min dangantakar da yake tsakanin mu? Kai adalin sarki ne amma kasa sani a yau a yanzun mulki ya haramta maka har abada kujeran da kake kai na cikin Jikin Anum ce, amma a matsayin ka na wanda yake iko na yau da na gobe zaka iya taimakawa wurin hukunta masu laifin da ake tare da su "
Shigo da Bingel aka yi, sannan Gidado ya juya ga Sarkin gida.
"Ina jin ka sarkin gida"
" A lokacin da muka fahimci Sarki Bello yana tare da Aminatu ba zai iya rabuwa da ita ba, sai kawai muka yi amfani da yadda yake gaya mana abinda take mishi na gujewa shimfidar shi, naso Aminatu tun daga ranar da na fara ganin ta, dan haka burina na raba ta da Sarki Bello duk da Abokina ne tun yarinta,sau gashi ba mutu akan matar shi, lokacin da na fahimci kudirin Waziri shima ta tafi akan soyayyar Aminatu da kishin ta sai na boye nawa halin na tsaya a bayan shi muka yi ta cutar da Sarki Bello ina kuma karawa Waziri kaimi, lokacin da yake adawa da Bello,duk da Galadima yaso ya fahimce mu sai muka yi kokarin dakatar da shi ta hanyar lalata duk wani shirin sa.
Amma daga baya sai da ya gano akwai hannuna a jikin Bello dan haka ya min gargadi akan na cire ko kuma ya kashe ni, nayi bakin cikin haka, shi yasa koda muka dawo wajen gari na sanar da waziri sai yayi kokarin dauke kai kamar bai san muna nan ba, har zuwa Gidado da shiga masarautar da yayi yana zaga gari, tun lokacin muka so kashe shi, toh sai muka fahimci ba zai iya mulki ba, sai ta gaya mana dan uwan shi yana nan mayaki ne, koda aka fara binciken sai ga Matar Lamidon ta bayyana, ba wai iya Lamido ne zai iya da ita ba,hatta Gidado zai iya sarrafa baiwarta sama da Lamido, sai aka yi dace babu wani alaka akan shi da ita, sai dai da zai tafi ya bayyana min na gayawa Baffa'm yana son Yarinayr, ni kuma domin na haifar da gaba da kiyayya a cikin gidan Bello sai na gayawa Baffa'm amma idan ta auri Gidado mutuwa zai yi ya haɗa ta da Lamido, koda yazo sai aka yi dace ya amince, amma shi bai da ra'ayin Anum,har na raka su zuwa Borno anan na gayawa Gidado cewa.
Mahaifin ku baya kaunar ka domin kai na kasashe ne, ba zaka iya mulki da kome ba, shi yasa na dauki matar da kake so ya bawa Dan uwanka dan baka da amfani, na cusa mishi tsanar dan uwan shi kafin su zo Gobir, so nake Yaran Bello su kashe junan su bakin ciki ya kashe Amunatu ni kuma na kashe Bello na dauke Anum, sai aka yi dace daga Uwar har Uban sun tankwara Gidado, har aka yi bikin bayan tafiyar Gidado, shine na gayawa Lamido domin idan gidado yazo lamido ya sa a kashe shi. Nace mishi naji labarin matar ka Dan uwanka yake so, har ba bashi wasikar gidadon da na ajiye, wanda na samu a ranar da na shiga dakin shi a Maiduguri. Sai dai na lura soyayyar Yaran Amunatu halittace daga Rabbil Alamin ba zasu tab'a cutar da juna akan mace ba. Kwarai naso dawowarsa Lamido ya kashe shi,sai akayi rashin dace shi kuma a bangaren mulki Lamido ya hana Waziri sakat, ni kuma a cikin gidan su, sun hana ni sakat shine muka hada karfi da karfe muka kashe shi sannan muka tura Barkindo ya fadawa Anum ce wa Gidado ne ya kashe mata mijinta yadda koda an wayi gari za'a bashi mulkin zata hana ga hanyar zuciya ta kashe shi a gaban jama'a. Sai akayi dace ta zauce a kan mijin ta har yau bata dawo daidai ba, sai dai a yadda Lamido ya soke ni, na zata zan samu kulawa daga Waziri amma ina mutumin nan yasaka aka kai ni kogin wajen gari aka wurga ni a cikin ruwa wannan itace cin amanar da aka yi bayan wanda muka yi, A yanzun na ƙara yarda da Bello yayi Kuskuren bawa mayaki mulki da manazarci ya bawa mulkin TOH wallahi babu wanda ya isa ya kawo har yau, domin a cikin shekaru talatin da wata shida da kwanaki ake shirin nan kai kuma a cikin wata daya da kwana takwas ka gama shirin ka wannan shine ake kira Jarumta ba iya takobi ya. Ahhhhhh!" Yayi shiru sakamakon soke Sarkin gida da Waziri yayi a makoshi.
