Share this page
shiga masarautan, kai tsaye aka wuce da ita dakin BARKINDO, anan aka shiga cire mata kayan ta, aikuwa suka shiga dambe kamar zasu d'aga dakin. Sun yi nasarar cire kayan ta, domin nuna mata karfi suka yi, har aka kaita ban dakin suka mata wanka, ana ne suka shafa mata abu a fuska, tunda ta yanki jiki ta faɗi ko tafin hannun ta bata iya d'agawa. Hawaye ne ya fara zuba daga Idanun ta. *Waye zai taimake ni? Waye zai cece ni! Allah ka duba maraicina karka bari a wulakanta Martaba ta* a hankali ta lumshe idanun ta. ** Zaune yake a gaban masalaci, wani irin sanyi da rashin sukuni yake ji, a hankali kamar wanda iska yake mishi rad'a, a ran shi da kunnen shi ƙwaƙwalwar shi da zuciyar shi yake jin wani irin sautin murya wanda yake manne a cikin maganaɗisun kunnen shi, ya jiyo sautin Muryan ta. *Waye zai taimake ni? Waye zai cece ni? Allah ka duba maraicina* Yarrrrr yaji wani abu yana tasowa tun daga tafin kafar shi, yake jin abin. Lokaci guda zuciyar shi ta shiga bugawa akai-akai kamar zata tsaga kirjin shi, wani irin haske ne ya gifta ta idanun shi, zubewa tayi a wurin kamar matacce. ** A hankali suka gama shirya ta, sannan suka shigo da ita dakin, suka kwantar da ita, kafin suka fita. Sun same Barkindo zaune a zauren Fulani suka ce mata.. "An gama fulani" Bata ce kome ba ta d'aga musu hannu, fita suka yi ta cigaba da shayar da shi madara me hade da maganin karin lafiyan maza, sai da ya sha ya koshi suka fara hira, ganin ya takure wuri guda. "Jeka ka huta, yau na baka damar hutawa sosai" tashi yayi yana gyada mata kai, ya nufi bangaren shi. "Jeka Yarona ka cire kwadayin surar da yake haukata ka." Ta fada fuskar ta babu imani. Haka yake tafiya, yana jin shugaban ƙaramar hukumar wandon shi tana reto da tsalle, har ya isa dakin shi. Hango mace yayi a gadon shi an zare mata kome tana kwance haihuwar Uwata da ubanta,baki daya sai ta rude ga wutar sha'awar da ta Kunno Kai, rike kan shi yayi, sakamakon wani irin taku da yake ji a bayan shi, juyawa yayi yaga ba kowa, da sauri ya nufi gadon, ya zauna yana kallon gefe da gefe, dan jin wani irin sauti kamar ba zare takobi ne ko wukane bai sani ba, cire kayan shi ya fara yi tare da nufar gadon ya kwanta, ya ma rasa me zai mata kawai ya tsaya yana kallon ta, haka kawai yake hango wani inuwa yana tunkaro su, da sauri yayi baya, rufe idanun shi yayi, kafin ya bude ganin wani gawurtaccen zaki a gaban shi, bai san lokacin da ya fasa ihu tare da suma ba, a hankali Zakin yake gurnani, yana zaga gadon. Shafa bayan Zakin wani tare da jan labulen gadon da zanin gadon ya lullube ta, ba zai iya gane fuskar ta ba, amma haka kawai yake jin bugun zuciyar shi yana kara tsananta, mayafin da yake rufe a fuskar shi ya ja, wani igiyar jiki me ɗauke da wani munduwar azufar, sai zoben azurfan da yake hannun shi, ya zare tare da sakawa a cikin igiyar, ya daura mata a wuyar ta, dishi dishi yaƙe gani, har zai fita ya cire wani guru da yake kugun shi ya daura mata, ta cikin zanin, d'ago ta yayi Kirjin ta yana hade da na shi. Fuskar su yana hade da juna, yana jin fitar numfashin ta. Ajiye ta yayi tare da juyawa ya bar zakin a gefen ta. Iska ne ya dauke shi ya b'ace. Haka suka kasance har asuba, a firgice