Share this page
samari karti majiya karfi da kyau, sai da ta kai matasa biyu idan ba kowa ya dauki abinda yake so ba, ba zaka banbance su ba, ga lamido tun wani zuwan shi kasar sudan aikin jahadi ya kuma dauki wata dabi'ar su, shine saka mayafi a rufe fuska. Idan ya lullube fuskar shi zaka dauka irin Bararojin nan ne ko irin larabawan kauye kyawawan nan, a duk lokacin da Fulani ta lallee shi sai ta ga kamar Baffa'm ne a gaban ta, sai dai a lokacin da suke basu wuce matasa yan shekaru ashirin da biyar ba, bangaren Gidado wata mahaukaciyar shakuwa suka yi da Fulani Bintu wanda yasa kowa yake da yakinin son juna suke, ita kanta son shi take kamar tayi Hauka. Haka yasa a cikin gidan Fulani Aminatu tasa aka hana mata bayi zuwa cikin gidan sai dai bayinta masu zama da ita sune kawai zasu shiga su taya Innayoh aiki. Sai dai a lokacin ne Lamido ya hango wata makarantar irin ta addinin musulunci, duk da lokacin ana maganar auren su ne, amma haka ya roki Alfarman a barshi ya tafi makarantar, kallon shi mai Martaba yayi yana faɗin. "Lamido ka girma fa, kuma kasan Gidado ba zai yarda yayi aure ba sai kayi, karatun zai dauke ka shekara nawa?" "Allah ya baka nasara akan abinda ya shafi addini ne, zai dauke ni kamar hudu zuwa biyar" "Allah ya maka albarka" "Amin Ya Allah, amma ina son mu tafi da Gidado." "Sarkin yaki kana jin mataimakin ka zai tafi niman ilmi da girman shi " "Allah ya baka nasara, sarakuna anan su da niman ilmi babu laifi idan ya tafi, ga karfin damtse ga na ƙwaƙwalwa, ranar da Masarautan gobir ta fada hannun shi tabbas ilmi da adalci zai yi aiki" sarkin yaki ta fadi haka, yana yar dariya domin yasan a duniya idan akwai abinda lamido ya tsana shine ka kira mishi mulki, baya son mulki ya amince ya zama garkuwa ga ahalin shi koda haka zai zama fansa ga rayuwar shi. Sallama yayi musu ya nufi cikin gidan, anan ya samu Bintu ta saka Ammyn a gaba tana murmushi, ita kuma tana bata labarin yadda Lamido sukayi Kuruciyar su, kamar kazar da ya sha ruwa ya wuce abin shi, tare da nufar dakin shi. "Ammyn dukkan su biyu ne basu magana ko Hamma Gidado ne kawai?" Murmushi tayi tana bin shi da idanu. "Shi daya ne, na Lamido kuwa sadaukarwar ce a gaban manyan idan ya zama dole yana yi!" "Ammyn kuma haka ba zai tab'a" "A'a ba zai tab'a kome ba shi ba, sai dai yana tauye kan shi da na kusa da shi, iya Gidado yake iya fahimtar shi da Innayoh, ban tab'a fahimtar shi ba, asalima kamar surukar shi yake kallona kunyar shi da yakanar shi tana damuna, ba laifi sadaukarwar amma kuskure ne tauye kai" a cikin maganar Ammyn dai ta fahimci wani abu daya, rashin maganar Gidado yana mata zafi amma shirun da Lamido yake yi yana mata yafi kome munanna mata, domin ta kara da cewa. "Nasan a farkon ciwon gidado Hussain na manta da Lamido Hassan, amma ko da na dawo gare shi sai ya manta da ni da kome na shi, wanda haka kamar kuskure ne ka manta da wani abin da kake so ko sau daya ne da ina son na zauna da shi mu zanta irin na d'a da Uwa amma na rasa wannan hubb'asan!" Tab'e baki Bintu tayi dama bai tab'a burge ta ba, Allah ya gani tana Tausayin Ammyn domin