Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [3/28, 11:47 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: ƘALLABI...! A tsakanin Rawuna.. ** ~FREE BOOK~ Na Mai_Dambu EWF *Har ila yau SADAUKARWAN taku ce Aminan kwarai a gudu tare a tsira tare* Zahran Addah Ramlah Da UMNASS din Mai_Dambu GODIYA TA MUSAMMAN GA SANAH MATAZU Shimfida. Kasar gobir na ɗaya daga cikin kasashen hausa na ainihi, ance ita ɗin tsohuwar daula ce kuma wata babbar kasa ce da tayi iyaka da Agades daga arewa, tayi iyaka da Zamfara daga Kudu, tayi iyaka da Mayali daga Gabas, sannan kuma daga yamma tayi iyaka da Konni. Amma magana anan itace, asalinsu ba hausawa bane tunda wasu nacewa asali waiƴ daga gabas ta tsakiya suka fito musamman ma Misira, inda ake da yakinin cewa Sarakuna ukku daga cikin sarakunan Misira gobirawa ne. Sarkin Gobir Mai daraja Alhaji Abdulhamid Balarabe Salihu ya taɓa faɗar asalinsu a wata fira da jaridar 'Daily Trust' tayi dashi, shine yake cewa: Gobirawa sun zone daga misira (egypt). Har Yace su jikokin Annabi Nuhu A.S ne kuma sun bar misira saboda wahalar mulki na sarakunan lokacin. Shine suka sauka a wani wuri mai suna Gubur. Daga nan ne suka samo sunan Gobir. Yaci gaba da cewa daga baya sun isa Yemen, sunyi yaki sosai a kasar saboda su suna da jinin yaki da jarumta. Daga nan kuma sai suka isa libya, a haka suna matsawa har suka zo wani gari mai suna Azbin inda yanzu mutanen Taureg suka mamaye. Da suka bar Azbin sai suka shiga sahara, har suka kafa wani gari mai suna Magali, daga baya sai suka bar garin izuwa wani mai suna Surukul (dukkansu yanzubsuna jamhuriyar Niger ne). A hankali suka riski birnin lalle da gwararramu a karni na 15 zuwa na 16. A lokacin kuwa, Sarkin zamfara Abarshi ke mulki wanda yake da zama a Katanga, kuma an samu har ya auri ɗiyar sarkin Gobir mai suna Fara, wadda ta haifi Sarkin gobir Ibrahim Babari.. Kafin Babari ya zamo sarki, ai sai dayayi faɗa da Sarkin Zamfara na lokacin kuma yaci karfinsa. Akan haka sarkin Zamfara ya kuduri niyyar halakashi, amma sai yayarsa ta maido dashi kasar mahaifiyarsu watau Gobir, a haka kuma har ya zama sarki (Watau yayi gado ta wajen Uwa). Babari ya roki Sarkin gobir ya bashi wuri a yankin Zamfara inda zai zauna, amma sai aka gargaɗi sarkin Zamfara da cewa kul ya baiwa Babari gurin zama domin nan gaba zai iya mamaye zamfara dukkan ta, ai kuwa daga bisani hakan ne ya faru, da yaki ya ɓarke a wajajen karni na 16 zuwa na 17, sai da Goburawa suka cinye har Alkalawa da yaki. (abinda ke nufin inda suke zaune ayau asali kasar zamfara ce) Sarkin Gobir Abdulhamid ya kara da cewa " A lokacin Sarkin Gobir Bawa Jan Gwarzo (Karni na 17), ance an ruwaito cewa Ko zakaru basa cara sabida jarfin tsafinsa, kuma aduk yake-yaken da sukeyi, gobirawa basu taɓa mika wuya ba. Ance sunfi gwammacewa a kashe su akan su mika wuya, shiyasa ake musu kirari da 'Gobir gidan faɗa'. Sarkin yace " Bawa jan Gwarzo bai taɓa yaki da Shehu Usmanu ba A zamanin jihadi, maganar gaskiya ma itace shehu ya koyar da 'ya'yan Bawa, ciki harda Yunfa, Atiku, Bello da Mayaki. Ance ma saida shehu yayi musu nasiha da kada su bari a samu rarrabuwar kawuna a tsakanin su. Sarkin yace " Mutanen dake kusa da Bawa sune suka haɗa kiyayya a tsakanin su, wanda yayi silar shehu yabar Alkalawa, daga baya kuma yaci gaba da jihadi a sassan