tayi tana kallon yanayin garin, tare da sauraron hiran da suke.
"Uban gidana, ai da ka fada tuntuni da mun san abin yi amma kayi ta boye mana" mika mata kofin yayi yana kallon kasa, a ranta ta ce.
*Lamido kenan maganar ma sai ka nuna mata mulki*
Shiru yayi kamar baya wurin yana kallon Mahaifiyar su, kafin ya mike bai ce musu cikin ku ba, abin sai da ya bawa Fulani Aminatu dariya.
"Innayoh wai yaushe zai dana jin nauyina?"
"Zai daina mana Insha Allah lokacin yana zuwa"
Kallon hanyar da ya bi ta juya wurin Innayoh ta ce mata.
"Na tausayawa matar da zata zauna da shi."
"Sabida bai nuna miki boyayyen halin shi ba, amma babu wani mugun abu a halin shi, asalima haka shine me kyau, duk inda zaka zauna ka nunawa mutane kai din na musamman ne, amma ba ka zauna duniya su goranta maka ba"
"Toh Innayoh" ta fada tana Murmushi dan ta san halin Innayoh,
Sauya kayan shi yayi ya fito daga cikin gidan, sannan ya fita wajen masarautan anan ya hango Gidado dasu Fulani Bintu suna ta yawo, bai bi ta kansu ba yayi ficewar shi daga masarautan.
A bakin kofa aka bashi kayan farautar shi ya nufi daji, idan yana jin nishada a rayuwar shi daji yake nufa yayi farautar, yana saka shi jin wani irin yanayi na musamman.
**
M. Gobir
A fusace ta kalle su, a daidai lokacin da Barkindo yake son shiga babban zauren.
"Taya haka zai faru? A ce ku kasa kamo mace daya a cikin rugar tsoron ta kuke ji? Matar nan na mata alamar da ba zata iya guduwa ba. Kuma da kun tafi akan lokaci taya zata gudu ku fita ku bani wuri"
Shiga yayi yana kallon ta, idanun shi jajjur.
"Me yasa kike tunanin zaki iya sakawa a cutar da ita," ya tambaye ta.
Wani mugun kallo ta mishi tare da tsuke fuska babu alamar wasa ta ce mishi.
"Ka b'ace min da gani" yadda ta daka mishi tsawa, yasa shi da baya tare da barin kofar da sauri duk rashin hankalin shi yasan halin ta idan ranta ya b'aci bata mishi na wasa, dan haka ya juya tare da komawa dakin shi. Yana barin wurin ta kalli Mandiya ta ce mata.
"Ki nimo min waziri maza"
"An gama Uwargijiya ta, baya goya marayu giwa me tafiyar kasaita" sannan ta fita, can ba da jimawa ba, sai gasu tare.
Da sallama suka shiga babban zauren tana zaune ranta a jagule.
"Wai kina da nima na?"
Kura mishi ido tayi na wani lokaci, kafin ta zuba mishi ido.
"Haka ne" daga haka ta mai da hankali kan abinda ta ke yi.
"Ina da abu me muhimmanci ina son tafiya"
Ya gaya mata.
"Tun da kana da abu me muhimmanci ka tafi, zamu yi magana amma karka manta da Haima" da sauri ya d'ago kai yana kallon ta.
Murmushi tayi tana wasa da warwaron hannunta.
"Ita da uwarta da take jin kanta ita wata ne ba, duk matan masarautan nan girmama ni suke amma matar ka ko hmm" ta fada tana kallon shi.
"Ranki shi dade me kike bukata!" Ya fada yana matse hannun shi.
"Yawwa dan gari ina so a saka idanu a duk motsin Barkindo, kafin ya zama sarki haka ba zai samu ba, sai da taimakon ka. Idan wani abu ta faru Bana tunanin zan iya yafewa"
Tana gama fadar haka ta juya tare da barin wurin, shi kan sa kamar an fara shi a wurin, jin jikin shi yana rawa, ba zata iya yafewa ba akan waye? Akan Yar shi mana, idanun shi sun cika da kwalla, baki daya ya rasa yadda zai yi da Bingel kai ko kashe ta yayi bai huce daga bakin cikin ta ba, mata sai ka ce jikanyar shaidan.
