Share this page
shi, matuƙar aka ce za a sanar da shi zasu iya daukar wani mataki akan haka, kawai mahaifinta ya dace yasan da zuwan mu" "Toh Jeki zan duba Al'amarin" Ya salami Innayoh, tun daga ranar aka sauya musu wurin zama aka zuba musu har da Bayi, ita kuma kwarkwarah Zaitunah sarki ya mata barazanar sai ya hukuntatta, matukar irin haka ya kuma faru, dake tasan halin shi ba iya ita ba, har matan auren shi, sai suka shiga girmama al'amarin Aminatu, har ta kai ga shi da kansa ya tura sako masarautan Gombe, cikin yardan Allah. Sai ga Sarkin Gombe da kan shi, lokacin da aka bukaci Innayoh ta kai Aminatu, basu kawo cewa Mahaifin Aminatu bane, sai da suka shiga babban zauren ganawa da bakin mai Martaba. Tsoro yasa ta fara kokarin juyawa da baya, sai da Mahaifin ta ya ce mata. "Ina zaki toh" a hankali ya juyo jikin ta yana rawa, kafin ta zube a can daga nesa, tana kuka. "Na rantse da Allah ban ketare iyaka ba." Girgiza kai yayi yana faɗin. "Na san abinda na bashi, kuma bana da yakinin har hakan zai saka ki kauce hanya, Allah ya albarkaci rayuwar dake tsakanin ku, Ubangiji ya sanya mishi albarka da jin kan ki, Allah ya huci zuciyar ki, Uwar Sarkin Gobir" da sauri ta d'ago kai tana kallon shi. "Insha Allah, yadda yazo a tsakiyar takaddama ya tabbatar mana kansakalin yaki ne, sarki ne da baya buƙatar zubda jini domin samuwar shi, dan haka ki kula da duk abinda zai haramta musu sanin asalin su." Hawaye na zuba a idanun ta ta ce mishi. "Abba bana son, dalilin da xai saka a san waye shi ko ita, bana son wata ƙaddara ta mai da shi ko ita wancan kurkukun da soyayya zan rene ta ko na rene shi, ba da buri ko daukar fansa ba, don Allah Ina niman Alfarma kar a mai da min rayuwar ta ko shi koma bayan baffa'm" ta fada cikin wani irin kuka. Tana me matsawa gaban mahaifin ta, ta rike rigar shi. "Shi kenan Tako, amma ban yi miki alkawarin haka ba, zan adana haka a raina amma Gobirawa basu boye kan su, idan Ni ban bayyana su ba, tabbas jinin su na kafiya da naci, rashin tsoro da tsayawa akan ra'ayin su zai bayyana su. Dan haka dukkan abinda ya biyo baya babu abinda zan iya" ba haka ta so ba, domin bata son wani abu ya kara alakanta rayuwar abin cikin ta da Masarautan gobir, sai dai Iyayen ta da magabata sun daura dammaran nima mata adalci akan abinda aka mata, dan sun fahimci masarautan tana cikin wani irin yanayi na yakin cikin gida ne. Kwanan shi Biyu ya koma bayan ya kara tattaunawa da Sarkin borno, akan al'amarin sannan ya bar masarautar. ** *Masarautar Gobir* Kwana aka yi aka wuni, ba a gan shi ba, dan haka Sarkin gida da waziri suka bazama niman, dakyar aka samo shi a saman inda yake shan iska, a cikin mawuyacin hali, an kwana an wuni akan shi ana fama da magani. Dakyar ya fara motsa hannun shi, haka ya waziri ya zauna a jikin shi na tsawon kwanaki yana jinyar shi, sosai. Bayan ya farfaɗo ne, ya fahimci halin da yake ciki sam sai ba magana, yana me jin wani irin sanyi da kunci yana ziyarta shi, babu Fulani Aminatu babu galadima, yaso yayi kuka amma ba hali. Haka al'amarin ya cigaba da tafiya, kullum ciwon gaba yake yi, sarkin gida da Waziri ne a jikin shi, sune kawai yake ganin yayi farin ciki. Da farko yana iya fita