tun daga ranar da aka haife shi, kiyi hakuri da abinda nayi amma ya zama dole ne nayi haka, na tura mishi daya daga cikin su."
Kallon Innayoh tayi taga ta cika mata Idanu, dan haka tayi kasa da kai tace mata.
"Duk yadda kika yi daya ne." Daga haka ta cigaba da gyara kumbar ta, ta wani dauke kai kamar bata taɓa magana ba, murmushi Innayoh tayi domin bata dauka Fulani Aminatu zata iya bayyana kishin ta kai tsaye haka ba, har zata bar wurin ta ce mata.
"Duk abinda zan yi ba zan taba yi dan jin dadin kaina ba, kuma ba zan yi dan na kuntatta miki ba, zan yi ne domin kare mutuncin ki" daga haka ta bar wurin, bata ji zafin yadda Fulani Aminatu tayi ba dan tasan dole tayi kishin Mijinta, abu na gaba shine addu'a kawai domin abinda tayi ya samo asali ne daga Inna Marwa. Ita din kusan Gwaggo takewa Sarki Bello kuma yau kwana huɗu kenan da zuwan ta. Sun je sun gaida da ita da Fulani Aminatu, kuma Alhamdulillahi Innah Marwa ta yaba da Aminatu sai dai bayan sun bar shashin ta, Ajuji ta ke fadawa Inna Marwa cewa.
"Uwa yarinyar nan bata haihuwa, kuma an bawaai Mai Martaba kwarkwarah yaki amsa"
Juyawa Inna Marwada tayi sannan tace mata.
"A kira min Jakadiyar Gobir"
"Wo!" Ta rike bakin ta, sannan tace mata.
"Baki da labarin Sarki Bello yasa a kashe ta, amma don Allah karki ce a bakina kika ji" shiru Inna Marwa tayi sannan ta ce mata.
"Toh tashi ki ban wuri, kuma a kira wacce take matsayin Jakadiya yanzun"
"Ai Innayoh ce wacce suka shigo tare da Aminatu"
"A kira min ita"
"TOH" kowa da aka kira Innayoh, tazo ta durkusa a gaban Inna Marwa, ta kuma kira Sarki Bello da galadima, suka taru a gaban ta.
Shiru tayi kafin ta d'ago kai, sannan ta ce musu.
"Innayoh kece Jakadiya ko?"
Gyara durkuson tayi, kafin ta ce mata.
"Eh Fulani Inna Marwa" murmushi dattijuwar tayi sannan tace mata.
"A matsayin ki ba iya Jakadiya ya kamata ki dauka ba, hatta fannin uwa ya ka mata ki dauka, shin uwar arziki zata so ganin ana jin ciwon abinda yake faruwa sanadin Yar ta?" Sunkuyar da kai tayi tare da damke zaninta, sannan ta girgiza kai.
"Toh me yasa Fulani bata bawa kwarkwarorin nan damar shiga wurin mai Martaba ba?"
"Laifina ne Fulani Inna Marwa. Nice ban tunatar da ita ba, insha Allah haka ba zai kuma faruwa ba"
"Yana da kai ki kara mata kima ta hanyar nasiha da tunatarwa, idan haka samu haka ba makawa an kashe bakin masu kaiwa da komawa, duk lokacin da Fulani ta shiga kwanakin ta na al'ada a tura mishi wacce zata dauke mishi laluran kwanakin, idan ta dawo kuma a dakatar da kowacce mace shiga turakar shi sai ta sake shiga kwanakin" idanun Innayoh ne ya cika da kwalla ta rasa kuka zata yi ko farin ciki, sannan ta cigabq da cewa.
"Yan mata hudu sun mishi yawa a bar daya me kyakyawar sura da nutsuwa"
"Toh Fulani Inna Marwa an gama" haka ta gama tsara kome, sannan ta sallami Innayoh, juyawa kan Galadima tayi sannan ta ce.
"Wani kokari kayi na matsalar Aminatu da Bello" gyara zama yayi tare da sunkuyar da kai kasa ya ce.
