Share this page
su yana da damar sarrafa na dan uwan shi. Sai da suka gama wanka yayi Sallah, a bakin rafin, sannan ya juyo ya dawo gidan, uwar tsoro tana kan gadon zaune, "Don Allah kayi hakuri na kai ka inda zaka kwana ina jin tsoro ne" Rike kugun shi yayi yana kallon ta, kafin ya kwashi kayan shi, ya kalle ta sannan ya fita babu musu ta tashi tare da saka shi a gaba suna nufi gidan su baffa'm. A hankali ta shiga tana sallama. "Anum lafiya?" "Bakon nan ne" ta fada Muryan ta yana rawa, "Wani bako?" "Wanda" "Ku shigo" Galadima ya fada, ba musu ta shiga. Baffa'm yana can cikin dakin yaji Muryan Anum bai kawo kome ba, dan haka ya fito, kallon Galadima yayi da ya rikice. "Lafiya?" "Aminatu!" Kallon Gidado yayi, da yake bin ko ina da Idanun shi. *Ka zuba ido zan dawo kuma sai ka ga abinda zai hana ka gani* Luuuuuu ya tafi zai zube a kasa, Galadima ya riko shi, Suka kwantar ta shi, shima kura mishi Idanu yayi yana musu magana irin ya kurame. "Anum kawo mana ruwa" da sauri ta mike tare da fita waje ta kawo ruwan, shafa mishi Galadima yayi Sarkin gida na mishi fifita. Bude idanun yayi akan Gidado, fashewa yayi da kuka. Yana girgiza kai. "Ka gaya min Ina Aminatu" a hankali yake juya hannun shi yana musu bayanin,.kuka suke baki dayan su ga samu ga kwanan Yunwa. "Ya koma wurin mahaifiyar shi, ya zauna nayi kasadar rabata da ni ba zan yi kasadar rabata da farin cikin da ta samu ba." Kallon su yayi cikin damuwa ya musu alama da su bashi alkalami,.dauko tawada aka yi aka bashi. A hankali ya fara rubutu. _Suna na Gidado Husaini! Ammyna Aminatu tana nan lafiya ita da Innayoh, Lamido Hassan yana can Kano yaje wani aiki me muhimmanci! Nazo ganin Masarautar mu ne da mafarkin ko wata rana zan amsa sunan d'a ga masarautan_ Dukkan su sai da suka yi kuka, Anum da ta gaji da kukan su, sulallewa tayi ta nufi gida, tana sauke ajiyar zuciya da ta shiga dan akurkurin dakin ta, ta kwanta. Washi gari. Da sassafe Fulani Haima ta dira musu, har dakin Anum ta shiga ko ina na dakin kyal-kyal, Kallon juna suka yi na wasu dakikai, kafin ta cewa Anum. "Idan baki son jin labarin mutuwar gashi ki shirya muje ki ganshi" Kura mata ido tayi kafin ta ce mata. "Waye shi?" "Idan muka je zaki gan shi" sannan ta ajiye mata kayan da ta kawo mata, ta fita bata san waye ba, amma wannan me kama da larabawan ta sata dole ta shirya, ta fito kamar wata gimbiya. A hankali Haima taja hannunta suka nufi keken dokin, irin me budadiyar bisa, suka fara tafiya kowa mamakin yadda haka zai faru ne. "Inono me kuma Yar Salihu tayi, yarinyar nan masifa ce a cikin al'umma" "Can da su gada, idan sun so su kashe ta ma ina ruwa na" -- Hango ta yayi sai yanzu ya kara kaifin basirar sa akan ta, baki ya sake yana kallon ta, ta zama tauraruwa a cikin duniyar shi, da ba so bane tunda har ya zo nan basu hadu da Bintu ba, tabbas a yanzun ne ya ga abinda yake so. Ga shi yau zai bar garin nan. Yana kallon keken dokin har suka bar rugar. A hankali ya shafa kan shi yana murmushin ƙarfin gwiwa da ya samu, idan ya tafi zai mishi bayani idan yazo ya taya shi yakin niman soyayyar shi. Haka Galadima suka raka