Share this page
ya girgiza kai. "Innayoh akwai abinda yake zagaye da shi, wanda nasan ba zai min dadi ba, amma gashi yana misho dad'i" Kallon ta Innayoh tayi, ita kanta bata san me zata ce mata ba, amma tabbas daga jiya zuwa safiyar yau taga sauyi a tattare da Gidado, amma dan ta kwantar da hankalin Bintu sai ta ce mata. "Kinsan wani lokaci kana tashi da farin ciki ko a kasin haka" "Innayoh ba haka bane, da alamun nice nake Hauka ta amma ga shi ya samu farin cikin da yake bukata" "Ki daina saurin yanke hukunci haka, bana jin akwai wani farin cikin da zai samu a tare da shi bayan ke" inji Fulani Aminatu, juyawa tayi tana me sunkuyar da kanta. "Fulani hasashen mu ne kawai, amma ai masu azancin magana sun ce labarin zuciya a tambayi fuska, na bar ku lafiya" Kamar wadanda ruwa ya cinye su aka rasa wanda zai amsa mata, sai gashi sun mata rakiya da idanu" Tana fita wurin shi ta nufa, ta zauna tana kallon shi yana rubutu da ajami, kafin ya d'ago kai yana kallon ta. Yanayin da ya ganta ne ya sashi ajiye alkalami da fatar da yake rubutun shi. Shiru yayi yana hango tulin laifin shi a gare ta, sannan ya haɗe hannun shi biyu yayi ta bata hakuri, a hankali hawayen da take dannewa ya shiga saukowa, akan kyakyawar fuskar ta. Baki daya ya rasa yadda yake ji, kawai tsintar kan shi yayi da kai hannun shi yana goge mata fuska, ya fara bata hakuri. "Ka daina ba ni hakuri, ka dawo daga Sudan amma ka gaza takowa kazo inda nake, sannan kayi wani tafiyar ka. Koda ka dawo ma mantawa kayi dani" Da hannu ya mata alama da tayi hakuri ta saurare shi. Shi kan sa yasan yayi mata laifi dan haka yayi ta bata hakuri. "Kayi hakuri nasan nayi laifi amma ki gafarce ni" yadda ya shiga damuwa, yasa ta hakura suka shiga hiran su, bayan ya dauke rubutun shi da yake akan Anum, dan yasan Fulani Bintu tana da ilimi arabiya kuma tana iya karance abinda yake rubutawa, duk fasalin da yake akan Anum bai dauka akan ya tsunduma a cikin soyayyar ta bane, a'a amma yana jin wani mugun girma akan ta, wanda yake yankar mishi da gaba. Kura mata ido yayi, kafin ya sauke kan shi kasa. Haka suka yi ta zaman shiru wanda dama dan halin Gidado ba magana yake ba, itama kuma sai ta zama kurma a gaban shi. A karon farko da yaji kamar ta azza mishi nauyi ne na shiga rayuwar shi, baya jin zai iya kin gaya mata matsayinta a gare shi amma maganar gaskiya ita ce bai san me yake ji game da yarinyar can ba. * Kano Tun bayan fitar su yakin ya samu raunika uku, wanda ya haifar mishi da zubar jini, sosai ya jikata amma taurin kai da kafiya irin ta gado, bai saka Lamido ya sare ba, sai da ya sare kak shugaban maguzawa, sannan ya dawo, tun kafin ya isa wurin Rundunar su ya fadi, sune suka karaso wurin shi, aka dauke shi. Sannan aka mai da shi masarautar Kano akan lokaci, koda aka shiga da shi gidan sarautar sosai aka tara masu maganin masarautar aka gaya musu shi Surukin gidan ne a kula da lafiyar shi. Bakin kokarin su, sun yi akan shi asalima sai da suka yi kamar ba zai tashi ba, kafin Allah da ikon shi ya basu ikon nasara aka shawo kan shi. Sai