Share this page
ya bata amsar, "Shi kenan Sarkin gida an gama" ta juya zuwa cikin sashin fulani, tana me shiga cikin turakar ta, ta same tana barci. Zama tayi a kasa tare da kurawa Fulani Aminatu idanu. *Idan har ya ki amincewa da Fulani fa shiga sashin Yahanasu Bingel, yana nufin bai yi na'am da cikin ba kenan? Wacce irin SO NE HAKA YAKE MATA? WACCE IRIN KAUNA SARKI BELLO YA KEWA AMINATU HAKA?* Bata da mai bata amsar tambayar ta, dan haka ta cigaba da zama tana kallon yadda take bar, har ta farka tana ganin Innayoh ta saka kukan shagwab'a. "Innayoh a saka min ruwan wanka jikina ciwo yake" "Toh fulan" fita tayi can sai gata da ruwan zafi da kuma kwababben Dilke na gyaran jiki, ta kai ruwan sannan ta zauna ta shiga shafe mata jikin ta, har ta gama sannan tafuta a dakin ta bar Fulani tayi wanka. Tana gamawa ta fito da saka wata farar rigar saki da zanin shi, ta kuwa cab'a kwalliya sosai. Ta goga turare a jikin ta sannan ta fito. "Innayoh Baffa'm ya hanani zuwa wurin Uwar Magaji" ta fada a sanyayye, "Yana da muhimmanci ki dauki abinda ya hana da daraja, ba kowacce mace bace take da darajar da kike samu, har abada wutsiyar raƙumi tayi nesa da kasa, dan haka ba kome dan Ya hana ki zuwa can ai ba wani mugun abu ya hana ba" Cikin tulin yarinta da sakalci ta ce. "Innayoh kin daina sona, kin koma bayan baffa'm" murmushi Innayoh tayi tana mika mata hadin ya'yan itacce, tana ci tana kallon Innayoh. Hana Fulani Aminatu shiga wurin Yahanasu Bingel ba karamin haifar da kananun magana yayi ba, domin har habaici sai da suka yi ta wurgawa Innayoh wai bakin ciki ne da kyashi ya hana Fulani Aminatu zuwa. Kalmar da Ajuji tayi amfani da shi wurin gayawa Innayoh magana tayi mata zafi inda tace mata. "Kina jin haushin dan yar rikon ki bata haihu ba, dan haka taki zuwa ganin Uwar Magaji, toh idan haihuwar banza ce ta dauki cikin mana ta iya ware cinyoyi amma bata iya daukar ruwa zuwa d'a ba" wani irin rawa jikin Innayoh ya dauka,domin maganar ya mata zafi. "Eh haka Allah ya ƙaddara, dake ya san haihuwa ba zata zama alkhairi a gare mu ba, shi yasa ya hana mu, ke da ya baki haihuwar sai ya baki dan taure wa ya sani ko yana bin bayin har da uwar dan dan taure bai gaji abin kunya ba" kai kai kai... Ina wutar da za a saka Innayoh, wannan maganar har gaban mai Martaba domin Ajuji ta kai karar Innayoh har fada. Kowacce ta mai da abinda ta fadawa Yar uwarta. "Ajuji wannan ba wani abin damuwa bane ai, na kasun Fulani Aminatu kika tab'a ita kuma ta tab'a naki, idan har kuka cigaba da jifar juna da kalamai marasa dadi dadi haka taya zaman lafiya zai wanzu? Kar na kuma jin haka!" Inji Waziri ya yanke hukunci. "Innayoh kiyi hakuri" Galadima ya bata hakuri tashi tayi zata fita Ajuji ta ce mata. "Tabbas sai na shayar dake mamaki" A gaban kowa ya fadi haka, murmushi Innayoh tayi sannan ta ficce abinta. "Ke dai baki da girma sai na jiki, kar naji haka ya faru" inji Chiroma, karfi da yaji suka tsawatar mata, kan Mai Martaba yana kasa, har suka gama bai d'ago kai ba. Bakin cikin da yake ciki Allah kaɗai ya sani. Har aka tashi a ranar bai fita ba, zama ya cigaba da yi ya rasa Meke mishi dad'i. Haka rayuwa ya