fada, a hankali aka wayi gari, ko bakin kofar shi baya iya fita. A hankali kwanakin suka yi ta tafiya aka samu wata biyar da faruwar al'amarin, a lokacin yana lissafin cikin jikin Aminatu yana niman wata takwas ba kwanaki, a hankali ya haɗa da watanin Barkindo Yazidu, sai ya samu ranar da aka haifi Yazidu a ranar ne kaddaran shi da Aminatu ya sauya, a ranar ta dauki gudan jinin shi, a ranar ne Allah ya albarkaci tsakanin su. Yayi kukan zuci yayi na sarari yayi na boye, yana zaune a wurin da bayan ibada baya kome, sai kiran Allah, yana kuma rokon Allah ya bashi damar da zai ha Aminatu ko sau daya ne, domin ya yarda ya Amince cikin na shine, sai dai lokacin ya kure mishi.. Cikin gidan sarautar Gobir, kamar yadda suka hada kai suka kori Aminatu, sai gashi lokaci guda Bingel ta hana kowa zama a kujeran Bello, ta ce mallakar dan ta ne, koda aka fara tadda jijiyar wuya dole aka bawa Yarima yakubu rikon kwarya, dan sun tabbatar Bello ba zai kuma zama a kujern ba, dan haka shima ai rikon kwarya aka bashi, dan haka suka ga babu wanda ya dace da mulkin kamar Yarima Yakubu, a hankali zaman lafiya da kwanciyar hankalin da aka samu ya fara zama tarihi, azzalumai sun yiwa masarautar kawanya, a yanzu ake mulkin kama karya, duk wanda ya nuna rashin jin dadin shi akan mulkin sai dai a wayi gari babu labarin shi, a wannan karnin ne aka yi ta yaki ana kama bayi ana gine su a masarautan, karfin mulki ya zarta na sauran sarakunan baya, sannan iko da barazanar yasa sauran masarautun shiga hankalin ta, yayin da suka dawo da dabi'un hana sarakunar masarautar Gobir aure haka ce ya faru, sun kuma yanke alaka da masarautar, mulkin da ake da takalar rigimar yasa kowa yake masifar tsoron su, ta kai mulki da ya yi mulki, Yarima Yakubu sai da aka aura mishi mata hudu lokaci guda, sannan aka hada mishi da kwarkwarori, haka yasa shi dauke kai da yan matan waje, domin tsabar jaraba baya damuwa da kayan mace ko.munin ya afka.mata yake, A hankali shima ya fara fuskar ta, wani irin matsala sai da Uwar shi ta hana idanun ta barci aka shiga gayyatar bokaye da yan bori, a take suka fadi ana jifan shi ne a cikin masarautan. Waziri zakaria yayi aure inda ya auri yar Limamin masarautar, inda aka sha shagalin bikin har lokacin shi yake kula da Baffa'm, kuma auren yayi ne da tilastawar Baffa'm, domin kaf duniya bai da wanda yake tausayi kamar Baffa'm, shima kuma yana masifar kaunar Zakaria sabida halayyar shi na kyautatawa a gare shi. ** Borno Watanin tara da kwanakin da bazata iya kidaya su ba, durkushe take, a kan gwiwar ta, tana rike da Fulani karama, Fulani tsakiya tana shafa bayan ta, suna mata addu'a, a karon farko da Innayoh ta kasa tsayawa akan Aminatu, idan abin ya murde ta takan ce. "Innayoh ki cewa Baffa'm ya yafe min, Ya Allah gani a hannun ka, ku bani wani abu na saka a bakina bana son maganar nan" Aikuwa aka dauko wani kara aka saka mata a bakin ta, ya cika bakin ta. Sannan ta shiga juya kanta, tun safiyar jiya suke abu daya, har wayewar gari yau, ta galabaita sosai, tayi laushi kamar ba ita ba, cikin kudirar Ubangiji, da ikon shi sarkin sarakuna, alkalan Alkalai, shugaban da babu wanin shi. Mai rahama da jin kan bayin shi, ya bawa Fulani