ta shuri ruwan, aikuwa inda yake ya sauya zuwa ruwa me kyau da ɗaukar ido, diba tayi da saka akan.
"Naga wanda zai sha ruwan nan"
Haka kawai take jin yin mugunta, tana tafiya aka yi dace wasu tsuntsaye suna ihun su na alamar a firgice suke, d'ago kai tayi ta Kalle su, murmushi tayi aikuwa suka fado suna me ci da wuta.
Tsabar masifar da take ji a ranar duk in da ta saka kafarta, wuta ne yake kama wurin yayi bakikkirin.
(Wannan shine yanayin da Baffa'm yayi kokarin hana Aminatun shiga idan har ta kai yanayin haka amadadin alkhairi a ranta amfani da baiwar ta zata yi tayi tana cutar da mutane, a binciken da aka yi wani cibiyar nazarin ilmin dan Adam, sun gano kowani dan Adam yana da Super natural,shine ake kiran shi da Kambun baka, kuma kowa yana da wannan baiwar sai dai wasu kalilin ne nasu yake fitowa, wasu kuma idan ya bayyana iyayen su na maza a boye musu dan kar ya zama tashin hankali a gare su da Al'umma)
Wannan yanayin ba karamin dadi ya mata ba, domin bayan ta bar rafin kafin kace kwabo al'amari ya karade ko ina hatta rijiyiyyon da suke kewayen, tsuntsaye kuwa tuni suka yi cida wuta.
Abin da ya d'aga hankalin mutane kenan suka shiga niman agaji domin dai basu ba shan ruwa, ruwan da ta dauka gidan su Baffa'm ta kai tagaishe da Sarkin Gida wanda taki yarda su hada idanun su. Shima kamar wanda yake tsoronta yaki d'ago kai ya kalle ta.
Tana barin kofar gidan ya D'aga yana bin sawun ta da ido, da sauri ya shiga cikin gidan. Ya kira Baffa'm da Galadima.
Kallon wurin suka yi.
"Wayyo Allah na" inji Galadima.
"Ta zarce Aminatu ko?"
"Kowani lokaci zata iya daukar yanayi akan kowa" baffa'm ya tambaye shi a tsorace, domin shima ya gama razana da yanayin Anum, dan haka suka bi bayan ta.
Sanin babu wanda ya gane me take ciki tana shiga cikin gidan takada shanun ta suka bar gidan baki daya, har yankin ta bari, ba tare da ta juya ba, kawai tafiya take da shanu, ta kai ko mugan namun daji suka haɗu da ita sai dai suyi ta gudun ta. Yanayin ta ta'azzara da ko wucewa tsuntsun yayi akan dabobbin ta,ta Kalle shi faduwa yake a mace.
A can kuwa hankalin mutane ya tashi ga ruwa ya lalace dan haka masu maganin dan masu duba,bokaye da yan bori. Suka tawo aka saka ruwan a gaba da bincike, Galadima da Baffa'm sai dare suka samu damar zuwa ganin ruwan,bayan sun gama abinda ya kawo sune suka dawo gida, a hankali Galadima ya sauke ajiyar zuciya.
"Sarkin gida me yan borin suka fada?"
"Sunce tsinuwa ce da alwashi"
"Sun mata wani abu kenan da har ta yi alwashin"
Girgiza kai yayi, sannan suka ce.
"Babu ita babu alamar ta fa a wannan yankin?"
Kasa magana suka yi suna nazarin ta ina zasu dakatar da ita.
**
"Boka ka duba al'amarin yarinyar nan ta bayyana yanzun haka ta gabar din mu sun mata laifi ta musu alwashin ruwan su ya koma na jini" bincike yayi sosai sannan ya ce mishi.
"Sai dai ka nimawa Danka auren ta ba dai kai ba, a yanzu haka tana gab da samun me iya dakatar da ita. Domin ƙaddara ta ja ta izuwa takin da mutuwa ce xata iya shiga tsakanin rikicinda ya kono kai"
"Ban gane ba?" Ya kuma tambaya,
"Ina tabbatar maka ba zaka iya ba, ba zaka iya dakatar da ita ba, Danka da yake sonta bazai iya ba sai dai idan zaku aura mishi ita bata sani ba, shima ba wai karfi zata kara mishi ba,idan yayi wasa mutuwa zai yi domin yanayin ƙaddara ba zai barta haka."
