a bashi duk daya ne, sannan ita matar da zata zauna a kasata bana jin zata samu karfin shiga cikin hayaniyar masarautan nan"
"Allah ya baka nasara, batun ka dawo da mulkin ba zai yiwu ba, domin ko al'umma sun bukata. Ba zan taba iya rike wannan muƙamin ba bayan dan uwana Yakubu Yana bukatar shine ɗan haka kai din nan dai kai ne zaka rike mana shi" shiru zauren ha dauka domin dukkan su, sun yarda fa Abinda Waziri ya fada koda an bashi mulkin Yarima Yakubu ba zai taba yarda ba, gwara mulkin ta cigaba da zama a hannun Baffan su domin haka ne zai saka a zauna lafiya.
Sannan ya gyara zaman shi ya ce musu.
"Batun fadada kadada fa?"
"Gaskiya akwai maganar ba zamu yi yaki ba, idan zamu fadadda kadada kuwa dole sai mun gina zaratan mayakan mu sannan mu tafi da'awa idan ba amshi mulkin ba muna da ikon fadadda kadadar mu, a gani na ko da zamu fadadda kadada dole zamu tura yankunan da suke jikin mune domin su cure a cikin mu yadda babu wanda zai mana tawaye. Sannan kuma akwai damar da mai martaba yake dashi bayan an daura auren shi da Fulani Aminatu yana da damar niman kwarkwara daga wadannan yankunnan da zasu shiga cikin masarautar mu."
Girgiza kai yai kafin ya ce musu.
"Bana sha'awan kwarkwarah, mace daya nake bukata sai dai idan halin haka ya taso zan kara aure"
"Toh Allah ya tabbatar da Alkhairi, haka yayi Wallhi" anan sai suka ajiye maganar ba za ayi yaki ba, kuma maganar aure, an shirya manyan daga masarautan suka tafi har Gombe da kome da kome, suka tafi dan har da mata da har da Jakadiya, idan aka ce sai an tafi an dawo ba zai yiwu ba sabida nisar tafiyar.
Duk da haka sai da Yarima Yakubu ya sake ce wani abu.
"Duk matan da suke cikin masarautan nan babu mace sai an tafi har zuwa wata nahiyar an dauko mace gaskiya wannan shine kwaba"
Babu wanda kula da zancen shi domin sun fahimci, lamirin shi babu ta arziki sai ta tsiya kuma da za a bashi damar haka ba zai iya ba, zunzurutun ya kular da kowa ne, shi din gashi nan dai,kamar me almatsutsai, kuma babu abinda yake damun shi.
Ko shi kan shi sarki Bello yana jinjina rashin mutuncin Yarima Yakubu, sannan batun bin yan matan bayin kuwa bai fasa ba, domin har yau yana bin su, kuma idan yayi abinda yake so dasu yai musu barazanar zai kashe su haka yasa musu matukar firgice da mugun tsoron shi....
_________________________________
*Ban sani ba gaskiya uzuri sun dan sakoni a gaba idan na kammala maybe Saturday Insha Allah zamu sake hadu amma babu Alhamis......*
#Freestorie
#Mai_Dambu
[3/28, 11:47 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: ƘALLABI...!
A tsakanin Rawuna
EWF
FREE BOOK
Mai_Dambu
**
~Masu azancin harshe sukan ce dakan d'aka shikar d'aka....masana harshe kuwa suka karasa azancin da da tankad'en bakin gado.... Inji Masana harshen Hausa~
Wannan haka yake domin sarakunan baya suna daukar ɗiyoyin su mata masu daraja su hawa wata masarautan, ba dan kome ba sai dan kulla alaka me kyau, sake raya zumuncin su.
Ko nace masarautan buba Yero! Masarautar ce da Fulani suka kafata,karkashin jagorancin Mujaddadi Shehu Usmanu danfodiyo, inda ya turo wakilin shi Muhammad Kwairanga. Ita kanta Gombe an samo ta ne daga wasu kabilun.
