su, tunda dole ka kare rayuwar ta."
"Kana nufin" ya tambayi Galadima tare da rike hannun shi idanun shi na cika da kwalla.
Gyada mishi kai yayi shima hawaye na zuba daga idanun su baki daya.
"Me yasa sai ita?" Ya tambaya cikin wani irin tashin hankali. Galadima shima zama yayi tare da sunkuyar da kan shi.
"Na tafi lardin sokoto ne domin dakatar da wani abun, Alhamdulillahi abu na gaba shine ba zan iya kome a tsakanin ku ba, kai ne kake da wuka da nama. Imma ayi nasara akan ka Imma kuma ayi akan ta."
"Ni kuma?"
"Eh kai! Kai ne na gaba"
"Galadima wai me yasa kake min magana a dunkule? Ka gaya min meye zai faru."
"Ba magana nake maka a dunkule ba, wallahi ban san dalilin ba amma ba makawa zasu iya bin ta kan ka"
Nuna kan shi yayi da dan yatsar shi.
"Kuma ni"
"Hmm! Kowani mutum yana bincike kafin ya aiwatar da kudirin shi, dan haka kayi kokarin ganin ka shirya." Mikewa Sarki Bello yayi tare da cewa.
"Wannan zancen banza ne, tunda ba zaka min bayani yadda zan fahimta ba, sai kayi." Baki daya dawowan Galadima bata mishi amfani ba, domin duk yadda yaso kare Aminatu sai ya samu Galadima yaki ba shi goyan bayan da ya dace karshe ma, sai ya kara fahimtar kamar ai da hannun Galadima a cikin abin da ake musu dan haka a zuciye ya shirya domin tunkarar makiyan Aminatu idan ya gama da su, zai dawo kan mutanen fadar.
Ana gobe zai tafi yakin bayan sallah isha.
Tana zaune a gaban shi.
"Baffa'm ka min alkawarin zaka dawo a raye!" Ta fada bayan ta kifa kanta a kirjin shi.
"Insha Allah zan dawo zan dawo miki da yardan Allah zan dawo kamar yadda na tafi"
"Baffa'm" ta kira sunan shi cikin shashekar kuka, hannun shi ya kai fuskar ta.
"Ba zan bari a ci mutuncin ki ba, kuma ba zan tab'a amince domin keta alfarmarki ba, ina son ki."
"Baffa'm Insha Allah zan haifa maka Yarinya Kyakyawa kamar ka, ayi mata irin wannan tsagon naka, ina son ta kasance mace Jaruma kamar kai."
"Ta zama me hakuri kamar ke" ya fada yana sumbatar goshinta, yau ne ranar farko da ta kalli cikin idanun shi tana son gaya mishi abinda take ji a kan shi. Amma kuka da shashekar da take ta kasa magana sai kallon cikin idanu juna suke, kamar ba zai dawo ba, hannun shi ya kai wuyar ta, ya janyo ta a hankali ya shiga sumbatar bakin ta, kamar ya had'a da ita ya cinye...
___________________
End of page 20
Romeo and Juliet sun haɗe sai a hankali 🚶🏾♀️🚶🏾♀️🚶🏾♀️
Kar wani ya ce min zai yi min kuka 🙄
*Ina sanar muku da sabon labarina paid book da zan fara Insha Allah next month me suna Zayn Malik June update Insha Allah amma karshen june Insha Allah dan haka yan kasuwa da ma'aikatan gwamnati da uwaren gida masu sana'o'i gani nan zuwa gare ku da sabon labari... Dan haka idan kun ji dadin Kallabi na san da kanku zaku zo saya 🥰🤩🤌🏽300₦ ne kunsan yadda muke a kasar nan babu yawwa Allah yayi mishi albarka*
#Mai_Dambu
[5/14, 2:22 PM] Pearl crystal: KALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
Na
Mai_Dambu
EWF
https://www.wattpad.com/1224376096?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
Lumshe idanun ta tayi tana kara rike rigar shi, tare da jin kamar su tafi tare, kallon yadda kwalla ke sauka akan kyakyawar fuskar ta yasa shi kai bakin shi saman siririn hancin ta ya sumbace shi a nutse. Sannan ya d'ago kanta yana kallon yadda zara zaran gashin idanunta suka mike bayan sun jike da kwalla, bakin shi ya kai kan idanun ta na dama, sannan ya mai da na hagun. A hankali ya janye daga jikin ta, yana me rike hannun ta.