""
A can dakin shi sintiri yake,
Yake yana nazarin yadda zai fita wato ya nufi rugar nan da suka dawo daga can, yasan anyi rasuwa amma baki daya bai san me ya faru ba, dan taki yarda ya fita waje ta ce bai saba ganin mutuwa ba, kar ya gani ya razana. Haka yayi ta nazarin abinda zai yi.
*
Sokkoto.
Ba laifi tafiyar bata wani tsawo, amma kuma tafi zaman da yake, amma kuma yana samun kulawa daga wurin Inna Marwa da Yaranta, haka kuma Galadima da Sarkin Gida suna bashi kulawa, sai dai zuciyar shi ta kasa kwanciyar hankali domin kullum da Minani yake kwana yake tashi har yanayin yake hasasowa a idanun shi, na yadda ta kara girma ta zama babbar mace.
Sai dai idan ya tuna da haka zai ta shi zana hotonta, dan dama ya fara haka tun daga masarautan su, dan haka ba sabon abu bane a wurin shi.
Bude yar karamar akwatin shi nan yayi ha ciro wata yar karamar jaka, wacce duk fadin ta bata wuce tafin hannun shi ba,ya ciro jigidar ta, yana kallon su yana murmushi. Irin wannan yanayin, idan ya tuna yana kara saka shi kamar ya fita ya bazama duniya niman ta, kamar yayi ta yawo kasa zuwa kasa nahiya zuwa nahiya lardi zuwa lardi kusufa kusufa.
Tabbas zai nimo ta, matukar tana raye sai ya binciko a duk inda take a fadin duniya.
*
Kasancewar mako guda aka bashi domin shiryawa, fitowa yayi cikin shigar yaki, kamar sauran mayaka. Gwanin ban sha'awa idan ka gan shi, amma kamilalliyar fuskar shi da bata da yawan fara'a ta nuna tsagwaron jarumtar shi da kamalar shi, da fari ganin shi yasaka baki daya dakarun fashewa da dariya, kasancewar shine yaro matashi a cikin su, isowar shi da shigar shi hadi da kwarjinin shi wanda ya fidda sirrintacciyar ikon shi da nasabar shi yasa duk suka sunkuyar da kan su, zuwa yayi ya tsaya a jerin gwano, Gidado ba gefe can yana rubutu, tare da kallon shi yana dariya.
Farko a rayuwar shi da yaga wanda ya dace dabi'ar kanshi, kamar Hassan din shi. Suna tawowa yake tambayar mishi.
"Kana ta shirin yaki baka shirin komawa gobir ne?" Tunda ta kalle shi sau daya bai kuma kallon shi ba, dafa kafadar shi yayi yana mishi alama da hannun.
"Malam ka saurare ni, dole mu koma domin niman hakkin Ammyn, sannan idan bata koma ba haka yana nufin ta gudu bata koma ba, nazarci abinda nake gaya maka idan har zaka shiga yaki domin kare wasu al'ummar me yasa ba zamu kare martabar mu ba, daga ni har kai sunan Shegu shine tambarin mu, ita kuma Ammyn fa? Ka duba makomar ta" daga haka ya juya gindin bishi ya zauna, yana kallon shi shi kan sa Lamido ya jima a tsaye kafin ya nufi wurin taron, wani ikon Allah sarkin yaki ya zuwa ya mika mishi tutar borno, a duk tafiyar yaƙin da za ayi matukar aks baka tuta yana nufin kai ne mataimakin shugaban rundunar yakin kenan. Abinda ya faru dayawan dattawan da suka jima sun ji haushinsa kuwa, abin bai dame shi ba, haka da sarkin yaki yayi yana nufin koda ta Allah zata faru da shi toh na gaba shine Lamido. Shine mataimakin shi, kuma haka ba karamin al'amari bane asha'anin yaki, duk wanda aka bashi mataimakin toh ana nufin ko Meye shi zai jagoranci rundunar, su kuma basu san da haka ba, taya zaa zabi wanda ba kabilar su ba, a bashi shugabancin rundunar yakin su.
