Share this page
fada cikin matsanancin bacin rai. "Ai yaki yarda a yi yakin gamayya ce, dan haka ka shiga da shi muga karyan kare matar shi." Haka suka yi ta tattaunawa, * A can wurin su sarki Bello, bayan an yi sallah kallon shi, sarkin yaki yayi tare da cewa. "Mai Martaba ban tab'a ganin yakin ka ba sai yau, a zaman da nayi da ahalin ku baki daya yakin su akan kasa ce da kara karfin mulki yau naga yaki akan mace da kare kimarta. Ya shugaba na, wacce irin kauna kake mata haka? Dukkan mu muna da mata da yara, matan mu har da sa'o'in yaran mu, ya shugaba bamu tab'a damuwa akan muna son su haka ba, kai kuwa a cikin Masarautan ka nuna Fulani Aminatu tafi kowa me yarinayr tafi sauran da shi" Gyara zama yayi yana kallon Sarkin yaki gyatsa yayi a hankali, sannan ya kalle shi da kyau ya ce mishi. "Ita din renon mashahurin marubuci ne, na san soyayya tun kafin na hadu da Aminatu, na karanta hikayoyin soyayya da kauna, sannan na rubuta labaru akan soyayya, yau da na samu matar da nake so idan ban mata soyayyar da na ke ji a raina ba me zan yi? Yarinya ce na same ta a lokacin, bata da hankali, bata da kome akan ta sai shirme duk abinda Aminatu zata yi koyarwa na ne, sannan bana jin koda xan mutu zata yarda ta zauna da wani namijin dan Ni daya nake gaban ta, nine murmushin ta nine dariyar ta, na mai da kaina sa'anta, sannan na zama abokin ta mijin ta, tana hira dani sama da yadda take da Jakadiyar ta Innayoh, na koya mata abubuwa da idan bana rayuwar ta zata iya kasa yin kome. Ba matan ku tafi ba a'a Tarbiyyar da na bata ne yake da bambanci da na kowa." "Ikon Allah, dama akwai wata soyayya ne da ta wuce ka auri mace ta haifa maka yara idan baiwa ce ka mai da ita sad'akar ka." Inji Sarkin yaƙi. "Kazo daidai kuwa. Toh duk ranar da ka ware macen da kake so, ba zaka tab'a farin cikin ganin ta cikin damuwa ba, Sarkin yaki kar dai kuna cikin.mazan da basu iya dauke Damuwar iyalin su sai ta kwanciyar aure?" Sosa kai sarkin yaki yayi yana kame-kame. "Kawai idan kuka ji bindin ku ta kumbura sai ku kai ta wurin abinda take bukata ba mamaki ma haka kuke hake musu" ya fada yana kallon sarkin yaki da yayi tsamo-tsamo kamar kazar da ruwa yayi mata duka. Murmushi sarki Bello yayi tana cewa. "Nasan yanzun tana can tana kuka. Insha Allah ina samun nasara zan tafi gare ta" "Allah ya baka nasara" "Amin Ya Allah" Bayan la'asar suka fito, anan suka ga ikon Allah, domin shugaban rundunar ne da kan shi, dan haka suka shiga filin. Kallon sarki Bello yayi cikin nutsuwa ya ce. "Me yasa ba zaka bamu ita ba kawai akwai mata dayawa sai ka samu sauran" zaro takobi sarki Bello yayi cikin takaici ya ce mishi. "Ban ji zan iya wannan kasadar ba" "Toh zaka gani domin ba zan kashe ka ba, akan idanun ka zan tafi da ita waye yasan me zan mata a hanya kafin na isa da ita Sahil tunda naji ance yarinya ce qarama daidai tashen balaga take kome ya daidaita a tare da ita zata ji sabon kugun" cikin wani irin fusata sarki Bello yayi kan shi da azazzaben kishi.... ____________________________ *Anya kuna tsoron Allah 😂🤣 wai page biyar a rana 🤔 yo ko dari na baku sai kun bukaci kari mu lallaba juna kawai a page ɗaya 🚶🏾‍♀️amma babu wasu dabarbarun da zan yi gaisuwar wannan shafin naku ne yan Fitilar hikayar Mai_Dambu🫶🏻* 🏃🤣 Nima nayi kan ku da azzababen sauri domin nayi posting kome zai faru oho....? #Mai_Dambu [5/16, 5:30 PM] Pearl crystal: KALLABI..! A Tsakanin Rawuna Na Mai_Dambu *EWF* https://www.wattpad.com/1225030646?