jarabawa ne haihuwa irin Lamido ita kan a tarihi bata tab'a ganin mutum irin shi ba, ba a tab'a ganin yana dariya ba, asalima kullum fuskar nan kamar hadari, ina dalili zata dami kanta. "Uwargijiya ta, na gaya miki halittar shi ce haka, lamido yaci sunan shi ne daga gare ki, abinda da yake ba kome bane sai mulki yake bin jinin shi, a duk lokacin da aka samu haka toh sai addu'a." Dariya Fulani Bintu ta saka tana kallon Innayoh. "Innayoh kina tsammanin aka bawa wannan mutumin mulki Masarautar Gobir ai a rabin sa'a zai saka. Fille kawunan mutane kawai Innayoh ki bar tunanin zai zama sarki Insha Allah Gidado Allah zai bashi lafiya shi ya dace da zama sarki." "A'a idan aka kuma maimaita abinda aka yi yadda aka yi akan Sarki Bello, hmm babu me kai labari baki ɗaya." Idanun ta sun kad'a jajjur. Dafe hannun ta Innayoh tayi tana kallon Fulani Aminatu. "Kiyi hakuri" "Innayoh ku daina maganar sarautar nan" "Fatimah zaki iya tafiya" Innayoh ta fada sakamakon fitowar da Lamido daga dakin shi. Zama yayi yana me sunkuyar da kaan shi. Ya jima a zaune a gaban ta, matse hannun shi, tashi Innayoh tayi tana jin wani irin Tausayin su. "Ammyna!" Kura mishi ido tayi. Kafin ta ce mishi. "Lamido nifa Mahaifiyar ka ce, Lamido me yasa." Tashi yayi ya zauna akan gwiwar shi. "Ki gafarce ni, ki yafe min, don Allah kiyi hakuri. Ban san yadda zan yi bane" "A'a ka sani me yasa gidado ke iya zama ayi hira da shi? Me yasa shi yafika bani lokacin ka haka zaka auri mace tana maka kallon azzalumin mutum? Ni Mahaifiyar ka ban samu lokacin ka ba balle matar da zaka aura" ajiyar zuciya ya sauke domin yasan bata san tafiyar su Sudan ba, dan haka cikin tausassawa ya shiga bata hakuri, yasan duk abinda yake bata so dan haka ya fada mata shirin sa na zuwa karatu shi da Gidado. "Innayoh kizo" ta kira sunan Innayoh, koda tazo, zama tayi tana kallon su, shi kan shi a sunkuye ita ranta a B'ace. Innayoh tasan ko wuka ta saka mishi ba zai kuma maimaita abinda ya fada ba, dan haka ita da kanta ta labarta mata, kallon shi tayi kafin ta ce mata. "Ai banga aibin zuwa karatun ba, kawai sai dai idan zaki ce baki son su tafi ne!" "Innayoh yayi tafiyar shi ya bar min d'ana da bai da baki" wata irin sirrintacciyar murmushi ya sauke yana kara sunkuyar da kan shi. Karon farko da ta ga Murmushin da ta kawata kyakyawar fuskar shi, me cike da haiba da kwarjini. "Innayoh kin ga ya mai dani mahaukaciya" "Ki ce dai kin ji dadin yayi murmushi kawai, amma ai abinda yake nufi a fili yake waye zai iya tunkarar Gobir bai da ilimin addini da na iya sarrafa al'umma? Ki bar shi kawai ya tafi Allah ya bashi abinda ya tafi nima." "A'a yayi tafiyar shi ya bar min Yarona wanda ya damu da kuka na, wanda ya damu da damuwa ta." "Kayya Aminatu kina kuma kara lalata kome kawai Kiyi hakuri ya tafi da shi, haka ma wani nasara ce ta rayuwa" Aikuwa Aminatu ta kafe tace ba zai tafu mata da Yaro ba da dinbin mamaki yake kallon yadda ta kafe, dan haka ya kaskantar da kan shi ya fara magana cikin tattausar lafazi ya ce... [5/30, 2:37 PM] Mai_Dambu: KALLABI..! A Tsakanin Rawuna EWF BABI NA ARBA'IN CIF