mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
_______________________
"Idan ka gama mafarkin ka na kullum sai kayi magana akwai wata bazawara a gefen mu ta yamma sai a mata magana ko" girgiza kai yayi domin ba sabon abu bane mafarkin shi, amma kuma yana da kyau ya bawa zuciyar shi hutu. Domin idan ya cigaba da haka zai samu matsala.
--
Sai da suka yi tafiya me nisa, kafin Sarkin gida ya ce mishi.
"Akwai rudaden mafarki mara tabbas, akwai boyayyen al'amari mara iyaka, akwai damar da zaka bincika me yasa ake bibiyar? Dama ne gare ka, na zama namiji ko kuma ka tabbatar a lusari har abada"
Kallon fuskar Sarkin gida yayi ran shi ya b'aci, amma kuma sai ya dauke kai kamar bai ji zafin maganar ba, asalima kamar bai damu ba, ya ce mishi.
"Zaka iya juyawa. Ka gayawa Baffa'm Nagode"
Ya kada dokin shi ya shige masarautan da gudu, murmushi sarkin gida yayi yana kara ji a ran shi Tabbas tarkon su ya kama kurciya.
**
Kano
Hannun shi a goye a bayan shi, Fulani Zainabu itama tana zaune a gefe sai Fulani Dijah da take ta dirzan kuka, kamar ranta zai fita.
"Ni kika watsawa kasa a idanu? Saboda wani sakarai can da na bashi kudi ya manta dake? Ni kika wulakanta kika wurge ni da takalmi a saman fuskanta? Na zata ko kare na kawo nace a zarga mishi igiyar ya zame miki ado dawa zaki Amince da shi ashe bakin ba haka ne, hasashena ne, lallai na yarda ka haifi mutum baka haifi halin shi ba, Abuh fita da ita bana son ganin fuskar ta."
"Abba kayi hakuri ba zan kuma, na shirya maka biyayya shima zan mishi biyayya"
Girgiza kai yayi yana faɗin.
"Ba zan kuma wannan kasadar ba, kije Allah ya miki albarka ba zan tab'a tirsassaki bin umarni na ba" sake rushewa tayi tana kuka, tana bashi hakuri amma fir yaki sauraron ta sai ma bata mishi rai da take yi.
Babban tashin hankali shi guda daya ne bai san me Lamido zai gayawa Sarkin Borno ba.
Hankalin shi yayi mugun tashi, hmm bai san waye lamido ba, shi mutum ne da magana bata dame shi ba, balle har ya kai gaba, kuma matuka gaya ran Sarkin Kano ya b'aci dan haka ya zauna shi da wazarin shi, suka tattauna akan batun tare da alkawarin zasu tura dan sako ya tafi har can ya basu hakuri domin kuwa babu dad'i abinda Yar su tayi.
*
Tafiyar kwanaki biyu, yayi bai tsaya ba dan ran shi yayi mugun ɓaci sallah kawai yake tsayar da sho, sai da yaga ciwon shi yana zubda jini ne yasa shi yada zango, sannan ya gyara ko ina ya kafa tantin. Sanan yayo itacce, ya hura sallah kawai yake yi ya dawo ya zauna, dare na fara rabawa ya koma tanti shi ya kwanta.
Bai jima ba Biyuna ya shigo cikin tantin ya kwanta a gefen shi, suka shiga barci. Domin ya gaji sosai dan haka ba tare da wani dogon abu ba, barci yayi gaba da shi.
**
Tafiya yake bai san inda yake jefa kafar shi ba, kawai yana tafiyar ne amma zuciyar shi a cunkushe yake, daga dan nesa ya hango wata mace zaune a kasar bishiya, tana mika mishi hannu,
Kafin ya isa gare ta, wasu abubuwan da ba zai ce gadu ba. Sun dabaibaye ta kafin jini ya wanke ta tun daga sama har kasa, gefen ta gawarwakin mutane ne.
Yunkurin isa yake son yi wurin ta, aka rike hannun shi.
"Ba zan tab'a barin kai ma kayi wanka da jini ba kamar ita." Juyawar da zai yi kenan ya farka, gaban shi har wani irin duka yake, bai tab'a fuskantar mafarki irin haka ba, tashi yayi ya fito waje yayi alola ya koma dakin ya tadda sallah.
Bayan ya idar ya jima yana addu'oi, sanann ya koma ya kwanta, kamar jira ake ya kwanta, ya fara wani mafarkin mace ce dauke da jini yana zuba daga jikinta.
