Share this page
dud duniya bata da wanda ta yarda da shi sama da kai? Meye ya faru wancan lokacin! Ina son sanin me ya faru! Domin idan na d'aga takobina sai na karar da duk wani makiyin Ammyna" "Yaki dan zamba ne, idan har kanq son sanin me ya faru wannan ranar sai ka shirya sai ka shirya sai ka ajiye zafin ran nan sai ka shiga cikin gidan sarautar sai ka binciko me ya faru da wannan zan iya ce maka Allah ya baka sa'a, na hakura da kome ne domin ita na ki amsar ku ne domin rayuwar ku da a can aka haife ku baka isa ka rayu cikin salama da aminci ba, a yadda naso ganin ka haka na ganka, amma bana son ka kuma tambaya na me ya faru, amsar ka yana can a can zaka same shi" Kakarin amai suka ji Anum tana yi, kallon kofar yayi sannan ya mai da hankalin shi wurin mahaifin shi da ya mike shida galadima, suka shiga cikin dakin. Kokarin amai take amma ta kasa, sai mika take tana rike cikin ta. "Galadima babu wani abun da za a mata ne?" Kallon kofar yayi sannan ya ce mishi. "Bana jin ina da maganin da zan iya bata, duba bayan ta an dake ta da wani irin guba ne shi yake sakata haka." Jikin Baffa'm yana rawa ya fito waje ya same shi zaune yana kallon kasa, yayinda yake zana kasa da karan dawa, zana da'iran Masarautar yayi sannan yayi ta fitar da wasu irin kofofin da ya fahimci suna cikin masarautan, tsayawa Baffa'm yayi akan shi. "Gidado ne ya baka labarin yadda masarautan yake?" D'ago kai yayi sannan ya mai da kasa, yana kara cire wasu kofofin da suke jikin masarautan. Wannan hali na Lamido da ban mamaki yake dafa kafadar shi Baffa'm yayi sannan ya bude baki zai kuma tambayar shi, taran numfashin sa yayi yana faɗin. "Wata mata ce ta dauki wancan mahaukaciyar na shiga na daukota" Daga haka ya tsuke bakin shi, yana cigaba da zana kome. "Yahanasu Bingel ce ta mata wannan aikin? Subhanallahi toh ya zamu yi da ita guba ne a jikin ta fa?" Nan ma shiru yayi yana kokarin fitar da wani abu ya ce. "Idan akwai danyen madara a bata da garin sabara" Ya cigaba da aikin shi, fita yayi ya dauko kayan shi a jikin dokin shi yq shiga rubutu babu ji babu gani, zuwa yanzun Baffa'm ya fara gano halin Lamido Hassan, tab ya fada a ran shi yana kara jin kaunar shi. Akan uwar shi ya tsawaita magana, akan kowa kuwa maganar takaitaccen ne. Fita Sarkin gida yayi ya nimo danyen madara ya kawo aka hada aka bata,.da tayi ta sheka amai sai da tayi wani irin haske. Fitowa Galadima yayi sannan ya zauna kusa da Lamido. "Lamido tun kafin kazo dan uwanka gidado ya sanar mana, sai dai bamu tsammaci ganin haka ba. Akwai abubuwa dayawa wanda nake son mu yi magana a kai, tashi muje ga daki can" Mikewa yayi ya bi bayan galadima, har cikin dakin, sannan ya amshi kayan shi ya ajiye mishi a saman wani gadon kara, zama suka yi sannan ya kalli Galadima. "Yanzu ka huta daga gobe zamu fara aikin da zai zame mana maudu'in nasara" Gyada mishi kai yayi, ya cigaba da abinda yake. Abin mamaki kallon shi yake cikin wani irin yanayi, mulkin da yakw kewaye da shi, kasaita da miskilanci, nutsuwa da mai da hankali akan abinda yake. "Baffa akwai wani abu ne.?" "Allah ya baka nasara mai martaba! Babu wani abu umarnin ka nake jira na fita" lumshe idanun shi yayi na wasu dakikai, kafin ya