Share this page
karki raba musu zumunci, ki bar su haka ko bata je ba shi zai zo ai" "Hm ya batun Hamza daga masarautan Fika?" Shiru yayi kafin ya ce mata. "Bingel ta ce a dakatar da shi, yaje a nime shi." Kikewa Maman Haima tayi zuciyar ta a tafashe. Zata d'aga murya ya ce mata. "Kin ga wuce can bana son ciwon kai" ya fada yana nuna mata hanya, fuu ta bar mishi dakin, aikuwa ya dafe kan shi domin wallahi ya rasa inda zai tsuma ran shi ya huta da fitinar bingel ya gaji wallahi kamar shima ya gudu dan ta addabi rayuwa shi. - A cikin gidan kuwa tun da Barkindo ya dawo bai kuma gigin fita ba, amma hankalin shi yana wurin Anum. Baki daya ya daina kula Bingel kamar xaya yi hauka, rarrashin duniyan nan babu wanda baya tayi ba, amma fir yaki kula. ** Zaune yake a gaban bokan wanda yake watsa abu a cikin ruwan wutan gaban shi, bude ido yayi ya kalli Yakubu. "Kana zaton cewa zaka yi dace na gamon abinda kake bukata?" Ya fada yana kara rintsa idanun shi. Kafin ya bude tarr yana kallon cikin ruwan wutan yana murmushi ya ce mishi. "Ka cire ranka babu nasara, domin ita din sai namijin duniya." "Mulkina fa?" "Cike yake da zubda jini! Ita ba zata kara maka kome ba sai zubda jini, dama ace zaka iya tankwara ne ba mamaki kayi nasara." "Taya zan gane ta ina bukatar ta domin mulkina" "Yakubu ba zaka yi nasara ba, sai dai da ace kana da d'a ne tabbas zai yi nasara" "Ka dai duba boka zan yi nasara naji haka a jikina, da wacce alama zan gane ta?" Yayi tambayar cikin kafiya da mugun naci. Zane yayi kafin ya kuma kallon shi. "Ka jima da haduwa da ita, sai dai ka cigaba da niman ta, ka aure ta idan ka same ta kazo nan sai mu san yadda zamu yi a nima maka yadda za a hana yanayin ta tasiri. Gyada kai yayi sannan ya ajiye mishi wata jakar fata me ɗauke da silalar zinari. Har ya mike zai bar bokar ya ce masa. "Akwai wani a cikin gidan ku, yana kokarin ganin ya taimaka an ture mulkin ka, ka dakatar da numfashin sa. Yana nan shi yake jan ragamar wasu abubuwan kawo kunnen ka!" Sai da ya gaya mishi wanda zai kashe. "Karka yarda ka bar wani wanda zai baka damar rasa ta, mutane dayawa suna niman shigowa a cikin su kuwa har da Tsohon sarki da ahalin shi, amma akwai mutanen da suke musu mubaya'a" Rintsa idanun yai kafin ya ce mishi. "Toh shi barkindo fa?" "Shine mutum na farko da zai ruguzaka daga sama har kasa, domin zaka taka abinda yake kokarin takawa Ita dai.. inma ka mutu Imma kayi rai tabbas xan baka wannan zoben da zai baka ikon tsorata kowa, ka cusa musu tsoron ka yadda zasu fahimci mulkin ka ne duk inda tsohon sarki yake a bazama niman shi ruwa a jallo" ** Yau bata shigo da sai yamma likis, tana shigowa ta kalli Baffa'm ta zauna ganin yana lazumi, tana nan a wurin har ya idar. "Anum lafiya?" Ya kalle ta cikin kulawa. "Lafiya kau Baffa'm, dama kawai nazo maka hira ne" ta fadi haka yana kallon kasa. "Toh madalla" ya fadi yana mata kallon Minanin shi, lokacin tana kamar ta, sai shegen barna da rashin jin magana, murmushi yayi sannan ya ce mata. "Har kin dawo kiwon kenan?" "A'a an hanani zuwa wai wani ya ce kar a kuma turani kiwo" kallon Galadima yayi da ya fito daga cikin dakin yana kuskure