sokoto. Dan gane da tsagun gobirawa, Sarkin yace asali basu da tsagu a fuska, amma sabili da yake-yake ne yasa suka rinka tashi daga nan zuwa can, don haka suka ɓullo da tsagu domin su rinka shaida junansu. (Bari mu daura labarin) _________________________________ (Yau Laraba/11/ ga watan Rabi'ul Auwal 1809. Karni na goma sha takwas) Da gudu Mahayi ya shigo masarautan tare da rike wasikar hannun shi, ya shiga har farfajiyar masarautan. Tsare shi sarkin Fada yayi tare da cewa. "Ilu dan Audu, Audu dan Uwaisu. Farin me farin aniya, baka zama jakadan alkhairi sai ta sharri" Dira yayi a kan dokin sannan ya wuce fada Sarkin fada yana biye da shi. Ilu dan Audu, dan sako ne duk wani sakon da zai zo fada toh ta hannun shi yake zuwa, kasancewar masarautan sun tafi yaki da wasu kabilar da take gabashin masarautan kuma babban abun damuwa shine karfin da wadancan kabilar suke da shi idan suka samu karfin ta hanyar kabilar Fulani waɗanda ake kiran su Rumada. Kasancewar suma Rumada bayin Fulani ne, kuma suna da matukar tasiri da karfi amma basu cika shiga abinda babu ruwan su ba, abinda ya kuma fusata masarautar Gobir ba kome bane sai yadda kabilar da suke kara samun ƙarfi sama da kowacce ƙabilar. Kasancewar su din kabilar sun fito daga kwararrafa ne, ana da yakinin Banza Bakwai ne, da suke da makotaka da Zamfara. Kafin Gobirawa su kwaci mulkin Sarkin Zamfara. Wanda shi da wadannan kabilun guda uku suka cure domin yaki da gobirawa. Zubewa yayi a gaban Sarkin rikon kwarya, wato Sarki Bello na biyu. "Allah ya taimaki mai martaba! A can filin dagga ana fama da yaki kamar yadda Yayanka mai Martaba sarki Ibrahim ya tafi wakilta wannan masarautan." Shiru yayi lokacin da Zakaria ya shigo. Sunkuyar da kai tayi kafin ya d'ago kai yana kallon Sarkin Bello me rikon kwarya ya ce. "Sai hakuri, domin sarki Ibrahim ya kwanta dama" a wani irin zabure mai martaba sarki Bello ya Mike. Jikin shi yana rawa. "Karya kake bawa! Karya kake bawa! Taya Jarumin sadauki irin mahaifina ba zai mutu a banza ba" wani irin kuka ya sake tare da kallon Sarki Bello cikin shashekar kuka ya ce. "Wallahi ba zan yafe hakkin mahaifina ba" riko shi sarki Bello yayi cikin matsanancin tausayi yana bubbuga bayan shi yana cewa. "Kayi hakuri, Allah ya gafarta mishi." Abin tausayi baki daya masarautan ta kare yaran kabilar Gobir da suke mulki sun kare sabida yakin da suke da kuma faffatawa. "An binne shi a can, amma mun samu nasarar farattakar mayakan da maciya amana, sannan mun dauko wasu yan tawaye zamu tawo dasu da bayin da aka kama" Cikin wani irin shashekar kuka Zakaria,.ya mike tare da nufar cikin gidan sarautar. Wanda izuwa yanzun labarin mutuwar mai martaba sarki Ibrahim ya karade cikin gidan. Kasancewar yana da ƙarancin shekaru yasa ta zama abin tausayi. Mikewa Sarki Ibrahim yayi sannan ya kalli Chiroma. "Idan kome ya lafa zan ba shi mulkin shi tunda na shine ni rikon kwarya nake" ya fada cikin sansayar murya wanda dama halin shi. "A'a Mai Martaba, idan har kai aka bawa mulkin muna da yakinin yaki ya kare, idan kuma aka bawa wani tabbas yanzu aka fara domin yakin bai kare ba" inji Galadima. Domin yakin har da Wazirin masarautan aka tafi. "Wannan maganar gaskiya ce, matukar muka sake ka bar mulkin baki daya masarautan Gobirawa zai zama tarihi. Amma idan muka barka akan mulkin nan ba mamaki