Share this page
yake kaf-kaf da ita, a yanzun yana jin matukar ya rasa Minani a rayuwar shi tabbas zai kasance mutum me matuƙar asarar mata amfani ita din rabin rayuwar shi ne, juyawa tayi tana kallon yadda kwalla yake zuba daga idanun shi. "Baffa'm kuka kake ne?... ___________________" End of page 18 Barka da warhaka ya hakuri da halina 😂🤣🚶🏾‍♀️free book kenan a amsa da hakuri 🤌🏽 #Mai_Dambu Yau na sha fama da network ne wallahi sai yanzu afwa [5/14, 2:22 PM] Pearl crystal: KALLABI...! NA Mai_Dambu EWF BABI NA SHA TARA *WANNAN PAGEN NA KUNE MUTANEN BAFFA'M DA YAR KWAILAR SHI MUSAMMAN AUNTY SA'A WAI AN SAUYA MATA NI 🤣😂🤌🏽 TOH A DAWO DA NI KAWAI* Janyo ta yayi jikin shi, yana shafa bayan ta, yana jin wani sabon kaunarta yana huda duk wani kusurwa na jikin shi, sumbatar goshinta yayi yana faɗin. "Ba kuka nake ma, ciwo na nafama" kifa kanta tayi a kirjin shi ta fara sauke ajiyar zuciya, samun kan shi yayi da kallonta musamman yadda zufa da gashin kanta ya lullube mata fuska. "Kin gaji ko?" Ya tambaye ta, bayan ya mike daga kwanciyar, ya dauki mayafi ya rufa mata, a hankali yayi ta wasa da gashin ta, da sauri ya nufi dan makewayin da yake cikin tantin. Ya zuba ruwa yayi wanka da alola sannan ya fito ya taimaka mata itama tayi wanka da alola, shi ya jasu sallah. Suna idarwa ya fita jim kadan sai ga Innayoh da kayan abinci har da y'ay'an itacce, gaushi da ya'yan Audiga. A take ta saka ta yin tsuguno akan gaushin da ya'yan Audiga, yana gyara mace sosai, dan haka tana gamawa ta sata a gaba sai da ta ci abinci sosai. Sannan ta bar tantin, shima ya shigo ya zauna ya fara cikin abincin. Yana kallon yadda take ta zuba gyagyadi, dan haka ya gyara mata kwanciya ya shiga harkan gaban shi. A cikin yanayin da yake, kamar ya koma gida jikin shi na bashi wani abu na daban, dan haka ya tattaro duk wani abinda ya iya domin kare lafiyarta sai da yayi, sannan ya cigaba da wasa da gashin ta, kafin ya kwanta. .... A hankali take ganin kamar ana wani sha'ani ko biki ne, sai dai kuma bai yi kama da bikin ba, domin dai wata mata ta gani lullube da mayafi, a gefen Baffa'm. Takawa tayi zata tab'a matar aka ture ta ta fadi. D'ago kai tayi, ta ga Baffa'm. Kafin ta mike ya riko hannunta. Bude idanun tayi ta gan ta cikin jikin shi, tura kanta tayi cikin murmushi zuciyar ta yana bugawa. Ganin shi a tare da ita yasa taji wani irin nutsuwa da barci me dadi ya dauke ta. * Washi gari Da wuri suka isa gombe, kuma Alhamdulillahi sun samu karba na musamman, domin a shashin Fulani Shatu aka sauke ta, anan suka zauna ana yi ta hada musu abinci kamar me, Kiran Innayoh yasa aka yi. Cikin girmamawa ta zube a gaban shi. "Innayoh ki bata wannan ta tabbatar ta ci a cikin abincin." "Toh Allah ya baka nasara" ta amshi kullin ta tafi da shi, ta bawa Fulani Aminatu ta gaya mata yadda zata yi amfani da shi. Bata samu ganawa da mahaifin ta ba, sai washi gari. Tare da Baffanta, suka zauna a babban Zauren Mahaifinta. "Alhamdulillahi Masha Allah, kin min abunda kowa ya kasa min, kin zauna da mijin ki lafiya. Haka ba ramin dadi yayi min ba, kiyi hakuri da halin da zaki shiga na rayuwa wata rana sai labari" Gyada kai tayi. Haka