Mika mishi hannu take, nan ma sake riƙe shi aka yi, a hankali garin ya hada jan haɗari me saukar da ruwan jini, duk da haka s
Jan hannun shi aka yi har kasar wata rumfa.
"Ba zan tab'a barin kayi wanka da jinin kowa ba. Kalli can suna yi ne, domin muradin su. Ba zaka yi wanka da jinin su ba."
Bude baki yayi zai magana ya kuma bude idanun shi, tashi yayi zaune babu shiri ya fara had'a kayan shi. Ya hau dokin shi ya nausa hanyar gida.
**
Har dare ya raba Baffa'm yana zuwa ya duba Anum, daga karshe suka bude hira.
"Yarinyar nan zata iya rayuwa a cikin gidan sarautar nan, amma matsalar tafi Aminatu tashin hankali!" Inji Sarkin gida.
Tattara nutsuwar su, suka yi suna kallon shi. Tare da jiran karin bayani.
Shima zama ya gyara sannan ya fara musu bayanin yadda ya samu labarin ta.
"Kasancewar mahaifiyar ta, tana da yanayi irin na Fulani Aminatu, amma su a kauyen nan kiranta suke mayya, karshe ganin zasu hallaka ta, sakamakon ganin da Bingel ta mata aka nime ta aka rasa.
Yarinyar ta taso cikin kunci da damuwa, yanzu haka aikin ta kawai shine ta musu kiwo su bata abinci. A duk lokacin da ranta ya ɓaci kudar zuma ne yake bayyana ya cutar da mutane. Na samu labarin ta shiga masarautar sau biyu kuma na farko anyi yunkurin dauke ta, na biyu kuma ta fito lafiya amma duk wanda yake tare da ita Inma a kashe shi ko kuma yayi wanka da.."
"Na jima da sanin haka, abubuwa masu tashin hankali yana zagaye da ita, ba ita take gayyato su gare ta ba, nasabar ta ke gayyatar duk wani me koshin lafiya. shi yasa nake ga matukar aka yi da ce daya cikin Yarimomina yace yana so ba zamu yi saki nadafe ba, zamu aura mishi. Domin jiya na samu labarin haka ta hanyar sakon da na turawa malam ya ce min kar mu sake ta amshi tayin Yarimar masarautar domin wanka zai yi da ruwan jini"
Baki daya kan Baffa'm ya daure ya rasa ta ina zai fara, shin matsalar Aminatu shi ya magance shi, matsalar Anum gidado da Yazid ba zasu iya magance shi ba, yana son yaga Lamido yaga shi kuma wacce irin ƙaddara ce da shi. Galadima ne ya katse shi.
"Ko za'a hada ta da Gidado ne?"
Gaban baffa'm Yankewa yayi ya fadi ya juya yana kallon kofar dakin.
"A'a mu jira dai muji dame zai dawo idan ya dawo da ita a ran shi ni da kaina zan nima mishi auren ta, idan kuma baya yi ba zan mishi dole ba, domin zai iya cutar da ita, ni kuma Aminatu ce rayuwata, idan na yi hka ban yiwa zuciyar ta adalci ba, mu saurari zuwan Lamido kamar yadda dan uwan haihuwar shi ya fada."
"Toh shi kenan Allah ya tabbatar mana da alkhairi." Galadima ta fada.
"Amin Ya Allah" inji Sarkin gida.
Washi gari. Ta farka a gajiye, kurawa dakin ido tayi sannan ta fito tayi alola kana ta koma dakin tayi Sallah, da rigar Barkindo, tana idarwa ta harari rigar, kafin ta cilla shi can.
"Sakarai"
"Anum kin tashi"
"Eh Baffa'm na tashi bari na zo"
A hankali ta fito ta same su zaune, mika mata madara Baffa'm yayi ta kai hannu zata amsa, kamar wacce ta ga giftawa abu, ta tafi baki daya zata zube. Riko ta yayi yana cewa.
"Subhanallahi!"
Tasowa suka yi, suna kamata tare da kwantar da ita. Hancinta ne ya fara zubda da jini sosai.
"Anum!"
Cikin wani irin zafin nama ta kai hannun ya wuyar baffa'm ta shake shi.