"Kin yarda na zan dawo ba?" A hankali ta bude idanunta da suka yi jajjur sannan tayi murmushin da bai hana kwallar zuba ba, ta ce "nasan zaka dawo" ta fada bayan ta kai hannun ta saman Kirjin ta, yana jin yadda yake bugawa.
"Ki fadi abinda yake ranki"
"Idan ka dawo zan fada maka" ta fada tana Murmushi sannan ta mike daga inda take, ta nufi tagar shi, ta tsaya tana kallon waje.
Hannun shi ta ji a bayan ta, ya kuma k'amk'ame ta mai da kanta tayi Kirjin shi, tana fesar da kukan da yake cin ta, kan shi ya saka a kadadar ta. Yana sauke ajiyar zuciya samun kan ta tayi da daura hannun ta a saman na shi. Wani irin kuka yana kara rugurguz mata zuciya.
Da sauri ta juya tana fuskar tar shi, d'aga kai tayi tana kallon fuskar shi domin ya fita tsawo sosai, kanta a kirjin shi yake tsayawa.
"Idan na haihu ba zaka kara kwarkwarah ba?" Ta tambaye shi da wata irin raunanin murya wanda yake dab da falasa kukanta.
"Ko baki haihu ba, har abada ba zan bari kwarkwarah ta fiki yawa ba"
Cikin rashin gamsuwa ta ce mishi.
"Duk da ban san kome akan Mahaifiyata ba, amma nasan fifitatta da baffana yayi ne ya janyo mata mutuwar ta, ina tsoron kar na zama daya daga cikin mugaye mata ne, shi yasa amma dan ta nice ka kawo duk wacce kake so"
Tana gama fadar haka ta juya zata bar shi a dakin.
"Na zata kin zo muyi sallama ne, a tunani zaki kwana ne fa?" Juyawa tayi tana kallon shi kafin ta ce mishi.
"Ina ga lokaci ya kusa d zan koyawa kaina ni ɗaya a matsayin matar da tana ganin sarki da iyalin shi"
Lokaci guda yaji ran shi ya b'aci,
"Idan na isa dake ki tsaya muyi bankwana idan ban isa dake ba, ki tafi abin ki, kina nufin abinda kike min zai saka ni fasa abinda ya zama kamar dole ne a kaina ne? Ko kukan Ni da borin ki ne zaki saka ni fasa abinda na yi niyya ne? Ki gaya min meye nayi Miki da baki iya adana kishin ki ne?"
Cak ta tsaya tana mamakin yadda har ya fadi haka a gare ta, juyawa tayi tana kallon shi. Sannan ta koma bakin gadon shi ta zauna tare da sunkuyar da kanta.
"Kayi hakuri" daga haka ta fashe da kuka, ta jima tana kuka samun kan shi yayi da son rarrashinta, kuma bai yi kasa a gwiwa ba, ya shiga rarrashin ta har tayi shiru, kusan wannan daren sun yi shi ne babu wani dadi babu wani abinda suka karu da shi, har kusan asuba, sannan ya janyo ta ya rungume ta sosai a jikin shi yana shafa bayan ta, har tayi barci. Sai da aka kiran sallah farko ya raba ta a jikin shi, sannan ya nufi ban daki yayi alola ya nufi masallaci, sai wurin karfe shida ya samu tana barci , a hankali ya zauna yana ja mata yatsun kafa, bude ido tayi akan shi.
Ajiyar zuciya ta sauke tana kallon shi, kafin ta mike zaune tare da rike mayafin a kirjin ta, tana kallon yadda yake mata wani irin kallo tun daga sama har zuwa yatsunta.
Shafa kan ta yayi ya ce mata.