suka yi ta mata nasiha. Har bayan wani lokaci sannan ta dawo shashin Fulani Shatu. A wannan kwanakin, da kan shi Sarki Bello yayi ta bin wasu sha'ani na masarautan. Kafin ya gano asalin abinda yasa ake bibiyar matar shi. Da kan shi ya samu Surukin shi ya gaya mishi abinda ya ke hangowa. Ya kuma ce mishi. "Idan Kilishi bata fita sabgar Aminatu ba, ba makawa zan dawo mata da kaidinta, kar ta kuma wannan yunkurin." "Insha Allah babu abinda zai faru" A bangaren Kilishi kuwa tayi tayi aikin ta yayi nasara amma ina babu abinda ya faru, dan haka ta saka a ran ta sai tayi amfani da karfin ta, dake bata da imani, tana cikin wannan yanayin ta aka aiko mata yarta da za ayi bikin shekara me zuwa ta fad'o daga sama ta mutu, shi ne abinda ta shiryawa Aminatu. Kuma dama Sarki Bello ya fada ta kiyayye shi, Mahaifin Aminatu bai gaya mata ba, sai gashi ana cikin kokarin sururar Yarinyar daya yar ta ma aka same ta ta mike kafin kace me sai gawa. Wannan tashin hankalin ba karamin haukatatta yayi ba domin bata tab'a tsammanin haka ba lokaci guda. Sai da aka yi addu'ar Bakwai sannan Sarki Bello ya dauki matar shi suka bar masarautan zasu koma gida. ** *MAYAKAN SAHIL* "Shugaban rundunar saura wata biyu mu isa masarautar" "Tabbas Lati nasara bata gare mu dan haka zamu tura budadiyar wasika ga Sarkin su, idan ya amshi abinda ake bukata toh idan bai amsa ba, zamu shiga cikin masarautan mu dauko ta" "Ya shugabana kana ganin haka babu matsala?" "Babu dan haka a cigaba da tafiya" haka suka yi ta ratsa tsakanin manyan duwatsu har suka yi tafiya me nisan gaske. ** *Bayan sati biyu* "Baffa'm! Amma mun kusan isa gida ko?" Ta tambaye shi. "Insha Allah nan da mako guda zamu isa lafiya" ya bata amsa, haka tafiyar ta kasance wannan karon yada zango kawai ake a huta, qashin gari a wuce. Amma bai hana mutumin nan turmushe yar kwailar shi ba, har addu'oi tayi tayi Allah ya kawo mata bakon ta, ta huta da jarabar shi. Bakon shima kamar yasan nufin ta yaki zuwa. Bayan wasu kwanaki suka isa gida lafiya, tun daga bakin masarautan ya fahimci galadima ya kintsa kowani dan Banza, a ran shi ya ji haka ma yayi mishi. Bai saurari kowa ba, sai da ya huta gajiya na tsawon kwanaki biyar sannan ya koma fada, aka cigaba da mulki inda shima yayi ƙoƙarin kamanta halin Galadima, kuma Alhamdulillahi sun tattauna sosai akan abinda ya shafe su har akan Aminatu. Kuma ta bashi kwarin gwiwa sosai akanta. Shi yasa yake mugun kaunar galadima domin ya mishi abinda bai zata ba, kuma yana cikin mutanen da yakeke girmamawa. * A duk lokacin da ƙaddara ta Kwankwaso maka kofa babu yadda zaka yi da ita dole ka bude mata, haka ce ga Aminatu domin ana cikin wannan yanayin musamman ita da sarki Bello aka fara tsiro da wani irin Gulma akan rashin haihuwar ta, wannan shine matsalar da dukkan su biyu suka fara fuskanta, maganar rashin haihuwa har cikin fada, kuma dake an shirya kome a nutse sai gashi sarki Bello ya fara fuskarta matsin lamba daga Wanbai, Sa'i, da sauran manyan fadar musamman da suka kasance kusan iyayen shi ne da baffannin shi, a lokacin Galadima ya tafi lardin sokoto. Mai Martaba sai da ta kai ya kasa barci balle ya