Kamar wanda aka watsa mishi ruwa haka ya mike, ya bar bokan cikin nashi binciken.
--
Tsawon kwanaki uku,tafiya yake ba dare ba rana, fuskar ta yayi fayau kamar wacce ta rasa jini a jikin ta, kawai kada shanun take, gajiya tayi da tafiyar ya samu wani kasar bishiyar, domin yanayin ta ta fara dawowa daidai, shi yasa taji gajiya zama yayi a kasar bishiyar wata tsohuwar tsamiya, ta lumshe idanun ta, wani irin gud'a aka rangad'a daga jikin bishiyar tsamiyar, gyara kwanciyar ta tayi tana me jin kamar an lullube ta d bargo. A hankali ta kwanta barci yayi gaba da ita.
Kallon rana yayi yaga yayi zafi burin shi ya samu wani wurin ya tsaya yayi sallah sannan ya cigaba tafiya. Hango shanu nata kiwo ne ya sa shi tunanin ai ya kusan gari, daga cikin yake hango wani katon mesa yana nad'e bishiyar da take kwance a jikin shi, kafin ya kuma sauka yana Niman hanyar da zai hàdiye ya baki daya, domin ya kwana biyu bai hàdiye dan adam ba, shi yasa da yazo wucewa ya hango ta kwance yaji ya samu kalacen shi na kwana da kwanaki kafin ta rube ya yarda kanta. Sai zaro harshe yake yana zagaye ya, amma zafin wutar da ke fita a jikin ta yasa shi kasa mata kome, sauka a dokin Lamido yayi ya zaro takobin shi, yana zuwa a hankali yadda mesa ba zai fusata ba.
Aikuwa yana isa ya samu dan bakin Naci ya fara na hàdiye kafarta zuwa gwiwar ta,. Dake mesan shima zalamamme ne da sauri ya zaro bakin shi daga kafarta ya nufi Lamido, a fusace shima cikin fushi da yi kan shi tare da sare kan shi da ya bude mishi. Aikuwa jinin ya ce watsu a fuskartar, abin ya firgitatta kenan ya fasa wata irin kara da ya haifar da kamawar bushiyar twamiyar nan, kafin ta kuma kara ihun ya maza ya toshe bakin ta, tare da fitar da ita kasar bishiyar tsamiyar, ya matse bakin ta da karfin tsiya wani irin tururi da zafi yake ratsa hannun shi, ta shiga kokarin kwace kanta, amma haka yayi nasarar matseta a jikin shi. Sai da ya tabbatar ta suma yanayin jikin ta da yake da zafi ya koma yayi sanyi, kamar wata matacciya, sauke ta yayi ya kwantar da ita sannan ya shiga kafa tanti a wurin ya gyara cikin ya saka ta, kafin ya cigaba da tattara mata shanun ta, kallon tafin hannun shi yayi yaga yayi jajjur. Kallon tantin yayi,
Sannan ya shiga niman tattara kome, ha kuma tsinko magani ya zo yayi ta dakawa da wani irin dutse ya matse ruwan a tafin hannun shi. Lumshe idanun shi yayi yana jin zafin na ratsa shi, sai da ya gama sannan yayi Sallah yana idarwa ya fita farauta. Haka ya samo fakara guda uku wato kajin daji, ya kawo ya gasa, sannan ya ciro bushashen naman da Innayoh ta hado mishi ya koma gefe ya ci sosai, har dare bata farka ba, dan haka ya cigaba da hada wuta yana karatun Alqur'ani.
Anan ya raba dare bai kuskura ya shiga dakin ba, wuraren asuba ya ɗan ajiye Kur'anin ya kwanta yana me lumshe idanun shi. Ai kuwa barci yayi gaba da shi.
