Share this page
kai yayi, domin kosu abokan karatun shi bai nuna musu ya samu lafiya ba, kawai ya a mu'amalar su da yadda ya saba, lokacin da suka tambaye shi Lamido ya basu labarin ya zama sarki sai da suka tausaya mishi, domin burin shi ne ya zama sarkin amma rashin magana yasa an bawa dan uwan shi. Haka yayi ta tafiya da ciwo a tsaye, duk ya kare kamar kudin guzuri. ** Yanayin da ake zaune lafiya da sauke hakkin kowa yasa Baffa'm ya gamsu lamido ya dace dama da mulkin, gashi ko ina aka zaga sai addu'oi da fatan Alkhairi, haka yasa duk zaman da zasu yi su hudun nan akan yadda zasu kara nunawa lamido yadda ake mulki da hukuncin sa, Baffa'm sarkin gida, Galadima, da Zakaria. Duk wani cigaba na masarautar suna kokarin kawo mishi. Sai dai abinda ba za a rasa ba. Barcin la'asar take yau, cikin barcin kamar wata uku da suka wuce haka yau ma aka kuma mika mata ta'aziya, tare da bata hakuri, farkawa tayi taga ashe kuka take a barcin ta. Gidado ne ya fado mata. Mikewa tayi ta nufi wurin Innayoh. "Lafiya?" "Innayoh ina son ganin Gidado wallahi bai da lafiya ni dai Allah yasa ba mutuwa yayi ba!" "Kai haba Amunatu wani mutuwa kuma? Kawai yana nan lafiya" Bata labarin mafarkin da tayi tun maiduguri, shiru suka yi kafin kuma Innayoh tace mata. "Wani lokaci mafarkin bayan la'asar ba gaskiya bane domin akwai shaidanu da suke amfani da haka, kuma ai babu kyau." Ta amince da abinda Innayoh ta fada ne kawai amma zuciyar ta bai mata ba, dan haka suna cikin tattaunawa Lamido ya shigo ya zauna yana kallon su. Da gudu Anum ta shigo tana haki. "Ammyn kice ya barni don Allah zan tafi rugar gona ce" Kallon shi Ammyn tayi sannan ta ce. "Ka amince ta tafi" "Toh na Amince" ya mike yana dariya, Fita suka yi yayi kasa kasa da murya. "Sai kin bani ladan amincewa" "Kai Hamma na lura baka kome domin Allah ba, wannan ba halin mutanen kirki bane" "Toh ko na fasa?" "A'a indai ba zaka ji ma ba, don Allah kar ka sani barci" Dariya yayi kasa kasa, tun a zauren shi suka fara jaraba, itama Yar duniya ta zama sai yadda yayi da ita, dan haka suka kashe kan su akan jaraba, har cikin dakin su, sai da suka yi fatali da kome, cikin wani yanayi mara misaltawa, yau ce ranar farko da zai ce yaji dadin ya rabu da abinda yake ji, yanzu san yayi aure. Da ashe da zai rage maran shi ba ba auren yayi ba, wani irin rungume ta yayi yana sauke ajiyar zuciya, domin iya nutsuwa ya samu bai kuma san me zai ce ba. "Anum!" Ya kira sunan ta. "Na'am Saraki" "Ina son ki" "Toh yau na jiyar da saraki dadi ne?" Ta fada tana rufe fuskar ta a kirjin shi. "Hmm" ya fada yana kara matso na shanun shi, ai kuwa ya sake mishi wani sauti da ya kuma kashe mishi jiki, ya janyo ta sosai yana wasa da ita, "Muje kiyi alola" tunda taji haka tasan komawa zai yi, dan haka suka yi alola suka sake komawa kamar zai cinye ta haka suke ta gurzan juna, Ya rasa inda zai saka kan shi domin jin yake kamar ya boye ta a cikin jikin shi, sai da ya nutsa sosai, sannan ya janye tare da komawa gefe ya zuba mata ido tayi laushi, sanin ta gaji barci take bukata yasa shi daukar ta suka shiga wanka, ya wanke ta tass sannan ya dawo da ita ya gyara mata