa ga Ubangiji mai girma.
"Hussy!"
"Na'am Aunty Aysha."
"Miye kike so? Faɗa mini duk duniyar nan miye abin da kike so?"
Cikin jin wa su zafafan hawaye ta girgiza kanta tamkar tana a gabanta ta ce.
"Ba komai Aunty...abin da yake raina ba za ki iya cika mini shi ba, sai dai ina so ki tayani da addu'a Allah ya cika mini burina."
"Amin..Hussy, In Sha Allah zan tayaki da addu'a har burin naki ya cika, kuma ko ya cika Hussy Addu'a ta tana tare daku har ƙarshen rayuwata.."
"Na gode Aunty Aysha... Ina Baffa?"
"Baffa ya yi bacci, ya lectures?"
"Alhamdulillah! Lectures tana nan ana ta yinta da zafinta..amma gaskiya yanzu mun fi jin sauƙi saboda muna gida ba kamar da muke hostel ba..."
Nan suka ɓata dare suna fira sai kusan uku na daren agogon Nigeria sannan suka yi sallama.
****
Yau tun asuba Bahrain ya masifeni akan dole sai na bi ta school ɗin su na rakashi mun yi magana da malamin su dake son ganina.
Shiyasa na yi saurin kambala duk abin da nake ƙarfe bakwai da rabi muka fito muka je, daman daga school ɗin su zuwa gida bamu da wani nisa sosai. Faɗa mini suka yi wai ana aika mana taron iyayen yara amma bamu taɓa halarta ba shiyasa akace sai ya zo da maga'isan sa,dalilin kiran shi ne wai, bayan sallar azumi dake gabatowa idan Allah ya kaimu Bahrain zai yi walima tare da sauran en makarantar su, saboda haka akwai kuɗaɗen da zamu biya idan lokaci yayi, daman nasan ya yi hizib kusan hamsin da uku. Sai kuma kuɗin exam ɗin ƙare primary school zuwa Jss one da kuma kuɗin graduation.
Godiya na yi musu cikin tsantsar farin ciki na ce musu in sha Allah zamu biya komai da komai kafin lokaci ya yi. Daga nan nayi musu godiya na fito na nufi gidan Aunty Labiba.
Ina kan hanya na ci karo da Yaya Jafaru wanda ba zan ce ga daga inda ya fito ba.
Da murmushi ya tarbeni cike da nutsuwarsa ya ce.
"Beenafah! An tashi lafiya?"
"Lafiya lau Yaya Jafaru ina kwana."
"Lafiya lau, sai ina haka?"
"Gidan aikina zan tafi."
"Allah sarki! Nima na dawo daga raka Farisa makaranta ne."
Shiru muka yi na ɗan lokaci, sannan daga ƙarshe ya ce.
"Muje na raka ki mana."
Da sauri na girgiza kaina na ce.
"A'a Yaya Jafaru ka bar shi nagode."
"Ranar sai kika ji muna ta darga da Shahid, bai da kirki ko kaɗan, idan ba shi ba ina ruwansa da rayuwarku.."
Murmushi na yi na ce.
"Ba komai Yaya Jafaru kada ma wannan ya dame ka. Daman idan ba'a yi da kai ai ba kowa kake ba. Sai an jima."
"To ya yi, Allah ya tsare sai kin dawo."
Ina zuwa gidan yau na tarar da wani mutum zaune parlourn na Aunty Labiba. Duƙawa na yi har ƙasa na ce.
"Ina kwana."
Dauke kansa yayi daga kallon wayar da yake ya ƙare mini kallo tsaf sannan ya amsa gaisuwar da na masa sai kuma ya sake cewa.
"Wace ce ke?"
Ƙara saukar da Idanuna na yi na ce.
"Ni mai aikin Aunty Labiba ce..."
Cike da zallar nuna mamaki a maganar ya maimaita ya ce.
"Mai aiki?"
✍️ *OUM-AMEER* ✍️
*GANIN IDO* 🥀🥀
*ADABI WRITER'S ASSOCIATION*
*AMEENA IBRAHIM*
*OUM-AMEER*
*Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa*
*FREE-BOOK*
*PAGE 13*
Muryar Aunty Labiba na ji tana shigowa parlourn tare da su Hanan shirye cikin uniform ɗin su na Islamiyya ta ce.
"Barrister Beenafah ce fa. Mai aikina wacce Adeel ke yawan yin maganarta."
"Oh! Allah sarki. Wannan ita ce Beenafah? Da yake kin san ban taɓa ganin ta ba sai yau.... Sannunki."
Faɗowa Hanan ta yi jikina cike da jin tsagwaron rigimarta da ta saba tace.
"Aunty Beenafah ta shi muje makarantarmu..."