"Inna Marwa, basu da matsalar kome. Jinkiri ne kawai daga Allah, idan da zaa yi hakuri sai abin ya kasance"
"Ban gane ba?" Ta kuma tambayar shi,
"Dukkan su lafiyar su lau" ya fada a hankali, Inna Marwa irin matan nan ne da suka taso cikin iko da bada umarni, abinda ta sani shine mulki ya bi jikin da ta jinin ta, sannan tana cikin manyan matan masarautan Sokoto, domin tun zuwan shehu Usmanu danfodiyo, aka bada auren ta ga Wazirin Sokoto kuma babban Almajiri Shehu Usmanu danfodiyo, sai kuma aka yi dace mijin ta an bashi Sarkin rikon kwarya, har ya rasu, wannan dalilin yasa ta jin gaba da baya mulki ya samar da ita, bata cika zuwa ba daga biyar ko goma, amma idan tazo kowa na fadar nutsuwa yaƙe, (zamu iya kiran da da dowager Mother she is not empress but she has a more powerful than king) Dan haka ko a Sokoton tana da tarin Darajojinta, ga ilimin addini da Allah ya bata, haka ya cire mata kyashi da hassada, sannan kaifi daya ce bata magana biyu, idan tana wuri ba a kawo mata wargi, asalin bagobiyar ce da ta samu damar yin rayuwa kamar kowacce matar sarki, sannan tana Tausayin Fulani Aminatu, domin tana tsakiyar makiya ne, tun kafin ta iso aka gaya mata cewa Bello ya amshi auren bafulatana kuma sai yadda tayi da shi, a tunanin ta zata samu hamshaqiyar mace abin tausayi sai ta ga yarinyar kusan sa'ar jikan ta na goma sha biyar ce, sannan tasan tasirin kiyayyar kowacce masarautar domin ita ɗaya ce bagobiyar a cikin masarautar Sokoto, dan haka ta sha wahala da mijin su da kuma kishiyoyin ta da kwarkwarorin sarki a lokacin, kai tun kafin ya zama sarki ma yana da kwarkwarorin biyar da yazo ya zama sarki sai abin ya ta'azzara har ta kai sai tayi sama da wata biyu bata saka shi a idanun ba, domin ko tace tana son ganin shi basu barinta ta isa gare shi. Idanun ta ne ya cika da kwalla. Domin tuno rayuwar ta, yana yawan saka ta kuka domin bata mori miji ba, sai rabon Yara ne idan ya tsaga toh ko da rana ne sai ya tura Jakadiya ta dauko ta, haka ya faru ne sakamakon mugun son da yake mata, da Kwarkwarah ce ba za'a tab'a damuwa ba sabida sun san ba matar sarki bace, amma matar sarki matukar sarki zai so ta tashiga uku.
"Ka koyawa kanka boye soyayyar ta, domin shine makamin da za a yake ku, ka rungume abinda suka baka." D'ago kai yayi ya kura mata ido. Sannan ya ce mata.
"Inna Marwa idan na ajiye sarautar akwai me tuhumata ne da naso mata ta" rike hannun shi Galadima yayi yana girgiza mishi kai.
Tabbas dan dan uwan ta yayi nisa, itama da haka ta samu yanci a Sokoto da yau bata yi kuka ba.
Sai dai ita mijin yayi kokarin yaki da soyayyar ta ya kuma zauna lafiya, a duk lokacin da yake tare da ita yana yawan gaya mata ya nisan ta kan shi ne domin ta zauna lafiya da sauran matan da Alummomin masarautan,. Kasancewar ta bagobiyar a cikin Masarautan fulani. Dan haka dukkan hanyar da zai nisanta shi da ita yake bi, ba wai dan baya son ta ba. Idan ta kama ya nisanta kan shi da ita har abada toh zai yi kuma zai iya domin ita da yaran ta su zama abin alfahari a cikin Masarautan, kuma izuwa yau itace mahaifiyar Sarkin da yake mulki.
Gyada kai tayi kwalla zuba mata ta ce mishi.