cigaba da tafiya sarki Bello bai taka kafar shi ya shiga wurin Bingel ba, asalima mantawa yayi da ita domin Allah ya gani baki daya mantawa yake da batun cikin, a gefe guda kuwa kashe Fulani Aminatu yake da soyayyar shi yaki barin ta ta je taga uwar magaji. Tayi borin tayi mita tayi masifa tayi fushi yaki ko maganar baya so. Ranar wata Jumma'a. Bingel na zaune, a wurin shan iska da yake bayan gidan Fulani, itama Fulani ta fito zata wurin ta hango Bingel, wacce tayi shar da ita. tayi kyau ta murje har tana wani ja-ja-ja, da sallama Fulani ta shiga wurin Innayoh da yan matan bayi suna biye da ita. Da kayan ciye-ciye. Murmushi Bingel tayi ganin yadda itama Fulanin take murmushi daga hangota. Ban da soyayyar sarki Bello bata ji ta isa ta tsaya inda Aminatu take, ban da kudirin ta babu abinda ya isa kusantota da Fulani. Shinfida Kilishi harira tayi, rahi ta ajiye matashin hannunta Innayoh ta ajiye kwandon ya'yan itacce, tsayawa a kan Bingel Fulani Aminatu tayi. "Kiyi hakuri ban samu zuwa duba ki ba, ya Barkindo!" Cike da mamaki Bingel take kallon Fulani Aminatu. "Yana lafiya" ta amsa tana me jan bakin ta tayi shiru. "Kina hutawa ne?" Ta fada itama tana nufar wurin zaman ta. "Eh toh abinka da Kwarkwarah mara daraja nan ne ya dace na samu salama" kunya ce ta kama Fulani Aminatu. "Waye ya gaya miki baki da daraja? Ki bar saka haka a ranki wata rana ke fa uwar sarki ce!" "A'a wannan sai ku Ya'yan da aka haife a cikin gidan sarauta. Kune kuke da iko da daraja mu bayi ya'yan makiyaya, ai nayi kuskuren hada kai da matar sarki Yar sarki." Wannan juyayyen kalmomin Bingel yana fisgar zuciyar ta, amma sai ta dake tana cewa. "Ai ba daga nan take ba, babu wanda yafi wani a wurin Allah sai me tsoron shi." Fulani ta gaya mata. Innayoh bata so wannan musayar kalaman ba, domin abin ya d'aga mata hankali. "Hmm! Kamar da gaske tunda gashi nan kin hanani ganin Mai Martaba" wani irin duka gaban Fulani Aminatu yayi bakin ta yana rawa ta ce mata. "Toh amma ai nadan yana zuwa wurin ki, Kum." "Inji waye? Ai tsakanina da shi tun ranar da ya wulakantani" ta fashe da kuka da ya gigita Fulani Aminatu, jikin ta har rawa yake, Innayoh ta d'ago makirci ne kawai, zama Fulani Aminatu tayi a gaban Bingel tana rarrashin ta. "Ko sau daya ne ya kamata ace ya nuna min kulawa da sakamakon abinda na nasamu a gare shi..." "Da naki akwai wanda ya isa ya hukunta ni ne" mikewa Fulani Aminatu tayi zata nufi Mai Martaba, Innayoh ta rike hannunta irin rikon da ita kanta bata tab'a jin anyi mata ba, idanun Innayoh yayi jajjur. "Innayoh ku mai da ita shashin ta" Haka Innayoh ta tisa keyar ya har sashin ta, shi kuma ya tsaya Tare da kallon Bingel din yana mamakin yadda take da kwarin gwiwa. "Kar na kuma ganin ki anan, batun cikin kuwa tun muna mu biyu ki nime mishi uban shi" "Allah ya baka nasara uban shi kuma?" Ta tambaye shi cikin kuka. "Na gaya miki, tun wuri kafin kome ya dagule miki" Daga haka ya bar mata wurin, ai kuwa tsakanin shi da Fulani sai da aka artabun shi kuwa ya saka mata karfi yayi ya mata bulalar shi ne shiga jiki shine maganin ta, dan idan ta fara kokarin karkace mishi sai ya hau bulalar shi ya zane ta har