ware su akan kofar dakin. "Allah ya baka nasara a huta lafiya" ya fito yana kakkabe rigar shi. Haduwa suka yi su uku suna kallon kofar dakin shi. Kallon kofar Baffa'm yayi a karo na babu adadi ya ce. "Daga ni har uwa shi babu wanda ya daurawa kan shi mulki da alamu dai mune muka.damu da mulkin shi kuma mulkin ce ta dame shi." Hango shi suka yi ya goya hannu a baya yana kai gwauro ya mai mari, fitowa yayi sannan ya ce. "A cikin masarautan yan majalisar sarki nawa ne? Ina son sunayen su kafin faduwar rana, sannan ina son sanin halayyar su domin cimma abinda ya kawo ni" "An gama ranka shi dade!" Inji Sarkin gida, a take suka dauko tawada da alkalami domin Baffa'm baya rabuwa da su. Kafin sallah azahar an gama rubuta mishi kome, sannan suka mika mishi bayan ya ja su sallah, fita yayi wajen gari ya nimo abinda zasu ci, a hanyar shi ta tafiya yaji ana bada labarin abinda ya faru a masarautan Gobir jiya. Bai wani ji ko dar ba, asalima kamewa yayi ya nufi farautar shi bayan ya gama ya dawo, da kan shi ta fede barewar ya gasa musu, sannan ya koma gefe yana kallon waje, shigowar Sarkin gida amatukar rikice yana yarfe zufa. "An saka lada domin kamo wanda ya balla kofar birnin" kallon shi Baffa'm yayi ya ga ya kauda kan shi. Cikin sand'a ta fito zata fice, Baffa'm ya ce mata. "Ya jikin naki?" "Da sauki" ta fada muryan ta na rawa. "Anum karki fita domin an saka a kamo ki a mace ko a raye?" "Wayyo Allah na, toh meye nayi kuma?" Ya tambaya tana jin Kwaila na cika mata Idanu. Share ta suka yi kowa ya kama gaban shi. Bayan sallah Isha suna zaune ta dama musu fura da Sarkin Gida ya sayo a rugar su. A hankali Galadima yake mika mishi wasu bayanai. "Ina ga kamar ka fara ta kan Chiroma!" "Ka gaya min labarin abinda ya faru ta nan zan iya kamo bakin zaren." Mikewa Baffa'm yayi domin zasu fama mishi ciwon da yake ran shi ne, a hankali galadima ya shiga bashi labarin abinda ya faru. Har zuwa inda ake zargin Aaminatu da cikin su. "Mutumin da ya aikata haka a ranar da aka shirya kashe shi ta gudu, sannan Bello yaki amsa mata ne Sabida yana amsa mata zasu iya kashe dayan su,.matukar ya amince cikin na shi ne. Wallahi bai ki Aminatu dan abinda aka fada ba,.sai dai matukar tana raye a cikin masarautan ba zai iya kare ya ba" Anum da bata da kwarin zuciya sai kuka take tana kallon lamido da ya bata tausayi kamar me, amma fir babu alamar fushi bacin rai ko damuwa akan fuskar shi mai hatta idanun shi basu nuna tashin hankalin shi ba, kallon shi take da dukkan zuciyar ta, tana jin yana mata wani irin bugawa a duk lokacin da ta kalli fuskar shi, wani irin abu yana yawo akan ta, Tausayin shi da kuma na iyayen shi suna kara samun daraja da matsuguni a zuciyar ta. D'ago kai yayi, idanun su suka sarkafe da juna, tsuke fuska yayi alamar bai son wannan kallon. Sunkuyar da kai tayi kasa, sannan ta mike tsaki yaja. Tun da ta shiga dakin ta kasa barci, tana leken shi. Sun jima suna hira, da Galadima kafin suka yi sallama ya wuce dakin shi. Fitowa yayi ya ganta zaune tana.kallon kofar shi tayi nisa cikin tunani, alola yayi ya barta a wurin. Wa shi gari suka tashi da wuri shi da galadima, suka nufi kasar sokkoto, bayan gari ya waye ta fito tana kallon kofar