Share this page
kofar shashin da aka mallakawa Fulani Aminatu. Kallon Sarkin gida yayi ya nufi kofar, da sauri ya bude mishi ƙatuwar zauren da aka kawata shi da kome kalar zinari da ratsi-ratsin Ja. Sannan an kawata zaurenta (wato a can baya ana kiran Falo da suna Zaure zamu dauki haka a matsayin zauren kawai ba) A cikin zauren kuwa shirya wasu irin mayafai masu matukar kyau da ɗaukar hankali, wasu shara-shara wanda zai zama hijabi ga mazan da zasu tawo ga Fulani ba sai sun isa cikin zauren ba, daga can zaka iya magana. Kuma zata baka amsa sarki Bello kawai yake da hurimin wuce mayafan kuma tsarin shine haka yace baya son Fulani tayi cuɗanya ga wasu mazan musamman bayi ma. "Allah ya baka nasara,.tsarin yayi ta gabas maso arewa nan turakar Fulan..." Sarkin gida bai idda maganar shi ba, yaji sautin muryan Mai Martaba ya ce mishi. "Shiiii!" Sannan ya cigaba da wuce mayafan, bayan ya dakatar da Sarkin Gida ga bin bayan shi. Yana zuwa ya bude kofar dakin da aka ware domin ita Fulanin. Murmushi yayi sannan ya fito izuwa wurin Sarkin gida. Suka fita har zuwa shashin sa, ya zauna kallon Sarkin gida yayi sannan ya shiga cire rawanin shi. "Jafar kai da waye kuka yi aikin?" Cikin girmamawa Sarkin gida ya ce mishi. "Allah ya baka nasara, da nisan kwana ni da wasu bayi biyar ne" saka hannu yayi a kunnen shi yana me kishingida a inda ya zauna. Jijjiga kunnen shi yayi. "An gama ranka shi dade, an cika umarni." Mikewa Sarkin gida yayi da sauri ya fita daga cikin shashin Mai Martaba, ya nufi Bai wato gidan bayi. Yana shiga ya kira bayin nan maza da suka yi aiki ya musu magana, cikin matukar farin ciki suka zube a gaban shi suna masu godiya da sakawa auren albarka. Anan suka tattara iyalan su, suka bar masarautan bayan Sarkin gida ya basu dawakai da guziri masu yawa ya ce. "Sarki Bello yayi muku afuwa, kuma ya baku damar ku tafi kuyi rawa inda kuke so, amma kar ya kuma ganin fuskar ku a cikin masarautan wannan shine daidaiton adalcin da ya muku" "Mun gode kuma mun yi na'am da wannan halin girman da yayi mana, a isar mana da sakon godiya, Allah ya albarkaci rayuwar shi da Fulani Aminatu." Sannan suka bar masarautan ta kofar Bai, wato kofar bayi nan. Sarki Bello ya dauki matakin haka ne, domin wasu dalilai irin ta gidan sarautar su, amma idan da lokaci yayi haka zai bayyana kan shi. ** Masarautan Gombe. Tun kafin a daura auren, aka turo kiran Innayoh wacce ta farka tun karfe biyu na asuba tana shirya kayan Fulani Aminatu, da sauri ta fita bayan ta rufe kofar sosai ta nufi shashin Mai Martaba Sarkin Gombe. A bakin kofar shi ta same shi yana tsaye shi da Babayo. "Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana, barka da dare" "Innayoh ba zan gaji da baki amanar Aminatu ba, idan wani abun farin ciki ya faru kece zan yi alfahari dake, kuma kamar muradin mahaifiyar ta ce, idan akasin haka ya faru kamar faduwar ki ce, ga Aminatu nan tarbiyyar ki ce nan da wasu sa'o'in za a daura auren ta da Sarkin Gobir, kuma an shirya kome na tafiyar ku, kayan ta ma sun yi gaba. Kar naji kar na gani, idan ƙaddara ta fado bata da inda ya wuce masarautar da yafi wannan." Wani irin kwalla ne ya cikawa Innayoh idanun