"Tashi kiyi sallah"
Tashi tayi a jikin ta a mace, jan mayafin yayi daga ita har mayafin suka zube a jikin shi.
Kyakyawar riko yayi mata tare da juyar da ita, lumshe idanu tayi tana jin bakin shi a wuyar ta, har zuwa kirjin ta, daga nan bata kuma fahimtar kome ba, sai da ya kai ta duniyar da bata zata ba, ya tara mata gajiya sosai, sannan ya dauke ta cak zuwa ban daki suka yi wanka, ta fito ta gabatar da sallah, sannan ta koma ta kwanta, tana son tayi kuka amma zuciyar ta tayi wani irin tauri, sai ajiyar zuciya take saukewa, lokaci zuwa lokaci.
Yana zuwa ya same ta a kwance, ya kwanta a bayan ta. Ya shiga rarrashinta tun tana daurewa har ta shiga kuka, baki daya ya lalace a wurin ta, ya manta da kowa sai ita, a hankali ta janye jikin ta jin ana ta buga tamburan masarautar, wanda yasa ta mike tana jin gyaran muryan Sarkin Gida, da kan shi ta fita ya amso mata wani irin kaya da aka masu iri daya, kome har da alkyabbar shi, da takalmin shi, an yin shi babba Alkyabbar har baya gashi an saka wasu irin kyalkyali kamar wata dawisu karamin kyau tayi ba, haka da taimakon shi ta shirya, suka fito har zuwa wurin cikin abincin, d'ago kai tayi taga Innayoh, kallon juna suka yi, a cikin kwayar idanun Innayoh ta ga kwarin gwiwa da juriya. Dan haka ta sunkuyar da kai ta fara cikin abincin. Tana ci tana share kwalla. Hannun shi na hagu ya daura akan nata, yana kallon yadda take goge kwallar ta, daura hannun shi yayi a saman nata, tare da matse hannun. Bata wani ci sosai ba, tabawa tayi yana kallon Innayoh, jin jina kai tayi tare da yada mishi kai.
Bayan sun gama ya mike, kasa tashi tayi sai da ya dauke ta, sannan Sarkin gida ya dauki kayan shi na yaki ya fitar da shi, haka yake tafiya da ita a hannun shi, tunda ake a tarihi ba a tab'a samun haka ba, asalima a ƙasar Hausa ba a tab'a haka ba, sai abin ya zama sabon alamari. Lokacin da suka fito baki daya mahakuntar masarautan ne a waje, komawa gefe galadima yayi dan yana hango karfin hali a wurin sarki Bello, yayin da Fulani Aminatu keta sharan kwalla, zama yayi yana share kwalla shima, a karon farko a rayuwar shi da ya kasa samawa abokin shi kwarin gwiwa, a karon farko da ya gaza fitowa ya gaya mishi makomar shi da Fulani Aminatu, a karon farko da ya ci amanar yarda da yayi mishi.
Yana kallon yadda Sarki Bello ya wuce da ita sashin sa, domin ya rarrasheta, sai da ya zaunar da ita, sannan ya rike hannun ta, yana murza yatsun ta.
"Ina jin zafin hawayen ki a zuciya ta, ina jin kamar ban Miki adalci ba, ki yi kokarin taimakona da hakuri man, ta ina zan samu kwarin gwiwar dakatar dasu, ta wurin ki ne idan ban samu ba ina fita gawata za a dawo Miki dashi."
Da wani irin sauri ta d'ago kai idanun ta na kara zubda kwalla hada hannayen su tayi wuri guda, tana matse su.
"Ba zan kuma kuka ba, kayi min alkawarin zaka dawo a raye, don Allah kar ka ce ba zaka iya ba" rungume ta yayi yana sauke ajiyar zuciya.
"Matukar bata Allah bace ta faru dani Insha Allah zan dawo da kafana." Rike hannun yayi sosai. Yau tafi bashi tausayi sama da kullum.