dakin shi. Cikin sand'a ta leka kofar. "Kina niman shi ne?" Da sauri ta juya tana kallon Sarkin gida. "Baba sarki kawai ina mamakin taurin zuciyar shine jiya kaga dai yadda Baffa'm ya mike yana jin babu dad'i amma shi ko a jikin shi " "Waye ya gaya miki bai ji ciwon abinda aka gaya mishi ba?" "Ina fa, kawai ni zan baka labarin abinda na gani. Bai da imani zuciyar shi bai tausayi, zuciyar shi tana buɗe ne domin kai hari ko kare kai akan Idanuna yayi ta sare mutane yana karya su, dube hannuna? Karya ni yayi shi yasa ma.kasa barci ina mamakin da kuma hasashen mutanen da suka yiwa Ammyn mu rashin mutunci, wallahi kareraya musu katarya zai yi!" Baffa'm da yake daki fitowa yayi yan kallon ta kafin ya ce mata. "Me ya faru a ina kuka hadu?" "Baffa'm ban san a inda muka hadu ba, sai dai na farka naga ya kai ni tantin shi, daga nan kuma wasu suka kawo min hari ya kare ni, sai lokacin da Gwaggo Bingel ta saka aka kama ni jiya aka kai ni cikin masarautan ya shiga ya dauko ni bayan ya kar-karya musu hannaye da kafa, Akan Idanuna ya rike hannun arnen daji Baffa'm sai da suka gudu dakan su." Shiru suka yi itama kamar wacce aka matse bakin ta take ta zuba. "Kenan yanzu haka an san fuskar Lamido?" "A'a Baffa'm ai yaki sakewa suga fuska shi, na rantse duk a rufe yayi ta yakin nan kawai Baffa'm karka ce mishi ni na gaya maka wallahi karya min kafa zai yi nan gaba." Cikin zolaya sarkin gida ya ce mata. "Ai tunda kika bada labarin nan kamar a kunnen shi, domin ko bamu gaya mishi ba dole zai sani" "Baba sarki taya zai sani bayan ba a gaya mishi ba? Ni dai zan tafi!" "Toh ai zai biyo ki har gidan ku" da gaske ta razana kawai ta fashe da kuka tana faɗin. "Don Allah karka gaya mishi wallahi ban san me yasa na gaya muku" "Jeki Anum tunda kina tsoron shi" Fita tayi kamar munafika tana ajiyar zuciya, da tasan za ayi haka wallahi da bata tada fada ba. ** Har gari yawaye ana jin kara da saurin algaitu, abinda ya saka dayawan mazauna birnin tsorata kenan, suka ki fitowa daga gidajen su domin ba a tab'a jin haka ba, a baya bayan nan amma wani tsoho ta tabbatar kimanin shekaru dari hudu da suka gabata kafin shigowar musulunci anyi haka akan sarkin da aka yi gardama akan shi, har aka kori ahalin shi. Lokacin da Sarkin ya dawo masarautar haka ce ta faru daga nan aka fara samun matsala da Sarkin da yake mulki, sannan ya kara da tarihi zai mai-maita kan shi, fatar su daya shine kar a zubda jini akan sabon Sarki domin haka zai iya sakawa mulkin ya zama ta jinsi biyu ne domin akwai masu bukatar haka. Shiru kowa yayi kafin suka ce mishi. "Idan har sabon Sarki ya hau ba azubda jini ba haka yana nufin an samu adalci kenan" "Eh haka ne amma dole a fara amfani da niman agaji domin kare shigar su cikin mulkin" -- "Wayyo Allah!" Ya farka yana ido tare da rike kunnen shi da yake mishi kamar an raba shi da dodon kunnen shi. "Innah! Wallahi ba zan tab'a kyale shi ba sai na dauko Anum na aure ta" "Aikin banza kayi min shiru sa'an ka idan ma baka girme mishi ba, yazo ya mangare ka, shine ka fadi kamar wanda aka sare kan shi wawa Lusari da ana cewa kai Lusari ne ban yarda ba, sai yanzun sakarai tunda ta hudu da wannan Tsinannen da ya sani yin dunguren masa sau