ta, iya soyayyar da zai nunawa yar shi ita ce koda wani abu zai biyo baya bata da inda ya wuce nan lallai Fulani Aminatu tayi dacen Uba na gari. "Insha Allah babu abinda zai faru da zai kawo ta ma sai alkhairi" "Maza ki shirya ta akan lokaci ana daura auren zaku dauki hanya" ya fada tare da barin wurin, sai da ta daina hango hasken fitilar shi, sannan ta mike ta koma shashin Fulani Aminatu. Suka ci-gaba da shirin su. Kamar yadda ka tsara haka ce ta faru, ana daura auren da manyan manyan akwatin gwala-gwalai da suturanta masu yawan gaske daga masarautan elkaname aka kawo mata, sannan aka akwai wanda aka Kawo mata daya masarautan gobir na auren tare da manyan akwatin nan zinarai. Na auren ta wanda lokacin da aka shigar da shi cikin gida abinda matan mai Martaba suka fada shine. "Amma dai sayar da Fulani Aminatu mai Martaba yayi ko? Wannan in ba sayar da ita yayi ba ina za a kai wannan kayan me mugun yawan gaske sai kace ita ce tafi kowa." Sun manta akan ta aka ya fara aurar da Y'a, kuma ya fara bikin shi na farko a cikin masarautan, dan haka ya saka aka daura duk kayan a kai mata kayan ta tayi ta sakawa tana ado dashi. Sannan kafin su bar masarautan yayiwa Innayoh Alkhairi me tarin yawa, aka bata bayi kowa daki sai da suka bata bayi, lokacin da aka kawo na dakin Kilishi kiri kiri Innayoh taki amsar su, da sauri Jakadiya Jebu ta koma tana me gayawa Kilishi abinda Innayoh ta ce. "Ki mai da su bama bukatar su, muna da wadatattun bayin da zasu mana kome." Lumshe jajjayen idanunta Kilishi tayi ta mike tare da gyara mayafin ta, ta fito harabar masarautan. Tana fitowa bata tsaya ba ta tsinke Innayoh da mari wacce take rike da Fulani Aminatu zata shiga leken dokin da aka kawo mata daga masarautan Yola. "Tasss" sautin marin ya karade harabar masarautan. Rike hannun Innayoh Aminatu tayi cikin tsananin tsoro tare da kifa kanta a kadadar Innayoh. "Fulani kilishi a iya yanzun baki da iko dani ko Aminatu, sabida muna ƙarƙashin mulkin masarautan Gobir ce, yin haka kamar lakatar rigima ce, dan haka ki mai da bayin ki bama bukata. Idan wani abu ya faru ba iya su zai tab'a ba, hatta ke da kike da mafarkin goben ki. Idan kuma aka samu akasin haka matar sarki ce fa" ta fada maganar cikin wani irin dakiya. Sauke hannu Kilishi tayi tana kallon ta. Tabbas tsoro ya danne kashin bayanta, ba zata iya aikata wani abu ba, dan haka ta juya ta bar harabar da bayin ta. Juyawa tai tana kallon Innayoh da itama ta juya tana kallon ta. Juyawa Innayoh tayi ta shiga cikin keken sabida yadda Aminatu take kara riko hannun ta. Suna shiga aka fara busa algaitu tare da barin masarautar. Riko hannun Aminatu tai tana faɗin. "Daga yau babu tsoro babu shakkar kowa Insha Allah kina inda za a baki kariya da kulawa. Ba zaki kuma kuka ba sai dai ki ga wasu nayi amma ke, Ya kare a wurin ki" Yadda Innayoh take mata magana da yadda take kara nuna mata wasu abubuwan har barci ya dauke. ... Kasa zama Kilishi tayi tana kallon bayinta, kafin ta juya tana me fita daga cikin zauren ta, ta nufi katangar da yayi iyaka ga masarautar. Zuwa waje tana hango yadda ake tafiya da Fulani Aminatu. Wani irin bakin cikin ne ya cika mata rai tana tuna