bakin shi, tab'e fuska yayi alamar babu ruwan shi bai san da zancen ba, zama shima yayi yana faɗin. "Kuma ba a gaya miki sunan wanda ya hana ba?" "Eh ni na hana domin ana bibiyar lamarin ta, idan ta cigaba da zuwa kiwo zasu tozarta ta" inji Sarkin gida yana shigowa daga waje. "Toh malam sai ka mana bayani yadda zamu fahimta" itama kallon shi take. "Ina ji a jikina surukar mu ce.." Ai kafin ya karasa maganar Anum tayi wuf ta bar gidan. "Amma wallahi baka da kirki, ka Kore mana ita, sai ka zauna ka mana abinda zamu ci" "Ai ni ba zan yi kome ba, kawai a dama tura a sha" tattaro hankalin shi sarki Bello yayi cikin nutsuwa ya ce mishi. "Ina jin ka sarkin gida taya ta zama surukar mu?" Gyara zama yayi sannan ya ce musu. "Jikina yana bani wasu abubuwan da ban tab'a jin su ba, ita kuma yarinyar zata iya kasancewa tafi Fulani Aminatu, matukar a cikin yaranka ba a samu wanda zai iya kasadar zama da ita ba, toh ina ganin me zai hana kai ka..." Mikewa yayi a fusace, yana me barin wurin. "Me yasa ka fadi haka?" "Tun yanzun an mishi ta'aziya, me kake tunanin xai faru? Idan har shine kadai zai iya da ita? Idan ya kasance ina cikin wadanda aka mika sakon ta'aziyar su, toh lashakka zaka taya ni ganin ya mallake ta" " Ka kara dulmiyar dani, baki daya na rude ban fahimtar me kake nufi?" Galadima ya kuma tambayar shi. "Nan da wani lokaci zaka fahimta, fatana dai Allah ya takaita mana" sun jima suna tattaunawa kafin suka yi shiru. -- A cikin masarautan kuwa, Yakubu baki daya ya haukata masarautan da niman Anum ba iya Anum ba, mutanen da yake takun saaka dasu, kiri-kiri babu abinda suka mishi yasa aka musu kisan gilla a cikin Masarautar a gaban kujeran shi, daga cikin yan Majalisar da aka kashe akwai Babban limamin masarautar, wanda shi ne farko, amma abinda ya gayawa Yakubu ya saka kowa ya kuma razana. "Ka zata zaka kuma wani wa'adi ne? Ai na jima da sanin sunan ki sarki ne a baki, ku tsummayi shigowar fusatattun zakuna! Kai Yakubu ta yaro kyau take bata karko sun turo ka, ka kashe mu ba damuwa amma ka sani kai da barci cikin salama ya kare domin sai ka gwammace mutuwa da rayuwa" Haka aka suka yi ta caka mishi takobi, sai da ya daina numfashi, farkon a tarihin da ba a tab'a samun irin wannan tashin hankali ba, ita kanta Bingel ta razana. Dan haka ta boye Barkindo a dakin ta, domin tasan zai nime shi. Ai kuwa haka ne ya faru, juyawa yayi yana kallon su. "Ku dauko min wancan lusarin bana kaunar shi bana kaunar ganin shi." Kikewa Chiroma yayi tare da cewa. "Duk wanda zaka kashe ka kashe amma ba zamu tab'a baka damar ka tab'a Yazidu ba domin mulkin shi ne kake son saka san zuciya a kai" "Ku yanke min kan shi nace" "A'a fa Yakubu! Kara fara laifin da ba zaka iya dakatarwa ba, gaskiya ya gaya maka ba zaka kashe Yazidu ba, domin kowa yasan shine sarki na gaba!" "Kun isa ne ku kama min su a kai su gidan yarin!" Haka suka kama Chiroma da Waziri Zakaria aka wuce da su. Dama daga cikin mutanen da aka kashe akwai Barden gobir, har lokacin da ya mutu yana tare da Baffa'm, kuma shi yake tura musu d wasu abubuwan na labarin da aka samu, sai Majin Gobir shi ya farga da fahimtar da sarki Bello kullun