shi, har ya bar nahiyar domin sarki Bello ya ce a mai da shi, zasu nime shi kuma su tabbatar da ya bar masarautar da iyakar Masarautar yadda babu wanda zai iya cutar da shi, sun tsaya sai da ya bar nahiyar tare da sakon lallai ta turo musu Lamido domin ana bukatar shi. Cikin masarautan suka isa, Haima tana gaba. Anum na baya cikin bayi. Sarki yakubu yana fitowa daga cikin gidan zai nufi fada idanun shi ya sauka akan kyakyawar fuskar ta, wacce ta zame mishi haske a duniyar shi na Malik yauumindi, bai tab'a ganin macen da take da wani sa sassanyar kyau da yanayi kamar ta ba, duk da yarinya ce karama amma kuma ta gigita duniyar shi, kasa tafiya yayi yana bin su da ido.... _Love is beautiful_ Da fatan kun fara fahimtar Sunan labarin... Barkindo, Gidado, Sarki Yakubu, Dukkan su akan Mace daya tal..... Bari mu ga ta inda sunan zai kumq tabbata akan itace ko wata ce.....ayi hakuri da rashin wutar mu😭😿 #Mai_Dambu [6/3, 9:36 PM] Empress Anum: KALLABI..! A Tsakanin Rawuna EWE BABI NA ARBA'IN DA SHIDA BARKA DA WUNIN JUMMA'A 🕌🕋 "Allah ya baka nasara ana kallon ka fa" inji Dan madabin Gobir, cikin wata irin shu'uman murmushi ya yayi gyaran murya. "Tabbas na ga mace a wurin nan" ya fada yana karawa gaba, tabbas bai tab'a ganin macen da tai tafiyar bazata da zuciyar shi ba sai yarinyar nan, dan haka ya kudiri Aniyar idan ya nimo wancan yar baiwar toh ba makawa zai kara da wannan kyakyawar yarinyar domin ta zame mishi wurin hutu na musamman. Har yau da yake jin shi da girma ya hau kan shi bai hana shi raba tsakanin cinyoyin mata ba, ya baje gumin shi a tare da su ba. Tafiya suka yi me nisan gaske, kafin suka isa wani shashi na musamman, sai da Fulani Haima ta juya tana me kallon Anum, kafin ta cewa masu tsaron kofar shi. "Ka cewa Barkindo mun zo da ita" "An gama Ranki shi dade" Da sauri ya juya zuwa ciki, can sai gashi ya fito ya ce a basu hanya, matsawa Haima tayi tana me kallon Anum. "Yana jiranki" Matse hannun ta tayi tana kallon kasa, idanun ta ne ya cika da kwalla. "Toh" ta fada, kafin ta fara tafiya kamar wacce kwai ya fashe mata, a cikin ta. A hankali yanayin wurin ya shiga dawo mata kamar wacce take mafarki, daurewa tayi ta isa har cikin babban zauren shi yana zaune daga shi sai wata farar riga irin na mutanen kasar Larabawa, gashin nan ya kwanta a kirjin shi lum, yar kasumbar da ya tara ya kara kawata fuskar shi wanda ya haifar mishi da kwarjini. Bakin shi wani irin ja yayi me daukar hankali, kamar jariri. Sai idanun shi da suka kasance farare, masu kyau da ɗaukar yanayi na musamman. Fari ne kyakyawar dan hasken fatar mahaifiyar shi ya dauka amma a yanzun da kamanin shi ya ke juyewa ya fara fuskar ta ayar tambaya a wurin mutane, amma kasancewar yana da goyan bayan uwar shi dq waziri yasa babu wanda ya iya tofa albarkacin bakinsu, asalima ai ana samu haka yaro ya dauko kamar wani a cikin dangi (🤣🤌🏽😏😒😂🤣 kuce fit ku ga yadda zamu yi da ku) toh haka ya kasance ga Barkindo, d'ago kai yayi ya kuwa yi dacen itama ta d'ago kai suka kalli cikin idanun juna, a hankali ya mike kamar mara cikakken lafiya ya fara taku a hankali ya isa