"Sarki Bello! Ashe kana raye? Barka da zuwa kasuwar ƙaddara. Kayi kokarin niman dalilai uku! Me yasa aka kashe Ibrahim, me yasa aka kashe sankira me yasa aka kashe Jakadiya, me yasa aka kashe Sanda. Idan kayi haka ba zaka yi danasani ba, amma ina mika maka ta'aziyar rashin da za yi akai-akai domin zaka yi kuka zaka kayi ya jin tsanar kan ka na Barka lafiya ka kula da ita. Ana iya addu'a ƙaddara tana sauyiwa, ka gwada hakan zaka fahimci abinda nake nufi"
A hankali jinin da yakd zuba a hancin ta, ya tsaya cak gyara mata kwanciya suka yi suna kallon juna, wani irin Tausayin Baffa'm ne ya kama su, domin tun yanzu an mishi ta'aziya ina kuma lokacin yayi, su waye zasu mutu? Zama yayi kamar yayi ta kurma ihu, ya rasa gane Meye ake nufi da abinda aka fara mishi. Dafa shi Galadima yayi sannan ya ce mishi.
"Karka damu wani lokaci Aljanu basu da gaskiya, dan haka ka daina saka kan ka a damu"
Zare hannun shi yayi a kan fuskar shi.
"Ban san ta ina zan fara ba, kuma ban san waye zai zama farko ba, Allah karka nuna min wannan lokacin"
**
Tun jiya da ya shigo gidan ta saka aka hana shi fita, musamman da aka kai mata rahoton cewa an dake shi.
Fitowa yayi zai wuce ta ce mishi.
"Ina zaka? Mandiya bata gaya maka cewa ina niman ka ba?"
"Innah ta gaya min"ya zauna yana kallon ta.
"Inna kina son Baffa'm?" Tambayar yazo mata bazata, dan haka ta dube shi kafin ta shashantar da shi.
"Kana kula da lafiyar ka, idan ka cigaba da fita zasu cutar da kai"
"Tambayar ki nayi,Kina son Baffa'm?" Yadda yayi maganar da dakakiyar murya yasa ta juyawa tana kallon shi.
"Waye ba zai zo Baffa'm ba? Ina son shi mana?"
"Ban ga alamar haka ba, idan har kina son shi ba zaki tab'a mantawa da shi ba da har sai an tuna miki shi ba. Anya Innah baki da masaniyar abinda yake faruwa?"
A matukar raxane ta kalle shi kafin ta ajiye kofin hannunta.
"Kasha wani abu ne?"
Kikewa yayi tare da kallon ta.
"Gaskiya nake son sani, idan har mace zata manta da mijin da ya yantatta, ta bude shafin rayuwa cikin farin cikin da annashuwa Meye sunan ta? Idan har mace zata rungume mulki ta ma manta da mijin auren ta Meye sunan ta? Innah da kina son shi ba zaki tab,'a mantawa da shi ba. Inna mutumin da kika yi gudun ƙaddara domin shi amma kika manta da shi!
Ikon Allah gaskiya kin bani tsoro wallahi dan haka ki goge suna...."
Tasss ta wanke shi da mari, wanda ya sashi kusan faduwa, yana rike da kuncin shi.
"Karka sake raina ya ɓaci domin sai na saka an maka abinda baka zata ba!"
"Me zaki min? Me zaki aikata wanda baki aikata ba? Wacce irin adalci ne baki aikata ba? Na zata zan yi alfahari da kasancewa dan Sarki Bello sai gashi ina jin tun ba ajiye ko ina ba na fara danasanin haihuwa ta sa kika yi,me yasa baki yi barina ba? Me yasa baki haife Ni a gawa ba? Shi halicci jini ce haihuwar mutum ake da shi, dan halal shi kadai ya san halicce, ki fara shirin fuskar..."
Sake kifa mishi mari tayi ta tare s cewa.
"Dakaru! Ku kai shi gidan horo a hora min shi nan da kwana uku"
"Ai na zata kashe Ni zaki saka a yi, na rantse da Allah idan na fito ba zan taba raga miki ba, sai kin gaya min me yasa ake bibiyar rayuwata? Sai kin gaya min me yasa ake son kashe ni? Sai kin gaya min me yasa na kasancewa Lusari idan ba haka ba, abinda zan aikata gaba ba zai mana kyau na. Kin zalunci ruhina
*Insha Allah on 25 this month zan fara posting din ZAYN MALIK a Arewabooks! Wattpad da Whatsp kuma ranar 1/7/ Insha Allah domin tafiyar tare zaku iya sauke baku manhajar nagode sosai ₦300 ne a grp ga masu son private zasu iya min magana*
"Ku fitar min da shi! Bana son ganin shi matukar na ci-gaba da ganin shi sai na sare kan shi bana son ganin lusarin D'a irin mara amfani" ta fada da ƙarfi.