zamu samu salama da nutsuwa, sannan Allah ya albarkaci da abubuwan cigaba. Idan kuma aure kake bukata zamu nima maka auren daga ya'yan manyan masarautu. Da suke zagaye da mu har ketaren mu." Inji Chiroma. Duk yadda Sarki Bello ya so kauce musu, haka suka mishi dabaibayi da mulkin. Har aka dawo da mutanen da suka tafi yaƙi. Inda aka dawo da Waziri cikin wani mugun hali. Domin kuwa ya jikata sosai dan dole aka kai shi gidan shi Jinya. A cikin gidan sarauta kuwa akwai yaran Sarki Ibrahim marigayi, uku mace daya, maza biyu Zakaria shine Babba mahaifiyar shi me Suna Gambo, baiwa ce kafin sarki Ibrahim ya yantatta. Sai matar shi Ajuji wacce ya haifi yara mata biyu. Fulani Kyauta domin an tabbatar da ta jima kafin ta haihu har ana mata gorin haihu. Sai na biyun su Yakubu ana kiran shi sarkin yaki,. kasancewar an haife shi ne a wani rangadin da Sarkin yakin sarkin musulmi yazo Zamfara zai wuce sokoto. Shine ya tsaya a masarautar Gobir. Inda yana isa aka ce ai mai dakin sarki tana kan gwiwa. Shine yayi tofi aka kai mata ai kuwa tana sha ko minti ɗaya ba a kara ba ta haifu danta namiji. Koda aka kawo yaron fada, Sarkin yakin sarkin musulmi yayi mishi addu'a. Sannan ya wuce anan mai martaba da manyan fada suka yanke hukuncin yiwa Sarkin yakin sarkin musulmi wato Sarkin Bauchi a lokacin. Sai sauran dakunan kuwa kwarkwarori ne, kuma basu haihu ba. Duk wannan yanayin da aka gaya musu labarin yasaka jikin kowa yayi sanyi musamman da masu kishin akan danta ne zai yi mulki, sai gashi an fitar da sanarwar labarin Sarki Bello za a rantsar. Kasancewar Yarima Zakaria shekarun shi sha takwas ne, sai Yakubu me Shekara sha biyar, Fulani Kyauta. Tana gab da za a aurar da ita ne. Wannan tsarin da akayi ya fitar da tashin hankalin da ake samu tsakanin Gambo da Ajuji, dan dole suka rungume ƙaddara. A lokacin Sarki Bello yana da shekaru talatin a duniya, babban damuwar shi yayi rayuwa ta yanci da walwala yana son koda zai yi aure baya son ya auri yar mulki domin zata iya saka shi ya bukaci mulki shi kuma abinda ya tsaya nake nan. Bayan wasu watanni aka shirya bikin nadin sarautar sarki Bello, wanda aka kai gayyata ga sarakunan yankin gaɓar kogi Chadi zuwa bainuyo, sannan aka kai har zuwa kwara kasancewar tarihi ya tabbatar akwai milawa Fulani ne kuma Gobirawa ne, sannan aka kai yankin kasar Gombe inda Sarki Muhammad kwairanga yake mulki. Sannan aka kai masarautar Kano, zuwa Yola inda Modibbo Adama yake mulki. Sannan aka kawo Bauchi ga Sarkin yakin sarkin musulmi. Kafin aja wuce da na zaria, domin shine nadin sarautar da za ayi na Muhammad Bello na biyu. Wannan nadin sarautar ya tara al'ummar sarakuna daga manyan yankunan arewacin kasar. Sannan an kai sakon gayyata har maradi domin can ma akwai wata masarautan Gobirawa. Kuma sun tabbatar zasu zo ayi bikin da su. Lokacin da za ayi nadin Sarkin Musulmi da kan shi, ya halarci taron nadin sarautar, yadda mutanen Fada suka gayawa sarki Bello, sun roke shi da ya fada ba zasu kuma yaki ba, idan ma za ayi yakin toh sai ta hanyar yad'a kalmar Allah. Wato jahadi. Haka kuwa ya kasance, mulki aka bashi bayan nadin sarautar da kwanaki Allah ya amshi rayuwar Wazirin sarki Ibrahim,me suna Musa dan Musa. A lokacin yaran Waziri sun so a basu sarautar gidan su, amma kasancewar akwai sauran sarakuna sai suka bada shawarar a bawa Zakaria