Ruwa ne gaba da bayan ta, wanda yake cike da jini makil, kai hannu yayi zai riko ta. Amma ina tayi nisa domin ta nutse sosai, fadawa yayi shima ya hango ta kwance. Daukar ta yayi zai fito fa ita yaji ya kasa motsi daga wurin juyawa yayi zai duba yaga kafarta daure da igiya, gidado ne ya kai hannu zai amshi ta wani ya bangaje shi ya amshe ya,.shi.kuma ya kamo wanda ya dauke ta a hannun gidado bayan ya nuna mishi takobi, juyawa yayi ya zai mikawa gidado ita, aka wurge su da wani mashi... Bude idanu yayi sakamakon jin takobi a wuyar shi, Anum ne rike da takobi tana kallon shi.
"Waye kai? Kai barawo ne? Gaya min waye kai?" Buge takobin yayi daga ita har takobin suka fadi can, sake mikewa tayi, ranta a B'ace ta zata kowa kamar Barkindo yake. Kawai ta kuma tawowa kan shi da takobi tana cewa.
"Sai na kashe ka tunda ka sato Ni" juyawa yayi yana mamakin taurin kai irin nata, kafin ta matso gare shi ya samu damar tsayawa da kyau tana zuwa ya kauce mata, tare da damke keyarta ya D'aga ta cak da kasa. Kallon yadda take mutsu-mutsu yasa shi sake ta, aikuwa ta fadi a kan hannun ta.
"Kasssss" kashin hannun ya bada sauti. Wanda yayi sanadin sumarta.
Sai da yayi Sallah sannan ya koma wurin dokin shi ya dauko kayan aiki ya zo ya kama hannun ya rike addu'oi yayi sannan ya tofa a hannun ya daure mata shi. Sannan ya watsa mata ruwa, ba wai ayayyafa ba, a'a Juye mata yayi a firgice ta bude idanun ta sai lokacin ta ji idanun ta ya cika da kwalla ta ce mishi.
"Kai Azzalumi ne mugu mara imani, Allah sai ya saka min". Ta fada tana matsar kwalla, sunkuyawa yayi zai dauki kayan aikin shi a tunanin ta wani abu zai mata, aikuwa ta fashe da kuka, tana kame kirjin ta. Tabe baki yayi sannan ya dauki abinda zai dauka har tana jin kamshin turaren shi.
"Mugu" ta fada kasa kasa, nan ya juya baya kallon ta,.kafin ya mike abin shi bai kuma bin kanta ba.
"Hala bayan jin ne shima Mugu barawo me kama da yan fashi"
Ita a tunanin ta satotta yayi shi yasa ta rufe idanun ta,.tayi ta gaya mishi.magana abun haushi ko cikanki bai ce mata ba, har ya gama abinda zai yi gari na wayewa ta wuce ta dauki sauran ruwan shi tayi alola, sannan ta gabatar da sallah,.tan idarwa taga ya haɗa wuta yana dumama namar shi, hàdiye yawu tayi.tana kallon shi. Yana halkance da ita amma ko ta kanta bai bi ba, da gayya ya saka namar nan a gaba ya cinye,.aikuwa ya sha bambami.
"Allah ya isa min hàdiye yawun da nayi Mugu me kama da bishiyar kuka,.ka karya min hannu sannan ka cinye kazar jinyata, Allah sai ja gani a ƙwaryan cin tuwon ka, zaka sha mamaki. Idan ba tsoron ba ka bude fuskar ka mana! Yaji tsoron a bashi ruwan madaci ya sha, ragon maza Lusari" wani kallo ya watsa mata, tayi maza ta rufe bakin ta, tana hàdiye yawun tsoro, kafin ta fara kwalkwal da idanu.
"Idan na rashin imani ba, taya zaka cinye abu kaɗai baka ce min bismillah ba, ai ko na maida mugun yawu, Yanzun idan ka mutu wuta za a saka ka...." Wani irin fisgota yayi tare da zare takobin shi ya mai da ita jikin shi yana me buge kifiyar da aka dannota da shi, a hankali mayafin da yake kare a fuskar shi ta warware,aka kuma wurgo musu wani wanda ya dauke rawanin shi da hular baki daya. Tana jikinshi ya sakala hannun shi akan cikin ta, yayi ta kabe harin har sai da mutanen suka gaji dan kan su, suka bayyana sanye da bakaken kaya,juyo da ita yayi da tayi mutuwar tsaye, ya ce mata.