Haka ya haifar da gulma da tsegumi, yayinda shi kuma Sarkin yaki ta bada haka ne dan ta nanne zasu cimma burin su na maida su masarautan su, idan har ya iya tsayawa a matsayin mataimakin shugaban rundunar toh tabbas zai iya da mayakan gobir. Sauran dabara kuma tana hannun duk wani me ƙoƙarin ganin ya kwato hakkin Bello wannan shine makasudin bashi tutar. Kuma hallo dai idan suka yi nasara dole shi zai kafa tutar a sasansanin abokan yaƙin. Yin haka kuwa itace ribar tura shi matsayin da yake.
Haka suka bar masarautan, zuciyar shi ta tafi ga yaki.
A wannan lokacin wasu daga cikin rundunar su, suka kullawa kan su sharrin idan aka samu nasara toh a warware idan kuma aka fadi....
*Kuyi hakuri na gaya muku gaskiya ina da abubuwa dayawa a gabana yau din ma kawai kar na barku haka ne yasa na muku kaɗan sai tambaya ake ana jira labarin Kallabi ban yi rabi ba, idan nace zan yi gudu dayawa kuma labarin can make sense*
_zan yi Amfani da wannan damar domin na tallata muku sabon littafina me suna ZAYN MALIK 300₦ne zai zo Insha Allah 1/7/..._
#Mai_Dambu
[5/29, 8:35 PM] Mai_Dambu: KALLABI..!
A Tsakanin Rawuna
*EWF*
BABI NA TALATIN DA TAKWAS
https://youtu.be/KBR-LrH5RZg
PLEASE Subscribe My channel Ontop Hausa novel.. thank you
Lallai sun shirya mishi gadar zare, yadda idan ya fada ciki sunan shi ba zai kuma bayyana ba balle har a kai ga kiran shi Jarumi, sai dai sun manta da akwai Allah, da wannan yanayin suka isa masarautar Chadi, inda aka kuma had'a runduna guda aka nufi inda xa ayi yaƙin. Kuma wani abinda ya kara basu mamaki yadda Sarkin yaki yake jan shi duk wani abu me muhimmanci yana tare da shi abin har ya fara basu haushi, bayan sallah isha ya dawo yana me niman inda zai zauna, sai suka hana shi.
A miskile ya kalle su, bakin shi yana motsi, kamar me magana sai kuma ya lashe fatar bakin shi, sannan ya dauke kai ya nime wani wurin zai zauna sarkin Yaki ya mike a inda yake ya ce mishi.
"Allah ya baka nasara ga wuri zauna"
Wani irin yarrrrr yaji tun daga tafin kafar shi har zuwa tsakiyar kan shi, a hankali ya zauna tare da daura daya akan daya.
Yadda ya zauna sai da rabin su, suka mike tsaye, sai abin ya zama kamar ya fito shugaban ne baki daya. Mika mishi taswirar kasar yayi da yadda zasu yi yakin, cikin wani irin kaifaffen idanu tare da baiwa akan yaki ya fara kallon taswirar yana me kura mishi Idanu, a hankali ya kalli sarkin yaki, lashe bakin shi yayi tare da mishi alamar yana bukatar alkalami, daga can nesa da su aka ce.
"Dama da kurma aka zo yaki? Toh idan aka samu matsala fa?" Duk da a hankali suka yi maganar, sai dai dan banzan kunnen shi me kama da na maciji yasa shi jiyo abinda aka faɗa.
Mika mishi alkalami da tawada aka yi, ya saka taswirar a kasa, sannan ya shiga kasa kan rundunar yakin kowani mutum da yake da karfin gaske aka saka shi ya jagoranci rundunar shi, shi da Sarkin yaki suna gaba.