da za a kashe shi. Dan haka suka samu Babban limamin suka gaya masa, shi kuma ya saka Sarkin gida dauke Baffa'm, a yanzun dama shirin su shine su samu hadin kan yan majalisun sarki yadda su zasu musu bori a sauke ykubu sai a bawa Barkindo rikon kwarya, amma ina tare da taimakon boka aka tarfo aikin su, amma sun san ba ayi haka dan kome ba sai dan munafukan da suke cikin su, Haka aka kwashe gawarwakin su, aka mika ga ahalin su. Dan haka me kula da maganin masarautan yayi kokarin tura sakon ga sarki Bello ya san yadda zai yi kafin su cimma shi, kuma yana fatan haka. ** Bayan kwana biyu. Dakin Ammyn su ya nufa ya zauna yana kallon tana lazumi, yana wurin har ta idar sannan ya dawo gaban ta ya zauna, hannun shi ya saka a cikin Aljuhun shi ya ciro jakar fatan da tsagiyarta yake ciki ya riko hannunta ya daka mata a cikin shi. Kallon jakar tayi tana tuna ina ta san shi, a hankali ta d'aga jakar kamshin turaren bada ba zata tab'a manta ba a kundin kaddaran rayuwar ta bugi hancin ta. Lumshe idanun tayi zuciyar ta yana wani irin bugawa. Ta d'ago da hanzari ta zuba mishi ido. Bakin ta yana rawa ta ce mishi. "A ina ka samo turaren baffa'm!" Sharrr sai ga hawaye. "Lamido gaya min a ina kasamo shi? Yaba raye? Ya yake? Yana barci? Yayi aure ne? Yaran shi nawa?" A hankali ya riko ta, tare da saka kanta a kirjin shi, hawaye na zuba daga idanun shi, yana jin kukan ta kamar ana zuga mishi bulalar wuta. "Hassan Wallahi ban tab'ata raba shimfida da wani..." Rufe mata baki yayi da hannun shi na dama. "Ba yau ba na saba ganin kukan ki, ko ba kome ki bani damar wanke ki mana, ki yi shiru ki daina kukan nan " Ya fada yana share kwalla. "Yana ina?" Ta fara juyawa tana niman shi. D'aga kan shi yayi sama sakamakon kukan da yake son cin karfin shi yana tuna kalman soyayyar da Baffa'm yayi amfani da shi wurin rarrashin ta. _Ina Fatah koda zaki dawo gare ni ki dawo min Minani yar shekaru goma sha takwas da ta bar gaba na da cikina! A wancan ranar naki amincewa ne domin na baki kariya, ki tambayi Innayoh ina sonki so mara iyaka, Ina jiranki! Ban san wani irin kunya nake ji ba da na kasa zuwa gare ki! Ba wai ban san inda kike bane! A'a ina kunya had'a Idanuna da Yarinyar da take kallon cikin Idanuna, ta ce min Baffa'm wata rana zaka rabu da ni zaka nisanta kan ka dani! Ina kunyar Baggara nan wacce ta fito ruwa biyu da kabilar fulani! Ina kunyar zuciyar da ta amince da namiji irina! Ina tsoron kar na zo Yarana su tuhume ni! Ina kunyar jinsin larabawan ta kalli cikin Idanuna yace bata yafe min ba! Ina shakkar matar da zata ce min jeka Bello bana son ka! Ina dari-dari da matar da zata kalli cikin Idanuna ta gayawa Yarana bata son ganina sabida na kasance mara adalci da sassauci! Na kasance mutum me matuƙar son akan Shi! Ina kunyar kar nazo a gaban Yarana ki juya min baya! Ina son ki! Jarumin kinnan yana nan yana dakon Sarauniyar Gobir kyakyawar mace me ɗauke da kamala da nutsuwa! Nagartacciyar mace me ƙoƙarin Yarda da kowa! Ina kunyar Kawar dan dalago tace bata son gani na! Uwar Hassan da Hussaini! innar Lamido da Gidado! Ina nan kamar matashi dan shekaru ashirin da biyar ki bani damar ganin ki a matsayin Yar shekaru goma sha uku baya! Na shirya rayuwata dake_ Kifa hannun shi yayi tare da cewa... $$$$$$$$ *Rabona da nayi kuka a page tun kwarkwarah yau gani ina kuka a zanttukar Baffa'm 😭😭😭🤌🏽 domin kiyayye gaba Yau page daya gare ku ba zan iya kuka akan masoya ba!