samu natsuwa da Aminatu,.itama ta rasa kuzarin ta, musamman da ta ga halin da yake ciki, a wannan lokacin Innayoh ta amsa uwa domin taki yarda ta bar Aminatu ita ɗaya, a duk lokacin d ta zauna tana nazarin halin da take ciki zama take ta dauke mata tunani. Ana cikin wannan lamari sai ga sako daga shugaban Rundunar Sahil ya turo da sakon lallai sarki Bello ya turo mishi da Fulani Aminatu zai kai ta ga Sarkin su. Dama an gama fusata shi, da maganar haihuwa yana jin haka ya ce. "Ka je ka gaya mishi ko baiwar masarautar Gobir ba zata isa gare su ba, balle Matar da nake tsannanin Kauna idan bai tattara haukar shi sun bar min kasata ba, idan na fito sai na sare kan shi na ajiyewa Ungulu suyi watanda da shi" Da sauri dan aiken ya juya. "Amma ina ga tunda haihuwa ce bata yi me zai hana ka bas...." "Nasiru Chiroma!!! Sai na yanke harshen ka idan ka kuma furta wani kalma ga Minani!" Ya fada da ƙarfi sai da fadar ta amsa, wannan yanayin ya tsorata su. Baki daya aka rasa me magana dan haka suka taru a wuri guda. Cikin fushi ya koma cikin gidan. Yana shiga cikin gidan, ta samu labarin yana wurin shan iskar shi. A hankali ta nufi wurin da kayan marmari. Yana tsaye ta shiga da sallama. Bai amsa ba, sai ma huci da yake ta faman yi, wani irin iska ake lokacin guda ya haɗa da wani irin bakin haɗari, da sauri ya juya zai sauka yayi karo da ita. "Ina ga kamar akwai abinda kuke boye min ko?" Ta fada mishi. "Kin ga ki tafi zan zo" Murmushi me ciwo tayi tare da cewa. "Yau kwana huɗu kenan, ina son ganin ka babu halin ganin ka, na tafi turakar ka kaucewa Sarkin gida na koma zaka zo, wai akan haihuwa ce ake min haka? Ni fa ba dabba bace. Sannan Ni ba yarinya bace, kai ka girma da tunanina haka. Ba zan hana ka yadda kake so ba, amma idan nice bana Haihuwa me zai hana ka kara wata matar...." "Keeee" ya daka mata tsawa, wanda ya firgita da ita, murmushin takaici tayi sannan ta ce mishi. "Idan ba haihuwa kake so ba me yasa kake korata daga ganin ka?" Takaici yasa shi rab'a gefen ta ya nime wucewa. Rike hannun shi tayi. "Yau ce rana ta farko da ka min haka, amma na maka uzuri domin nasan baka kome sai da dalili. Karka manta ka koyar min da kome ne da kanka ni dalibar ka ce, sannan wannan shine yanayi na farko da na fara fuskarta rayuwa ta a haka. Duk laifin da xan yi maka Karka juya min baya domin shine abu mafi raunin da zai kashe ni" wani irin juyawa yayi ya shiga sumbatar bakin ta. Ya Allah Ya zai yi da kaunar Yarinyar nan. Abinda ake shirin ya aikata shine katangar farko da xa a mishi da ita. Wani irin kaunarta yake ji me tattare da damuwa. Aikuwa iskar da ake ya sauko da ruwa me karfi. Yana zuba akan su. Domin iska ya yaye rumfar da yake wurin. A hankali ya janye bakin shi daga nata, sannan ya rungume ta. "Kiyi hakuri da duk abinda zan miki" girgiza kai tayi tana Murmushi hawaye na zuba mata. "Ba zan tab'a mantawa da haka ba" rungume ta yayi. Ita tana kuka shi kuma yana na zuci. * Lokacin da me sako ya dawo da labarin abinda sarki Bello ya ce ran shi ya B'aci dan haka ya tura sako kuma Masarautan ya basu wa'adin kwanaki uku su turo Fulani Aminatu ko kuma ya shigo ya sare kan sarki Bello