"Kana zaton dan ka ajiye mulki zasu fasa yakar ka ne? Kana zaton ko kayi nisa da gida zasu fasa bibiyar ka ne? Kowani motsinka suna tare da kai ita ce basu kauna a cikin Masarautan. Zuwan ta ua kuma karawa mulkin ka albarka, zuwan ta ya saka kaf nahiyar nan babu na biyun ka, daga shekarun da ka aure ta zuwa yanzu ka duba sauran yankunan da suke kewaye da kai? Ka san ko yaki babu wanda ya tunkare ka da shi? Shin kasan me yasa hil ta nime aba da ita? Domin karfin tsafin su ya kara samun daraja, sannan a kodayaushe ko wani lokaci ta haifawa sarki Arkhan da namiji, kenan Masarautan nan kowa yasan abinda yake faruwa kai ne basu bukatar da cigaba dan haka ruwan ka ka zauna da matan ruwan ka ka rabu da su amma tabbas shirin su akan Aminatu rubutacciyar al'amari ne ko ba yau ba" sannan ta juya ga galadima.
"Sarkin gida ya gaya min abinda ya faru, waye kuke zargi da sakawa a tare Ku?" Shiru tayi tana kallon galadima. Nan ya shiga mata bayani tare da abinda ya sani, sannan ya kara da cewa.
"Ina zargin Yakubu ne, domin na a an zane min shi kwanakin baya, idan ba shi ba toh ban san waye zan kama ba"
"Toh ka tabbatar yayi alaka da Kwarkwarah da aka zab'a mishi sauran a maidawa Chiroma a gaya musu ni Marwa na dawo mishi da tarkacen shi, kwarkwarah daya ta wadatar da shi. Alakar ka da Kwarkwarah ba shi zai saka Aminatu ta wanke kanta ba, sai dai idan yau ta zubda jinin haihu shine kawai zai dakatar da kome, ba naki aminatu bane kiyayyar da ake mata idan baka da lissafi kaima shiga cikin su zaka yi tashi ku bani wuri"
Daga haka ta juya kanta, dakyar ya mike tsaye kamar zai fadi, tana halkance da shi, amma ta dauke kai. Yana fita kuwa ya nemi wuri ya zauna, wani irin zafi yake ji.
"Dama abinda ya hanaka tsayawa a tsagina kenan?"
"Abubuwa dayawa sun faru amma yanzu a dakatar da wannan batun mu fuskanci gaba."
"Amma kasan ina sonta ko?"
Ya tambayi galadima.
"Na sani" idanun shi ne suka yi wani irin ja...
Wannan shine abinda ya faru, dan haka Inna Marwa tana cikin masarautan kuma ba a daina kawo mata gulmace-gulmace ba, dan ma ta toshe kunnen ta, ta kima fatattaki masu kawo mata gulmar.
Koda Innayoh ta tafi dakin bayan tare da taimakon wasu manyan bayi mata suka shiga duba yan matan sai dai cikin ikon Allah zun zabi Bingel duk yadda aka yi sai da ta fi sauran matan dan haka suka tambayi sunan ta.
"Ya sunanki?"
"Yahanasu" janta aka yi zuwa wani sashi na daban, aka shiga mata gyaran jiki, tsawon kwanaki uku ana gyara mata jiki, sannan Innayoh ta sallame sauran yan matan, ita kuma aka kai ta wurin Inna Marwa. Kallon fuskar ta yayi sannan ta ce mata.
"Ki sani ba wai zaki iya zama wata abu me daraja bane ke kamar juji ce, a duk lokacin da ya kwaso sharan shi akan ki zai watsa, bari na gaya miki ko me zaki yi ba zaki tab'a samun damar inda kike ba, ki ajiye a ranki Aminatu bata miki kome ba, idan kuma wani abu ya biyo baya, zamu saka a zartas da hukuncin bisa ga abinda kika aikata"
Shiru tayi, bata tab'a tsannan kanta ba sai yau dan haka bata iya magana ba, domin akan ta isa ga sarki Bello sai da aka gaya mata magana. Dan haka Inna Marwa ta cewa Innayoh.