* #Mai_Dambu [6/10, 8:35 PM] Black Girl: https://www.wattpad.com/1234365059?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=w6SQiOLvH1n6bRVKIs495zuqY%2BqhQqolUkGBDXIZw%2BnC9mXb0%2B8iJP3GeakcdA1mLb4y7IeFZ3R1z%2BZjwSYm9FX%2BdTcc0iqqDELF6GJHcMaoZ3AMiQxk7pPKu1nBFZwx KALLABI..! A Tsakanin Rawuna *EWF* _INA KUKE MANTAN ALFARMAR MAMAN ZEEY ME KAYAN MATA TA ZO MUKU DA ZUMAN MATA TACECCE WANDA YA SAMU HADI NA MUSAMMAN GA KYAU GA AIKI BABU KARYA BABU ALGUS IDAN KINA SHAN JABU MAZA TUNTUBE NUMBER NAN DOMIN RABE AYA DA TSAKUWA:08130169642_ BABI NA HAMSIN DA UKU Yadda ta kuma rikice mishi, ya sashi kifa kanta yana jin babu dad'i, ita kuma shi kuma kwalla, dakyar ya shanye kukan shi. "Hassan ina yake?" Ta kuma tambayar shi cikin shashekar kuka, "Yana nan lafiya, nazo niman Alfarmar naje na gan shi ne!" D'ago kai tayi tana kallon shi da tulin hawayen da ya ke kwaranya. "A'a basu da imani zasu kashe min kai ne, ina jin tsoron zuwan ku gobir, ni daya nayi laifi ban da ku!" Ta fada bayan ta mike a rude, baki daya ta rasa inda zata saka kanta, kawai ta shiga had'a kayan ya, sai da ya rike hannun ta. "Ammyn!!!" Cikin tattausar murya ya ce mata. "Zauna ki fahimce ni" Sake rushe miahi tai da kuka, har jikin ta yana rawa, baki daya ta gama rudewa. "Zauna babu abinda zai same ni" Zama tayi cikin bin umarnin shi, ta rike hannunsa. "Tsoro nake ji" "Babu abinda za su iya min wanda Allah bai min ba, Ammyn domin kare darajar ki nake raye, idan ban wanke ki ba, meye amfani na? Ki kwantar da hankalin ki matuƙar namiji kika haifa wallahi sai na shafe tarihin wadanda zuka goge miki bacin rai. Na miki rantsuwa da Allah da ya halicce ni" Wani irin tashin hankali ne ya kuma samun matsuguni a fuskarta, ta rike shi tana me jin kamar ta mutu ta huta da bala'in da take hango mishi mara iyakar. Rike hannun shi cikin matukar tashin hankali,tana girgiza kai ta kasa magana, kai Fulani Aminatu ta shiga tashin hankali da bata tab'a shiga ba iyakar rayuwar ta, gani take kamar kashe shi za ayi, dakyar da sidin Goshi suka samu damar tayi barci lokacin da yake labartawa Innayoh abinda ya faru, kura mishi Idanu tayi Murmushi tayi sannan ta ce mishi. "Karka sake ka bar yankin nan babu saka albarkan ta, domin shine adon tafiyar ka." Gyada mata kai yayi tare da gamsuwa da shawaran da ta bashi, A cikin gidan kuwa, Fulani Bintu ne a gaban Mahaifiyar ta Fulani karama. "Umma baki daya ya sauya, Umma ban san ya zan yi da shi ba" Tsannanin Tausayin yar autar ta, ya kalle ta, sannan ta ce mata. "Zan baki shawara, ki dauka sannan zan tuntube alguboro da maganar, ki fita barkan shi na wani lokaci, idan ba shi ya nime ki ba, kar naji labarin kin tafi wurin su" "Fulani kuma zai zo?" Murmushi tayi sannan ta gyada kai, tana faɗin. "Da izinin Ubangiji zai nime ki, matukar bai ni Meke ba, toh ki hakura da shi babu so a cikin al'amarin shi" Hawaye ne ya zubo