wani" ta fada cikin shahshanci da shirme.
"Ai daga ni sai dan dalago muka ji idan ma kin ji labarin a wani wurin toh ga wanda ya faɗa!" Ya nuna mata dan dalago.
"A'a yana magana ne?" Ta tambaye shi, tana zare ido alamar a tsorace take.
"Kwarai tunda ai ba ni na baki ba? Kuma zai gayawa Hammanki duk abinda ya faru, dan haka ki yar da shi domin munafuki ne" k'amk'ame dan dalago tai tana kuma kallon shi.
"A'a ba zan yarda shi ba, Hamma na ne ya bani shi tun yana jariri"
Share ta yayi domin ya lura ba zata tab'a yarda ta rabu, da dan dalago ba, shima kuma bai san ya akayi yake son ta rabu da zomon ba. Ajiye dan dalago tayi ta zauna tana kallon yadda ya dauki baka yaja. Sannan ya sake a jikin mutum mutumin ciyawa da aka ayi. Kallon shi tayi ta ce mishi.
"Baffa'm!"
"Hmm!"
"Ka koya min nima" ta fada tana mishi kwal-kwal da idanu.
"Aikin maza ne ba na mata ba" ya fada yana cigaba da harbawa.
"Don Allah" ta fada cikin wata irin murya, sake kwarin yayi ya juya yana kallon ta.
"Kin ci abinci kuwa?"
"Na ci"
Zuwan su Innayoh wurin ya sata juyawa.
"Innayoh kice ya koya min" sumkuyar a kai Innayoh tayi da sauran bayi matan.
"A kula da ita ta daina fitowa da rana ko da sassafe"
"Baffa'm" ta fada hawaye na zuba mata, bai kula da ita ba. Ya cigaba da abinda yake yi har aka wuce da ita. Sakata suka yi a tsakiyar su, a hankali ta juya tana kallon shi yana abin shi. Juyawa tayi ta cigaba da tafiya, sai lokacin ya juya yana bin su da idanu. Bayan ya gama horon ya koma sashensa yayi wanka sabida zufar da yake karyo mishi.
.....
Wajen hantsi aka fito da wasu bayi mata biyu, sun ki magana kawai sun amince da sune suka turo macijin. Shiru fada yayi kafin ya bude baki kamar ba zai magana ba ya ce.
"A kashe su."
"Mai Martaba! Babu kuskure a hukuncin ka?" Inji Chiroma,
"Me zan musu? A cikin gidana a da'irar sansanina suka farmaki matata?" Ya fada,
"Haka ba zai kara kome ko ya rage kome ba, sai dai tarin bakin jini da ita Fulani Aminatu" Yarima Yakubu ya faɗa bayan ya mike zai bar fadar.
"Wannan shine mafi munin yanayi a tarayyar ka da Yarinyar da aka alakanta rayuwar ka da ita" ya sakai yafita.
**
Zauren Fulani Aminatu.
Jakadiya Rama ce a bayan Ajuji, bata zauna ba tana tsaye tana kallon kyawun zauren Fulani Aminatu.
"Lalle maraba da zuwa, yau muke shirin kai Fulani taga Yayunta"
"Ba zuwan tattaunawa nayi ba, an san Fulbe da kunya da kawaici sai ga labari yana yawo a cikin gidan Fulani Aminatu ta yarda da al'adar su tana bin Mai Martaba har turakar shi? Koda yake taya yar kwarkwara zata yi kunya! Kamar yadda kika saba turata ki turata ta hana shi idda nufin shi na kashe bayin da basu ba basu gani ba. Idan tayi hakuri zata isa inda yake, karki manta a nan macen da ta isa mace take rike kambunta ba kwaila ba"
Har ta juya zata tafi, Innayoh ta ce mata.
"Mace da ta isa mace ita Jarumin sarki ke bada rayuwar shi domin kare nata, idan har kwarkwarah tana da bakin magana toh tabbas matar sarki idan ta tashi magana ba za a ji muryan kowa ba! Ba zan raba had'in da Allah yayi ba, sai dai maki gani zai iya mutuwa"
"Ke baiwa!" Ajuji ta daka mata tsawa, murmushi Innayoh tayi sannan ta ce mata.