Faduwa sarkin gida yayi yana shure-shure, har rai yayi halin shi.
Da gudu yayo kan Gidado,kafin ya iso barkindo ya yi wani tsalle ya dira tare da suke junan su. Inda ya kare Gidado.
"Yazidu!!!" Ya kira sunan shi da ƙarfi, a hankali Barkindo ya kuma soke shi sai da ya fito waje, shi kuma ya koma da baya ya rike gefen cikin shi.
"Shiiiiiiiii" Gidado ya durkusa kadan a gaban shi.
"Ayya karshen tuka-tiki tak, ka kashe Ubanka yau Danka ya kashe ka, kun bata rawan ku da tsalle babban burina a wanke kanku daga zunubi, maza ku fitar da shi, daga masarautar nan sannan a bawa Yazidu kulawa a lullube karagar da farin mayafi, nayi alƙawarin kafin Lamido ya cika arba'in zaku biya bashin da kuka ci, dan haka Bingel ku fitar da ita daga masarautar kar na..."
"Mahaifiya ta ce "
Juyawa yayi ya fuskaci Barkindo.
"Idan na ce dan yi amfani da zuciya har kai sai na datse wuyar ka, balle ita laifin ka na hada ni da matar dan uwana, dan haka ta fita a cikin masarautan kai ne dan uwana da bani da wani bayan shi ka sake ka kulla wani abu a ranka wallahi mutuwar wulakanci sai tafi kome wanzuwa a rayuwar ka, dan haka ka bi bayan su a jinyace ka, Muna da Ammyn da Baffa'm zasu bamu soyayyar da ya dace mulki kuwa babu kai babu shi har duniya ta tashi idan aka kwana biyu zan san yadda zan yi da kai lowa ya b'acce min a fadar "
Akan lokaci kowa ya kama ganin shi, shi kuma ya zauna a kasar fadar baya. Kowa ya watse, Baffa'm da ya zauna shima a gefen shi, sai lokacin ya daura kan shi a kafadar Gidadon, yana kuka hankali.
"Ina son ku babu wanda na ware saboda daukakar shi, tunda na dauki littafin ka na soyayyar bayan mutuwa. Na fahimci kai taka baiwar daban yake, da na kuma duba wata rubutun ka me mulki a Shari'ar Muslunci, sai na fahimci kai zaka iya mulki amma rashin baki ba zai baka damar haka ba, domin mulkin ce ta zabi Lamido ba ni na zabe shi ba, ban san dalilin da yasa suka min haka ba, ka yafewa dan uwanka da ni kaina "
Murmushi yayi sannan ya ce.
"Maguzanci da rashin wayewar musulunci yasa aka yi kome da kuma amfani da duba haramun ne a musulunci, ban san dalilin da yasa kuka yarda da cewa Lamido idan suka hadu da Anum zasu bada sa'a me yawa, a'a haramun ne soyayyar da ƙaddara ce ta haɗa su. Nasan kome zai faru yana kan turban addinin gargajiya da aka fara ne tare da yarda da Camfi, matsalar Anum ba wata matsala bace idan za a magance shi haka ma Ammyn za a iya magance nata idan har za'ayi amfani da magungunan Musulunci, ba wani tashin hankali bane. Sannan ranar da Lamido ya cika kwanaki arba'in ka koma bakin mulkin ka, domin kai ne ka dace da zama sarki a lokacin nan domin abinda Anum zata haifa mulkin na Uban shi ne."