"Insha Allah zan dawo"
"Na yarda kuma nasan zaka dawo, tashi ka tafi Jarumin maza" ta fada haka tana me goge fuskar ta, babu musu ya mike, ita kuma ta rike hannun shi suka fito, akan fuskar ta kawai zaka iya karanto damuwar ta, bama sai kasha wahala ba. Dan haka suka nufi wurin da dawakai suke jiran shi. Tsayawa tayi sannan ta zare hannun ta acikin na shi. Kafin ta juya zata bar wurin.
"Ai zaki tsaya kiga tafiya ta" cak ta tsaya batq bukatar juyawa ta kalle shi matukar tayi haka zuciyar ta zata iya bugawa. Dan haka tana tsaye bata juya ba, tana jin ana Mishi addu'a. Har zai tafi wurin dokin shi, sai jin hannunta yayi a cikin nashi ta saka mishi wani abu. D'ago kai yayi yana kallon ta, ta juya a hankali. Kallon abin yayi sannan ya kalle ta, murmushi yayi domin ba kome bane sai gashi wutsiyar zomon ra dan dalago. Kallon shi yayi tare da juyawa ya kalli yadda ta kasa barin wurin. Takawa yayi har inda take, sannan ya kai hannun shi ya rungume ta, a hankali mutanen da suke harabar masarautan suka watse, sun jima a haka sannan ta juya tana ce mishi.
"Baffa'm ka tafi Allah ya tsare, ina nan ina jiran ka, sai ka gaya min waye ya baka damar cinye min dan dalago na" murmushi yayi yana me jan kumatunta.
"Da gaske me Fulani zata min idan na dawo?" Bakinta ta kai kunnen shi ta fada mishi wani abu, zare idanu yayi yana kallon ta, kafin ya sake dariya me sauti sannan ya ce mata.
"Kin ci bashi yar nan zan dawo da izinin Ubangiji" daga haka ya juya, kallon shi take tana murmushi, wani irin hadari ne da iska ya kamkama, tana tsaye a wurin har ya haura dokin shi, ya kad'a linzamin ya juya da sauri, suka bar masarautan daidai ana ruwan sama da karfi, zubewa tai a wurin tana me rike kirjin ta, sakamakon ciddar da aka buga, (wato tsawa) kuka take son yi amma ina ta kasa koda tari ne, hawaye ne ke zuba daga idanun ta, tana zaune a wurin sai da aka saka mata lema akan ta, Sannan ta d'ago kai, Innayoh ce tsaye idanun ta yayi jajjur.
"Tashi mu tafi"
"Innayoh zan jira shi ne" ta fada a sanyayye.
"Ba dawowar yau bane ko gobe, Addu'a zaki mishi"
"Toh Uwata" ta fada a sanyayye, d'ago ta tayi, sai kuma ta koma zata zube, Innayoh ta kuma rike ta da kyau, suka nufi cikin gidan.
A hanya suka hadu da Ladidi tare da Tabawa, sai matar Chiroma da yan mata bayi a bayan su.
"Ranki shi dade" suka gaishe ta,
"Ku taimakawa Innayoh kaita cikin gidan mana"
"A'a su bar shi" Inji Innayoh, kawai ganin su yasa ta jin wani irin yanayi a jikin ta.
Cikin mamaki matar Chiroma ta ce.
"Ita Fulani Aminatun ta fi kowa ne da ba a rike ba? Ku kama ta." Kawo hannun da Ladidi tayi, bata san lokacin da ta fasa ihu tana birgima kumfa na fita a bakin ta da hancin ba.
A tsorace suka ja da baya.
"Karku sake yunkurin kawo min farmaki. Bana son fitina" ta fara kanta a sunkuye, janyota Innayoh tayi suka wuce su.
Suna shiga shashinta, ta zube a zauren tana kuka kamar ranta zai fita, zuwan Sarkin gida da Galadima yasa Innayoh fita, can sai gata da sabon ƙwarya, shake da madaran saniya. Aka bata tasha, a hankali zanen da yake wuyarta ya shiga bajewa. Kwanciya tayi a wurin gwanin ban tausayi. Fita Innayoh tayi.
