fuskar jemage me ya kawo ki?"
"Inji Fulani Bingel ta ce tana son ganawa da kai yau din nan"
"Wuce kafin na d'anna miki" ya fada, yana murmushin mugun ta, a matukar tsorace ta juya, ya kuwa ya dauki lemon da yake wurin ya daidaita da mazaunin ta ya jifeta.
"Ki ma kuma dawowa" ya fada tare da tintsirewa da dariya,
Sai da ya gama abinda yake so tare da takalar Magana sannan ya wuce.
"Tir albasa bata yi halin ruwa ba, sam bai kama da jinin Sarki Bello ba." Inji Sarkin Fada wanda aka dawo da shi sarkin gida a yanzu.
"Ka iya bakin ka, domin idan maganar nan ta fito fili kaf duwatsun garin nan sai ya kare a bisa kan ka" sarkin yaki ya fada mishi.
A hanyar wucewa bangaren Bingel, kuwa ya hadu da Mai Martaba, sarki Yakubu tare da su waziri, cikin jin haushin Yazidu din Sarki Yakubu ya ce.
"Ka biyo mu"
"Ni fa babu inda zai, haka kawai sai kace a kaina aka fara haihuwar namiji za an hana ni sakat,"
Ya fada yana zumbura baki kamar yaro karami, cikin kulawa da rarrashi waziri ya ce mishi.
"A'a yarima Barkindo mulki na ka ne, karka kuma cewa baka son." Dan yana ganin girman Wazirin ne amma sai da yayi mishi wani irin kallo irin kai waye da zaka ce sai nayi abinda bana so. Cikin fusata suka shige babban zauren Bingel, wacce take zaune bayi mata suna mata tausa. D'ago fararren idanunta tayi ya zuba akan Barkindo.
"Ki gaya musu nifa ba zan yi mulkin nan ba?" Sai da tayi shiru, kafin ta mai da dubar ta kan su,
"Ranki shi dade, sam Yarima Yazidu bai kama da wanda mulki take yawo a jinin shi ba" inji Yakubu.
"Ban gane me kake nufi ba, idan mulki bai yawo a jinin shi kai me yake yawo a jikin ka?" Inji Chiroma,
"Chiroma rawanin ka yana lilo"
Murmushi tai tana jin su, suna musayar yawu. Hannun ta dunkule ta kai habb'arta, tana murmushi. Idan ka ganta zaka rantse da Allah mulki ya haife ta, nan kuwa tsabar duniya ce da samun daula ya sa ta manta bayan ta. Amma yau sabida wani kishin-kishin da ta ji ana cewa bata da asali baiwa ce aka yantattu zuwa kwarkwarah yasa take son yau ba gobe ba, ta sada Yarima Barkindo ga mahaifarta.
"Mandiya" ta kira amintacciyar baiwar ta.
"Na'am uwar gijiyata"
"Ka saka Yarima Yazidu a gaba ya tafi ya shirya zamu tafi rugar gona"
"An gama Ranki shi dade"
"Ina zamu Innah?" Dauke kai tayi tana kallon su Waziri.
"Bamu san me yasa Fulani ta bukaci ganin mu ba" waziri ya a tambaye ta.
"Hmm! Kwana biyu ban ga Fulani Haima ba, ko bata jin dadi ne?" Ta fada tana kallon gefe,
"Da akwai abinda Fulani Bingel take bukata ne?" Waziri ya tambaye ta, domin duk lokacin da Bingel ta tambayi Haima yasan babu mutunci a al'amarin ta, yar shi ce da matar shi, ba karamin kaunar yarinyar suke ba, gata da shiga rai, sannan duk lokacin da tazo cikin gida Bingel sawa take a ciyar da yarinyar kamar zata mutu, haka ake dura mata abinci. D'ago kyawawan idanun ta tayi tana kallon shi.
"Zamu tafi ruga da ita ne ko baka bukata ne" abin tausayi kamar zai kwanta tabi kan shi,ya ce mata.
"Bata da lafiya ne"
"Yayi! Sarkin rikon kwarya kana sane da wa'adin yana kan zuwa ko?"