Tarihi ya nuna a karni na 13 aka fara sanin garin Gombe, sai dai kafin wannan lokaci an yi wadansu mutane masu karama da sarauta da ake kira ‘Soninke Mandigos’, wadannan mutane su ne suka samar da tsatson garin Gombe, kuma littafin ‘Tarekh-el- Sudan’ (Tarihin Kasar Bakake) na musu lakabi da ‘Fararen Shugabanni’.Wadannan mutane ana kuma kiransu da ‘Kaya- Manga’. Sun mulki yammacin Sudan na wasu karnoni da dama. A cikin Kaya-Manga an samu wani mutum da ake kira Bin-Kaya Mob, wanda sarki ne a wata masarauta da ake kira Mande, a yammacin Sudan din, wanda kuma wannan sarki ya ci zamaninsa a cikin karni na 10.
Sarki Bin-Kaya Mob yana matukar ji da jikansa Bin-Abubakar, wanda har ta kai ko kuda ba ya so ya taba shi. Ya mayar da shi dan lelensa kuma shafaffe da mansa. Hakan ce ta sanya Kaya Mob ya bai wa jikansa wani bangare na masarautar tasa da ake kira Ukuba. Bin-Abubakar kaka ne ga Aliyu Ukuba, wanda shi kuma yake mahaifi ga Usman. Aliyu Ukuba shahararren malami ne, ya haddace Alkur’ani, wanda daga baya aka hada shi aure da ’yar gidan wani attajiri a garin Tibati, inda kuma suka haifi Usman. Zuri'ar Usman ta rayu na wasu tsawon karnoni har zuwa lokacin da suka tashi daga yankin gombe.
A cikin shekarar 1913 Hedikwatar Gombe ta tashi daga garin
Gombe zuwa Nafada, wanda a cewar Nasarawa Nafada ta fi
saukin zuwa daga manyan garuruwan Arewa irin su Kano da
Bauci da Maiduguri da sauransu. Har ila yau a wannan shekarar
aka girke sojoji masu lura da shige-da- fice a kan iyaka. Sarkin
Gombe Umaru ya halarci wani hawan daba da aka yi a Kano,
lokacin da sarki Edward na III ya kawo ziyara Kano. Bayan sarki
Umaru ya dawo daga Kano ne, ya sake zabar wani
gari da ake kira Doma karkashin Akko. Inda a shekarar 1919 aka
sake rada wa garin suna Gombe-Doma.
A kuma wannan shekarar ce aka mayar da Gombe- Doma zuwa
masarautar Bauci, sannan aka rage mata dagatai zuwa 3, wanda
a da take da 13. Daga nan kuma sai aka dawo garin Gombe.... Takaitaccen tarihin masarautar Gombe.
__________________________________
Masarautan Gombe
Kallon Kanin shi jibril wanda suke kira Babayo, yayi cikin nutsuwa sanna ya ce mishi.
"Jibril ina ganin kamar ba zasu amshi tayin ba?" Shiru yayi kafin ya sunkuyar da kan shi cikin ladabi da biyayya.
"Hamma Shehu, babu inda ba zasu so tayin ka ba, sabida Fulani Aminatu tana da nagarta, kuma kai ma nagartaccen mutum me, sannan idan yadda ka hango ne, Sarki Bello ya dace da Fulani Aminatu, kuma idan kayi nazari a da tarihin shi yana daga cikin sarakunar gobir da suke kin tashin hankali ba laifi bane idan aka bashi tunda har aka yi nad'in sarautar babu wanda yayi yunkurin bashi mace. Haka yana nufin cewa sun gaji da bawa mazan masarautar mata ne sabida.."
Shiru yayi yana kallon kasa, gyara zama Mai martaba Sarkin Gombe ya ce.
"Babayo kana hidima da Aminatu domin Buba ne ko kawai dan ni ne?" Haɗe hannun shi yayi cikin tsannanin tsoron da tashin hankali kan shi sunkuye ya ce.
"Ina yi ne dan Fulani Amrah" d'ago kai Mai Martaba Sarkin Gombe yayi ya kura mishi ido. Sannan Babayo ya cigaba da cewa.
"Nayi mata alkawarin tsayawa Aminatu, bakwai dan Abubakar yana son ta ba, sai dai muna duba Gombe mu ne kafin mu zartar da hukunci. Sannan idan na duba ita kanta kafin ta san Meye soyayyar ya dace a fitar da ita daga cikin masarautan yanzun take da shekaru goma sha biyu. Daidai ta tashi a hannun mijinta. Sannan haka zai saka ta taso da soyayyar mijin ta da kuma sanin sha'anin mulki."