waziri duk da lokacin shi din Yaro ne, haka Sarki Bello ya janyo shi har cikin fadar. Sannan yaki kallon Zakaria a matsayin dan Yayan shi, kallo yake mishi irin na wa da kani. Shima kuma Zakaria yana mugun ganin girman Sarki Bello, idan ka cire Yakubu da kiri kiri yake adawa da sarki Bello. Tare da gaya kishi cewa. "Ka bar murna karen ka ya kama kura! Inda rai da rabo wata rana kallo zai koma sama shawo ya dauki giwa" domin wani irin masifaffen kishin sarki Bello yake sannan ba iya shi ba hatta dan uwan shi Zakaria. Sai da Yakubu ya farmake shi kamar zai kashe shi. Wannan yasa aka saka Idanu akan Yakubu domin adawar shi tana kazamta. Sannan bai da burin da ya wuce ya nufi Katangar bayi ya saka ana ware mishi kyawawan yan mata ana kai mishi dakin shi. Yana tarayya da shi kuma mai Martaba yaji labarin bai da ikon ya hukunta shi domin a cikin wannan yanayin baya son a samu rabuwar kai... _____________________________________ Hello' Fanmily dama na gaya muku zaku iya samun posting kafin Azumi... Karku manta labarin FREE BOOK ne... Comments da Voting shine price na labarin. And inshallah zai na zuwa muku sau uku a sati Daya.. Saturday. Monday. Thursday inshallah.... Sabida ina da abubuwa dayawa kuma ina typing paid book so. #Freestory #mai_Dambu.... [3/28, 11:47 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: ƘALLABI....! A tsakanin Rawuna ** ~FREE BOOK~ Masu iya magana kan ce wanda ya riga ka kwana zai rigaka tashi haka.. inji Malam BAHAUSHE. Abinda ya faru kuwa duk yadda Sarki Bello yaso had'a kan Yayan Wan shi abun ya ci tura musamman yadda Yakubu yake kara baudewa,yana kara fusata ga kuma yadda yake illa a cikin katangar bayi yasa Sarki Bello ya taka har wurin Ajuji. Tunda ana gaya mata sarki yana iso gare ta, ta gyara zaman alkyabarta ta, sannan tayiwa Jakadiya Rama magana da cewa. "Jakadiya zai iya shigowa" Duk da bata sannan me ya kawo Mai Martaba sarki Bello ba, amma tayi imanin cewa ya kara mata daraja a cikin gidan duk da ba a bawa danta mukami ba, amma tabbas haka ya nunawa Mutanen cikin masarautan cewa ai tana da kima. Cikin sallama ya shiga babban zauren ta, wanda yake dauke da bayi mata suke mata hidima. Zubewa duka yi tare da gaishe shi. Jakadiya ta amsa. "Mai Martaba ya amsa, kuma yana son magana da uwar Dakin ku zaku iya fita" Fita suka shiga yi daya bayan daya, dakin ya rage sai Jakadiya. "Me ke tafe da Sarki Bello?" Murmushi yayi cikin dattako, sannan ya ce mata. "Nazo ne domin kece kika fi dacewa ki gargadi Yakubu. Barnan shi a cikin masarautar nan tayi yawa. Idan ya cigaba da haka abun ba zai mana dadi ba? Kin san da naga ake gane zurfin ruwa, kuma idan har akwai sa'a toh tafiyar ba zata zama mara amfani ba" Ya cire mulki yayi mata magana ba fahimtar juna. Amma sai bata ce kome ba, asalima tayi na'am da yadda yazo mata domin tasan ba karamin al'amari bane a Kore Yakubu daga masarautar. Dan haka bayan tafiyar shi, ta saka aka kira mata Yakubu da yake dakin shi yana masha'a da wasu bayi mata. Sai da ya gama abinda yake sannan ya saka aka fitar da baiwar. Yayi wanka ta shiga cikin gidan sarautar. Dakin Mahaifiyar shi ya nufa. Sannan ya zauna yana kallon kayan marmarin da aka ajiye mishi. Tab'awa yayi tare da cewa. "Iya kiran me kika min?" Shiru tayi kafin ga fara cewa. "A yayinda Duniya ta juyawa fatake baya, zai yi