Yadda suka shirya yakin sai ya baka mamaki. Masu sulke da garkuwa sune a gaba. Masu kibbau a bayan su, masu Mashi abaya su, su kuma suna bayan masu Mashi da takobi kenan. Wannan abin ya bawa kowa mamaki. Sannan ya kalli sarkin yaki kamar ba zai magana ba, a matuƙar gajiye ya ce mishi.
"Idan muka fadi toh tawagar suka mana haka" sannan ya mike a hankali, ya bar wurin.
"Toh kun ji dai? Duk wanda ya bamu matsala zamu iya bashi sama da haka"
Yana gama fadai haka ya bar wurin, suna tashi aka fara kananun magana, akan me za a nadai lamidio damar mulkar su.
Yana shiga tantin shi, ya kwanta cikin gajiya da maganar da yayi. Yadda yake kwance Ammyn da Gidado a ran shi sai Innayoh. Yayi zurfi cikin nazarin yawan kukan da yake ganin Ammyn tana yi, kumshe dara daran idanun shi yayi,.masu kama da me jin barci, a yanzu da yake matashi kenan Allah ya zuba mishi kyau da haiba idan ya kai irin su ashirin tabbas za a mai ruwa rana da shi.
A hankali barci ya fara fisgar shi, jin kamar ana motsi a bakin tantin shi yasa shi jan takobin shi, tare da kura musu ido.
Haka suka gama zaga tantin basu shigo ba, ya kwanta abin shi.
---
A yayinda dare ya raba, kowani dan Adam barci yake domin hutawa, haka ya kasancewa Lamido yana ta sharan barcin shi kamar ba gobe, "shiiiiiiii!!!" Yake kara matsowa tantin shi, ko kadan bai dan kome ba, dan haka yana barci ne cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.
A hankali macijin yake kara kusanto shi, wanda tun daga nesa yake jin hucin macijin bude idanu yayi, ya mike zaune yana kallon kofar tantin shi a bude, murmushi yayi sannan ya koma ya kwanta, a hankali macijin ya nufe tantin, kato me girman gaske koda ya shigo bai farmake shi ba, asalima kwanciyar shi yayi koda macijin ya fasa kai zai sare shi, bai matsa ba sai dai shima macijin cak ya tsaya ya kasa aiwatar da kome, haka ya juya ya fita ya kasa kome. A daren macijin ya koma inda ya fito domin dama turo shi aka yi, take ya koma wurin waɗanda suka turo shi.
Ko a jikin shi barcin yi yayi sai da asuba aka samu wasu mayaka biyu sun mutu sakamakon saran maciji,
Da gari yayi haske aka yi jana'izar Mutanen, suka shiga niman yadda zasu cigaba da yakin su, ya dauke su kwanaki goma kafin aka fara yaƙin, wanda ba a dade da farawa ba, sarkin yaki ya samu rauni a kadadar shi dole aka bawa Lamido damar jagorantar yaƙin, gashi yaro karami ga tunanin gida da Sarkin yaki, haka yayi ta yakin nan ga dan banzan taurin kai, abu biyu ke iya tsayar da su, kula da lokacin Sallah da kuma rauni, ko ta abincin ba a kulawa, sai da aka shafe sati Daya ana bata kashi tare da jagorancin shi, Allah ya basu nasara dayawa mayakan sun gudu ba tare da sun tsaya ba, shi dai kamar jaraba. Lokacin da mutanen Sahil suka ga barnan da yayi musu, dole suka razana tare da juyawa da gudu, kafin shugaban su ya tsere yayi nasarar kama shi, da haka ya dawo da shi sansanin su.
Kallon shi yake cikin mamaki musamman lokacin da ya cire kayan yakin, ya nufi tantin shi.
"Kaii mayaki Jarumin amma kai jinin gobir ke yawo a jikin ka?"
Cak ya tsaya, zabga mishi naushi Sarkin yaki yayi yana faɗin.
"Me ka sani akan Gobirawa?"
"Taurin kai tsayawa akan ra'ayin su da karfin su. Kare abinda suke so! Shekaru ashirin da suka wuce" dawowa yayi cikin zafin nama ya fisgo lati ya wurga shi cikin tantin.
