Share this page
cikin Cell ku yanke masa duk hukuncin da ya dace da rayuwarsa mun baku dama.." Jinjina kai Baba ya yi ya ce. "Wallahy ni ma nan na baku dama! Marar mutunci wanda bai san harkar girma ba..." Rai babu daɗi Ammie ta ce. "Kayya! Dan Allah ku saurara Haba..." Kuka Jafarun ya fashe da shi sannan ya ce. "Dan Allah ku yi hakuri, wallahy daga yau har abada ba zan ƙara kallon ma inda take ba..." "Sai fa ka buɗe bakinka ka yi musu bayanin irin cin zarafi da toxarcin da ka bi ta da shi. Bana so wani ya riƙe ni a rai ya yanke min hukunci da cewa saboda ina da kuɗi ina iko na ci zarafin ka. Na fi ƙarfinka ta kowace fuska, waɗanda suka fika komai sun buga dani sun bar ni ballantana kai wanda ko a silifas ɗina ban kawo ka ba. " " Ai zan faɗa musu. Wallahy zan faɗa..." Daga nan ya zayyane musu duk irin yanda ya yi ta bibiyata da irin nasarar da ya samu ta haɗamu husuma da kuma bibiyata da ya riƙa yi a waya, har zuwa wurin bokan sa bai rage komai ba. Kuka sosai Mama take tana faɗin. " Allah ya isa tsakaninmu da kai Jafaru! Allah ya wadaran rayuwarka. Abin da kake yi kenan ashe bayan duk nasiha da jan kunnen da na yi maka. Mi kake da shi mi kuka kake taƙama da shi da har ka sanya kanka a cikin wannan masifar ka nemi rabata da gidan auren ta? Ashiru ma da ya fi ka sanin zafin ta ya turo neman aurenta Allah ne bai yi ba, sannan yana da sana'arsa yana da madogararsa, ya haƙura da ita ya yi mata fatan alheri ballantana kai...maimakon ka ɗauki maganar iyayenka ka haƙura ka je ka yi karatu ko don gobenka, shi ne kaje ka lalata karatun ka cinye kuɗin registeration har sau biyu, kana ɗaukar kuɗin kana kai wa wani ƙaton boka ƙaton mushriki saboda shafewar basira. Allah ya isa ban yafe maka ba duniya da lahira, ka je tunda ban isa da kai ba shi ke nan. Zumuncinmu kuma tunda ba kai ne ka haɗa ba, wallahy ba ka isa ka raba mana shi ba." Daga haka ta miƙe daga kan bench ɗinda take zaune ta yi tafiyarta. Duk kiran da Ammie ke mata bata tsaya ta waiwaye ta ba. Itama Ammien jiki a sanyaye ta kalle shi ta ce. " Jafaru ba ka kyauta ba. 'ƴar tawa ka ke ta bibiya ashe kana bin ta da sharri? Yanxu kai ba ka ji kunya ba? Da ace Fakiha ce ko Farisa wani ya dinga mata haka ya za ka ji a ranka?" Ajiyar zuciya Ya Mohaa ya sauke sannan ya ce. "Ku zama shaida...dukkanku ku zama shaida..idan har ya sake bin koda inuwar inda matata ta taɓa, to lallai ba zan tsaya tunani na biyu ba a kansa." Daga haka ya ja hannuna muka fice wanda a lokacin har an fara kiran sallar Magrib. Gidan Hajiyarsa muka wuce inda sai da muka shiga bakin Main door ya ce na yi musu sallama domin gobe zamu tafi, kuma asuba zamu yi. Ina jin haka na ce masa Allah ya kaimu rai da lafiya. A raina kuma nace ni dai Jafaru ka ja mini salalan tsiya, bukin Fakiha da Ya Ashiru da nake buri da saka ran a ɗan jira na yau ka gwanɓale mini shi. Ina shiga muka gaisa ya fita masallaci ni kuma na tsaya nan inda Hajiya wacce ta cika da farin ciki ganin Abeer da Mima suna yi wa su Aryaan wasa. Wurin