https://youtu.be/UMtk8EpcIUI Please subscribe Shiru yayi na wani lokaci kafin ya dauke kan shi, cikin wani miskilin yanayi yana kallon kasa kafin ya ce mata. "Don Allah ki bani aron shi." "Ba zan ba da Yarona ba, kayi tafiyar ka Allah ya tsare" ta fada da Murya me nuna rashin amincewar ta. Baki daya abin sai yazo mishi bakon yanayi bai tab'a magana da ita ba irin yau kuma a madadin tayi hakuri sai na kafewa da tayi. Duk sai ya rasa inda zai sakata, kawai ya cigaba da zama a gaban ta, ai idan ta gaji zata hakura. Ita kanta so take suyi hira da ita, so take suyi farin ciki taji damuwar shi amma mutumin nan ko nace bishiyar kuka zama yayi yana kallon kasa, sai da Innayoh ta kawo mishi dafaffe madara ta mika mishi. "Uwargijiya ta, ki mishi hakuri mana ki bashi Aron dan ki, dan zinari" "Innayoh!" Ta kira sunan ta, tana kallon shi. "Ko sau daya ba zai zauna da ni mu zanta irin na d'a da uwa ba?" Da sauri ya d'ago kai yana kallon ta, abin da ya fahimta, halin shi na ko in kula yana tab'a zuciyar Ammyn su, kamar yaro karami ya kara zama a gaban ta. Bakin shi yana rawa, sai yayi kamar zai magana sai yayi shiru, kura mishi Idanu tayi kamar ta rufe shi da duka, shigowar Gidado yasa shi sauke boyayyen ajiyar zuciya, kan shi a kasa zama yayi kusa da shi yana cewa. "Ya naga kunyi jugum jugum? Wani abu ne ya faru." Ya tambayi Ammyn su, bayan ya amshe kofin madaran Lamido ya sha rabi, Kallon su take cikin so da kauna, yadda Allah ya haɗa mata mutane biyu ma bambanta hali. "Wai zaku tafi karatu ne!" Ware idanu yayi akan ta yana kara tambayar ta. "Inji waye? Da gaske kuma?" Nuna mishi Lamido tayi. "Don Allah ina zamu? Gobir?" Rike hannun Gidado yayi yana girgiza mishi kai lamido yayi. "Makaranta zamu na tsawon shekaru uku zuwa hudu, kafin nan ayi dacen samun maganin ka ko" murmushi suka sakarwa juna da hannu yayi mishi alamar ya amince.. "Yaushe xamu tafi?" "Sai Ammyn ta amince" Ya fada Mishi yana kokarin boye damuwar shi, haka Allah yayi shi. Ba zaka tab'a gane asalin damuwar shi ba, a gaban ta ma kokarin yake ya boye gajiyar da yayi da maganar da suke, dan haka ya koma gefe ya kame kan shi kamar ba shi ba, haka tayi ta jan su da hira, wanda baki daya nasiha ce, da nuna musu girman Allah da tsoron shi, kafin ta dire aya tana cewa. "Ka saka min idanu akan shi, kusan shi amana ne a gare ka, don Allah kar ka bari wani abu ya same shi, bayi da baki kaji" "INSHA ALLAH" ya fada tare da kokarin mikewa daga gabanta dama tasan za ayi haka domin baki daya kamar mara gaskiya, shi kan shi ba zai ce ga hujjar shi nakin sakewa da ita ba, amma yau ya zame musu rana me daraja, domin har sun yi hira, dan shi dai bai shiga maganar ba, idan tayi tsawo ne yace eh ko a'a. Da wannan yanayin ya bar su, ya fita wajen gari..tunda ya fita a masarautan ya nufi bayan gari, a nan ya zauna yana busa sarewa. ** "Ba zaka tab'a zama sarki ba, amma tabbas idan har ka cika wandnan sharudar zaka cigaba da taka kowa ba tare da an fahimta ba, ka fahimci wani abu ba zaka zama sarki ba, sai dai ka nimawa Dan ka yarinyar da take da zubin halittar matar Bello an kuma haihuwar