kwanciya, tuni batun fita unguwa ya kare, ita kenan duk lokacin da taji kayan aikin inshallah bata kuma motsawa, domin wani kasala da gajiya yake saukar mata, kuma haka ce ta faru, dan haka ta cigaba da barci ta. Murmushi yayi yana kara jin soyayyar ta, yana kara samun daraja da matsuguni a ran shi. Kaunar ta kamar ya huda zuciyar shi, ji yake kamar shi ya dace da ita ba kowa ba a wannan duniyar, rike hannun ta yayi yana jin babban al'amari akanta wanda zai.iya cewa ya wuce babban karni, hannunta ya saka a kumatun shi yana murmushi lokaci zuwa lokaci. ** Bayan wata shida da barin shi gida, ciwo ya mishi rubdugu. Tabbas baya jin zai kai labari, ciwon tayi mishi kamun kazar kuka, babu shiri ya nufi Gobir domin idan dai mutu ya mutu a can....🤣😂💪 *Hmm! Nan kuka addabe ni da Lamido yanzun kiri kiri zaku.juya mishi baya* #Mai_Dambu KALLABI..! A Tsakanin Rawuna EWF *Wannan shafin na kune ahalin FITILAR HIKAYAR Mai_Dambu...❤‍🩹🥰❤‍🔥* BABI NA SITTIN DA TARA *ALHAMDULILLAHI! RIJIYA TA BADA GUGA.... FATA NA GARI LAMIRI 🥰🤩* Tafiyar tsawon kwanaki goma ya kawo shi Somalia a jigace, amma yayi kokarin hana shi haka, gani yake kamar idan ya bayyana ciwon shi zasu shiga damuwa sai yayi ta kokarin boye laluran shi har suka fahimci kamar yana boye abu, ganin bai basu fuska ba, yasa suma suka share batun. Tare da shiru na musamman kakanin Anum sukayi domin bikin jikar su. Wani irin gaggawa yake ji a ran shi, dan haka a daddafe yayi kwana biyu yana jiran, ranar na uku bai gaya musu ba, sai dai sun fahimci ya kosa ya bar garin dan haka ya riga su tashi tun asuban fari. Ya saka kai abin shi bai da lafiya sosai amma haka yake kokarin ya isa wurin dan uwan shi. Idan zai mutu ma ya mutu a hannun biyun shi, dan shine fatar shi baya son ya mutu a hannun kowa sai a hannun dan uwan shi. ** Kallon shi take tana kara facce hancinta, cikin shashekar kuka. Kusan sati biyu zuwa uku kenan tana yawan zama tayi ta kuka tana masifa ita ɗaya, yau ma a dan gajiye ya zauna a gefen ta, sannan ya ce mata. "Dazun Innayoh take gaya min baki da lafiya nace mata ai na lura kusan da zazzaɓin dare kike kwana shine ta ce min wai." "Ba sai ka gaya min ba kawai kayi shiru" ta kwanta a jikin shi, rumfa yayi mata, ganin yadda take kara narkewa yasa shi janyewa. "Akwai bikin da za ayi nan da sati me zuwa kuma ana son ki je amma ba zaki ba sabida yanayin ki" "Mutuwa zan yi?" Kura mata idanu yayi.kafin ya ce mata. "A'a kawai ki huta sabida laluranki" "Wacce irin lalura?" "Juna biyu" ai kuwa ta fashe da kuka, ita fa tunda Bintu ta ce mata Umma Haimah tace tana da ciki ta zama sai godiyar Ubangiji,.domin abin kuka da wanda ba na kuka ba kuka take mishi, yanzun haka bukatar ta yake amma sabida kukan jaraba ya gwammace ya hakura, shima Innayoh tana gaya mishi ciki ne da ita ya dan d'aga mata kafa, amma wallahi baya gajiya da ita ne Allah ya gani. "Anum!" "Meye toh?" Ta tambaye shi, "Ina son na gaida Baffa'm karami ne ina cewa zaki yarda?" Shiru tayi kafin can ta fashe da kuka, tare da mannewa da jikin shi,.wayyo jikin shi wani azazzaben rawa ya dauka, ya shiga wurgi da kome na jikin ta, idanun shi ya sauka akan na shanunta, da