abinda hare ta gaya mata. "Matukar ta shiga masarautar Gobir ba zaki iya mata kome ba, karshe sai dai ki rasa duk wani damarki. Tauraron ta yana haduwa da na Sarkin Gobir babu wanda ya isa ya iya samun gallaba akan su sai ƙaddara ita kuma wannan ƙaddaran zata zo ne kamar yadda guguwar yashi take tawowa daga tsakiyar sahara. Karki sake amon ki ya cigaba da kewaye ga Fulani Aminatu. Idan kuma haka ya faru tabbas da walakin goro... Domin Ubanta zai iya shirin yaki domin d'igar kwayar hawayen ta d'aya tal" Dunkule hannun tayi tana jin wasu irin kwalla na zuba mata, tabbas ta so daukar fansa akan Yarinyar sannan abin da ya kuma d'aga mata hankali yadda hare ya ce. "Yarinyar zata rayu cikin aminci da salama, zata yi farin ciki a farko a tsakiyar zata fuskanci rayuwarta na tsawon lokacin da ban san adadin shi ba. Kuka da kukan wasu zubda jini zai yawaita bayan shekarun rayuwar ta. Amma zata dawwama cikin farin ciki, kin ga yanayin da yake cikin ƙwaryan jinin! Kinga bakin duhun da ya ratsa hasken nan guguwar ƙaddara kenan, wannan hasken ita ce zata biyo bayan kome a wannan gefen matukar ka tunkaro ta domin cutarwa ba mamaki kanka ya sauka daga gangan jikin ka domin" "Hare nayi farin cikin fuskar ta shekarun rayuwar ta, kuma zan yi farin ciki mara misaltawa domin wannan abin farin ciki ne ya same ni bana fatar Aminatu ta rayu cikin salama." Ta fada tana dariya. "Tana da uwa a gefenta, ba zata yi kunci a fili ba, amma a cikin ta zata yi bakin ciki kowani mutum yana tafiya ne bisa jagorancin ƙaddaran sa, amma ba makawa zata isa inda baki zata ba akwai tafiya me nisa da zai cimma kafin wannan lokacin karki sake a samar da fitilar da zata isar da ita ga ƙaddaran ta. Yawan adawar ki yawwan nasarar ta." ___________________________ *Hi my beautiful mommy's and sister's Barka da Juma'a! Please a ta'ayani sharing mana 🔥 i can't wait to see Sarki Bello da Fulani Aminatu ga Azumi Yazo 🤣🏃 fa ya muke ciki zan gudu nan da jibi wato Sunday idan nayi posting Insha Allah sai Bayan sallah* #Mai_Dambu [3/28, 11:48 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: KALLABI...! A tsakanin Rawuna Na Mai_Dambu EWF https://www.wattpad.com/1205468431?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=jBs9Dv1EFyPUnLBE9l6ckoD6pAsV9A8few5U6c%2F%2F9NmiM0LtJVNAr%2BHtZYxDeN5g1snT5Dl6VUKqJ54qxgM%2B8KZ75nwrIveEGvLj7JCUZz0XPfayJSn65EUggB9zTXfc ** Tabbas Hare ba zai mata karya ba, zata so ganin bayan Aminatu domin da taimakon shi aka rufe bakin kowa na masarautar akan mutuwar Kwarkwarah Amrah Mahaifiyar Aminatu ba dan haka ba da yau bata raye. Kurawa tutar Masarautar Gobir idanu tayi. "Ina ma da Sakinatu ne a wancan matsayin ba zan yi nadama ba, haka ma sai dai ya saka mai Martaba dawo da ni matsayina. Kai ina ko ana hamaza hamata sai na ga bayanki Aminatu." Ta fada tana kara dukar jikin katangar. A hankali ta juya haduwa Jakadiya Jebu ce a tsaye kanta a sunkuye. "Ya?" Ta tambaye ta. Gyada mata kai Jakadiya Jebu tayi. "Inda ba kasa lallai nan ake gardamar kokuwa" Gyara zaman mayafin ta tayi, sannan tayi gaba tana murmushi, Jakadiya Jebu tana take mata baya.. --- A hanya kuwa kamar wacce aka mintsina ta bude idanunta. Tare