Share this page
"Kai Masha Allahu! Gaskiya na ji daɗi kuwa, Allah yasa alheri da albarka ya bada sa'a." "Amin. Kin san course ɗin kuwa?" Girgiza kaina na yi na ce. "Ni ina zan sani Ya Jafaru idan ba faɗa mini kayi ba." "Karatun zama Lauya zan yi..." "Wayyo Allah Ya Jafaru! kamar dai, irin na Aunty Labiba kenan? Na san itama Barrister ce.." Fuska cike da annuri ya ce. "Ƙwarai kuwa..." "Kai masha Allah. Amma fa Ya Jafaru karatun nan kamar ana kashe kuɗi sosai?" Jinjina kansa ya yi ya ce. "Eh, akwai kashe kuɗi, amma daman akwai Wan Mamanmu Kawu Usman, shi ne wanda ya biya mini lokacinda na yi diploma ta a nan Zacas, to yanzu ma shi ne ya nemo mini wannan admission ɗin kuma shi zai ci gaba da ɗaukar nauyin komai har na kambala kamar yanda yayi mini a baya in sha Allahu." Bansan lokacin da wasu zafafan hawaye suka wanke mini fuskata ba. Kallon shi nake tamkar zan kifa na ce. " Yayan Mama?" " Eh. Shi ne babba a gidan su, daga shi sai ita,mutumin kirki ne duk yaran en uwansa da ba su da ƙarfi matuƙar dai suna son karatu shi ne yake ɗaukar nauyinsu, hatta su Farisa da kika gani idan term ya yi yana turo wani abu yace a haɗa a musu registeration." Jinjina kaina na yi ina share hawayena na ce. " Kenan dangin Uwa idan kana da su suke taimako?" Girgiza kai yayi ya ce. " A'a Beenafah. Kowa yana da haƙƙin taimakawa danginsa, walau dangin uwa ko na uba, kawai ya danganta daga hali da kuma zuciya mai kyau. Itama Mama Ko cikin dangin na ta ai akwai masu hali da yawa amma Kawu Usman shi ne kaɗai mai zuciyar taimakawa..." Hawaye na gudana sosai akan fuskata na ce. "Duk da haka Ya Jafaru, na san tabbas da muna da su muma da ko yayana ba za su juya mana baya ba kamar yanda Daddy ya mana..." "To sun yi muku nisan da ba za ku iya zuwa inda suke ba ne?" Girgiza kai na nayi ina mai jin wani sabon nauyin a ƙirjina na ce. "Bansan ya zance maka ba Ya Jafaru...Mahaukaci shi ne mahaifinta kamar yanda ta faɗa mini, shi ne ya raineta tare da wasu mutane wanda bayan rasuwar sa suma ta neme su ta rasa. A duk lokacinda ta ce mini na daina wahalar da kaina wurin nema mata magani domin Hauka gado tayi.... sai in ji tamkar na haɗiye zuciyata na mutu....Bamu da dangin mahaifiya,babu wani wanda zamu kira namu a gefen mahaifiyarmu...dangin Uba kuma; Daddy ne kawai kuma ya yafe mu...." A hankali kukan da nake riƙewa ya kubce jin wani abu da ya taso ya motsa ciwon da yake kwance a cikin akwatin sirri na ba tare da na shirya ba. Murya kamar zai yi kuka ya ce. " Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Lallai kina da babban Ciwo a zuciyar ki. Haƙiƙa, na ji matuƙar takaici da baƙin cikin da ba zan iya rungumeki a ƙirjina na rarrashi zuciyar ki ba Beenafah, da ace zan iya da na yi domin na nuna miki irin matsayi da girman da kike da shi a zuciyata. Ki yi haƙuri ki share hawayenki, duk inda kuke Allah yana sane daku, kuma ko Daddy bai taimaka muku ba, akwai mutane da dama waɗanda tarayyarku ta domin Allah da su ba za ta bari ku tagayyara ba...." Ni dai har muka ƙarasa ƙofar gida ban sake ce masa kanzil ba, domin firar da muka yi tayi matuƙar sosa mini zuciyata da turani cikin mummunan yanayin da na jima ban shige sa ba. A nan ƙofar gida na karɓi kayana, bayan na gama sai ta kaina, a hankali nayi sallama na shiga gidan.   