"Ki sanar da Fulani Aminatu, za'a kai Bingel ga Bello tayi hakuri duk wanda ya zabi tafarkin gaskiya Allah zai bashi ikon cimma inda yake."
Gyada kai Innayoh tayi sannan ta fitar da Bingel, aka mai da ita inda suke, sannan aka ware mata bayi mata biyu, daya babba me suna Lanta da Goshi,. Aka bata su zasu taimaka mata da duk abinda take bukata, sai gefe guda kuma aka bata wata dattijuwa me suna Larai, ita kuma tana saka ido ne akan duk wani motsin ta. Wannan shine abinda ya faru.
*
Tunda Innayoh ta gaya mata cewa ai za a tura kwarkwarah sashinsa, ta shiga daki ta rufe kofar, shima da kan shi yazo amma fir taki bude mishi kofa, abin ya bashi haushi dan haka ko da ya fusata dukar kofar yayi sai da kofar ta karye. Nufarta yayi tana zaune. Durkusawa yayi a gaban ta.
"Ko duniya zata juya Miki baya ina tare dake, me yasa zaki tona min asiri domin jin dadin wasu? Me yasa zaki juya min baya domin wasu? Kin san yadda nake jin ki a raina? Kin san yadda na damu dake? Me yasa ba zaki gane ba, don Allah kar ki kuma nisanta kan ki dani, ina iya tasa rawa farin cikin, indai ke zaki rayu cikin salama...
#Mai_Dambu
[5/16, 5:31 PM] Pearl crystal: KALLABI....!
A Tsakanin Rawuna
Mai_Dambu
*EWF*
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA
Muryan shi na rawa ya rike hannun ta.
"Zai fi kyau ki min duk borin da zaki yi, kin ji ki yarda Sarki Muhammad Bello bawan ki ne ke daya." Ya rike hannun ta, idan mutum yaga yadda sarki Bello ya koma sai ya tausaya mishi, domin baki daya ya sussuce, rufe mishi kofa tayi amma ji yake kamar zuciyar shi tana ciwo. Saka hannun ta yayi a kirjin shi.
"Kin ji yadda yake bugawa, daga ranar da aka ce babu ke wallahi azim bata da amfani a jikina, kece zuciya ta. Wannan domin na rayu nake tare da ita, bayan nan ke kece dukkan min nasara ta, idan na rasa ki toh ba mamaki ba zan kuma amfanar rayuwa ta ba, don Allah ki rufa min asiri, motsin ki kawai ake bukatar kiyi iya shi zai iya hana ni sukuni. Kwarkwarah ce bata da iko, kawo kunnen ki na gaya miki dan ko dakin bana son yaji abinda xan gaya miki" share kwalla tayi ya mika mishi kunnen.
Magana yayi mata, ta d'ago kai tana kallon shi, rike hannun ta yayi tare da cewa.
"Na rantse da Allah sarki na miki alkawarin haka ko muna tare ko bamu tare"
Ya fada yana kallon yadda ta kuma narke mishi, babu wani bacin rai a fuskar ta, sai dai kishin da yake hangowa,motsa baki tayi zata mishi magana ya kai bakin shi kan nata, kallon shi tayi ido cikin ido, kashe mata ido yayi, ya shiga taune bakin kamar zai cinye ta,, a hankali ya tura hannun shi cikin rigarta, kafin ta san me yake shiri yayi sama da rigar ya wulli da ita, tun daga bakin ta yake lashe ta, wani irin yanayi ya wurgata. Abin sai ya hadu biyu, ga sarkar jinin al'ada gata Ni'imar da ake tsokano ta, kai bakin shi yayi wuyar ta, yana wani shegen lasarta ya kuma dawowa habb'arta yana lasar wurin da cizon shi. K'amk'ame shi tayi ta fashe da kuka tana faɗin.