da ya kwashe kwanaki goma yana kwance, baya tashi saboda yankar da suka mishi cikin shi. A ranar da ya cika sati biyu,ya fara fita daga cikin dakin da yake, yana bin masaukin shi da idanu. A hankali yake takawa har ya fita can wajen masarautan, yayi hanyar bayi. Wai dan jikin shi ya warware yasa shi wannan zagayen, a hankali yake tafiya yana kallon yanayin masarautan, sai da yayi yar tafiya kaɗan kafin ya iso wani wadataccen lambu, wanda yake dauke da dashe dashe iri iri na nau'in ƴaƴan itacce, dake ya iso ana bayi ne, kamshin kasa ya ja ra'ayin shi ya shiga cikin lambun, muryan mata yaji a dan gaba kadan, sai bai bi wannan hanyar ba, ya bi wani a hankali yake takun shi irin ta zaratan maza, wanda suke cike da samartaka. Yake ratsa cikin lambun. Har ya isa faffadar fili tana zaune ita ɗayan ta, tayi zurfi cikin karatun a wani irin fata take karatun ta, bai lura da ita, domin shi yana bin wuri me damshi ne, da inuwa ya zauna,. Ita kuna taji motsin sa, bata zata namiji bane, ta dauka bayin ta ne, ta d'ago kai zata daka musu tsawa, idanun ta ya hango mata kyakyawar halittar da ta jima tana mafarkin samun shi a duniyar ta, tun daga kafar shi take kare mishi kallo har zuwa kyakyawar surar jikin shi wanda yake nad'e irin ta sadaukan maza da suka san Meye ake kira kyau, wato fari ne wanda ba za a kira shi da fari kal ba, domin yana da duhu kaɗan, yana da fadin kirji da murda'murd'an kwanji, daga cikin shi a wani tsuke yake, amma faffadar kirjin shi wanda yake dauke da cura-curan kwanji, suka kara fitar da halittar shi,fuskar shi dauke take da zagayayyen saje, da wata kakkauran gashin baki, sanye yake na rigar saki, wato yar shara mara hannu, goshin sa nad'e yake da farin kyale sabida ciwon da yaji a wurin yaji har Goshin ta, idanun shi kuwa fararre ne, amma kwan cikin idanun ruwan gwal ne, har wani daukar budewa yake da tufewa, gashin kan shi me laushe irin ta Fulani ko ace shuwa Arab, sai wani daukar idanu take baka kirin irin ta hausawar ainihin, wato gobirawa. Fuskar shi me ɗauke da kamala da nutsuwa ta kara kyau da haiba, kwarjinin shi tana bayyana ne a duk lokacin da ya motsa fuskarsa, Lamido yana da wani irin kyau wanda sajen shi da suka kwanta ya kara bayyana kyan shi, idan ka gan shi zaka dauka irin larabawan kasar Qatar ne ko na kasar Yemen, domin yanayin shi zubin su ne, Ita ɗaya ta gama wasafa kyan shi, tana kara kallon shi lokacin.da yake kara kusantowa gare ta, dauke kai tayi tare da jan mayafin ta, zuciyar ta yana wani irin bugawa. Ta cikin mayafin ya ce mishi. "Karka karaso nan." Sai lokacin ya dube ta,.bayin ta sun iso suna kokarin tsalla ihu. "Nan lambun matan cikin gida ne, an haramtawa namiji shigowa nan maza kafita" bai dube su ba, kuma bai yi abinda suka umarce shi ba, dan haka ya cigaba da matsowa kusa da su, mikewa Fulani Dijah tayi cikin nutsuwa. "Duk da bamu san waye kai ba, yana da kyau ka mutuntta mata don Allah" juyawa yayi yana me barin wurin, va tare da ya ce musu kala ba. "Uwar ɗakina ai shine bakon mayakin da ya shiga yakin nan" wani irin dafe