Share this page
da yauki, sannan yana wani irin daukar idanu kamar karanmiski, sai zaren audigar da take kadi da shi, wanda idan ta cire y'ay'an audigar take zama yayi kadin zaren. A hankali ta karkade mayafin sannan ta kalli Jakadiya ta ce Mata. "Jakadiya kenan, ai idan ba aji mutuwar sarki a bakin bafade ba, ai ba za aji a bakin wawa." Tana gama fadar haka ta juya tana bin bayan Innayoh da harara, har ta kusan kulewa ta ce mata. "Mai Martaba yana niman ki" "Toh" daga haka bata kuma juyawa ga Jakadiya ba, domin matukar ta juya gare ta, zata iya magana maganar kuma da zata yi bata son ya zama kamar fidda amo ne daga danyen karfe. Tana shiga ta samu Fulani Aminatu, dauke da dan zomonta, a duniya Fulani tana masifar kaunar dan zomon ta da ta saka mishi dan dalago, wanda Hamma Buba ya bata shi kafin ya tafi sokoto karatu. Dan duk abinda ake Buba bai sani ba. "Innayoh" ta kira sunanta a wani irin shagwababben murya. Kafin ta cigaba da cewa. "Dan dalago yaki cin kome" yadda tai maganar gwanin ban sha'awa ce, domin irin Yaran nan ne da matukar suka samu gata da kulawa za ayi tabararrun yara ne masu cike da hutu. "Toh ranki shi dade, ya zanyi da dan dalago tunda yaki cin kome, ba mamaki azumi yake?" Innayoh ta fada mata haka, d'ago kai tayi tana kallon Innayoh kafin ta sunkuyar da kanta ta ce. "Innayoh!" "Na'am ranki shi dade, kiyi hakuri mai martaba yana kirana, idan na dawo xan saka dan dalago ya ci abinci ko kuma yau na saka Sarkin gida ya yanka mana dan kai da kunnuwa" "A'a Innayo kar ya yanka min abuna, zai tashi" ta fada kamar zata yi kuka, fita Innayoh tayi da sauri ta nufi babban shashi, da sallama ta shiga tana me zubewa akan gwiwar ta. "Allah ya baka nasara, Allah ya baka lafiya! Allah ya tsare ka da tsarin shi Uban Aminatu Uban Sakina." Murmushi mai Martaba yayi, Sarkin Fada yana cewa. "Mai Martaba ya amsa Jakadiyar Alkhairi, Mai martaba ya kuma amsawa Uwa ga Fulani Aminatu" Jibril ne ya gaya Zama wato Babayo, ya fara magana cikin dattako. "Innayoh, Mutanen Aminatu sun iso,za a daura auren Ranar Juma'a, gobe kuma bamu sani ba ko zaku yi wani abin da ya shafi al'ada irin taku ta mata. Akwai sako daga masarautan elkaname wato masarautar borno na turare. Anan cikin gida kuma Balkisu ta gaya min wai ana wanka da madara da wasu al'adu, gobe insha Allah zata zo tare da Fulani Shatu zaku tsaya akan al'amarin Aminatu." "Insha Allah zan tsayar da hankali na da nutsuwa ta akan kome ba Fulani Aminatu" ta fada kanta a sunkuye. Gyara zama yayi tare da cewa. "Ban sani ba ko akwai yan dabarbarunku na mata, ki samu Fulani Shatu zata miki karin bayani" "Inshallah zan same ta Yarimar gambawa" jinjina kai yayi,sannan suka sallame ta, bata koma shashin su ba, sai ta wuce cikin gida anan ta samu ana ta aiki kamar yau ne bikin. Saukewa da daurawa na manyan tukwane. Jakadiya ta tsaya akan kome kamar me, wuce su tai sabida yadda bayi suke kaunarta duk inda ta wuce mika mata gaisuwa ake. Har ta isa shashin Fulani Shatu, tun daga bakin kofar tayi karo da Kilishi. Cikin girmama ta zube tana gaishe ta. "Rike gaisuwarki Innayoh, ai yanzu