Aminatu damar daure wata biyu irin mahaukaciyar nishi, wanda take da yakinin gabobin jikin ta sai da suka kareraye, sakamakon fitar wani basadaukin jaririn da ya fadi daga kasarta, hannun daya akan kirjin shi, daya a bayan shi, idanun shi a rufe rub, yana kwance mahaifar shi bata fado ba, a hankali ta kura mishi ido, tana jin Fulani Babba wato uwargidan Mai Martaba tana faɗin. "Bai zo da rai ba ko?" "A'a Fulani a duba dai! Unguwarzoma duba shi dai" A hankali ta cire abin bakin ta, ta ce. "Lamido" hawaye na zuba daga Idanun ta, mika mata shi aka yi ta dauke shi, cikin wani irin soyayyar shi, sake murdewa maranta yayi suka amshi Lamido. Sake nishi tayi tana dukar matashin gaban ta, Allah kadiran Ala manyasha'u, sai ga wani jarumi yazo cikin abin al'ajabi da yafi na Lamido, domin mahaifar su, ta daure shi tam, sannan yana fitowa ya fara fasa musu ihu, kukan shi ne ya sa aka san labarin cewa yazo duniya. Shi kuwa Yallabai Lamido, sai a hankali aka fahimci, tsabar hakuri ne kawai amma idanun shi biyu, Innayoh ce ta fahimci haka, lokacin ta kumshi ruwa a bakin ta, ta fesa mishi, ya fashe da kuka. Daga wannan kukan ya cigaba. Mika mata dayan aka yi wato Hussain ta sake murmushi, tana cewa. "Gidado Hussain" Haka suka gyara ta, rabon Aminatu da tayi dariya tun kafin a haifi Yarima Yazidu, yau gata tana murmushi har hakoran ta, suna bayyana. Aka gyara musu wurin kwanciyar ta, tun daga ranar kula da su ya dawo hannun unguwar zoma da Innayoh, Mahaifin ta da Fulani Shatu sun zo sun ga yaran, ta tausaya mata sosai wani ikon Allah yaran nan farin fatar uwar su, kawai suka dauka amma hatta yatsun kafa da na hannu Allah ta raba gardama, na Baffa'm ne. Tun ranar da ta yi.magana da fadar sunan su, bata kuma daura idanun ta akan su da sunan nata ba, sai cikin dare idan suka farka, wani lokaci ma Lamido zata jima tana jin motsin shi ta farka, amma baya kuka. Haka aka yi yar karamar liyafa na jin kamar an yi suna, ta cigaba da kula da yaran ta. Mahaifin ta kuwa da dan uwan shi, suna zuwa lokaci zuwa lokaci.. haka Nuna Yayan ta yazo yayi mata wata biyu ya koma domin ya girma sosai, a tunanin shi Fulani Aminatu ta rabu da sarki Bello ne, dan haka zuwan da yayi bai boye mata bukatar shi ba, kallon shi tayi har ya gama maganar shi bata ce mishi cikanka ba, dan har ya bar garin bata d'aga ido ta dibee shi ba, Allah na tuba ai duk maza kallon mata take musu, akwai wani ne bayan Bellonta wanda yake cika mata Idanu da zallar soyayyar gaskiya, tasan cewa yayi haka ne domin kare rayuwar ta, amma bata san me yasa yaki amsar cikin jikin ta ba, Haka suka yi ta kula da Yaran, dan haka ta mai da hankalinta kan Yaran ta, sai dai a duk lokacin da ta tuna da Ubansu sai tayi kuka musamman Lamido da babu abinda ya bari na Baffa'm, yanayin shi yanayin Baffa'm. ** A zaune ya same ta tana wasa da ruwa, zama yayi ya mika mata hannu. "Bani na sha Aminatu" mika mishi zata yi aka buge ruwan, wasu irin mutane ne, da bakaken kaya. Zata kuma mika mishi suka buge ruwan, zata yi na uku daya cikin yaran ta ya tsaya a gaban mutane, ya hana su kifar da ruwan. Daya dan kuma yana kwance cikin jini yana mika musu hannu. "Aminatu wadannan fa" "Da shi wancan da