"Ranki shi dade ina sane yanzu yana da shekara sha takwas, saura shekara tara."
Ya fada cikin matsanancin damuwa, yau ban da Allah bai bashi haihuwa ba, ai da sunga duniya, da wannan yanayin suka mike zasu tafi ta ce musu.
"Muna bukatar dukiya daga Baitul Mali, sannan a bada dawakai sauran ai ba sai na fada ba"
"Toh an gama" karfin da Bingel take da shi a yanzu a masarautan ko Yakubu da yake sarki bai da shi, asalima wani irin shakkar ta kowa yake, tun wani yaki da aka yi ta bada umarnin a tura dakarun, da yadda ta shirya kome na yakin kamar namiji yasa kowa yake masifar tsoron ta, domin anyi nasara a yaƙin kuma Alhamdulillahi.
A hankali Bingel ta zame musu alak'ak'ai, sannan duk wata mace da take cikin masarautar bata isa ta nuna mata kyau da iko ko kwalliya ba, ko bikin sallah za ayi kowa bayan Bingel yake, abinda ya haɗa suke nan da matar waziri, dake kowa ya dawo bayan ta, har su Ajuji sun dawo kasanta, ita kuma matar Waziri ta ce ba zata bautawa wata mace ba, shine take jin haushi ta, har take hucewa akan Yar ta, Haima.
Yarinyar yar shekara goma sha biyu ce, ba laifi tana da kyau, kasancewar kakan yarinyar mace bararoji ce wacce ta fito daga kabilar woddabe bororo, kyawawa ne masu kyau da ake kira kyau, sannan uwa Uba fara ce sol shi yasa tun yanzu ana yawan kawo mishi kamun kafa.
Bayan an gama shiri suka nufi rugar gona, tafiya ce da ba zata tab'a mantawa ba, sanadin shi ta zama uwar sarki me jiran gado. Dan haka sun shiga garin da la'asar. Lokacin mata sun watsa an bar wata kyakyawar mace a tsakar gidan tana surfe, yarta da gashi ya lullube mata kai tana zane jikin Turmin da take daka, sai jan hanci yarinyar take.
"Gafara dai ina mutanen gidan nan Fulani Bingel Yahanasu tazo ganin gida" kamar waɗanda aka koro su, daga cikin dakunan su.
Turus suka tsaya sabida wancan bingel din an gaya musu budurwa ce ta yau kuwa babbar mace ce, da katon saurayin ɗa.
(Bingel tana matsayin Empress ce, the mother of next King, that's why take Abu like she zata juya duniya da masarautar kuma haka ne, she have more great power da tasan weak point din kowa, so she already achieve luckily bata jiran wani ya tsaya mata zata iya fight domin samun achieve dinta Allah yasa kun fahimci abinda nake nufi)
Wata Daadah ce ta fito ta kalle ta, sannan ta ce mata.
"Ki koma inda kika fito"
Shiru tayi domin ba zata iya bada hakuri ba, kar bayi da fadarwar ta su kai tsegumin masarautan.
"Kaka har dani" ya fada yana kallon Daadah da zata shiga cikin dakin ta.
"Eh"
"A'a Daadah, Bingel shigo." babban wansu ya fada lokacin da ya shigo gidan.
Shiga daki kowa yayi fadawan suka tsaya a waje.
Har lokacin matar nan bata daina dakar ba, kwal aka buga mata kwallon mangwaro. Bata d'ago kai ba, haka bata fasa ba, zuwa wata dattijuwa tayi ta shiga gaya mata magana.
"Matsiyaci dai bai ji dadi ba, yar banza mayya" ta mangare yar.
Cikin matsanancin kuka Uwar take magana da wani harshe wanda yake da alaka da labarci ta ce mata.
"Waan ka xumahay maalin maalmaha ka mid ah ma awoodi doontid inaad sidayda oo kale u ooyaan oo aad maqasho Anumullah"
(Kiyi hakuri wata rana sai labari, ba zaki cigaba da kuka kamar yadda nayi ba, kin ji Anumullah."