tsakanina da ku sai Alkhairin tunda Naji mai Martaba yar lelen shi a takaba zata kere" Murmushi Innayoh tayi bata ce kome ba, daga can dakin Fulani Shatu ta ce. Hmm Kilishi kenan, dan tsakon da uwar shi ta kasa ai Allah ke ci da abin shi, ai Aminatu ta zama kainuwa. Idan ana faɗin mai rabon ganin badi toh ko da jinjibi Aminatu ta ketare iyakar kowa" Dariya Kilishi tayi sannan ta ce. "Zuciyar mutum birnin sa, ai ba sabon abu bane carar zakara da tsakiyar rana, sai dai abid'a Sa'a da tagomashin alkhairi." "Sa kai yafi bauta ciwo, wani da barci wani da munshari. Toh bari mu ga waye me sa'a a tafiyar da babu guziri" inji Fulani Shatu. "Ina niman tsari ga kukan Jaki, ai a nan nake da iko a can kuwa zaman takaba ya isa haka" tana fadar haka ta juya zata bar wurin. Fulani Aminatu ta ce. "Da alamu dai tsayuwa bata karewa me shirin gyaran wata ba, bari mu jira muji ra bakin ki" a fusace ta juya tana kallon Fulani Shatu, kafin tayi kwafa. Kallon Innayoh Fulani Shatu tayi sannan ta ce mata. "Ki dauka naji dadi da mai Martaba ya amshi bukata na, na barin ki a wurin Aminatu. Domin ba zata yi maraicin Uwa ba, ke din kamar wata Alkaryar ce a gare ta. Ki nuna mata yadda ake magana da yadda ake mu'amala da kowa. Ƙarki sake ta zama matattarar sharan kowa ki nuna mata babu Maraya sai rago, ki tsawatar mata, ki nuna mata kuskuren abu. Yarinya ce karki ce zaki barta tayi wasa kamar yadda take so, nan da shekara daya ba mamaki ta fara neman zama mace, domin idan ta samu kulawa kashin girma ne da ita. Ƙarki manta mareniya ce, Gwargwadon abinda kika bata gwargwadon yadda zata kula da kanta da ahalinta. Masarautan da zata shiga babban masarauta ce me ɗauke da manyan alamura ban sani ba ko zata iya dauka bazata iya dauka ba, amma na had'aki da Allah ki nusar da ita abinda ya da da domin da shi zamu yi alfaharin mu basu Y'a. Ƙarki sake abin kunya ya dawo Masarautan nan domin zai fi kyau a ci mu da yaki sama da a wayi gari masarautar mu tana fuskarta barazana da tsangwama sabida kuskuren wasu mun." Mika mata kayan tayi tana gaya mata yadda zata yi amfani da shi, da ku taimakawa Aminatu. Sannan ta ce mata. "Akwai baki a cikin gidan nan ba mamaki zasu iya zuwa domin neman ganin Aminatu wannan hurumin ki ne a ganta yadda ya dace hurimin ku ne ki barta yadda zasu tafi da kowa, amma ki sani muna da kyakkyawan yakinin cewa ke mutum ce guda ba bari ba, Aminatu tana hannun Allah tana hannun ki duk abinda ya dawo ke ce me mafi girman laifi." Gyada kai Innayoh tayi, a yau wani nauyin ne ua kuma hawa kanta sama da koda yaushe, kuma a tsarin sarakuna babu abinda suke gudu kamar abin kunya basu kaunar su ji an shi a cikin masarautan su. Ga kuma Aminatu da kowa yasan yadda ta taso a cikin matsue da tsangwama ya isa ya karya zuciyar Innayoh. Haka tayi ta godiya sannan ta fita daga shashin ta nufi nasu, koda ta isa shigar da Aminatu kewaye tayi ta ajiye ta tana faɗin. "Kiyi shiru bari na Miki wanka" ta fada a hankali, fita tayi ta haɗa ruwan zafi sannan ta kawo madaran turare da Kwababben sabulu da lalle ta shiga wanke Aminatu da shi, tana gurje mata