Share this page
labari ba, kafin Allah da ikon shi ta sauke ta lafiya, inda ta samu yan biyu, Na farkon mace ce tabarkallah sai na biyun namiji ne, haka suka gyara ta da yaran sannan aka gayawa iyayen ta, barci da gajiya ya dauke ta, dan ko kan Yaran bata kuma bi ba, A ranar aka shirya daya daga cikin dakarun da aka bar mata, yaje can masarautan ya gaya musu ta sauka lafiya, Daga nan aka shiga hidimar kula da me jego da Yaranta, bata cika magana ba domin tayi wani irin sanyi, sai dai idan ta ga Yaran tana yawan zubda kwalla, na son su da Tausayin su. Wani irin kaunar sune daram a ranta, musamman da ya kasance Yaran sun dauko ubansu ne, haka yasa ta dauki niyyar sai ta rama abin da aka musu. ** Ranar da ta cika kwana tara da haihuwa a ranar me sakon ya iso ya fadi haihuwar a masarautan Gobir, sabon biki aka dauka na tsawon wunin ranar, su Ammyn da Innayoh a ranar suka fara shirin zuwa suna. Haka a cikin matan gidado ya tura Haimah kasancewar bata da ciki, Bintu kuwa tana da ciki itama ko yau ko gobe, A cikin kwana biyu suka tafiya, lallai sun shirya tafiya suna domin ba karamin kayan arziki aka tafi da shi ba, kwananta goma sha tara suka iso dan haka aka fara hidiman zuwan su, ita kanta lokacin da ta ga Innayoh da Ammyn bata san lokacin da ta fara kuka ba, sai da tayi me isarta, sannan tayi hakuri. Daukar Yaran suka yi. "Wa aka fara haifa ne?" "Gata nan" kakar Anum ta nuna mace. "An mata suna ne?" "Eh taci sunan Amrah shi kuma namijin aka mai da mishi sunan Uban shi" Kallon Anum Ammyn tayi tana kara jin kaunar ta sama da kullum kaunarta mara algus, haka yasa ta kasa boyewa tayi ta saka mata albarka, kwanan su biyar suka dawo Gobir. Bayan wata shida Gidado da Barkindo suka zo ganin Yaran, cikin farin ciki da jin dadi aka karbe su, inda tayiwa Barkindo karba na musamman, sosai tayi ta rawan kai akan Barkindo, inda lokaci lokaci tana wurgawa Gidado magana, bai D'aga kai ya kalle ba, asalima daukar Yaran yayi shi da Nuraim suka fita yawo a bakin kakar ta take jin labarin ai Gidado dan gida ne, ita ce dai bakuwa a cikin su ai kuwa taji haushin sa. "Dan niman suna " Babu wanda ua kulata, shima kuma.baya ta ita domin abin da yake gaban shi yafi karfin kanshi. Satin su daya suka juya abin su, * Bayan shekara biyu. Sanye take da kayan alfarma, tana tsaye ita da Barkindo suna gaisawa. "Kin san bana gari jiya na dawo shine naji labarin zuwan ki" "Eh haka Haima ta gaya min wai baka gari nace mata zan jira ka, ai tunda mu ma zamu kwana biyu anan ya batun iyali?" Shafa kan shi yayi tare da cewa. "Eh toh mutum me kazamin tabo irina baya samun wata mace daga gidan dattawa, dole sai dai ya nimawa kan shi wata daga inda yake tunanin zai samu" Murmushin Tausayin shi tayi sannan ta ce mishi. "Ayya ka godewa Allah da ya barka a raye shima arziki ne, ya Gwaggo Bingel?" "Tana rugar gona, a can ma naga Yar kawu Shagari na fara mata magana dake naga itama kamar ki take amma iyayen ta suka ki" Shiru tayi sannan ta ce mishi. "Kana son ta ne?" Murmushi yayi sannan ta ce mata. "Eh Anum ina son ta" "Shi kenan zan gayawa Ammyn da Baffa'm sai a nima maka auren ta" "Nagode sosai Anum, ina Amrah da Lamido?" "Suna fada wurin Baffa'm" "Toh bari na nufi wurin su." Har zai tafi sai kuma ya dawo. "Na miki laifi me girma don Allah ki yafe min son zuciya ce ba kome bane ya janyo haka" "Duk da ban san me ya faru ba, amma na yafe maka" "Nagode sosai