da tashi zubur tana raba idanun ta. "Innayoh dan dalago na" itama Innayoh raba idanu tayi tana kallon ta. "Mun bar shi a gida" Sake ware idanun tayi kamar zata yi kuka ta ce. "Haba Innayoh, me yasa zaki bar min shi bani da aboki kamar shi fa" murmushi Innayoh tayi sannan taja mayafin da yake can gefen keken sai ga kejin dan dalago har da abincin shi. "Ahhhh dan dalago na" ta wani sauka a hankali tana zare ido. Sai wani murmushi take. "Innayoh iya zamu ne? Har yanzu bamu isa ba?" "Eh tafiyar ce da tazara" Innayoh ta bata amsa. Sunyi tafiyar wuni guda suka yada zango. Kallon ta Innayoh tayi sannan ta ce mata. "Ba kowani abinci ake saka mishi rai ba, wani ana hakura da shi ne domin kare kanka da rayuwar ka" dake an kafa musu tanti ne, fitar da dambun nama Innayoh tayi ta madara. Ta ajiye mata. A hankali ta dauka ta sha, sosai sannan ta ci namar ma. Wani goran duma Innayoh ta mika mata da ruwa a cikin sha, sannan ta ce mata. "Kiyi hakuri, matsayin ki ya wuce shan ruwa a haka." A hankali ta kwanta a jikin Innayoh tana sauke ajiyar zuciya. Koda aka kawo abincin da aka dafa, sun samu Fulani Aminatu tayi barci, dan haka suka tafi da shi, dan Innayoh ma tace ta koshi.. Washi gari. Kafin a kawo abin karyawa, Innayoh ta dama mata fura da sauran madaran ta zuba zuma wadataccen ta bata tasha, koda aka kawo shima mai dawa aka yi. Wurin Galadima aka tafi da maganar abinda Innayoh tayi jiya da kuma Yau. "Ku kira min ita" Tana cikin kintsa Fulani Aminatu aka sake mata sallama. "Innayoh Galadima yana son ganinki" "Toh gani nan tafe" kallon Fulani Aminatu tai ya rufa mata kanta da babban jam mayafi me ratsin zaren ruwan zinari. "Yanzu zan zo, ƙarki sake wani ya kawo miki abu ki amsa kin ji nan babu wanda ya dace ki yarda da shi sama dani kin ji uwar ɗakina" "Toh" Sannan Innayoh ta fita, fadawa biyu da suke gadin kofar tantin ta kalle su ta ce musu. "Karku sake wani ya wuce ku ya shiga cikin tantin" "An gama Jakadiyar alkhairi" Wuce su tayi ta tafi yar tantin Galadima, tana isa tayi sallama. "Shigo Innayoh" aka mata iso a cikin tantin Galadima. Cikin girmamawa da kaskantar da kai ta shiga tantin yana kishingida ya gama karyawa. Shiru tantin ya dauka kafin Innayoh ta d'ago kai ta ce. "Allah ya baka nasara, an ce kana nima na?" Jinjina kai yayi kafin ya ce mata. "Eh na samu labarin an kai abincin Fulani Aminatu amma baki amsa ba har sau biyu? Ko Meye dalilin haka?" Gyara zama tayi tare da sunkuyar da kan ta. "Tuba nake ranka ya dade idan nayi kuskure a wannan bigirin a hukunta ni!" Shiru yayi kafin ya kuma cewa. "Ina son sanin hujjar haka" "A yayinda Duniya ta cika ta tumbatsa gamu mutane masu son kaiwa kololuwar damar da Fulani Aminatu ta samu, ai kasan zuciya bata da kashi kowa zai yi fada ne domin samun damar da ta samu" murmushi yayi sannan ya ce mata. "Haka yana nufin baki yarda da kowa ba kenan?" "Ko daya ba haka bane, nauyin Fulani Aminatu ya rataya a bisa kafaduna dole na kiyaye abinda zai wargaza min amanar da yake kaina" ta fada tana matse hannun ta. "Me Innayoh take bukata a bata domin ciyar da Fulani Aminatu da hannun ta?" Ya tambaye ta. Murmushi tayi tare da cewa. "Allah ya baka Yawan