jiki. Fulani Aminatu fara ce kyakyawar gaske bata dauko kalar fatar mahaifiyar ta ba, sai ta dauko na Baban ta, sannan yanayin kyanta da jikinta na Mahaifiyar ce. Haka yayi saka mutanen gidan tsanarta domin itama Uwarta sabida kyanta ya kara rura wutar kishinta, a wurin Kilishi da sauran matan, sai da ta mata wanka sosai sannan ta fito da ita zuwa dakin su, ta shirya ya tsaf kafin ta shafe mata jiki da turare. Bata gama kimtsa ta ba, aka musu sallama daga bakin kofar shashin su.... __________________________________ *Ayi hakuri ban gama ba idan na gama zaku ji ni insha Allah a kai kai... Nagode sosai da jirana da kuke* #Mai_Dambu [3/28, 11:48 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: ƘALLABI...! A Tsakanin Rawuna Na Mai_Dambu EWF ** https://www.wattpad.com/1204063012?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published Wannan pagen gaisuwar taki ce Momyn noor Nagode kwarai da gaske 😍 A dan rude suka kalli kofar dakin, babban mayafi ta rufawa Fulani Aminatu. Jakadiya Jebu ce da wasu manyan bayi mata suka shigo cikin dakin, dauke da manyan manyan tasa na damamiyar lalle da yaji turare. Kallon su Innayoh tayi kafin ta sake murmushi ta ce musu. "Daga ina haka?" Wani irin kallo Jakadiyar tayi mata sannan ta ce mata. "Ana babbakun giwa wake na zomo, Malama bamu hanya mu wuce, Fulani Aminatu zo ki cire kayan ki za a miki wanka da.." Bata kai aya ba Innayoh ta ce mata. "Haba ai ko min saurain unguwar zoma ta jira haihu ko? Ki mai da shi an rigada an gama bamu bukatar na kowa sai na Allah" dariya takaici Jakadiya tayi kafin ta ce mata. "Kina wasa da ni ko?" "Jebu ke kudi tara ta ce da zan yi wasa da ke? Ko ke Kanwar kakata ta ce da zan dara dake? Ga hanya nan. Kika sake wani abu ya same ta toh wallahi da baikon Sarkin Gobir akan ta ki jinjina girman rundunar mayakan su mana" murmushi tai sannan ta koma gefe ta tsaya. "Me furcin ki yake nufi?" Inji Jakadiya Jebu, murmushi Innayoh tayi sannan ta nuna mata hanya. "Kowa ya ci tuwo dani hmm miya yasha. Ni jakar kaza ce sai na shiga sauran kajin suke shi Innayoh inda rai da rabo zaki biya bashin da kika ci" inji Jakadiya, Dariya Innayoh tayi sannan ta ce mata. "Haba? Gaske toh ai kafin ayi ɗaran akayi kwanɗi, dan haka ki ajiye a hannun ki wata rana ba mamaki Masha ruwa magirbi" a fusace suka fita da kayan. Murmushi Innayoh tayi sannan ta cigaba da shirya Fulani Aminatu.. ** Masarautar Gobir. Ana cikin fadanci sunkuyar da kai Shamaki yayi sannan ya ce. "Allah ya baka nasara, ya kuma taimaka dirken gobir" jinjina kai Sarki Bello yayi yana sauraron Shamaki dan yasan akwai magana a bakin shi. "Sarki ya amsawa shamaki" inji Sarkin Fada, cikin wani irin shakka da abinda zai fito bakin shi Shamaki ya ce. "Allah ya huci zuciyar Barden Gobir" "Sarki ya Amsawa Shamaki ya fadi abinda yake bakin shi" Sarkin Fada ya kuma faɗa, ganin Shamaki na gumi yasa Sarki Bello kara jinjina abinda yake son fada ba karamin abu ba ne. Caraf Sarkin Zagi ya fara magana. "Allah ya baka nasara da nisan kwana, Shamaki ya kasa magana ai abinda yake son fada ba kome bane yaji rad'e rad'en