"Baffa'm don Allah ka bari zan bata jikina"
"Minani ba zan bari ba, duk ranar da na kuma kamaki da laifin rufe min daki, sai nasan me xan Miki amshi horon ki" ya dukkufa da aikin arziki, bai kuma haukata ta ba, sai da ya tsaya akam Cibiyar ta, wani irin mika take tana kuka tare da niman ya kyale ta, amma bawan Allah nan ta shiga jifarta ta da salon shi masu mantar da mace (🤣😂 malam Bingel na jiran Zariyar wandon ka🤣😂)
Ai fa kamar zata suma wani irin rawa jikinta ya kama sai dai na shi rawan da jikin shi yake Naci kaniyar nata, wani matse cinyoyin ta yayi tare danna Zariyar shi akan tsakanin cinyarta, ya haɗe cinyoyinta ya matse yana wani irin gurnanin (🤣😂 yau sai hakuri mun sake layi dayawa ayi ta salati 😂😹🤫) zur-xur ya watsa mata ruwan shi a jikin ta, janyo matashi tayi ta rufe fuskar ta, sam taki yarda ta kalle shi, dariya yayi ta mata karshe da yaga taki kula shi kawai ya fara mata cakulkuli, babu shiri ya shiga zillo, har ta fada kirjin shi. Kwantar da kanta tayi a kirjin shi tana ajiyar zuciya. Shafa Bayan ta ya shiga yi yana rarrashinta,
"Ki gyara jikin ki kin ji ko!" Ya fada bayan ya ja mayafi ya bar dakin shima bangaren shi ya nufa yayi wanka tare da sallah da ta kubce mishi, yana murmushin jin dadi. Sai yanzu yake kara jin kaunar Yarinyar sama da koda yaushe.
Bayan sallah Isha aka shigo da Bingel bangaren shi, yana rubutu tare da saka kan shi aikin zanen Fulani Aminatu. D'ago kai yayi ya kalle ta sanye take da farar alkyabbar, sau daya ya Kalle ta bai kuma sha'awan kallon ta ba, tun fil azal Allah ya saka mishi kyamar kwarkwarori, abubuwa dayawa na faruwa da su, dan haka yaji har ya koma ga Allah ba zai tab'a ajiye ta ba, sai dai ƙaddara ta riga fata. Yana zaune ta sabule alkyabbar, sanye take da wasu irin kananun zanin saki, K'ugunta cike yake da dam da jigida, irin ta mutanen kurmi, mazaunanta zuwa kirjinta an rufe shi da mayafan, a hankali ta shiga warware su.
"Koma inda kika fito" cike da mamaki ta kalle shi. Mikewa yayi a hankali sannan ya tako gaban ta.
"Har abada ba zan taba kallon wata mace ba, dan haka bana jin kin cika macen da xan kalla idan ina bukatar mace Ni xan nimawa kaina wata wasu ba, kin zata dan mun je garin ku sai na amshe ki? Ke baki san wani abu ba, yar da take da Albarkan iyaye da a Ubangiji nake nima bake da kika yi gudun wuce Sa'a kar na kuma ganin ki a turaka ta, domin xan baki mamaki fita nace, sarkin gida kar a kuma kawo min inuwar ta ma"
"Maza fito, an gama ranka shi dade" tisa keyarta aka yi gaba, sannan ya sauke ajiyar zuciya yayi sannan ya ce a ran shi.
*Taya zata burge ni? Duk abinda ake nima a wurin mace Aminatu na dasu, tun babu kome nake taɓa su, balle kuma yanzun da suka cika kirji*
Ya fada yana murmushin jin dadi, har sai da wakilin babban birnin hada soyayya ya motsa matse shi yayi domin baya son RIGIMA irin na shi.
*
Washi gari haka labarin bai kwanta da Bingel ba ya zaga Masarautan, Inna Marwa ta mata tass, domin tasan ta gayawa Iyayen gidanta ne, su kuma suka sake labarin shi da ya fisu danyen kai yasa aka kawo ta gaban bayin Masarautan za'a zane ta.
....
"Don Allah ki tashi kiyi wani abu zane ta za ayi."