Cike da mamaki yake kallon shi kafin bakin shi na rawa ya ce mishi.
"Baka sha'awan mulkin ne?"
Hawaye ne ya zubo mishi sannan ya sake murmushin yake ya ce mishi.
"Har abada na yafe mulki da duk abinda yake cikin shi, ina nan domin kare kujeran daga masu kawo hari "
"Don Allah kar ka ce min haka?"
"Wallahi na fada Baffa'm na haramtawa kaina kamar yadda dan uwana ya haramtawa kan shi farin cikin shi domin ni na hakura ka cigaba da rike mulkin kafin muga abinda zata haifa "
Duk yadda Baffa'm yaso yayi mulkin haka yaki, koda suka shiga cikin gidan Ammyn ma tasaka baki amma fir yaki sai ma cewa da yayi zai bar masarautan baki daya yasa suka hakura, tare da mamakin yadda yaki amincewa.
*
Bayan kwana biyu ne aka yi addu'ar arba'in Lamido Baffa'm ya koma kan mukaddashin Sarkin Gobir kafin asan abinda Anum zata haifa. Washi gari shi da Barkindo da ya samu lafiya, suka shirya suka raka iyayen Anum Somalia, a ranar da zasu tafi ne Kakar Anum take kallon Ammyn kafin ta ce mata.
"Tun da na ganki Aminatu nake ganin kamar ki da Yar Uwata Amratu, wacce aka ce Sarkin Gombe ya mai da ita kwarkwaran shi"
"Ikon Allah kece Rusailah?" Innayoh ta tambaye ta, ai kuwa take aka fasa tafiyar aka bude sabon filin hira, da koke koke da kaunar juna, ita kan Yar macukule sai zare idanu da zaran an bata haushi sai ta saka hannu a baki ta fashe da kuka (🤣🚶🏾♀️😒😏😂 Anum yar macukule
#Mai_Dambu
[6/26, 10:51 AM] Zahrah Maman Khausar: KALLABI..!
A Tsakanin Rawuna
EWF
BABI NA SABA'IN DA SHIDA
ALLAH YA BAKU HAKURI TEAM YAR MACUKULE 😜
________
Sosai aka kuma ganin juna kafin suka kuma sake shiri kiri-kiri Ammyn taso bin Kanwar Mahaifiyar ta, sai da Rusailah tayi ta fada kafin tayi hakuri, ana gobe zasu tafi ne Ammyn ta lura da baki daya bata ganin Haimah, dan haka yana zaune Anum na cin abinci dan baki daya taki yarda da kowa sai Saraki.
"Bana ganin Haimah?"
Shiru yayi kamar bai ji ta ba, dan wani lokacin haka yake wannan bakin halin idan har yana gaban Anum toh wallahi duk wanda zai mishi magana baya tab'a amsa mishi.
"Magana nake da kai fa"
Dakyar ya d'ago kai yana kallon bakin Anum da tayi dagaje -dagaje da furar da yasha zuma tana ta lasa, kura mata ido yayi kafin ya cewa Ammyn shi.
"Tana gidan su"
"Ka kyauta? Kana ganin haka shine adalci? Ita Meye laifin ta? Tasan halin shi d shegen riko dan haka ta sassauto da murya ta ce mishi.
"Ba a hukunta laifin wani akan wani, ka duba da kyau ita taimako tayi idan Allah ya hada ka da shu'umin uba ya zaka yi?"
A hankali ya d'aga habbar alkyabbar shi ya goge mata bakin ta, sannan ya mike.
"Zan duba"
"kayi hakuri" ta fada mishi.
"Ya wuce ai Ammyn"
"Saraki ina zaka?" Aum ta tambaye shi.