Anum da baki bincika Laifina ba, kika yafe min" Yana kallon su, ran shi ya gama ɓaci amma bai ce mata kome ba, sai da suka rabu, ya hango ta shine ya sauko. Kallon juna suka yi kafin ta dauke kai cikin tsanar shi ta wuce. Cikin zafin kishi ta fisgo ta tare da rike damtsen hannun ta. "Idan na kuma ganin ki da shi sai na baki mamaki" "Haba? Kai ka isa hana ni farin ciki ne? Wallahi baka isa ba, kuma.ba shi ba duk namijin da ya min sai na kula shi, Mugu mara imani Gara da Baffa'm ya hana ka mulki tunda zuciyar ka babu Allah a cikin shi, kuma yadda ka kashe min mijina haka dan kashe ka" Murmushi yayi tare da cewa. "Allah ya baki Sa'a " sannan ya wuce abin shi, Tun daga ranar suka shiga takun saka shi da Anum, shi yana kokarin fahimtar da ita ba shi ya kashe Lamido ba, amma ita kullum kara tsanar shi take yi, haka yasa shi zuba mata ido. A bangaren Ammyn kuwa ita da Baffa'm, yanke shawara suka yi ba tare da sanin su ba, aka tura wakilai aka.nimo auren Anum kakanta da kan shi ya ce a je wurin dangin Ubanta da suke ruga, Baffa'm da.kan shi ya shiga har rugan ya nimawa Gidado auren Anum, jikin mutanen rugar na rawa aka bashi ya kuma nimawa Barkindo auren Asma'u yar Kanin Bingel idan ya gaya musu maganan da yayi tasiri a zuciyar su. "Idan baku rufa mishi asiri Ba, waye zai rufa mishi? Kuna ta hana shi bayan Allah bai hana shi ba, don Allah kar ku ki shi bai da laifi." "Mun shi ba sai ka ce kome ba, wallahi mun gode sosai" Suka fada, Bayan saurin auren ne aia fara shagali na fitar hankali, duk da Gidado bai sani ba, ana cikin shagalin iyayen Anum suka.kawo kayan da ake na amarya, aka kuma gaya mata bori da rikici babu wanda bata yi ba. Babu wanda ya bi ta kanta, har aka kai ta shashin ta na da can kuma duk yafi ka sauran matan girma, lokacin Haimah tana goyon Yaron ta me sunan Baffa'm, Bintu kuwa ta yaye yarta me sunan Ammyn tana laulayi. Ai kuwa Gidado yana ganin takaici domin daina cin abinci tayi tana kwance, Innayoh tayi tayi amma fir taki. Zuwa tayi ta gaya mishi taki cin Abinci. Yana cin abinci ne a gaban Bintu ya mike abinshi yana wanke hannun sannan ya nufi sashin ta, sai Bori take. Tana ganin shi ta fara cewa. "Wallahi karka tab'a ni idan ba haka ba zan kashe kaina" "Akwai guba me kisa a hankali akwai wanda yake kisan farar daya akwai kuma wanda ba sai ka wahala na wuka" ya dauki kunun tsamiyar ya rike yana fifitawa, sannan ya cire alkyabbar ya janyota da karfin tsiya ya murde ta, sai da ya bata ta shan ye tass, har da gyatsa sannan ya sumbaci kunnen ta, zuwa bayan ya, hannun shi ya kai tare da yamutsa na Fulaninta ta, fashewa tayi da kuka. Sannan ya kyale ta. Haka zaman su ya kasance, shi kan Barkindo yana can ana shagali da amarya. A hankali ya zama Anum idan taki cin Abincin toh wallahi Gidado zai bata da karfin tsiya kuma yana gamawa ya murzata son ran shi, ganin haka yasa ana kawo mata abinci take ci bata son yazo ya rabe ta. Wannan salon ya bawa Bintu haushi, Haimah kan babu ruwan ta,zuba mishi ido tai musamman da taji labarin shi ya fara son Anum aka bawa Lamido, sai ta saka a ranta babu ruwanta da tashin hankali duk abinda ya ga yayi mishi wallahi yayi sai dai zata gaya mata gaskiya ta bar wahalar da shi mahaifin tane ya kashe mata Lamido. Amma koda ta samu Anum kin bata fuska tayi, shi kuwa a bangaren shi, yanayin rayuwar gidan shi ya sauya, sannan ya hana a kaiwa Anum Yaran ta, suma dake basu san