gabanta, kallon yadda ta sunkuyar da kai tayi, a hankali yake lura da yadda take damke hannun ta. Tattausar hannun shi ya kai kan nata, ya daura saman hannun ta, d'ago kai tayi tana kallon shi. Murmushi yayi yana kallon cikin idanun ta. "Me yasa baki sona?" "Rayuwa ta da taka akwai banbanci!" Yatsar hannun shi ya kai kan bakin ta, yana shafawa. "Idan na gaya miki kece rayuwata zaki yarda?" Ya kuma tambayar ta, "Ba wannan ne ya kawo ni ba, dama kai ne kasa a kawo Ni?" Komawa yayi ya zauna yana kallon yadda take bin shi da ido, "Zo ki ci abin karyawa nasan baki karya ba!" Ya fada yana kallon kayan abincin da yake gaban shi. "Na koshi" "Anum bana son gardama yana fusata ni" ya fada a sanyayye, "Ko baka fusata ba, ai dama ya ci ace ka fusata zan tafi." Ta juya zata bar wurin. "Ai babu me bude miki kofa sai da Izinina dawo ki zauna ki karya." "Malam ba zan karya ba dole ne? Ba zan ci ba nace, nan Maman ka ta sa ku ka min fyade, haka bai isa ba? Sai da ta kuma turo wasu." Juyawa tayi idanun ta sun yi jajjur zuciyarta yana suya ta ce.. "Ba zan tsawaita magana ba, amma ba makawa idan aka kuma maimaita abinda ya faru" juyawa tayi zata yi magana ta ganshi a bayan ta. Kara matsowa yayi ya saka hannun shi ya bude mata kofar, kirjin shi yana gogan bayan ta, har tana jin bugun zuciyar shi. Ƙasa fita yayi jikin ta ya dauki wani irin rawa, a hankali ta juya tana kallon shi, kallon juna suke sosai. Kamar zasu iya daukar abinda yake fita a cikin idanun junan su. Hannun shi duk biyu yana harde kirjin shi. "Ko min kankantar so ki min mana" ya fadi haka yana me sumbatar goshinta, sanyi lebban shi da kamshin turaren shi, suka cika ta Lumshe idanun tayi takai lokaci me dan tsawo kafin ta bude idanu ta. Yatsar shi ya kai kan bakin ta, yana gogawa burin shi bai wuce ya cafke wannan bakin yayi ta taune shi ba, amma ya bawa kan shi hakuri da sannun matankadi yake shiga gora tura kofar yayi, yana kallon yadda kwalla ya cika mata idanu, jam hannun ta yayi suka shiga cikin zauren ya zaunan da ita, sannan ya kwantar da kan shi yayi akan cinyar ta, yana kara sauke ajiyar zuciya, ita kuma ya barta cikin tsannanin damuwa. Aikuwa bata san lokacin da ta daddage ta zuba mishi duka a gadon baya ba, juyawa yayi ya kalle ta. "Ina sonki" ya fada yana kallon yadda ta kuma had'a rai, kwalla yana kokarin sauka daga idanun ta, ture kanshi tayi, da sallama aka shigo zauren. "Allah ya baka nasara Fulani tana isowa" mikewa yayi da sauri ya riko hannunta, ya nufi dakin shi da ita sai da ya kai ta can kuryan dakin shi ya boye ta, sannan ya dawo yana zauren har ta shigo, kallo yadda yake haki yasa ta mishi wani irin kallo. "An ce min baka da lafiya, kuma nazo naga kana gudu?" "Eh ina motsa jiki na ne" "Toh yayi kyau" ta fada tare da juyawa zata fita. "Kana da bukatar wani abu ne?" "A'a" ya fada yana me zama kamar bai damu da kome ba, har zata fita ta kuma cewa. "Sai naga kamar Barkindo yana boye wani abu?" "Baki yarda da ni bane?". Ya mai da mata tambayar shi, "Nq yarda da kai mana Ubana" daga hakata bar dakin amma zuciyar ta sam bata yarda da shi ba, kawai abinda tayi shine bayan