sai ta bada hakuri. Bayan wata bakwai rigimar masarautan taki ci taki cinyewa, Sarki Bello yaki amsar cikin Bingel, gashi abin tausayi cikin ya girma sosai dan dole Fulani Aminatu ta saka shi duk ranar Lahadi yana shiga wurin bingel yana duba ta, wannan abin yafi kome d'aga mishi hankali domin yarinyar kwararriya ce a akan namiji, sai da ya murde ta shigar shi na karshe da bai kuma sha'awan shiga ba, domin tayo kan shi zata mishi iyayi ya murde hannun ta, baya ga cikin tafi ƙarfin ta domin rinjayar ta yaƙe. Tun daga ranar bai kuma kallon inda take ba, karshe da Fulani ta tambaye shi ya ce mata ya daina shiga domin Yahanasu Bingel ta so kishi fyade Allah ne ya dubi zuciyar shi bai da mugun nufi da ba haka ba, da tuni ta lalata musu tarbiyyar da yake da ita. Sake baki tayi tana kallon katon basamuden mijin ta da yake karkace kai yana zuba wata irin magana mara dadi. Girgiza kai tayi tana cewa. "Allah ya ganar da kai baffa'm." Dariya ta bashi yayi ta mata dariya tare da jan hancin ta, suka lula wata duniya na daban. A hankali wasu irin yanayi suka shigo rayuwar su, ba kome ya haifar da haka ba, sai yawan ganin gilwan mutum da Innayoh a cikin wasu gidan, ba ita daya ba hatta Fulani Aminatu ta gani dan haka da kanta tayi kokarin dakatar da haka, sai aka tare da Innayoh da magariba tsakanin lokacin Isha da magariba aka razanata ta hanyar saka mata abun da ya sumar da ita, aka raba ta da kayan jikin ta, aka barta tsirara. Wannan abun ya daki kowa na masarautan, Innayoh tayi kuka kamar ranta zai fita, domin tana jin tana gani aka rasa wanda yayi mata haka, an samu Dakyar wanda ya ga lokacin da abin ya faru, sannan ya ce ya san mutum daya da yayi haka domin yaji Muryan shi, amma kar a fada shi ya bada shaidan, sarki Bello yayi alkawarin haka, kuma ya cika alkawarin domin an samu hannun sankira da Sanda. Suma suka ce umarni aka basu, aka basu dan haka babu tausayi ko adalci a ran Sarki Bello ya ce a kai su cikin al'umma a tozarta su, sannan a yanke musu kan su tab'a Innayoh kamar Aminatu aka tab'a domin dukkan su wasu tsoro ne ya kama.su, dan dole aka hana kowa shiga wurin su. Wannan hukuncin da sarki Bello ya yanke ya tsorata kowa domin gani suke matukar aka kuma wani yunkuri Tabbas zai iya tawo mugama da uban kowa ba, domin Innayoh ta wuce haka a wurin shi. Bayaan wata kusaan biyu wadanda suke cikin kaddaran shi da Fulani da Innayoh, Bingel ta sauka lafiya, inda ta samu dan ta namiji, cikin dare aka buga musu kofa suka tafi ganin Yaron, cikin farin cikin Fulani ta dauke Yaron ta d'aga sama, tace. "Barka da zuwa duniya Magajin Gobir Yarima Yazidu Muhammad Bello Barkindo na farko a masarautan Gobir." hawaye ne ya sauka daga idanun ta ya sauka akan fuskar Yaron da ya bude idanun shi akan ta. Mika shi tayi ga Innayoh ta bawa Bingel kallon Fulani Aminatu Ajuji tana tana cewa. "Kuka fa yanzun kika saka kafar yin shi, kuma Yaro ba zai ci Yazidu ba." "Sunan Yaron kenan" Galadima ya fada daga bakin kofar yana bayan Mai Martaba, koda suka shiga cikin dakin, yaron aka basu amma fir sarki Bello yaki daukar Yaron. Murmushi yayi lokacin da ya ga fuskar shi. Haka suka fito, a wani irin bukace