"Rufe idanun ki, ki rike ni sosai"
Kallon shi take sai da ya kuma.daka mata tsawa ta rungume shi tare da boye fuskarta a jikin shi kafin ya samu damar daure ta da rawanin shi ya tam, sannan ya shiga wani irin yakin kota kwana da mutanen da bai san Meye hujjar kawo musu hari ba....
🚶🏾♀️🚶🏾♀️🚶🏾♀️
*Let me waka kai da kazo ganin tsohon ka kaine da shiga yaki na gaya mishi gaskiya ne ko na bari Gobirawa su gaya mishi... Yau na hada muku na yau baki daya domin ba zan yi na dare ba kar ma ku saka rai 👋🔥😍*
#Mai_Dambu
[6/13, 1:14 PM] Black Girl: KALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
EWF
https://www.wattpad.com/1235671083?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=MYIWO8gUzpQ0yHQ9kgF1eyJbcpuX1wMTK9bK4wLygGB63lrJDtyzbPi0oLk1cjgwHzoEkrSFfPyxYC4utoLinogQNDpAd9GNT10bbRT8IKFcBHw%2Bo1xZVxarbLu%2Fx%2BOy
BABI NA HAMSIN DA BAKWAI
_Wannan shafin naku ne Yan GRP din Queen Bee ku more muhawaran ku, yawwa ku gaya min waye ya dace na sheke lamido ko gidado 🤩🤣😍_
*Sorry page 56 nayi typing errors inda na ce kawanya suka mishi tare da kira mishi ido, sannan dayan su ya dafa kafadar shi! So typing errors ne kuma ajizanci irin na dan Adam ayi hakuri 😍🥰💔🔥🤩🤌🏽*
Ba tare da ya juya ba, ya rike hannun arnen dajin ya rike kashin hannun sai da arnen ya kwala ihu, sauran suka ja da baya a hankali ya dawo da shi gaban shi, ran shi yayi masifar ɓaci, sake matse hannun yayi, sai da kashin hannun ya bada wani sauti ji kake "karkassss" ai mutumin a take ya zube sumamme, kallon sauran yayi tun bai musu magana ba, da gudu suka fita daga kokon dutse. A duniya Anum bata tab'a jin tsoro irin na yau ba, dan haka ganin yana takowa wurin ta, ta shiga ja da baya jikin ta yana masifaffen rawa, domin wani irin tsoro ta bata musamman da ya kasance ita da shine a kokon. Fashewa tayi da kuka tana kokarin ja da baya, a hankali yake takawa yana son ce mata ta tsaya amma fir taki, wani irin fisga ya kai mata, tare da cillata gefe can kanta ya bugu da wani dutse, kallon inda ta mike yayi yana kallon kasar da take barci har lokacin, ta saje da dutsen ba zaka ce akwai kasungumin maciji ba a ramin ba, kallon Anum yayi da take sume, kanta yana zubda jini.
Komawa yayi ya had'a wutar ta shiga harkokin gaban shi, sai da ya gama gasa namar, idanun shi nakan macijin, ya dauki kayan aikin shi ta nufi wurin Anum din, cukurkuden gashin kanta ya tattara ya gyara kamar yadda Innayoh takewa Ammyn su, ya dauki magani ya saka mata, sannan ya daure ciwon bayan ya tufke mata gashin a tsakiyar kanta, sannan ya koma gefe ya dauki ruwa ya tsiyayya mata a fuska. A matukar firgice ta farka, ganin ya cigaba da abinda yake yasa ta gyara zaman fatalarta, tana me kallon shi cikin mugun tsoro.