ta, idan kai ka ce zaka yi zaka iya mutuwa, domin nan da wasu lokuta wata guguwa me hade da dunkulen siffar Zaki zata kuma bayyana.." Wani irin baki da farin hayaki ne suka hadu wurin guda suka fantsamo sama kamar zasu duke fuskar shi, kare fuskar yayi yana kallon bokan.. "Ba zan tab'a barin haka ya faru ba" Dariya bokan yayi sannan shiga yiwa kan shi kirari. * Allah ya bashi sa'a ya fito daga masarautan ta kofar bai, duk da ya samu sama da shekaru yana zuwa dajin, kusan kullum idan ya fita niman ta baya samunta haka yau har ya cire rai zai same ta, ya jiyo sautin wakar ta, cikin sassanyar murya wacce ta karade sunkurun da take da shanun ta, yar kimanin shekaru goma sha huɗu, sandar kiwon da yake kafadar ta, sanye take da farin kayan saki ta asalin Fulanin usul, gashin ta da aka mata kitson doka ya sha wuri da wasu tsagiya, cikin harshen gurbataccen Hausar da zaka fahimci kamata ake tana kwacewa take rera wakokin hausa musamman wanda ake a dandali, wanda daga baya aka sabunta shi, K'ugunta cike yake da wurri, wanda aka ajera su kamar jigida, ba kasafai ake samun yan mata da shigar wurri ba, a rugaggen Fulani amma ita an makara mata wurrin ne sakamakon karfin yanayin ta, da idan aka mata abu wasu, ba zata iya kome ba sabida mugun ta, sannan masu taimaka mata ba zasu iya cutar da kowa ba.. _Charman duddu charman duduwa charmagade_ _Charman duddu charman duduwa charmagade_ _Akwai wani bako a gidan mai gari Charmagade_ _Baya sallah bayan lazimi_ _Charmagade_ _Baya nima 'Yan matan gari_ _Charmagade_ _Ko ya nima wai zai ba shima_ _Charmagade_ _Innata landiyo mana_ _Baba na Landiyo mana_ _Charmagade_ A hankali ta fashe da kuka, cikin shashekar kukan ta cigaba da wakar. _Don Allah mai Tafiya ka jira ni sako zan baka daure ka kai ga masoya_ _Yarinya kyakyawa lamarin ki na ban mamaki_ _Don Allah mai Tafiya ka jira ni sako zan ba daure ka kai ga masoya_ Ita ke wakar ita ke amshin, baki daya jikin Barkindo ya mutu sabida tana wakar ne cikin Kadaici da tarin kewa. Dan haka bai yi kokarin dakatar da ita ba, asalima sai ya lame a jikin itacce yana sauraron zazzakar Muryan ta. _Don Allah mai Tafiya ka jira ni duba_ _Sakon nuna sauri ne don Allah ka karb'a! Zaki yi mamaki sakon da zan zaka kaii_ _Shi yayi alkhairi da na juya ban kuma cimma ba_ _Don Allah mai Tafiya ka jira ni sako zan baka daure ka kai ga masoyina_ _Akasi akan hanya...._ "Washhhhhhh" ta ji an fada da ƙarfi yasa ta juya da sauri itama, Barkindo ne ake dambe da shi wasu mutane, "Auya maza kisa sake ta" ta fada cikin rashin tsoro, "Jarmai ka amshe sandar hannunta ka kwala mata a kafa. Naga ma yar budurwa ce, maza yaga mana rigar mutuncin ta kafin mu kar wannan anan" Wani juya sannan tayi tare da d'aga shi sama. "Eeeyyuuuuu idan wani ya tako nan sai na sanya shi ya manta da nonon mamar shi maza ki zo" Matsalar bata iya banbance mace da namiji, a waka zata banbance amma ban da a magana fatar baki. Dake sakarai ne sun zata cika baki take, yana zuwa kuwa da Allah ya bata sa'a ta juya sandar ta muka mishi a hakarkari sai da ya fadi sumamme. Bakar zuciya ne da ita, da shi ta