suka yi fulu-fulu kamar an cika musu iska. Wani wawan sura ya kai musu yana sauke ajiyar zuciya, sai yanxun ya kara gane banbancin mace me ciki da mara ciki, a lokacin da take babu cikin daban yanayin ta, yanzu da take da ciki kuwa Wayyo Allah, zuba take bana wasa ba, ya gigice ya sussuce, kawai Gara yake diba son ran shi, murzata yake yana kara yamutsa na Fulanin ta, sai da yayi yadda yake so, sannan ya mike yana yiwa Allah godiya. Ban daki ya shiga ya tara ruwa yazo ya dauke ta ya kai ta yayi mata wanka, sannan ya dawo da ita dakin ya kwantar da ita. Sannan ya koma yayi na shi ya fito. Zama yayi a bakin gadon, tayi kyau sai wani haske take, hancin nan ya kara tsayi, kana kallon ta kaga me ji da rikici, tashi yayi ya nufi dakin shi na nazari ya shiga rubutu, kafin ya dawo ya, gefen ta ya kwanta. A hankali kwanaki suka yi ta tafiya, har tsawon kwanaki goma, Da safiyar Laraba Gidado ya ya shigo garin, dakyar ya isa gidan galadima. Karban shi galadima yayi yana cewa. "Me ya kawo ka a wannan lokacin, bayan ina jin kishin-kishin akwai lamarin da ake shiryawa, tun jiya nake ta bibiyar Lamido bai saurare ni ba. "Me ya faru?" "Au yaushe ka fara magana?" "Ba shine me muhimmanci Ba, ina son sanin meke faruwa?" "Wallahi ban sani ba. Asalima baki daya tun jiya lamido ya hana kowa shiga fada sabida ana zargin za a kai hari cikin masarautar?" "Hari?" Jikin shi yana rawa ya mike, "Dakata! An san ka shigo gari ne?" "Eh!" "Subhanallahi toh.maza mu bar gidan nan" Da sauri suka fita tare da fita ta kofar baya, "Ku bisu." Juyawa suka yi suka ga ana bin su. A can masarautan kuwa daga Lamido har yan gidan hankalin su a tashe yake. "Sarkin Yaki ka futa maza da barade a dauko Husain" Babu musu aka futa,. Cikin ikon Allah aka same su, kafin Maharan su fara kashe su aka kawo musu dauki, Aka mai da su masarautar, yadda yake aman jini, sai da aka hada da masu magani, Haima tana kuka tare sa rike hannun shi. "Yaya kayi hakuri, ana cutar da ku amma ban san yadda zaku kalle ni " murmushi yayi sannan ya ce mata. "Babu kome " Sai da yayi kwana biyar sannan ya ji sauki. Anum tazo ta gaishe shi. Da magariba Yana tsaye gaban Anum yana shiryawa. Ita da kanta take nad'e mishi rawani. "Anum yau naga Husain da sauki zan leka shi kafin na tafi wirin taron, kuma ki ji abin dadi yana magana!" "Eh haka naji " ta fada kamar bata damu ba, kuma dama babu wani abinda zai dame ta. * "Galadima ka yi kokarin dauke Lamido domin wallahi an shirya gobe da asuba za a kashe su baki daya, don Allah naji labarin ne zan gudu garin mu ba zan iya zama da Masarautan da cin amana da zibda jini ya zame musu kwalliya ba" Kallon sarkin Yaki yayi sannan ya ce mishi. "Ban san ya zan yi ba, ban san ya zanyi da Bello ba, amma ba makawa wannan shine cikon kaddaran Amunatu ganin abinda zai hanata kuka. Ka kula da kanka amma kai ma rayuwar ka tana cikin hatsari." Kasancewar dare yayi dan haka ya rako Sarkin yaki. "Ka jira mu a wajen gari samu fito an jima" "Shi kenan" ya fada tare da juyawa ya tafi shima ya koma gida yayi shiri. Yana shiga cikin gidan, ya samu labarin Fitar Lamido a gidan. "Kash, ina Gidado?" "Yana