Munira na zagaya muka gaisa, nan ta shaidamin cewa na aurar da Haulatu tana Mafara aka kaita. Allah sanya alheri na yi mata sannan na fito shaf-shaf na shiga sashensu Aunty Ziza ita da Suwara. Zaune na tarar da su da paper da Biro a hannun Suwara. "Miye kuke yi?" Dariya suka yi sannan Aunty Ziza ta ce. "Girke-girke ne nake koya mata Theoretically, kafin mu fara practical.." Jinjina kai na yi ina murmushi na ce. "Mun yi mubaya a domin kujerar ki ce,kuma mun bar miki kayan ki. Allah ya ƙara basira da zaƙin hannu. Gaskiya na yi farin cikin ganin yanda kuka haɗe kanku haka. Allah ya ƙara muku zaman lafiya ya ƙara buɗe Ya Emraan hanyoyin arziki..." Hannuna Aunty Ziza ta riƙe tana wani irin murmushi ta ce. "Ina mai ƙara baki haƙuri Beenafah. Muma ɗin nan muna alfahari da samun ki kuma muna gode miki, domin shigowarki rayuwarmu ce wasu abubuwan da yawa suka sauya. Alhamdulillah da irin samun mijina a lokacin da yake Naval officer, a yanxu ma Alhamdulillah zan ce domin samun sa da darajarsa sun ƙara yin sama, ta dalilin ki da yarjewar ubangiji ga shi zamu ƙara yin gaba muma zamu koma UAE da zama,... " Cikin wani irin farin ciki na ce. " Dan Allah da gaske kike? Yaushe?" Dariya Suwara ta fashe da ita ta ce. " Ni fa daɗina dake azarɓaɓi Aunty Beenafah." "Wallahy kin ji na rantse miki bani da wannan labarin.." Aunty Ziza na dariya ta ce. "Sai Suwara ta haihu tukun.." "Wayyo Allah daɗi. Allah ya nuna mana ya sauketa lafiya. Mu gobe zamu tafi in sha Allahu, sai kunxo. Don dai kam, nasan abun da zai dawo damu ƙasar nan ba kusa ba." "Allah ya kai lafiya. Idan kin je muna gaishe da Mijinmu..." Dariya na yi sannan na ce. "To a nawa?" "Ko nawa kike ce." Cewar Suwara tana dariya. Waje na nufa ina faɗin. "To ba za a faɗa ɗin ba. Ku da yanzu haka ma baku fi minti biyar da gama magana da shi ba, shi ne za ku wani aike ni da saƙon renin hankali. In ƙulle gaisawa ta fatar baki daga nan har Dubai saboda ga Beenafahr iyayi." Dariya suka bini da ita har muka shige sashen Hajiya sannan muka sallar Isha muka fito har mota suka rakamu. Bayan mun fito gidan Ammie muka wuce itama na yi mata sallama. Ta ji mamaki da ta ji zancen tafiyarmu wai gobe-gobe. Amma kuma tuna irin abin da Ya Jafaru ya yi sai ta ga cancantar hakan, duk da cewa an kai ƙarshe da shi kuma yayi alƙawarin ha zai ƙara ba. Sannan aka sake shi Baba ya riƙa shi shi da Ya Hamza suka kai shi asibiti. Kallon yanda Bahrain yake ta wasa da su Aryaan na yi ina murmushi na ce. "Za su yi kewar ka Uncle Bahrain..." Hawaye na gani a idonsa sai kuma ya yi murmushi ya ce. "Tun ranar da kuka tafi gidanku na ke kewar su ai." Dariya Ammie ta ce. "Ai a ranar kasa bacci ya yi, sai ga shi ya dawo ɗakina ya kwanta wai kewar yaransa ta hana shi bacci." Dariya na yi na ce. "Allah sarki uncle Bahrain! To ko dai na bar maka su?" "A'a, ki dai bari idan lokacin cire su a Nono ya yi ni zan je da kaina na dawo da su." Fira muka ɗan taɓa sannan daga ƙarshe Ya Mohaa ya shigo suka gaisa da Ammie, haƙuri ta