Miƙewa na yi da sauri na nufi ciki janye da hannunta,muna shiga na rungumeta ina shaƙar daddaɗan ƙamshinta na ce.
"Wow...My Hanan! ƙamshinki mai daɗi, uniform wankakku kuma gashi an goge su sun yi kyau, yau kin yi kyau kin ji ko tawan....amma kema kin san cewa ba zan iya zuwa makarantarku ba dan Allah kada ki ci gaba da rigima, ki je makarantarki kin ji ko?"
"To za ki tsaya har na dawo?"
"Sosai ma. Yi maza driver yana jira kar ki yi latti."
Daga haka ta fice tana mini bye-bye yayin da ta bar Adeel nan tsaye yana mai bina da kallo wanda da alama akwai abin da yake so ya tambayeni ko ya faɗa mini.
"Aunty Beenafah amma dai kin taɓa yin makaranta?"
Dariya ce ta suɓuce mini ba tare da na shirya ba sannan na gyaɗa masa kaina na ce.
"Eh, na taɓa yi mana..."
"Aji nawa kike to?"
"Kamar ajin da kake yanzu."
"J.s one kenan?"
"Eh."
"Wace school to?"
"Ban sani ba.."
Ɗan Jim ya yi kaɗan jin amsar da na bashi wanda a zatona zai sa kai ya wuce ne amma sai naji ya sake yi mini wata tambayar da cewa.
"Aunty Beenafah kinga karatun da kika koya mini ranar? Wallahi Uncle Daniel ya ce na iya sosai haka ma a islamiyya kullum yanzu ina cikin waɗanda suke saurin iya karatu saboda kina duba min"
Ina kan cire hijabina kawai na ce.
"To ka ji daɗi..."
"To ke Aunty Beenafah duk ya akayi kika iya komai da komai?"
"Ta hanyar koya mana, kamar kai yanda ka ke yi."
"To ta ya ya?"
Hannayena na saka na riƙe ƙuguna ina kallon sa na ce.
"Ban sani ba Adeel! Ban sani ba na ce. Ka wuce kada ka yi latti."
Na ƙarashe maganar ina mai yi masa nuni da ƙofa.
"Allah baki haƙuri."
Banza na yi masa tare da yin gaba na bar shi a nan. Zuwa gobe bai hana idan muka sake haɗuwa ya ci gaba da damuna da tambayoyin da har zai kai ga ƙureni.
A kitchen na samu Aunty Hajjo na gaisheta sannan na tambayeta na ce.
" Ashe Aunty Hajjo Babansu Adeel a gidannan yake yau? Lissafina ya ɓace wallahi. Allah yasa kada Aunty ta ji haushin cewa na karya mata doka."
Girgiza kanta ta yi ta ce.
"A'a, ba a nan yake ba, ina ga tafiya Maman Tima tayi shiyasa yake nan...Ɗauki ga kaya can ki wanke in ji Aunty Labiba."
Ɗauka na yi naje na wanke mata na dawo da su sannan na wuce wurin aikina.
****
Aysha kuwa, Tun da Husaina ta kira ta, ba su ƙara cikakken wata ɗaya a birnin London ba. Daman faɗuwa ce ta zo dai-dai da zama domin auren ƙanwar Ahlan Firdausi saura kwanaki kaɗan wanda bayan auren iyaka sati biyu zuwa uku azumi.
A Abuja suka sauka kamar yan da ta nemeshi alfarma domin a Sokoto ainahin gidan auren su yake sannan shi Ahlan ɗin ɗan Sokoto ne har iyayensa a can suke zaune. Shi ne ta roƙi alfarma akan ya bari su fara sauka nan in yaso daga baya sai ta taho idan bikin ya tashi.
Sanin irin wahala da ƙuncin da ta shiga sai bai yi yunƙurin hana ta ba, sai dai kuma yace mata ba zai je gidan na su ba a yanzu, sai idan sun tashi komawa zai zo ya gaishe su.
Abin da Mummy ta yi har yau ya kasa mantawa, shiyasa yanzu ya ɗauki hanyar yin baya-baya da Ita kada shima laifin Ayshar ya shafeshi.
Driver ne ya zo ɗaukarta tare da Humaida da kuma twins.
Tana haɗa ido da su ta wani fashe da kuka da gudu taje ta rungume su. Su ma kukan suke kamar yanda ta ke yi tamkar za ta ɗauke numfashi bama kamar Husaina.
Hannu Humaida ta miƙa ta janyo Baffa tana faɗin.
"Come here my boy...Tun kana baby gashi ka dawo babba"
Mota Hassana ta nufa tana faɗin.
"Please every body should hold his tears please.....ku jira idan muka koma gidan sai ku ci gaba."
Motar suka nufa ba tare da kowa ya tanka mata ba suka shige sai gida.