"Tayi barci"
"Aminatu zata iya Fuskar ta barazanar Kawo Mata hari, sai dai kuma me yiwa ta kare kanta, a duk lokacin da ta sunkuyar da kanta karki yi kokarin dakatar da ita, mugu ne yake tunkarar ta. Abinda yasa na ki bashi goyan baya kenan, domin idan ya ce sai nayi magana rayuka zasu ɓaci, Innayoh masarautan nan akwai munafukai ne, idan na ce zan hana ya amshi kwarkwarah abin da zasu ga Aminatun zai iya shafar rayuwar shi, ya kasa fahimtar haka, kai sarkin gida kasan kome kafin mu shigo masarautar nan daga Sokoto, karewa ma sai da muka yi yar dabara sannan muka shigo cikin gidan nan."
"Kashedi suka mana kar ya shiga cikin al'amarin Aminatu da Bello ya zamu yi? Ana son mulkin ne yanzu da karfin tsiya, shi yasa aka tinxira mutanen Sahil domin suyi yaki ba wai dan basu razana bane da gargadin shi. Idan aka kashe shi a yaki abu na gaba za a mika Aminatu ga mutanen Sahil idan kuma yayi nasara a yaki, TOH akwai yiwar a koma yakin cikin gidan......
______________________________
*Ayi hakuri zaku ga labrin kamar ba yadda nace ba wato na zamanin da can, so nayi amfani da salon na musamman ne na saka mana loveromance yadda zai tafi da zamani. Kuma ina fatan xaku fahimci haka idan kuka dubi tsofin English novel na ancient zaku samu an yi mushi kwaskwarima yadda zai tafi da zamani soyayya kuwa ko a kissosin Manzon Allah ana gaya mana tsarin soyayyar gidan shi, S.A.W Nagode*
Na fara jin barci idan na fara rubutun nan anya nima ba wadancan ne suka min nasu yar dabarun ba..
🤣🤌🏽😂
Barka da warhaka a cancare lafiya..
Please share comments and vote
#Mai_Dambu
[5/14, 2:25 PM] Pearl crystal: https://www.wattpad.com/1224701901?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
KALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
Na
Mai_Dambu
*EWF*
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
Zaro idanu Innayoh tayi, cikin tashin hankali tare da rufe bakin ta.
"Yakin cikin gida?" Ta kuma maimaita tambayar,
"Eh Innayoh, idan har muka basu goyan baya yanzun zasu iya ɓullo mana ta inda bamu zata ba, amma idan muka koma gefe dole shiri zamu yi na tsawon dawowar shi, dan haka kiyi kokarin ganin kin taushi Fulani Aminatu" inji Sarkin gida,
Wato al'amarin yana son kasancewa ne Sarkin Yawa ya fi Sarkin karfi, duk yadda zasu yi ba zasu iya ba, dole sai sun ninka karfin sarki Bello.
"Shi kenan, Insha Allah zan kiyayye kuma zan yi kokarin tausar zuciyar ta." Inji Innayoh, sannan suka bar shashin, cikin gidan kuwa babu wanda ya kuma d'ago zancen Fulani Aminatu kowa ta kasan shi yake, dake abin ya hadu ta ko ina sai gashi kowa yakin yake da son samun damar da yake ganin shine mafi alkhairi a gare shi.
*
Ana ruwan saman amma zuciyar shi tayi nauyi, kallon shi sarkin yaki yayi.
"Allah ya baka nasara idan suka yi nasara akan mu fa?" Juyawa yayi ya kalli sarkin yaki sannan ya dauke kai, abin ya bashi mamaki.
"Idan ka dawo daga yaki kazo ka samu wani yana tarayya da me dakin ka ya zaka ji?"
Shiru yayi bai kuma magana ba, shima Sarkin yaki maganar ta dake shi sai ya ce.
"Tuba nake, Allah ya huci zuciyar ka" murmushi sarki bello yayi tare da cewa.
"Ba fushi nayi ba, ai bana fushi akan abinda na san zan dawo maka da abinka"
Tsayawa suka yi a kasar wani dutse na dan lokaci, kallon rundunar yayi sannan ya ce musu.