"Dole ai! Dole ki ce baki sona, dole Kice haka,bayan naga kome da idona tundaga ranar da na ga abinda muka shirya ga Mahaifiyar Anum ba gane zaki iya kome sannan itama Anum baki kyale ta ba,me ta Miki?" Ya fada da ƙarfi lokacin da ake kokarin fita da shi.
"Idan ita ce ki bar wahalar da kanki domin Allah yana tare da ita, ni da kike so gashi ko kare kaina ba zan iya ba.."
Haka yayi ta mata bankada a gaban jama'a, sam wasu maganar shi bata basu muhimmanci ba,tasan dai ta tsani Anum amma ai bata kuma turawa a mata kome ba waye yake bibiyar gudan jinin ta?...
_INSHA ALLAH zuwa dare zaku samu kari_
**Insha Allah on 25 this month zan fara posting din ZAYN MALIK a Arewabooks! Wattpad da Whatsp kuma ranar 1/7/ Insha Allah domin tafiyar tare zaku iya sauke baku manhajar nagode sosai ₦300 ne a grp ga masu son private zasu iya min magana*
#Mai_Dambu
[6/8, 8:21 PM] Black Girl: KALLABI..!
A Tsakanin Rawuna
*EWF*
https://www.wattpad.com/1233953200?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=x%2B7khMrhY1CJjNb7qVDRqxqk9PEQdpl3ou5lB8YYW9p4Vg4QXAy32eH2HxnsEOaeGSIC7O%2BbBTdQQkW5BtSKwp22e%2FfYwKNNHow3vu%2FNnigQx6Psqd1%2FQKcktMK4ZKME
BABI NA HAMSIN DA DAYA
_________________________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
____________________________________
Rufe bakin ta, tayi tana jin wani irin faduwar gaba ba dai ana niman son ganin ganin bayan su bane? Ita da Barkindo?
A rikice da alamun tashin hankali ta dakawa masu tsaron kofar tsawa ta ce musu.
"Maza ku dawo min da shi"
"Toh" suka juya da sauri aka tafi har an kusan shiga dashi aka musu magana.
A fusace ya kwace hannun shi daga nasu, ya saka kai ya nufi wurin da ake ajiye dawakai ya dauki daya, ya dauki guda daya ana tare tare ta finciki dokin suka bar masarautan. Tafiya yake amma hankalin shi ba a kwance ba, dan haka yana cikin tafiya yaga ana bin shi. A matukar firgice ya karawa dokin gudu, sai da suka yi ta wasan tsare sosai, kafin ya samu damar isa hanyar da zata kai shi gidan Baffa'm. Harbin dokin shi suka yi,ya tintsira can gefe guda, akan dokin. Da sauri ya mike zai gudu suka mishi kawanya.
Kad'awa bishiyar da suke kasar ta ya fara,
D'ago kai suka yi suna kallon saman, wani mutum ne zaune akan bishiyar, hannun shi dauke da takobi tsiraran, dirkowa yayi akan bishiyar yana kallon su,.a hankali ya ja Barkindo wanda ya gama razana, ya tura shi gaban su.
Warware mayafin fuskar shi yayi,.sannan da gudu suka sauko daga kan dokin suna masu zubewa a kasa mai da mayafin yayi ya rufe fuskar shi, juyawa yayi ga Barkindo yana kallon shi, cikin tsannanin so da kauna, yana ganin yadda jikin shi yake rawa ya ce mishi.
"Ka koma gida, ku bashi doki kuma ku tabbatar kun same ni an jima"
"Toh" sai da ya hau dokin ya juya ya kalli mutumin wanda a karon farko yaji mutumin ya kwanta mishi a rai, amma tsoron su yasa ya kasa bayyana haka a ran shi. Shima juyawa yayi ya keta dajin da matsanancin gudu wanda shekarun shi sun boye yanayin shi.
*
Cikin farin ciki da annashuwa Innayoh take mishi hidima, turo Yarima Bana aka yi ya kira shi, bayan sun gaisa da shi yake gaya masa sakon mai Martaba.
"Ina zuwa" ya fada mishi, sannan ya cigaba da sauraron Gidado.