ƙara ba shi sannan muka fito zamu tafi. Kallon sa na yi na ce. "Dan Allah ina neman alfarmar 5M" Jinjina kansa ya yi ya ce. "Cash kike so ko transfer?" Kallon sa na yi da mamaki na ce. "Ba za ka fara tambayata mi zan yi da zunzurutun kuɗi har haka ba?" "Har abada ba zan tambaya ba, ai daman tun da muke baki taɓa tambayata kuɗi ba. Yau ɗin ta kasance mini rana ta musamman. Duk abinda kuma za ki yi da su,na san mai muhimmanci ne..." "To na gode, Allah ya saka da alheri ya ƙara arziki." Ya Hamza na ce ya bini ya karɓa kuɗin sannan na koma ciki na cewa Ammie. "Ammie zan ba ki kuɗi dan Allah ki ba wa Ya Ashiru hannunki da nasa." Jinjina kanta ta yi tace. "In sha Allahu kuwa. An gode, Allah ya amfana." "Amin Ammiena, sai da safe." Bayan mun fito sai da muka biya ta gidan Daddy ya yi wa Mummy gaisuwa sannan muka biya gidan Aunty Labiba sannan bayan mun koma gida Ya Hamza ya zo tare da Bahrain suka karɓi kuɗin suka wuce. Washegari tun asuba kuwa muka fita har da Biba a wannan karon. Kaduna muka yada zango inda muka kwana ɗaya gidan Aunty Nadeeyah kamar yanda na roƙi alfarma sannan shi kuma ya je ya duba aikinsa sannan muka wuce Abuja muka wuce. ******* Su Ammie kuwa, sai da ta tsaya aka yi bukin Fakiha da Yaya Ashiru wanda ya ji matuƙar farin ciki na zuwa bukin sa da ta yi sannan ga kyautar kuɗi har 10M daga gareni wanda ni ma kaina ban san 10m ɗin ba ne, ni dai kuɗi na tambaya kuma na ɗauka su aka bani ashe ashe an ninka mini. Ya yi matuƙar farin ciki da shi iyayensa da en uwansa ba kaɗan ba. Sai godiya yake yana faɗin dan Allah ta isar da saƙon godiyar sa zuwa gare ni. Bayan an kammala bukin da kwana biyu suka juya suka koma gida tare da su Ya Hamza har da Aunty Hussaina wacce ta dinga kuka akan cewa ta tafi da ita kamar yanda ta saba a da. Cikin dangi aka binciko yara guda biyu aka kawo wa Mummy Zaliha, sannan kuma aka kai Kayan auren Ya Hafiz wanda za'a yi nan da wata uku. Wanda idan an yi auren ne yace zai kai ta gidansa domin matarsa ta ci gaba da kulawa da ita. Nan ne Ammie ta bashi shawara akan cewa ya sake komawa makaranta tun da wancan da ya yi ya riga ya zama wasted. Amma idan ya jona in sha Allah ba jimawa zai ga ya kambala. ******* Muna komawa da sati ɗaya ya koma aikinsa wanda ya dawo fita sau uku a sati, Monday, Wednesday da kuma Friday. Rayuwa muka sake shimfiɗawa sabuwa mai cike da zallar farin ciki muna renon yaranmu. Muna nan tsawon wata uku wanda a lokacin ne su Aryaan suke watan su na bakwai a duniya. Ina kitchen tare da Madam Amima tana haɗa breakfast ya kira ni a waya. Ina shiga na gansu yana kwance su Aryaan na ta hawansa suna tsalle-tsallensu na ce. "Miye wani gani ga gaka amma sai ka kirani a waya?" Murmushi ya yi mini sannan ya ce. "Because. Tomorrow, is going to be special. Very, very special." Cikin farin ciki na ce. "Wow! Tun ban ji ko miye ba na ji cewar something special ɗin ya yi deeping in to mah heart..." Kinkimar Aryaan na yi na kashi wurin Biba da sauri sannan na dawo na tallabi Arhaam