Mikewa tayi zata gudu bai ce mata kome ba, ta juya da sauri ta kwashi kayan ta bar kokon dutsen, domin ba karamin razana tayi ba, ko jiya da yayi yakin bai bata tsoro ba kamar yau dan ita ba sabon abu bane w wurin ta masu bibiyar ta. Amma hali irin nashi da matukar tsoron
Dake ya fahimci ta gama tsorata da shi, shima hada kayan shi yayi ya bar ramin, ya fito taga tana ta kuka, tana kallon yan tumakanta da suka mutu, kusan bafulatani baya son ganin gawar dabban shi haka ne ya faru da Anum, dan haka ta shiga kokarin kad'a sauran dabbobin su bar wurin. Bata san yazo ba, sai jin hannun shi tayi ya amshi tsumagiyar hannun ta, sabida da hannu daya take amfani, juyawa tayi ta kalle shi, idanun su ya sarkafe da juna,. Janye nashi yayi daga cikin nata, ya juya ga dokin shi.
"Hari kwanta ta hau"
Ba musu dokin ya kwanta, kallon ta yayi tare da mata alama da ta hau, girgiza kai tayi tana ja da baya.
"A'a ka bar shi, wallahi na yafe kawai ka bar ni na tafi don Allah idan dan abinda na maka ne kayi hakuri"
Bai ce mata cikanta ba, ya wuce yana koran shanun, ta razana iya razana tsoron Allah take da tsoron shi, haka yasa ta kallon dokin cikin damuwa ta hau, mikewa hari yayi tare da bin bayan shanun, addu'a take Allah ya kubutar da ita a hannun shi domin ta fara fahimtar ba mutumin kirki bane, haka suka wuni suna tafiya sai dare suka yadda Zango domin sun hada da kiwo.
"Ni zan shiga gari ba zan kwana a nan ba"
Wani matsiyacin kallo ya mata, ta koma gefe ta zauna, ya fito da namar da basu ci ba, koda sun tsaya sallah take shima ba a cikin kwanciyar hankali ba, dan haka ko ruwa taki sha, tashi yayi ya nufi wani lambu ya kunna itacce,wanka yayi sannan ya dawo yayi ya samu bata nan, kuma bata dauki kome nata ba.
"Tagwai!" Ya daka mishi tsawa, gurnanin shi yaji, a can gaba da su, da wani irin azazzaben gudu kamar Baffa'm lokacin yana matashin sa, yabi inda yake jin gurnanin tagwai. Hango ta yayi wasu mutane suka gudu da ita akan doki.
Ajiyar zuciya yayi tare da juyawa ya kalli tagwai.
"Koma kai sa biyuna ku zauna zan dqwo sa ita" juyawa tagwai yayi, abin shi shi kuma ya yarfe hannun shi.
Kafin ya gyara tsayuwar shi, ya bi bayan su da wani irin gudu, wani irin kara Hari yayi tare da d'aga mishi kafa sama yana haniniya.
Gudun da suke da doki ba na wasa bane, ita kan amai tayi ta kwarawa ahannun su. Sai da suka iso bakin kofar Masarautan, aka bude musu kofar suka shiga, yana zuba dake zuciyar shi a harzuke take duka ya kaiwa kofar ya tasa ita daga jikin ganuwar ta fadi "ribbbn!" Sannan ta tsaya cak sakamakon dakarun da suka yo kan shi. Ba tare da ya dauki takobi ba, suka Afka mishi, ai kuwa sai da suka rena kan su, domin ya haukace musu sukar su yake yana hada musu aiki na musamman. Sai da ya kareraya su, sannan ya wuce abin shi, cikin masarautar ya shiga.
Maganar Gidado ya dawo mishi.
_Ban tab'a ganin masarautan da take da tarin Darajojin irin namu ba! Ka ganta kuwa?_
Shiga cikin masarautan yayi yana niman ta, hankali tashe sai da ya gama ratsa gidajen talakawa, sannan ya wuce ainun cikin harabar masarautar, can karshe ya tsaya, yana kallon ko ina, jin hayaniya yasa shi bin wurin, wasu kartin maza ne rike da Barkindo Bingel tana zaune tasa a daure Anum, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce.