"Zan tafi unguwa ne na sayo miki rake" dariya tayi wanda ya bayyana hakoranta baki daya. Sannan ta gyada mishi kai.
Fita yayi har gidan su Haimah, hannun shi rike da inda ya gogewa Anum baki yaki sakewa, da sallama ya shiga cikin gidan. Sake mafificin da take fifita Mahaifiyar ta tayi jikin ta yana tsuma.
"Assalamu alaikum babu kowa ne?" Ya kuma sallama a karo na biyu.
Cikin raunaniyar murya ta amsa.
"Wa'alaikumunsalam shigo"
Ta fada bayan ya ja mayafi tana rufe jikin ta.
Kallon ta yayi yaga har kafarta rawa yake, wani mugun tsoron shi take ji, a hankali ya isa gaban ta, tana kokarin juyawa ya janyo ta jikin shi, a hankali ta sake wani irin kuka, tana me ƙoƙarin janyewa daga jikin shi.
"Ya isa!"
"Ka gafarce ni, da Mahaifiyata aka min barazana wallahi ban so a yi haka ba"
Sake rungume ta yayi yana faɗin..
"Shiii ban tambaye ki ba, kawai ya isa ya jikin Umman taki?"
"Tana daki" ta fada cikin matsanancin kuka , matseta yayi a kirjin shi yana shafa bayan ta.
"Ya isa haka!" Gyada mishi kai tayi sai da ya tabbatar tayi shiru sannan ya janye ta jikin shi suka nufi wurin Ummanta da take kwance ba lafiya.
"Sannun da zuwa kai ne da hantsi haka?"
A hankali ta d'ago tare da kallon Haimah da take rab'e,
"Toh ki bashi ruwa mana" da sauri ta juya zata fita ya dawo sa ita.
"Dawo ki zauna"
Kallon Umman ta tayi sannan ta sunkuyar da kai,
"Da ka bari ta kawo maka ruwan" ganin yadda ta dage yasa shi sake hannun Hasinah ya kalli Maman Haimah. Ita kuma ta fita da sauri.
"Tunda ta taso a rayuwar ta babu abinda ta sani sama da tsoro, musamman na bingel, tunda bingel ta gane yadda azzalumin Uban su yake ina-ina da Haimah yarinyar nan ta daina farin cikin ya kasance bata da wani aiki sai amsar cin zarafi daga Bingel. Zan so ka duba bayan ta, zuwa kirjin ta, kuma a haka nake hakuri. Kasan yadda mace take ji idan ta fahimci mijin ta ya ajiye wata mace? Ita kuma tana sa karfin da zata iya gogawa da kowa? Haka nake kallon Haimah ta taso kamar baiwa domin baiwa ta fita daraja, ban kuma fahimtar tsagerancin Zakaria ya kai haka ba, sai da na fahimci ya jima yana jifar ahalin shi da kowa da kowa da mugun nufi, bani mantawa ya tab'a daukata muka je wurin wani boka, inda yake gaya mishi ba zai tab'a mulki ba sai dai dan shi yayi mulki, a ranar nayi kuka kamar raina zai fita Sabida sabon al'amari ne da yazo min sai akan ne yake gaya min ai shi babu bokayen da bai sani ba, Dan t yana shekaru sha takwas, kenan tun nad'a sarki Bello. Don Allah ka yafe mana ni da ita wallahi bata da cikakken farin cikin idan ka cire ta a jikin ka ka ga halin da nake ciki ya nakasa ni ban sani ba ko zan rayu, Haima yar kace, idan ma kana ganin zaman ku ba zai yiwu ba, zska iya sake ta amma ka nima mata miji na gari wanda zai rike maraicin ta, domin tun tana yarinya take cikin maraici har girman ta, muna raye amma bamu da yadda muka iya haka ta rayu a cikin wannan yanayin don Allah ina niman gafarar ka"
"Ya wuce wallahi babu abinda kuka mana, kuma taku jarabawar kenan" ya fada daidai shigowar ta, da ruwa ta ajiye mishi.
"Gashi" tausayi ta bashi, daukar ruwan yayi ya kurba kaɗan sannan ya mike yana me kallon ta.