"Innalillahi wa'inna alaihil raji'un, Jama'a Zahira ta zage ni jama'a ku fito ku ji abinda take faɗa ita da yarta" kar dama jiran wannan yanayin suke, matan suka fito zasu rufe ta da duka,, hayaniyar ce ta ishe Barkindo ya fito yana cewa.
"Wai baku gajiya ne da ihu?" Yana fadar haka fadawa na shigowa tare da daka musu tsawa, takowa yayi yaga matar a durkushe.ita da yarta.
"Sannun kin ji!"
Ya d'aga ta.
Kallon kwayar idanun ta tayi ya ga yana dawowa wani irin kan shi ne yayi wani irin amsawa, ya durkusa.
"Allah xanuun baa i haya, salaan, ma garanayo inaad indhahayga fiirin doonto, waan ka xumahay."
(Wayyo Allah na shiga uku ban san zaka kalle ni ba, don Allah kayi hakuri ban san zaka cutu ba)
"Shikenan Daadah kizo matar Salihu ta cinye miki jika an shiga uku" suka kuma rufe ta da duka, kamar sun samu jaka. Fitowar Bingel a gigice tawo kan danta.
Tana ganin matar tana kuka. Dan karta nuna mugun halin ta ta kalli matar tsaf sai da gaban ta ya fadi, domin babu abinda ya rabata da Fulani Aminatu, wani irin yamm jikin ta yake tana jin duk inda aka shiga aka fita matar tana da nasaba da Aminatu, take mata yatsu tayi tare da ɗaukar kai kamar bata ji ta ba, tsagwaron mugunta da makirci ta ce musu.
"Kai dalla ku kyale ta, babu abinda zata iya, na yarda da ikon Allah ta fada amma a kasar ranta sai da ta murje yatsun baiwar Allah nan, tana d'aga kafarta matar nan ta zube a wurin a sume, wani irin ja garin yayi, Salihu da ya ga haka, cikin tashin hankali ya nufi rugar su, amma ina kafin ya isa shanu sun ka shiga zibewa suna kamawa da wuta. A duk lokacin da ranta ya ɓaci, abinda yake faruwa da ita kenan. Wanda ya nuna tana da boyayyen al'amari a tare da ita, kafin su isa rugar rabin dabbobin sun mutu, haka ya samu ya isa ya sami yar su karama Anum tana ta gudu daga daki zuwa waje, tana dauko garin maganin da ya ajiyewa mahaifiyar ta, idan ta ga alamar ciwon zai tashi ta jika, abinka da yarinta ita kawai Zubawa uwar take. Yana zuwa bai tsaya wata wata ba ya dauke ta, zuwa cikin dakin ta, a take ta shiga hada mata maganin, sai da ya saka mata sannan ya koma gefen yana kallon ta . Mikewa Anum sauran madaran da yazo da ita yayi ta sha.
"Sannun ko?" Ya fada mata,
Kallon uwar tayi ta koma gefe, tana kallon kafar uwar, wanda yayi jajjur. Abu hudu yasa Bingel yin haka na farko kamar Matar da Aminatu na biyu bakin cikin tafita kyau a duniya tana adawa da matar da zata fita kyau ko yaya ne, balle wacce zata yi kama da Aminatu na uku ta tab'a mata Dan ta da take ji kamar duniya ta akan shi na hudu saurayin da aka bata wanda ta gujewa kaddaran auren shi take aure. Dalilin da yasa tayi wannan abun Kenan, bayan nan tana da kudiri dama kuma ta jima tana niman haka, yau ta samu. Bindi yuri ya gaya mata.
"Idan kika sake danki ba zai yi mulki ba, zamu kama miki kowa amma ki sani danki ba zai taba mulki ba sai an samu mace me irin jinin Aminatu, dan haka ki tabbatar kin samu mana irin ta da ita zamu yi aikin."