"Fusatar na me? Kin ji haushi ne? Idan rana tafito tafin hannun bai kare shi. Iya yau gare mu gobe ta Allah ce kiyi shiru ki ja bakin ki koma gefe kiyi kallon abin da zai faru ga sarki da Kwailar matar shi, barin da ba zai tab'a goguwa ba a tarihin masarautar nan labarin da zai zauna daram a zukatan al'ummar wannan yankin. Mun iya magana amma mun fiso ayi maganar mu haka zai karawa shukar mu yabbanya"
Kasa magana Ajuji tayi ta saka kai ta fita, sannan ta juya ta kalli Fulani Aminatu, da tayi tsuru-tsuru tana kallon su. Baki daya ba zata ce ga inda Maganar ya dosa ba.
Dan dukawa kaɗan Innayoh tayi tana kallon Fulani Aminatu.
"Daga yau ba zaki kuma fita ba, ki zauna anan, amma zan tura ayi magana da Baffa'm ki roke shi da ayi musu afuwa"
Hannun ta Innayoh ta rike, tana kallon ta kamar zata yi kuka.
"Innayoh yaushe zamu bar nan bana son nan mu koma gida" murmushi Innayoh tayi sannan ta ce.
"Zan kika fara zaman nan"
Mikewa tayi ta saka aka kira mata sarkin gida, can sai gashi ya zo.
"Fulani tana son ganawa da Mai Martaba ka gaya mishi"
"An gama" sannan ya fita, har fada anan kan tattauna batun abinda ya faru jiya, sarkin gida ya gaya mishi sakon Fulani Aminatu. Babu musu ya mike. Gyara murya Waziri Zakaria yayi ya ce.
"Baffa'm" cak ya tsaya kunya ta kama shi sam ya manta ko zai tashi sai an sanar yau sai gashi ya mike. Komawa yayi ya zauna, yana muzurai. Take sarkin fada ya fara kokarin mikewa yana faɗin.
"Gyara kintsi! Mai martaba zai tashi aikin gaggawa" watsawa Waziri harara yayi, yana tashi ya nufi shashinsa, Waziri da Galadima suna biye da shi. Yana shiga ya cire kayan baki daya ya sauya. A zauren shi ne farko ya gansu zaune dauke kai yayi kamar bai gan su ba.
"Baffa'm" inji Zakaria,
"Ban san yaushe na zama kakanka ba, amma zan hukuntaka zan baka aikin kula da bakin da zasu shigo da fita na masarautar nan baki daya daga yau aikin ya fara"
"Baffa sabida kawai nayi abu karami za a mai dani duba gari" Galadima bai ce uffan ba, sai da ya fita ya mike shima yana faɗin.
"Yawwan duba gari idan ka fita"
"Kawu har da kai?"
"Toh na daina"
Shi kuwa yana fita ya nufi shashinta ta, tun daga babban zauren ya fahimci yar sakalcin tana daki, yana shiga ya same ta, da dan dalago.
"Yawwa dan dalago, yaushe samu tafi gida na gaji da nan" gyaran murya yayi U shiga cikin dakin. Gyara zama tayi tana kara daura zomon kan cinyarta.
Shiru yayi yana jin tana zuba shirme da dan dalago.
"Tashi" ya fada mata, mikewa tayi ya kalle ta da kyau sannan ya ce mata.
"Baki iya kawo ruwa bane ga bako?" Ajiye zomon tayi, ta fita tana faɗin.
"Ai Innayoh ta gaya min" ta fada bayan ta nufi wani daki na musamman da aka ajiye kayan Abincin da aka tanada, wani tire ta dauko ta kawo dakin, an saka dan gamon da ake sakawa a kasan kwarya ya rike yar kamar ƙwaryar da yake rufe da damammen fura da nono. Sai kamshi kanumfarin da masoro da citta yake.
Dauka tayi ta mika mishi, tana faɗin.