mata, tana addu'a Allah yasa ya nime ta, Allah yasa kar ya manta da ita, Allah yasa ya biyo sawun ta" "Amma me yasa ba zaki duba al'amarin Abba lawan ba? Yana son ki kuma ba zai tab'a wulakanta ki ba, ka zauna da wanda yake son ka yafi ka zauna da wanda kake so" Sunkuyar da kai tayi sannan ta sake kuka cikin muryan kuka tace mata. "Ina matukar son shi, ba zan iya hada son shi na wani ba, bana iya barci idan ban gan shi ba kiyi hakuri" ta fada tare da da barin dakin tana share hawayen ta, dawani irin tausayi take bin bayan ta, tana jin ina ma zata iya sauya mata ƙaddara da zata sauya, mata babu wanda ya kaita. Ban da Uwa babu me iya jin zata sauyawa dan ta ƙaddara kamar ta, ƙaddaran so masifa ce. ** M. Gobir "Kayi hakuri kazo kaci abinci kaji zama da yunwa zai iya illata lafiyar ka" Shiru yayi kamar baya cikin dakin sai da ta dame shi sannan ya tashi zai fita. "Me kake so?" "Anumullah!" Ya fada cikin wani irin yanayi, fuskar shi ta koma asalin kalar tausayi, idanun shi fararre sun fara yin ja, cikin wani irin yanayin da shi daya yake jin ciwon abu ya kuma kallon ta. "Ina son ta! Ina jin kaunar ta, ina jin wani mahaukacin son ta" ya fada a karo na babu adadi, sannan ya juya ya fita. Fita tayi tare da kiran mandiya, suka tafi ɗakin sirrin bingel suka yi magana sosai kafin mandiya ta bar dakin, ta dauki dakaru guda goma suka fita ta kofar bayan masarautar. Shi kuwa wurin zaman baffa'm ada can baya ya tafi ya zauna, dake wurin mallakar ahalin gidan ne sai Bingel ta hana kowa zaman wurin daga ita sai Barkindo,toh nan je ya zauna, yana kallon yadda kowa yake rayuwa daga sama, yadda ya zauna sai ya baka tausayi. Akwai abubuwan da ake boyewa a masarautan wanda ba a bukatar ya sani musamman Mahaifiyar shi, yana wurin yaga wasu manyan mutanen fadan sun wuce, kamar zai bi bayan su. Sai ya fada ya cigaba da zaman shi. -- Dayawan mutanen da suke zauren Bingel,manyan fada ne da ya gayyace su tare da shirya musu shagali, kallon su take musamman waziri da yaki sake jikin shi. "Waziri ka ci mana" A hankali ya fara cin abincin, sai da ta bari sun kusan cinye abincin kafin tace musu. "Gubar da take cikin abincin zai dauke awa uku kafin ka fara amai da gudawa, daga nan zaka cigaba da zazzaɓi ne tsawon kwana takwas,daga nan zai dauki kwana biyu kafin ya gama tsinka maka hanjin cikin ka, musamman na samo shi a wurin maguzawan asalin wadanda suke yawo a cikin daji kamar Bororoji!" "Ahhhhhh" maza suka fara kokarin yin amai murmushin keta tayi sannan ta ce musu. "Abu daya nake so sani waye yake bibiyar Gudan jinina?" Baki daya suka rude, shigowar Barkindo dakin taron ne, ya sata d'ago kai. "Inna me yasa? Wai me yasa ba zaki bar ni na huta ba? Me yasa ba zaki bar ni na sararra ba? Shi kenan idan Mutuwa ta ALKHAIRIn ne Allah ta dauki rayuwata ta na huta." Ya fada yana jin wani irin kuka. Zubewa yayi akan gwiwar shi, yana rike kirjin shi da yake mishi ciwo. "Ban rasa kome ba, amma na rasa soyayyar Uwa ta, na rasa soyayyar yarinyar da nake so! Wai duk wannan faffutukar duk kawai haihuwata da akayo a cikin Masarautan nan ne?" Ya tambaye ta da karfi yana wani irin kuka, wanda ya karya kowa