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published BABI NA ASHIRIN DA UKU Kaurewa wurin yayi da azababben yaki, me cike da kishi. Wato duk da bai cika shiga yaki ba. Amma yau sai da ya kure Sarkin Yakin sahil, domin baki daya sauya mishi salo yake. "Duk akan Matarka kake yakin nan?" "Toh dama akan ka zan yi yaƙin" ya fada a fusace, bayan ya kai wata gagarumar sara, Murad ya tare da sauri. Duk da yasan bakar magana ya gaya mishi bai hana shi takalar shi da wata maganar ba "Idan na kashe ka ɗauke ta zan yi" ya gaya mishi haka, "Sai dai idan bana numfashi matukar ina raye sai inda karfina ya kare." Haka suka yi ta yakin babu wanda ya samu nasarar koda lakatar jikin dan uwan shi, sai da rana ta fadi dai-dai lokacin sallah, Murad ya samu nasarar yankar Baffa'm a kirjin shi. Sai da ya durkusa,. Sake kawo mishi sara yayi ya kare da takobin shi. Dole aka buga tamburan a tsayar da yaki, lokacin ibada ya kusa, jinin da yake zuba ba na wasa bane. "Idan ka sake ka dawo gawar ka za a dauka wannan shine gargadina da kai ka bani Aminatu" bai tanka mishi ba, ya koma wurin su, yana isa suka taso zasu rike shi ya d'aga musu hannu, sai ya shiga tantin ya cire kayan, yayi wanka sannan yayi alola ya gabatar da sallah, yana idarwa ya kira Sarkin yakin shi, ya dinke mishi ciwon, duk da zafin da yake ji bai kai zafin kishin da yake ji ba. Dan haka cikin karfin hali ya kalli sarkin yaki. "Idan muka yi sallah Isha a gaya mishi za a cigaba" Da sauri ya kalli Baffa'm. "A cikin daren ka zubda jini fa?" "Umarni na baka" da sauri ya fita ya isar da sakon Baffa'm, bayan sallah isha aka kewaye filin da wuta yadda ko ina zasu ga yadda ake yakin sosai. Bayan ya idar ko abinci bai ci ba, sai niman nasara a wurin Ubangiji, sannan ya fito filin. * Ta dauki kofin kindirmo zata kai baki, kamar wacce aka mata wani abu, sake kofin tayi ta fita da gudu kafarta babu takalmi. Tare tare ake da ita. Dakyar Waziri Zakaria ya samu nasarar cafke ta. Wani irin ihu take tana dukar shi da yakushin sa. A lokacin Innayoh suka iso da hansiya. Suka rike ta, "Fulani ina zaki da alumuru nan, yanzu aka shiga sallah fa." "Don Allah ku kyale ni, wani abu ya same shi." "Innayoh ki tafi da ita, insha Allah Baffa'm zai dawo" kuka ta saka tana kara kokarin kwacewa, amma haka Innayoh ta wuce da ita, dakyar aka samu ta nutse, amma burinta shine ta tafi wurin shi. A masallaci Waziri yake labartawa Galadima, kallon shi galadima yayi. "Ba mamaki taji hakan ne a jikin ta, son da sukewa juna ne ya haifar da ko ya dayan su, ya shiga wani hali zai ji a jikin shi." Yana gama fadar haka, ya wuce, daga gidan shi ya bada sako aka kaiwa Innayoh, dakyar ta sha. Daga nan sai barci. * Tunda suka dawo yakin, Shugaban runduna yake samun galaba akan Baffa'm, amma Naci da taurin kai, a duk lokacin da ta tafi