"Ban umarce kowa da shiga yakin ba, ku bar ni nayi yaki domin kimar mata ta. Dan haka ku naku yan kallo ne"
"Allah ya baka nasara, babu abinda zamu yi kenan?" Sarkin yaki ya tambaya.
"Babu abinda zaku min yakin nawa ne, ba na kowa ba. Idan kuka shiga bani da bakin da zan kare al'umma ta balle Mata ta, idan nayi kuwa har abada ina cikin kundin tarihin masarautar Gobir."
Shiru suka yi na wani lokaci, kafin ruwa ya tsaya aka cigaba da tafiya, har zuwa filin da mutanen Sahil suke.
**
Masarautan Sahil
Kallon tursi yayi da take murmushi, sannan ta shafa kokon kan dan adam da wani irin ruwan dalma tana faɗin.
"Arkhan! Leka ka ga uwar Sarkin gobe duba kyakyawar surar da Allah ya mata"
Lekewa yayi, yana murmushin jin dadi, kallon Aminatu yayi da Innayoh take rike da ita.
"Amma ina ɗaya abokiyar tafiyar take?"
"Ba a san inda take ba, duk iya bincike na bamu ga inda take ba, amma nan da wasu shekaru zata bayyana abinda Uwa hil ta gaya min kenan"
"Dukkan su jini daya ne, bayyanar ta zai kuma haifar da wata tarzoma ne?"
"Idan muradin ka bai cika ba, dole sai bayyanar ta zai cika maka duk wani muradin ka"
"Bana fatar haka"
Dan d'ago kai tayi ta ce mishi.
"Sakon mu ya shiga cikin gidan, amma kalli yadda karfin abin jikin ta ya lalata shi" kurawa kokon kan yayi idanu.
Lokacin da Aminatu ta ture baiwar da tazo rike ta, wani irin siririn kifiya ne yayi wani irin fitar bazata daga hannun ta.
"Tabbas ita ce!"
"Dama na gaya maka tana nan"
Wani irin dariya yake fadar yana ɗauka, sannan ya ce mata.
"A shiga shirya min turaka na, yau akai min Yan mata masu tashen balaga, dasu zan gurje amarcina kafin zuwan ta "
A duk lokacin da sarki yake cikin fara'a da farin ciki ana ware mishi yan mata masu tashen balaga, wadanda nonuwar kirjin su basu kai ga girma ainun ba, masu cikakken budurci wadanda zai kwanta da wannan zai sauka da wannan, haka tsarin shi yake, idan aka gama da su za a kai su can cikin gidan shi n bayan masarautar a iya yanzun ba 'a san iya adadin matan shi ba, domin a labarin kunne ya girmi kaka, an ce sun kai dari da wani abu, kuma bai fasa kudirin shi ba.
Har dakaru zasu mike ya ce musu.
"A nima min har a can wurin dattijon nan domin matan su, sun fi sauran matan nan tsafta, wani irin kamshi yake fita a kasar su, jikin su kamar ana wanke su da ruwan madara" gyada mishi kai suka yi, duk da su matan wadancan kabilar idan ya kwanta dasu, bada jinin su ake ga hil, sauran dake nasu ne babu abinda yake faruwa.
Dan haka kafin Sa'a uku, an shirya yan matan an kai mishi turakar shi, sa nan aka zo aka gaya mishi.
Murmushi yayi sannan ya ce.
"Tursi me zaki bani, domin naji dadin juya kwankwasona."
Rufe idanu tayi sannan ta bude da sauri.
"Ka kori yarinyar wurin dattijon nan babu alkhairi a tare da ita, kashe ka zata yi" sannan ta mika mishi wani kofin zinari, shanyewa yayi sannan ya kalle ta.
"Toh naji zan Kore ta" ya fada bayan ya mike, ran shi ya gama biyawa akan yarinyar tursi ta shigo da wani magana ba zai tab'a yarda ba, sai ya lashe kirjin ta zuwa kasar ta da yake fitar da kamshi nan.
*
Fulani Aminatu
Sai da rana ta fadi sannan ta bude idanunta, kanta yana sarawa a hankali ta mike tana kallon Innayoh.