"Me yasa? Ina Aminatu da Bello?" Cikin jin haushi ya zabga mishi naushi, sai ta ya tintsira, sannan ya fita yayi wanka tare da sallah, yasan sarkin yaki yana son magana da shi amma fir yaki bada fuska, yana shiga cikin dakin yayi kwanciyar shi ko abinci bai Nima ba. Kowa nason sanin waye Bellon nan amma Yaron nan yayi fuska kamar bai san abinda ake bukata ba,
Yana barci Lati ya farka, kallon shi yayi, yana kara lissafin shekarun tabbas jinin Bello ne a gaban shi, motsi yayi ta yi tare da tashin Lamido, wanda yake son rama barcin kwanakin da bai yi ba.
A hankali ya bude idanun shi masu cike da barci, ya tashi zaune sannan ya warware mishi igiyar ya nuna mishi hanya, sanan ya koma ya kwanta.
"Babu inda za ni sai na gaya maka abinda yake faruwa a cikin masarautan gobir"
D'ago kyawawan idanun shi yayi da suke cike da mugun barci, ya kura mishi su.
"Su da wacce tsiyar tarkacen su bana son jin labarin" ya fada sannan ya koma ya kwanta. Ya cigaba da barcin shi.
"Sai na baka labarin kome da kome koda zaka kashe ni ne!"
A baya so a ba yadda ya iya da mutumin ya bashi labarin abinda yake faruwa, tsabar miskilanci. Sai ma gyara kwanciyar shi da yayi ya juya mishi baya. Sam Lamido wani irin mutum ne da baka iya gane Damuwar shi akan fuskar shi, kullum kamilalliyar fuskar shi boye abinda yaƙe ran shi, Lati yayi mamaki yadda Lamido bai fusata ba, Asalima sai share sa yayi ya kama barci, dan sauraron shi ya saurare shi amma baki daya yaki nuna yaji shi.
Washi gari suka cimma garin Sahil da yaki, wanda haka yayi masifar d'aga hankalin mutanen masarautan, babban burin shi yayi arangama da sarki Arkhan, kuma Allah da ikon shi yayi haka, domin bai fito daga fadar ba sai da ya yanke kan dan banza hankalin shi ya kwanta. Basu wani tsaya ba. Suka bar ba kasar.
Tafiyar kwanaki suka yi sannan suka isa Chadi kwanan su biyu, suka dangana da borno cikin farin ciki da jin dadin shehun Borno ya tarbe su, bayan an yi musu kyakyawar walima. Tun daga bakin kofa ta zuba mishi ido.
Duk kin Baffa'm da yaki sai da ya Haifi mayaki, ta fada a ranta. Lokacin da ya iso kan shi a sunkuye ya tsaya a gaban ta, jakar da yake hannun wani mayaki ya karba tare da ciro kan sarki Arkhan!
Kallon shi tayi tare da cewa.
"Me yasa ka kawo shi nan?"
Mikawa mayakin yayi, sannan ya karkade hannun shi ya cewa mayakin.
"Ka binne"
Sannan ya shiga cikin gidan,
"Ni dai wannan halin naka ya ishe ni" ta fada a r
Tsawa ce, rudewa yayi yana kallon Innayoh kamar zai yi kuka har idanun shi yana cika da kwalla.
"Na gaji da shariyar ka, nice mahaifiyar ka idan ban san dariyar ba yaushe zan san kukan ka? Na yarda kayi yaki amma wancan mutumin yana da nasaba da ni waye shi"
A sanyayye ya ce mata.
"Arkhan Sarkin sahil wanda ya nime a ba shi ke"
Wani wawan jiri ne ya kwashe ta kamar zata fadi, rike ta Innayoh tayi, wuce su yayi ya kawo mata ruwa ta sha, wai a haka bai gaya mata kome ba, shi kan sa baya jin magana akan haka shi yasa yaji dadi da Gidado bai ji labarin ba, duk yadda Innayoh taso jin labarin fir yaki gaya mata, dan haka ya share su tare da tsiro barcin hutu.