da shi, Fulani Aminatu ta rike hannun shi. Suka wuce sashin sa. Shi kan shi haka kawai yake ji kamar idan a wannan daren bai kusanci Aminatu zai iya mutuwa, tun zauren shi na farko yake ji kamar ya cinye ta..... *🙄King maker' na fadar sarki Bello kun dai ji Yan FITILAR HIKAYA MAI_DAMBU SUN DAURA AYAR TAMBAYA AKAN KU HAR KAI GALADIMA 🤔 KO DA YAKE ANCE BA AKIN TA BABBA DA NA GABA AKE GANE ZURFIN RUWA TAYIWU KUN HANGO ABINDA BAN HANGO BA, WANNAN SHAFIN NAKU NE YAN FITILAR HIKAYA TA... AYI COMMENTS NA BOOK A TATTAUNA MATSALAR RAYUWA NAGODE SA HADIN KAI DA KWARIN GWIWA DA KUKE BANI😹😂🤣* _INSHA ALLAH ZUWA DARE MAYBE IDAN NA GAMA ABINDA YAKE BANA_ #Mai_Dambu [5/22, 10:21 AM] Mai_Dambu: KALLABI...! A Tsakanin Rawuna Mai_Dambu *EWF* https://www.wattpad.com/1227758084?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published BABI NA TALATIN CIF Cikin rawan jiki da tarin zazzaɓin da ya rufe su dukkan su, suke makale da juna, sai kuka take tana jin shi, tana ganin shi amma ta kasa janye wa daga jikin shi, murdawan da maran shi yayi a karo na babu adadi ya kuma haifar mishi da sabon bukatar ta, bai tab'a mata irin wannan abin ba domin Sa'a daya zuwa biyu yake janyewa daga gare ta, amma yau sai gashi, ya kasa koda motsin rabuwa da ita, sai ma kara nanuke mata da yayi ta yi, kiran sallah farko ya sa shi mirginawa ya fadi ƙasa, yana juyi. Kusan ita kan zazzaɓi ne ya rufe ta, kamar wanda suka suma, basu farka ba sai da hasken rana ya hudo ta tsakanin tagar dakin, shi ya fara farkawa ya tsinci kansa a kasa, a hankali ya ja alkyabar shi ya shiga ban daki yayi wanka, babu kwari a jikin shi haka ya fito, sai da ya gabata da sallah asuba, yana idarwa ya nufi ban daki ya kara tara ruwa ya zo ya taimaka mata, tayi wanka kusan a zauna tayi Sallah, tana idarwa ta koma ta kwanta. Wunin ranar a dakin tayi, sai can yamma Innayoh ta kawo mata kunun tsamiya. Aikuwa tasha sosai. Kusan bata bar turakar shi ba, sai dare inda ta leka masu jegon sannan ta nufi bangaren ta. Sam Sarki Bello yaki bada hankalin shi akan jaririn da uwar shi, har ranar suna, babu wani dauki ko murna da farin ciki, asalima sai ya tattara al'amarin shi kan Aminatu, wacce basu kwanaki biyu me kyau basu yi fada ba, dan tace dole ya kula da Barkindo Yazidu shi kuwa ya ce nan duniya babu me saka shi daukar Yaron, ita kuwa ta tsiro da sakawa ana kawo mata Yaron hira, dalilin haka ya daina shiga bangaren ta, wanda Innayoh ta farga da haka ai kuwa ta ce mata. "Aminatu ki dawo hankalin ki, abinda kike aikatawa kuskure ne, kina son bawa Makiya damar da xasu cutar da alakar ku, daga yau ba za a kuma kawo mana Yarima Yazidu ba" Tura baki tayi tare da bawa bayin ta suka mai da shi. Tun daga ranar bata kuma turawa a karbo shi ba, asalima sai ta daina shiga wurin Mai Martaba, shima dake yana da wasu abubuwan da suka sha kan shi, sai ya ajiye ta a gefe yq cigaba da haka, ranar da ya samu sarari ya nufi ɓangaren ta, tana kwance kanta yana kallon sama, ya shiga ganin yadda take ƙwance yasa shi kwanciya kusa da ita, a hankali ya juyar da fuskar ta, suna kallon juna. Lumshe idanun ta tayi tana kokarin juya bayan ta, janyota yai da karfi yana