"Baki tashe ni sallah ba?"
"Eh wai naga baki jin dadi ne" a hankali ta shiga ban daki, ta tsuguna zata yi fitsari jini ya sauko mata, sai da ta gama fitsarin ta wanke wurin sannan ya haɗa ruwa tayi wanka, sai da tayi wanka sosai, sannan ta shirya ta fito,
"Innayoh bani kayan wankina" ta fada tana neman wurin zama. Dauko kayan tayi ta mika mata, sai kamshin turaren suke, ta koma ban daki ra gyara jikinta, sannan ta fito saka wani riga tayi iya kwanjin ta, sannan ta kwanta tana kallon tagar dakinta.
"Ba zaki ci abinci ba?"
"Innayoh na koshi" ta fada tana kallon waje.
Yadda ta juya baya ba karamin damuwa ta saka Innayoh ba, dan haka ta zauna a wurin har aka kira sallah Isha sannan ta fita, sai lokacin ta fara kuka, kuka sosai take tana jin kamar ta mutu ta huta da wannan yanayin da take ciki. Har taji motsin Innayoh sannan tayi shiru kamar tana barci.
"Gashi inji Galadima wai a baki wannan kisha"
Tashi tayi zaune tana kallon ƙwaryan zuma ce me hadi,sai da ta sha sosai sannan ta koma ta kwanta.
*
A can wurin kuwa har dare ruwa ake, dan haka sarki Bello da jama'ar shi, komawa ƙasar dutse suka yi aka kwana, bayan sun yi sallah asuba. Aka tura dan aike ya gaya musu ga sarki Bello da tawagar shi.
Aikuwa kamar jira suke suka fara maguzanci, ta hanyar bubuga abu ana ihu.
Sai da aka bari rana ta fara ketowa, sannan dukkan su runduna biyun suka bayyana a filin,
Shugaban rundunar sahil, ya fara magana da cewa.
"Zamu kyale alummarka idan ka bamu Aminatu, idan kuma ka ki zamu yake ka har zuwa masarautar ka"
Murmushi sarki Bello yayi sannan ya ce mishi.
"Toh Allah ya baka sa'a, amma da sharadi idan kayi nasara a kaina, ka ɗauki Aminatu. Domin Ni daya zan yi yaki da kai, sannan na baka damar kwace masarautar. Da yardan Allah idan ni nayi nasara akan ka, zan kashe ku baki daya kuma ba zaku kai labari ba"
Dariya suka saka mishi, musamman da suka lura da sarki Bello bai kai shugaban runduna wato Murad.
"Toh shikenan, Hil ta bani nasara" shugaban runduna ya ce.
"Alhamdulillahi Ubangiji ka bani nasara" inji Sarki Bello,
Komawa gefe lati yayi tare da shugaban runduna ya ce mishi.
"Ya shugaba shi daya zai yi yakin ba tare da yaji tsoron yawan rundunar mu ba, sannan kaga jama'ar shi basu da yawa, akwai abinda ya taka matukar bamu samu yadda muke so ba, zai karar damu dan haka ka wakilta wasu, yaki da shi muga yadda zamu shawo kan shi a yaƙin"
"Na gamsu da bayanin ka dan haka a ware mutane na musamman mutum goma su ji dashi"
Haka kuwa aka yi, ba wani dauki lokaci ba aka fara yaƙin, kamar zasu samu nasara akan shi, amma Allah ya bashi nasara, bai kashe su ba amma kuma ya nakasa su. Sannan ya koma gefe yana haki ya ce musu.
"Ka haɗa kan rundunar ka, ku bar min da'irar wankina" inji Sarki Bello.
"Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare."
"Toh Allah ya bamu nasara" aka sake turo mishi su.
Allah ya kuma bashi Sa'a kan su, haka yakin ya kasance babu sassauci sai lokacin sallah ne kaɗai ya sa sarki Bello hakura da yakin akan sai bayan la'asar, haka ce ta faru.
...
"Lati gaba dani zai kara na ga dai jikata min dakaru yake kuma yana yaƙin kamar wanda yake da karfin ifiritai" Murad ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 39