"Zan wuce, gobe Insha Allah zan mai da Anum da kakar mu Somalia zan fadawa Baffa'm za a gyara muku sashin bingel sai ki zauna a can ita kuma ta koma dakin ta,.idan tana da ra'ayin idan bata da shi ta gayawa Baffa'm kafin na dawo"
"Me yafi haka dadi! Ai bata da wani zab'in da ya wuce haka waye zata samu da zai rike ta kamar kai? Ubangiji ya karawa Fulani Aminatu da Sarki Bello nisan kwana, ya jikan Lamido da Hadizah ya sauki Fulani Anum lafiya"
"Amin Ya Allah " ya fada tare da musu sallama, bayan tafyyar shi Innayoh taxo da wasu bayi suka kwashe kome na gidan sannan aka ɗauki Umman. Haimah zuwa cikin gidan,
Su kuma washi gari suka bar masarautan tare da nufar Somalia inda ya bar Barkindo sabida ya zama shine Babba da zai tsaya a gidan kusa da Baffa'm.
Sai da suka kwana uku a hanya, yada zango kawai suke suyi sallah da hutu sannan su wuce har tsawon kwanaki biyar, a ranar ne suka yi wani hatsari domin an toshe hanyar wucewar su, garin su bude hanyar ne wasu irin gwamki wato biri me suffar mutane, suka dumfari keken da mata suke ciki, ihun Anum ya ji ya juya hankali zaro kwari da bakar shi yayi ya jera guda bakwai a cikin shi sannan ta ja da mugun karfi yasake musu, cikin wani azazzaben zafin nama yake sake musu bakwai-bakwai. Yana isa cikin shi kuwa ya zare takobin shi, ya shiga azababben yaki yana kashe su kamar ya samu kiyashi, duk bala'in fadar su sai da ya zame musu alak'ak'ai ya zame musu kamar guguwar annoba, sarar su yake kamar ya samu damin dawa, sai da ta kai yana girbe su kamar wanda aka bashi nomar masara, jikin shi sai digar jini yake kamar an juye mishi jinin su akan shi.
Sai da suka shiga gudu yana bin su, domin yau sun gamo da gamonsu, kafin ya kyale su.
Juyowa yayi ya nemi wani dutse ya zauna a kai, a take dakarun suka fara tona rami kafin ace me sun tona rijiya, dan haka a lokacin aka shiga diban ruwa ana wanke shi da shi, baki daya dakarun sun shiga hankalin su, domin wani lokaci idan yayi abu zaka rantse da kasungumin mayaki ne, dan haka da suka ta zuba mishi ruwa.
Sannan bayan an wanke shi ya nufi keken da take ciki ita da Mahaifiyarta da kakarta.
Tana ganin shi ta fashe da kuka. Tana kokarin saukowa daga cikin keken.
"Ki zauna yanzun zamu tafi"
Daga haka ya rufe kofar, ta wuce abun shi duk ihun da take, bai saurare ta ba.
Haka suka cigaba da tafyya, kallon shi Bintu tayi tana son magana amma tsoron amsar da zai bata yasa har suka isa Borno inda suka samu kyakkyawar tarb'a.
Kwanan su biyar suka wuce, Somalia bayan tafiyar su Bintu take kaiwa Uwarta korafin alakar Gidado da Anum. Bata kulata ta ba, sai ma fadar da ta mata akan ta kwantar da hankalin ta, su zauna lafiya.
A kwanakin da suka diba kafin su isa Somalia, dakyar ya kaucewa Anum baki daya gani take kamar Lamido ne,
Koda suka isa bai yarda ya kara kwana ba, domin suna shiga cikin gari ya juya tare da musu sallama, haka tayi ta ihu tana kuka, dafe kirjin shi yayi yana jin zafi. Bashi take so ba, mijin ta take so, mijin ta take bukata, ya hakura da ita har abada ba zai,kuma saka kan shi cikin al'amarin ta ba.