dakin shi" "Toh muje" a tare suka fita, basu tsaya ba suka bar masarautan da Gidado. Kan idan ya kai shi zai dawo ya dauki Lamido. ** Da gudu Barkindo ya shigo da Bintu suka hadu. "Ina Anum?" "Tana sashin Hamma" "Toh don Allah muje a fitar da ita ko a kaita wani wurin!" "Me ya faru?" "A daren nan an shirya juyin mulki ne a kowani lokaci" Haka yasa suka nufi wuri Anum, a daren suka gaya mata, durkusawa yayi a gabanta. "Da gaske ni Lusari ne! Amma zan yi wannan aikin ko zaki kirani Matsoraci, zai maidake sashina na tura a ceci rayuwar Mijin ki, Innah da Gidado sun shirya juyin mulki." Ya fada bayan ya fisgo hannun ta, ya wuce da ita sashin sa. Fita Dijah tayi ta nufi wurin su Ammyn Sarkin gida ya hanata shiga. "Ina Lamido?" " Tafi unguwa da wazari " "Me yasa dakaru..." Kallon shi tayi tare da shafa gefen cikin ta da taji abu ya hudata ta baya, a hankali ta kalli Chiroma. "Dauke ta ka kaita ciki inda Amunatu da Bello suke." Gurnanin zaki hade da wasu irin sauti na kuka kamar kukan jarirai, zaki ne tsuntsaye ne, ga iska tana kad'awa da guguwa. Shaƙar iska Yakubu yayi ya ce. "Sarkin gida kayi aiki me kyau Kafin su iso gubar ta gama aiki, Shi kuma Gidado da Galadima na samu labarin sun mutu domin a ruwa suka fada bayan sun sha kibiyar sihiri. Ina Anum take?" "Babu ita babu labarin ta, Yar Sarkin Borno tana tare da Amunatu a ciki." "Toh amma kusan babu yadda muka iya ai Yar Sarkin Kano zata bisu Lamido." -- "Mai Martaba ci abinci mana!" Inji Waziri, "A koshe nake." "Ka taba wani abu yanzu zamu koma ai" ruwa ya dauka ya sha, jikin shi yana bashi kamar akwai abinda yake faruwa da Anum.. Hango Tagwai yayi ya fadi yana birgima, kafin Biyuna shima ya fadi yana kuka. "Muje gida ba lafiya " Kofin ya ajiye suka bar wurin taron, tun a hanya yake jin kamar wuyar shi da cikin shi yana zafi, gudun dokin da yake ne yasa shi tari da jini. Murmushi Waziri yayi sannn ya dauke kai Burin shekaru hamsin burin shi da ya zama sarki ya cika. Ya kashe Lamido ya kashe Gidado, wannan ciwon zai barwa Baffa'm da Amunatu da ta kubce mishi. Tun daga farko har zuwa yau aikin shi ne, taya zai barwa wasu gadon shi ta. --- Lokacin su galadima suka fita, dama shiri aka musu, suna fita akayi ta musu ruwan kibau, haka ayi ta samun su, garin su kauce ne dawakan su, suka fada babban kogi, sai da aka haska aka samu sun nutse kafin gawar su ya taso. ** Koda suka shiga cikin masarautan, dakyar ya sauko a kan doki ya shiga cikin gidan, yana bude kofar su Ammy, Dijah tana mikewa da gudu suka sake mata mashi, sai da ta huda kirjinta ya same shi, shima suka zube. "Hassan!" Ta fada tana tari, jini yana zuba mata, Baffa'm yana zaune yana kallon ikon Allah. Takobi Waziri ya dauka ya sari bayan Lamido. Sannan ya shigo cikin dakin Sarkin gida yana jan su kafin aka cire Dijah a jikin shi. "Hhhh!" Ya fashe da dariya yana kallon su. "Sakarkaru, ai dama nasan da shirin ku. Kuma kamar yadda sakaran can ya gaya min haka na bawa Gidado. Alhamdulillahi Anum tana hannu na gari, bana jin haka zai ishe ku domin ita ce bukatar ku. " Saran shi Sarkin gida yayi, ya fadi. "Waziri ai kai kan da wancar matar. Aahhhh!" Yaja