wannan na kwancen na kane." "Waye ya mishi haka?" "Wancan mutumin" ta nuna mishi wani mutum da yake tsaye da takobin yana digar da jini hannun shi rike da wata yarinya da take ihu zata kwace daga hannun shi, ihu ya fasa tare da mikewa ya fara kokarin daukar Yaron, zai ceci rayuwar shi. Bude idanu yayi yana zufa sosai. "Duk inda Aminatu take Allah ya sauke ta lafiya wata tara da sati Uku, yau da samun cikin ta, sanda ya bada lissafin Yarima Yazidu shekara daya ba wasu kwanakin." Ya fada shi kadai wani lokaci mafarki Ishara ce, musamman wanda za ayi shi daga sulisin dare, ya fi tabbatarwa. "Ya Allah nasan kana tare da Aminatu Ubangiji ka bata kariya!.... *Anya ba zan dauki break Ba ya ci ace anan Na gama BOOk one daura asalin labarin gaskiya zan huta Mu hadu ranar Laraba sai mu daura daga ko🥰😍🤩 kwana ɗaya tal kawai xan yi na gaji ne wallahi* _ZAN YI AMFANI DA WANNAN DAMAR NA TALLATA MUKU SABON LABARI NA, ZAYN MALIK 300₦ NE_ #Mai_Dambu [5/23, 11:37 AM] Mai_Dambu: https://www.wattpad.com/1228157440?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=hQhEFKQf4nmhtboYdY8JT4pN56n17r4nnon3IlVjP9K8xJ1%2FCAxTJK5T7P87rS%2FJRxzFBKThXwulDYCxF26ltKF%2F22lIK7oBVCX40toXQ2E2kr%2FAc5PjWNaimVhs20xM KALLABI...! A Tsakanin Rawuna Mai_Dambu *EWF* BABI NA TALATIN DA DAYA *Kun yi min alkawarin Ba zaku nime kari ba🙄🤫* "Kana kara kuskuren kiran abin cikin Aminatu shege sai na zubar ma da hauran ka, wallahi" ya wurgar da shi can gefe, sannan ya cire rawanin shi da alkyabbar. "Duk wanda ya kuma aibanta abin cikin ta ya shirya sai naga bayan shi." Suna ganin fushin sa, amma akan cikin Aminatu fushin yafi na koda yaushe. "Au da ka ki amsar Yarima Yazidu shine kake tsammanin zamu amshi cikin Aminatu? Mulki kuwa yanzun ka fara domin ba gudu ba ja da baya" Ran shi ya kara B'aci ya juya yana kallon su, sannan ya fita. "Shamaki abinda kuke bai dace ba, don Allah ku daina ingiza tashin hankali haka." Inji Galadima, "Nafi'u muna gab da isowa gare ka." Inji shamaki. Cikin kamar jira yake duniya tasan da zaman shi, ai kuwa ya saka mata tashin hankali da mugun zazzaɓi ciwon yau da ban na gobe daban, gashi bata cin kome sai ruwa, haka yasa masu magani da son bin kwakwafi aka fara kawo mata dauki da jike jike, a haka aka samu wata mata ya kawo mata wani saiwa tun kafin a hada, ta cewa matar. "Kin karbo ne domin azubda cikin jikina?" "Wane mutum Allah ya baki nasara wallahi bani aka yi na kawo" "Ki mai da musu kayan su, ki je Allah yana nan" ba iya matar ba, kiri-kiri aka fara kaiwa cikin farmaki da baki da kuma jifa. Ana cikin wannan yanayin ne mutumin da ya shiga dakin Fulani Aminatu ranar ya bayyana da cewa cikin Aminatu na shine. Maganar da ta kai har fadar sarki, ga Fulani Aminatu da take tsaye jikin Innayoh, dan bata da sauran sukuni ga ciwo. "Kace cikin Fulani Aminatu naka ne?" "Eh Allah ya baka nasara, kuma Galadima Nafi'u ne ya sani na lalata alakar ku don Allah a min rai" Kurawa juna Idanu suka yi shi kan shi Galadima zufa ke zuba mishi, balle Aminatu, ga Baffa'm. Shiru fadar yayi kafin sarki Bello ya ce. "A sauke Galadima akan matsayin shi, Aminatu ba zan mata kome ba, ta bar masarautan nan ta koma Gombe, duk inda yayi mata shi kuma