Suna shiga gidan jiki na rawa ta faɗa jikin Mummy Zaliha ta fashe da wani irin kuka tana faɗin.
" Ki yafe mini Mummy...Dan Allah ki yafe mini, I promise you ba zan ƙara yin abin da bakya so ba..."
Taɓe baki tayi still Ayshar na rungume a jikinta ta ce.
"Ah to! Mutum dai ya ga abin da zan iya, ni ba kamar sauran iyaye ba ce, yaro bai isa yace zai takani ba, Ƙaryar sa wallahi, don har yanzu ban haifi wannan ɗan ba, saboda haka sai ki kiyaye na gaba."
"In sha Allah Mummy zan kiyaye."
Zaunawa suka yi a tare sannan ta janyo Baffa a jikinta ta rungume shi tana mi shi murmushi tana faɗin.
"A'ah! Ga mu yau ga mutanen London... Ina Abbanka?"
Cikin jin wani sanyin farin ciki Ayshar ta karɓe zancen da cewa.
"Abban shi ya wuce Sokoto Mummy, sai dai idan ya dawo."
"To Allah ya kai shi lafiya. Shi ma ai Hafiz ya kirani ɗazu ya ce mini in sha Allah satin nan mai zuwa zai dawo ya ganki..."
"Allah sarki! Allah ya dawo da shi lafiya."
"Amin. Ina Salma?"
"Salma tana can na ce Ahlan ya wuce da ita kafin mu zo, ta girma sosai, ina tsoro kada iyayenta su ce za su riƙeta su yi mata aure."
Miƙewa Mummy ta yi tana faɗin.
"To idan sun riƙe ta ba sai ki samo wata ba. Gari da yawa ai maye ba zai ci kansa ba. Ni ɗaukar mai aiki da kuma korarta a wurina tamkar saka riga da cirewa ne...Ku tashi muje mu ci abinci, nasan matafiya na jin yunwa."
Haka suka zauna suna ta cin abinci, faɗar irin farin cikin da Aysha ke ciki ma ɓata baki ne. Duk inda Mummy ta saka ƙafa tana tare da ita a wannan ranar hatta bacci ɗakin Mummy ta yi shi tare da ita, komai ya dawo mata sabo.
****
Haka muka ci gaba da rayuwa komai na tafiyar mana a hankali dai-dai da matsayinmu, wanda shi ne silar farin cikinmu da walwalarmu.
Yau azumi ya rage saura kwana biyu.
Ina kan mopping Aunty Hajjo ta shigo ta miƙo mini leda tana faɗin.
"Ga Kayan Azumina nan da aka kawo mini tare da an gani ana so."
"Kayan Azumi da an gani ana so? Miye hakan yake nufi to Aunty Hajjo?"
Kallon sama da ƙasa ta yi mini kamar dai wa can lokacin sannan ta ce.
"Wai ni kam, shekarunki nawa ne Beenafah?"
Kai tsaye na ce.
"Sha shida nake da kamar."
"To yanzu don Allah so kike ki ce mini baki taɓa gani ko jin kayan see I love ba? Da kayan azumi?"
Bakin gaskiyata na ce.
"Da gaske nake Aunty Hajjo."
Gyaɗa kanta tayi ta ce mini.
"To amma kin san aure ai?"
"Eh, munyi auren Aunty Aysha a lokacin."
"Ok to kamar haka, wanda yake so ya aureni ne ya kawo mini kayan azumi da kuma kayan tsaida shi a matsayin wanda zan aura, an yi mana engagement Kenan, daga haka har mu kai ga yin aure.."
"ohh! Na fahimta yanzu, Allah yasa alheri."
"Amin."
Aikina na je na ci gaba da yi. Bayan na kambala ina shirin zuwa gida sai Aunty Labiba ta dawo, daman yau koda na zo bata nan ta fita aiki.
Bayan mun yi mata sannu da zuwa ta kirani waje ni da Aunty Hajjo ta nuna mana kaya ta ce.
"Ga wannan, kowa ya ɗauka ya kai gida. Ke Beenafah ga naki can kema Hajjo ga wanda za ki ɗauka can..."
Godiya muka yi mata sosai sannan na fita har babban titi na samo mai Napep muka dawo gidan na ɗauka na kai gida cike da jindaɗi.
Da muka duba kayan ashe gero ne tiya goma, shinkafa tiya biyar,sugar tiya ɗaya, dabino tiya ɗaya sai kayan Tea wanda In Sha Allah idan muka lallaɓa zai ɗaukemu har ƙarshen azumi sannan da kuɗi dubu goma.
Cikin nuna zallar farin ciki Ammie ta ce.