Murmushi tayi tana kallon yadda mahaifiyar ta take kuka kan danta, dama tasan fushin na lokaci ne idan ta sauko zata yi hakuri dan haka ta shiga basu labarin abinda ya faru da ita inda ta karkace kai ta zuba musu karya har da cewa ai daga fita fitsari ne bata kuma fahimtar kome ba, sai ganin ta yi a turakar sarki Bello, ashe ya fada soyayyar ta kuma yayi alƙawarin ba zai yiwa matar shi kishiya ba shine ya mai da ita kwarkwarah, amma matar shi ta tafi bar masarautan sabida abin kunyar da tayi, shi kuma ya tafi jinya ba a san ma inda yake ba, sharu goma sha daya kenan gudun gori yasa ta kawo dan ta, amma tunda basu bukatar tan zata koma tasan da sarki Bello yana nan yadda yake ji da Barkindo ba zai tab'a yafe abinda Zahira tayi yiwa ɗan ta ba,
*Jaruman mu gudu sun bayyana.. Barkindo Yazidu, Fulani Haima, Gidado Husaini, Lamido Hassan, Anumullah ya kuka ce?😍🥰🤌🏽🤫*
_ZAN YI AMFANI DA WANNAN DAMAR NA TALLATA MUKU SABON LABARI NA ZAYN MALIK PAID BOOK 300#_
#Mai_Dambu
[5/27, 9:03 AM] Mai_Dambu: KALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
Mai_Dambu
*EWF*
BABI NA TALATIN DA SHIDA
_DA KAKKAUSAR MARTINI DA HADE FUSKA NA FUSATA NAYO KAN YAN GRP DINA 😡🚶🏾♀️😒 ZAN BAKU AMSA KU MU HADU IDAN BABA BAHARI YA KUMA LASHE ZABEN WASU SHEKARU TAKWAS 🤣😂 WAI YARIMA BARKINDO SHINE YARIMA LUSARI 😏🙄😭😿 WANNAN ABU TA CIJE ZUCIYATA MU HADU A KOTU KAWAI 😡💔_
Yadda take maganar cikin karayar zuciya yasa baki daya kowa ya fusata, cikin shashekar kuka, take rike da hannun mahaifiyar ta.
"Itama zahirah ba laifin ta bane, haka na faruwa da ita ne, idan mutanen wannan gida suka dame ta, dan haka karki saka tashin hankali a ranki zai ji sauki" inji Yayanta, can kuwa suka samu yayi ta amai, kafin ya samu nutsuwa, kallon Mahaifiyar shi yayi ya ce mata.
"Innah ya matar basu mata kome ba ko?"
"Babu abinda suka mata" gyara kwanciyar shi yayi yana lumshe idanun shi, tashi yayi zai fita ta rike shi.
"Ni fa lafiya ta lau, kuma ba zaki ajiye ni" da Idanun tayi mishi alama da inda suke. Kamar yaro karami ya koma ya kwanta sannan ya juya mata ba, can dai ya ishe su da mutsul mutsul, dan dole ta saka Mandiya ta kira mata sarkin gida, ta gaya mishi ya zuba idanu akan shi.
Haka ce kuwa ta faru, a can dakin Mahaifiyar Salihu yana durkushe, gaban ta.
"Wannan asarar da ka yi kace min ba zaka rabu da yarinyar nan ba? Yau ka dubi yadda bingel ta koma, ban san inda ka kwaso mana annoba ba, gaskiya ka san yadda xaka yi da ita"
"Inonon ya xan yi da ita kuwa? Ba zan iya rabuwa da ita ba, ina son mata ta. Ina kaunar ta duk abinda zaki fada zan yi ba zan kauce ba, amma ba zan sabawa Allah akan ki ba."
Ta san duk cikin yaran ta, shine kawai take iya juya rayuwar shi, kiyayyar Zahirah ya samo asali ne tun daga ranar da ya dawo daga fitar da yayi lokacin da aka hada auren shi da bingel ta gudu, dan haka shima ya haɗa dabobbin shi, ya bar garin gashi dama Allah ya daura mishi kaunar ta, toh ta gudu dan haka ya bazama duniya, malam Jauro kuwa bakin ciki yasa shi faduwa, tashin da bai yi ba kenan sai a kiyama, yanayin yayiwa Daadah tsauri domin tashiga tashin hankali kamar me, kafin Allah ya rage mata damuwa, dan haka ta zuba idanu tana jiran zuwan ranar da bingel zata zo.