kirjin ta, tayi tana me d'aga mayafin ta. "Kika ce me Jimo?" Da sauri ya watsar da littafin ta, ta bi bayan shi. Har yayi nisa ta sha gaban shi. "Kai ne ka katse min farin cikina. Ko ba kai bane ake son a hada ni da shi dan Sarkin Gobir ko? Shine ɗan niman suna ka shiga yaƙi?" Bai kalle ba, ya ratsa ta gefen ta ya wuce abin shi. Sake shan gaban shi tayi cikin fada da masifa. "Akan me sai ni? Baka da buri ne?" Wani irin kallo ya mata daga kasa har sama, sannan ya tabe baki ya wuce ta. "Baka da imani, baka da tausayi domin cimma burin ka shine zaka lalata min tawa burin. Ai nasan kome akan ka, tun wuri ka janye domin ba zan tab'a auren wanda aka kama Mahaifiyar shi da abu..." Tunda yake bai tab'a fuskantar wani cin zarafi ba sai yau,.a fusace ya kaiwa bishiyar ayabar da yake wurin wani bahagon naushi, karyewa yayi, ita kanta sai da ta razana. Takowa yayi gabanta, ta fashe da kuka zuciyar ta yana wani irin bugawa, ta kame tare da cewa. "Kayi hakuri ban san ranka zai b'aci ba, don Allah ka gafarce ni. Amma nima ina da buri me yasa ba za a barni Nacika ba, sai a min karantsaye sabida kai, dan Sarkin kofa nake so don Allah" tana fadar hakan tana kuka, kuma har lokacin gabanta bai daina faduwa ba, shi kan tun da ya ga ta rude ya bar ta a wurin yayi tafiyar shi, ba zai kuma kwanan Kano ba, ita kuma ko a kafa aka daura mishi ya yafe ta, abu biyu da bazai tab'a hada kowa da su ba, sune Ammyn da Gidado, wannan cin zarafin da tayi mishi ya dakushe duk wani abinda za a bashi akan ta, baya kaunar ta bai taba tsanar wani abu a rayuwar shi kamar ita ba. Baya fatar ta zame mishi ƙaddara. Ran shi kara ɓaci yake, yau da namiji ne wallahi sai ya kwashe hakoran shi a ƙasa, amma mace ce bai da yadda zai mata domin matukar ya mare ta sai ya suma balle kuma ya dake ta, yayi imani da Allah sai an kuma haihuwar watan ta, Haka yayi ta haɗa kayan shi, yadda ranshi ya ɓaci, gurnanin biyuna yaji a a bayan shi, juyawa yayi yana kallon shi, kafin ya cigaba da hada kayan shi. "Dawo" domin ya san yau ba ita ba barci dan ma ba tagwai bane shi ai iyaka ne, "Kyale ta" ya kuma gaya mishi, kwanciya yazo yayi a kusa da shi, ya na jiran shi har ya gama, sannan suka bar dakin da Masarautan baki daya, idan ya tuna maganar ji yake kamar ya tarwatsa ya huta, sabida ciwon da zuciyar shi take yi, a yanzun ya fara hango dalilin da yasa Gidado ya nace mishi akan maganar Ammyn sai yaki tanka maganar, shi bawai yana kin maganar bane, a'a baya son ya d'aga mata hankali ne, yafi son ya bita a laluma, yasan har yau tana son mijin ta, sannan yana son yayi amfani da yardan ta, wurin nima mata hakkinta, bayan haka baya son saka kan shi cikin al'amarin masarautar su. Abinda ya fahimta ita da Innayoh suna boye wani al'amari me girma, dan yakan ga sun zauna suna tattaunawa akan rayuwar ta, shi bai cika son takurawa ba, shi yasa a kome yake kamewa, amma wancan mahaukaciyar yarinyar ta mishi sanadin farin cikin shi. Sannan ko babu kome ta saka shi son ta koma ya bincika rayuwar mahaifiyar shi, amma yaji zafi sosai. * M. Gobir Durkushe