ta bar harabar gidan sai kuma ta koma, ta same shi, yana zaune a inda ta bar shi, yana nan zaune. "Har yanzun baka ta shi ba?" "Fulani ki shiga ciki ki duba, tunda baki yarda da ni ba.." "A'a wallahi na yarda kawai kayi hakuri." Aikuwa tana gama fadar haka ta bar zauren zuwa dakin tana zaune inda ya bar ta, mikewa tayi ya ce mata. "Ina zaki?" "Inda na fi wayo" "Toh yi hakuri ki zauna domin kuwa Fulani tana zargin ina boye dake!" "Wai na tambaye ka, shin har yau kana shan nono ne ko Ya?" "Ban gane ba?" "Eh zaka gane" ta fada tana ƙoƙarin barin dakin, tare ta yayi yana kallon yadda take huci. Hannun shi ya kai habb'arta ya d'aga kanta. "Anum ki bani aron yau a matsayin soyayyar mu don Allah mu wuni a tare zan mai daki da kaina" "Kai da har yau ba a daina kuka da kai kamar jariri ba kai ne xan karar da ranar yau a tare da kai, ji wani magana kamar ta masu shafar Aljanu bani hanya na wuce ko kafin na sauya ra'ayina na maka mugun rashin mutunci. Duk yadda yayi da ita taki, fir sai kara rikice mishi take, bai san lokacin da ya rungume ya ba, domin gani yake zata iya kwace mishi kowani lokaci. Sanya kanta yayi a kafadar shi yana shafa bayan ta. "Ke ce kaddaran rayuwata,.idan na rasa Ni har a abada ba zan tab'a Moran kaina.ba, don Allah ki tausaya min ina sonko" "Na gaya maka ba zan tab'a son ka ba, mahaifiyar ka ta ruguza duk wani yardan da na.maka, ban san cewa akwai ranar da zata iya hada kai da wasu ya cutar dani ba, .. *Na fita unguwa na gaji wallahi barci naje ji gashi kamar yadda Mom Ases ta roka na baku ko ba yawa ne gashi nan.ba yawan gaskiya* #Mai_Dambu [6/5, 9:52 AM] Empress Anum: BABI NA ARBA'IN DA BAKWAI Haɗe hannun shi yayi yana kallon ta, cikin murmushi ya saka hannun shi a habb'ata shi yana kallon ta, jan yaji yayi kamar wanda ya ci wani abu me yaji wannan ya fesar da iskar bakin shi yana kallon ta tare da murmusa mata, ya ce mata. "Yar kwaila kika ce me?" Wani irin kululun bakin ciki ne ya tsaya a wuyar ta, ta zabga mishi harara. Mikewa yayi, bai kula ta ba ya nufi can dakin shi, "Lusari kawai" ta fada tana Murguda bakin ta. "Sai kace namijin gaske" Cak ya tsaya murmushi yayi tare da nufar cikin dakin yayi abinda zai yi sannan ya fito, kallon ba zaka ce ya ji zafin Abinda ta gaya mishi ba, dan mutum ne da yake son ta kuma baya jin zata tab'a gaya mishi abinda zai saka shi ya fusata, a hankali ya fara kokarin cire rigar shi ya fara, yana takawa wurin ta, tsoro da fargaba ya sa ta yin baya, jikin ta ya dauki wani irin rawa. "Bana son haka." Murmushin ƙarfin hali yayi yana girgiza kan shi. "Me yasa kike tsorona Jarumar mata?" Wata uwar harara ta wurga mishi tana, cewa. "Ni bana son Iskanci." Ta fada tana zare ido, dariya ya sake me sanyi yana kallon ta. Har suka dangana da bango ya kai hannun shi bangon da sauri ta juya tana kallon hannun kafin ta juya suna fuskarta juna. "Rigana da na nemi cirewa, kika tsoro ta idan kuma na kwabe gaba da fa" "Subhanallahi" ta fada tana me rufe fuskartar, kan shi ya kai wuyar ta yana faɗin. "Ba zan tab'a ci daga haram ba, ina son abu toh ina ji a raina na mallaki abun naci na koshi ba