biyu, ka sani babu kai babu ita domin kowani lokaci zata iya sanadin da zamu bar cikin masarautan nan wawa kawai" "Taya? Idan Anum ce zan saka Haima ta dauko min ita nan da jibi kawai kwantar da hankalinki" Yanzun ta kara tabbatar da cewa kande ta haifa sakarai shashasha barekata Lusari mara amfani kullum dakikiyar ƙwaƙwalwar shi bata ja cikin takaici ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana ji kamar ta kefe dan banza da kari. "Allah wadaran naka ya lalace.... 🙄🤔 You Bingel me kike nufi Baby Barkindon ne ake mishi wannan cin zarafin?😭😿🚶🏾‍♀️🤣😂 Yau yan team Barkindo hankalin su zai tashi. Team Lamido Nasan sarai fatar nasara zasu mishi. Team Anum kuma fa? Ina team Haima? Ina Team Dijah da Gidado... #Mai_Dambu.. [6/14, 9:35 PM] Black Girl: ƘALLABI...! A Tsakanin Rawuna EWF https://www.wattpad.com/1236043581?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=shN0izK%2BvPG7my4lHE%2BY%2Bwcqf7lTxjS9g7dWSvA39z5lZtMTJVaXZiiy50m6J162o1IYDWtfUqMhQfJY9a7bWqJYH1H5qtkKFGKxwAHu%2BAs8S8b8Z%2BnwblglajaIyFmJ BABI NA HAMSIN DA TARA "Sakarai dalla matsa min, kasan waye shi? Idan ya dawo masarautar nan babu wanda ya isa kwatar ka domin idanun shi sun nuna ba iya fushi yake ba da aka tab'a ta fansa ce a ran shi!" Dan haka karka sake ka janyo mana ita" "Toh ina son ta ko kashe ni zai yi wallahi ina son ta!" Ya fada yana me barin dakin ta, ya nufi dakin shi. * A fada kuwa shiru suka yi aka rasa wanda zai iya bayani. Can Waziri ya ce musu. "Ya kamata a kama wanda yayi wannan takadarirrancin sannan bai dace ace masarauta guda a samu wanda zai mata wannan aika aikan ba, gaskiya yq ka mata a dauki matakin da ya dace" Kallon shi Yakubu yayi kuri kafin ya ce mishi. "Dalla rufe mana baki, me yasa baka fito ba lokacin da ake tashin hankali kai ga ka nan dan iya? TOH babu wanda zai kai kan shi ga mallaka idan zaka iya madalla ga hanya sarai kunsan wanda yake janyo mana jidali zaku ce ayi shirin yaki, yakin taci kaniyar ta" ya fada tare da mikewa yana Banka musu harara,shi fa tun ranar da aka kuskure shi yake jin Haushin kowa,gani yake kamar da gayya aka mishi haka, sannan kuma babu wanda yace a yi shirin yaki dan an kawo mishi hari sai dan an karya kofar birnin yaga shegen da zai shirya yaki babu sanin shi. Har ya isa bakin kofa ya ce. "Dan munafunci ran ku yafi raina ne?nan aka shigo aka min yankar mutuwa baku tsaya min ba amma dake kunji labarin an shigo zaa yi barna kun taso da Kawuna kamar kadangaru, naji wani dan banza ya fita shirme akan karya kofa da akayi" Nan ya zauna yana masifa kamar zai make su, sannan ya bar su sake da baki. Zaune yake a gaban bokan shi yana kallon ƙasa. "Har yau baka samu nasarar hada ta da danka ba? Lokaci yana ta kurewa, domin an yi shigar farko shiga na biyu ba zai maka dadi ba, ka tabbatar ka tura shi gare ta, Zakin ya dakatar da al'amarin ta, idan aka kuma samun damar ya mallake ta sai dai ka gudu domin akwai matsala" Cikin kaskantar da kai ya ce. "Uwar Yaron taki nutsuwa duk yadda naso fahimtar da ita taki barin yarinyar ta rabe shi." "A'a kodai taki Yaron ta rab'i Yarinyar? Amma ita yarinyar tana na da nata gudunmawar matukar kasamu kan ta burin mu a samu kanta kawai na wai a tirsassata ba" Gyada