da yake yawo a cikin masarautar nan ne akan Sarkin Gombe zai baka auren Yar shi ne dan ya fidda fulanin da suke cikin masarautan nan" ya fada yana muxurai. Dama shi sarkin Zagi an tanade shi domin sake kowacce irin magana da tayiwa kowa nauyi toh shi ko a gaban waye zai fade ta sai dai idan Sarkin ba adali bane yasaka a zage sarkin Zagi. Shiru fadar yayi kowa yana jiran aji me Sarki Bello zai ce. Har ya mike ya zai bar fadar aka shiga cewa. "Gyara kintsi mai martaba zai tashi" a hankali ya mike ya bar fadar, bin bayan shi da ido Shamaki yayi yana sauke ajiyar zuciya, domin abin da bai zata bane. Kallon Sarkin Zagi yayi tare da mai da hankalin shi kan kujerar da Sarki Bello ya mike. "Barka da arziki" Chiroma ya fadawa Shamaki, girgiza kai yayi. "Kana tsammani da Iro ne tuni ba a sauke min rawani na ba" murmushi yayi shima ya bar fadar yana dariyar Shamaki. Haka dayawan dattawan fadar suke mishi barka da arziki, domin kuwa ta tsallake rijiya da baya. -- A can turakar Sarki Bello, zama tayi yana cire kayan shi, Sarkin gida yana bakin kofar shiga. A yau yana jin tsohuwar al'adar shi tana kuma yawo a ranshi. Gyaran murya yayi Sarkin gida ya shigo tare da zubewa kasa. "Tashi bana son kana min haka." Tashi yayi ya zauna yana murmushi. "Allah ya baka nasara." Kallon juna suka yi kuma suka sake murmushi lokaci guda. "Ina son shiga dawa" ya fada yana kishingida, a saman gadon shi. Gyara zama sarkin gida yayi yana faɗin. " Ba dai da rana nan ba? Wani ya bata maka rai ne?" Yayi mishi tambaya biyu lokaci guda, sai kuma ya gyara zama sannan ya cigaba da ce mishi. "Tsohuwar al'adar ka ko? Amma me zai hana kayi rubutu, ko kuma kayi barci yadda suka zama al'adar ka" Murmushi yayi yana faɗin, "Maza a shirya min baka" mikewa Sarkin gida yayi ya fara kokarin fita. "Karka manta har da kai a tafiyar" juyawa yayi cikin girmamawa ya gyada kai. Wato Sarki Bello yana da wasu al'adu guda uku, da kowa a cikin Masarautar yake kokarin kiyayye shi. Al'adar shi ta farko ita ce farauta, duk wani fatar dabba daji da aka kawa da ita a cikin masarautan Sarki Bello ya kamo ta, kuma shi daya, tun yana Yaro yake fita dawa. Al'ada ta biyu ba kome bane facce rubutu, Sarki Bello ya kasance hazikin marubuci da yayi shura a nahiyar da babu irin shi, idan wannan dabi'ar ta motsa mishi wanda jama'ar masarautar suke mishi lakabi da al'adun, toh kafin ya zama Sarkin rikon kwarya yana iya zama yayi kwanaki yana rubutu ko kukan tsuntsayen ba a son su gifta ta inda yake sabida yana bawa ƙwaƙwalwar shi damar nazari da rubutu, kuma yana rubutun ne da ajami. Sai al'ada ta uku, duk ranar Laraba baya zuwa fada ba dan kome ba sai yana ware wannan kwana ɗaya yayi barci da wasu abubuwan da suka shafi rayuwar shi, Allah ya zubawa Sarki Bello fasahar magana domin matukar zai bude baki yayi magana Insha Allah sai ya sauke hankalin mutane, wannan halin na shi yasa dayawa talakawa suka yi na'am da shi a matsayin sarkin rikon kwarya. Yan mata dayawa suna kaunar Sarki Bello, tun kafin ya zama sarki Ubangiji ya saka mishi farin jinin yan mata, dan ma idan zai shiga cikin gari