ya tafi da ita. Haka aka kuma kai sakon, sarki Bello bai ce uffan ba, domin yana bukatar Galadima. Abin sai ya hadu mishi kome yayi tsanani, dan haka ya tura Sarkin gida cikin sirri ya lardin sokoto, domin ya taso Galadima. Abu goma da ashirin shi a can bai da sukuni domin mutanen fadar sun Bayyana mishi bukatar su, ba zai cigaba da zama mace babu albarka ba, tunda ba zai yi aure ba dole ya nime kunyaga ko kwarkwarah, kuma yadda suka kawo hujjar su, sai ya kasa magana. "Matukar aka baka auren mace ba zaka mata adalci ba, amma idan aka baka kunyaga ko kwarkwarah dole zaka sauke nauyin ta domin zata fi Fulani Aminatu baka lokacin ta, dan haka a matsayin mu na manyan fada mun yanke shawarar baka kwarkwarori daga kowacce gida, idan kuma kana ganin abinda muka yi ba daidai bane toh ka basu Aminatu domin kowa yasan kasar Sahil matsafiyar kasa ce da suka yi imani da tsafi yaki da su kamar yaki ne da rundunar bakaken ifiritai, dan haka ka basu ita ai shima Sarki Shehu Usmanu yasan cewa Yar shi tana da abinda Arkhan yake nima suka baka auren ta me yasa bai rike yar shi ba? Me yasa bai bata tsaro ba, matukar zaka shiga kasada saboda ita dole ka amshi batun mu ko ka janye daga shiga yakin ka bashi ita su tafi.... __________________________ End of page 19 idan kai ko ke ce a matsayin sarki Bello ya zaka yi wanne xaka dauka zaka bada Aminatu ne ko zaka shiga yakin ne domin ita sannan ka amshi kwarkwarah... [5/14, 2:22 PM] Pearl crystal: https://www.wattpad.com/1223755152?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=5iXl3uke3sxzQOZVr%2BxMAKDP6eN42Ax4Ot6%2BxVKTareIlzg7OpeSh1RbIOS3Ug0rr8GGs3jYj5ArMbFIJM3y35oDHQehEsNhoUayOKN16aISPA5uCj65DE6pck%2BUtftx KALLABI...! A Tsakanin Rawuna Na Mai_Dambu EWF BABI NA ASHIRIN Da wani irin tashin hankali yake kwana yake tashi, bawai dan bai da karfin kwatar kome bane, ko ba zai iya tsayawa Aminatu bane sai dai kuma yadda suke had'e kai da matukar tashin hankali. Domin kiri kiri suka juya mishi baya. Kawai abinda suke so zai yi dab haka baki daya ya kuma rudewa. Ga shi babu Galadima, shima an can galadima addu'a yake Allah yasa kar ya amince da bukatar su, domin akwai son rai a cikin shi. Ba sarki Bello suke son yaka ba, Tarayyar shi da Aminatu ne, ya jima da sanin haka tun tafiyar su Gombe suka nuna basu son shi da Aminatu domin baya fahimtar kome idan aka ce Aminatu tana nan gani yake kamar dan bata kasance daya a cikin su ba, amma bai ga abin tashin hankali akan ta ba.. * Yau kwana bakwai kenan da ta sanya shi a idanun ta. Ya zabge sai tarin kasumba, da sallama ta shiga cikin dakin shi. Yana kwance kasancewar yau Laraba. Kallon fuskar shi tayi tana tafiya a hankali dan bata son ya farka, kallon shi tayi na wani lokaci sannan ta shiga ban daki ta dauko tasa, da ruwa sai sabulu, tana fitowa ta ja wani karamin adaka ta dauki aska. Kallon shi tayi ta zauna a gefen gadon, sannan ta goga mishi sabulun da ruwa ta fara mishi askin kasumabr da ya tara. Cikin kulawa da tattalin shi. Yana kallon yadda ta rame, wani karin kyau da ya ga ta mishi shine hancinta da ta saka aka huda mata, yayi mata mugun kyau, ya lura a yanzun take tashen yan