kai yayi yana kallon kasa, kafin ya ce. "Babu wani hanya ne?" Zane yayi ya kuma gogewa sannan ta kuma yi ya goge kafin ya D'aga kai yana kallon sama, kallon yanayin taurarin yake kafin ya ce mishi. "Hanyar da muke da ita bai zama dole ba, domin ita ƙaddara rubutaccen al'amari ne zai faru kuma zai kasance, sai dai mu kara lullube wani abun cikin sauki zamu same shi. Tabbas akwai tarnaki da kura, akwai abinda na gaza fahimtar shine ita din waye zai ja linzamin ta? Ba a kutse a ƙaddara da nayi na sauya mata, domin a lissafin da yake nan Danka yaja da baya, ka gaya mishi ya janye kudirin shi har kaima, domin guguwar da take kusanto ku ba karama bace, burin ka na can baya ba zai kammala ba sai ka sake tattara kayan da ka watsa ka shiga a kuma damawa da kai shine zaka iya tsayawa dan ka, amma mulki ba naka bane" "Boka akwai wani abun da yake shirin faruwa ne?" Ya tambaye shi a kage, "Eh akwai mara dadi mara kyau mara kyan bada labarin shi, idan ka sake aka kuma gano haka toh ba makawa akwai abinda ba zan yi fatar faruwar shi ba kaje nan da wasu kwanaki ka dawo" ** Yau kwana biyu da tafiyar su Lamido da Galadima burin su na sanin akan yadda zasu samu hadin kan sarakunan yankin ne babban damuwar shi. Yana son lallai ya koma Borno ya gaji da zaman nan babu dan uwan shi da Ammyn da Innayoh,. Duk sai yake jin kamar bai da lafiya, a tafiyar su da ya kara fahimtar waye mahaifin su, sannan ya kara samun wani abin da ya rasa a can wato ilimi akan mulki. Domin koda suka je wurin Sarkin sokkoto, ya nuna mishi koda ya bashi goyan baya dole sai ya koma masarautan Kano anan zai iya samun damar da yake bukata da zai iya fuskar ta masarautan Gobir da mutanen ta. Sannan akwai sarakunan yankunan dole ya nime hadin kan su, idan yayi haka zasu taimaka Mishi. Akwai kimanin sarakuna goma sha biyar da suke zagaye da Masarautar, sannan idan suka samu goyan bayan su, kamar ya samu mulkin ne, dan haka kwanan su uku suka dawo. -- Shiru suka yi suna kallon Baffa'm da ya nutsu yana.sauraron galadima. "Ina ganin mu fara da sarakunan yankin nan mafi mu shiga fada, idan muka shiga fada sauran ba zai bamu wahala ba, amma nan da kwana uku zan binciko matsalar da ake fama da shi a masarautun kewaye" "Amma ina jin tunda kuke ta shirin ku nan da son komawa gobir kun taɓa daura akan Bingel da Gambo? Tare da Matar Chiroma? Ina da yakinin sun kasance sun san kome!" Inji Sarkin gida, murmushi Lamido yayi sannan ya mai da hankalin shi kan abinda yake sannan ya ce. "Zargi haramun ne" Juyawa suka yi tare da zuba mishi ido, Lumshe idanun shi yayi sannan ya kura a kasa, yasan suna nuna karin Ilimi akan haka. "Idan muka shiga jikin mutanen fadar zaka samu basu da wani karfi sai abinda aka saka su, idan na fahimci abinda yake tafiya shi kan shi Sarki Yakubu ba shi bane sarkin Sarkin yana tsakanin su yana kuma mulki cikin takatsantsan yakubu da sauran mutanen bauta mishi suke" Gyara zama suka yi, tare da kallon shi. "Me kake nufi?" "Chiroma ba makiyi bane, fin karfin shi aka yi haka kuma bingel tazo da nata matsalar aka mata romon baka, kenan idan muka ce zamu shiga kai tsaya samu tab'a kan me uwa da wabi, Abu maki Alkhairi shi ne mu fara bincike da kyau mu nutsu