wuya ya fahimci inda ya dosa, ba zan tsawaita nusar da kai zafin da yake cinkushe cikin sahara ba, sai dalilin me matukar muhimmanci ya iske ka." "Kenan an samu baragurbin da ya fitar da tsumammiyar ma'ajiyata? Lallai dan Mutum mugu ne, yayinda yake take laihin shi ta hangi na wanin sa!"ya fada cikin matsanancin fushi, "Ke Tallafi bani ruwan randan kasar nan ko zata sanyayya zuciyar Yarima na! Kome yayi tsannanin sauki yana tare da shi. Ba a kashe zafi cikin ruwan sanyi. Koda ciwo ne da zafi ake kashe zafi." Mika mishi ruwan tayi tana cewa. "Duk iyawar me iyawa matukar zai kai tufkar hanci dole a canza launin farautar... Kasan yadda ake farautar Zaki? Dan haka karka sake a kuma ɗibo gurbattani a kawo min domin ba zai mana dadi ba, kuma zasu zantar da duk hukuncin da yayi musu. Ka tausayawa Yayarka ta samu majingini a tare da kai" Wannan abin yayi mishi tsauri amma babu yadda ya iya dan dole ya hakura da gargadin da ta mishi. Har zai fita ta Kalle shi ta ce mishi. "Ban sani ba ko akwai wani darajar bayan haka a cikin fadar shi. Amma naji yana faɗin ba zai taba wanzar da zamanin shi ba tare da ku ba, shi din ma kamar wata damar ce da ta wanzu a gare ka. A koda yaushe zaman lafiya yafi zaman dan sarki idan ta kama da shi sarkin da kan shi. Haka ya ce nai" Gyada kai yayi kafin ya fice daga zaurenta. *** Kasurgumin daji ne mara kan gani me ɗauke da manyan kwazazxabai da kurmi. Hadi da manyan duwatsu, dan tafiya kadan zaka yi zaka taradda wata korama, sauka suka yi akan dawakan su. Sannan suka daure dawakan kafin suka isa bakin koramar wacce take fitar da wani sirrintacciyar zafi da dumi. Daukar wasu fararran duwatsu suka yi sannan suka watsa a cikin koramar. "Ga bakin gida, ga irin mutanen karni ga masu bukatar biyan bukata." Rabewa ruwan yayi suka wuce ta kan hanyar da ruwan yake, babban fili ne iyakar ganin ka idanun ka. A hankali suke takawa har sun ka isa wani wawwakeken lambu, shiga cikin lambun suka yi tare da tsinkar ƴaƴan itacce, suka fara sha. Wani irin hadiri ne ya gangamo kafin kace me garin yayi matukar duhu. Dariya wani dan tsabubburin mutum ya saka tare da durowa gaban su, kamar dan biri. "Akan mulkin masarautan ku! Ai ku koma daga nan zuwa shekaru goma ku dawo. Amma ba makawa wasu shudadden al'amarin zai faru. Imma a mutu Imma ayi rai sakon daga kai da kai ne. Ƙwayoyin halittar bil'adama tana bisa ga muradin dan haka ga wutar can. Gutsira dan itaccen ka kashe kiyayyar ka... Amma ba zaka tab'a soyayyar da take cikin dinbun zukatan al'umma ba. Akwai Sa'a amma zama haka na tsawon shekaru goma akwai barazanar ko ta kwana wannan hangen dan tsinbura ne maza a tafi ayi ta aikin ba tare da kallon abinda zai dawo ba. Domin har yau taurarin ba zasu yi gamayyar halitta ba. Wannan a saka a cikin babban magudanar ruwan masarautan.. Sa'a tana gare mu" Fitar da sulallar zinari yayi kafin ya zuba mishi. "A cikin matan da suke cikin masarautan bayi ayi kokarin tara su a kara gine katangar masarautan da su... Kamar yadda muka yi bayanin karnin da ya gabata" Godiya suka Mishi sannan suka juyawa tare da barin dokar dajin. "Kana ganin idan har aka yi haka babu wata matsala?" "Gaskiya babu domin na yarda da shi sama da kowa bani tab'a yarda da aikin kowa sai dan tsinbura" Duk da kasancewar Muslunci tana wanzuwa a cikin masarautan amma kuma sha'anin