take bayan Bingel, ana zuga mata bulala, tana kuka Mahaifiyar ta tana tsaye tana kallon ikon Allah, shi kansa waziri ya kasa magana, shigowar Barkindo wanda ya cab'a kwalliya zai tafi wurin Anum ya shigo mata sallama, yaga Haima ana zane ta. "Meye haka? Meye laifin ta?" Ya ture me zaneta, yana me tsayawa a gabanta. Ajiyar zuciya Mahaifiyar ta tayi, tana me karasawa wurin Haimah da take kuka. "Meye tayi kake tambaya na?" "Kai cigaba da dukar ta" "Idan ka cigaba da dukar ta, sai ba saka an sare maka hannun ka" kowa yasan Barkindo ko takobi bai taba dauka ba, dan haka da yayi maganar uwar bata zata zai iya aikatawa ba, dan haka ta bugawa badakaren tsawa, shi kuma ya zare takobin da yake kugun me tsaron kofar ya saka a wuyar badakaren tare da cewa. "Rayuwar ka ko mutuwar ka..... 🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️ *Mu hadu bayan babban sallah 🤣😂🏃😹* #Mai_Dambu [6/8, 1:04 PM] Empress Anum: KALLABI..! A Tsakanin Rawuna EWF BABI NA ARBA'IN DA TARA "Yazidu!" Ta daka mishi tsawa, juya fararren idanun shi yayi akan ta, da suka yi wani irin ja, cikin yanayin shi me kama da shagwab'a karfin hali ya ce mata. "Ki dakatar da umarnin ki" yadda yayi maganar dole ya burge ka, domin yayi maganar cikin yanayin cikakken namiji a turance ana cewa (gentle tone) irin cikakken me fada magana da cikawa, takaici ne ya cika bingel ta ce wa Badakaren. "Kuje" haka ya saka kai ta fita, cillar da takobin yayi tare da kallon hannun shi da yayi ja, alamar bai saba ba. D'aga Haima yayi, yana jin shashekar kukan ta, na tab'a shi sosai. "Idan hukunci ne ni ya dace a hukunta, ba ita ba domin ai ita yar aike ce, a musulunce ba a taba jakade. Domin aikin shi yake da aka saka shi, Innah me kike so nayi ne? Me yasa ba zaki zauna da kowa lafiya ba! Mama riketa ku isa gida" Aikuwa yana juyawa zai bar wurin Haimah ta nemi zubewa kasa, da wani irin sauri ya d'ago ta. "Nagode" ta ce mishi, daukar ta yayi tare da fita da ita har bangaren su. Yana kaita bai kuma bin kan uwar shi ba, ya wuce wurin Anum abin shi. -- Sai da suka fara zuwa gidan su, aka ce ta tafi kiwo. Dan haka da azama ya karkata kan dokin shi, ya nausa cikin dajin. Yau tayi kiwo ta gaji dan haka ta samu kasar wata bishiya me sanyi ta jingina, tun daga nesa ya hango dan haka ya sauka akan dokin ya daure, a hankali yake takawa har wurin ta, durkusawa yayi a gaban ta sosai, ya kai bakin shi, zai sumbaci bakin ta. Aikuwa garin ta dakatar da shi ta kaiwa shugaban ƙaramar hukumar wandon shi suka, sai da idanun shi suka juya, kafin ya tintsira can ya suma. "Wayyo Allah na" ta toshe bakin ta tana kallon shi, goran ruwan ta, ta fara sheka mishi, tana yi tana kallon shi, ya farka amma dake yana son ya kuma rudar da ita sai ya dauke numfashin sa, sai da ta kai fuskar ta domin jin ya farka, kawai taji lebban shi masu sanyi akan kumatun ta, sai da ta wani irin zabura, kafin ta d'aka mishi bugu. "Wayyo Allah" sai da ya mike zaune yana kallon ta, yana murmushi. "Kin zata na mutu ne?" Kwallar da take dannewa ne ya zubo mata. "Kasan ka bani