Shi kuma garin yawo da shanun shi ta fada yanki Somalia, a can yayi ta kiwon dabbobin shi, har Allah ya haɗa shi da abu Zahirah, wani balaraben kauye, yana da tarin dukiya da Darajojinsa a garin domin attajiri ne, yara auren wata mata me suna Rusailah, yaran su uku. Akwai Aliyu shine Babba, sai Atika sai Zahirah.
A duniya babu abinda balaraben nan ke kauna da riritawa kamar matar shi da Yaran shi, shi yasa yaki yarda ya aura kowa yaran shi sai mutumin kirki, haka matar Aliyu yar Sarkin Somalia ce, shi yasa Atika sai da ya tsaya sosai akan ta da mijin ta, Matar shi da Yaran shi yan baiwa ne, idan ka rike su da Amana Allah sai ya rufa maka asiri tare da bude maka kokofin samu, ya hadu da ita ne, lokacin bara wuce shekara goma ba, ya badu da ita.
Duk da bai so ya takura ta ba, sai dai a yar tafiyar da yayi da ita ya kaita gidan iyayen shi, ya fahimci yarinyar tana da boyayyen al'amari, lokacin da mahaifin shi ya ganta shi da kan shi yayi mishi sha'awan ya aure ta.
Babu yadda ya iya ya yarda aka aura mishi ita, sai a daren ranar mahaifin shi yake gaya masa.
"Nayi maka auren nan ne domin itace yalwar arzikin ta, kuma itace zata iya zama da kai babu wani abu da zai bayyana damuwa a gare ka, ina baka shawaran ka rike ta da amana domin ba kasafai ake samun irin su ba"
Zan iya cewa dakyar ya barta ta cika shekaru goma sha biyu, gashi Allah ya taimaka ta kara girma, a duk lokacin da ta zauna tana gaya mishi Yayarta da wani ya tafi da ita bata san hanyar gida ba, koda ya tambaye ta cewa tayi daga kasar Sahil suke,. Rufe mata baki yayi tare da bata hakuri ta manta da su, ai ba zata kuma haduwa da su ba, har kwanan gobe bata manta da sunan Yayarta ba, Amrah!
Shekara daya ta haifi Aliyu sai da ya cika shekaru biyu ta yaye shi dan wani irin gata ake nuna musu ita da Yaron, musamman da Abu Zahirah ya fahimci matar shi irin mata nan ne da baka taba gajiya da su, bai kuma rikicewa ba sai da ta kuma haihuwa, ai bayan tayi arba'in idan ta sakata a daki sai tayi da gaske.
Asalin su ƙabilar baggara ce, su ba Fulani ne, wasu nau'in jama'ar shuwa Arab ne, da suke yawo kamar bararoji. Suna yawo da shanun tumakai, da awakai. Matan su ana yawan rigima akan su, dan Allah ya yi musu baiwa na musamman, idan har ka aure macen su, toh sai kayi da gaske xaka iya adalci, haka suke.
Tsakanin Atika da Zahirah shekara daya, sun dauki soyayyar dunya suka daurawa Yaran su, tare da tattalin su Gara Aliyu namiji ne, yana fita. Tun lokacin da Salihu ya shiga yanki Somalia da dabbobin shi, sai ya hadu da abu Zahirah, anan ne suka makalewa juna, domin bata wuce shekaru goma sha uku ba, ganin nagartaccen halin shi da ilimin shi ya sa Abu Zahirah ba shi auren ta, anan aka sha bikin,suka zauna na wani lokaci. Dan ma shi Salihu yawo da dabbobi ya hana shi aure da wuri dan haka ya ɗauki auren shi a matsayin abinda Allah ya hukunta mishi, dan ya bar gida da kusan shekaru takwas ya auri Zahirah, aure da rabo domin bata jima ba ta samu cikin Anum, bayan ta haihu suka cigaba da soyayyar su, shekarun Anum bakwai suka tattaro zuwa ganin gida. Suna zuwa kuwa Inonon ta ce ba zata zauna da suruka bakarabiya ba, dan bata mata kama da me gaskiya ai Mayun larabawa ne, dama kafin su tawo sai da Abu Zahirah ya gaya mishi asalin yar shi da wacece ita. Ya ce yaji ya dauka, domin ba karamin son ta yake ba, musamman ta bangaren d'aga buje.