"Baffa'm amsa ka sha?" Ba musu ya amsa, ya dama a hankali sannan ya fara sha, yana kallon ta komawa gefe tayi can ta zauna tana wasa da dan dalago.
"Zo kisha"
"A'a na koshi"
"Toh zaki dauki kayan ki" a hankali ta taso, tana kallon shi kafin ta ce mishi.
"Me yasa ba zaka sha ba?"
"Ban iya cin abinci ni daya ba"
Zama tayi sannan ta ce mishi.
"Innayoh ta hana ni cin abinci da wani"
"Ni ne wani?"
Sunkuyar da kai tayi tana matse hannun ta.
"Waye ni?"
"Baffa'm"
"Toh daga yau ni ba baffa'm bane, Nima ina son zama abokin ki kamar yadda kike daukar dan dalago"
Sake baki tayi tare da cewa.
"Toh ai kai ba zan iya daukar ka ba, kayi kato" ta fada kamar zata yi kuka.
"Toh lallai dole kiyi abokata dani"
"Ayya taya zan dauke ka kamar dan dalago?"
*Da alamu idan aka kwana biyu kallon dan dalago zata maka ka yanke dan banza ka huta, domin shi ya hana ka samun kanta*
"Toh shi kenan, me yasa kika tura a kira ni." Shiru tayi tana kallon kasa ta rasa me yake mata dad'i domin ta manta yadda suka yi da Innayoh.
"Baki ji bane?" Da sauri ta d'ago kai tana kallon shi kafin abin ta dawo mata rai, d'ago kai tayi tare da amsar ludayin hannun shi. Tana sha tana magana baki daya jikinta rawa yake ta ce mishi.
"Baffa'm! Ka gayawa Mai Martaba ayiwa su Hakama da Arewa afuwa ba zasu kuma ba. Idan aka kashe su ba zai kawo karshen kiyayyar ba. Haifar da shi zaka yi a madadin a haifi da me idanu ba. Baffa'm rayuwa da mutuwa duk na Allah ne muke sayan kiyayya muke sayan soyayya. Idan har mae martaba ya musu afuwa zai iya wucewa. Amma kiyayya tana iya rayuwa na tsawon karninnika a dakatar da kiyayyar tun Yanzun!" Murmushi yayi tare da kallon ta sannan ya ce mata.....
__________________________________
*Kai ma mai martaba da rigima kake taya Fulani zata dauke ka kamar dan dalago. Ka mata bayani yadda zata fahimta kasan yadda aka saka mana idanu yanzu tace kayi kato Allah kadai yasan abinda su Ooo zasu fada kaico☹️🤔*
#Mai_Dambu
[3/28, 11:49 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: KALLABI...!
A tsakanin Rawuna
Na
Mai_Dambu
EWF
**
*Fatan Alkhairi gare ku Yan uwa da abokan arziki Nagode sosai 😍🥰🤩🔥*
"Me kike so?" Ya tambaye ta cikin tattausar harshe. Goge kwallar da yake zubo mata tayi har lokacin jikinta rawa yake.
"Baffa'm a yafe musu" ta furta bakinta yana rawa, saka hannu tayi ta rufe bakin, domin wannan ne karo na farko da ta samu kanta da rokon wani , kuma baffa'm ba wani ba ko mahaifinta bata tab'a samun damar zama da shi haka ba. Kallon ta yake a hankali shekarunta basu kai rike abinda ya fada ba, girman ta bai kai shi ba.
Dan bata da wannan girman,
*Innayoh* zuciyar shi ta furta, kenan .
"Toh zan gayawa mai Martaba, amma zaki yi abu daya?" Da sauri ta d'ago kai tana kallon shi. Hararan dan zomon ta yayi da yazo kusa da ita.
"Zaki mai dani abokin ki?" Ya fada yana kallon cikin idanunta, itama shi take kallo, lashe bakin ta tayi tana me ƙoƙarin janye idanun ta daga kallon shi da ya mata kwarjini. Da sauri ta dauke kai tana kallon dan dalago.