zai fadi, sautin kukan ta yake ji, sai ya koma ya tsaya, da wannan yanayin yake yaƙin tare da rokon Allah ya bashi sa'a. Har kusan goshin asuba, kafin Allah ya bashi sa'a,ya sari shugaba runduna a kirjin shi, faduwa yayi. Ya kuma kai mishi sara, duk da Baffa'm baya gani sai yayi amfani da sautin numfashin sa, da haka baffa'm yayi ta saran shi, har sai da ya daina numfashi.sannan ya fadi akan gwiwar shi yana aman jini. Da gudu sarkin dakarun suka zo su dauke shi, daga nan shima shugaban rundunar Sahil aka dauke shi domin ya jikata, Baffa'm kan sai da ya share awa biyar kafin ya farka, sallah yayi saboda jikin shi akwai raunika. Sannan ya saka kayan shi na sarauta ya nufi inda rundunar Sahil take, suna ganin shi suka fara ja da baya, tantin Murad ya shiga yana kwance magashiya wato rai kwai-kwai mutu kwai-, kwai, murmushi yayi sannan ya ce. "Allah ne ya bani nasara akan ka, sannan na Barka ne a raye domin na nuna maka karfin Addinin Musulunci, ku tattara naku ya naku, ku bar min da'irar ta, na baku sa'a daya, idan kuka sake naji labarin kuna nan zan muku kisar wulakanci. Yanzun kan ku tafi ku rayu" "Mutanen da suke kewaye da kai, ba masoyan ka bane. Makiya ne da suka bamu damar fuskantar ka. Kayi yakin neman su waye suke maka yankan baya?" Gyada kai yayi tare da cewa. "Ba zan yarda da kai ba, domin an hada kai da kai dan tozarta Ni, dan haka kai da wata tsiyar na rundunar ka ku tattara ku bar min Alkarya ta" "Babu shakka, kai mutum ne me nagarta, na yarda da kai na roke ka da Allahn ku kar ka bari wani abu ya same ta, domin tana tsakiyar kaddaran ta ne" Kura mishi ido yayi kafin ya saka kai zai fita Murad ya ce mishi. "Tunda ka bani damar na rayu, ni kuma zan tabbatar ba biyaka halaccin da ka min." Fita Baffa'm yayi, ba'a yana jin dadi bane amma yau ya kudiri Aniyar ido hudu da Minanin shi. Har ya fara tafiya, jiri ya kwashe shi, kama sarkin yayi yayi, aka nufi Masarautan da shi. ** Tana tsaye a saman wurin shan iska, ta hango kura na tashi daga nesa, haka ya kara tabbatar mata da shine ya dawo domin ta ga tutar Masarautar ce, dan haka ta sauko tare da murar waje, da gudu tana me ratsa kofofin cikin masarautan har ta iso wajen Masarautan, sama labari ya zo an yi nasara tun safe ita ce dai ba a gaya mata, ba, domin xata iya shiga kuncin son ganin shi. Bata tsaya ba, duk da kuwa Innayoh tana biye da ita, haka ta wuce cikin kasuwar da yake wajen Masarautan tana kara tunkarar kofar garin da kafarta, tana isa ta tsaya daga bakin kofar bayan an bude mata, kurawa ƙurar da take kara tunkaro su tayi Idanu. Yadda take sauke numfashi, zaka rantse da Allah mutuwa zata yi, sai lokacin Galadima da waziri suka iso, tana kallon inda dawakan suke kara zuwa a guje, a hankali ta d'aga kafarta, ta fara takawa cikin wani irin kaduwa sakamakon hango shi da a goye a bayan Sarkin yaki, ji take kowani numfashin ta da sunan shi take fita, lumshe idanun ta tayi ta fara kokarin isa wurin su, da suke gab da isowa kofar Masarautan. Linzamin dokin shi yayi a gaban Fulani Aminatu, kama kama akayi tare da saukar da shi, keken dokin aka kawo aka shiga da shi, itama Aminatu ta shiga, har