"Na yarda da kai, ku shirya kome yadda zai tafi" ya fada,
"Allah ya taimake ka, Ubangiji ya baka nasara Allah ya kare ka gaba salama baya salama"
Lumshe idanun shi yayi tare da jinjina kai, ba wai yana da zabin ba da auren Yar shi karama bane sai dai bai da yadda ya iya ne kawai, sannan tun lokacin da yaji ra'ayin Sarki Bello yaji a ran shi Aminatu ta dace da shi sabida tashin da tayi a cikin gidan sarautar a ware, kasancewar mahaifiyar ta kabila ce ba bafulatana bace kuma uwa Uba baiwa ce a cikin masarautar sarki ya yantatta. Sannan duk cikin masarautan tafi shiri da Babayo kasancewar shine mutum na farko da ya fara nunawa dan uwan shi dacewar ya shigo da ita cikin masarautar a matsayin kwarkwarah mana. Kuma Sarkin ya amince.
Mahaifiyar Aminatu ta kasance daga cikin bayin da aka kamo cikin ganimar yaki, kuma aka kai su shashin Fulani kilishi, maketaciyar mace mara imani, ga cin zarafin bayi kamar me.
Kasancewar Babayo yana yawan kai sako yake ganin yadda ake cikin zarafin bayin, yaso shi ya nemi Amrah, amma sai yaga koda ya nime ta, ba zata samu sauki ba a gidan shi domin shima lokacin matar shi tana da Masifar kishi. Amma idan a Kwarkwarah ne sarki zai d'aga darajar ta da kimarta. Da wannan ya bawa Dan uwan shi shawara kuma yayi na'am da shi.
Za a iya cewa table rabo ne ya tsaga bata jima da tarewa, sai ga ciki a lokacin sarki Shehu yana da mata hudu, kuma dukkansu yaran su manya.
Uwargidan Mai Martaba itace Fulani Shatu yar Sarkin Yola, sai Fulani Habibah daga masarautan kano,Hajiya kilishi daga nan yar wazirinsa ce.
(Ga masu bukatar Wata Alkaryar 300 uku me zasu iya tuntubar wannan number 08130269641)
Sai Fulani Maimuna daga daga nan cikin masarautan yar Kanwar mahaifin Sarki Shehu ce, sannan suna da yara kusan kowanni daki, babban abinda da yake faruwa su sauran matan basu kai Kilishi azababben kishi ba, domin ita baki daya gani take itace ta dace da Mai martaba ba su ba, haka yasa kowa take ganin zata taka, su kuma sauran suka ce basu iya ji ba, kalmar nan ne da ake cewa Haushin kaza huce kan dami, shine ana kawo Amrah ta sakata a gaba dama kuma tun can haka ne ta tsani Yarinyar tun farkon kawo ta. Amrah ta sha bakar wahala a hannun kilishi.
. Haka yasa koda tazo haihuwa ita da kanta ta haihu domin Kilishi ta hana kowa shiga cikin dakin ta, koda ta haihu an ji kukan jaririya, amma ba a ji motsin uwar ba. Dan haka baiwar da take tare da ita Innayoh itace ta shiga ta ga rai yayi halin shi. Ga jaririya a gabanta. Abin tausayi haka Innayoh ta dauke jaririyar ta kaita wurin Fulani Shatu. Babu laifi ta amshi yarinyar amma ranta bai so haka ba.
Lokacin da Mai Martaba yaji labarin mutuwar Amrah, da sakon da ta bawa Babayo, yayi kuka kamar zai yi yayya anan ya shiga bincikar dalilin da ya hana Jakadiya, kasa fadar gaskiya suka yi karshe Innayoh ce ta gayawa Babayo, wanda a lokacin shine mafi kusanci da mai martaba, amma yaki amsar mulki. Domin yace a bar shi lafiya da dan uwan shi. Shi ya gayawa mai Martaba abinda ya faru, shi kuma ya rantse ko za a bar shi a duniya shi da kilishi ne ya yafe ba zai kuma zama da ita ba, wannan dalilin ya kuma haifar da tsannar Aminatu a ran Kilishi.