rai duk abinda aka bawa Innayoh zata iya sarrafa shi domin Fulani Aminatu" "Toh shi kenan, an bawa Innayoh damar dafa duk abinda Fulani Aminatu ta ke so" "Godiya muke, Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana" ta fada tare da barin tantin. Tun daga wannan ranar Innayoh ke sarrafa abinda Fulani Aminatu take bukata, har suka dauki tsawon kwana ki goma sha uku, saura kwana ɗaya su shiga cikin masarautar Gobir. Daga inda suke suna hango katangar masarautar da tutar ta.. ** Masarautar Gobir A cikin masarautar biki ake sosai, kamar yau aka daura auren shi kan shi sarki Bello ba karamin al'amari bane a wurin shi domin ya yantar da bayi babu iyaka, an fitar da abinci daga Baitul Malin masarautar an rabawa talakawa sadaka. Kowa sai albarka yake saka mishi. Tun safe sako ya isa ga amarya da tawagar yan daurin auren nan sun dawo, amma ba zasu shigo da hasken rana ba. Sai gobe da yamma, hard'e hannun shi yayi a kirjin shi. Idanun shi akan sansanin da yake hangowa. Baki daya bai tab'a shirywa kan shi wani abu ba, balle ya ce ya ware shi a matsayin ranar auren shi. Shi kan sa auren yana jin wani irin dauki da son zaman shi magidanci ne ta fuskar sarautar shi, amma ta fuskar soyayyar da zai yi bai shirya mata kome ba. Sai dai a lokacin da Sarkin Gombe ya bashi auren Yar shi yayi mamakin da bai ki amsar auren ba, sai ma karba da yayi da hannu bibbiyu duk da kuwa masarautu da dama sun daina basu auren Yaran su mata gudun kar su zama zawarawa. Sai dai abinda Sarkin Gombe yayi akan shi ya matukar saka shi amsar auren Fulani Aminatu. Koda kuwa bai ganta ba yana ji a ran shi zai amshi auren da dukkan zuciyar shi. Domin masu iya magana sun ce zoka ci tuwo yafi tuwon dadi. Duk da yasan itama Yarinyar da za a bashi tana da wanda take so. Amma haka bai wani dame shi ba. Kawai abinda ya sani zata amshi aauren ne domin biyayya ga mahaifinta. Bayan nan kuma zata zo domin zama matar shi. Sai dai yasan ba mamaki itama taji tsoron zamanta bazawara. Wani irin kunci ne ya cika mishi zuciya. A hankali ya juya ga kallon sansanin su. Domin yana jin wani irin nauyi a ran shi. Idan ta shigo masarautar bata son auren shi fa? Zata iya daukar kiyayyar shi tayi ado da shi. Anya bai yi kuskuren auren ta ba? Domin yasan matukar bai mata ba, ba zai tab'a jin dadin zama da ita ba, duk da zaman shi marubuci ya sha rubuta hikayoyin kiyayya akan sarakunar da suka shude wasu sabida soyayyar da sukewa matan suke mutuwa akan matan ko matan su shayar da su guba. Hankalin shi ne yayi mugun tashi. Kusan raba dare yayi a saman katangar, yana jin wani irin yanayi da damuwa. Har sanyin asuba ya mai da shi can shashinsa domin ba dan sanyin ba, Toh zai gwammace ya dawamma a wurin da ganin abinda zai rusa mishi farin cikin shi. Washi gari Juma'a. Masarautar ta tashi da wani irin biki na auren shi, duk abinda ake yana can tukarar shi a kwance, bai ji a ran shi ya fito ba. A can cikin gidan. Ajuji mahaifiyar Yarima Yakubu ce gaban Gambo cikin tsannanin b'acin rai ta ce. "Ban ji kina magana akan Bello ba, kina nufin ki bar kishi mulkin da ya dace a ce Yaran mu ne akai?" Kallon Ajuji Gambo cikin sannan ta ce mata. "Bani da hurumi