numfashi, kafin ya cire wukar da Sarkin Gida ya soka mishi ya dab'a mishi a kirji, ya fadi a wurin yana nishi da ihu. "Kashe namiji irina sai kun zauna kun yi nazarin wata shida, amma kashe munafiki a cikin awa daya zan yi. Kafin rana ta bude za ayi jana'izar mutuwa ta, amma ku sani kafin rana ta fadi kawunanku da shi za a kafa tarihin masarautar nan! Tunda aka haife mu bama kome saida sanin juna, zai dawo idan na zai kamar ruwan k'ak'a." Kafin ya kuma magana sun yanke wuyar shi, " A warware kowa a sanar gobe da safe mutuwar matashin sarki. A tabbatar an kafa matakan tsaro, Baffana kayi hakuri, nima ina son mulki kai kuma jama'a suka zab'a, wannan dan banza tsageran zai hana ni rawan gaban hatsin shi yana kashe shi. Sahil ai ni na saka su kashe ka su karbi Amunatu, kai komi ma idan ka sani ni ne, na shiga jikin ka na nayi ta saranka, Hatta Jakadiya Rama da sauran su nine nan, taya zan bar maka mulkin bayan uban da ya haife ni kashe shi nayi sabida kujeran. Dan haka na maka uzuri zan Barka a raye." Akan Idanun Ammyn da Baffa'm aka kashe Lamido, suka ja gawar shi har waje, aka ajiye ta. Ita kan Ammyn suna fara jan gawar ta suma, dama Bintu tun ganin an kawo Dijah itama ta zauce tare da kurawa jini ido, Ajiyar zuciya Baffa'm yake. Allah bai bashi ikon magana ba, iska aka.fara tare da ihu ana kuka, yasa kowa tsoron komawa gida aiki ya gama, sannan aka saka bayi suka gyara ko ina, shi kuma Lamido gawar shi suka ja har fada. Kafin kace masarautar an. Kuma shiga wani irin yanayi. A daren aka baza labarin mutuwar sarki Hassan da Hussainin shi... *Ina baku hakuri ba lamido ba Gidado kowani team nayi musu adalci ko?💪😂🤣* #Mai_Dambu [6/22, 10:21 AM] Zahrah Maman Khausar: KALLABI...! A Tsakanin Rawuna EWF BABI NA SABA'IN CIF _EH SABA'UNA😂🤣 ALHAMDULILLAHI NAGODE SOSAI DA YADDA KUKA AMSHI LABARIN_ Hankali Galadima ya janyo Gidado zuwa bakin gaba domin yadda ya sha ruwa kamar ya mutu, a hankali ya kwantar da shi, shima kwanciya yai yana tari, kafin ya Kalli Gidado. A hankali ya mike, duk da jikin girma haka yayi ya matse cikin shi yana aman ruwa da jini. "Ka tashi ka tashi domin gaskiya ta rayu koda zamu rasa rayukan mu ba zamu tab'a gudu ga abokan gaba ba, tashi Sarki Husain masarautar Gobir tana ci da wuta karka sake wutar ta cinye da Abinda kake so! Anum tana hannun makiyan ka, ita ce makami me linzamin da ta rage maka, ita take da ikon tafiyar da kome." Ya jima akan shi, kafin ya fara tari yana amai. Bude idanun yayi yana mika hannu. Dariya Lamido yake mishi tare da mika mishi hannu, sai kuma ya mai da hannun shi a hankali yana kallon hannun. "Ka tashi Ammyn da Baffa'm suna jiranka, itama tana jiranka. Zam tafi bana son na makara ne." Har ya juya zai tafi ya d'an juya kadan sannan ya ce. "Nagode da bani damar haka da kuma hakuri da kayi dani, ina maka fatan Alkhairi " a hankali ya cigaba da tafiya a cikin wani haske har ya daina ganin Lamido, a firgice ya farka kallon galadima yake kwance. A hankali ya kai hannu zai cire kibiyar yaji gurnanin zakin su, cire hannun shi yayi Tagwai ya cire kibiyar da bakin shi, kallon Biyuna yayi yana tsaye shima, tashi yayi ya nufi wurin