"Itace Uwar Barkindo?"
Ya nufi wurin, yana jin tana cewa.
"Kuyi ta dukarta sai ta mutu shi kuma ku kai min shi gida"
"Innah don Allah ki kyaleta! Bata miki kome ba ni nayi laifi da na fara son ta don Allah!"
Anum da ta gama razana, jikin ta rawa yaƙe, Lamido komawa yayi gefe yaga yadda zata yi idan aka tsula mata bulala, aikuwa katon dogarin ya zabga mata bulala da tambayar.
"Waye yake baki kariya"
Cikin tsannanin azaba ta ce.
"Akwai wani bayan Allah ne? Ko an ce muku Lusari zai iya kare rayuwa ta ne? Gwaggo Bingel sai kin kashe ni kin binne gawata zan san kin tsane Ni, lusarin danki kuwa wallahi ko yana mutuwa ya dawo ba zan tab'a kaunar shi ba."
"Anum!" Barkindo ya daka mata tsawa,
"Uwata ce fa!" Ya fada yana nuna kan shi, tare da nufar ta.
"Uwar ka ce sai aka ce me? Ko an ce maka ni ba tsaga jikin uwa nayi ba fito ba? Banza Lusari namiji yana nan wanda aka haife shi domin kare darajata ba irin ka Lusari me fitsari a wando ba idan ya ga abun tsoro tir da haihuwar ka, ka tambaye ta shin kai jinin Sarki Bello ne ko kuma a kwararo..."
Kifa mata mari yayi tare da cewa.
"Ku zane min ita ku kai min ita turaka na." Ya fada cikin jin haushi.
"Banza kawai idan ka cika namiji yanzu ka kai ni turakar mana"
Ran Barkindo ya ɓaci sosai, shi kan shi Lamido Hassan a karon farko da ya fahimci, yarinyar bata da tsoro bai san lokacin da ya tako wurin yana gyara zaman mayafin gushe fuskarsa ba, ya na isa wurin me zaneta ya D'aga bulalar shi kuma ya rike, tare da jan hannun mutumin yayi sai da kashin hannun ya karye, sannan ya murde shi da bulalar ya watsa gefe, kana isa gaban Anum, kallon shi tayi hawaye na zuba a saman fuskar ta.
"Waye kai? Me yasa kake tarar aradu a kaina?"
Tawowan dakaru tare da nufar shi ya sashi sake igiyar ya nad'e hannun shi yayi kan su kamar mayunwancin zaki, da ya jima yana farauta bai samu abin da zai ci ba, baki daya a tafashe yake da su gani yake kamar dama can akwai jikakkiyar su da shi, jinin shi tana wani irin dumi, haka yayi ta karya musu kasusuwa, sannan ya nufi gaban Barkindo da yake nuna mishi takobi. Mangare shi yayi ya fadi can sumamme kafin ya juya ga Bingel da take cikin firgici.
Takawa yayi gaban ya ta daura kafar shi daya akan hannun kujeran ta.
"Fitina barci take babu ribar tadda ita, ita kuma wancan abin inuwar ta hutu yake bukata da salama, idan kika sake na kuma ganin burbushi wani da sunan ki. Sai na karya wuyar lusarin danki, idan na fito farauta kowa komawa gefe yake, haka zalika idan nq ce abu nawa ne kowa shiga hankalin shi yake, kin zauna kina wani kafaffu akan mulkin da ba zaki dawwama a kai ba idan na kuma fito ba fito dake gawarki ma ungulu ba zasu ci ba, domin ni wutaaaa ne!"
Ya fadi haka tare da ture kujeranta sai da suka yi dunguren masa sau biyu kafin ta tashi, a hankali wani irin gud'a ya cika masarautar tare sa buga tambura da algaitu yana tashi a masarautan, juyawa yayi a hankali kamr zai kallenta, iska ya fincike mayafin. Gefen fuskar shi me zubin da na Mahaifin shi ta bayyana, gyara mayafin yayi yana mata gargadi da hannu, sannan ya kunce Anum ya dauke ta, ya saka ta a kadadar shi ya nufi wajen masarautan.