Koda na shiga na tarar da Bahrain ya dawo daga makaranta yana kwance saman varender da alama zafi yake ji tunda ya kwaso rana. "Oyoyo Aunty Beena ta..." "Bahrain ka dawo?" "Eh na dawo yanzu, sannu da zuwa." "Yauwa, Ina Ammie?" "Ta shiga gidan Maman Fakiha." "ok." Na faɗa ina mai samun wuri na zauna  tare da haɗa kaina da gwiwa na ci gaba da tunanin rayuwa... "Aunty Beenafah an ce yau kowa ya tabbata ya kawo kuɗin Hadisin sa fa, Malam yusuf yace idan baka zo da kuɗin ba ba zai barka ka shiga ajinsa ba..." Ɗagowa na yi a hankali na ce. "Nawa ne kuɗin?" "Ɗari biyar da hamsin." "Ok, zan baka idan za ka tafi. Ka ci abinci?" Girgiza kansa ya yi ya ce. "A'a, Ammie nake jira." "Tashi ka ɗauko mini wuri na juye abincin sai na zuba maka." Tashi ya yi ya ɗauko na juye, ledoji ne da yawa, wanda har abincin safe akwai da aka rage, abincin rana ma ta zuba mini daban, sannan har da Cake ɗinda mukayi sai da ta sako mini da wasu lemukan kwalba." Da sauri ya tashi ya zuge jakar makarantar sa ya ɗauko empty roba ta Rufaida Yoghurt yaje ya ɗaurayeta ya kawo gabana ya ajiye cike da farin ciki ya ce. " Aunty Beenafah zuba mini Irish da ƙwai ɗin a nan in tafi da shi islamiyya..." Zuruuu! Na yi ina kallon sa har ya dasa aya sannan na ce. "Ina ka samo wannan robar?" Kallon robar da ya ajiye a gabana ya yi sannan ya kalleni ya ce. "Su Ramadan suka zo da ita a ciki muka sha." "To amma miyasa ka ɗauko ta? Bance maka ka daina tsinto tarkace kana zuwa da su gidannan ba? Duk abin da ake baka daga gidanku baka gode ba? Kana fa ganin don kada ka gani ga wasu yaran muke haƙura da wasu abubuwa mu yo maka siyayya, amma kai baka gani ko... " Sunne kai ya yi a ƙasa a hankali cikin taushi ya ce. " Ina gani Aunty Beena, ki yi haƙuri.." Jinjina kaina na yi na ce. " Ya kamata ka gane cewa kai yanxu ba ɗan ƙaramin yaro bane, nan gaba kaɗan ba jimawa zaka shiga secondary, ka riƙa abubuwa na masu hankali bana son rashin dangana...Kaga waɗannan yatsun nawa?" Na ƙarashe maganar ina mai ɗaga masa yatsun hannuna na buɗe su na ci gaba da cewa. " Ka kalle su ka gani,...kai ma kuma ka kalli naka Bahrain...hatta yatsun hannunmu ba tsayin su ɗaya da juna ba, to kamar haka ne, dole a makarantar ku sai ka samu wanda zai zo da abinda baka da shi kamar yanda kai ma kake zuwa da abinda wani bashi da shi. Saboda haka ka riƙa tsayawa ga abinda kake da shi ka dai na sanya ido ga abin wani, kada ka sake ɗauko ko murfin gora ne ka zo da shi gidannan bana so..." Jinjin kansa ya yi jiki sanyaye yace. " In sha Allahu ba zan sake ba ki yi haƙuri. " " Ba komai, tashi ka yi sauri kaci abincin lokaci ya tafi." Bai yi nisa a cin abincin ba Ammie ta yi sallama ta. Bayan na gaisheta ta miƙo mini dubu uku tana faɗin. "Kinga Kuɗi