su. Zubawa sukayi suna gurnani. Dawowa yayi ya dauki galadima ya sab'a shi a kafadar shi, suka nufi Masarautan. "Karka bar kowa da rai, kar kayi irin Kuskuren da muka saka lamido yayi na kin kashe kowa. Ka bayyana a matsayin shugaban su" Haka yake ta nanata mishi kalma daya, har ya isa Masarautan, buga kofar yayi aka ki budewa, gyara rike galadima yayi cikin wani irin fushi da fusata ya saki da kofar da kafar shi, wani irin faduwa kofar tayi tare sa karyewa. A hankali ya shiga kofar birnin yana kallon yadda aka zuba masu tsaro. Sauke galadima yayi sannan ya kalli yadda suka yo kan shi. "Idan kuka sake nayi amfani da iyawata matan ku da Yaran ku ne zasu zama marayu da zawarawa, idan kuka yi mubaya'a zan baku yanci. Ni Husainin Muhammad Bello." Kamar jira ake ya ida Fadar sunan shi Masarautan ta dauki sabon gud'a, tare da buge buge kamar yadda aka yiwa Lamido. A hankali suka yi ta Zubawa akan gwiwar su, suna bada hadin kai. * "Gud'ar me nake ji?" Chiroma ya tambayi Waziri, "Gud'ar kasancewar Barkindo ya zama sarki na gaba " "Bana tunanin haka!" Bai kai ga rufe baki ba, dakaru biyu suka shigo fadar. "Yarima Gidado ya dawo." Zubur suka mike. "Kenan gud'ar nan Washi suka yiwa Lale Maraba da sabon Sarki? Haka na nufin jinin Bello ne zasu rike masarautan nan" murmushi Zakaria yayi sannan ya kalle su Ya ce. "Kowa ya koma gidan shi, kafin rana ta fito" Haka kuwa ya faru kafin Gidado ya iso masarautan kowa ya kama gaban shi. A can kuwa Bingel da Barkindo sun juyawa Anum tunani da duniyar ta, domin baki daya sai da suka bata labarin cewa ai Gidado ya kashe lamido ne sabida yana son ta, sannan kuma yana son mulki, shi yasa ya nimo magani yayi baki. Dakyar suka dakatar da ita a daren domin birkice musu tayi tana son ganin Lamido. "Idan muka barki wallahi kashe ki zai yi akan mulki, domin idan yasan ba zaki yarda da shi ba toh abinda zai yi kenan, ke baki da Buri ne akan cikin jikin ki" kallon su take domin bata yarda lamido zai mutu ba. "Kun zata zai mutu ne haka, ina ji a jikina bai.mutu ba yana raye" Duk yadda suka so mata bayanin mutuwar Lamido taki yarda akan ya mutu, sai da aka yi sallah asuba. Lokacin labari ya karade ko ina, sannan Alkali da Liman da Baffa'm da Allah ya hana shi magana suka shiga kan gawar Hassan, a lokacin Gidado ya shigo. Ajiyar zuciya Baffa'm ya sauke tare da kallon Gidado. "Suturar mutane biyu za ayi ga Gawar Galadima shima" "Ta mutane uku ne Gidado Hadizah ma ta mutu" jijiyar jikin shi ne ya mike murda'murd'an a gaban goshin sa da ilahirin jikin shi. "Innayoh da wasu bayi zasu kula da ita." Shigowar Waziri da su Chiroma suna kuka yasa baffa'm kallon su sai lokacin hawaye ya zubo mishi, yana kallon lokacin da suka yi ta saran Lamido, haka yasa shi ja da baya. Fita Gidado yayi ya koma cikin gidan tare da nufar sashin Ammy ya samu da mutane har da bingel. Sannan ya nufi sashin sa, zam-zam da turare tare da likafanin, shi ya sayawa kan shi ne lokacin da malamin su ta tafi Umrah ya da sako a kawo mishi ashe wa Hassan ya sayawa, sai da ya fito ko d'igon kwalla babu a ran shi, zuciyar shi zafi take, a lokacin da ya kai har an rasa yadda za ayi da