Cikin ko in kula ta ce.
"Toh Innayoh ina ruwan mu"
"Tashi muje zaki gane haka" babu shiri Innayoh ta fita da ita, daidai ana daure ta, sarkin gida yana shafawa dorinar shi mai.
Sai kuka take shi kuwa mai martaba ya bar wurin ma, yana tafiya daga nesa Innayoh ta mata alama da fuskar roko. Yana magana da galadima da yake tausar shi yaji muryan annurin zuciyar shi ta kwaso da gudu tana faɗin.
"Saurayi!!" Wani irin abu ya ji ya cika mishi kai ya tsaya cak.
"Yawwa jima! Dan dakata ai baka gama aikin ba!" Ta zare mayafin ta ta daura a K'ugunta tam, sannan ta sake murmushin. Takowa take cikin ganiyar kuruciya da yarinta, ita kanta bata san tana wani abun ba, sai dai shi ya hangota tana juye Kuruciyar ta. Dan gulma shi kan shi galadima yaki tafiya. Kamar wacce aka ingiza ta ya kwashi wani mahaukacin gudu. Ta nufe shi. Tana isa gaban shi ta fada kirjin shi, wani ajiyar zuciya ya sauke zuciyar shi tana bugawa a guje kamar wanda yayi wasan tsare.
Bakin ta ta kai kan na shi, sannan ta kyalkyale da dariya tana fadin.
"Baffa'm a yafe mata bata san dokokin Masarauta ba, shigar sojar badakare ta mishi kaji saurayi" yadda tayi maganar yasa shi dauke ta cak ya nufi bangaren shi yana cewa galadima.
"Toh Galadima ka dai ji abinda tace a yafe mata dan haka ayi yadda ta ce"
"Toh Sarkin Gida ka dai ji Fulani tace a yafe mata, Uwa Mabada mama kenan An gama Ranki shi dade Mahaifiyar Sarkin gobe" inji Galadima, dan dole aka janye zane Bingel, cike da wata irin kiyayyar Fulani Aminatu Chiroma ya bisu da idanu,babban burin shi ya mallaki Aminatu domin an gaya mishi itace kashin bayan dukkanin mulkin Bello, shi yasa yayi fatan sanadin da zai raba su, shi ya same ta, amma kullum kullum kara mannewa junan su, suke.
Ita kuwa makira wani narkewa tai a jikin shi tana wasa da rawanin shi, sai ga fadawa da sauran yan majalisar sarki sun shiga juyawa cike da kunya, kowa na cewa lallai mai martaba da Fulani basu da kunya a gaban jama'a ma!
(Ji fa sai kace akan su ake! So karku manta hawai asalin al'adar nake son watsi da shi ba, duk wanda ya ga cover din shi yasan ancient love story ne ba wai old model ne, dan haka ayi hakuri dani labarin d'aga buje dai ba zamu fasa shi ba🤣😂😹👌 sai dai mun iya takun mu ko me kuka ce?)
Yana shiga cikin bangaren shi ya dire ta, ya shiga kallon kugun ta, cire alkyabbar yayi da babban rigar shi ya watsar ya kuma cire rawanin shi.
"Don Allah maimaita min tafiyar nan" juyi tayi a gaban shi tana dariya, aikuwa ya shiga takun kamar mazaunin ta zasu sauko kasa, wani dadduma ya kai mata tare da mannata da kirjin shi yana jin wani tulin amabaliyar son kasancewa da ita, juyar da ita yayi ya shiga matse ta yana kara Haukace mata, karshe Fadar da bai je ba kenan (🤣😂😹 chaii)
Aikuwa cikin fushi Chiroma ya nufin bangaren Inna Marwa, ya gaishe ta cikin girmamawa.
"Chiroma da alamu kana ta cewa" gyara zama yayi tare da kwashe Abinda ya faru ya gaya mata. Murmushi tayi tana me ajiye Alqur'anin hannun ta.