ta farka, ta kalli inda yake kwance kamar gawa da gudu ta nad'e kayan ta, ta saka tare da gigicewa ta nufi hanyar waje, zaki yana biye da ita bata sani ba, duk inda take giftawa babu me lura da ita, haka suka bar masarautan. Kuma wani ikon Allah ta samu masarautan kofar su a bude har ta, bar masarautan. Garin gudu taji an damke ta tare da rufe mata bakin ta, wani abu ta shaka ta koma jikin mutumin ta kwanta. Wani barci ya ɗauke ta,, har ya sabata a kadadar shi jin gurnanin zaki yasa shi juyawa a matukar raxane ya sauke ta tare da juyawa da mugun gudu, zagaye ta Zakin yake a hankali guguwa me karfi ya tashi, a hankali iska da kura yayi ta tashi har suka bar masarautan tare da sauka a cikin dakin ta, sannan ya koma bakin gadon ta ya zauna kamar yadda aka umarce shi. ** Bubuga kafar shi aka yi ya bude idanun shi, a hankali yake son tuna abinda ya faru, amma kamar mafarki. Tashi yayi lamido ya tambaye shi. "Meye ya faru?" Da hannun shi yayi Mishi alama da hannu.. "Mafarki nayi" "Mafarki kuma" gyada mishi kai yayi, tare da riko hannun shi suka tafiya. "Wani irin mafarki kayi?" Girgiza kai yayi tare mishi alama da ya manta kome, haka suka koma gida. Kwantar da shi yayi tare da komawa inda abin ya faru, ya zauna yana kallon wurin. Mafarkin da Gidado yayi, kusan dukkan abinda ya faru da ban mamaki. Haka ya gama ya koma, ** Washin gari Ana shiga dakin Barkindo aka sake shi a sume, kuma babu Anum babu dalilin ta, ai da sauri aka bazama niman ta, shi kan shi an samu ya farfaɗo amma da ihu, yana zabura tare da fadin. "Wayyo Allah na ga zaki nan ga mutumin zai sare min kai" sai aka yi ta faman surfa Mashi hayaki har manyan fada sai da suka zo duba shi. Karshe haka aka kira masu maganin masarautan, lokacin da babban cikin su ya shigo dakin juyawa yayi ya kalli Bingel. "Abu daya kike son aikatawa kuskuren da xaki iya rasa rayuwar danki. Ita yarinyar ba kasafai ake samun ta ba, sannan daga yadda naji kamar hadi gwiwar yanayi ne na musamman. Ina baki shawaran karki sake aikata hakan domin zaki yi danasanin, iya jarabawar shi ce soyayyar ta, kin san ma'anar zakin da ya gani? Kin san halin da kika cilla shi. Ki gode yana raye." Daga nan ya nufi inda Barkindo yake fisge fisge,.kamar mahaukaci, abu ya tab'a a cikin goran shi ya shafa mishi a Goshin sa, a hankali ya kwanta sai barci. Lumshe idanun shi yayi hannun shi yana dafe a Goshin sa..... *Na tafi kallon Film Allah ya kai mu gobe mu daura 🤫🤣😂🤔* [6/1, 8:27 AM] Empress Anum: KALLABI... A Tsakanin Rawuna EWF https://www.wattpad.com/1231240183?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=OgQPQmFoBGYe1XAHNfSmZxKcWEky2WEWM7hySgqTOpmL%2FxN0WcKYNWrGT6z7zD3FI9XH7MN42tyfAHsfobkquI5x28Nk65FnGxBJFOiSR0OtUTWYRTVSp%2Fa4dCUapnnO BABI NA ARBA'IN DA BIYU A hankali ya juya yana kallon su, Kafin ya juya ya kalli Barkindo, cikin mugun tausayi da bai tab'a jin na wani a cikin masarautan nan ba, tun bayan sarki Bello bai tab'a jin wani a cikin masarautan ba, sai Barkindo wani irin Tausayin shi Yaron ya cika zuciyar shi, bai da laifi ko daya bai san kome ba, Asalima masu laifin daban hukuncin laifin ya sauka a bisa ƙaddaran shi. "Yarinyar zata iya sauya ƙaddaran shi, idan ta amince da shi, amma