tsoro, wallahi na zata ka mutu ne." Ta sake kuka me ban tausayi, zama yayi yana kallon ta. "Kiyi hakuri kinji" "Toh ya zanyi da kai? Ka addabi rayuwata ka takure min da nacin balai',mahaifiyarka bata sona idan ka dage sai ni zaka iya samun matsala da ita don Allah ka tafi a rayuwata" wani irin fisgota yayi, ya haɗe bakin shi da nata sai da taji kome na kanta ta tsaya cak, da wani irin zafin nama ta kwace bakin ta a cikin nashi, tare da kai mishi duka a kirjin shi, rike hannun ta yayi ran shi ya gama b'aci ya ce mata. "Meye kike bukata da na zama wanda zaki amshe ni a matsayin abokin rayuwar ki?" Cikin kuka ta ce. "Wallahi bana son ka ko kaɗan, asalima baka min ba ne, don Allah ka rabu da rayuwata, bana sonnka ne da ina son ka zan amshe ka" Mikewa tayi a hankali, zata bar wurin ya mike shima ya rungume ta, ta baya yana jin wani irin yanayi na tashin hankali a zuciyar shi. "Anumullah karki sani fadawa tashin hankali, Anum ina son ki da zuciyata, don Allah ki soni mana, wallahi ba zan tab'a barin kiyi kuk...." Aka buga mishi itacce a keyar shi, ajiyar zuciya ya ja, ya zube a bayan ta..zagaye su aka yi mutane sanye da bakaken kaya. A hankali ya janyo shi tare da tallafe kan shi suka durkusa tare. Kwalla ne ya cika mata idanu. "Yazid tashi don Allah" ta faɗa cikin kuka, jijjiga shi take tana kuka. "Ku dauke ta, ku bamu shi mu gama da shi" Haka suka janye ta tana kuka, tana kokarin kamo shi, "Mai gida gaskiya wannan yar fulanin ba laifi ko na sha ruwa ne" Fisgo ta yayi tare da d'aga rigarta, a tsora ce ta take mishi kafa da mugun karfi, sai da ya fasa ihu, ya kuwa tsinka mata mari, tare da finciko tsumman da take daure kirjin ta da shi ta fara kokarin kwabe shi. "Aah ahh!" Ya mike yana tangadi, daukar itaccen da suka buga mishi yayi ya kaiwa mutumin bugu, sannan ya maxa ya cire rigar shi ya bata, aikuwa suka rufe shi da duka, kamar zasu kashe shi, wani irin ihu tayi, a hankali ta zube a wurin sakamakon naushin ta da aka yi ta baya, gyara mata kwanciya yayi tare da warware daurin yana me arba da. Karan kukan zuma me hade da gurnanin zakin, a lokaci guda suka rude. Kafin su ankara sai sake musu kibbau ake kuma abin mamaki shine a lokaci guda ake sake musu uku uku, warware mayafin shi yayi shi da Sarkin Gida. Wato ba kowa bane sai sarki Bello. Ganin yadda Sarkin gida ya nufe su, ya riko hannun shi. Nuna mishi yadda Barkindo yake kokarin mikewa, komawa bayan wata bishiya suka yi suna kallon, yadda ya dauke rigar shi ya lullube ta, sannan ya fashe da kuka. "Tir da wanda ba zai bawa soyayyar shi kariya ba, Anum na gaza" ya fada da karfin kamar tana jin shi, saka mata rigar shi yayi. "Waye shi?" "Baka gane shi ba ne? Ai Yarima Barkindo ne wato Yazidu" kura mishi Idanu sarki Bello yayi, suka fito daga bayan itaccen, tare da nufar wurin su. Yana ganin su ya mike yana me daukar takobi,.yana nuna musu. "Karku zo nan" murmushi sarki Bello yayi sannan ya isa gaban shi, ya saka mishi kafa, tafiya yayi zai fadi ya riko bayan rigar shi ta ciki, domin ya lullube Anum da alkyabbar shi ce, shake wuyar