akan masarautan nan ina zaune ne Sabida Zakaria, idan ta b'aci masai idan tayi kyau rijiya" Jikin ajuji a sake ta bar shashin Gambo, domin tasan tunda ta gaya mata haka ba zata tab'a karya maganar ta ba. ... Wuraren yammacin ranar aka shigo da amarya da tawagarta, yana kallon su, har aka wuce da ita a keken doki har shashinta. Baki daya bayin gidan da sauran bararorin gidan jira suke a fito da Amaryan sarki. Bude kofar keken wani badakare yayi, Innayoh ta fara fitowa, tana rike da hannun Fulani Aminatu wacce ta sha jan mayafi har kasa, tana tafe a hankali tana kara rike hannun Innayoh. shiru wurin ya dauka kafin Jakadiya Rama ta sake gud'a me mugun karfi da amo, haka ya tabbatarwa kowa Fulani Aminatu ta iso cikin masarautan. "Ke Amaryan ma yarinya ce." Inji wata baiwa. "Eh lallai wannan reno aka kawo mishi kenan?" Kafin kace kwabo maganar kankantar shekarun Fulani Aminatu ya zaga masarautan har ya fada kunnen sarkin gida, shi kuma ya samu Sarki Bello da maganar. Yana zaune, a wurin shan iskar sarkin gida ya zube a gaban shi. "Allah yabawa takawa lafiya, nazo ne da wani batu" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce mishi. "Ina jin ka" Ya fada yana lumshe idanun shi. "Yanzu naji labarin wai Fulani Aminatu yarinya ce karama" ya fada yana sunkuyar da kan shi. Ware idanu yayi akan Sarkin gida, kafin ya ce mishi. "Ka nimo min Galadima yanzu" "Allah ya baka nasara an gama" ... A can cikin gidan kuwa Jakadiya Rama ta wuce shashin Ajuji, cikin dakon gulma ta guntsa mata labarin, Fulani Aminatu. Murmushin gefen baki tayi sannan ta ce mata. "Me kika fahimta akan Yarinyar?" "Uwar ɗakina. Akwai sulke a tare da ita. Duk harin da za a kai matukar ba a fara fatattaka sulken ba babu wanda ya isa ua cimma ta." "Lallai kuwa Sarkin Gombe ya san kan duniya. Muje zuwa" injin Ajuji. Baki daya labarin ya shiga lungu da sakon masarautan, labarin da ya raba kan mutane dayawa har wajen masarautan kawunan jama'a ya rabu, sannan ana ta samun sukar masarautan Gombe. Bayan wani lokaci, manyan fada sun tura sakon niman zama da mai martaba. Kallon Sarkin Fada yayi sannan ya ce mishi. "Bayan sallah magariba akwai liyafa sai a tattauna a can." "Toh Allah ya baka nasara, takawarka lafiya a huta lafiya" Zubawa Galadima idanu yayi yana jiran karin bayani. "Wato lokacin da muka isa masarautan Gombe, Sarki Shehu Usmanu ya min bayanin da ya gamsar da ni, da gaske yarinyar karama ce ainun, domin shekarun ta goma sha biyu. Asalima yanzun take wasan kasar ta. Sai dai mahaifi irin shi ba zai jure abinda yake shirin faruwa da ita ba. Ta rasa Mahaifiyar ta daga isowar ta duniya, shima bai samu ya bata kulawar da ya da ce ba, sabida katangar da aka mishi tsakani da ita, Innayoh da Fulani Shatu suka yi dawainiyar renon ta. Babban tashin hankalin ba kome bane sai jifarta da ake ta ko ina na masarautan, haka ya saka masana suka saka shi a gaba da lallai ya dauke ta daga masarautan. Sau biyu yana zuwa wurin marigayi sarki Ibrahim amma yana jin amsar tayin shi na dan kome ba sai dan wasu dalilai gudu biyu" Ciki da mamaki yake kallon Galadima, kafin ya gyara zaman shi yana mishi kallon karin bayani. "Dalili na farko