"Hana shi hukunta yarinyar da tayi ne ko kuma akwai abinda yake kasan ranka bayan haka?" Ta tambaye shi, jikin shi da bakin shine ya fara rawa. Murmushi tayi, Inna Marwa Allah ya mata wani irin baiwa ne na kana zuwa gaban ta domin wani manufa take iya d'ago ka, daga maganar ka kawai Allah yake bata sa'ar fahimtar ka, idan kuma ta kalli fuskar ka, jikin ta yana bata wani abu na daban akan ka, shi yasa dayawan yan majalisar sarki sun ki yarda su isa wurin ta, ba karamin abu bane ta wurga musu magana a bakin su, sannan su fitar da abinda yake ran su.
"Fisabilillahi Inna Marwa, taya zai dauko bafulatana a cikin masarautan gobir, baya ji baya gani akan ta. Dan kawai ance mishi ita yar baiwa ce,.tana bunkasa mishi mulkin shi."
"Eh toh ban fahimci abinda kake kokarin fada, Imma ka min bayani yadda majiyyai na zasu tsinkaya Imma ka kwashi sawayen ka ,.kabar min bangare na"
Kamar wanda ake tsikaran shi da allura ya fara gaya mata, abun da yake ran shi, sai da ta bar shi ya gama bata labarin ta ce mishi.
"Ba Bello bane matsalar ku ita Fulanin ce baku bukatar ta, sannan kowa ya samu Fulani ba zai taba barin wanin shi ya samu ba, Chiroma ban san me zan gaya maka ba, amma ka boye ciwon da yake ranka, ba iya yau na fahimci adawar ka ba, idan ka boye yayi maka amfani idan ka cigaba da bayyana shi zaka wahala, kamata yayi ka haɗa kan su, ba wai ka raba kan su ba, na sha mamaki akan abinda ka fada wato Bello bai da ce da Aminatu ba, toh shi kenan zaka iya tafiya"
Daga haka ta nuna mishi illar hassadar da ya kasa boyewa,ta mishi hannun ka me sanda, yadda me hankali zai fahimci abinda ta gaya mishi gaskiya take fada.
A bangaren Bingel ba karamin al'amari ta tsinci kanta ba, domin bata san zata fuskanci tozarci haka ba, daga can ɓangaren Inna Marwa ta tura a kira ta, ta mata tass sannan ta tura aka kira matan Masarautar baki daya, ta ci mutuncin su baki daya har sai da suka yi fatan Allah yasa ta bar masarautan akan lokaci.
Ta ce musu.
"Kuna renon akuya da fatar kura ku ajiye a ranku matukar baku nime takunkumi ba, zata cinye duk abinda ta samu maza ku bar min bangare na."
A can bangaren Baffa'm, mantaewa suka yi da duniyar kowa suka shiga duniyar su iya su daya suka fahimci yaren su, ai kamar yadda ya saka a ran shi bayan magariba ya dawo da ita, Innayoh ta saka ta agaba da gyaran jiki wani irin gyara ake mata, sannan Inna Marwa ta sa Innayoh hanata fita, aka tura mishi Bingel aikuwa ya koro ta, abin dariya idan kuma ya nime ganin Fulani Aminatu a hana shi, wannan abin haushin kamar zai tadda fadar karshe daina zuwa zaman fada yayi....
#Mai_Dambu
[5/20, 10:31 AM] Mai_Dambu: BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI
Inna Marwa bata yarda zai iya daina zuwa fada ba, sai da aka kawo mata karan shi, kamar tayi ihu a nan ne tasa aka kira shi tayi mishi fada, tana kawo zancen Bingel ya kalle ta, sannan ta ce mata.
"Inna Marwa kyamarta nake ji, wallahi ba zan iya mu'amala da baiwa ba, kazamtar ta nake gani don Allah kar ki takura min"
Shiru tayi tana kallon shi, jinjina kai tayi sannan ta ce ya tafi.
Bata wani Jima sosai ba, ta koma sokkoto. A wannan lokacin ne wasu abubuwan marasa dadi suka fara kunno kai, tsakanin yan majalisar shi, akan na lallai sai dai ya san yadda zai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 39