"Kai fa Baffa'm" hannun shi ya kai saman labbenta, a hankali ya d'ago fuskarta da daya hannun shi, yana shafa kyawawan labbanta. Sosai ya janyo ta jikin shi yana kallon kwayar idanun ta. Kafin ya kai kai shi zuwa kunnen ta.
"Abotar mu babu karya, babu cikin amana gaskiya zamu kulla. Sannan zamu tafi ko ina tare kin yarda domin har wajen masarautan nan zan kai ki" kamar wata gunki haka ta tsaya yana magana da ita, a hankali ya mike ya barta durkushe da gwiwowin ta, sai da ya isa bakin kofar ya juya yana kallon ta. Murmushin gefen baki yayi sannan ya fita a dakin.
Zubewa tayi tana ajiyar zuciya, domin baki daya ya saka ta wani irin yanayi.
Tunda ya fita ya nufi shashinsa, ya rubuta sako zuwa ga mutanen fadar sannan ya badda umarnin a dakatar da kashe su hakama da arewa, sun samu afuwa daga Fulani Aminatu, dan haka wannan ba aikin shi bane, ita tayi musu afuwa kuma shima yayi musu, dan haka ayi kokarin kiyayye abinda da zai kuma had'a su.
**
Wurgi yayi da kofin hannun shi tare da fasa ihu yana faɗin.
"Ba haka nake son mulkin ba, ba haka nake so, so nake ayi mulkin da ko kasa taji takun mu sai ta girgiza. So nake talakawa su ji tsoron mu, kamata yayi mu addabi kowa da yaki wancan mutumin ya hana. Dole mulki ya dawo hannuna domin mune muka cancanta."
"Karka manta jarmai yayi mutu, yanzun saura tsinbura, idan har muka yi hakuri lokacin da ya fada na zuwa mana"
Kallon madubin gaban shi yayi, bai san lokacin da ya dauki kofin da yake shan ruwa ya wurgi madubin da shi. Yana ƙara faɗin.
"Lokaci-lokaci lokaci lokaci! Yaushe lokacin zai yi ne?" Ya fada da karfi, dafe goshinsa yayi sannan ya kwanta.
**
Shekaru goma sha tara.
1789
Masarautar Sahil.
Masarauta ce ta suke tsakiyar sahara, masarauta ce da take da karfin mulki da ta tsafi. Musamman camfe sunyi imani da camfe.
Masarautar an wani gari ne aka ganta a wannan wurin da Alummomin ta, sun shafe sama da karninnika a wurin, basu tab'a fita yaki ba, amma kuma babu tsuntsun da ya isa ya gifta ta masarautar. Suna da wata gunki da suka sassaka shi da itacce me suna hil ita wannan gunki siffatar kamar mace ce da goyon daya, gefen wuyar ta kuwa kamar an sare ta, a duk bayan shekara biyar ana sadaukar da jinin wasu kabilu masu suna Na.
Wadannan kabilun sun kasance wasu shashi na larabawa makiyaya da suka yo hijira daga wata Alkarya da take tsakanin kogin Nile da kasar Habasha, kasancewar ana samun rashin zaman lafiya da kabilun yankin wurin. Cikin dare suka fada masarautar Sahil. Koda gari ya waye aka ga baki nan aka tafi masarautan inda aka samu sarki Arkhan aka gaya mishi. A lokacin sarki yana cikin matsanancin damuwan rashin da namiji.
Ana gaya mishi ya tura a kira bokan shi me suna zeela, kafin dan aiken ya iso bokan ya bayyana.