A hankali yarinyar ta taso babu soyayyar kowa sai ta Innayoh, domin shi kan shi Mai Martaba ya tsani yaji sunanta ko ganin ta, wanda bayan rasuwar Mahaifiyar yake mugun kaunarta. A hankali aka wayi gari baya son ko ganinta, haka yarinyar ta zama kamar yar tsakar gida. Tana da Shekara biyar suka saba da Buba dan gidan Babayo, wanda shi yana da shekaru goma sha biyar a lokacin.
Haka ya taimaka mata sosai har take jin kamar shi ne kome nata, ana cikin haka Mai Martaba suka tafi wani gari garin numan, bikin kamun kifi ana ya hadu da wani mutumin da yaga sarkin Gombe yayi ta bin tawagar shi har ya samu ganin shi.
"Allah ya taimaki mai martaba, hmm kana raye amma shukar ka tana bushewa, ko baka bukatar bishiyar tayi yabanya ne? Zanen ƙaddara tayi tawo mugama da wasu manyan manyan alamura. Faruwar wasu abubuwan zasu biyo bayan kyakyawar yanayi me ɗauke da manyan ginshikai. Masu biyu zasu kasance a danbar kowacce ƙaddara, idan har zaka daka ta tawa, domin samun alaka me karfi ka gwada mika yasashen tsiron nan da yake gidan ka, amma bari na gaya maka bai zama dole haka ya zama karshen wasu abubuwan ba, kamar haka itace tushen wasu matsololin sannan karshen wasu matsalolin. Hawaye zai ta zuba, domin share duk wata cutar bayan kasa dole wannan tsiron na gidanka zata fitar da manyan manyan alamura. Kayi kokarin nan da shekaru bakwai masu zuwa ka gaggauta habaka yabanyar ka"
Daga haka yayi tafiyar shi, shiru suka yi daga shi har Babayo. Kafin suka kalli juna.
"Hamma kaina ya kulle" inji Babayo,
"Nima haka, Allah yayi mana jagora,amma abun da duba yanayin maganar shi domin yayi maganar cikin gaurariyar hausa ce." Inji Sarkin Gombe, shiru Babayo yayi sannan suka wuce inda zasu zauna kafin a fara bikin.
Bayan sun dawo suka samu yarinyar bata da lafiya, abin tausayi haka Uban ya wuce, kasar zuciyar shi yana jin zafin wofatar da ita da yayi, tun daga lokacin. Babayo ya mai da hankalin shi kan yarinyar, har zuwa lokacin da suka fahimci shakuwar so Buba, hankalin su ya tashi, domin bayan nan sun kuma cin karo da wani mutum a lokacin wani bikin sallah, ana bikin sallah, shima ya gaya musu haka amma sai basu dauka da gaske Ba.
Sai da aka yi karo na uku zuwa wani yaki da aka yi da wasu maguzawan dutse, da suke gaban shi garin Gombe suka sake jin irin wannan maganar, tun daga nan hankalin shi ya tashi ya shiga niman masarautan suka kasance masu kwazo da rashin tsoro, a lokacin sarki Ibrahim ya tab'a zuwa da wannan batun sarki Ibrahim ya ce mishi.
"A kullum kabilar mu suna facaka ne cikin jini, sannan mu bamu kasance masu tsoro ba,kullum kwayar jinin mu barandami ne, bamu fita niman aure dan mun san ba bamu za ayi ha taya zaka kawo yarinya me daraja cikin mu? Shin kana ganin yin haka ba zai hanata fuskarta takaba bane? Duk wani namiji a masarautan nan an hore shi da yaki ne! Dan haka ba zan maida maka Y'a bazawara ba ka kai ta wani masarautan."
"Naji abinda kace ko yaranka maza ai xaka iya nima musu auren tunda itama Yanxun take da shekara bakwai" domin lokacin shekarun ta bakwai ne, kuma Sarkin Gombe ya kagu ya dauke ta a cikin masarautan sabida yadda take Fuskar ta yawan rashin lafiya da yanayin takurawa.