hararanta, a shagwab'e ta tura mishi baki. ta fara kaukauce mishi baki daya ya kasa gane mata dan haka ya saka kan shi rarrashin ta karshe sai ma kara rikice mishi take, bai san lokacin da yayi zuciya ya tattara kayan shi ya bar mata dakin ba, dan shirme sai ta fara kuka, Innayoh tana ganin yadda ya fito ta fahimci ran shi a b'ace yake dan haka yana barin bangaren ta shiga tayi ta mata fada, haka suka cigaba da kasancewa wanda ita kan ta Fulani bata da hujjar da zata ce ga dalilin da yasa take mishi kuka idan ya nime ta, sai dai abu daya ta sani bata son ya tab'a ta, kusan kwanaki sha biyar, suna haka ranar ya gayyace ta, dakyar ta shiga turakar shi, nan ma da ya nime hakkin shi kuka ta saka mishi, yaji haushi ya nime ta da karfi, bai tab'a yarda bata son ya tab'a ta ba, sai da ya gama kome ya gan ta ta suma a kakkafe, hankalin shi yai mugun tashi dan haka ya saka mata ruwa, tana farkawa ta fashe da kuka, tana ture shi. "Wai meye na miki ne?" Ya tambaye ta cikin sigar rarrashi, amma fir taki magana, abin ya bashi haushi dan haka ya kokarin shanye bacin ran shi, ya taimaka mata tayi wanka, sannan ya dawo da ita sashin ta, domin taki kwanciya a wurin shi, babban kuskuren sarki Bello shi ne kasa hakuri ya fadawa mutane uku da ya yarda dasu a duniya, ya gaya musu halin da yake ciki, musamman da ya fahimci sun fishi sani akan mata, Galadima rarrashin sa yayi, Sarkin gida ma haka, Wazir kan dariya yayi mishi yana faɗin.. "Baffana ayi hakuri zata daina lokaci ne, idan ka duba aminatun da ba ita bace yanzu ita na da ai har cinye mata zomo muka yi, ta yanzu kuwa ta san meke cikin rayuwa ita kanta rayuwa ce bata gama sani ba" "Kyale shi zakiri'a yayi hakuri yanayi ne haka muke fama da matan mu tsofai-tsofai" inji Galadima "Allah ya baka nasara a bita a hankali, ba halin ta bane akwai abinda yake damun ta." Iya wannan hiran suka yi, bayan kwana biyu, yana kwance Kadaici ya dame shi ga kewar ta, dan haka ya tashi lokacin dare yayi fa, dan kafa ya dauke, ya nufi bangaren ta. Babu kowa a hankali ya isa cikin babban zauren ta, babu kowa daga can dakin ta ya kamar ana magana, kuma Muryan namiji ne, a hankali ya ja numfashi kirjin shi yana dukar tara tara. Bai yi kasa a gwiwa ba, ya tura kofar. Zindikin gardi ya gani a tsaye babu kome a jikin shi ya tsaya a bakin kofar Fulani Aminatu yana cewa. "Ki fito mana,so kike wancan lusarin ya shigo ya same mu ko so kike Innayoh munafika ta fito ta same ni" cak sarki Bello ya kura mishi ido, duk da dakin babu wadatar haske, bai san lokacin da ya dauki kaskon runshe ya watsa masa ba, ya kuma bishi da mugun duka, amma dake a shirye mutumin yake, girgiza yayi ya bace a hannun sarki Bello, ya bayyana a bakin kofar fita ya ware murya ya ce. "Kwartoooooo" sai da ilahirin bangarorin ya amsa, sannan ya b'ace. Kafin kace kwabo an bazama zuwa sashin Fulani Aminatu, bayi da dogarai, sun cika kofar sashin. Allah sarki ita kan tana can ban daki tana barci, a cikin ruwa bata san me duniya suke ciki ba, barci sosai take a cikin kwarmin wanka, kafin kace me dakin ta ya kama da wuta, sarki Bello yana tsaye yana kallon Ikon Allah sai da aka shiga kao dauki cikin