Maman Abul ta zo ɗa zu ta kawo su wai dan Allah ki yi haƙuri idan ma wani laifi ta yi miki kiyi haƙuri, idan ma kuɗin ne kuma ya yi miki kaɗan ga dubu ɗaya ta ƙara miki a sama.." Dariya na yi ina mamakin wautar Maman Abul na ce. "Allah sarki! Wai ita a yanda ta tsammaci abun kenan?..." Itama Ammie dai dariyar ta yi sannan ta ce. "Haka fa ta yi ta roƙona na ce mata ba abinda ta yi miki tsohon gidan aikinki dai kika koma." "To kam a mayar mata da kuɗinta." "Babu yanda ban yi da ita ba akan ta karɓi kuɗinta amma ta rantse tace ba za ta karɓa ba, kuma ko ba za ki dawo ba ita kyauta ta baki." "To,an gode Allah ya saka mata da alheri...bari na tashi na wanke kayan Bahrain don in samu su bushe da wuri. Ga abinci nan, amma kam yayi mana yawa sai dai a rage a kaiwa su Farisa..." "Hmm! Yanzun nan Jafaru ya gama faɗin a ajiye masa abinci yana nan zuwa idan ya dawo zai ci. Shi ma kuma Hamza kin sani a nan zai ci, saboda haka ki rufe ki ajiye." Bayan na kambala sallar Magrib, Bahrain na dawowa daga masallaci na karɓi kuɗin hannun Ammie na ce mata wani magani zan siyo kawai na ja shi muka je can Landmark na siyo Rufaida guda biyu da wani ƙaramin Ice-cream na dubu ɗaya da ɗari biyar wanda ba don kowa na yi hakan ba sai don shi. Ammie za ta buɗe baki ta yi magana, na ce mata dan Allah kada ta ce komai, farin cikin Bahrain shi ne farin cikina.                        ****     Daddy Mudassir..., akwai wani babban abokin shi, Alhaji Mansur Anka wanda yake da 'ya'ya Maza en biyu kamar yanda Daddy yake da su. Kullum roƙonshi guda a wurin Daddy shi ne; Ya amince da su haɗa auren Yaran na su sai abin ya yi armashi. Kullum akan wannan maganar yake wanda sai yau ya samu haƙarsa ta cim ma ruwa, domin sun samu daidaito da shi da Daddy akan yaran za su zo suga juna, idan Allah yasa sun shirya kan su shikenan, amma kuma auren sai sun kambala karatunsu da suke yanzu nan da shekara biyu cikin ta uku. To shi ne bayan ya dawo ya zaunar da Mummy da Aunty Aysha ya yi musu bayani,to shi ne Mummy ta ce ya bata kwana biyu har ta yi shawara, to a cikin kwana biyun ne ta kira Uncle Isma'il ta ce tana so yaje garin Anka ya binciko mata tushen Alhaji Mansur, daga nan ya dawo cikin Gusau ya binciko mata rayuwar shi da ta 'ƴaƴanshi sannan a wanne mataki suke na rayuwa. Da yake Uncle Isma'il ɗin ba na wasa bane, take ya cika mata aiki,wanda Daddy na dawowa kamar yan da ya saba bayan sun gama dinner ta hau yi musu bayani. "Amm! Kamar yanda mukayi da kai Alhaji, zancen yarannan na ce sai na yi shawara, to na amince Yaran su zo su nemesu, idan sun amince fine, idan kuma ba su amince ba to tabbas babu wanda zai musu dole.." Jinjina kai Daddy ya yi ya ce. "To ai nima hakan ita ce matsaya ta, kuma ba za'a yi auren ba sai bayan sun kambala karatun su..." Cike da mamaki Hassana ta kalli Daddy ta ce. "Auren waye Daddy?" "Aurenku ke da er uwarki..." "Amma daddy dan Allah yaushe rabon da irin wannan auren..." Hannu Mummy ta ɗaga mata sannan ta ce. "Ya isa! Ai ya kamata ki jira