matancin ta, a hankali take askin har ta kusan karewa, bata yi zato ba balle tsammanin kawai ta ji ya riko hannun ta. Wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana kallon shi. "Na saka ki ne?" A hankali ta ajiye askar. "Barka da hutawa" ta fada fuskarta tattare da damuwa. "Yawwa yan mata" murmushi tayi me ciwo, sannan ta shanye tana kallon shi. "Akwai wani abu ne?" Ya tambaye ta yana me tashi zaune, bayan ya dauki madubi. "A'a" kallon yadda take wasa da kafaffunta ya yi. Murmushi yayi yana jin wani kalar tausayi take ba shi, wato tayi sabon lalle shine bari ta zo ya gani. Tashi yayi daga gadon ya nufi ban daki ya jima, sannan ya fito daure da wani katon mayafi kamar amawali a kugun shi. D'ago kai tayi ta Kalle shi tana masifar kaunar shi hadi da kewar shi. Wani irin mahaukaciyar kewar shi take, a hankali yake tafiya ta kurawa surar mijinta idanu, yadda yake tafiya irin ta cikakkun maza masu tsannanin kuzari da lafiya. Mikewa tayi ta nufi wurin da kayan shi suke ta kuma dauko wani amawalin, ta nufe shi cikin nutsuwa hadi da wani taku, kamar ba zata yi tafiyar ba, kafatar ilahirin jikinta wasu mahaukatar motsawa suke, kura mata ido yayi har ta iso gaban shi, ta fara goge mishi kirjin shi me ɗauke da wasu tarin kwanji da gargasa, janyo ta yayi ya mannata da jikin shi. Yana tuna yadda kome ya faru har ya wuce shekarun baya. Yarinyar nan da aka kawo babu kome a kirjin ta yau ita ce a gaban shi cikakkiyar mace me nutsuwa da tarin Darajojinta. Mikewar da kafarta tai alamar zata kara tsawo domin goge mishi kan shi, aikuwa ba zato kawai taji ya dauke ta cak. Wani ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta cigaba da goge mishi, tana gamawa ta fara alamar zata sauka, bai dire ta ba sai saman lafiyayyen gadon shi. A hanya ya zauna da ita. Yana kallon yadda take kokarin boye damuwar ta. "Nasan kin ji labarin abinda yake faruwa" damke amawalin tayi ta kura mishi Idanu kafin ta sake murmushi da ya boye kukan da take yi. "Ba ga kamar sun fika gaskiya ne" bai zaci haka daga bakin ta ba, ya kura mata ido. "Ta ko ina sun fika gaskiya, shi mahaifina yasan da haka ai ya haɗa ni da kai. Sannan me yasa bai rike ni ba? Me yasa ya baka aurena bayan yasan akwai wannan yanayin a tare da Ni" fuskar shi ya kai daidai fuskar ta, ya ce mata. "Ƙaddaran So shi ya sa shi tunanin idan ya haɗa mu, Allah zai bani ikon kare rayuwar ki da darajar ki" hawaye ne ya zubu mata tana kallon shi. "A'a son zuciya ce" yatsar hannun shi ya kai bakin ta, yana gogawa sannan ya mike, amawalin kugun shi ya fadi ƙasa, bata iya d'ago kai ba sabida kunya. "Sun bukaci ka bashi ni, shine ka ki?" Ta kuma tambayar shi. Murmushi yayi tare da cewa. "Matar da nake so zan bawa wasu yan iska? Ke ki bawa ba zan basu daga masarautan nan ba, dan haka idan zaki kwanta ga amawali nan ki shiga ban daki kiyi wanka" ta fada yana cigaba da aikin shi. "Amma kwarkwarah fa? Idan ka ajiye ta ba zan kuma samun damar kusantar inda kake ba." Juyawa yayi yana kallon ta kan ta a sunkuye, takawa yayi gaban ta, ya zauna a gefen ta, sannan ya shiga cire mata mayafin kanta da duk wani abinda yake tare da ita. Bai tsaya wata