kome ba Abba suke kiran shi dake suna yawan ganin shi tun basu yi wayo ba yana zuwa musu duk bayan wata uku. Anum tayi bori tayi fada tayi rigima, karshe haka ta hakura sai dai ranar da ya nime ta, tayi kuka domin bata iya boye Abu ba ta ce mishi. "Ko me zaka yi bana son ka, bana kaunar ka, Sarakina nake so" Da wannan ya hakura da ita ya zuba mata ido, har tsawon watanni shida, babu abinda ya haɗa su, Sai dai ya fita harkanta inda ya saka matan shi a gaba yana ririta su, bai D'aga kai ya ce mata dan taki bashi hakkin shi ba ya tsane ta ba a'a sai ma kauda kan da yayi, watanin su takwas suka tafi Somalia, a nan yar karamar hatsari ya faru, inda har ya kai ga sun kwana daki daya, gado daya. Duk yadda yaso kauce mata, amma haka bai samu ba, sai da ya ratsa tsakanin rayuwar ta shima yaji yadda kome yake, taci kuka kamar ranta zai fita domin a gidan kakanin ta abin ya faru, duk yadda taso kar ta kwana daki daya da shi. Washi gari da bori ta fito babu wanda ya kulata, sai shi din shima kawai rarrashinta ta yake amma ina. A ranar da kakan ta fahimci wani abu ya shiga tsakanin su, musamman yadda taga shi Gidado yake rawan jiki akan Anum din ta shiga hada mata wasu maganin mata na gyaran jiki, wanda tayi ta dura mata , dare nayi suka Kore ta wurin ga wani fitinannen turaren da yasa shi sake lazimin da yake, ya turmushe yar banza ya sha masifa da rashin kunya, tsiwa kuwa ba iyaka, haka ya bar ta cikin takaici da Haushin abinda ya mata, shi kan ko cikin dare sai da ya kuma, tayi kuka har ta godewa Allah. Ganin abin kunya zasu yi, yasa shi tattara ta suka bar garin amma kafin su isa gida ya murje ta son ran shi, suna dawowa gida ya watsar da ita ya shiga tarerayar matan shi, suma babu laifi a dakin Bintu ya fara sauka dake a dakin Haimah ya fita, haka ya kwashi kwana biyu, amma bawai dan ya manta da Anum ba, maganar gaskiya Anum daban ce a cikin mata, sannan ya koma dakin Haimah, a daddafe ya dawo dakin Anum zata mishi iyayi ya ce. "Kin san mata biyu gare ni rike abin ki bari na tafi wurin matana" "Sai me maciyi amana ka kashe min Lamido ne dan kawai kayi ta kwanciya dani sai kazo kayi tayi" Murmushi yayi mata kawai, ya dauki kayan shi ya bar mata dakin ta, Haka suka tayi babu dad'i, karshe Haima ta same ta ta kwashe kaf abinda ya faru ta gaya mata, sannan ta ce mata. "Idan yayi miki, ki kyautata mishi idan bai miki ba zaki iya kome ba kashe shi ba idan kin so ki kashe har da mu, wallahi kin yi butulci, ko Ni da Mahaifina yayi laifin ban tsane shi ba, shi da babu laifin da ya miki kin tsane shi. Ba karya bane ki tambayi Innayoh Gidado ya fara son ki, kafin Lamido. Ni kuma Lamido naso, nayi fatan da shi na samu, da na samu madadin shi na hakura, ki godewa Allah duk abinda ya faru a masarautan nan duk akan ki ne ba akan kowa ba, domin a mallakawa Barkindo ke aka kashe Lamido, sannan Gidado da aka bashi mulki ya haramtawa kan shi ya gwammace ya zauna a matsayin me kare kujeran lamido karami. Kafin kasamu wanda zai so ka shine wahala idan ka same shi sai ka rike shi hannu bibbiyu. Ya rage naki kiyi tunani akan rayuwar auren ki" Daga haka ta fita ta bar ta. A ranar tayi kuka, tayi danasanin abin da ya faru amma taya zata manta da Lamido? Dan haka ta tattara ta nufi cikin gidan,.inda ta samu Innayoh da maganar bata boye mata ba, ta gaya mata gaskiya, dan haka ta saka a ranta zata rike auren ta da daraja da kima amma batun so