Tunda da suka zo kowa ya tsane ta, wai idan aka mata abu sai ta shiga daki ta zauna mugunta da zalinci, wannan yanayin ya haifar musu da yawan mace macen dabbobin su, ai suka kara fusata.
Wannan kenan.
Bayan ta farka ta kalli yarta , tana shafa kanta. Jikin ya yana bata kawai ta koma gida, ta bar musu Anum ba dan bata son yarinyar ba, amma ita ce dolen su, kallon kofar wajen tayi, Insha Allah zata dawo gare ta, a yadda take jin wani irin zafi ba alamun wani abu na gab da isowa na cutarwa, dan haka ta bude kwatinta, dauko warwaron rage nisan tafiya tayi, ta saka sannan ta sumbaci gashin yar.
"Zan dawo bi'izinillah" daga haka ta matse warwaron wanda yayi daidai da shigowar wasu kartin maza, iska ce me karfi ya shiga shawagi a dakin suna kallon ta, har ta b'ace.
Wannan abun ya d'aga musu hankali ta tafi abinta. Fita suka yi suka bar gidan. Domin dare yayi kuma Bingel tana gidan bata bar gidan ba burin ta a sace mata Zahirah a tafi da ita inda zasu yi aikin gadar da jinin ta ga mulkin su. Sai dai ita bata shigo rayuwar gidan ba, sai da Ubanta ya shirya ta ko ta kwana, ta bar musu dai yar su.
Washi gari aka tashi babu ita, abin da ya saka Salihu yankar jiki ta faɗi, kafin a ce an yi wani abu rai yayi halin shi, bakin ciki da damuwa, sun hana shi sakat da matar shi. Sannan sun kuma yi sanadin guduwar ta, yayi imani da Allah kafin rasuwar shi abin cutarwa ta gani ta gudu, bakin cikin haka yasa shi faduwa sai gawan shi.
A ranar bata zauna zaman makokin ba, tayi tafiyar ta kayan da ta kawo duk ta raba musu. A hankali tsana da tsangwama ya dawo kan Anum,
**
Zaune yake yana shan kunun alkama,
Zama Gidado yayi gefen shi yana murmushin jin dadi.
Juya mishi hannu yayi tare da mika mishi wani littafin shi.
Kallon shi yayi fuskar shi babu yabo babu fallasa,
"Ya Gidado kace Bana ya dake ni" ta kwaso da mugun gudu, garin ta boya a bayan Gidado ta yi kwallo da kunun Lamido, ya watse musu a jiki. Yadda zaku san miskilancin shi ta kai innanaha,(kai ko Wancan basamuden Samande da basamuden Jordan suna magana ai ko motsi 😏) kamar ba shi ba ya cigaba da bude Litafin. Ita kuwa ta makale a bayan Gidado.
Kallon Yayanta.
Kallon shi Gidado yayi ya tambaye shi da hannu me. Da hannun,
"Me ta maka?"
"Kaiwa yarinyar nan sai ta shiga dakina ta min barna"
Juyawa yayi ya kalle ta. Tayi raurau da idanun ta.
Tambayat ta yayi da hannun.
"Me yasa kika mishi barna?" tura baki tayi tana kallon shi.
"Shima me yasa ya gayawa Fulani karama nice Naci nakiya?"
Duk wannan abinda suke yana jin su, bai d'ago kai ya kalle su ba, asalima sha'anin gaban shi ya fi karfin shi bai da wani lokaci.
Juyawa Gidado yayi zai mishi magana, wani tamke fuska yayi dan shi baya shiga harkan yarinyar sam bata jin magana, amma yadda take son Hussain yasa shi dan sakewa da ita. Amma shima ba wai yana magana ko shiga shirginta bane a'a asalima bai mata da wasa idan ta fara haukar ta yana zuwa wurin zata shiga hankalin ta.