shi ma na kai shi tare da buge mata warning na ce kada ta kira a waya da sunan suna kuka. Dariya ta yi sannan ta ce shikenan to. Ɗakin na dawo na kulle ƙofar na jinjina a jiki ina masa wani kallon ina murmushi. Tasowa ya yi yazo ya yi trapping ɗina tare da matso da fuskarsa ya ce. "No questions..just trust your Husband." Maƙalƙale wuyansa na yi tare da haɗe bakinmu wuri ɗaya na bashi wani zazzafan kiss Sannan na janye ina kallon ƙwayar idanunsa na ce. "Da wannan daddaɗan albishir...Let's get down to bed...i promise to feed you with the best breakfast..." "And I will for ever be grateful BibiLove." Kan gado muka faɗa na kashe sa da zazzafar ƙauna sannan muka yi wanka a tare muka fito. An yi mini albishir ɗin da ban san ko miye shi ɗin ba. Sai da gari ya waye yace mu shirya zamu tafi. Sai da muka hau jirgi sannan na kallesa na ce. " Wai dan Allah ina ne muka nufa haka?" Pcap ɗinda ke kansa ya cire ta ya ɗora a kaina yana murmushi ya ce. "we are travelling to the world for you...just you only...trust your Husband,  I assure you za ki ji daɗi sosai." Murmushi na yi tare da jinjina masa kai na nace. "Thank you Dayaa. Thank you for loving me." Tafiya muka yi mai ɗan nisa sannan muka sauka a wani Private island resort. Kyakkyawan farin yashi ne malale a wurin, ga pure Crystal blue water suna ta tsalle gwanin burgewa. Haɗaɗɗen wuri ne mai daddaɗan yanayi wanda ban taɓa zuwa ba. Kallon sa na yi cike da farin ciki na ce. "Farin cikina, wannan wace duniyar ce muke?" Hannuna ya sumbata yana murmushi ya ce. "Where every queen deserves to celebrate her birthday...Maldives...The land of blue waters. Romantics nights...and unforgettable Love." Hannuna ya ja ganin yanda na sanƙame ina ta murmushi yayin da wani irin tsabar daɗi ya ƙumeni. Ya ce. "Mu huta tukun." Haɗaɗɗen lounge muka shige wanda ya kama mana na musamman, bayan an gama shigar mana da kayanmu, mukayi wanka muka ci abinci, muka yi sallah sannan muka zauna zaman hutawa. Sai da dare ya yi misalin 11:30pm, wanda resort ɗin ya ɗauki wani haske da sheƙi gwanin burgewa sannan muka shirya cikin wata shigar da ban taɓa ganin irinta a jikin sa ba ya ja hannuna zuwa wani kewayayyen wuri da aka ƙawata na musamman. Ga wani romantic music da yake tashi a hankali wanda ke saka zuciyoyi amsawa da kuma zama yardajjin juna. Fireworks ne suka tashi sama suna tartsatsin wuta a lokacin da 12:am dot tayi clocking. "Happy birthday my queen BEENAFAH..." Kallon sa na shiga yi babu ko ƙyaftawa yayin da rai na da ruhina suka amsa da wannan farin ciki mai sa kuka. Hakan yasa ban san lokacin da wasu hawayen suka shiga wanke mini fuska ba wanda ban ɗauke idona ba har saida rubutun ya ɓace a hankali wani ya fito da zanen. "Happy Birthday Bibina....I love you." Ji na yi ya ɗoramini kanbu a kaina sannan ya kama hannayena ya sumbata. Ya sumbaci goshi na zuwa lips ɗina zuwa wuyana Sannan ya yi mini murmushi ya ce. "Wish you many many wonderful years ahead sarauniyata." Hawayena ne suka ƙaru sannan na