Abin al'ajabi kwana aka yi ana buga tamburan masarautar, an je an duba babu kowa haka algaitu da ganguna akwai masarautar ta kasance w cikin wannan yanayin har bayan fitar Lamido, daya daga cikin manyan tsofin masarautan da kan shi ya fito yana shaƙar iskar da take kad'awa.
"Bayan zama da dakon Allah ya bayyana zakin Bello."
Dakyar aka kai Bingel shashin ta, shima kuma Barkindo haka, aka wuce da su.
--
Yana fita da ita ya samu dokin shi, kwantar da ita yayi a saman dokin sannan ya jata har wurin da wuke, kwantar da ita yayi yana kallon yadda tayi laushi, magani ya kwaba sannan ta kifa ta, bata so haka ya janye rigar ta ta baya ya shafe ta da shi, sannan ya koma gefe yana zaune yana gadin ta har gari ya waye, amai tayi tayi jikin ta yayi mugun laushi, juya bayan ta yayi cikin rikici ya fashe da kuka tana buge hannun shi, tare da tirje mishi, fisgota yayi ya sakata a kirjin shi ya matseta, yana jin hucin zazzaɓi a jikin ta, sannan ya d'aga rigar ta ya shafa mata, d'ago yayi ya ga.kanta yayi bata, a hankali yake kallon yanayin zagayen fuskar ta da bakin ta, maida mata mayafinta yayi ya kwantar da ita, sannan ta hada kan kome ya shafa bayan tagwai.
"Idan ka san inda take zama ka kai mu" wani irin rangaji Zakin yake mishi, sannan ya tattara kayan shi ya daura a saman saniya guda ita kuma ya dauke ta akan dokin tana rungume da ita, tagwai da biyuna suna gaba, shi kuma yana kan dokin a bayan shanun, sai da suka shiga cikin gari har gidan su Baffa'm ya Tagwai ya tsaya a nan, sauka yayi da ita ya shige da ita cikin gidan yana sallama.
"Ikon Allah Daga ina bawan Allah?"
Sarkin gida ya tambaye shi, bayan ya d'ago daga wankin da yaƙe, mika mishi Ita yayi tare da cewa.
"Na hadu da ita ne tsawon kwana biyu a hanya cikin halin rashin lafiya" ya fada bayan Sarkin gida ya juya da ita, jan mayafin shi tayi, daidai shigowar Baffa'm da GALADIMA, baki daya rawanin ya kunce, D'aga kyakyawar fuskar shi yayi ya bi bayan Sarkin gida da shi har cikin dakin tana rike da mayafin,
"Barka!" Suka ce mishi juyawa yayi ya zuba idanun shi akan Baffa'm, gaban shi yana faduwa, wani irin sanyi da zazzaɓin da bai san lokacin da ya dirko mishi.
Rike kirji Baffa'm yayi tare da jin kamar zai fadi, sai da Galadima ya rike shi. Yana nuna lamido da hannu bakin shi yana rawa...
*Gaskiya ina fama da mura 🙄😒*
#Mai_Dambu
[6/14, 9:28 AM] Black Girl: KALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
EWF
BABI NA HAMSIN DA TAKWAS
Kurawa juna ido suka yi, kafin Lamido ya janye yana me shafa kan shi, abu daya zuwa biyu suka tsirga mishi, na farko bakin cikin yadda Ammyn tayi ta kuka akan Mutumin gaban shi, na biyu kuma wani mahaukacin soyayyar mutumin da yake huda duk wani sassa na cikin jikin shi, cikin wani ɗan uban sauri zuciyar shi take bugawa kamar zata dirko daga kirjin shi, Tausayin kan shi da kuma yadda yake kallon mahaifin nashi, yasa shi takawa gaban shi tare da rike hannun Baffa'm ya kai fuskar shi.
"Me yasa?" Ya tambaye shi hawaye na sauka daga idanun shi.
"Me yasa ranar ka ki amsar uzurin ta? Me yasa ka juya bayan ka bayan kasan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 39