ko wani wurin yana yawan rufe fuska shi da rawani, sabida kambun idanu. Shi da Sarkin Gida Aminai ne na kud da kud, tare suke samartakar su. Wanda sunan shi Jafar, duk da wannan yanayin Sarki Bello bai tab'a zuwa yaki ba, domin yasha fada shi matukar zai samu damar da kowa yake samu toh shi ba zai yi yaki ba, yakan fada cewa. “Matukar takobi ba zata sauya al'umma ba toh tabbas alkalami zata iya sauya su” wannan maganar ta isa har kunnen mahaifin su tun yana raye, yayi baƙin ciki sosai da ya haifi dan da bai damu da yaki ko zubda jini ba. Koda mahaifin su ya kira shi a irin baiwar da Allah yayi mishi yayiwa mahaifin su magana irin ta hankali sarki Jatau ya kwana da maganar Bello toh ya za ayi su yaki kamar a jinin su yake gudan jinin su duk digon barandami ne. Yaki da nasara suka sani babu ruwan su akan kome zasu yi yaki. Lokacin da Sarki Jatau ya tashi yaki, aka kashe shi kafin ya mutu sai da ya tuna da kalaman Bello. “Baba karka manta yakin da za aka tafi bai zama dole ka dawo ba, idan kayi hakuri kuka janye yakin Alummomin da suke iyaka da masarautar mu zasu kwana cikin salama. Idan ka duba yakin nan bai sama dole ayi nasara ba ka duba lamarina" sai da ya gayawa Sarkin yaki abinda Bello ya gaya mishi. Haka lokacin da Ibrahim zai tafi sai da ya Bello ya nusar da shi illar yake yaƙen da suke amma ina su din wasu irin halitta ne masu matukar taurin kai da taurin zuciya, kuma duk abinda suka daka a gaba sai sun same shi. Wannan kenan a cikin al'adar Sarki Bello, Shiryawa yayi cikin kayan farauta, sannan ya dauki mayafi ya rufa, daidai shashin sa bayi ne mata da kunyagi suka taru, suna gud'a daidai fitowar shi, gud'a suke har ya fito ya haura saman doki, Sarkin gida ya kama dokin shi ya fara ja, amshi linzamin yayi ya kad'a kan dokin shima da sauri Sarkin gida ya haura na shi suka fita da gudu. Da sauri sarkin gida ya cimma shi. Sannan ya mika mishi jimammiyar fatar barewa. Wanda aka yi rubutu a ajami a cikin shi. *Ka gaya mishi ya kula* Kumshe Idanu yayi masu wani irin sheki kamar an diga musu mai a cikin su, ya kuma zaburar dokin shi suka nausa dawa. Tun daga nesa yake shakar kamshin ana bin su, dan haka ya kalli sarkin gida, yayi mishi alamar su kara gudu, haka suka kara gudu sosai wanda har suka b'acewa masu bibiyar su, ta wannan ɓangaren gare abokai guda biyu sun yi zarra domin sun iya sukwa akan dawakai. Bayan sun shiga cikin dajin, suka daure dawakan su a kasar wata bushiyar loko, suka shiga cikin dajin sai da ya daure jejen sosai yadda babu wanda ya isa ya shiga musu. Tafiya suke amma babu wanda yayiwa dan uwan sa magana sai da suka isa gaban wata korama, wacce take bawa rafin masarautan ruwa. "Allah ya baka nasara akwai abinda yake damun ka" murmushi yayi sannan ya kalli gaban su inda wata gada take shan ruwa. "Kaga gada" sarkin gida ya kuma Magana, saka hannu yayi a bakin shi, har tasha ruwa zata wuce sai kuma ta kalle, dan haka ta rab'a gefen su zata wuce. "Baka yi..." Dake hannun shi Sarki Bello yayi. Shiru yayi har ta wuce juyawa yayi ya ga ta b'ace. "Ba gadar da kasaba gani ba bace." Kallon shi yayi