lokacin bata iya ko magana, daukar kan shi tayi ta daura akan cinyarta, ta fashe da wani irin kuka, wanda ba zaka iua fassara shi ba, domin ba kukan farin ciki ba kukan bakin ciki ba, rungume kan shi tayi har suka shiga da shi cikin turakar shi, yaga rigar jikin shi aka yi take aka fi aka kona bushashen ganyen kaba, aka kona shi tare da dutsen kwalin, aka shigar barbada mishi a ciwon. Sannan suka fita bayan sun gyara mishi kwanciyar shi. Tunda suka dawo aka yi ta bada labarin abinda ya faru, kowa jinjina mishi yake, ita kan tana makale da shi kamar zata koma jikin shi. Har qashin gari, tana barci a kasa hannun ta yana cikin hannun shi, ta jingina kan ta da shimfidar shi, bude ido yayi a hankali yana kallon dakin, kamshin turaren shi ya tabbatar mishi da cewa yana dakin shi ne, jin dumin yayi a hannun shi. A hankali ya juya yana kallon ta, tana rike da hannun shi ga shi ta jingina bata jin dadi kwanciyar kawai babu yadda ta iya ne ma, haka ya saka shi mikewa a hankali ya zare hannun shi cikin nata, ya sannan ya sauka ya gyara mata kwanciya, yana zaune cikin so da kauna, Tausayin ta da yadda ta rame yasa zuciyar shi yayi sanyi. Tashi yayi ya tafi ban daki ya gabatar da alola, sannan ya fito yayi sallah da ake bin shi, sannan ya gabatar da Wanda ya ce shi, sannan ya koma bakin gadon ya zauna yana kallon ta, yana jin wani irin sonta na kara fisgar zuciyar shi, a fisge yake jin tana kara samun matsuguni, hannun shi me lafiya ya kai yana shafa fuskar ta, kasancewar bata san ya farka ba. A hankali ya koma ya gyara mata kwanciyar ta, sannan ya shigar ta ita jikin shi, shafa fuskar ta yayi yana mamakin ramar da tayi s cikin kwanaki biyu, gashi har nonuwar ta sun rame, ya gane haka ne da ya cusa hannun shi cikin rigarta, hadiye yawu, yayi yana kara jin kewar ta, kallon hancin ta yayi yana jin idan ta haifa mishi yarinya mace, zai yi fatar ta dauko siririn hancin ta, domin yafi kome daukar hankalin shi, sumbatar bakin yayi.... ____________ *Ban gane ba🤔🙄☹️ kowa sai cewa yake zan kashe wani dan nice me hannun shika 😭😏😡 na kuma jin tarin ku sai na kashe Fulani Aminatu kowa ya huta* Ku yi hakuri pagen ba tsawo. Thank 🤩🤌🏽 #Mai_Dambu [5/16, 5:30 PM] Pearl crystal: KALLABI...! A Tsakanin Rawuna. Mai_Dambu EWF BABI NA ASHIRIN DA HUDU A hankali yake isar mata da sakon isowar shi, a tunanin ta mafarki take, sai da ta bude idanunta tarr akan shi, sannan ta fahimci shine ba wani, rike hannun shi tayi tana girgiza mishi kai. Dan sumbatar bakin ta yana jin kewarta na kara samun matsuguni a ranshi, zai kuma kai hannu ta mike zubur, kafin ya riko ta ta dira da sauri ta shige ban daki, wanka tayi sannan ta gyara jikin ta kasancewar har lokacin bata gama Al'adar ta ba, ta fito ta same shi kwance, sassanyar murmushi ya sakar mata, "Yaushe kishiya na yazo?" Ya nuna mata gefen shi ta zauna. Zama tayi, tana wasa da hannun ta, yau da ta gan shi sai ta nime duk wani damuwar ta, ta rasa. Riko hannun ta yayi yana wasa da shi. "Fulani Aminatu" ai kamar jira take ta fashe da kuka. Sosai bai hanata kukan ba, dan haka ya zuba mata ido, sai da tayi ta koshi sannan ta mike zata fita. Riko