dakin aka kashe wutar da ta fara ci, duk yadda yaso boye damuwar shi ya kasa, duka daya yayiwa kofar ban dakin ya balle, sannan ya same ta, tana ya barci cire alkyabbar shi yayi ya dauke ta, cak ya nufi bangaren shi da ita, bai iya magana ba, domin bakin shi ba zai iya fadar kome ba, itama ya raba ta da can ne domin kare darajar ta, ya kwantar da ita. Haka aka yi ta bincike har gari ya waye, a lokacin ne maganganun iri da kala suka yi ta fitowa, wanda idan aka saka maka wuka a wuya na zaka iya tantance wane ne gaskiya wanene karya ba, domin dayawan mazan dogarai sun tabbata da Fulani Aminatu tana fita cikin dare, bayan nan sun sha ganin maza suna shiga sashin ta, lokacin guda fadar Bello ta kama da wuta, inda baki daya yan Majilisar shi, suka ce mishi ya sake Aminatu. Galadima ne kawai yake bayan shi. Ita kanta Aminatu bata san Meke dabaibaye da ita ba, da yamma take kokarin fita ya kalle ta. "Da alamu abin kunyar da kika ja bai ishe ki ba, sai kin fita kin nuna musu fuskar ki, na isashiya da take bin maza da auren ta take gayyato su" Rau-rau idanun ta yayi alamar zata yi kuka. "Nayi kokarin na boye haka amma bani da iko, ashe abinda ya faru da Innayoh ba sabon abu bane, wannan wacce irin cin amana ne" hawaye ne ya zuba mata ta goge tana murmushi. Sannan ta saka kai zata fita. "Insha Allah kin fita kenan daga rayuwar bello" cak ta tsaya. Kalaman ta ne suka shiga dawo mishi. _Duk wuya duk rintsi Baffa'm karka juya min baya! Nasan akwai lokacin da haka zai faru_ Rintsa idanun shi yayi yana jin wani abu yana danne zuciyar shi. "Ki fita" ya tako yana ingijeta waje, zai kuma ta juya a fusace idanunta sun koma kore shar. Ta dakatar da shi. "Ya Isa haka! A kowacce ƙaddara akwai taƙi nasan wata rana zanen ƙaddara ta zata zo taki ya isa Bello" ta fada tana Murmushi. Wani irin tawakkali Allah ya daura mata,.me matuƙar nauyi. Dake goshinta tayi tana jin kamar wani irin abu yana yawo a jikin ta, da sauri ya bude kofar zata fita ya riko hannunta, ya fisgota kirjin shi, yana me fashewa da kuka. Sai ta tsinci kanta da shafa bayan shi. "Kuka kuma?" Ta tambaye shi tana janyewa. "Aminatu me yasa kika zabi haka?" Dariya ya bata, tq juya da sauri ta barshi durkushe. Tana futa wani irin guguwa da ta turnike masarautar baki daya ya dauka, tana isa bakin kofar ta, kafin ta bude kofar kamar wanda aka daki kofar ya balle, shiga tayi ta samu Innayoh durkushe tayi kuka har ta godewa Allah. "Innayoh" tana kiran sunan ta, ta yanki jiki ta faɗi..ita kanta Innayoh kuka take, ta dauke ta zuwa dakin ta, wannan tambarin ya fito a gefen wuyar ta. Haka tayi ta kokarin ganin ta nimo.magani, amma ina, Da wanda ya bada shaidan farko da na biyu da duk wanda ya bada shaidar haka aka yi ta samun gawarwakin su, a zube. Cikin hanzarin Galadima ya shiga cikin dakin shi yana durkushe a kasa, kuka yake kamar Yaro karami. "Ka bude idanun ka. Sharri ne fa" "Ba sharri bane gaskiya ne ai na gaya maka ta sauya, ta daina amsar gayyata ta, ta daina idan na takura sai na amshi hakkina suma take ashe tana da masu.." "A'a sai kace baka san kome ba akan masarautan nan" "A'a Galadima dara min Yahanasu Bingel da abinda ta haifa