abokin ta a mishi bulala har ya mutu, cikin idan ta haife shi ta dawo a sauke haddin zina" "Bello!!" Ta kira sunan shi da ƙarfi. Bai saurare ta ba, yasa kai zai fita, ta janye jiki daga Innayoh. Ta kwasa da gudu ya nufe shi tana me rike hannun. "Nifa tarbiyyar ka ce, ban tab'a hada ka da kowa ba, asalima da kai na bude ido, da kai nayi wayo. Kai ka yanta ni daga Yara ka mai da ni babbar su, taya wani zai fadi wani abu akan tarbiyyar ka, har ka amsa, taya wani zai kawo soki burutsi ka amsa, Bello ba wai sai ka yarda dani ba, na yarda a tafi a haka amma karka shegenta min abinda nayi Imanin na ka ne, yar mu ce, yarda kayi fatar tazo Allah ya bamu lokacin da muke bukata" A hankali ya zare hannun ta cikin na shi. Yana mata wani irin kallo me sanyi tare da wasu ma'anoni daban daban, wani sashi na zuciyarta yana fassara mata haka, riko hannun ta yayi ya kaita har bangaren ta, duk da tafuya suke a harabar masarautan, tsayawa tayi kamar xata fadi. "Ka min magana Baffa'm" ta fusge hannunta daga na shi. Ta koma kamar zata fadi, tare ta yayi cikin zafin nama. "Kin manta da abu a jikin ki ne da kike niman faduwa" Kallon shi tayi. "Ka yarda na kane?" Ta tambaye shi, hannun shi ya kai bakin ta, hawaye na zuba daga cikin idanun shi. "Kome bai kure ba, lokaci bai kure ba, ki tafi bana son ganin ki cikin masarautan nan, ki tafi kiyi nisa" Bakin ta ya kasa furta ko tari, sai hawayen da yake wasan tsere a idanun su. "Ka ce min baka son gani na sabida abin kunyar da aka ce nayi, kace na tafi na dawo ka yanke min hukuncin zina? Ka gaya min a wani matsayi ka ajiye Ni?" Bakin shi yana rawa ya kura mata ido. Ƙasa yayi da idanun shi da yake cikin rawanin shi, sannan ya riko hannun. yana jana, tafiya nayi kamar zan fadi ya tare ni, daukata yayi har sashin ya kai ni, Innayoh tana hada kayan mu tana kuka, ajiye ni yayi sannan ya juya abin shi bai kuma bin ta kaina ba. Da dan kuzarina na hada da sauri na tafi da gudu ma rungume shi. "Baffa'm ka gaya min wani abu, don Allah ka gaya min wani abu " a fusace ya ce mata. "Ya zan yi da ke? Ya zan karbi abin cikin ki? Taya zan gayawa duniya matar da nake so tana dauke da cikin wani na" da sauri ta dawo gaban shi, tana me rufe mishi baki. "Karka shegenta min cikina. Nagode Bello zan tafi na Barka kuma nayi maka alƙawari zan haifi abin da nasan naka ne, amma ka sani ka zuba ido ka saka idanu zaka ka abinda zai saka ka daina gani" Ta juya wurin Innayoh, zata yi magana. Kawai sai yankar jiki zata fadi, Innayoh ta rike ta. Ajiyar zuciya ta sauke, tana lumshe idanun ta. "Innayoh wai da gaske cikin jikina shege ne?" Shafa kan ta tayi tana kallon waje inda Sarki Bello yana tsaye. "Kayi duk abinda zaka yi amma karka saka yawun ka akan cikin da nayi Imani na ka ne" jan kafa tayi a hankali ya bar dakin. Mai da ita Innayoh tayi ta gama hada kome, sannan ta hadarhada nasu da kayan Fulani. Aka yi ta daurawa akan manyan raƙumai guda shida. Sannan aka bata keken doki da dakarun guda hamsin, su raka. Abin tausayi, tana kallon shi a wurin shan iskar shi, ya juya mata baya. Har ta shige cikin keken, goge kwallar da yake bin fuskar ta tayi, tana shashekar kuka, tana son shi sosai amma haka zata bar shi. A hankali