kiji kafin ki yi saurin yanke hukunci. Alhaji Mansur Anka na san kun san shi, to akwai yaran shi maza waɗanda suma twins ne su biyu, shi ne yake neman alfarma da a haɗa ku aure. Ma su kuɗi ne sosai kamarmu kada ku damu, kuma suna da aikin yin su, wanda suma a waje suke zama da kasuwancin su kamar Mijin Aysha. Amma kuma duk da haka, babu wanda zai muku dole, za su zo in sha Allahu kuga juna, idan kun shirya shi kenan ayi, idan kuma baku shirya ba dole a fasa." Miƙewa Hassana ta yi ta shige ciki kawai ba tare da ta yiwa kowa magana ba, yayin da kuma Husaina ta yi murmushi ta ce. "Ba komai Mummy, Allah ya nuna mana." Jinjina kai Mummy tayi ta ce. "Amin." Miƙewa Aysha ta yi tana faɗin. "To! Mudai kaya kai takalmi hannu, koda bayan mun tafi ne duk abin da aka yanke daga baya zamu ji, Allah ya sanya alheri da albarka ya ba su fahimtar juna..." Kallonta Mummy ta yi ta ce. "Shin wai yaushe ne tafiyar ta ku?" "Next week Friday ya ce mini." "Tau ya yi, Allah ya kaimu." Hannu Daddy ya miƙawa Baffa yana faɗin. "Zo nan Alhajina.... Gobe ya kamata mu fita tare tunda dai za ka gudu ƙasar aro ka barni nan a Nigeria." Ciki Ayshar ta shige ita da Husaina suka bar Mummy nan ita da Daddy suna ci gaba da tattaunawa.             ✍️  *OUM-AMEER*  ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM*      *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *ArewaPen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* *PAGE 19*     "Hussy! Yanzu shi ke nan duk tsawon shekara da na share ga shi har zan koma ba zan sanya su Ammie a idona na ba?....da gaske shi ke nan su Daddy sun bar su a can? Anya Hussy Daddy da Mummy sun yi tunani mai kyau kuwa?" Lokaci ɗaya Husaina ta ji hawaye sun cicciko idanuwanta tana mai girgiza kanta ta ce. "Haka muka baro su yashe a tsakar gida Aunty Aysha. I don't know where they are.....Har na mutu ba zan manta irin rabuwar da na yi dasu ba. They need help Aunty Aysha, but... Haka na baro su ba tare da sanin wata makama b...." Tsit! Suka yi a ɗakin lokaci ɗaya tamkar ruwa sun cinyensu ganin Hassana ta shigo. Ɗan wawwara idanuwa ta yi ta kalle su sannan ta ce. " Why are you mute?.... And dukkan ku you guys looked worried. What's happening?" Ajiyar zuciya Husaina ta sauke tana mai lumshe idanunta ta buɗe tana kallonta ta ce. "Aunty Aysha is leaving tomorrow, and she's afraid kada ki ƙi saurarar wanda su Daddy suka zaɓa miki..." Wayarta ta ajiye a saman haɗaɗɗen gadonta tana mai taɓe baki ta kalli Aunty Ayshar ta ce. "A gaskiya Aunty Aysha su Mummy ba su so gaskiya ba, yanzu ke da za ki Auri Ya Ahlan haɗa ku akayi? Ba haɗaku akayi ba, shi ne ya ganki can yace yana sonki babu wanda ya haɗaku. Kuma wallahi bet me Aunty Aysha, da ace haɗaku akayi da Ya Ahlan da yanzu bakwa zaune lafiya, wata ƙila ma da bakuyi aure ba. Sannan yanzu da ma cewa akayi yaje ta ƙarƙashin ƙasa ya nemi aurena wata ƙila idan akwai rabo zamu iya shirya kanmu... " Murmushi Aunty Aysha ta yi ta ce. " Wannan ɓaragurbin tunani ne Hassy, sam bai kamata ba. A al'amari irin wannan da ake so a ƙulla alheri ya kamata ki riƙa kyautata za to. Ki bashi dama ku haɗu, ki buɗe zuciyarki ki daure ki bashi matsuguni koda kaɗan ne.." "Tau ya yi Aunty Aysha, I will try in gani Ko zan iya." Miƙewa Aunty Ayshar ta yi ta shige wurin wanka ta bar su nan kowace riƙe da waya a hannunta suna danne-danne.                        ****    A hankali rayuwa ta ci gaba da tafiyar mini a gidan Hajiya Batula Attahiru Araam. Tun da wuri nake isowa nayi aikina na kambala sannan mu dawo ɗakinmu zaman kashe wando, su yi ta fira suna dariya wanda babu abinda yake ɗaga su sai idan an kira su da sunan wani uzuri.   Gida ne mai cikakken 'ƴan ci da walwalar duk wata halitta dake rayuwa a gidan. Idan naga irin abin da su Munira suke yi a gidan ina shan mamaki domin duk yanda nake ganin  'ƴan cin gidan Aunty Labiba to wannan gidan ya fishi 'ƴan ci nesa ba kusa ba, sai dai kuma; abin da na lura da shi shi ne, suna da matuƙar tarbiyya da kiyayewa, domin wurin maza daban wurin mata daban, babu wanda yake zuwa wurin wani idan ba da wani ƙwaƙwƙwaran dalili ba. Duk bayan kwana biyu kwana uku, Haula ta kan je kasuwar tudun wada ita da driver ta amso duk wasu kayan buƙata na cefanen gidan. Itama Munira duk wani aikin da za'a yi wurare da dama ita ake aiki amma kuma babu wanda yake fita ba tare da driver ba. Wani lokacin mu tafi tare da su, wani lokacin kuma su tafi abin su. Su Munira duk da cewa suma ɗin ba sa'annina ba ne,amma ba su damu da ƙarantata ba, domin sun fi sakin jiki dani fiye da Aunty Hajjo. Farkon zuwana gidan ina ganin cewa ai ba wani dogon aiki suke ba, sai da na shigo sati na uku a gidan sannan na fara ganin ayyuka tamkar za su yi ajalinsu, musamman dafe-dafen abinci da kuma saukar baƙi kamar ana wani buki kullum haka gidan yake. A nan na gasgata zancen Aunty Labiba da ta ce gidan su gidan mutane ne. Ko en uwan su kawai da suke yawan zuwa sun isheka ciwon kai. Aunty Ziza kuwa, duk yanda suka so na sake da ita na kasa, kamar yanda itama kullum abubuwanta a kaina ƙara tsananta suke a duk lokacin da zamuyi ido biyu wanda ban san dalili ba. Yau ma ina cikin goge-goge a parlour kamar yanda na saba sai na ji an zo da gudu an rungumeni gam wanda ba shiri na juyo muka haɗa ido da Adeel. Tamkar wata sauna, haka na rungume shi gam a jikina yayinda idanuwana suka cika da ruwa hawaye. "I miss you Aunty Beenafah." Janyewa na yi ina mai kallon fuskar sa na ce. "Nima nayi kewarku Adeel.... Ina Hanan?" "Hanan tana can ɗakin Aunty Hairiyyah tana kuka..." "Subhanallah! Miye ya same ta?" Dariya ya fara a hankali ya ce. "Ni na yi mata Ƙarya na ce mata Aunty Hairi ta dawo, shi ne taje ɗakin wai nemanta take, da bata ganta ba shi ne take kuka....Zo.. Zo muje ki ganta Aunty Beenafah." Hannuna ya ja muka fito daga parlourn muka ratso wata hanya duk cikin ruffing ɗin muka shige cikin wani katafaren kyakkyawan ɗaki mai ɗauke da kayayyakin burgewa, ga manyan tidy bears nan jejjere, frames ma gasu nan da na real hoto dana