idan har taki amincewa babu dole, kuma duk wanda ya tunkare ta, tabbas abinda bai faru akan Fulani Aminatu shine zai faru, domin akwai kariya a tare da ita." Rufe bakin ta tayi cikin tashin hankali, ta ce mishi. "Ba dai itace Kallabi a tsakanin rawuna ba" har ya isa bakin kofar fita daga cikin dakin, ya juya a matukar sanyayye ya ce mata. "Bani da tabbas" ya fadi haka domin kare darajar Anum domin kuwa idan ya sake ya fadi wani abu toh ba makawa rayuwar yarinyar yana cikin hatsari, fita yayi cikin nutsuwa, amma a zuciyar shi babu nutsewa tun jiya yaji haka a ran shi, itace sanadin dawowar jiya da aka rasa Yau, dan haka ya nufi inda gidan shi yake ya shiga ya fara rubutu cikin zafin nama, sannan ya kira wasu Amintattun bayin shi. Daya ya tura shi yankin sokkoto da sakon galadima, biyu kuma ya basu sako su tabbatar saka a kofar Masarautan. Inda me zuwa Sokoto ya gajarce mishi tafiya, yadda zai isa Sokoton da sauri. A can cikin masarautan kuwa, shiru kowa yayi da bakin shi domin kuwa abinda ake nima ne, gashi ya zo cikin kankanin lokaci, a sace aka fara yunkurin niman Anum. Domin cika burin su na zama sakarunan masarautan. ** Kwana biyu ya dauka, kafin ya warwarewa, dan haka babu bata lokaci suka fara yunkurin tafiya makaranta, har sun gama shirin su, ranar da zasu tafi har iyakar Borno da Chadi aka raka su, sai dai koda suka tafi Gidado yaki mai da hankali ga karatun sa, Makarantar yana karkashin koyarwa Imam shafi'i, ana koyarwa sosai. Sun tafi sun bar Fulani Aminatu da mugun kewar su. ** Sokoto. Lokacin da sako ya iso wurin Galadima, duba sakon yayi tare da nufar wurin Baffa'm ya zauna ya ce mishi. "Lokacin komawa gida yayi, cikin wannan makon zamu koma kaje Insha Allah Aminatu tana nan tafe" kallon shi yayi kafin ya ce mishi. "Ban gane me kake nufi ba?" "Sakon da aka kawo min yana da nasaba da ita, bari na karanta maka kaji yadda sakon yake" _AMINCIN ALLAH YA TABBATAR A GARE KU, KAMAR YADDA NA GAYA MAKA KUYI NISA KUYI DOGON TAFIYA YADDA XA A MANTA DA KU, INSHA ALLAH ALLAH XAI KAWO MAFITA. ALHAMDULILLAHI MAFITA YA ISO LALLAI INA SON NAN DA MAKO GUDA KU ZO GIDAN DA YAKE KUSA DA RUGA.... YARINYAR TA BAYYANA SAI DAI A WANNAN KARON AN SAMU AKASI DOMIN RAYUWAR TA YANA CIKIN BARAZANA KOWA YANA BUKATAR TA, IDAN DA HALI KUZO AKAN LOKACI, DOMIN KU BATA KARIYA AMMA NASAN TANA TARE DA KARIYAR UBANGIJI DOMIN ZAKUNAN DA SUKE ZAGAYE DA AMINATU SUN KASANCE TARE DA ITA KUZO DOMIN ZAME MATA GARKUWA_ "Kenan Zuri'ar Aminatu suna raye?" Baffa'm ya fadi haka, fuskar shi tana kara bayyana tashin hankali, shi yanzun da tsufar shi ina zai kai budurwa? Ai abin kunya ce ace yau yana auren yar cikin shi ga shi bai san me AMINATU ta haifa ba. Galadima kamar ya karanci abinda yake kwance akan fuskar baffa'm ya ce mishi. "Malam Jarumin soyayya bafa yarinyar ce zaka aura ba, ina jin wani al'amari akan cikin da Aminatu ta tafi da shi, ina ga shi zai kasance da ita." Murmushi baffa'm yayi yana shafa kan shi da ya kara bayyana girman shi, wato furfura. * A cikin satin suka yi sallama da Inna Marwa, mai maganin shi ya je da kan shi ya amshe su, ya kawo su masaukin da yayi musu kusa fa ruga, sannan ya shiga har cikin rugar suka nime mace dattijuwa da zata