shi sarki Bello yayi yana faɗin. "Namiji baya kuka a gaban mace haka kuma,.karka sake kuka a gabanta, dan haka dauke ta mu tafi." Ya sakar mishi wuyar shi sannan yayi gaba, asalin abinda ya faru, Baffa'm ya fito farauta ne, shi da Sarkin Gida sai yaji ihun Anum. Shine suka tawo wurin su, daukar Anum Barkindo yayi ya sakata a kadadar shi, sannan ya juya ya nufi hanyar da suka fito, shi kuma Baffa'm ya tsaya tona rami, ya zuba mutanen domin matukar aka san shi yana raye abubuwa dayawa zasu faru, sarkin gida ya kada mata shanun ta, suka dawo gida. A hankali ya kwantar da ita, yana kallon Galadima da yake gidan, kamar yasan shi amma ba zai iya cewa ga inda ya san shi ba. Gara Sarkin gida yana yawan ganin shi a cikin masarautan. Kallon rashin yarda yayi musu, shigowar baffa'm ne ya sashi sauke ajiyar zuciya, yana kallon su. "Rayuwar shi tana cikin hatsari domin sun kawo mishi hari, sannan sun taba wacce babu abinda ta sani, ina ga a raka shi zuwa gidan kar ya Kuma fitowa. Ka godewa Allah ka tsira yau gobe na zaka tsira a hannun su ba" "Toh ranka ya dade, za ayi haka" inji Sarkin gida. Sannan ya saka Barkindo a gaba, zasu fita. "Ba zan tafi ba sai na san su waye ku?" Shafa kan shi Baffa'm yayi yana kallon Galadima sannan ya ce mishi. "Barkindo Yazidu, Ni ne mahaifinka sarki Bello" cak ya kura mishi ido. Zunzurutun ya shiga kaduwa, bakin shi yana rawa ya ce mishi. "Baffa'm!" Sai ga hawaye sharr. "Zan gayawa Inna kana raye" Girgiza mishi kai yayi, sannan ya ce mishi. "Idan kayi haka zasu kashe ka, sannan zasu karya ta ka, karka sake kayi magana domin a haka ma niman rayuwar ka ake" kuka ya saka mus riris. Tsaki Galadima yayi ya fita domin wallahi baya jin Yazidu dan Bello ne ko za'a kashe shi a dawo da shi. Dan Banza min yaro Anum, ganin aika-aikan Gidado tayi kawai ta firgita baya jin sun kuma haduwa har ya bar kasar, wannan me zubin yan daudun ne dan Bello? Ya wani harari kofar dakin, domin haushin su yake ji baki daya. A hankali ya koma gefe ya tsaya har Baffa'm ya raka Barkindo Yazidu waje tare da shafa kan shi. "Babu abinda zai kuma samun ka, Sarkin gida rike hannun shi" Haka suka tafi, lumshe idanun baffa'm yayi cikin nutsuwa, hawayen tausayin Yaron ya sauko mishi, domin yanzu ya kuma kara tabbatar da haka, maganar shugaban rundunar Sahil yana kara dawo mishi ruhin shi. _Kasan abinda zaka yi tun wuri amma ba makawa sai sun shiga da'iran soyayyar ka da Aminatu! Kayi sake dayawa makiya sun samu mafaka a tare da kai, sun san sirrin ka sosai akan Aminatu. Ka sadaukar da haka a matsayin bata kariya ko kuma ka zabi mutuwar ta a matsayin abinda zai kashe wutar da take ruruwa a zukatan makiyan ka_ Shafa kan shi yayi yana kallon bayan. "Kana tsammanin zai iya shiru da bakin shi?" Inji galadima, "Gaskiya ta bayyana min a kowacce ƙaddara akwai faduwa da nasara, kafin ikon Allah ne ya kawo Anum cikin mu, a yanzun wannan yaron makami ne me linzamin da zamu harba shi cikin masarautan! Tunda mulkin shine zai gada idan bana nan yanzu nasan zai fara nashi kokarin ne, domin fahimtar waye