Bayan sati Uku ya dawo daga can amma Bintu tana Maiduguri zata kai wata biyu, dan haka yana dawowa ya shimfida rayuwar auren shi da Haimah, duk sa har lokacin bata sake jikin ta da shi ba, sai dai Tausayin ta yasa shi jan ta a jikin shi, kallon kirjin ta yayi musamman kan nononta da ya sha bulalar Bingel, sai bayan ta shima ya sha duka dan sun farfashe sai tabon bulalar, da wannan ya shirya rayuwar shi da ita, sai da ya jinjina hakurin ta, domin tana jin shi har ya samu gamsuwa da ita bata koyi tari har ya gama, ba karamin wahala ya bata ba, amma yarinayr nan ko motsi bata yi ba, shi da kan shi ya taimaka mata ta gyara jikin ta, sannan ta dawo ta fara kokarin gyaran dakin da suka bata musamman gadon, yana fitowa ya samu tana shimfida zanin gadon.
Amsa yayi ya shimfida mata wannan ya riko hannunta,
"Ke ba baiwa bace ke ma Y'ace karki kuma wahalar da kanki kin ji ko?" Hawaye ne ya zuba mata ta zube a gaban shi tana faɗin.
"Don Allah duk ranar da ka ga na fara kokarin kauce hanya, ka kashe ni shine Alfarmar da nake roko a wurin ka, karka bar ni na zama guba a wurin mutane"
D'ago ta yayi ya Kum rungume ta.
"Waye ya ce miki zaki zama guba? Babu abinda zan miki" tun daga ranar ta zama wata irin baiwa a wurin gidado, shi kan shi baya jin dadin yadda take tsayawa kamar baiwa, dan haka suka janyo ta a jikin su ita da Barkindo, basu suka yi laifi ba amma sune suke amsar laifin da wasu suka yi .
Bayan Fulani Bintu ta dawo, taso fitar da kishin ta akan Haima, amma Gidado da Innayoh suka ki, sai da ya bude mata wuta ta nutsu, daga baya sai ta fahimci Haimah tana da hakuri bata ma cika magana ba,
**
Bayan wata takwas.
A hankali yaji wurin ya dauki sanyi, kafin kace kwabo ya fara atishawa, tafoya yake cikin sauri har ya fito inda haske yake.
Hango Lamido yayi rike da Yara biyu,
Kallon shi yayi sannan ya sake murmushi yana mika mishi daya yayi hannun shi.
"Dawa suke kama?"
Leka fuska jaririn yayi yana kallon shi, yana kallon shi.
"Dan waye?" Juyawa yayi ya kalli Anum da take kwance.
"Itace ta haifa"
"Lamido!" Ya kira sunan shi.
"Gidado zan tafi Nagode sosai kacewa Ammyn ta daina kuka, nasan kewa take kuma ga shi nan ya zo kace ta daina kewa kaji, shi da Anum yanzun mallakar ka ne, karka haramtawa kan ka abinda yake halal a gare ka. Nagode sosai kacewa Baffa'm sakon shi yana isowa sosai, shi da Ammmy, ga amanar nan ka rike su domin naka ne"
Bude baki yayi yana son magana amma ya kasa furta koda kalma ɗaya.
"Ba zaka kuma gani na ba, har abada nagode "
Daga wannan zancen ya nufi wata kofar azurfa ya wuce ta jikin kofar, kallon yaran yayi yana kallon shi, ya taka a hankali ya ajiye mata Yaran ta, sannsn ya tsaya a kan ta.
Bude idanun shi yayi tare da kallon waje sabida sanyin da yake ji a mafarkin har lokacin,tashi yayi jikin shi yayi sanyi. Nufar cikin gida yayi.
Jiki a sanyayye ya zauna yana kallon Ammyn kafin ya ce mata.
"Kina lissafin cikin Anum?"
"Eh toh ban san watannin cikin ba, amma ina kyautatta zaton ta kusan haihuwa."
"Ta haihu! Domin Lamido ya gaya min ta haihu, idan har abinda nake ji gaskiya toh Anum ta sauka lafiya,kuma ta samu Yara biyu itama..