Lamido saboda raunin jikin shi, shi ya kwabe tare da zama ya wanke dan uwa shi tass, sannan aka d'ago shi ta shirya shi. "Ban tab'a kawowa da kaina zan shirya ka ba Hassan na san kai zaka shirya Jana'izata ba ashe ni zan shirya naka. Kafin yau na zata Ni zan mutu amma yau da na ga ni nake shirya gawan ka na yarda da cewa cuta ba mutuwa bace! Allah yasa Aljanna ta zama makomar ka." Sannan ya mike ya kalle su, kafin ya ce. "Bari na gyara jikina" Fita yayi daidai lokacin da Barkindo ya rako Anum, dauke kai yayi kamar bai ganta ba. "Laaa kaga Hamma Lamido" ta nunawa Barkindo Gidado, d'ago kan shi yayi ya zuba a bayan Gidado gaban shi ne ya fadi. Kafin yayi magana Anum ta biyo Gidado da gudu tana rike hannun shi. "Dama nasan baka mutu ba, da aka ce min Gidado ya kashe ka Sabida mulki da kuma ni, nace musu karya ne kai Jarumi ne ba zaka mutu a hannun Gidado ba, domin kana son shi ba zaka bari ya kashe ka ba" Juyawa yayi tare da sunkuyar da kan shi. "Kiyi hakuri Ammyn tana ciki" Ja da baya tayi tare da rufe bakin ta. "Ina Lamido?" Bai bata amsa ba, ya shiga abin shi. Da sauri ta juya wurin Barkindo da yake ji kamar ya sake fitsari a wando dan tsoron irin kallon da Gidado yayi mishi, kamar Lamido ne yayi mishi wannan kallon, a raxane ya rakata har kofar Ammyn ta shiga. Daidai Innayoh ta fito daga dakin da ake suturar Hadiza. "Innayoh Ina Lamido?" Cikin karfin Zuciya Innayoh ta ce mata. "Ki shiga wurin Ammyn" a hankali take ratsa mutane, tana shiga ta kalli Ammyn da Bintu. "Ammyn Ina Lamido?" "Sun kashe shi" inji Bintu. Dariya ta kama yi tana cewa. "Ba fa zai mutu ba" Shigowar Baffa'm da wasu maza aka fita da gawar Hadizah, sannan aka kai babban zauren gidan. --- "Kayi hakuri!" Ta fada tana daure mishi ciwon shi, sannan ya dauki kayan shi ya saka. "Kin jima da sanin mahaifin ki yana cutar ai? Me yasa baki gayawa Lamido ba? Sannan a ranar kin san abin zai faru kika zo kina gaya min nayi hakuri, Haimah nasan mahaifin ya jima yana abinda ya gadama, idan ke ce wani hukunci zaki yanke!" Yana fadar haka saka alkyabar shi ya fita. Kuka ta zauna tayi tayi, koda ya fito hango Innayoh yayi tana rike da Anum, Bintu ta Fito da Ammyn. "Innalillahi wa inna alaihil raji'un allahumma ajirni fii musibati wa'akhlifni khairan minha, Wayyo Allah na Mijina wayyo Allah ku dawo min da Mijina na hada ku da Allah, don Allah Wayyo Allah Innayoh ki ce su dawo da shi wallahi bai mutu ba, wallahi bai mutu ba!" Rintsa idanun shi yayi yana jin kamar ana caccaka mishi kibiya a kirjin shi, cikin kuzari irinta sadaukan maza ya nufi inda gawar dan uwan shi take ya dauka tare da taimakon wasu daga cikin manyan fadawa aka fitar da gawan daga cikin gidan. Kwace rikon da Jakadiya tayi mata, ta nufesu da gudu, cikin ihu da karamin Hauka ta ce. "Ina sonka! Ina son ka!! ina son ka mijina!!! Wallahi nima mutuwa zan yi idan baka tashi ba!" Ganin ana ƙoƙarin rike ta, da gudu ta kuma shan gaban su, tare da kifa mishi mari. " Ina ka tafi aka kashe min shi? Meye nayi maka da muka cancanci kyautar mutuwa? A daidai lokacin da nake shirin gaya mishi na shirya zama da samun soyayyar gaskiya?" Ta

Chapter 35 of 39