shine idan sarki ya amshi auren ta, zata girma a matsayin bazawara har karshen rayuwarta bata san dadin rayuwa ba, sannan zata sha wahala a hannun kishiyoyin ta. Dalili na biyu kuma tunda Sarkin Gombe yazo ake kawowa Sarki Ibrahim saran shi, wannan dalilin ya hana shi karban auren amma daga baya da ya fahimci akwai kamshin gaskiya a maganar yarinyar shine ya gaya min ya kuma roke ni da na tsaya maka a baka auren Yarinyar. Sukar Sarkin Gombe ya bar shi akan adawa irinta manyan sarakuna kaji yadda aka yi kome." "Toh amma me yasa bai nimawa Zakaria ba sai Ni?" Sarki Bello ya tambayi Galadima. "Ba mamaki idan da shine akan kijeran da an fadadda yakin sa kai, karshe ya mutu, kowa yasan tun zamanin mahaifin ka ya fada kai baka son yaki, wannan nahiyar tana bukatar zaman lafiya ne" Galadima ya bashi amsar. Shiru yayi baki daya ya rasa me zai ce. "Toh yanzun ya zan yi da ita? Kasan dai yarinya ce." Dariya Galadima ya kyalkyale da dariya. Sosai kafin ya tsagaita da dariyar shi. "Kai kake karanta mana, labarin soyayya da kauna yau kuma kai zan tunawa baiwar da Allah yayi maka, Jarumin sarki dan soyayya ka fara akanta mana, idan bai yi aiki ba sai mu sauya salo amma maganar gaskiya zaka ajiye mulki ne ka fitar da soyayyar gaskiya daga zuciyar ka." "Taya Galadima?" Ya tambayi Galadima yana zare idanu. "Ka manta labarin Sarki da aljana da ka tab'a bamu? Da labarin Sarkin dodonin da Yar fulani!, Yau kuma sai ka bamu naka labarin Sarkin gobir da Fulani Aminatu" ya fashe da dariya, irin na abokan da suka san junan su, duk da galadima ya girme Bello amma kusan akwai amintaka a tsakanin su. Kishingida sarki Bello yayi cikin nutsuwa ya ce mishi. "Dukkan su, sun fada soyayyar gaskiya ne bayan ganin yan matan ni kuma ban ganta ba zan fada?" "Mai Martaba yana da ikon ganin ta, amma kafin nan ka fara ganin Innayoh ko zaka fahimci kome akan Fulani Aminatu." "Yaushe galadima ya zama ɗan kanzagi ne ban ban sani ba?" Mikewa Galadima yayi yana faɗin. "Na dibi wata guda ban ga iyalina ba, dan rashin Imani irin na Jarumin soyayya ya tsare ni jin kalar matar da aka bashi ko tausayin yan tsofin mata na bai yi ba". Lumshe idanu sarki Bello yayi dan yasan yana takalar shi da magana ne. Tafiya yayi yana mishi dariya, bude fararren idanun shi yayi wanda suke dauke da wasu irin maiko. Tashi yayi ya nufi shashinsa ya shiga yayi wanka sannan ya fito ya saka Sarkin gida ya kira mishi Innayoh. Yana zaune a babban zauren shi suka shigo. Zubewa tayi tana mika mishi gaisuwa. Shiru yayi yana nazarin ta, kafin ya ce mata. "Da fatan kun iso lafiya?" "Lafiya lau" ta fada. Daga haka bai ce mata kome ba, sai da ya gama abinda yake rubutawa sannan ya ce mata. "Kar a bar Aminatu tasan ni ne Sarkin . Umarni na ne" "An gama ranka shi dade" "Zaki iya tafiya" "A huta lafiya" ta fita, sai da ta samu damar fita ta sauke ƙatuwar ajiyar zuciya, tana kallon kofar. "Toh me yasa baya son Aminatu tasan shi sarki ne?" Ta tambayi kanta. Sannan ta bar wurin. Tana zuwa ta samu an Fulani Aminatu ta idar da sallah, abincin da aka kawo daga gidan Galadima, suka ci har da sauran bayin daga nan suka kwanta domin sun gaji. Haka aka yi ta

Chapter 4 of 39