kwaci kanta a cikin gidan su. Dan haka kiwo ya zama mata jiki ne, amma bata yarda wani yaci zalinta a ynzun duk da kuwa an dakatar da yanayin ta, da gudu wanda ya rike hannun Barkindo ya juya tare da barin wurin, cikin takaici ta kalli Barkindo. Sannan ta tab'e baki. "Anum" ya kira sunan ta yana mikewa, riko damtsen hannun ta yayi, a fusace ta juya zata mishi magana yadda ya narka da fuska sai da ya kashe mata jiki baki daya. "Ban iya ba, ba zan iya ba, asalima ba a haife ni domin yaki ko kare kai ba, amma qaddara ta samar da ni ta hanyar da kullum hango mutuwa nake" fauce hannunta tayi ta cigaba da wakar ta. _Shi yayi banbanci wurin kyau da hali da nagarta da shi zaka mika turare na_ _Don Allah mai Tafiya ka jira ni sako zan baka daure ka kai ga masoyina_ "Don Allah ki saurare ni" ya sha gabanta. "Na yarda ki koya min fadar kare kaina dogara sandar kiwon tayi ta daura hannu a kai tana kallon shi. "Bani da wayo na rasa iyayena Mahaifiya ta da mahaifina, har yau ina fuskantar cin zarafi daga kakata. Abinda ma dauka a shekaru goma baya a yanzu babu wanda zai takani na kyale shi. Ni Marainiya ce, amma ba mara zuciya ba, idan ka ga an cutar dani nice naso haka bani hanya" Ta rab'a gefen shi, garin yabi bayan ta, aikuwa ya taka mugun naya, "Wayyo Allah na!" Ya fada da karfi, juyawa tayi ta kalle shi, takaici ya kuma turnike ta. K'aya ce fa. Wani dauke kai tayi, ta tawo kan shi. Ba tare da ta ce mishi kalla ba, ta durkusa tare da kai hannun ta kan takalmin shi me zubin kayan jikin shi, wanda ya nuna daga inda ya fito. Ta kama kafar, ta zare da karfin tsiya. Wani bincikota yayi, cikin jin haushi ta fallawa fuskar shi mari, ji kake. "Tassss" wanda yayi daidai da zuwan Mandiya da wasu bayin Bingel. Da sauri ta fara kokarin mikewa amma ya rike ta da karfi. "Anum me yasa?" "Har abada tsakanin mu akwai babban iyaka" sannan ta mike tana me daukar sandarta, baki daya wani mugun kunya ce take dawainiya da ita, yadda take fa bakin jini a rugar su, bata san me yasa Barkindo yake mata haka ba, Asalima dayawan mazan rugar su, hanyar da tabi basu bi, domin suna kiranta da annoba, wasu kuma mayya suke kiranta. Sakamakon yanayin ta da idan ranta ya ɓaci zuma suna iya kusan hallaka mutum akan ta, a wannan bangaren ita kanta Inono ta razana shi yasa tayi kokarin dakatar da ita kafin ta zame musu annobar, ta ci wahala a hannun su shekarun baya amma a yanzu babu me ko lakatar ta, daga manya har yara kowa shakkar ta yake, duk ranar da suka dake ta Insha Allah, basu ba barci cikin salama, daga baya kuma duka da azaba yasa ta koyi wani mugun zuciya. Tun tana da shekaru goma sha daya ta fara dambe domin kwatar kanta, sosai take cikin uban Yara, haka yasa kowa ya kama dan shi, domin sunce kashi guda gare ta, idan ta damfara yaro ko yarinya da kasa sai kashin sa ta karye, idan kuma kaifi karfin ta idan ta kama ka sai ka sha mugun wahala domin ji zaka yi kaman ana dukan ka da danyen itacce. Wannan halin nata yasa aka kyale, suka shafawa kan su lafiya, ta bangaren tallar kindirmo, idan ta dauka da izinin Ubangiji sai na ta ya kare na sauran yaran bai