Aikuwa Gidado da ya dawo gidan aka bashi labarin zama yayi yana kallon Hassan din shi da yake barcin karya, wani abu yayi da hannu dole ya bude idanu.
"Ashe ka dawo naji labarin abinda ka dashi me ya faru?" Yasan ya sake ba bashi labarin abinda lati ya bashi, nan ya bashi labarin da ya sani sauran ya ajiye a ran shi.
Haka yayi ta nacin son ya san Meke faruwa amma Lamido yaki dole ya kyale shi. Amma yana ji a ran shi akwai abinda Lamido yake boye mishi, domin baki daya bai da gaskiya. Kuma yana jin wani irin kunci a ranshi wanda duk lokacin da ya shiga ko lamido ya shiga haka suke ji, suna raba damuwar su.
Kura mishi ido yayi kafin ya bar mishi dakin domin yasan ba zai gaya mishi ba,
**
Rugar gona.
Basu duba kankantar shekarun ta, Inonon tayi ta zuba mata tsumagiya, tana kara zane ta, abin tausayi ko ihun da yara suke idan ana dukar su bata yi, sai ajiyar zuciya.
Sai da suka gama dukar ta, sannan ta dauko barkono da bakin wuta ta danna mata a tafin hannun ta, sannan ta watsa barkono, wani kara yarinyar ta sake me hade da fitsari, bata koma motsi ba, "wuuuuuuuuuuuuj"
Suka ji karan kudar zuma juyawa kowa yayi yana son ya ga ta inda suke domin su gudu, suna zuwa baki daya suka yanyame yarinyar ko tafin hannun ta baka gani domin sun mata riga ne, a tsorace kowa ya watse ban da Inonon da take tsaye tsabar tsoro, a fusace zuman suka yo kanta, daya ne kawai ya zabga mata harbi a bakin ta biyu kuwa suka zuba mata a hannun ta, kafin kace kwabo ta fasa ihu tare da taka wutar da ta dauko. Garin turmushi da zafi ta zauna akan barkonon da ta saka mata, haka ta cika gidan da Ihu, babu wanda ya fito domin baki daya babu wanda yake jin a ran shi ya fito.
"Assalamu alaikum" ya shigo yana kallon gidan babu wanda da sauri ya dawo wurin Inono, sai lokacin zumar suka tashi daga jikin ta, yana kyalla idanun shi ya ganta, da sauri ya d'ago ta ya fita da ita.
Sauran mutanen gidan sun dauka cewar zumar ne haka.
Daukar ta yai suka bar rugar zuwa cikin gidan gonar, ajiye ta yayi yana kallon ta, ruwa ya diba ya watsa mata, ya kalle ta yana murmushi. Kallon shi tayi tana me zare idanu.
Hannun ya saka a cikin Aljuhun alkyabar shi ya ciwo mata abubuwan da na ciye-ciye. Kallon shi tayi tana ajiyar zuciya, take saukewa akai-akai tana kallon abin hannun shi, Anum tana cikin Yaran da Allah bai daura musu kwadayi ba, tun Uwarta tana nan, bata da kwadayi domin ko sun yi abincin dakyar take tsira da kason su....
*Barkan ku da warhaka ya iyalan ku ina muku fatan Alkhairi mun dawo bakin rai bakin fama*
_Zan yi amfani da wannan damar domin tallata muku sabon littafina me suna ZAYN MALIK 300# kallabi na da tsawo gaskiya ba zan iya kammala shi in 2 months ba, gaskiya amma idan na samu hali xan gama lokacin da ya dace idan ban gama ba zan fara Zayn Malik domin kar na kare a jikin free book 🤣😂 bamu nime kudi ba, idan kuma na gama zaku huta domin ALLAH DA GASKE KO RABIN LABARIN BAMU YI BA, IDAN KUMA KUNA SO A YANKE LABARIN SHI KENAN_
#Mai_Dambu
[5/29, 8:35 PM] Mai_Dambu: KALLABI..!