"Ina gaya maka ita din zinari ce a cikin tagula,ban tab'a ganin"
Ya fada yana mishi alama da hannun, bayani yake mishi ya dai fahimci duk akan mace yake bayanin shi amma bai kawo rashin akwai wacce zata fi Fulani Binta ba. A hankali ya saka hannun shi a hannun shi ya ciri wani jakar fata ya mika mishi.
"Ka bawa Ammyn inji Mijin ta har yau bai dai na kewanta ba, ina tsoron kar na kai mata ta ji haushina ne, ita yarinyar tana nan a tsakanin su. Idan kayi dacen samun ta ke isar da sakona! Kai nasan halin ka bai zama dole ka isar min da sakona ba. Amma zan zo don Allah"
Ya marairaice fuska.
Tsame hannun shi yayi daga cikin abincin ya kura mishi ido.
"Kana nufin ka tafi Gobir kenan" gyada mishi kai yayi. Yana kallon shi,.kafin ya kuma.bude mishi hannu yana mishi bayanin.
*Allah ya baka lafiya kayi magana kamar yadda kowa yake magana*
Inji Lamido yana kallon dan uwan shi, riko hannun shi yana faɗin.
"Insha Allah sai na taya ka yakin niman soyayyar ta!"
Idanu Gidado ne cike da kwallar farin ciki.
"Da gaske zaka taya ni yakin neman Soyayyar ta?"
Lumshe idanun shi yayi ya bude akan Gidado, kafin ya gyda kan shi.
"Zan taya ka"
Mika mishi hannu yayi tare da cewa.
"Alkawari"
"Nayi maka"
Murmushi suka sakarwa juna, sannan suka mike a tare Gidado ya raka Lamido wurin Mai Martaba,
Yana isa cikin babban zauren suka hadu da Bintu a gaban Mai Martaba.
Kallon Gidado yayi, sam ya sha'afa baki daya da ita, sai lokacin ya kalli Gidado ya tambaye shi da idanun.
"Ita kuma ya zaka yi da ita?"
Shafa kan shi, yayi tare da kanne mishi ido daya.
Zaro idanu Lamido yayi, tare da rufe bakin shi.
"Zaka iya dasu?"
Girgiza kai yayi yana rufe hannun shi, alamar babu soyayya sai zumunci.
Ware idanu Lamido yayi tare da cewa.
"Baka da Kirki"
"Barka dai Hamma Gidado?"
Murmushi yayi yana kallon ta, tausayi take bashi domin shi zuciyar shi bata cikin shi.
Da hannu yayi mata alamar, lafiya lau. Ya gida,
"Hamma Lamido Barka da hanya" dan yake yayi mata tare da wuce ta yana cewa lafiya lau.
Kallon shi tayi yadda yake wani dauke kai, kamar ba shi ba. Nan kuwa yafi kowa shiga tsakanin ta da Gidado.
Haka ta tsaya tana me sunkuyar da kai, alamar jin kunyar Gidado.
Tafa hannun shi yayi, ta d'ago kai tana kallon shi. Nuna mata hanya yayi su fita. Ba musu ta bi bayan shi. Shi kuma Lamido ya zauna a gaban mai Martaba yana gaishe shi.
"Barka da hutawa ranka ya dade!"
Sai da yayi shiru na wani lokaci kafin ya sauke ajiyar zuciya ya amsa mishi.
"Barka dai dai Lamido ya hanya?"
"Alhamdulillahi" can yayi shiru kafin ya ciro wasu fatar jimina ya mikawa Lamido.
"Daga Sarki Muhammad Bello na Gobir ya aiko Hussain da shi, ban san lokacin da ya tafi ba, amma ya bukaci a rike shi kar a kuma barin ya dawo Gobir, kai yake bukata ka tafi gobir!"
Kurawa fatar jiminan ido yayi ya rasa ma me zai ce, kallon rubutun iri daya da na Gidado.
"Baka ce min kome ba"
"Allah ya baka nasara, ni da duk abinda nake da shi ikon ka ne,bani da wani zabi ko ra'ayi sai abinda ka yanke a kaina,duk abinda ka yanke ba zan tab'a kin amincewa ba"
Wannan biyayyar da lamido yake mishi yana kara Mishi kaunar Lamidon yaso da shi Bintu take so da wallahi da kan shi zai bada auren ta, amma kash dayan biyun shi take so, ba zai takura ko ya hanata abinda take so ba, amma yasan hali irin na Lamido mace zata ji dadin ta.