zane gwanin burgewa. Sautin muryarsa, ita ta dawo dani daga duniyar kalle-kallen da na lula ya ce. " Kin ganta ko Aunty Beenafah?..ji bakinta na kuka..." Da gudu na yi kanta tare da janyo ta jikina na ce. "Ke...yi shiru my Hanan ƙyale shi sai na yi mishi duka. Buɗe idonki ki gani ga Aunty Beenafah.." Shiru tayi lokaci ɗaya tana mai haɗiye kukan ta tare da waro idonta ta kalleni da kyau sannan daga baya, bayan ta fahimci ni ce sai ta wani ƙanƙameni tana dariya. Nima cike da farin cikin ganin su na rungumeta na ɗan lokaci, sannan daga ƙarshe na miƙe da nufin jan hannunta amma sai ta maƙale kafaɗa cike da shagwaɓa ta ce. "Ni ki goyani.." Dariya na yi na ce. "Yanzu kuwa." Hijabina na cire na goyata tsab, abin da ba za ta samu ba kenan a wurin Hajjo sai dai ni da ta raina, idan tana jin sangartarta. Parlour muka dawo na ci gaba da aikina Adeel na aikinsa na ciwon surutu wanda duk labarin akan abin da ya wuce ne na makarantar sa, islamiyya da boko. Yayin da Hanan ta wani lefe kamar mai bacci. "To ina Aunty Hajjo?" Na tambaye shi ina mai ci gaba da abin da nake. "Aunty Hajjo tana nan, yanzu da ƙanwarta take zuwa suna yin aiki tare..." "Ke!...Miye haka?" Cike da jin mummunar faɗuwar gaba na juyo domin in ga wane ne, sannan da wa yake magana. Sai gashi cikin rashin sa'a mukayi ido biyu da shi yana tsaye yana kallona. Cikin rashin sanin abin da na yi kawai na yi shiru tare da kawar da kaina gefe na ce. "Ina kwana." "Ba ta da lafiya ne? Da za ki wani ɗora ta a baya haka.." Sai yanzu na fahimci zancen sa, ai kuwa within seconds na dire ta ƙasa ina faɗin. "Lafiya ƙalau take..." "Mts! Yanzu yarinya kamar wannan kike ɗorawa a baya salon kawai ki koya mata rayuwar lalaci..." "Uncle Emraan ita ce fa ta ce ta goyata.." Cewar Adeel yana mai nufar inda yake tsaye tare da Hanan ɗin. Wuri ya samu ya zauna ba tare da ya amsa ba. Saman jikin shi Hanan ta haye yayin da Adeel ya zauna a gefen sa tare da riƙo hannun sa ya ce. "Uncle Emraan wannan ita ce fa Aunty Beenafah, wadda ranar koda ka zo gidanmu har ta riga ta tafi." "Ok..." "Kuma ta iya karatu, ita take taimaka mini idan an bani homework..." Da ido Uncle Emraan ɗin ya bishi sannan daga ƙarshe ya ce. "Adeel, ta shi su Aunty Dija sun kira suna so su yi magana da kai." Duk da cewa bana kallon su, murmushi ne ya suɓuce mini domin nasan ya gaji da halin Adeel wanda ni a karan kaina duk na tuno da shi sai naji ina jin kewar sa. Ji na yi ba zan iya ci gaba da aikinda nake ba, domin zaman sa a parlourn ba ƙaramin takurani ya yi ba,duk da cewa ban san zaman da yake ba. Ga shi itama Munira kamar wani haɗin baki daga zuwa kunna turare ɗakin Hajiya shikenan ba ta dawo ba. Har na kusa kai ƙofa na sake jin maganar sa a masarrafar saurarona da cewa. "Ke!" Juyowa na yi zuciyata na wani irin pumping a ɗan tsorace na ce. "Na'am." "Kawo min lemu." Juyawa na yi na fita na shige babban kitchen ɗin inda freezer take. Tsoro ne ya kamani domin ban taɓa zuwa inda take ba da sunan amfani. Hakan yasa na wuce cikin