Koda matan Sarki suka ji labarin ana nima mata babban gida a cikin gidajen sarautar kasar nan abin yayi musu zafi dan haka suka hasala...🔥
____________________________________
Hi guys barka dai Wayyo kuka ta kira cigaba cigaba... TOH gashi nan thank you 😍
#Mai_Dambu
[3/28, 11:48 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: ƘALLABI.....!
A tsakanin Rawuna.
EWF
Na
Mai_Dambu
https://www.wattpad.com/1201408229?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
**
_Soyayyar gaskiya tana faru ce a bisa wasu manyan ginshikai! Imma ƙaddara ta haɗa imma kuma lokaci ya haɗa sai dai mafi girman soyayyar gaskiya ita ce ƙaddarar da zata zo bazata_
A hankali rayuwa ya cigaba da tafiya tare da fatan samun daidaito akan Al'amarin Yar shi, har tsawon kwanakin da basu kirguwa. Kwanaki sun rikide zuwa makonnin,. Da tafiya ta mike makonnin sun rikide zuwa watanin. Watannin sun juya tare da curewa wuri guda inda suka haifar da shakaru.
A cikin wannan yanayin Fulani Aminatu tana da shekaru goma sha,, gefe guda kuma Kilishi ta sakota a gaba, inda take ganin kamar ai ita da take da Yarinya mace budurwa ta dace Mai Martaba yayi magana akan ta, amma ya karkata ga Aminatu dan hakan suka hade kan su kaf matan mai martaba idan ka cire Fulani Shatu itace kawai taki shirya al'amarin su domin ta fahimci wani abun da basu fahimta ba, na Mai Martaba yana kokarin fitar da ita ne dan halin da take fuskanta. Shi yasa bata takurawa kanta da azababben kishi akan Aminatu ba.
Sauran matan sun gama ajiye magana daya akan Fulani Aminatu, dan haka Fulani maimatu ta same Mai Martaba a babban zauren shi na hutawa. Cikin nutsuwa ya Kalle ta domin yasan matukar zata zo gaban shi da nata bukatar zata zo, dan haka ta zuba mata ido.
"Allah ya baka nasara, dama akan batun Fulani Aminatu ce,Mai Martaba kana ganin a dauki Yarinya karama a bada ita aure babu wani abu? Sannan wani masarautar ce za a bada aurenta ga Yayunta Mata Fulani Barirah da Fulani Saudatu, ga Fulani Sakinatu duk Yaran da suka fito cikin jinin sarauta ne ita kuma Yar yantacciyar baiwa ce fa"
Murmushi yayi tare da cewa.
"Bakar Saniya...
Mai fidda fararr Madara ta samar da ita taya zan iya juyawa ƙaddarar ta baya? Masarautan da za a kaita aure kiyi hakuri lokaci zai nuna mana ko ina ne" ba haka taso ba, taso taji ina ne za a kai Fulani Aminatu.
*
Tawagar Gobirawa.
Sun yi tafiyar tsawon mako uku zuwa hudu kafin suka isa garin Kano, inda suka samu kyakkyawar tarba daga Sarkin Kano, shi kuma yayi musu tanadi na musamman, inda ya bada wakilin shi tare da wasu manyan mutanen Fadar shi. Tare da rubuta wasika izuwa Sarkin Hadija, dan haka babu b'ata lokaci aka sake tadda dawakai da kayan Alfarmar tare da akwatin gwala-gwalai izuwa masarautan Gombe.
Tafiya ce wacce aka yi ta a cikin kwanaki biyu rak,Mai Martaba sarki hadeja ya basu wasu mahaya kasancewar tafiyar har da rakumai kusan guda saba'in shima kuma Mai Martaba Sarkin Hadeja ya bada wasu manyan munduwar zinari ga amarya sannan ya kuma kara wasu manyan dagatai da zasu yi rakiya har fadar Gombe.
Kafin su baro garin haɗeja, Sarki Abdullahi na Hadeja ya bada wasika ga amintattacen mahayin shi kamar yadda Sarki Muhammad na Kano yayi mishi. Ya bada wasikar a kai ga Sarkin Bauchi, tafiya ce ta tsawon kwana biyar.