"Ka sani Ya mai Martaba, kukan ka ma shekaru arba'in zai kare ne da zaran ka samu daya daga cikin yan matan da suka yo gudun hijira, ka yi tarayya da ita kafin kusfewar rana da wata. D'igon ruwan da zai shiga jikin ta shi zai haifar maka da namijin duniya. Zaki kuma gamzaki wanda zai zama fasa taro. Idan aka samar da shi dole jinin uwar ya zama sadaukarwa ga Hil uwa mabada mana. Kafin nan bari na gaya maka sawaye mutane nan nan. Su din mabiya wata addini ne masu dabi'ar dukawa. Sannan suna da wata baiwa na musamman na iya sarrafa maganin kowacce ciwo, sannan suna da wata irin karfin da ya fi na sihiri. Sadaukar da jinin uwar zai karawa masarautar mu karko da nisan kwana. Dan kuma zai kasance gaggarabadau. Sai dai tasirin su yana faruwa ne daga daren da rana da wata suka yi kusufe. Idan kuma namiji ya aure su, suna iya kara Mishi karfin mulki karshe mulkin yana iya dawowa hannun su, ba zan yarda da wannan yanayin ba shi yasa nake kallon Gara ka ajiye dayan su domin samun wannan babban rabo"
Kallon boka zeela yayi kafin ya bude baki yayi magana bokanya Tursi ta bayyana.
"Zeela me yasa kake aiki da jahilci? Ina gaisuwa Mai Martaba. Babu macen da zata haifa maka da namiji a cikin su, dan ko an haifa zai koma. Ita wannan macen da zaka sadaukar ba a haife ta ba, sai dai taurari sun tabbatar tana cikin su. Kafin nan a cikin matan a duba mace da take da alamar wata a jikin ta idan aka samu sai a fara kawo maka ita sauran mutanen ayi sadaukarwa da su. Domin idan ba haka ba zasu yi tawaye kuma zasu iya daukar kasada domin baiwar su bata kanannun mutane be."
**
"Shugaba akwai matsala anan" wani matashi ya faɗa.
Jinjina kai tsohon yayi tare da cewa.
"Amjad ka ɗauki ke su, ƙaddaran tana tare da su, ku bar wannan nahiyar ku tafi." Ya kalli wata karamar yarinya da take tsotsar hannu.
"Karka had'a su wuri guda, domin zasu iya bayyana baiwar su ka raba kan su. Idan ta kama bauta ce ma su. Ban shirya ganin tashin hankali"
Zana inda suke yayi sannan ya d'aga hannu yana addu'a, tare da yiwa Ubangiji kirari, wani irin duhu ne ya mamaye inda suke kafin ya shiga washewa. Babu mutumin da Yan matan.
Suna barin wurin dakarun sarki na zuwa aka kwashe su da karfin tsiya aka kai su fada, anan aka shiga duba su babu yan matan.
"Kai me farin gashi ina sauran Yaranka"
"Babu su iya mune"
"Ku sake dubawa, ko ku kashe su baki daya."
"Da haka kuka yi tabbas da yafi sauki akan mu bayyana muku inda sauran suke"
"Kenan kun san inda suke?"
"Bamu sani ba, amma mun san kana niman Kallabi."
"Tursi babu wani mafita?" Zeela ya tambaye shi.
"A sadaukar da jinin su amma ba dukkan ba, domin ba mamaki yan matan su kuma haifar masu irin wancan baiwar"
Haka suka wuce da mutanen a take aka yanka tsohon sannan aka watsa jinin shi ga abin bautar su hil. Kafin nan kuwa garin ya dauki wata irin hadari da ruwa lokacin guda..
Bayan shekaru sha tara.
Bincike suke baki dayan su bokanya Tursi take kafin ta d'ago kai tana kallon Sarki Arkhan.
"Akwai yiwuwar akwai dayan su a raye sai dai sun yi wata irin nisa na ban mamaki." Sake mai da kanta tayi tana cigaba da bincike jini ya shiga suka daga hancinta. D'ago kai tayi tare da cewa.
"Tafiyar shekara hudu zuwa biyar zai kai mutum inda suke, sai dai tauraro daya ne yake bayyana, daya yana boye. A cikin wannan yanayin cikar shekara biyar din nan wata da rana zasu samu kusfewa a cikin wannan yanayin Imma a kawo maka dayansu ta samu digon ruwan ka Imma ayi ra zubda jini domin nan da wani lokaci shekarun fuskarta rayuwa ce"
"A ina? Yaushe?" Sarki Arkhan ya tambaya a gaji burin shi magaji. Burin shi a haifa mishi da namiji,
"Idan har kayi hakuri hakan zai faru ne ta sanadin shekarun rayuwar macen da zata iya daukar haka"
Shiru yayi yana kallon su amma baya jin yana da rabon samun da namiji, kuma Sadauki wanda zai dauki mulkin kasar baki daya. Baya son ya rasa wanda zai gaje shi da karfin sihirin shi yana da y'aya mata babu adadin amma namijin yake nima.