rungume shi sosai ina mai jin wani abu na musamman a ƙirjina. Sosai yau ya tuna mini da Abbie...ni mi zance da wannan mutumin da ya wuce in yi ta masa addu'a ta alheri ina faranta masa ransa da ƙaunar duk abinda yake ƙauna a duniyar nan dama lahira inda can ne matabbata. Wata diamond necklace ce mai numfashi ya fito da ita ya ɗoramin a wuyana yana murmushi ya ce. "Wannan Gift ɗin mijin ki kenan Bibi..." So nake in daina kukan in gode masa, amma kuma na kasa dainawa. Girgiza kansa ya yi tare da saka hannunsa ya share min hawayen yana murmushi ya ce. "Haba Bibi! Wai miye haka ne? Muna ta abin farin ciki ke kuma kina zubo da hawaye...oya! Maza maza ki haɗiyesu, ko kaɗan bana son ganin hawaye a nan. Ba wurin su ba ne. Farin ciki ne kawai ya kawo mu nan ɗin." Hannu na saka da sauri na goge hawayen, tare da fatan Allah yasa kada su zama marasa jin maganar mijina, domin idan suka yi yunƙurin ƙara zubowa tabbatas ba zan taɓa gafarta musu ba. Hannunsa na kamo na yi twisting a nawa, happily na jinjina masa kaina ina murmusawa na ce. "Ban san waɗan ne kalmomi ne zan yi amfani da su wurin gode maka ba. But...abinda na sani kai ne rayuwata, kai na daban ne a duniyata, ina ƙaunarka..." Murmushi ya yi ba tare da ya saki hannun nawa ba ya ce. "Since the day I married you...my life become complete...you gave me peace, you gave me two beautiful souls Aryaan and Arhaam, and...you are my whole world..i will keep loving you , until we grow old together, har abada matsayin ki ba zai canza ba." Rungumesa na yi tare da fashewa da kuka ina faɗin. " Please allowed me....dan Allah karka hanani kuka ka ji...wannan na zallar farin ciki ne, I love you." Wayarsa ya ciro ya kira, ban ankara ba kawai na ji murya su Ammah suna mini Happy birthday. Cikin farin ciki na amsa su sannan ya kashe ya kira su Jadda..da haka haka sai da ya kira kowa da yake namu suka tayani murnar zagowar ranar haihuwata. Na yi farin cikin da ban taɓa jin irin sa a rayuwata ba, wannan duniyar da wannan ranar sun kasance na musamman a cikin tarihin rayuwarmu. Har abada ba zan daina alfahari ba, domin miji ne wanda ya cancanceni nima na cancancesa. Sai da muka yi sati ɗaya cif muna nishaɗi sannan muka juya muka koma gida. Haka rayuwa taci gabar mana da tafiya har sai da Su Arhaam suka ci ka shekara ɗaya cif wanda a lokacin ne shima Bahrain ya zana jarabawarsa ta kambala secondary school. Nan suka shirya suka zo inda nake a karon farko tun bayan aurena da Ya Mohaa. Tare suka zo ita da Bahrain, Ya Hamza da kuma Aunty Hussaina. Bahrain hadda kukan farin cikin yanda yaga su Arhaam suna gudu akan ƙafafunsa ko'ina. Sai taɓara yake musu shi da ya Hamza su kuma suna dariya. Kwana biyu suka yi muka shirya a tare muka wuce Qatar wanda shi ne zuwana na farko su kuma Ammie na biyu. Garin ya ƙayatar dani matuƙa musamman gidan kakanni na da ya kasance na musamman. Abiyh ya yi kukan farin ciki sosai da zuwanmu. Ni kam muna isa ko kwana ɗaya ban yi a gidan ba na bi Annie muka wuce gidanta