ba. Ya kwantar da ita sannan ya ja mayafi ya rufe su. Tana gaban shi shi kuma yana bayan ta. "Ba maganar wasa nake ba, wannan maganar na gaske nake rayuwar mu zaka duba." Juyo da ita yayi da karfin tsiya yana kallon ta. "Innayoh ce ta tsara miki abinda zaki gaya min?" "Ina son ka fahimci." Bakin shi ya kai habb'atar, cikin kwarewa gami da kewar ta, ya shiga bin ta. Baki daya sun yi kewar juna, sai ka rasa ita ce ko shi? Domin yadda suke gurzan juna, kamar sun shekara basu hadu bane, dan haka sosai yake murzata yana kuma hake ta lungu da sako na jikin ta. Sosai ya gauraya mata lissafi, sai da ya hanata sake furta kome sannan hankalin shi ya kwanta, ya bata kan shi da rayuwar shi. Baya jin zata kuma bukaci ya bata wani damu. Sai da ya gama sannan ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya. "Na gaya miki bana son kina shiga harkan mulkin ko?" Buɗe idanun tayi tana kallon shi. Sannan ta ture idanun ta. Tana sauke ajiyar zuciya. "Kwarkwarah zaka yi fa! Ba kishiya ba balle ka ce min na amince a zauna lafiya! Baffa'm kawai ka tura ni wurin su zai fiyye min kwanciyar hankali da ina kallon ka bani da iko da kai sai na tambayi kwarkwarar ka" tana gama fadar haka ta fara kokarin mikewa. "Ke" ya daka mata tsawa. A Matukar raxane ta zuba mishi ido. "Ki dawo nan ki zauna sai kin maimaita abinda kika faɗa" "Akan me zan maimaita? Ai nasan dukkanin kunnen ka sun ji abinda na ce maka. Ka mika ni gare su idan bana nan zaka iya auren ka, da dai ina kallon yadda zaka dauko min kwarkwarah bani da iko da kai laifi ne dan nayi magana akan ka?" Kura mata ido yayi yana mamakin yaushe Aminatu ta fara kokarin mishi tsaurin ido. "Yayi kyau!" Ya fada bayan ya dauki amawalin shi ya daura ya nufi ban daki yayi wanka sannan ya fito. "Ba zan basu ke ba, kuma akan idanun ki xan kawo kwarkwarah har turakata" bata san lokacin da ta fashe da dariya ba, ta ce mishi. "Eh me zan yi? Ka zata xan yi wani abu ne? Amma tabbas ba zan kuma had'a shimfida da kai ba, ka tafi ka tara bayin gidan nan ka kwana dasu." Kura mata ido yayi yana mamakin yadda yarinyar ta Haukace mishi. "Innayoh ce ta turo ki?" Yadda yayi maganar babu wasa a cikin shi yasa ta juyawa cikin fushi. "Eh wani abu ne?" Ta fada bayan ta gama saka kayan ta. "Babu shakka kin janyo mata masifa domin sai na saka a zane min ita" a tsorace ta juya tana yarfe hannu ta. "Wallahi ba ita bane, kawai ni ce na kawo kai na, wallahi Innayoh bata san kome ba" tura ta ban daki yayi ya shiga shiryawa, yana mamakin kishi irin na Aminatu, domin babu abinda ya sakata wannan fadar sai zafin Kishi, yana gama shiryawa ya fita bai kuma, bin ta kanta ba ya nufi fada. Suna kus-kus ne, amma ana ganin shi suka yi shiru. "Sarkin yaki a shirya min tafiya yaki ni daya" "Ya batun karin Mata" "Bana bukata" kuma dama an gaya musu an ga Fulani Aminatu ta shiga shashin su. "Akan me? " Suka tambaye shi baki a hade. "Akan babu wanda yake da iko da ni sai Allah, dan haka kar a kuma min maganar wata mace Aminatu ta wadatar dani" Takaici yasa suka shiga mikewa zasu bar Fadar. "Karka manta babu Sarkin da aka tab'a kaiwa wannan lokacin bai da Zuri'ar shi sai kai, idan har