Itama tafi mutunci da Gidado, shi kuwa ba kaka bane wani alamari ne ba daba a zuciyar shi akan Fulani Binta.
Girgiza kai Gidado yayi yana mata fada, duk da da ba magana yake ba amma kan fuskar shi zaka fahimci yadda yake fadar, dake itace yar karamar yarinya a cikin gidan kuma autar mai Martaba, fashewa tayi da kuka ta nufi wurin Innayoh da gudu, na kuka. Yadda take kukan yasa Fulani Aminatu ta fito.
"Uwata me aka miki?" Tura baki tayi tayi tana kallon Gidado.
"Ammyna Bana ne ya haɗa ni da Hamma Gidado! Shine yayi ta min fada bana son faɗa"
"Gidado me tayi maka?" Lumshe Idanun yayi ya sannan ya sake mata murmushi, daga idanun Gidado ta fahimci girman soyayyar baffa'm da ya mata yasa ta fahimci yanayin Yaranta, ko bata fada ba Gidado sak baffa'm ne shi kuma basamude wallahi bata san wani irin mutum ne shi ba, sannan shi ko yan mata baya iya d'ago kai ya dube su, tana da yakinin matar shi zata sha wahala, amma Innayoh tana yawan gaya mata matar Lamido sai tafi kowacce mace daraja domin namiji ne me iya boye halin shi.
Kura mishi ido tayi tana murmushin, duk da an bata shi da kunu haka bai saka ya nuna alamar damuwa ba.
"Gidado me ya ke damun shi?"
Murmushi yayi yana mata magana da hannu.
"Wai zasu tafi yaƙi ne yake ta dube dube" ya fada mata da hannu.
Zungure mishi Goshi tayi tana cewa.
"Ka daina saka Bintu kuka san zane ka, Uwata kiyi hakuri sai na zane miki shi kin ji"
"A'a Ammyn karki dake shi, ko Hamma na" jan hancinta yayi sannan ya nuna mata hanya suka. Nufi cikin gidan ya rakata. Suna barin wurin ta raka su da ido,, wurin Lamido ta nufa ta zauna. Sai lokacin ya ajiye littafin hannun shi.
"Me yasa baka gaya min yaki zaku tafi?" Sunkuyar da kai tayi yana wasa da kasa.
"Ubangidana, ga madara me zafi ka sha."
Murmushi yayi yana kallon ta, cikin siririn murya kamar ba zai magana ya ce mata.
"Innayoh ba zan jima ba, wannan shine fitar farko da zanyi idan na dawo toh idan ban dawo ba addu'ar ki shine abinda zai taimaka min"
Murmushi Fulani Aminatu tayi sakon ta yake bawa Innayoh, bata san wani irin mutum ne shi ba, sam baya magana da ita sai dai Innayoh baki daya babu shakuwa a tsakanin su..
*Ban sani ba ko zuwa dare zaku samu kari ba, Sabida satin nan baki daya muna biki Yayan su Walid so INSHA ALLAH sai Monday zan yi missing din ku🤌🏽😂🤣 Masu tambayar ko ina da hadi da gidan Sarauta wallahi ko daya bani da hadi da su sosai, amma akwai dan kaɗan so rubutu ne kawai yake iya bayyana ka kamar wani bayan kai din bawan Allah ne🔥🤩🥰🏃😹😂ZAN YI AMFANI DA WANNAN DAMAR DA NA MUKU SABON LABARI NA ZAYN MALIK PAID BOOK 300#🤣*
#Mai_Dambu
[5/28, 6:53 PM] Mai_Dambu: KALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
EWF
BABI NA TALATIN DA BAKWAI
Kallon juna suka yi da Innayoh, kowacce fuskar ta dauke da murmushi. Shi kan sa yanayin sakewar shi zai saka ka fahimci yana cikin yanayi na musamman, amma ba wai akwai murmushi bane kawai fuskar ce a sake ba kamar dazun ba, Wani sirrintacciyar murmushi ne, wanda sai ka nutsu zaka fahimci cewa yana yi, juya musu baya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 39