hannun ta yayi. "Dawo ki gaya Meye na Miki?" Ya tambaye ta, Cikin shashekar kuka ta ce. "Babu kome" rungume ta yayi tare da cewa. "Toh shine zaki tafi ki bar ni? Baki tunanin ciwo na ne?" Girgiza kai tayi sannan ya zauna a gefen shi tana shafa kan shi. Wani gyara kwanciyar shi yayi tare da narke mata kamar me jin zafin ciwon jikin shi. Ita kanta mantaewa tayi da kome, haka suka kasance a dakin yunwa ya fidda su, bayan sun karya, ya dawo dakin yayi wanka ita kuma ta koma bangaren ta, ta shirya amma bata kome ba, dan tasan dole za'a zo gaishe shi, dan haka ita da Innayoh suka shiga babban zauren girkin ta, suka fara abinci ana fita da shi bangaren mai Martaba, kuma kamar yadda tayi hasashe ne, an jama'ar da suke ta shigowa ba iyaka, sai dare ta samu damar zuwa wurin shi, a daddafe haka aka yi ta hidima a gidan kamar ana biki, na tsawon kwana takwas, kafin jama'a suka tsagaita. Duk da ciwon shi akwai wasu a kirji da damtsen hannun shi, bai hana yau da yake ganin jama'a sun tsagaita ya janyo ta jikin shi ba, kura mata ido yayi, a hankali na tura hannun shi kan lallausar matashin audigar shi, wato kirjin ta, da dukiyar Fulanin ta da yake fisgar shi. A hankali ya daura hannun shi, ya ji sun cika mishi hannu sama da kullum, murmushi yayi yana kallon yadda ta lumshe idanun ta. Murmushi yayi domin yasan ba makawa zai buga shagali yau, aikuwa yadda ya saka a ranshi haka ya shiga lugwaigwaita yar mutane, tun daga sama har zuwa ƙasa, baki daya yasata mantaewa da sunanta sai sunan shi.(🤣🏃☹️😭 Wallahi mutumin nan ya isa da ciwon amma yake shirin buga isa) aikuwa bai kuma rikicewa ba, sai da ya d'aga buje, ya fahimci iya shi daya ne a wurin, sai gashi har da wata irin shashekar yaushe gamo, itama Yar banza shiru kuke ji, ta mika mishi rayuwar ta da kome nata, sai yadda yayi da ita. Aikuwa taga aya domin Baffa'm sai da ya juye mata ruwan jikin shi a kanta, sannan ya rungume ta, dan ma jikin shi da ciwo, haka ya hakura da sauran ya barta. Itama almura ko a jikin ta. Haka zaman jinyar su ya kasance, domin gefe guda ba jinya ake ba, soyayya ake shanyewa. Sai da suka kwashe sati biyu, sai dai ta fita bada umarnin abinda za'a girka. Har ya warke sumul kamar ba shi ba, kafin ya kome fada. Ko hutawa bai yi ba, Chiroma ya gabatar mishi, da Kwarkwarah biyu. Shiru yayi kafin ya ce musu. "Amma!" "Ka amsa tunda ai yarjejeniya ce" hankalin shi idan yayi dubu sai da ya tashi. Yana cikin wannan yanayin Wanbai ya bashi wasu biyun, zasu kara mishi Galadima ya ce musu. "A ka'ida hudu sun isa, idan kuma aka kara toh wallahi ba zamu amshi sauran ba ma balle ƙarin" dake yana cike da Galadima dauke kai yayi yana kallon ƙasa. Haka aka gama zaman fadar. A lokacin sarki Ibrahim kwarkwarah daya yayi sannan zamanin mahaifin su kwarkwarah daya yayi itace ya haifi Yara mata daya tana aure a kwantogora, daya tana aure a daura. Dan haka babu wasu yan uwa da suke cikin fadar sai galadima, koda ya dawo maganar kwarkwarah ya fada kunnen Aminatu, tana zaune a dakin shi. Ya shigo da sallama, kallon shi tayi sannan ta mike tana me cire Damuwar ta a gefe guda, ta taimaka mishi ya rage damuwa. Nasihat