Naci da karfi ba, sake ranki yar Kwaila ta." Ya fada yana me juyawa kamar bashi ya bata tsoro ba." Ajiyar zuciya ta sauke tana hararan shi, a ranta tana fadi.. "Dan renin hankali" Juyawa yayi yana murmushi ya ce mata. "Ke kin ga gobe na kashe bakin kirana lusari" Wani uban gatsine ta mishi, bai san lokacin da ya fashe da dariya ba, sabida gatsinen har hancinta sai da ya koma wani dan karami. Dama gata nan yar mitsitsiya, kawai damuwa ce irin ta Barkindo domin ko kirjin ta babu wani cikar tashin hankali, sai dai tana cikin shekarun balagarta ce, matuƙar ta samu kulawar namiji toh idan ta tashi habbaka na fitar hankali zata yi. Haka zaman su yayi ta tafiya idan ta mishi tsaurin ido, ya mike tare da nufarta. Take zata karyar da kai tana bashi hakuri, baki daya saka mata wani irin shakkar shi yayi, amma bai mata kome ba, sai dai tana fara mishi tsiya zai taso. Sallah kawai yake d'aga shi a wurin ta. * Fada Hankalin shi yana wurin yarinya da ya gani, dan haka bai san me suke fada ba, suna mishi bayani akan abubuwan da ya faru ne, nan a mafarkin shi hango yadda yake juyata yana hutawa da ita, shi a duniyar shi akwai abinda yake hana shi d'aga buje ne, ai ko bai d'aga na matan shi ba, ya d'aga na kwarkwarah, kuma ba laifi yana samun yadda yake so har yayi ya kara, "Allah ya baka nasara an samu matsala wanda yayi harbin ba a same shi ba, kuma wanda ya tsira daga harin ya ce ba zai gane shi ba" "Toh a rufe binciken daga baya a buɗe! Ina son gobe a fito min da jerin sunayen" shiru yayi yana nazarin abinda zai fada, so yake ya ce a fitar mishi da jerin yan matan bayin da suke cikin masarautar amma da ya tuna cewa za a iya samun matsala tuni ya fuskar kamar ba shi ya fara kokarin danne kwadayin shi. Allah ya gani ya kwadaita da K'ugunta, domin shi kawai idan mutum ya gani duniya ce, tana juya shi kamar ba a jikin ta ba. Lashe baki yayi yana jin Basarakiya me tagwayen yara tana juyawa, jinjina kai yayi sannan ya ce musu. "Ina son gobe na huta" Duk lokacin da ya ce yana son gobe ya huta toh sunan san ranar matan shi da kwarkwarori basu da hutu, sun rasa wacce irin halittace da shi da idan ya saka mace a gaba a daki yana gurgura sai a hankali, shi yasa matan da suke kewaye da shi suke Hauka kamar me. * Kano ta dabo tumbin giwa ko da me kazo an fika, sai dai wannan kirarin na kanawa bai hana su gane gaba da gaban ta ba, domin kuwa lokacin da Lamido ya isa masarautan ya samu tarba na musamman, domin sai da yayi kwana biyu me kyau kafin ya samu ganawa da Sarkin Kano da kuma Sarkin yakin Kano. Cikin girmamawa ya zauna yana me sauraron su. Sarkin yaki ne ya yanke shirun. Da cewa. "Yarima Hassan, ga tsarin yadda yakin xai kama, sai dai maguzawan suna da horon yaki da kibau, sannan suna iya mana kofar rago" "Nawa adadin matakan mu?" Lamido ya tambaye shi,mai Martaba yana jin su, "Dubu daya ne" Shiru yayi yana kallon kasa kafin ya matse yatsar hannun shi tayi kara, ya ce musu. "A kasasu gida hudu, kaso na farko su kasance masu garkuwa, kaso na biyu masu Mashi, saboda kason farko zasu kare su, masu dawakan maguzawa zasu kawo musu hari, kazo na uku