suka shiga barin masarautan sai lokacin ya juyo yana kallon keken yana jin wani irin nauyi da wani duhu yana rufe idanun shi, kafin ya fahimci abinda yake faruwa, ya yanki jiki ya zube a wurin, Wannan shine karshen labarin Soyayyar Sarki Bello da Fulani Aminatu... * Tafiya ce suka yi na kwana da kwanaki, kallon Innayoh Fulani tayi cikin dan sauran kuzarin ta, ta ce mata. "Wai ina zamu?" "Gombe!" Dafe cikin jikin ta tayi, sannan ta ce mata. "A'a ba zamu can ba, bq zan jawa mahaifina abin faɗa ba, su sauke mu, mu tsaya a wata Alkarya amma ban da Gombe abin kunyar yayi yawa, za a mishi dariya" Haka suka tsaya bayan sun bada umarnin dakarun su koma, ita zata su tafi, iya kayan amfanin ta suka ɗauka a cikin kayan su, sauran ta ce musu a kaiwa Sarkin gida. Sannan suka musu sallama. Haka suka yi ta tafiya ba dare ba rana, dake Allah yana tare da su, basu hadu da wani abun tsoro ba, sai da suka tsaya wani gari ne suka huta na kwanaki, kafin suka.samj ayarin fatake da zasu masarautar Elkanemi wato masarautar Borno, nan suka shiga cikin ayari, raƙumi daya suka dauka innayoh tana baya Fulani tana gaba, wani ikon Allah babu ciwo ko laulayi sai kunci, har suka isa garin Borno a lokacin. A kofar shiga garin suka tsaya aka gama tantance su, sannan suka samu damar shiga garin. Kasancewar Innayoh ta dibe wasu daga cikin kayan ta, da duniyar ta, dan haka suna shiga garin, Fulani ta bukaci su shiga cikin masarautan. " Na zata zaki so zaman cikin al'umma ne" "A'a Innayoh, abun cikina mulki da jarumta ke yawo a jinin ta, ba zan zauna a cikin mutanen gari ba, bari na kai ta inda algaita da tambura zasu tuna mata asalin ta, amma bana son ki koda wasa a fada mata waye ita" "Duk yadda kika ce haka zan yi" tsawon kwanaki suna tafi basu wani huta ba, koda suka shiga masarautar ma, babu hutu sai na sallah, gashi suna zuwa ciwon ya dawo danye, sun samu ma an karbe su a cikin masarautan.dan ma sun fada yaki ne ya saka suka baro garin su, haka yasa take aka kai su shashin bayi, A hankali rayuwa yake tafiya, rashin maganar Aminatu da kamewar ta, yasa ake mata kallon jinin sarauta yake bin jikin ta. Gashi masarautan suna da matukar kirki da adalci tare da kare hakkin wanda aka zalinta, sai dai ta bangaren su bayi ne ake samun matsala, wanda ta kai baki daya sun saka Aminatu da Innayoh a gaba, sarkin Borno me suna Sultan Muhammad Omar Elkanemi, yana da mata hudu da kwarkwarori uku, sarki ne da ya gina mulkin shi da adalci da sanin ya kamata, duk bayan wata biyar. Sannan matar shi Uwar gida,Me suna Hadizah Suna kiran ta Fulani Babba, me bi mata Rukayyah suna kiran ta Fulani karama, sai ta uku me suna Hawwa'u suna kiran ta Fulani Kulu, sai Amaryan shi wacce ba zata wuce Sa'ar Aminatu suna kiran ta Fulani Amarya,. kasancewar sarki Muhammad Omar,.Allah ya bashi yara maza kusan ashirin da wani abu, ga ya'yan kwarkwarah. Jakadiyar masarautan me suna Baabaghana, tana da kirki mace ce da bata wani dauki rayuwa da zafi ba, ita ce tayi magana da Sarkin gida wanda ya kasance mijinta, ta tsawatawa bayin. Dan dole suka kyale su. Duk wani aikin wahala Innayoh take yi, Fulani Aminatu tana daki dan bata iya sakewa da kowa, itama Innayoh abin kunya ce