Innayoh yana dawo mata akan labarin da ya iso su. _Karki sake ya fahimci baki girme tashin hankali ba, haka zai ajiye ki a ran shi. Ban hana ki jin kishin shi ba amma maganar ki mishi yaji bai taso ba, shima tilasta shi aka yi, sai ki nuna musu kina maraba da zuwan su, matukar kika rike mutunci mutanen banza ma mutumtaki zasu yi_ Da wannan ta shiga Taimaka masa, har ya shiga wanka, yana fitowa ya samu ta cire mishi wasu kayan sawa, zai da ya shirya ta rike hannun shi zuwa inda zai ci abinci. Zama yayi yana wasa da abincin. "Allah ya baka nasara, kaci abinci" wani irin fisgota yayi tare da rungume ta, ita kuwa ta bashi wani irin lafiyayyen runguma, ba tare da sun fahimci kome ba, kawai suka fada wata irin duniya, sanin cewa bakin kofar akwai dogarai yasa shi daukar ta cak zuwa turakar shi. Daga shi har ita burin su,.shine amanta da damuwar su, bai san wani irin so da bukatar ta yake ba, sai dai wannan ita ce rana na farko da suka zama kamar basu ba, domin gata nan yar mitsitsiya, ta dauke nauyin shi da bukatar shi, tsabar jaraba tun daga gado saman Kilishi, wurin hutawa duk sai da suka yada zango a wuraren, kafin suka samu nutsuwa a lokacin suna kwance a tsakar dakin. Juya mishi baya tayi tana murmushin jin kunya. "Fulani Minani" ya kira sunanta yana shafa bayan ta, ita kuwa burin ta bai wuce ta dauko mayafin da zata rufe jikin ta ba, janyo ta yayi yana kara yaba halayyar ta, na kunya da kawaici. Tashi yayi ya dauke ta yana faɗin. "Ni ba mijin ki ne kuma sirrin ki, idan har kika cigaba da kunya ta wacece zata min yadda kike min?" Boye fuskartar tayi a kirjin shi, haka suka yi wanka har aka gama, bata d'ago kai ta kalle shi ba, asalima yau ya lura wani irin yanayi yake ciki, domin taki saka kaya amawali ta daure a kirjinta, kuma har a dare sallah ne kaɗai yake bada damar saka kaya. Taki yarda su kuma magana akan kwarkwarah, asalima mantar da shi zancen tayi sai ma shagalin da take mishi, tsawon kwanaki suna kara kaunar juna, da ɗaukar bukatar juna. Da fari burin magauta ita Fulani Aminatu tace ba ta amince ba, sai a goranta mata tare da tuna mata ai ita yar kwarkwarah ce, sai aka yi rashin dace bata nuna haka, musamman wani hidimar da aka yi a gidan galadima, suka hadu akayi ta jefa mata habaici yar batalikan nan bata d'ago kai ta lalle su ba, asalima nunawa tayi bata san suna yi ba. Kuma haka ya faru ne sakamakon kokarin Innayoh ta ce mata. *Zasu nemi gaya Miki magana! Zasu takale ki da haibai ci. Zasu bakanta musu ki nuna musu ke mutum ce ba dabba irin su ba, don Allah kar ki nuna ko akan fuskar ki* Shi yasa suna fara cusguna mata, suka ga fuskar ta sau murmushi take. Asalima tashi tayi ta koma wurin matar galadima, babu abinda yake kara bawa kowa haushi yadda shigar ta, nutsuwar ta kamalarta. Bata yi kama da mutanen da basu san ciwon kan su ba, har suka bar gidan bata d'aga ido ta kalle su ba, asalima sai suka fara kokarin dakatar da junan su, domin an ce shiru ma magana ce. Tsakanin ta da mijin ta, kamar hanta da jini domin babu ruwan su, duk abinda za a yi sai ayi. A ranar wata juma'a, aka shigo da kwarkwarorin cikin masarauta. Sai da aka kawo