na shiga cikin gidan tana musu aiki, kiri kiri suka ki yarda dole suka tura Anum, kuma dama abinda yake bukata kenan shi yasa yayiwa masu niman Anum iyaka. Kuma alhamdulillahi, lokacin da Baffa'm yayi ido biyu da Anum, haka kawai jikin shi ya bashi girma da nasabarta da Fulanin shi, dan haka yayi ta tambyar ta, tana bashi amsa har ya zuba mata ido. "Yanzu idan kina gama mana aiki kiwo?" Ya tambaye ta, "Eh Baffa'm!" Da wani irin sauri ya zuba mata ido. Ƙasa magana yayi yana kallon ta, baki daya ta rikide ta koma mishi Minani. Haka ta wuce ta cigaba da aikin ta,.har ta gama ta ajiye sannan ta musu sallama. Zuwan su baffa'm yasa ta samu nutsuwa kuma bata cika zuwa tallar nono ba, Ganin haka yasa idanun Sarkin gida Galadima da Baffa'm, ya tsaya akan ta asalima ita kanta ba zata ce ga dalilin da yasa take jin dadin zaman wurin su ba, amma kuma tana farin cikin zama a cikin su, tana gama musu aiki zata dauki shanu su tafi kiwo. A cikin gidan su akwai yan mata uku waɗanda sa'o'in ta ne, Sumaye da Marka. Kusan kan su daya, duk da basu sonta amma kuma duk lokacin da zasu kiwo a tare suke fita kiwo. Amma idan suka fitan kowa kama gaban shi yake, domin iyayen su. Suna yawan gaya musu cewa idan tafiya ta haɗa su da Anum toh dauke kome zata yi tayi, duk da har cikin garin aka nime su bada wacce zata na aiki ana biyan ta, suka ce su ba bayi bane. Sannan suka tura Anum, ita fa da bata da galihu. Haka bai musu ba, sai da suka ga yarinyar ya fara samun farin ciki, yau kamar kullum tana gama hada aikin ta kalli Baffa'm ta ce mishi. "Baffa'm zan tafi kiwo ina ce babu ruwan wani abu?" "Eh babu kome" "Toh shi kenan zan tafi" Har zata fita ya kirata. "Anum!!" "Na'am baffa'm!" "Baki da aboki ko kawa ce?" Yar dariya tayi sannan ta ce mishi. "Baffa'm bani da su, sai dabobbin da nake kiwo" "Toh Allah ya dawo dake lafiya" Gyada kai tai tana cewa. "Amin" Tana isa gida ta samu lamiyo suna jiran ta, suna fita suka shiga kawo mata labarin da suka ji iyayen su na fada akan ta kama kurwan Barkindo.. "Allah sai ya saka min domin ni ba mayya bace." Ashe labarin ya gama karade rugar bata sani ba, sai da suka tafi cikin daji suka haɗu da sanin gidan Malam Yaroji Suna ganin ta suka fara mata dariya suna cewa. "Anum ashe maitarki ya kai har kin kama sarkin gobir" Banza tayi da su, sannan ta wuce. Aikuwa suka shiga binta, inda suka kore sauran yaran ita kuma,suka tare ta. Abinda ya faru a dakin Barkindo ne ya dawo mata, a hankali ta juya zata bar wurin kanta yana sara mata. Fisgota Rabi'u yayi ya matse ta da bishiyar rimi. "Sani na jima ina fakon yarinyar nan ban san me yasa nake jin azabar kwadayin ta ba," ya matse wuyar ta a jikin bishiyar. "Yawwa kwabe mana ita Sani" idanun ta sun yi jajjur, ga kwalla da yake shirin zuba mata, garin kiciniyar cire mata gwadon ta, suka tsinka wurin da yake kugun ta. "Wuuuuuuuuuuuu" suka ji kukan kudar zuma, juyawa suka yi basu gan su ba, har sani yayi nasaran cire mata dan bingilin rigar ta, motsi tayi a hankali ya juya, wani murgugegen zaki ya hango, da ya fasa ihu tare da kartawa da gudu, shima Rabi'u, yana juyawa suka yi ido hudu da shi, aikuwa ya bi bayan Sani, zuman nan suka bisu har gida, suna harbin su. Durkusawa tayi