bokanci yana kara samun damar wanzuwa a cikin masarautan. ** Bayan kwanaki Yarima Yakubu ya cigaba da zuwa fadar ana zama dashi sai dai zaman babu wani alkhairi. Domin kiri kiri yake karta rashin arzikin shi. Idan ran Waziri Zakaria yayi dubu b'aci yake. Yau ma ana zaune ana fadanci ya shigo cikin fadar daidai magatakarda yana karanta sakon Sarkin Gombe. Kallon Sarki Bello yayi kafin ya kalli magatakarda ya ce. "Kai tafi can! Ka koma ka gayawa Sarkin Gombe cewa shi wannan baffan nawa kasancewar jimawa da yayi yana zama basir ta cinye mai kuzarin shi" "Tir da halin ka wallahi." Kallon Zakaria yayi tare da cewa. "Gaya min uwanai ta min baki na? Ko ubanai ya min baki na? Kaga ba zan iya dundduke ina zaman jiran gawon shanu bayan nasan me bisa kai nai. Imma ka yarda an ci amanar mahaifin mu imma ka zauna zaman karen farauta sa" ya fada yana kwabe fuska. "Hattara dai kasan me zaka fadi a gaban Mai Martaba sarki Bello." Wani makawa Sarkin Fada yayi harara. "Kai kunshe min bakinka. An ce maka kowa maroki ne? Sai manyan suna zance a bisa sha'anin mulki ku da kuke karakad'anna karan kad'a miya kuna tsomma bakin ku acikin zancen mu" Cikin fushi Waziri Zakaria zai magana , Mai Martaba ya d'aga mishi hannu. "Da kabarni na gyara mishi zama, me bakin zuciya kawai. Allah kadai yasan Meye zai iya aikatawa dan fuskar shi ta nuna rashin amincin shi" Wani irin kallon banza yayi tare ba mikewa yana kallon Sarkin Zagi ya ce mishi. "Ka gayawa musu duk wata tafiya tana bisa hanya ce amma tashi tafiyar da ya hana kara faɗin kadada zata iya fadawa cikin hatsari dan haka a yi nazarin dakatar da yaki." Shiru fadar ya dauka, shi kan shi sarkin Zagi kasaka magana yayi dan yasan tabbas Mai Martaba yaji abinda ya faɗa Yarima Yakubu ya faɗa. "Me yasa ba za a dakatar da shi ba!" Murmushi mai martaba yayi tare da kallon Galadima. Mikewa zai yi fadawan da suke tare da shi suka mike tare da kare shi da babban rugunar su, suna faɗin. "Gyara kintsi mai martaba zai tashi" haka ya tashi suka buda mishi hanya ya wuce fadawa na take mishi baya, har shashinsa. Kallon Sarkin gida yayi sannan ya ce mishi. "Ka min magana da Waziri da Galadima da waibai da Chiroma" "Allah ya baka nasara an gama" ya juya ya fita, bayan kamar minti talatin sai gasu, basu shiga ba sai da Jakadiya ta musu iso. Yana zaune a jikin tuntun, ya ɗan yi kwanciyar hutawa. Zama suka yi sannan suka kuma gaisawa. Shiru suka yi kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Me kuka gani da sakon Sarkin Gombe? Sai batun wancan sakaran nasan ya bakanta muku, amma akwai gaskiya a maganar shi. Irin su ba a hana su fadar albarkacin bakinsu. Domin akwai gaskiyar da gyaran da suke sun a cimma." Ya fada yana wasa da wukar hannun shi. Gyara zama Waziri Zakaria yayi tare da cewa. "Duk da na kasance yaro ma kananun shekaru ina ga Baffa ka amshi auren ta ko Baba Chiroma ba Galadima" "Kwarai kuwa Zakaria nima nayi na'am da wannan sakon Sarkin Gombe. Wanbai baka ce kome ba kai da Chiroma" inji Galadima, ajiyar zuciya suka sauke. "Mun amince, sai dai kasan cikin gidan dama akwai kishin da ake na kujeran da kake kai,ka nusar da ita gaskiyar kujeran domin akan ta Yarima yake wannan shaguben" inji Wanbai. "Tun fil azal bana jin zan iya zama dindindin akan karagar domin ga me ita nan. Idan al'umma suka bukaci

Chapter 1 of 39