"Allah ya dafa maka! Jeka ka huta zuwa ji bi ka tafi"
Duk da akwai ciwo a jikin shi bai hana amsawa da toh ba, wannan hakurin nashi, tun yana yaro ya taso da shi.
Haka ya mike ya fita yana dafe gefen cikin shi, ya fita yana jin kamar jini yana fita daga wurin, lumshe idanu shi yayi tare da rike wurin.
Har ya fita waje ya same Gidado da Bintu suna zaune, kusan irin hiran kurame da me magana, bai bari sun san yana wurin ba ya wuce su.
Koda ya koma dakin shi kwanciya yayi yana me duba daka matashi a kan shi yana jin yadda ciwon yana mishi zafi ga wani irin ciwon da yake mishi, haka ya mike tare da saka alkyabar shi ya nufi gidan Sarkin yaki, yana shiga gidan ya yanki jiki ya fadi.
"Innalillahi wa'inna illahi raju'un! subhanallahi sannun kaji" sarkin yaki ya kai shi dakin dan shi. A daren aka kira me maganin masarautar da kan shi ya shiga duba shi, ya bashi magani tare da saka mishi maganin da zai janye gubar ciwon da yake damun shin.
Ana cikin saka maganin yayi barci, gashi yana jin barcin amma mafarkin da yake marasa dadi da ma'ana yasa baki daya yaji kamar zai yi Hauka, farka yayi yana jin jiri, saka kwanciya yayi.
Sanye take da farin kaya wanda ya rine da jini, tana tsaye akan kokon kawunan mutane, takawa yayi kai hannu yayi zai rikota. Aka janyo shi fisge hannun shi yayi zai rikota, ya hango tana tunkarar wani irin kujera me zubar da jini, na zuba a cikin kujeran, a hankali ta juya zata zauna ya fisgota tare da rungume ta, a hankali tayi baya da kanta. Jini yana zuba a gashin ta da fuskar ta, so yake ya ga fuskar ta..amma jinin da ya bata mata ya hana shi ganin ta.
Sauko da ita yayi ya juya zai bar wurin Amma Gidado ya mika mishi hannu, kallon ta yake yana kallon gidado da wasu mutane biyu suke kokarin karbar ta.
Mika musu yayi! Ya juya zai bar wurin.
Yaji wata irin k'ara....
_Kash me yiwan na bata muku! Me yiwan na dadda muku! Koma ya ta kasance ba zan yi kasa a gwiwa wurin daidaiton ra'ayin yan amana ba! Sai dai zan yi Fatan ku fahimci yar karamar sakona na gaya muku a baya zan kuma tuna muku a gaba labarin inma ya doke Kwarkwarah itama matar sarki ne Imma ya cimma Kwarkwarah itama matar sarki ce! Koma ya ta kasance ina muku Fatan alkhairi daga me daraja🤌🏽🥰🔥_
#Mai_Dambu
[6/9, 9:29 AM] Black Girl: BABI NA HAMSIN DA BIYU
___________
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
___________
Bude idanu shi yayi gaban shi yana tsannanta faduwa, a hankali ya mike yana kallon Gidado da yake ta barcin shi hankali kwance, zama yayi sosai ya tankwashe kafar shi yana kallon yadda dan uwan shi yake ta barci, baki daya ya shiga zulumi.
Tasowa yayi zuwa wurin kwanciyar Gidado ya kwanta a gefen shi, tare da karanta wasikar jiki.
**
Kallon Mahaifiyar ta tayi da take zuba mata man shanu a cikin tuwon dawa miyar kubewa, sai tashin kamshi yake.
"Inna don Allah kiyi hakuri!" Ta fada cikin matsanancin kuka.
"Haima na gaya miki ba yau ba, ki fita idona ki daina kai kanki wurin Bingel, amma baki ji ki fita hanyar Barkindo"
"Inna naji ba zan kuma ba"
Shigowa Waziri Zakaria yayi yana kallon su, bai ce musu ƙalla ba ya wuce abin shi, tashi Maman Haima tayi ta nufi dakin shi.
Zama yayi ya zabga tagumi yana nazarin yadda kome yake kara lalacewa.
"Sannun me gida"
"Yawwa! Me kuma Haima tayi?"
"Kawai bata jin magana ne bana son tana shigewa Barkindo ne tunda uwar shi bata son ganin ta."
"Toh Allah ya kyauta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 39