ni da twins muka kwana sannan washegari muka shirya har Ammie muka haɗe gidan Noura inda ta yi aure gidan wani bawan Allah mutumin kirki da shi. Munsha zumunci mun zaga Qatar mun yi yawo mun buɗe ido na tsayin wata ɗaya sannan muka shirya da nufin ƙetarawa zuwa ƙasar Yemen. Sai ranar za mu fito ne naga Aunty Hussaina da Raihab suna magana wanda ni dai jikina ya gama bani cewa akwai wani abu. Hakan yasa ban yi ƙasa a gwiwa ba na tambayi Ammie wacce ke riƙe da hannun Aryaan na ce mata miye tsakanin Aunty Hussaina da Ya Raihab. Kai tsaye ta ce mini ta ba shi ita, aure za suyi daga zaran mun koma gida. Wallahy sai da na yi kuka saboda murna, Aunty Hussaina tana bani tausayi a rayuwa. Musamman yanda aka yi ta fasa auren ta samari kuma suka janye. Ashe rabon babban mutum ce ita mai babbar harka Raihab Abdulmajeed. Ga kuɗi ga Addini domin babban Ustaz ne bawan Allah wanda idan ya fara kwararo maka karatun Alƙur'ani mai girma sai ka ji kamar ka sume tsabar daɗi da ƙwarewa. Yemen da muka sauka, Ammie ta yi kuka sosai lokacin da ta yi ido biyu da Ummie wato matar Sheikh da kuma en uwanta su Nina. Sheikh ya yi matuƙar farin ciki da ganinmu musamman ni da ya gani da yara, wai ni 'ƴar Mulaifa ce har da jikoki. Ammie bata san ma mi za ta yi wa Sheikh a duniyar nan domin faranta masa ba. Ya riƙe ta tamkar uba Ummie ma ta riƙe ta tamkar ita ce ta haife ta. A yanxu dai iyayenta suna da hali da zarafin da ba ta isa tace za ta nuna musu wani iko ba, domin sai dai ma ita su bata,domin wannan zuwanma sai da Abiyh ya kawo takardu akayi rubuce-rubucen da ya mallaka musu abubuwa ita da Annie wanda ya ce mallakinsu ne domin shi bai san mi zai yi da wani abu ba a yanzu, rayuwar farin cikin da yake ciki kawai ta ishe sa. Sai dai yace Alhamdulillah. Tambayarsa ta yi tace mi yake so ya ce mata baya son komai. Shi ganinta ma da ya yi a cikin farin ciki ya wadatar da shi. Ya Mohaa aka yiwa magana akan ya tsantsara masa gida na musamman wanda zai kasance ita ce wacce ta gina masa a matsayinsa na mahaifin ta. Sannan ta bashi kuɗi da shi iyalansa kyauta ta ban mamaki. Bayan mun gama yin sati biyu muka wuce Canada inda gidanmu yake. A nan muka tarar da Dr. Basheer wanda ya shirya mana zama da mutanen kamfanonan kamar yanda yace a baya. Nan muka yi zaman meeting ɗin na tsawon sati ɗaya domin har da na Wazeermed da FruitWave. Sannan bayan an akai matsayar komai an buɗe mana account ɗinmu. Sannan aka raba shares ɗinda za su riƙa a cikin account ɗin kowannen mu duk ƙarshen shekara. Sababbin ma'aikata aka sake naɗawa a nan NordicBag da kuma Abuja. Bayan komai ya kambala muka wuce Sudan muka ziryace su na tsawon sati ɗaya sannan suka koma gida mu kuma muka wuce Saudiyyah Wurin Umrah har da Ya Mohaa inda muka yi ibada muka huta na tsawon wata ɗaya sannan muka koma gida. Sannu a hankali muna tafiyar da rayuwar har su Aryaan suka cika shekara da wata bakwai. A lokacin ne aka cire su a Nono amma kuma ya ce bai yarda a kai su ko'ina ba a bar shi da yaran shi