Kuma a yadda aka san masarautun arewa suna da kyakkyawar hadin kai da taimakon juna, haka yasa suka marawa Masarautan Gobir bayan, domin a tarihi ya tabbatar da cewa babu masarautan da suke sa karfin jarunta da kuma yawan sadaukai. Ko yayya suka shiga yaki ba a kada su, sannan dayawan masarautun suna kokarin Niman taimakon su tare niman goyan bayan su a yaki, haka yasa dayawan mutane ke tsoron wanda zai bude baki ya ce yana da alaƙa da masarautar Gobir. Sabida karfin mulkin su. Da kuma iya sarrafa yaƙi.
Sannan sauran masarautar suna kokarin inganta zamanin lafiyar al'umma su,ba dan kome ba sai dan kar a fara yakin da za a yi asarar rayuka da duniyoyin alumma. Sannan babban abinda kunya ce ka shiga yaki baka da masu taimaka maka, masarautar Gobir ita ɗaya ke idda yaki babu mataimaki sai Allah wannan yasa kowacce masarautar ta shafawa kanta ruwan sanyi.
Baya haka haka kamar yadda sukewa Masarautar Gobir hidima itama masarautar da zasu shiga wani abu tabbas zasu iya taimakawa, wannan shine ake kira da karfin zumunci da dangantakar dake tsakanin masarautun.
Koda mahayin ya isar da sakon Sarkin Bauchi, aka fara shirin tarban bakin masarautar Gombe,. Sannan aka musu kyakyawar tanadi, kasancewar masarautar Bauchi tana cikin manyan Masarautun da Shehu Usmanu danfodiyo ya kafa da kan shi inda ya turo wakilin shi yakubun farko haka ya haifar da wani irin daidaiton tsari a garin da masarautan baki daya.
Bayan kwana shida suka iso masarautan Bauchi, kuma Alhamdulillahi sun samu irin tarban da ya dace dan dama tun fil azal mutanen Bauchi akwai karamci da amsar bakon su,. A ranar Sarkin Bauchi ya tura sakon zuwa ga sarkin ga bakin shin nan zuwa. Kuma tafiyar kwana ɗaya ce da wuni. Dan haka ya gaya musu zasu taso nan da kwana biyu.
.....
Masarautan Gombe.
Tun daga yanayin gyaran masarautan tare da kula da wasu manyan bangarorin cikin masarautan yasa kowa ya sha jinin jikin shi. Tabbas duk inda ake tsammanin za a kai Aminatu babban masarauta ce me karfin iko da mulki. Kaf masarautan babu wanda yasa inda za a aurar da Fulani Aminatu, amma Innayo ta sani, .haka Jakadiya Jebu tayi ta bugun cikin Innayo amma bata taɓa bude bakinta domin magana ba. Baya kadan a cikin masarautan.
Ana tsakiyar fadanci Mahayin barci yazo, cikin girmamawa ya isa gaban mai Martaba. Ya zube.
"Sako daga masarautan Bauchi, domin isa da bayanin jibi insha Allah baki suna nan zuwa"
"Ku bashi sulallar zinari, sannan akara mishi dawakai uku, a bashi bayi mata biyu, tukwaici ne ga sakon da ka kawo"
"Allah ya kara girma da daukaka, Ubangiji ya jibanci al'amarin ka"
"Sarki Ya amsa" sannan Mai martaba ya kalli kanin shi Babayo ya matsa kusa da shi,.ya fada mishi bakin da suke zuwa.
"Masha Allah, surukan mu na wannan masarautan mai albarka zasu taso jibi talata, zasu huta Laraba da Alhamis, ranar Juma'a Insha Allah muna fatan daurin Auren a cikin masarautan nan" inji Babayo, kafin kace kwabo Sarkin gida da Sarkin Zagi sun isa cikin gidan sun sanar baki daya hankalin kowa ya tashi daga wata masarauta ce? A cikin gidan kuwa tun da aka yi sanarwar Innayoh ta saka Fulani Aminatu a daki ta hanata fita sabida tasan zuwa kowa ya wasa wukar shi da fitinar shi dole a shirya ta, dan ma an kawo mata jike-jike Baffanta Babayo idan ba haka ba ai da yarinyar ta kad'e har buzun ta.