a kasa tare da fashewa da kuka, tana kame jikinta kuka take tana jin wani irin tsanar kanta, me tayi da ake mata haka? Ina dangin Mahaifiyar ta suke da ita kanta Mahaifiyar ta? Me yasa?" * Jikin Barkindo sai da aka yi da gaske domin mahaifiyar shi taso janyo mishi masifa, kiri kiri hauka ya kusan turmushe shi, dan haka babu shiri da taimakon Waziri aka yi ta niman masu jinyar shi, gefe guda kuwa ana tuntubar Yakubu akan murabus domin Barkindo ake son bawa mulkin, sai dai ta gefen Yakubu yaji dadin mulki dan haka suka yi ta Jifar Barkindo abinda ya kara haukata bawan Allah nan kenan, domin sai an yi kamar ya samu lafiya kwana biyu kawai kwana biyu sai ciwo ya kuma tashi, dalilin da Yasa Bingel tawowa har ruga. (Me zai faru?) Bayan ta dawo daga kiwo ta shigo cikin gidan, duk da taga fadawa amma bata kawo a ranta wani abu bane, dan haka ta shiga cikin gidan, tana shiga Bingel tana mikewa. "Muje" ta ce mata. "Muje ina?" Ta tambayi bingel, "Ko ina ma zaki gani" "Bafa inda zani" ya fada tana gifta gefen ta, rikota tayi da karfin tsiya, zata kai ta, wani irin gurnani taji a bayan Anum, babu shiri ta sake ta. "Ba zan je ko ina ba" tafauce hannun ta, Daga haka ta wuce dakin ta, kamar zata yi hauka haka take ji, girman kai ya hanata rokon Anum sai dai ta dolanta mata tafiya, ita kuwa tace bata san da haka ba. Haka ba. Koda ta koma ta samu waziri yana jiran ta, zama tayi a hankali kafin ta fashe da kuka. "Me yasa sai Yazidu? Me yayi da ya cancanci haka? Tun daga ranar da ya ga yarinyar nan ya koma sai a hankali ashe kaddaran shi tana hannun ta." Jikin shi yayi mugun sanyi dan haka ya shiga bata hakuri. "Kiyi hakuri ki saka ido akan shi, Insha Allah zai samu lafiya" "Amma dole sai da taimakon ta zai samu lafiya!" Ta fada. "Shigowar ta masarautan nan kara sabunta Bala'i ne, barta a inda take" Ya gaya mata, sannan ya mata sallama. Ya nufi gidan shi, a hankali ya tsaya a kofar Aminatu yana kallon sashin da ya tsufa babu alamar an tab'a zama a wurin na tsawon shekaru, wurin ya koma kamar kango, idanun shi ne ya cika da kwalla, sannan ya wuce. * Wani bushashen tuwo ta zubawa Idanu, a hankali ta mike zata koma bakin gadon ta, zoben da bata san da zaman shi ba ya fito ta cikin rigar ta. A hankali ta rike zoben tana kallon shi lallai tana son ta tuna inda ta ga zoben, yaushe ta saka a wuyar ta, "Toh ko na Aljanu ne?" Shiru tayi sannan ta ce. "A'a toh ya kenan idan ba Aljanu bane?" Abinda ya faru yau baki daya yasa ta, jin tsanar kanta da duk wani wanda zai shigo rayuwar ta, Washi gari bayan ya tafi gidan Baffa'm ta dawo ta samu an cika a kofar gidan su, kamar dama jiran ta ake suka yayyako mata, kukan zuma suka ji, a tsora ce suka yi baya. "Ke mayya ko.?" "Ku ga maita a ƙwaryan cin abincin ku" ta fada tana rab'a gefen su. "Ke Wallhi idan baki sake kurwan yaran mu ba sai mun kashe ki" inji baban Sani. "Yanzu ma Meye zai hana?" Kura mata ido yayi kafin ya ce. "Wato baki da kunya" "A'a ba haka bane ka tambaye su Meye suka yi na kama kurwan su, idan suka fada da bakin su, shine zasu samu idan suka ki fadar gaskiya toh kuyi hakuri" ta wuce abin ta baka kuma.bin ta kan kowa ba, Babu yadda suka iya dole suka koma tare da tambayar yaran su, kuwa