akan Aminatu da na raya mafarkina akan ta." Girgiza mishi kai Galadima yayi yana faɗin. "Kayi kuskure, Aminatu renon kace idan tabi maza laifin ka ne da baka gyara kome ba, balle Bana tunanin haka daga gare ta" Duk yadda Galadima yaso fahimtar da shi, abin ya ci tura sai da Sarkin Gida ya shigo yake gaya musu abinda yake faruwa. Suka fita a tare, a lokacin hatta gidan ya rude da tashin hankali, ko gulmar maganar kayi za a same ta, ka fadi kana aman kumfa. "Maza ka shiga ka dakatar da ita, domin abin zai iya ta'azzara ya fi haka muni"inji Galadima, ya mika mishi garin maganin da ya shiga aka zuba mata a ruwa aka watsa mata, tunda ta sauke ajiyar zuciya ta cigaba da barci, a ranar an ga tashi hankali a masarautar domin ba a tab'a samun haka ba, dan haka kowa ya kama gaban shi, haka aka yi ta tuka bala'i, ita kan tunda ta samu labari abinda ya faru ta kwanta jinya, wannan abin da ya faru babu Bingel da Ajuji sai Gambo ta zo kuma karfafawa Innayoh gwiwa, haka yasa suka samu dan nutsuwa, haka kwanaki suka yi ta tafi, yayinda Barkindo Yazidu ya cika wata uku, wanda yayi dai dai da faruwar al'amarin wata biyu da sati biyu, dan bayan sunan shi haka ya faru. A bangaren Aminatu kuwa, ta koma yau fari gobe tsumma, a hankali aka fara rade-raden ai ciwon da take na samun ciki ne, wasa wasa sai ga maganar har fada, a kunnen Sarki Bello. Tun daga kasar zuciyar shi yake jin wani al'amarin me girma akan cikin Aminatu, wani irin bugu zuciyar shi take, abu biyu yake yi farin cikin da ya danne bakin cikin shi, soyayya da kaunar Aminatu da Abin cikin ta, sai dai lokaci guda Yarima Yakubu ya wargaza farin cikin inda ya ce mishi. "A ka'ida idan mace tayi abin kunya tana matar sarki koranta ake ko a kashe ta, yau sai gashi masarautar mu ta amshi cikin Sheg....." Basu san lokacin da ya dira a gaban shi ba, sai shake shi da yayi yana faɗin. "Karka kuma sheganta min jini na...... 🤔 Toh Allah ya kyauta.... *Ina son nayi amfani da wannan damar domin tallata muku sabon labarina me suna ZAYN MALIK PAID BOOK 300# KU NUNA MIN KAUNAR TA HANYAR SUBSCRIBES DIN SHI AN FARA PAYMENT* SAI NA GANKU.... #Mai_Dambu [5/23, 11:37 AM] Mai_Dambu: https://www.wattpad.com/1228430528?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=i%2FeZ6zl503kr1KKqVKqg9L1GV2P%2BmbtAguJT6F0JpE%2BmkGWBgRFUJfuXsJ5e%2B%2BmhDBAYkUb8erKmXwvtgJQNeCbRdobA%2Br7xJKxVzcSn60WQEUQWFo%2B6%2BX4Cgp4iX8M4 KALLABI...! A Tsakanin Rawuna Mai_Dambu *EWF* 🫶🏻 ```Insha Allah ba zaku kuma jin ba dadi ba mafarin farin cikin wasu da karshen wasu zai fara ayi shagali lafiya❤‍🩹🫶🏻😍🫣``` BABI NA TALATIN DA BIYU Duk yadda Aminatu taso kin shiga cikin gidan haka Innayoh ta tisa keyarta, ai kuwa tayi ya kukan da ya sakar mata da zazzabin me zafi. Duk wani kulawa an bata, tare da mata abinda ya dace, ita kuma Fulani Babba ta nufi shashin Mai Martaba, inda ta tafi wanke kanta akan bakin da bata san da su ba, kuma ya amshi uzurin ta, sannan ya sa aka kira mishi Innayoh ya ji dalilin zuwan su, shi kan shi sai da ya jajjanta musu, sannan ya ce mata. "Kina ganin a tura mishi da sakon tana nan ne ko a bar shi?" "Allah ya baka nasara makiyan sun kewaye

Chapter 16 of 39