"Kince daga nan zuwa Nahiyar shekaru huɗu zuwa biyar. A shirya yaki domin dauko ta" ya fada cikin izza.
"An gama"
**
Masarautar Gobir.
Yau kwana huɗu kenan ana niman dan dalago, sama da kasa babu labarin shi. Abin duniya ya taru ya dame Aminatu, tana zaune ta Zubawa kofar shigowa zauren ta ido, ga bayi mata sun yi jungum-jungum.
"Ayya Fulani ki saka wani abu a bakin ki mana"
"Taya zan yi hakuri bayan an nime shi an rasa" ta fada tana kuka.
Shigowar Mai Martaba da kwana uku kenan baya nan, ya shiga cikin zauren da Sallama. Mika mishi gaisuwa suka yi kafin kace me sun cika mishi gaban shi da abincin, sannan suka bar wurin. Mika mata hannu yayi ta taso, fashewa tayi da kuka. A hankali ya janyo ta jikin shi, yana me kallon ta, turaren da Innayoh ta saka mata yana ratsa hancin shi. Saka kan shi yayi a dokin wuyarta, ya shiga goga hancin shi, yana tambayar ta.
"Ke da waye?"
"Dan dalago ya b'ata" ta fada tana zubda kwalla, dumin kwallar yana ratsa jikin shi sabida saukar da yake a hannun shi. Juyar da ita tayi yana kallon yadda fuskar nan tai jajjur. Lashe bakin shi yayi a hankali ya kai bakin shi kan nata. Ya sauke mata karamin sumbata, lumshe idanun ta tayi kwalla na zuba mata.
"Baffa'm!" Ta kira sunan shi, tana me janye fuskar ta, a hankali ya mai da ita ya kwantar, yana kallon yadda take shirin bare mishi baki, juyawa yayi sannan ya mike. A shekarun shi yana bukatar abokiyar rayuwa, shi kuma matar da yake kallo tayi kankanta.
Fita yayi baki daya, sannan ya koma shashinsa.
"Ka kira min Galadima" ya fada a sanyayye,
"An gama"
Bayan wani lokaci sai gasu tare sun shigo.
"Allah ya baka nasara, gani nan"
Shiru yayi, kafin ya ce mishi.
"Ina bukatar wacce zata dauke min nauyin Aminatu."
"Allah ya baka nasara, kayi hakuri mana. Akwai alkhari a tarayyar ka da ita idan ka sako wata cikin al'amarin ku zai lalace. Kayi hakuri"
"Toh ya zanyi?"
Mikewa Galadima yayi, sannan ya kalle shi.
"Kai namiji ne, janta jikinka sakata a jikin ka zai saka kaji sauƙin wasu abubuwan, ka koya mata zama a jikin ka yadda kome nata zai tsayar da kai amma matukar ka sake taraba shimfida da wata haka zai kasance mata tashin hankali. Zai haifar da kishi idan har wacce zata zo ka mai da ita abar biyan bukata Aminatu zata wahala. Don Allah kayi hakuri"
Shiru yayi bai ce kome ba, kafin Galadima ya cigaba da cewa.
"Kai ka gaya min baka son ayi kishi me zafi a gidan ka kuma kana niman baiwa dan nasan ba aure zaka yi ba sai dai Kwarkwarah" haka Galadima ya gama maganar shi bai ce uffan ba. Har ya tafi.
Wa shi gari
Tura sako yayi a kawo mishi Aminatu kasancewar ranar Laraba ne. Tunda aka fadawa Innayoh, ta sakata a gaba tayi mata wanka, a wurin wankar take kallon kirjinta da kan dukiyar fulanin ta yake dan turo kai. Kasancewar ta daura mata mayafi, a saman jikinta. Goge mata jikin tayi sannan ta ce mata.