kare ba, shima duk ranar da take jin nishadi take daukar na Inono, idan kuwa aka sata dole ta dauka Insha Allah haka zata dawo da shi ya lalace har na sauran Yara, wannan yasa tafi son tafiya kiwo, domin idan ta shiga cikin gari talla maza kamar zasu kamata su boye ta, musamman da Allah yayi mata diri tun bata cika budurwa ba, akwai diri, gata kana ganin ta kaga bakar labarabiya, wacce take da sirki da kabilu biyu,wanda ya hadu da fatar ta ya haifar mata da wani irin dubun fata me kyau(dark brown) idan ta samu wasu shekaru zata fi haka tsawo da cikar halittar jikin, kugun ta kamar wanda aka zana mata shi domin duk wanda ya san kalangu haka Anum take, a yanzu da yan kananun nonuwarta da suka fara tasowa idan suka fi haka tabbas za ayi kerarriyar budurwa ce da babu irin ta a cikin rugar su, idan tana tafiya kuwa zaka ratse da Allah tana yanga ce nan kuwa haka tafiya yake, shi kan sa Barkindo a da can tausayi ne yake kawo shi wurin ta, tun bingel tana hana shi zuwa har ta fahimci duk lokacin da bai zo ba, kamar zai mutu yayi ta mata abin kunya kenan ko yayi ta tsinkata a gaban bayin ta, sai dai wani harin da aka taba kawo mishi yasa ta haramta mishi fita daga masarautan.... [5/31, 10:08 AM] Empress Anum: KALLABI..! A Tsakanin Rawuna *EWF* BABI NA ARBA'IN DA DAYA. A wannan harin sai da yayi dogon jinya ganin haka yasa bingel tallafe rayuwar shi, sannan ta hana kowa zaman lafiya a cikin masarautan, sai ya kasance matukar zai fita da masu raka shi, amma shi dake yana son rayuwar yanci baki daya yaki amince, yau ma yana fita, ta saka a aka biyo bayan shi, dama tasan matukar zai fita wurin Anum ce, shi yasa yau ta kudiri Aniyar sai ta razana Anum yadda ko gobe ya zo zata ji tsoron tsayawa da shi. .... "Sannu Barkindo sannun" wani kallon banza yayi mata, cikin masifa ya ce mata. "Rufe min wawwaran bakin ki, sai da na gaya miki karki gaya mata ko?" Ya fada a tsawace domin yaji Haushin zuwan ta, tashi yayi ya nufi Anum, ya kuma shan gabanta. "Me yasa kike tunanin ban dace dake ba? Anum!" Ya kira sunan ta da sassanyar murya. Kura mishi ido tayi kafin ta sakar mishi murmushi ta wuce, rike rigar ya yayi ta baya. "Ki saurari sakon zuciyata" a fusace ta juya. Kwallar da ta gani a cikin kwayar idanun shi kwance shi ya hanata kara mishi mari. "Kaso me son ka ai yafi kaso me kin ka" ya fada yana me sake rigar. "Toh naji sake ni." Ta fada a hankali, sannan ta bar shi wurin a ajiye, sake d'aga kafar shi yayi zai bita yaga wulgawar abu bai san sa'adda ya fasa ihu tare da komawa baya a tsorace ba, jikin shi yana wani masifaffen rawa. Wani mugun takaici ne ya kara cika Anum, cikin ban haushi ta ce. "Me akayi da mutuwar zuciya! Wallahi gara mutuwar gaba zaka bazama duniya niman magani sakarai kawai" Haka bayi mata da maza suka ja shi zuwa rugar dan Mahaifiyar shi tana can, yamma likis Anum ta koma ruga. Tun a hanya ta fahimci Gwaggo Bingel tazo, dan tasan haka kawai ma Barkindo yakan zo balle kuma tasan ana bibiyar lamarin shi. Sai da ta kai shanun garken su, sannan ta dawo cikin gidan. Dake itama Yar duniya ce tana shiga ta wani dauke kanta