sosai. Kar mu shiga jerin marasa adalci" Cike da mamaki suka bi shi da ido, me yasa tuntuni basu fahimci haka ba? "Assalamu alaikum!" Tayi sallama da raunanin murya, wanda yake nuna alamar tsoronta,domin leken su take ya kai ayar maganar kamar ance ya d'ago kai ya sauke akan ta, tamke fuska yayi sam bai san me yasa take addabar rayuwar shi da idanun ta me kama da na bududdugi ba, dan haka ya tsuke bakin shi kamar baya cikin cikin gidan, muryan ta na rawa ta ce. "Baffa'm ina wuni ya kwana biyu? Baba galadima ina wuni, Baba sarki ina wuni?" Kasa kasa tayi da murya ta ce. "Hamma Lamido ina wani" banza yayi da ita, kafin su gama amsa mata cak ya bar wurin. Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon Baffa'm. "Lafiya lau Anum tunda suka tafi sau yau kika zo" Sosa kanta tayi sannan ta ce. "Baffa'm hannuna ne yake kumburi, ka gani shine ban fita ba" Kallon hannun yayi sosai kafin ya ce mata. "Me yasa baki kawo an duba miki ba, galadima ware hannun mu gani" Zama tayi galadima ya fara ware hannun yana gama gani ya ce mata. "Waye ya miki daurin?" Juyawa tayi ta kalli kofar dakin sannan kasa kasa ta basu amsa, "Toh kuwa shi zai duba babu wanda zai duba hannun, Lamido!" "A'a ko zata dai shiga ya duba" Kamar zata yi kuka ta ce. "Baffa'm!!" "A'a galadima ya fito dai ya duba mata a kan idanun mu!" Dan dole suka kira shi ya fito, Fitowa yayi ya kalle ta, sannan ya samu wuri ya zauna, ya kalle bayan ya yarfa mata harara kasa ƙasa. Matsawa yayi gaban ta yana faduwa, ji take kamar zuciyar ta zai fado. "Na gani" ya ce mata, mika mata hannun yayi, ya fara dubawa, bayan ya gama duba daurin ya ce musu. "Idan na mata taje tayi wasan banzs hannun ya rube yanke shi xan yi da takobina" ya fada yana kara tsuke fuskar shi. Sannan ya mike zuwa ciki ta fito da kayan aikin shi, wani hade rai yayi domin akwai salon mugun a daurin da zai mata, kama hannun yayi ya rike sannan ya d'ago yatsar shi biyu ya tohfa addu'oi, sannan ya saka ya fara murza hannun zufa ne ya shiga karyowa daga duk wani gabba na jikin ta, ilahirin kofofin gashin jikin ta ya bude sosai, murza hannun yake cikin keta domin ta gane gobe karta kuma zuwa ta gotar da ciwon, ta takarkare ta fasa wata irin ihu, tare da mikewa ta zube a jikin shi, kanta na tsakanin wuyar shi daya hannun ta na kan kirjin shi daidai wurin zuciyar shi. Cikin ko in kula ya cigaba da aikin shi, yana gamawa yaji sautin zuma da suka fara kokarin isowa gare ta, bai fasa abinda ya saka a gaban shi ba, sai da ya gama sannan ya fara kokarin ture ta. "Ke tashi bana son Hauka" "Aikuwa ga zahiri daga kai har ita ba a san waye mahaukaci ba, domin ita dai bata da alamar rai kai kuma da ranka kana shirme." Birkitotta yayi yaga kumfa na fita a bakin ta. Shi kan ya gaji da jidalin yarinyar nan, tunda ya hadu da ita yake dawainiya da ita bai san ya zai yi da ita ba wallahi. Kamar ya make fuskar ta ya dangwarata sannan ya tafi ciki ya dibo ruwa ya watsa mata, wani ajiyar zuciya ta ja sannan ta fashe da kuka. "Taya aka yi kika fama ciwon ki?" "Baffa'm wasu ne suka biyo garin ja gudu ne na fama ciwona" girgiza kai yayi sannan ya koma daki ya kwanta. Ta jima a gidan sannan ta bar gidan, tana fita ta juya tana kallon