domin su ne farin cikin sa. Iyaka idan mun tashi mu shirya mu ziyarci su Aunty Ziza ko kuma su ziyarcemu da su Hairiyyah wanda a yanzu duk muka kasance a gari ɗaya. Bayan wata ɗaya da Yayesu ya zo mini da Admission letter na shiga jami'a, daman ina nan ina classes a online har na samu ya samar mini takardun kambala secondary. Cikin ikon Allah na fara karatuna a hankali komai yana tafiyar mini daidai, kwatsam sai kuma ga ciki. Sosai ya ɗaga hankalin sa musamman ganin sabon yanayi a tattare dani na tsananin rashin lafiya na laulayin ciki wanda ban yi shi a lokacin cikin su Aryaan ba. Nasha baƙar wahala ga karatu ga laulayi wanda ban samu wani sauƙi ba sai da cikin ya gota watanni huɗu. Yaso na ajiye karatun nace masa a'a ya bari in sha Allahu zan lallaɓa. To fa da gatan da yake mini da kuma kulawar en uwa da abokan arziki sai abubuwan suka ɗan sauƙaƙa a gare ni. Inda a kullum kwanan duniya ba na taɓa gajiya wurin godewa Ubangijina akan irin mijin da ya bani sai dai godiya da sambarka. A haka na lallaɓa ina year two first second semester na samu ƙaruwar wani ɗa namiji wanda da kansa ya saka masa suna Abdallah. Domin yace mini yana son sunan a rayuwarsa. Nan akayi shagali na musamman inda muka samu halartar wasu da yawa daga cikin dangi waɗanda kuma ba su samu zuwa ba, suka yi ta yi mana fatan alheri. Haka na ci gaba da tafiyar da rayuwar iyalina wanda nake matuƙar nuna iyakar ƙoƙarina wurin ganin ban gaza musu da komai ba, duk da dai ita rayuwar nan ba za ka taɓa zamowa 100% ba sai dai ka yi abinda kake iyawa kabar wa Allah saura. Shima Mijina yana iya ƙoƙarinsa a komai, lokacinsa, rayuwar sa da komai nasa namu ne akan gaba kafin shi, inda a yanxu suma su Aryaan an saka su a makaranta. Sannan Hajiya Batula ta dawo nan inda muke zaune kamar yanda na roƙesa, ganin irin albarka da yake ta samu da alheri, yasa ya manta komai, har jin cewa da yake ba zai iya zama da ita ba yanzu komai ya wuce a rayuwarsa. Duk ƙarshen shekara muke shiryawa muna ziyara duk inda ya dace, birthday na ma da na su Arhaam idan ya tashi baya mantawa, daga zaran an tashi yake samun ƙasa ta musamman domin muje muyi celebration. Ya cika mini duniya ta da farin ciki ya bani dariya da walwala kamar yanda shi ma yake iƙirarin na yi masa. A yanxu kullum lissafi nake wanda ni ka ɗai na barwa kaina sani sai kuma Allah. Saura kwanaki ashirin da ɗaya mu cika shekaru biyar cif da aure, wanda shi Sam ban taɓa jin ya yi lissafin wannan ba. To shi ne nake so nima in yi surprising nasa da bukin weeding Anniversary ɗinmu wanda zan shirya komai a ɓoye sannan in haɗa da bukin birthday ɗinss wanda a lokacin ne zai cika 52Yrs a duniya. Ina so in faranta masa, duk da cewa a kullum cikin faranta masa nake, but I want this one to be different. Something that's gonna be special and unforgettable. Wannan dalilin ne yasa na shiga neman shawarwari a wurin Raihab mijin Aunty Hussaina wacce ke da yarinya mace da kuma Bahrain da kuma Aunty Labiba da sis Noura.

Chapter 62 of 67