#Mai_Dambu
KALLABI...!
A TSAKANIN RAWUNA
EWF
BABI NA SABA'IN DA BAKWAI
ALHAMDULILLAHI....
Shiru Innayoh tayi itama da take sauraron su, kafin ta ce mishi.
"Husaini kayi mafarki da Lamido shi ya gaya maka?"
"Eh wallahi har yanzu ina jin kamar ina mafarkin ne domin yanayin da nake ji a mafarkin har yanzu ina jin haka"
"Allah ya gafarta mishi yasa mutuwa hutu ne a gare shi, toh yanzun bari muga yadda abin zai kasance zasu turo dan sako ai"
Haka suka yi ta tattaunawa akan haihuwar Anum har Haima ta shigo da kayan ciye-ciye dake tasan Gidado yana son ya'yan itacce, ta ajiye mishi.
Murmushi yayi tare da cewa.
"Nagode"
Sannan ya fara kokarin.
Koda Baffa'm y shigo suka gaya mishi, murmushi yayi irin na Manyan ya ce musu.
"Idan maza ne sare kan su zan yi da ba zasu kwace minani na ba, idan kuma mata ne ina da sauran dakuna a gidan nan dai na ajiye su ayi ta shagali da sabin amare"
"Baffa'm!!" Yadda ta kira sunan shi a shagwab'e yasa dukkan su, kowa ya watsa a zauren.
Matsowa yayi inda take yana kare mata kallo.
"Meye a ciki amarya uwargidan Baffa'm"
"Baffa'm!!" Ta kuma kiran sunan shi tana shafa Fuskar shi.
"Ni ka daina tsokana ta"
"Toh Allah ya baki hakuri" ya fada tare da kallon ta yana me nufar dakin shi, har yau ruwa tana maganin daud'a domin Basu bar farantawa ranau ba, sai dai kuma a duk lokacin da take tare da shi idan ta tuna Lamido baya kuma gane kan ta, tayi ta kuka kenan tagaya mishi hakurin Lamido da sadaukarwar shi, shi yasa yanzu yake mugun lallabata.
**
Somalia
Rayuwar Anum ba za a ce bata cikin gata da soyayya ba, amma kuma Saraki shine sunan da take kwana take wuni tana kira, duk da duk bayan wata biyu Baffa'm yana aiko mata da duk abinda yake ganin zata bukata,. Sannan suma kakanin ta attajirai ne hakan yasa suka dauke mata kome bata bukatar wani abu domin gata da soyayya tana samu a wurin su.
A hankali kwanakin suke karewa, wasu shafuka na rayuwa tana buɗe mata, tun bata cikin hankalin ta, har ta fara dawowa hayacinta, sakamakon dawainiyar ciki girman shi tashi da kyar zama da kyar ya saka ta fahimtar rayuwa a matsayin ka na Uwa ba karamin abu bane, dake iyayen basu barta a haka ba, suna nima mata magani sosai abin gwanin ban tausayi har ta samu lafiya, ta fara gane sauyin ƙaddara da ta samu, ta kuma shiga auna ciwon da Ammyn take ji akan kashe mata D'a da aka yi, yanzu ta fahimci yadda kowacce mace take ji idan ta rasa mijin ta ba ma kamar uwar da ta haife shi, tayi kuka tayi kuka babu iyaka.
Tsanar Gidado kuwa yana ranta daram, bata jin zata iya mantawa da shi domin shi ya kashe mata mijin ta, shi ya yanke mata jin dadin rayuwa da mijin ta.
Dan haka ta kullace shi a ranta sosai ba na wasa ba.
Yadda take jin idan ta gan shi kamar ta kashe shi, shi yasa ta ajiye a ranta koda bata kashe shi da hannun ta ba, abin cikin ta zai kashe shi.
A haka rayuwar tayi ta tafiya, har ranar da ta kuma tsintar kanta a wata
Duniya domin fitar da nauyin da yake kafadar ta, an sha godon nakuda, kamar ba zata kai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 39