ne? Shi yasa na gaya mishi nine mahaifin shi" Shiru Galadima yayi sannan ya ce. "Amma ina ganin kamar babu fa'idar fadar haka domin wannan yaron da Yan daudu ya dace ba Yarima ba, kaga kallo daya kayiwa Gidado jinin ka ya tafasa wannan kan ban ga kome ba sai karin takaici da bakin ciki." "Amma ai kasan dana nane! Idan nace zan ki amsar shi waye yake da shi sama dani?"inji baffa'm. "Dan Yakubu dai! Wallahi wannan ba danka bane, na gaya maka gaskiya wannan da dan daudu dan me bin mata bayi katangar su" "Ka fara bani haushi" baffa'm ya gaya mishi. "Yo ba gwara na baka haushi ba, wallahi duk ranar da Aminatu tazo sai na gaya mata kayi aure a boye" ya fadawa Baffa'm haka. "Alamarin ka yana bukatar tsayawa ka'in da na'in domin makarai sun fara kokarin maka kutse shugaban magulmatan Gobir" Wata dariya Galadima ya bushe da ita yana me tafawa da Baffa'm, yana kara jin kaunar shi sama da koda yaushe. "Akwai abinda Uba ga Lamido Hassan yake boye da shi" "Babu kome domin wannan bakin nawa aminatu ta rufe min shi duk ranar da ta dawo ta cinye min shi zan bude shi fa magana" "Na shiga uku! Bari sarkin gida ya zo ya nimo mana yar bazawara mu bawa Sarki Bello damar dawo da samartakan shi" "Ai har abada babu macen da zata iya da Mai Martaba na, sai Aminatuna Minani na, ita ɗaya ce zata iya zare min idanu idan...." Numfashi yaja, ranar da suka yi rayuwar aure na karshe, ya dawo mishi fil a ran shi, ganin kome yake kamar yanzu abin yake faruwa, ba zai manta da shekaru ashirin da bakwai baya, tsabar ya rude rasa inda zai tsomma ran shi yake ji ranar, a daren da aka haifi Yarima Yazidu, ji yake idan bai raba jikin Aminatu ba zai iya mutuwa, baki daya a daren ko nutsuwa babu a tare da shi, aikuwa lokacin da ya shiga ƙoƙarin ratsa tsakanin ta, me ta zare idanu tare da jan numfashin ta, idanun ta a warwaje, ta k'amk'ame tana me ƙoƙarin fashewa da kuka. Ilahirin jikin ta rawa yaƙe tana ji kamar ta ture shi, duk da zazzaɓin da ya rufe ta bai hanata k'amk'ame shi ba, tana sauke ajiyar zuciya, shi kan shi ba zai ce me yake ji ba, amma zazzabin da yake ji ya haura tunanin shi. Hawaye ne ya gangaro mishi, daren da na zai manta ba, daren da ta zame mishi daren su na karshe, dare me cike da tarihi da ban mamaki, daren da ya rubuta ba zasu kuma cimma shi ba har abada... _Da matukar ciwo cutarwa ne me girma! Mugunta ne mara iyaka a rabaka da abinda kake so_ 😂🙄 Cewa nayi fa bayan babban sallah kun _cika min tangaraho da sako Fisabilillahi! Ai kuma ya dace ku kara yawan comments da vote 💪 Wattpad da ku nake! Whatsp gaskiya kuna kokari Wallhi! Musamman GRP dina! Ba zan manta da ke ba, Laweesah Babbar Yar adawar BARKINDO! Maman Noor! Yar gaskiya da amanar Sarkin Gobir na gobe! Yan fitilar Hakaya masoyan BARKINDO Kenan ban ware kowa ba, kune asalin masoyan BARKINDO_ #Mai_Dambu https://www.wattpad.com/1233720659?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published KALLABI..! A Tsakanin Rawuna EWF BABI NA HAMSIN CIF ___________ _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan

Chapter 25 of 39