store inda kwalayen lemuka suke na zaro ƙwaya ɗaya na fito na zo na tsaya a gefen sa na ce masa. "Ga shi..." A hankali ya ɗago kansa daga kallon wayar da yake ya kalloni... Sai dai kuma;lokaci ɗaya fuskar sa ta yi wani irin sauya wa tare da nuna zallar ɓacin rai ya ce. "Miye haka? A gidanku haka aka koya miki yanda ake bada lemu... Infact a ina kika ɗauko shi?" Kallon lemun na ƙarayi da kyau sannan na kalle shi na ce. "Daga Store..." Lumshe idanunsa ya yi sannan ya buɗe cike da rigima ya daka mini wata uwar tsawar da sai da na ja baya ba shiri da cewa. "Mts! Get out from here...." Jikina na rawa na ce. "Dan Allah ka yi haƙuri.." "Leave I said!! Stupid girl kawai... Mts!" Fitowa na yi da gudu riƙe kuma da lemun a hannuna na yo wurin da su Munira suke wanda hankali tashe kowa ya shiga tambayata lafiya, har Munira na faɗin. "Aunty Ziza ce Beenafah?" Da sauri na girgiza kaina ina share hawayena da tafin hannuna na ce. "Wannan Mijin na ta ne yace in kawo masa lemu,shi ne naje na ɗauko kuma sai ya fara mini ihu.." Kafin na iyarda rufe baki har Haula ta karɓe lemun da yake hannuna ta taɓa shi, tuni ta wani zare ido tana faɗin. "Na shiga uku! Wannan ai ba'a fridge ba ne... Ina kika ɗauko?" Ina mai tsatstsareta da ido na ce. "A Store ne..." "To a can kika baro masa abin da kika ɗaura lemun akai?" Girgiza kaina na yi na ce. "A'a, a haka na kai masa." Dariya suka fashe da ita wanda har sai da naji na tsargu na ce. "Miye abin dariya a nan?" Tsahirtawa Munira ta yi domin bani amsa ta ce. "Wai Ya Emraan ɗin za ki kaiwa abu a hannu? To bari in faɗa miki, ko Aunty Ziza ta kai mishi abu haka a hannu ƙarshe kenan, wallahi ba zai karɓa ba, kuma ki ma gode Allah bai faffallo miki mari ba.... Imagine! Lemu a store ba'a fridge ba, mutuminda ko sanyin me za'a yi sai ya sha abu mai sanyi...." " Ai ban iya buɗe fridge ɗin ba." "To amma ai akwai wani ta hanyar fitowa, sannan akwai shi a ɗayan parlourn..." Hannuna Haula taja muka koma kitchen ɗin ta nuna mini yanda zan buɗe fridge ɗin ta ɗauko wasu kalolin drinks sun kai uku, sannan ta ɗauko wani silver tray mai kyaun gaske ta ɗora akai, ta ɗauko glass cup guda biyu ta ɗora ta ajiye a gefe, sannan ta sake haɗa wasu lemukan a kan wani babban tray daban da cups sai ta kalleni ta ce. "a duk lokacin da akace ki kawo Lemu ko ruwa, to haka zaki yi, kuma sai ki kwatanta da yawan mutanen, don kada yayi yawa ko kuma yayi kaɗan. Ni zan kai wannan a parlourn baƙi, ke kuma ki ɗauka ki kai masa wannan.." Bansan lokacin da hawaye suka cicciko idona ba, cike da shakku na ce. "Dan Allah ki yi haƙuri wallahi ba zan iya kai masa ba.." Cikin nuna alamun mamaki ta ce. "Saboda me to? Ya Emraan ba shi da matsala Beenafah, ke ce kika ɓata masa rai. ki daina jin tsoron mutane, idan ba haka ba duk wanda ya kwaso sharar sa wallahi akan ki zai zube ta. Musamman yaran danginsun nan masu zuwa, wallahi ba su da kunya, a gidannan an daraja mu amma su idan suka zo wulaƙanci kala-kala. Kwana biyu don hajiya tayi

Chapter 14 of 67