"Fulani idan Baffa'm ya tab'a jikin ki karki gayawa kowa kin ji, mutuwa ake idan kika fada, karki ji tsoro kin ji amma kiyi shiru da bakin ki" gyada kai tayi tana kallon Innayoh, haka ta gama shirya ta, sannan aka raka ta har babban zauren shi suka dawo, yana zaune yana rubutu. D'ago kai yayi ya mata murmushi. Ganin haka yasa ta nufe shi ta zauna. Haka ya cigaba da rubutun shi, sannan ya tura mata wani katon tire dauke da kayan ciye-ciye.
A hankali take ci tana mishi magana, sannan ta tura tiren komawa gefe tayi ta dangwali tawada ta manna mishi a gefen kumatun shi inda ya lubb'a. Lashe baki yayi yana ci-gaba da aikin shi dauke fatar raƙumin tayi da yake rubutu a cikin shi ya nade can ta ce mishi.
"Baffa'm har yau babu dan dalago"
*Ina zaki ga dan banza bayan ni da su waziri mun cinye dan banza*
Abinda ya faru, duk yadda yabi sai ya lura dan Zomo dai ya hana shi samun hankalin ta, shine yasa Innayoh ta kama dan banza aka bawa Sarkin gida ya yanke aka gasa musu, ya haɗa da guzirin shi.
Tunawa da yayi shima cikin jimamin ya rungume ta, yana bata hakuri. Gudun kar amishi kallon zallamamme amma babu abinda ya isa hana shi samun matar shi, yanayin da yake samun kan shi yasa baki daya. Cikin wani irin shiririta ta fara kokarin zamewa a jikin shi tana wani irin yauki da kiriniya, tana wani irin zamewa kamar karkashi. Baki daya kamshin ta da wani yanayi me dadin Bala'i yana ziyarta yanayin shi na lafiyayyen namiji cikakken jarumi. Wanda ya san me yake yi kuma yasan waye shi.
A hankali ta d'ago kai tana kallon yadda ya lumshe idanun shi, hannunta, ta kai kan tawadar ta shiga zana mishi akan fuskar shi. Bude Idanu yayi akan ta..
"Ah" had'a goshinsa yayi da nata,
"Zan miki bulala"
"Kayi hakuri" lallubar hannun ta yayi tare da jifa yatsarta a bakin shi yana tsotsa yana me lumshe idanun shi.
"Baffa'm!"
"Hmm"
"Karka cinye min hannu"
"Hmm" ya fada bayan ya bude idanun shi kanta, zare yatsar yayi yana me sumbatar tafin hannun ta.
"Baffa'm! Wata rana zaka yi fushi da ni?"
Sosai ya ware idanu shi akan ta, yana kallon cikin idanunta, itama shi take kallon.
*Fulani Aminatu ita zanen ƙaddara ba bawa keda ikon zata ba, ilahi yake zanata idan har akwai tafiyar Ƙaddara toh ba makawa sai na mai da ita sadaukarwar ƙaddara*
A zahiri kuma murmushi yayi mata,yana jan kumatunta ya ce mata.
"A'a"
Mai da kanta tayi ta kifa a kirjin shi, tana jan shashekar kuka.
"Baffa'm!"
"Hmm! Fulani"
"Karka zama kamar Baffana kaji. Karka manta dani kaji"
*Waye ya gaya miki marubuci yana rubuta labarin shi! Idan babu toh tabbas ba zan taba bada labarin mu ba*
"Ina tare dake" ya fada mata,
"Baffa'm! Karka zama sarki domin akwai dodanin da zasu shiga cikin mu"
*Ba halicci wani dabbar da zai shiga cikin mu ba*
Kukan da bata san dalilin shi ba, bata kuma san hujjar yin shi ba, take yi tana karawa, har da shiga jikin shi, ajiyar zuciya ya sauke. Sakamakon jin tayi shiru, yana leka fuskar ta yaga tana barci, gyara mata kwanciya yayi sannan ya dauki kayan rubutun shi ya ci-gaba yana yi yana
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 39