mata su, tana kallon su daya bayan daya. Idanun ta ne ya sauka akan Bingel, cike da mamaki take kallon ta. Kafin ta cewa Innayoh. "Innayoh na gan su, Allah ya basu Sa'a da iya daukar kome" "Amin uwar ɗakina" sannan aka wuce da su,. Shiru tayi tana nazarin wannan al'amarin domin gudun kar ce zata hana shi zama da mace yasa bata yi wani abu ba. Da daddare, tana turakar shi shi, kanta a sunkuye tana yanka mishi lemo ta ce mishi. "An kawo yan matan fa" "Sai aka yi Ya?" Ya tambaye ta, "Wai dama na tuna maka ne, daga gobe zasu fara amsar ragamar aikina." "Guduna kike Aminatu?" "A'a ba haka bane" ta fada tana mika mishi lemon, "Toh ki kyale su, a wurin" "Amma" "Amma me?" "A'a babu kome" daga haka ya janyo ta jikin shi, sannan ya shiga bata labarin abinda ya faru, nan ta manta da batun kwarkwarah ta shiga dariya. -- "Wai kuna ganin har sarki Bello zai nime mu?" Daya cikin kwarkwarah ta tambaye sauran, "Me zai hana, mun fi matar shi kome fa me zata nuna mana da ya ce farin fata." Bingel na gefe bata ce musu kome ba, har suka gama hiran su. -- Kamar yadda dai suka saba, haka ya shiga karatun d'aga buje, babu ruwan shi da wani abu wai da aka ajiye mishi, sosai ya gurje matar shi. Ai kuwa yana zuwa fada aka kawo korafin an kawo mishi mata amma Fulani Aminatu ta hana su isa gare su, zasu dauki mataki akan shi da Aminatu. Murmushi yayi tare da cewa. "Idan kun dauki matakin iya kaci kuce na bar muku mulkin ku, kuma dama kamar kun san akan k'aya nake, idan kuka amsa sai na dauki mata na mu bar Masarautan babu wanda zai kuma ganin mu balle ya dame mu. Suma matan da kuka bani kazamai ne da suna da tsafta ba zan guje su ba," daga haka ya kade alkyabbar shi ya bar su a wurin tunda sune suka zabi haka bai ji yayi danasanin maganar da ya gaya musu ba, tunda suka fahimci hanyar da zai balle mulkin ma yake sai suka shafawa kan su ruwan sanyi, domin haka ba karamin koma baya bane a cigaban su. Bayan wata guda, lokacin Fulani Aminatu tana hutun Sallah, a lokacin Innayoh ta mata magana akan lallai a shirya daya daga cikin kwarkwarah ta tafi wurin mai Martaba, bata so ba domin shiru tayi taki magana, ita kuwa Innayoh bata kuma mata magana ba, amma tayi gaban kanta, domin kuwa bata jira abinda Fulani Aminatu zata ce ba, ta bada umarnin a shirya daya daya cikin yan matan nan, a kai wa Mai Martaba.... _________________________ *Wayar Charge na ya kone, wannan ma dakyar na muku wannan domin muna fama da rashin wuta ga kuma bani da abin Charge sai kun ganni kawai* Please vote and Comments share... #Mai_Dambu.. [5/16, 5:30 PM] Pearl crystal: https://www.wattpad.com/1225391554?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published KALLABI... A Tsakanin Rawuna Mai_Dambu. EWF *Gaisuwar wannan shafin naki ne Asli Smasher💕 Kaunarki da Fulani Aminatu ta musamman ne🥰👌 Ina taya Fulani Aminatu kaunarki tace a mika sakon godiya❤‍🩹 Sosai sosai amma zama da Kwarkwarah fa jazamun ne* BABI NA ASHIRIN DA BIYAR Sosai Innayoh ta tura aka gyara daya daga cikin yan matan, sannan ta dawo wurin Fulani Aminatu. "Na miki abinda ban tab'a b'ata ba, amma qaddarar mutum yana zane ne

Chapter 13 of 39