A Tsakanin Rawuna
*EWF*
BABI NA TALATIN DA TARA
*ABIN DA KA SAMU YAU, NA WASU NE WANDA KAYI HAKURI KA SAMU GOBE SHINE RABON KA DOMIN KAIWA GOBEN SHINE ME WAHALA FATAN ALKHAIRI NAGODE SOSAI 🥰😍*
Kasa tayi da idanun ta, tana kallon hannunta idanun ta sai kara cika yake da ruwa, gyara zama Barkindo yayi yana kallon hannun ta, kafin ya rike tafin hannun yana hura mata iskar bakin shi.
Bayan tafiyar Mahaifiyar ta da rasuwar mahaifin ta yau ce ranar farko da wani ya tausassa mata ya kuma tsaya mata, a hankali take sauke ajiyar zuciya irin me hade da kukan nan irin wanda ba kasan lokacin da zai zo maka ba, Anum fara ce kal kamar uwarta, ga ta da Ubangiji wanda ya ke cunkushe, musamman da babu uwarta sai ya hargitse ya cunkushe kamar ba jikin mutum yake ba.
"Ci kin ji" ya fadi mata yana kallon yadda take kuka.
"Kina son wani abu ne?"
"Ummina" ta fada cikin bagwaren fulatancin da bai zauna a harshen ta ba.
"Kiyi hakuri bata nan amma zata dawo kin ji maza ci sai na mai dake" girgiza mishi kai tayi tana kallon kasa.
"Toh tashi na kai ki gida" wani masifaffen shasheka ta ja, tana kallon shi.
"Kina jin yunwa ko?" Ya fada bayan ta koma wurin dokin da ya kawo su, ya ciro abinci da ya tawo da shi nakiya ce da alkaki, da taji zuma ya mika mata. Duk da tana tsoron shi bai hanata kukan ta ba, sai ma kin amsar da tayi ta rikice mishi da kuka. Zama yayi ya sakata a gaba.
"Toh ya isa mana." Ya fada mata cikin rarrashi, ya jima yana rarrashin ta. Kafin ya ta amsa taci kadan.
Jan ta yayi suka yi ta yawo a cikin gidan gonan, sun yi yawo sosai sannan, sai da dare yayi sannan ya mai da ita gida, abinka da yarinta. Shiga cikin gidan ta yi tana rakube rakube har ta shiga dakin su.
Kwanciya tayi a kasa, dake ta gaji barci yayi gaba da ita a wurin, sashi gari matar Haladu kanin Salihu me suna Tani, ta bude kofar dakin ta watsa mata sauran ruwan kanzon da dabbobi suka sha, da mugun tsoro ta farka ta fara sosai jikin ta, ai kuwa su da sauran matan Yan uwan bingel suka rufe ta da bulala, tasha mugun bugu. Sai dai kamar abin hadin baki suna mata dukar, bata motsa ba har suka fita. Tani tana aikin diban dawan da zata surfa taji kamar abu ya shiga rigar ta, karkade shi ta je yi ya zuba mata ciwo, wani irin ihu ta kwala tana tuma da tsalle, Larai da Iyatu da gudu suka shiga cikin dakin su, nan ma suka hadu da nasu, tun daga ranar ya zama ko me suka yiwa Anum, sai an musu abin da ya sa suka fara ja da baya da ita kenan, aka shiga turata kiwo. Barkindo kuwa mahaifiyar shi da ta nime shi ranar da ya bar gidan koda ya dawo, sakawa tayi aka rufe shi a daki na tsawon kwanaki...
A kowanni rana na duniya sai ta fita da kiwo, tun bata iya ba dan wani lokaci shanun shiga inda zasu cutar da kan su suke, wani lokaci kuma su ja ta,
**
Bayan shekara takwas
A hankali rayuwa yake tafiya kwanaki yana komawa mako, makwanin suna rikidewa zuwa watanin yayinda watanin suka yi shura izuwa shakaru, a hankali Lamido da Gidado suka zama
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 39