"Wallahi Beenafah kar ki ji irin yanda zuciyata ta yi sanyi. Mun gode wa Allah mun gode wa wannan baiwar Allah, Allah ya saka mata da mafificin ya raya mata yaranta ya kuma ƙara mata zaman lafiya da Mijinta."
"Bari Ammie! wallahi ni ma daɗi ya hanani ma yin magana. Aunty Labiba mutum ce,Allah ya saka mata da alheri."
"Aunty Beena ni dai bana son Kunu...in dai kina so in yi azumi duka kamar yanda kika ce to ni ba zan sha Kunu ba."
Dariya muka yi ni da Ammie sannan ta ce.
"Kai dai da kunu kam Bahrain akwai tsatstsaurar gaba sosai.."
"ƙyale shi Ammie, samun wuri ne kawai, can da da bai ga kayan Tea ɗin ba ai dole yasha ko baya so..."
Ammie na dariya ta janyo shi jikinta tana faɗin.
"Haba Beenafah...Autan na wa kike wa haka? Ya fa kusa sauke alƙur'ani ga shi kuma zai ƙare primary ya je Js One... Ko don ƙoƙarin nan da ya nuna da ƙwazo ai kya masa abin da yake so ba tare da ƙorafi ba."
"Haka ne kuma Ammie, amma dai hakan ba shi ne zai sa yace ba zai ci abinda yake gaban sa ba."
Nan muka yi ta fira, muka ci abinci sannan Bahrain ya shirya ya wuce islamiyya.
Bayan na kambala sallar magrib, ina zaune da litattafan Bahrain ina dubawa Ammie ta zo ta tsaya a kaina tsawon lokaci ba tare da ta furta mini komai ba.
" Ammie kin yi shiru kina ta kallona..da wata maganar ne?"
Jinjina kai ta yi ta ce.
"Beenafah, kinga dai tsawon shekarun da muka kwashe ina ta fama da ciwo, a hankali aka yi ta magani, sai ciwo ya yi kamar ya tafi sai kuma ya dawo baya, komai ya lalace mana, duniya ta yi mana ƙunci da zafi, a hankali sai ga shi kuma Allah cikin ikon sa yasa na samu waraka wanda a yanzu in sha Allahu, ina fata da roƙon Ubangiji yasa ƙarshen wahalar da za ki yi dani kenan. To Alhamdulillah! Ga shi cikin ikon Allah abubuwa suna ta sauƙaƙa agaremu ba kamar can baya da muka baro ba a lokacin da kuma bamu tsamma ta ba. To ni shawarata a nan ita ce; Idan Ubangiji ya nuna mana bayan sallah lafiya, ya kamata ki koma islamiyya. Karatun boko ba dole ba ne kuma ba addini bane, abu ne mai kyau wanda yin sa yake da matuƙar amfani idan an samu dama da lokacin yin sa. Amma idan damar hakan bata samu ba, sai a haƙura. Tun da har na samu sauƙi haka, ya kamata ki haƙura da bokon tun da kinga yanda rayuwar ke tafiyar damu, sai ki koma islamiyya, idan kin tafi kin gamo aikinki kin dawo ƙarfe biyu, ki yi duk abin da zaki yi ki gama ƙarfe uku ki wuce wurin neman ilimi, domin shi ne gaba da komai kuma shi ne rayuwa ko ince shi ne abin da aka gina ɗan Adam domin shi."
Cike da jindaɗin maganar da tazo mini da ita na ce.
" In sha Allahu yanda kika ce haka za'a yi Ammie. Allah ya ƙara miki lafiya yasa mu dace."
"Amin."
"To amma kuma Ammie...barinki ke kaɗai wuni ɗaya zungur..."
"Haba! Kar ki damu da wannan, ke da ke barina tun ƙarfe tara ko sha ɗaya na safe kikai ƙarfe biyu ko ma fiye da haka, mi zai sa ki damu don kin fita neman ilmi. Yanzu ga Maman Fakiha a kusa dani, sannan kuma ga Jafaru da Hamza dake yawan shigowa akai-akai sun ɗaukeni Uwa suna kulawa dani, suna yawan shigowa muna fira da su ba ma kamar Jafaru. Saboda haka kar ki damu in sha Allah lafiya za ki riƙa dawowa kina tarar da ni babu abin da zai sameni."
" Shi kenan Ammie, Allah ya nuna mana."
" Amin Yah Allah. Ta shi ki jiƙa mana gero tun da yanzu kada a manta gobe a markaɗo shi da wuri a Tace shi."
****
Unguwar Gwaza,
Gusau, Zamfara State.
Nigeria.
Babban gida ne mai yalwa wanda ke ɗauke da doguwar verandar tare da jerin ɗakuna. A gefen yamma, manyan Bayika ne guda biyu yayin da gefen
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 67