kafin ya ce mishi. "Kamar ya? Ban gane ba?" "Ita din yar aike ce, ta riga mu shigowa dajin rufe mata kofar da muka yi kasa ba zata iya isa waje har ta bada labari ba!" Inji Sarki Bello, " Na razana!" Inji Sarkin gida,haka suka ci-gaba da farauta, har suka isa wani kurmi. "Ranka ya dade ba a shigowa nan domin akwai wata zakanyar da take farautar." Bai kai aya ba suka ji gurnanin zakin, kallon Sarkin gida yayi. A hankali ya zaro wani guru ( am so sorry da wasu abubuwan da zaku ji ko zaku yi karo da shi labarin it's was about 200 yrs ago ne wato kamar a ce ancient ko? Toh akwai gurru akwai laya akwai baka, akwai maita akwai kambun idanu, akwai baiwa irin ta da kamar a ce supernatural ban san yadda zan muku bayani ba amma akwai tsohuwar al'adar can da jimawa ayi hakuri da abinda xa a gani kafin musulunci ta shiga cikin al'umma ne labarin amma zamu kiyayye abinda zai tab'a kimar al'adun Hausawa da ita kanta hausar Nagode) Sarakuna da Yaran su a wannan lokacin, suna shirya kan su ne musamman Gobirawa wanda kaf tarihi an san su da zallar jarumta da iya yaki, yana daukar gurrun ta saka a cikin Aljuhun rigar sarkin gida,. Cikin wani irin zafin nama, ya falla da gudu aikuwa zakanyar tana najin haka ta fito da gudu ta rufa mishi, sai da yayi gudun fitar hankali suna ratsa kwazazxabai, ya samu damar zaro kibiyar shi. Kafin ta cimma shi ya zabga mata harbin da ya ratsa cinyar ta ya maka ta sa kasa, bata iya tashi ba komawa tayi ta kwanta, zuwa yayi kanta ya tsaya, sannan ya ciro takunkumi ya daure ta da shi,. Sai lokacin ya lura da ashe namiji ne. Shafa gurrun sa yayi tare da dafata, sai gashi a wurin da ya ajiye Sarkin gida. "An gama farautar yau! Taya kasan da zakanyar?" Sarkin gida ya tambaye shi. "Amma ranka shi dade kaji dalilin da yasa Sarkin Gombe baka Yar shi!" Da wutsiyar ido ya kalli sarkin gida, sannan ya saka hannu a bakin shi yana girgiza kai. "A bakin mutane!" ** Masarautan Gombe. Shiru Kilishi tayi tana kallon Jakadiya Jebu, kafin ta ce mata. "A nimo min amintattun bayin masarautan gobir, su zasu min wannan aikin" "An gama uwa mabada mama koda uba nai sarki ne" inji Jakadiya, da sauri ta fita ta nime wasu bayin biyu suka tafi har inda aka saukar da baki mata aka tawo da wasu mata biyu. Suka isa dakin Kilishi. A yau Alhamis aka saka Fulani Aminatu a lalle, cikin wani kyakkyawan shiga ta jajjayen karanmiski, wanda ya fidda hakikanin kyanta da kankantar shekarunta. Dake Fulani suma suna da al'adun aure, an yi mata babu iyaka. Washi gari juma'a bayan sallah asuba aka daura auren Fulani Aminatu da Muhammad Bello Sarkin Gobir, inda aka bada sadaki mafi girma da daraja... _________________________________ *Hi ya kuke! Alhamdulillahi na gama rabin aikina Insha Allah zaku na jina duk bayan kwana ɗaya! Yau nayi Insha Allah dai friday ku amshi wannan yanayin da farin ciki 😍🔥 ko ya haduwar Fulani da Sarki zai kasance 😍 Nagode sosai keep yourself in this journey ba zaku yi danasanin karantawa ba gaba kadan zaku fi kowa bukatar shi ma kamar yadda muka tafi a Bororoji 🔥* #Mai_Dambu [3/28, 11:48 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: https://youtu.be/0_JKoaXCVOc ƘALLABI...! A tsakanin Rawuna Na Mai_Dambu EWF ** *Godiya da fatan alkhairi son so daga Mai Daraja😍🔥* Barka da Juma'a# Masarautar Gobir. Mai Martaba Sarki Bello, yana tsaye a saman masarautan, wurin an ware shi ne domin shan iskar sarki da iyalin shi ko kuma baiwar da ya yantatta da zama sad'akar shi. Wurin kamar tsarin gidan sama ne amma ba gidan sama bane anyi yar rumfa me ɗauke da wasu kyawawan mayafai, wanda ya kara kawata wurin. Asalin kasar wurin an shimfida mishi wasu irin kilisai tare da wasu irin dardumar yar gata. Sannan an saka wasu matasai tare da wasu abubuwan kamar katifa da ya sha adon sarakunan kasar Hausa. Sarki Bello zaune cikin wani irin nishadi da nutsuwa, yana kallon tafin hannun shi. Sanye yake da shigar sarakunar dake ranar yau ya kasance juma'a. Murmushi yayi yana kallon tsuntsayen hasbiya da suke dan dandamalin da aka jera wasu kyawawan tukwanen shuka da furanni masu kamshi me dad'i. A lissafin da aka yi dangane da daurin auren shi yau aka daura, daddin daddawa yanayin Nahiyar ya tabbatar da haka, duk da basu samu labarin daga can ba, dan tafiya ce ta tsawon kwanaki kafin a iso ga raƙumi kenan, ga hangarman doki zai iya kwashe satittka kafin ya iso masarautar. A hankali ya cire rawanin kansa yana kara sauraron tamburan da ake bugawa a masarautan baki ɗaya. Uwa Uba ga tashin algaitu da kakaki, haka kawai yake jin tsigar jikin shi yana mikewa wanda ya haifar da tashin gargasar jikin shi. A hankali ya mike yana me isa yar dandamalin yana kallon yadda ake shiga da fita a cikin harabar masarautan. Tsintar kan shi yayi da nad'e hannu a kirjin shi yana jin wani irin daidaiton nutsuwa na shigar shi. Yana jin wani irin kemawa da kamala na shigar shi na asalin igiyar aure da ya hau kan shi. A hankali ya juya cikin natsuwa ya zura kafar shi a saman kyakyawar takalmin fatar da yake kofar mashigar wurin shan iskar. Juyawa yayi ya hango rawanin shi, murmushi ya sake sannan ya koma ya dauki rawanin ya daura akan shi, yana me juyawa a sanyayye cikin taku irin na asalin sadaukan maza, irin mazajen da suka san me ake kira da jarumta. Wanda galibi basu damu da nunawa duniya su din wasu bane , sai dai aikin su ya nuna haka. Tunda ya fara saukowa Sarkin gida ya tare shi da bayanai. "A bisa yakini da lissafi ana tabbatar da an daura auren mai martaba da Fulani Aminatu, sannan ana saka ran nan da makwani biyu sun iso cikin birnin nan. Sarakunan da suke karkashin jagorancin masarautan nan sun kawo maka ziyara. Akwai kyakkyawar liyafar da aka shirya domin tayaka murna. Sannan manyan manyan Fadar ka sun baka hutun wata guda domin amarci." Ban san yadda zan muku bayanin irin yanayin da mai martaba sarki Bello yake ciki ba amma yana cikin yanayin nan ne da Bature ke kiran shi(romantic moment) shi kan shi murmushin da bai san yanayi ba yake sakewa. Idan da zaka kalli kwayar idanun shi zaka fahimci yana cikin wata mahaukaciyar yanayi ne me matukar daukar hankali. Sai da suka yi tafiya me tsawo har zuwa shashin sa sannan ya tsaya cak yana kallon

Chapter 3 of 39