sune masu kibbau, idan suka jifo nasu aka mana garkuwa, toh kafin su sake shiru kazo na uku sun mai da musu, kazo na hudu mune da dawa kai sannan agana mu akwai hamsin masu ɗauke da garkuwar yaki. Sannan duk wani jarumi da aka san bai da wasa a bashi damar jagorantar runduna, idan muka samu aka musu shigar farko, toh daga nan runduna zata fashe kowa ya kama gaban shi, sai mu tafi kamar mun sare, amma zaku dawo mu kara musu kawanya. Wannan shine shirin idan akwai gyara a min magana sai da safe" Ya bar su zaune cike da mamaki. "Adamu kasan yaron nan jinin shi a ta fashe yake? " Mai Martaba ya fadawa sarkin yaki, murmushi yayi sannan ya kalli sarkin yaki ya ce mishi. "Lokacin da Bello yazo da Uwar yaron nan fa tana karama, har nake mishi shu'umanci cewa yana d'aga mata kafa, kaga yaro Allah ya fitar da shi cikin mutane masu hakuri da son zaman lafiya!" "Allah ya baka nasara ai bagobiri ne, dole jini ya tabbata akan shi ko ba dan kome ba, kodan zargin yaran da ake ba halattatun yaran Sarki Bello bane." "Na yarda kan yanzu jinin Bello ne, waye zai ki kyakyawar hadi haka?" "Gaskiya Allah ya baka nasara babu wannan ai sa'a ne samun shi, tun bai sama sarkin ba kome na shi a sama da umarni ne,.tun bai shiga cikin jinin shi ba yasan yadda ake yaki da kasafin yaki, idan kuma ya zama sarkin ya zama dole daular ya girgiza sansanin mayakan shi, sannan a yadda ya kasa mana kome bana jin zan iya rage kome ko kara kome domin duk abinda yayi haka shine dai-dai, duk me hankali ya ga wannan al'amarin zai gane jagoran mayakan ba karamin mutum bane" "A cigaba da shirin farmaki kawai amma kome ya tafi yadda ya tsara." "Insha Allah haka za ayi." Koda sarkin yaki ya bar zauren mai martaba ya shiga cikin gidan shi, ya wuce dakin uwargidan shi, Fulani Zainabu, bayan ya zauna ta tashi zaune tana mishi barka da shigowa. "Fulani nazo ne akan maganar Hadizah akwai ɗan Sarkin Gobir da suka zo niman aurenta, amma yana zaune ne a masarautan Borno. Nazo ne a matsayin wanda ya ke niman abu, ba a matsayin uba ba." Shiru zauren yayi sannan ta ce mishi. "Ban gane wani sarki ba, ai sarkin su na yanzun bai da d'a sannan Dan kwarkwarah kuma gaskiya a duba abin da dai dan Bello da Fulani Aminatu ne zan bashi domin samun kyakyawar nasaba da kuma mutanen kirki da zasu rike maka dan ka shine babban nasarar mu" "Dan Bello ne da Aminatu, Yarima Hassan su yan biyu ne Hassan da Hussaini,, Hussaini kurma ne Hassan suke fatan a bashi mulkin domin." "Toh me zai hana, ai Bello da Aminatu mutane ne ko da basu Haifa ba matukar suka ce a bada za a bada" "Kenan Fulani Abu ta bada umarnin a bada yarta kenan?" Lumshe idanun tayi sannan ta sake murmushi. "Duk yadda ka ce" Da wannan suka tsayar da magana sannan, ya fita. Washi gari, Sarkin yaki ya gabatar da Lamido, dayawa dakarun basu yi na'am da shi ba, sai da ya fara musu bayanin yadda yakin zai tafi sai a lokacin ne suka fara jin qarfin gwiwa da lallai sun samu shugaba. Dan haka cikin kwanaki biyar, aka shirya yaki tare da hada kome. Sai muce Allah ya bada sa'a. * M.Gobir Yamma likis ya sakota a gaba, har harabar masarautan, ya