Fulani tayiwa wasu mutane aiki bayan itama matar sarki ce, dan haka ta dauke aikin kome, tunda suka zo basu tab'a gayawa kowa haln da suke ciki ba, shi yasa ake ganin kamar basu da daraja, ana hada dakin su da suke kwana aka shiga aka ɗauki wasu kayan kwalliyar Aminatu, yan kunne. Ran Innayoh ya ɓaci zata yi magana Fulani Aminatu tace mata. "Innayoh na rasa wanda nakewa kwalliyar sai kayan ne zan ji zafi su? Bar su rabon su ne, bana son ayi magana yanzu sai an bincike mu taya muka samu, karshe har abin ya kai gidan sarautar bana so" Haka yasa Innayoh tayi shiru, har tsawon kwanaki uku, ranar na hudu sai ga dogarai sun zo, suka sa aka fito da Aminatu, Innayoh tana can tana aiki kawai aka je aka gaya mata, kamar mahaukaciya haka ta bi bayan su, tana jin wani irin tashin hankali, ba kowa bace yasa a dauko Aminatu sai kwarkwarah sarki me suna Zaitunah, lokacin da Innayoh ta isa ta samu an d'aga bulala za a zane Aminatu, da sauri ta kare bulalar. "Ita din Yar sarki ce! MATAR Sarki Ce, Uwar sarki nan gaba Matar Sarkin Gobir ce! Ita ce Fulani Aminatu Yar Shehu Usmanu Kwaranga, matar Muhammad Bello Jatau Gobir, ƙaddara ya kawo mu nan, ba dadi ko farin cikin ba". Sake bulalar dogarin yayi, har Aminatu ta tattare jikin ta tsabar tsoro, "Kin zo kina Ihu kamar kina masarautar Gobir, a ina ta samu zinari haka!" "Kyautar daren farkonta ne da sarki Bello ya bata saboda tukwaicin daren a matsayin ta na budurwa da ya dauka kuma matar shi, Uwar ɗakina tashi, Allah ya kawo mana gimbiya lafiya" ta d'aga Fulani da take kasa, tana jin wani irin kaskanci, yafi ta tafi masarautar su da Abin kunyar da aka laka mata, Ba a san waye ya tafi ya gayawa Mai Martaba ba, sai gasu har da Yan majalisar shi, "Takawar ka lafiya, bauna saniyan sake, toran Giwa kake, an gaida me takalmin karfe kowa ka taka, ya taku.." Jikin Aminatu ne ya dauki rawa, ta rike Innayoh, tana kuka kamar anna zane ta. Dukkansu, wurin suka zube har da Aminatu da take kuka, suka mika gaisuwa. Sarkin fada ya ce. "Algoburo ya amsa, kuma yana umarta da Fulani Aminatu da Jakadiyar khairi su shiga cikin gidan sarauta, sannan yana isar da sakon kwarkwarah Zaitunah ta same shi a turaka, sarkin gida a kai Fulani Aminatu wurin Fulani Babba, ga yar su a cikin bayi wani irin sake suka yi da haka ya faru, maza ta iso ta wanke kanta, Yar shi ce, kuma matar Abokin shi marubucin soyayya kuma Jarumin sarki.... *🤔🙄 Naji haushi da ba a tsula.mata bulalar nan ba, na gaji fa idan na kai page na 40 zan ajiye... ina son nayi amfani da wannan damar domin tallata muku sabon littafina me suna ZAYN MALIK 300₦* #Mai_Dambu... [5/24, 9:46 PM] Mai_Dambu: https://www.wattpad.com/1228747221?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=viElUVTkA2QTWJZl7%2Fw1H6yfaDs5GI3psThFGZOhL4ewJ6K7hkratY0vlPthM30P0DFl6028O9dY7IuENt3syuuraMJ262evrrIuDheuYKUyaQOb7Ij0QiUgqYYLRzjt KALLABI...! A Tsakanin Rawuna Mai_Dambu *EWF* BABI NA TALATIN DA UKU. M. GOBIR Bayan shekara daya, masarautan ta zama masarautan mafi karfi a cikin nahiyoyin baki daya, domin idan aka kai da zancen mulki ne tsagoran Jarumai da yakine sai da ta mamaye manya da kananun yanki tsabar karfin mulki, ya kasance a lokacin

Chapter 17 of 39