Tun daga ranar da aka sanar bakin Gombe na zuwa aka kara yawan tsaro aka kara yawan kulawa ba musanman, sannan shi kan shi Mai Martaba Sarkin Gombe Alhaji Shehu Usmanu, babban Addu'ar shi a fitar da Aminatu lafiya haka zai daka shi jin wata irin nutsuwa.
**
Rana bata karya kamar yadda aka sanar ranar Laraba talata da magariba, bakin Gobirawa suka iso. Sannan suka yadda zango a wajen garin gombe tare da tura bayi mata karkashin Jagorancin Jakadiya Rama. Tun kafin su iso aka shiga fadar da labarin ai bakin. Daga masarautar Gobir ne, kafin kace me labarin ya karade cikin gidan, take kowacce mace ya kama kanta da Yaran ta, tare da ganin adalcin da Mai Martaba yayi na aurar da Fulani Aminatu ga masarautan da kullum cikin shirin mutuwa yayi ya kyauta (shi fa Mahassadi kullum haka yake da zaran yaga can bai ci ba toh gaba zai ci kamar ba anan ake son sanin ina ne za a aurar da ita ba yau kuma ana ganin adalcin Mai Martaba)
_____________________________
*Hey gashi nan babu yawa. Amma da za a kara comments da Voting maybe na kara wani abu wannan labarin ba zance zai kai kwarkwarah ba amma ba mamaki suyi kunnen doki please share it*
#Mai_Dambu
[3/28, 11:48 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: ƘALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
Na
Mai_Dambu
https://www.wattpad.com/1202777502?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=%2FTkRLP2mVOiOibQOmSAZomlKU5lZCJrKgGsadyz5zbb1oHJQIrUZmlujwcmwOYjvR2oNox9TifPEUZMrn51misnMzQo8zFd8GVZXdYgFwL3EV0XzHOhA8qWeZfnQs9hF
**
EWF
```Wannan shafin gaisuwarki ce Mammyn Afreen ki more pagen da gasken gaske... Ina son COMMENTS ɗinki na musamman ne🔥😍 Nagode```
_Mai yiwuwar tafiya ce mikakkiya! Domin duk zaren azabarin da zaka kulla sai ka samu yana sarkaffe da al'amurra mabanbantan ra'ayi! Mai yiwuwa kuma gajeruwar tafiya ce me kunshe da kaddararren al'amari! Ban sani ba amma matukar alkalami na Ya bani dama ba mamaki muyi fidda asalin kalmar kamar yadda muka saba cin karo da kowacce tafiya Nagode Mabiya ƘALLABI A TSAKANIN RAWUNA...🔥Son so daga Mai Daraja😍_
A hankali labarin Auren Fulani Aminatu ya zama mafi girman labarin da ta wanzu cikin masarautan da kewayar ta, ya kasance ko Innayo ce ta gfta gulmarta ake da ya feccenta. Kasancewar Innayoh ba karamar mace bace domin akalla tana shirin dosar shekaru Talatin. Amma a kasancewar ta baiwa mafi kusanci ga Fulani Aminatu dayawan mutane suke kiranta da Jakadiyar alkhairi. Musamman ma bayi yan uwan ta, domin ta kai kololuwar sanin Darajar kanta da kimarta.
Mace ce da ta fahimci abinda take, kuma su din can bayi ne na amana, wanda tarihi ya nuna tun da aka kafa masarautan zuri'arta take cikin masarautan kuma suke aikin Bauta, gashi ana hasashen Mai Martaba Sarkin Gombe zai barta da Fulani Aminatu. Kasancewar kamar Uwa ce a wurin Aminatu.
Tana zaune Jakadiya Bimbi tazo cikin tsananin son jin wani abu daga Innayoh ta ce mata.
"Jakadiyar alkhairi, wai da gaske uwar dakin ki. Sarkin Gobir zaa aura mata?"
Murmushi tayi sannan ta mike, bayan ta tattara zaren da take yin adon fure a jikin farin mayafin siliki, wata yadi ce da ake zuba da shi daga nahiyar gabas. Mai tsantsi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 39