kamar bata ga halittu a wurin ba, tana tafiya tana waka. Kura mata ido Bingel tayi, cikin takaici ta ce. "Ke" bata juya ba, "Innah ki kyaleta, bata son magana." "Ku kawo min ita nan" "Innah nace don Allah ki kyale ta" ya fada Muryan shi na rawa, Finciko Anum suka yi tare da dangwarata a gaban Bingel. Har lokacin bata d'ago ta kalli Bingel ba, sai ma wakar da ta cigaba. "Ku zane ta" "Yahanasu ki kyale ta, bata yi kome ba. Zalinci zai yi yawa tunda bata miki kome ba, mu da muke tare da Anum zamu bada shaidar halin ta bata magana da kowa bata shiga harkan kowa, bata damuwa da kowa abinda ta saka a gaban ta take yi don Allah ki rabu da ita" "Daadah marin Yazidu tayi, shi din sa'ar ne?" "A'a dauka nayi rana daya kika haife mu" ta fada mata magana tana me juyar da kanta. Wannan abun ya batawa Bingel rai, bata san lokacin da ta bada umarnin ayi ta dukar Anum din ba, "A'a Innah, ki kyale ta nace, don Allah ki kyaleta" ya fada yana kokarin tashi, amma ta sa aka rike shi, tare da saka wa a cigaba da abinda ta su,sai da suka mata dukar da za a ce ta fadi ko tana nishi, amma yadda bata yi ko tari ba, haka ta mike tare da kad'e jikin ta, sannan ta ce mata. "Ba mamaki ki kara sakawa gaba a dake ni, amma tabbas indai akan lusarancin Yazidu ne yayi ta shan duka a hannuna. Ban san ni ba ko mata maza kika haifa" Tana gama fadar haka ta juya zata bar wurin, sabida dukar ya shiga jikinta. Ga zuciya da tayi, yankar jiki tayi ta suma. Tashi yayi yana dingishi, ya isa wurin ta, a hankali ya dauke ta, zuwa dakin ta, ya kwantar da ita yana shafa fuskar ta. Shi kan shi a dame yake da halin uwar shi, balle ita. Tashi yayi zai fita ya hadu da Inono. Tana shiga da ruwa ta watsa mata, ajiyar zuciya ta sauke, sannan ta lumshe idanun ta. Sake shigowa dakin yayi yana kallon ta, jin yadda yake kallon ta yasa ta juya mishi baya, zama yayi yana bata hakuri, da ya ishe ta. Mikewa tayi ta ce mishi. "Tashi" ba musu ya mike, kawo shi tayi bakin kofar ta tura shi da karfin tsiya sai da ya fadi. "Idan na kuma ganin ka sai na karya kafar ka" "Anumullah" ya fada da ƙarfi banza tayi da shi, ta rufe yar kofar dakin. Haka ya xauka a bakin kofar anyi anyi ya tashi yaki, uwar shi tana zuwa bata tsaya ba, ta shiga cikin dakin ta riko hannun Anum da karfi ta fito da ita, tana me cewa Dogarai. "Ku wuce mana da ita cikin masarauta taso muje" Zubewa a gaban ta Inono tayi tana faɗin. "Don Allah kar ki kashe ta." "Zan dawo da ita ne idan aka koya mata hankali." Haka suka dauke ta da karfin tsiya aka daurata, sannan aka daurata akan doki, shi kuma akeken doki daban haka itama uwar da mandiya da ban. "Idan muka isa a shirya ta, a kai ta dakin shi kafin nan akwai maganin karin lafiya a zuba mishi, na lura sha'awar ta ne yake damun shi ita kuma zuba mata banju, yadda ba zata iya kome ba, har ya gama lalata abinda take ji a ranta. "An gama Ranki shi dade uwar Jarumin maza" wani kallo Bingel tayi mata, kafin ta dauke kai ai tasan idan ba karya aka mata ba, waye Jarumin maza Barkindo yaron da ko wuka bai iya rikewa ba, kadangare sai ya kasa shi a gaba. Koda suka

Chapter 21 of 39