a zauren zuciya. Ban da uwar shi da ranta yake kara jagulewa. "Me yasa? A da can ina raye cikin salama me yasa sai kin kara min wani bakin cikin ne? Ya yasa ba zaki bar ni ba? Me yasa ba zaki gane ina da rauni ba? Mulki ba nawa bane, a duk lokacin da na hango kujeran fadar nan ji nake kamar zaki ne a wurin don Allah kar ki cusa rayuwa ta cikin Bala'i mana" Mikewa yayi yana faɗin. "Duk wanda Allah ya bashi gata toh zaka samu sai Allah ya kusanta al'amarin shi da wani tashin hankali,ni ko sunan mulkin bana sha'awa ba ayi ni domin mulki ba ki gane mana" Duk da kuka ya ci karfin shi, haka ya juya zai fita suka yi kicibis da Mai Martaba,kallon juna suka yi kafin Barkindo ya ce masa. "Ka gayawa mutanen ka su daina bibiyata bana son mulkin bana jin ina da rabo a cikin shi, bana jin ina da wani kaso a cikin mulkin don Allah ka daina bibiyar lamarina, ni na hakura da mulkin da kake faffutukar niman karka rasa shi, amma ku sani duk ranar da me wuri yazo dole ku nade tabirman ku" Ya fada tare da barin zauren yana jin tashin hankali, wurin zaman baffa'm yaje ya zauna yana jin wani irin kuka, yana wurin har kusan dare ya raba, ita kanta ta zo ta ga yana wurin -- A can bangaren ta kuwa Anum suka samu damar daukowa, tana durkushe Bingel ta shigo a fusace. "Ku zane min ita" "A'a Fulani idan aka ce za a mata wani abu zai iya zama matsala, karki manta ke da kike niman mafita idan har aka samu matsala kuma ai babu ba zai yi aiki ba" "Ki tura ta wurin shi" Babu musu suka nuna mata hanya, tare da kai ta wurin. Yana zaune yana kuka kamar yaro karami,sai kuka yake. Ta jima tsaye a wurin, a jikin shi ta ji ana kallon shi. Juyawa yayi yaga ita ne, duk da babu haske a wurin sai hasken farin wata da Yar fitilar mai. Juyawa yayi domin yau yadda yake ji kamar zai mutu da bakin ciki, ita kanta yau ta tausaya mishi yadda yake kuka, domin cikin zuciyar shi yake kukan, a hankali ta isa wurin shi, zama tayi har lokacin bai daina kuka ba, bata kuma ce mishi ya daina ba, a hankali ta kai hannun ta,cikin na shi bata ji kome ba sai dai zufar da hannun yake, dake zuciyar ta babu shi a cikin, babu abinda ya sauya tunanin ta ko jin wani abu. Cikin tafin hannun shi ta saka na ta, a cikin shi tana me damke hannun shi cikin rarrashin sa, a hankali ya kwantar da kan shi a kadadar ta. Ya jima yana kuka kamar ba zai daina ba, ga shi dare yayi sosai. Ko'ina shiru kake ji kamar babu wani ma'aluki a waje, shi kan sa kamar kar ya rabu da ita. "Kayi hakuri!" "Ina son farin ciki! Ina son rayuwar yanci, Anum kin san me? Na kasa samu farin cikin kamar kowa,Anum kowa na da yancin amma bani da shi,Anum karshe tsoron kowa nake ji har uwar da ta haife Ni" Juya hannun shi tayi cikin murmushi ta ce mishi. "Yarda yake kawo amana idan babu yarda babu amana, kayi a hankali da mutanen da suke tare da kai ba kowa bane yake da hakorin dariya ba, amma idan kayi hakuri zaka fahimci haka amma ka daina kuka, idan ya zama kowacce bakin ciki ana ganewa a kukan ka toh ai shi kawai ya isa ya makiya su yi maka kwaf daya, batun kace ba zaka yi mulki ba bai taso ba, kana sarki me jiran gado kace baka ra'ayin mulki gashi ni kuma Basarake