ka shiga yaki domin ta, toh abu na gaba dole ka nime macen da zata haihu domin matukar ka dawo a raye dole ka nime wacce zata haihu da kai" "Haihuwar nan dole ne?" Ya tambaye su a tsawace. "Dole ne domin ba zamu zauna da bakirariya ba, mun ji ka shiga yakin amma dole ka nimo wacce zata haifa mana magajin gobe idan ba haka ba, zamu yaki masarautan Gombe kamar yadda suka ci amanar aminci basu gaya mana Meke dabaibaye ga rayuwar Yar su ba." Shiru yayi yana fatar kafin ya sare Sarkin yakin Sahil Galadima ya iso, kusan haka aka rabu rai babu dad'i. Koda ya kome ya same ta kwance tana barci. *Itama tana cikin damuwa kenan?* Ya tambaye ta, tana jin babu dad'i a ran shi. Har inda take ya tsaya sai kuma ya kyale ta, ya koma babban zaure, yana kallon abincin da aka shirya musu, na musamman. Innayoh ce ta jagoranci kawo abincin, Tana gama basu umarni ya ce mata. "Innayoh meke damun Yar ki?" Shiru tayi sannan ta ce mishi. "Ana tunzura ta ne da magana mara sa dadi." "Waye?" "Ajuji" "Yayi kyau, amma ki gaya mata borin ta da rigimar ta ba zasu sauya kome ba, don Allah bana son tana haka." Ya fada yana daukar kofin da aka zuba mishi ruwa. "Insha Allah zan mata fada ma" d'ago kai yayi. "Karki mata fada domin ban shirya jin rigimar ta ba" ya fada yana cigaba da cin abincin. "INSHA ALLAH" Sannan ta fita daga Zauren. * Fada suke da wata mata, da ta shigo cikin gidan da tsohon cikin, a matukar tashin hankali, wasu mutane suka janyo ta waje, aka shiga rufe kofar Masarautan ga Baffa'm a tsaye kuka take da ihu tana kiran shi. Tun tana yin abin a cikin barci har Muryan ta ya fito ihu take, yana cikin cin abinci ya sake ya nufi cikin dakin da sauri ya same ta sai kuka take tana mika hannu,. Rike hannun yayi tare da sakawa a gefen fuskar shi. Sannan ya sumbaci hannun ta. "Fulani na! Gani nan a gaban ki" bude ido tayi, tare da kallon shi bata san lokacin da ta rungume shi ba,.tana wani irin kuka me mugun ciwo. "Baffa'm don Allah karka bari su raba ni da kai mutuwa xan yi" ta fada cikin matsanancin kuka. Rike hannun ta yayi yana kara jin wani irin kaunar ta, rungume shi tana kuka. Hannun shi ya kai bayan ta, yana bubugawa. "Ki bar kuka idan Allah ya ƙaddara abu babu me iya kauce mishi kin ji Minani" "Baffa'm tsoro nake ji, kullum tsoro nake ji kar ka rabu dani don Allah kar kar ka bari su raba ni da kai, don Allah Baffa'm." Yadda take kuka ba karamin al'amari bane a gare shi. "Toh Insha Allah babu abinda zai faru" ya fada, yana wasa da sumar kanta. Tun ranar bata kuma samun nutsuwa ba, sai ranar Juma'a da ta bar dakin shi domin zuwan bakon ta, a ranar Allah ya nufa galadima shima ya dawo. Gwanin ban tausayi idan ka ga yadda suka damu, kallon Galadima yayi sannan ya ce. "Na yarda haihuwa na Allah ne amma yadda suke kokarin ganin sun rabu da ita shine zuciyata ta gaza dauka. Galadima kayi wani abu." Shiru yayi kafin ya ce mishi. "Kayi hakuri tunda Sarkin gida ya kai min batun na shiga damuwa, wannan shine adadin lissafin kaddaran ta, Babu wani abinda xan iya yi domin kare ta, ko hanawa sannan kamar yadda kake son haihuwar ba zai zo cikin sauki ba, dan haka ka amshi bukatar

Chapter 11 of 39