shiga keken dokin,.sannan ya mika mata hannu wani matsiyacin tsaki ta ja, sannan ta shiga tana hararan hannun shi, damke hannun yayi yana kallon ta. "Yayi kyau tunda kin kasa gane son da nake miki". "Allah ya min tsari soyayya da lu..." Kur yayiwa dan matsitsin bakinta, jan yaji yayi kamar yaci barkono nace mata. "Haka ma yayi, Anum idan kika kuma kirana lusari sai na cinye bakin ki..." Ai batasan lokacin da ta rufe bakin ba, tana zare idanu, ina zata iya wannan haukar salon a ji labarin abin ya dame mata abin kunya a duniyar ta, dan haka ya matse bakin ta har suka bar masarautan. Ya kuma jan yaji ya ce mata. "Zan so na sumbaci bakin yadda gobe sai kin gane ni ba Lusari ba, ji bani damar haka" Kara rufe bakinta tayi, fir taki magana, a ranta kuwa ta zage shi ya kai sau goma, har suka isa garin su.. Fitowa ta fara kokarin yi, ya riko hannunta. "Ina sonki da dukkan fitar numfashina, kiyi hakuri ba zan taba Miki abinda baki so ba, sai da yardan ki, amma ki bar ni na sumbaci Goshin ki" a hankali ya janyo kanta ya sumbaci goshinta. "Nagode sosai da damar da kika bani, ina fatan nan gaba ki bani wani damar haka, ina son ki" ya fada bayan ya sake fuskar ta, wani irin sanyi jikin ta yayi ta fita daga cikin keken dokin tana kallon kasa, idanun ta yana cika da kwalla. Har yanzun tana jin sanyin lebban shi a saman goshinta, a hankali ta juya tana kallon shi, murmushi yayi mata, cikin wani kalar marairaice Fuska da ya kara mishi wani kafirin kyau, wani kolelen bakin ciki ne ya turnike ta, ta Murguda mishi baki ta arta a guje. Shi kuma ya fashe da dariya. * Tafiyar kwana ki biyu ya iso da shi gida, lokacin da ya shiga kallon Ammyn yayi cikin Tausayin iyayen shi. Yasan matukar ya sanar mata daga inda ya fito sai ta tsintsinka mishi mari, zai bari sai lamido ya dawo kawai ya gaya mishi. Amma maganar gaskiya, wancan yarinyar ta daki zuciyar shi bai san lokacin da haka ya faru ba, shi daya sai murmushi yake zabgawa, idan ya tuna yadda take mishi kallon tsoro, ga idanun ta da basu rabuwa da kwalla alamar idanun haka suke da maikon ruwa, haka Allah ya yi su,.masu ruwa ne haka kawai yaji duk inda yarinyar nan take tana da wani yanayi da su, domin ba iya soyayyar ta yake ji ba, akwai wani abu me girma da yake ji a kanta.... 😂 *Wai amarci nake ji kai mutanen nan da ban dariya kuke, ana bikin kanina ne,shi yasa na bata a rubibi. Ayi hakuri* [6/6, 5:28 PM] Empress Anum: KALLABI...! A Tsakanin Rawuna EWF BABI NA ARBA'IN DA TAKWAS Tun bayan dawowar shi, baki daya ya kasa sukuni, asalima ko wurin Bintu baya zuwa, idan kuma tazo yayi ta kau-kauce mata kenan, tun bata gane ba, har ta fara kokarin fahimta sauyi daga gare shi, amma dake ko ta ritsa ba gaya mata gaskiya zai yi ba, yasa ta zuba mishi ido, amma maganar gaskiya tana cutuwa, shi kuma dake hankalin shi yayi nisa a wurin Anum, idan ya zauna bai da aiki sai na rubutun yanayin ta, Yana zaune a bakin kofa, Bintu da Innayoh suna zauren. "Innayoh ya sauya dayawa." "Karki damu ba mamaki ko dan tafiyar da yayi ne" tashi tayi ta dawo bakin kofar tana kallon shi, sai yayi murmushi can kuma

Chapter 24 of 39