nake so" juyawa yayi ya kalle yana jin wani irin yanayi akan ta me mugun karfi, cikin marairaice fuska ya nufi Fuskar ta da fuskar shi. Wani irin jan numfashi tayi domin wannan shine karon farko da ta tab'a kai matsayi a irin wannan yanayin, hannun shi daya ya kai bayan ta ya kuma matso da ita jikin shi, yana sake wata malallaciyar numfashi, shi kan shi sumbatar bakinta da yake kamar jariri na niman bakin nono, haka ya gama mulmula bakin shi a saman nata, ya kyale ta cikin tsannanin kunya taki yarda ta kula shi. Dan haka da gudu ta nufi wajen masarautan. Bin bayan ta yayi shima, yana kwala mata kira, sai da ta zo bakin kofar fita taga a rufe masu kula da kofar kota kanta basu bi ba, ganin mace ce. A can masarautan kuwa zoben Sarki Yakubu ne yake sanar Mishi abin sa yake jira yana cikin masarautan, dan hakan ya shiga niman abin yana me bin lungu da sakon masarautar, tare da bin layin gidajen bayi yana niman inda yake, ga zoben sai wani irin zafi yake.mishi. -- "Mandiya ku kashe yarinyar matukar ba zata bashi gudummawar mulkin ba, bata da amfani bata da amfani a rayuwar shi, a kashe ta" "Allah ya baki nasara karki manta kashe ta ba abu me sauki bane domin suna tare da Barkindo a yanzun!" "A jika ta min shi yadda ba zai iya yin kome ba, duk wanda yake da hannu a cikin kare ta a binciko min a hankado min shi naga waye yake bata kariya bayan ina son ta zama ta Yazid. Matukar ba zata zama matar shi ba bata da amfani san haka maza shi yadda nace Matukar ban ji labarin sabo ba zan iya dauke haushina akan ki..." Ta fada tare da Lumshe idanun ta, siririn hawaye na zuba ta gefen idanun ta, bata san me yasa take son a kashe Anum ba, amma tasan ta sanadin Yarinyar kome nata da yake boye zai iya bayyana... --- *Anum kina cikin tsaka me wuya.... Ni fa yau na tashi da jin lalaci ina tunatar da ku sabon littafina me suna ZAYN MALIK 300# yana nan tafe insha Allah, ku fito ku nuna min love mutanen da ba su Whatsapp zan fara saukewa a Arewabooks on 25 this month* #Mai_Dambu [6/11, 10:14 AM] Black Girl: KALLABI..! A Tsakanin Rawuna EWF https://www.wattpad.com/1234905228?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published BABI NA HAMSIN DA HUƊU *Ina matan Alfarmar ga maman ZEEY me kayan mata tazo muku da sabon zumar mata me kyau da inganci! Ga masu bukatar zasu tuntube ta a ta wannan number... :+234 806 384 5136* Juyawa yai yana kallon ta, yana girgiza kai yana faɗin. "Yan mata sun rigida sun rufe kofar gari mu koma" bata kalle shi ba ta ce mishi. "Maza saka su bude min kofa ba zan kwana a cikin Masarautan nan ba" ta fada murya babu wasa, jin yadda muryan ta ya sauya yasa shi basu umarnin a bude karamin kofar, babu wani musu aka bude musu, a tare suka fita, suna tafiya amma babu wani magana a tsakanin su, dake tsakanin masarautar da rugar gona akwai tafiya me dan rata, sam basu damu da dare na, musamman shi Barkindo wanda magana na gaskiya Anum ke jan shi, yana mahaukaciyar sonta, irin son nan da duk abinda mutum zai maka baka tab'a ganin laifin shi balle a kai ga kaji haushin sa, so yake mata mara gundurar da hawa kai, son da yasa shi jin zai iya bijirewa

Chapter 27 of 39