suka gaya musu gaskiya. * Bayan shekara daya "Ka nimo Yarinyar ka aura itace zata hana ka sauka akan mulkin, karka sake suyi tunanin nimawa Barkindo auren ta, yin haka shine asarar da zaka yi domin lokaci yana gab da kurewa, magada kujeran zasu iya bayyana kowani lokaci. Dan haka maza ka nimo Yarinyar ka aura zaka kara karfi kamar yadda Bello yayi sannan sunan ka zai shahara a tambarin shahara, zaka yi suna da karfin mulki ka duba maganata Yakubu... Mai_Dambu [6/2, 12:14 PM] Empress Anum: KALLABI...! A Tsakanin Rawuna *EWF* BABI NA ARBA'IN DA UKU A zabure ya kalli malamin shi kafin ya ce mishi. "Ita yarinyar ce mulkina ko auren ta ne mulkina?" Ya tambaya cikin izza, "Itace kome naka" "Taya zan iya mallakar ta?" "Shine abu me wuya, domin yanzu haka Uwar Barkindo tana can tana niman hanyar mallakarta" Bude idanun shi yayi da suka yi jajjur, "Dole na mallake ta." * Masarautar Kano. Yau kwana huɗu kenan zuwan sarakaunan daular Usmaniyya, sarkin Zazzau, mai martaba Muhammad Lawal Fulanijo, sarkin Bauchi Ibrahim Yakubu, sarkin Gombe Shehu Usmanu Kwaranga, Sarkin Borno Muhammad Omar Shehuri, sun taso ne sakamakon karfin zumunci da kuma karin karfin Ikon da zasu nimawa jikan Sarkin Gombe Hassan Muhammad Bello Lamido, yau kasancewar ranar Alhamis sun taru ne a lambun, sun yi shiru kafin Sarkin Borno ya ce. "Lamido Hassan jarumi ne, kuma bana danasanin nima Mishi auren Fulani Hadizah." Shiru me martaba sarkin kano yayi kafin ya ce mishi. "Toh ba zan hana ba, amma kowa yasan Bello ya kori aaminatu ne daga..." Cikin matsanancin rashin jin dadin abinda ya fada, sarkin Gombe ya mike. "Babu damuwa, haka ma mun gode" "Shehu zauna ayi magana" Inji Sarkin Bauchi, duk da suna jin irin zafin da yake ji, amma sun yi kokarin dakatar da fushin su ne, ta hanyar maganar sarkin Zazzau da ya fara. "Koda mai Kano bai amince ba, a matsayina na Aminin shi zamu amshi haka amma abisa sharadin indai Jinin Gobirawa ne ke yawo a jikin shi na amince a turo shi." D'aga mishi hannu mai Martaba Sarkin kano yayi sannan ya ce musu. "Akwai wani shirin da nake, tunda shi jarumi ne, ka turo min shi na ga yanayin jarumtar shi a filin daga rana ita yau nake bukatar shi, idan har ya iya tunkarar abinda na sashi TOH ba makawa zan ba shi ita." Kasancewar ƙasar Kano tana da kyakkyawar alaka da masarautar Gobir, yasa take ganin kamar bawa Lamido auren Fulani Hadizah akwai munafunci,domin shi yadda aka gaya ámishi abinda Aminatu tayi yasa yake ƙyamar maganar auren, sai dai shi yasan matuƙar jinin gobir ne ba makawa zai iya kome. Amma dole sai ya tabbatar da haka ne da idanun shi, kawai shine zai iya bashi Yar shi, sun jima suna tattaunawa, kafin suka watse zuwa masaukin su, anan ma sun bawa Sarkin Gombe hakuri da ban baki domin sun san ran shi ya masifar baci, kuma sun san da haka kawai sun dage ne akan lallai yar Sarkin Kano zata iya bashi kwarin gwiwa samun mulki. "Idan har ya zo don Allah ka turo min shi kafin ya je kano" "Insha Allah" Sun nima Mishi auren Fulani Hadizah ne domin shirin su na tura su Gobir a nasu shirin kenan, domin koda tsiya koda arziki sai sun wanke Mahaifiyar su. * A yadda take lissafin yau saura kwanaki uku Yaran ta, su dawo daga inda suka tafi