ta gama ta rufe zuciyar ta. Haka kuwa ya kasance, shi kan shi Gidado ya ga canji, amma bai kawo haka ba, sai ya dauka ko ta fara son shi ne. Bayan wata biyu ta fahimci tana fama da cikin shi, a ranar tayi kuka kamar ranta zai fita domin cikin yazo mata bazata ne, haka tayi ta kokarin boye cikin har ya bayyana kan shi. Tasha tsokana a wurin shi inda ya daurawa cikin soyayar duniya baki daya. Bayan wata bakwai ta haifi Yaran ta mata tagwaye gwanin ban sha'awa, haka yasa Ammyn ta yarda da cewa rabon Yaran Yaran ne ya kashe Lamido domin yadda suka zo nan dole ya mutu ta ina zasu zo tunda a jikin Anum suke, Tsakanin ta Bintu shekara daya, Yaron da ta haifa, haka akayi suna Yaran suka ci sunan Zahirah da Rusailah, kwanan su Arba'in Haimah itama ya haihu, aka saka suna mahaifiyar ta. Haka suka cigaba da tafiya, wani abin mamaki shine gidan Gidado kamar masu gasar haihuwa, domin dai bayan shekara daya da rabi Anum ta kuma Haihuwar Ya mace aka saka sunan Innayoh. A'isha, Bayan sunan A'ishah ne wacce zasu kirata da khairi. Gidado ya zo ya zauna yana kallon ta yadda take bawa Yarinyar abincin ta. "KALLABI a tsakanin Rawuna, matar sarki Lamido Matar Galadima Gidado, Uwar Lamido Mamar Amrah, Innar Zahirah Babar Rusailah. Ummin A'isha Khairi, Macen da rayuka suka yi tawo mugama akan ta, Gidado yana niman yarda da amincewar soyayyar ta " Kura mishi ido tayi sannan tayi murmushin ƙarfin hali ta ce mishi. "So daya tak nayi bayan shi Gidado bai da muhalli a zuciyar Matar zaki sai dai zata shimfida dukkan rayuwar ta domin Biyayya " "Haka ma ya ishe ni Nagode da Alfarman da aka min " "Ina neman Alfarmar ka" "Ina jin ki" "Don Allah ka amshi mulkin nan kai ya dace da ka rike." Amsa yarinyar yayi ya zauna a gefen ta. "Kiyi hakuri, wallahi na yafe mulkin har abada ina kare shi ne domin Lamidona." "Dan nace bana son ka?" "Ko daya wallahi bana son raba kan Yarana ne, zama dani da kika yi ma ya ishe ni " Da wannan suka ajiye kome.. Bingel kan bata yarda da Allah ba, garin bin bokayen da zasu mata aikin da za'a kashe Anum ta hadu da wani shaidanin boka ya tsafeta yayi ta aikin bokancin shi da ita. A bangaren Barkindo ya cigaba da rike Wazirin mahaifin shi, sannan matar shi Yaran ya biyu, Me sunan Lamido da me sunan Baffa'm. Gidan Gidado kuwa Alhamdulillahi domin kowacce tasan darajar kanta babu kishi babu hauka, sai kyautatawa mijin su kayan Yaran su a hade yake da juna. Wannan yasa zaman lafiya ya wadatu a gidan. Mutanen rugar gona sun fahimci Anum haske ce a rayuwar su domin bata zama yar kaxa samu kaki dangi Ba. Tana nata kokarin akan su. Haka Innayoh ta zama kamar Uwa kome yanzu da ita ake yin shawara har shima Baffa'm, ta ko ina sai san barka. ******* ALHAMDULILLAHI anan na kawo karshen Kallabi a tsakanin Rawuna, labarin Masarauta Gobir kona ce daular Gobir wanda ya kafu tun kafin zuwan shehu Usmanu danfodiyo, tashin hankali da aka gani a cikin labarin ya faru a daular, tafiyar Aminatu ya faru amma ba mace bace ta tafita namiji ne, Daular Gobir sun yi fama da sharrin cikin gidan sosai dan haka a nan na kawo karshen labarin NAGODE SOSAI Allah ya bar zumunci ya kuma haɗa mu a wani labarin da ban dan sunan shi ba.... Fatan Alkhairi Insha Allah next labarin True life story ne amma ban mishi suna ba kuma.zai zo FREE BOOK 🤣 InshaAllah... Mai_Dambu Taku ce, kuma nawa ne.... An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 39 of 39