gidan kafin ta fara tafiya, a matukar razane, domin har ga Allah ta fara tsorota da mutane, musamman masu bibiyarta motsi taji ya juya a hankali bata ga kowa ba, tana juyawa ta fasa wani irin kara ta tafi zata fadi taji an tare ta. Jikin ta ne ya dauki rawa ta juya tana kallon Lamido da ya biyo ta, idanun ta ne suka cika da kalla sannan ra kalli Barkindo da yake tsaye, yana mata kallon mamaki. Rike hannun ta Lamido yayi me lafiyar ya janyota su tafi, ya rakata Barkindo ya sha gaban shi. "Sake min hannun ta" Banza yayi da shi ya janyo hannunta, zasu tafi bisa kuskure Barkindo ya riko hannun me ciwon, bata san lokacin da ta tafi luuu xata fadi ba, tare ta lamido yayi yana kallon fuskar ta yadda idanun ta suke shirin kafewa ya daka mata tsawa. "Bude min idanun ki" Ajiyar zuciya ta sake tare da fashewa da kuka tana me cusa kan ta a kirjin shi, d'ago kai yayi ya zubawa Barkindo idanu a hankali ya kai hannun shi ya matse kanta a kirjin shi da ƙarfi sannan ya halkantu da shugaban ƙaramar hukumar wandon Barkindo ya kai mata wani irin duka da sai da ya zube a wurin sumamme, d'ago kai tayi ya ce mata. "Kul!!" Mai da kanta tayi, tana jin sautin bugun zuciyar shi, kamar wanda doki ke tsere a katon fili me tazarar tsiya, a hankali ya janye ta daga jikin shi,itace mace ta farko da ya jibanci al'amarin ta bayan mahaifiyar shi.. cikin wani yanayi irin yanayi take kallon shi, suna tafiya fir yaki kallon ta asalima kamar bai damu da kallon da take mishi ba, tafiya take bata kallon gabanta, tana gab da hada kanta da bishiya ta saka hannun shi, ta hada kai da hannun shi. "Wash" wani fitinannen kallo ya mata ta shiga hankalin ta. "Nagode" banza yayi da ita suka cigaba da tafiya, har sun kusan gida, yaji ana ihu a bayan su, kanta yayi suka shige kasar wata bishiyar maje, a hankali ya kaita jikin bishiyar sannan ya toshe mata baki da hannun shi yana kallon ko ina na cikin duhuwar, kanta ta daura akan kirjin shi domin tana son sake jin bugun zuciyar shi, wanda yake sanya nata bugawa sama da sau dubu sau dunu, ture ta yayi yana hararanta, komawa gefe tayi tana me jin kamar tayi laifi. Sun jima a wurin har ya ga dai niman su ba zai kare ba, kawai ya fito... *Gaskiya gobe ku yi hakuri wallahi mura ya takura min kamar me na rasa yadda zan yi ga ciwon kai da zazzaɓi gobe zan huta jibi Insha Allah zaku ji ni Nagode da karanta labarin Kallabi 🥰👋🔥🤌🏽😍💪🤩* #Mai_Dambu [6/16, 12:42 PM] Black Girl: https://www.wattpad.com/1236555473?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=cw%2FwZI5fr%2BeCpKfQMrCUOvBgyawuQjW5VgjseXQmh%2F1r2dIBYDlPRF3rE2kTkA9CLjxHR0Mgdqhj1faEFF6kr%2Fi4jGRWzuom4xw%2FK%2BR3%2BkbLuwiAa2ZpPkiIjVh6DjLe KALLABI...! A Tsakanin Rawuna EWF BABI NA SITTIN CIF _Assalamun Alaikum yan uwa Barka da warhaka, Nagode sosai Alhamdulillahi jiki an murmure, ina mika sakon godiya ta ga Jama'ar Whatsp musamman yan FITILAR HIKAYA TA, da Jama'ar Wattpad Nagode sosai naga sakon ku🤩😍_ Fitowa yayi yana kallon su, kafin ya ce musu. "Na ce ba?" Juyawa suka yi a fusace, kallon yadda suke dauki Barkindo Yazidu ranga-ranga. "Sai mun baka.." takowa yake yana kallon su, da sauri suka saka shi a keken dokin shi suka bar wurin shi dariya

Chapter 30 of 39