karatu, haka ma Fulani Bintu kamar tayi tsuntsuwa ta iso su, kallon Innayoh tayi cikin farin ciki. "Innayoh idan suka zo ina son mu tafi Gombe da su." "Toh Allah ya amince." Shigowa Bintu tayi da bayin ta, dauke ga manyan kwalolli guda biyu, tana zuwa ta zube gaban Innayoh. "Gashi nan, kayan Hamma Gidado ne" "Yana godiya" idanun Ammyn cike da kaunar ta, take kallon ta. "Allah ya miki albarka" "Amin Ya Allah" inji Innayoh, Sosai take kaunar yarinyar, mikewa tayi cikin kunya da kamun kai ta bar gidan, "Innayoh yarinyar nan tana da hankali. Ubangiji ya sa matar shi ce" "Amin Ya Allah, amma alamun karfi naga me kiba, uban dakina ne dai har yau babu wacce ta taya min shi" inji Innayoh. "Babu ruwana ke kika ce matar shi sai ta fi ta kowa" Murmushi Innayoh tayi tana kallon gefen ta, kafin ta ce mata. "Saurin me kike? Ki zuba idanu da kanki zaki shaida." "Allah ya kai mu" "Amin" ** Masu iya magana suna cewa masha ruwa magirbi, mai rabon ganin badi ko ana surfa shi a turmi ne sai ya ga, a hankali ya fito wajen masarautan, yana kallon yadda kowa yake rayuwa, babban burin shi bai wuce ganin Anum ba, yasan zuwa yanzu ta manta da shi, amma shi bai manta da ita ba, mingira kan shi yayi jikin keken dokin shi, har suka bar Masarautar, sai da suka bar masarautan suka nufi gidan gona, "Yallabai mun iso" Bude kodaddun idanun shi yayi, kafin ya ce. "Toh Salahudeen" A hankali ya mike tare da rike jikin keken ya sauka, da taimakon Salahudeen din suke tafiya. "Don Allah kar ka ce nan ka kawo Ni" "Inshallah" suka cigaba da tafiya, har inda suke kiwo, tana zaune a bakin ruwa, a hankali ya mishi alama da ya bar shi, takawa yayi tare da nufar inda take kamar zai fadi. Zama yayi yana sauke ajiyar. "Hmm" ya ce mata. D'ago kai tayi tana kallon shi, a hankali abinda ya faru ya shiga dawo mata kai tiryan tiryan, kamar lokacin abin yake faruwa. Tashi tayi zata bar wurin ya rike wuyar hannu ta, "Anumullah" juyawa tayi a fusace, tana kallon shi cikin mugun tsanar shi. "Sake min hannu" "Anum ina sonki" cak ta daina motsin da take yi na yunkurin kwacewa daga gare shi. "Da gasken gaske ina sonki,, shekara daya da faruwar wancan al'amarin ba nufina ba kenan,. Ban san kome ba" Ya fada idanun shi yana zubda kwalla me zafi. A sanyayye ta zare idanun shi daga nata, "Toh na gode amma bari na gaya maka, bana sonka. Na tsane ka tun ranar da Uwarka ta bada damar ka wulakanta ni na tsane ka, na tsane ka tun daga karkashin zuciya ta, da zan samu damar kashe mutum kai xan kashe" tana gama fadar ta bar wurin, cikin tashin hankali yake Bin ta, amma bai saka Anum kula shi ba, sai kiwon ta da take yi, haka ba karamin tashin hankali ya shiga ba, kan shine ya fara sarawa yana me dafe kan shi, durkusawa yayi akan gwiwar shi ta sake wani marayan kuka me hade da nishi nishi. Cak ta tsaya zuciyar ta yana wani irin bugawa, kamar ta tafi amma haka ta kasa motsi kamar wacce aka daure, ta juya tana kallon shi. Amai yake na jini sosai, Da sauri ta tawo wurin shi. Kai hannu tai zata d'ago kan shi amma ya buge hannun ta. "Sannun!" "Bana bukata" Wani irin tausayi ya bata, dan dole ta hakura tare da tsayawa a wurin shi. "Meye Laifina? Me yasa ƙaddara ta tayi zafi haka? Na

Chapter 22 of 39