kallonta.
A hankali lokaci ya cigaba da tafiya, ya kasance duk sati Fulani Aminatu tana kai ziyara shashin sa, idan ta shiga tun ranar Laraba baza a kuma jin duri'ar ta ba, sai ranar asabar da yamma zata dawo shashinta, a lokacin idan ka gan yadda ta koma zaka yi tsammanin wani abu ake bata, sai kara kiriniya take, amma sabida sabo da tayi da zama a wurin shi dakyar Innayoh take lallabata, idan kuma taso sai ta tadda musu rigimar banza zata wurin shi.
A cikin wannan yanayin aka samu shekara daya da auren su, cika shekara daya yayi daidai da fara wani irin rashin lafiyar da ta fara, inda ta fara da wani irin abu a gefen wuyar ta, ya fito kamar bakin tabo.... Ba a lura da wuri ba sai da ciwon ya kwantar da ita, ana cikin haka wata Jumma'a aka wayi gari da mutuwar dabbobi cikin masarautar. ba a taba samun irin wannan annoban ba. Galadima ne ya nufi wurin shan iskar Mai Martaba.
"Allah ya baka nasara, ina ganin a fitar da Fulani Aminatu zuwa Sokoto ko za'a dace"
"Toh amma ina ganin kamar haka bai da alaka da mutuwar dabbobi nan?"
"Bana fatar haka"
"Allah ya baka nasara kazo" inji Sarkin gida.
"Lafiya?" Galadima ya tambaye shi,
"Fulani Aminatu ce"
Bai rufe baki ba, Mai Martaba har ya isa matakalar wurin shan iskar, kafin su zo tuni ya isa shashin ta. Tana kwance wuyar ta yayi jajjur, tabon bakin ya washe yayi ja.
"Baffa'm! Zan sha ruwa" ta fada a sanyayye, karban ruwan yayi ya bata tasha.
"Baffa'm akwai ciwo, cikina yana ciwo wuyana kamar wuta" ta fada hawaye na zuba a idanunta, d'ago yayi ya rungume ta, yana jin yadda jikinta yake firfitar da wani irin zafi. Janye kayan jikinta yayi bayan yayiwa Innayoh alamar ta fita, ya kwantar da ita ta shiga mata fifita. Dawowa wurin tafin kafarta yayi ya saka mata hannun shi yaji sanyi.
Tashi yayi ya lullube ta sannan ya bar shashin ta.
Fita yayi wurin Galadima, sun jima kafin zuwa dare suka fita daji, suka nimo saiwowi na bishiyoyi babu iyaka, aka kai cikin gida aka dake shi akan idanun Sarkin gida, aka dawo da shi nan aka hada mata magani kafin gari ya waye an yi mata wanka da shi. Sannan an bata wani tasha. Zuwa la'asar jini ya fara zuba bata, domin tana barci taji kamar tayi fitsari.
"Innayoh" ta kira ta.
"Na'am ranki shi dade,"
"Innayoh nayi fitsari"
Dubawa Innayoh tayi, taga kamar jinin haila ce, rangad'a gud'a tayi tana me fadin.
"Fulanina ta girma" kafin kace me labari ya karade cikin gidan, ana bada labarin girman Fulani, gyara ta Innayoh tayi sannan aka kwashe kayan aka kai wurin wanki. Innayoh da kanta ta wanke kayan.
Innayoh na fita ta kwanta, ko jimawa bata yi ba.
**
"Ban gane ba! Tsawon wani lokaci ka dauka da sanin haka?" Mai Martaba ya tambaye shi a fusace....
_________________________________
*Ina ga zan mai da posting din sau biyu a sati ko kuma kawai dan voting din ku gaskiya sai a hankali ku kara comments da Voting mana 🥰 ko kuma mu hadu bayan sallah Insha Allah*
#Mai_Dambu
[3/28, 11:49 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: KALLABI...!
A tsakanin Rawuna.
Na
Mai_Dambu
EWF
https://www.wattpad.com/1206974103?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
**
"Kayi hakuri amma ba yadda kake zata bane, kuma ba mayya bace" shiru yayi dunkule hannun shi yayi ya daki bango.
"Kenan duk kokarina sai da kome ya faru?"
"Ina ga da zamu iya dakatar da wasu abubuwan ba mamaki kome zai iya tafiya daidai" inji Galadima.
"Yanzu meye makasudin bayyanar abin wuyarta?"
"Baiwa ce da ita, da a ce zaka iya kusantar ta ne, haka zai ragu ko idan ta samu ciki zata samu lafiya, domin kaifin abu." Wani Zubawa galadima idanu yayi kafin ya dauke daga kallon shi ya cigaba da abinda yake.
Tun lokacin ya saka idanu akan sannan shima da kan shi yake nima mata magani, duk da bata dauki kwanaki me tsawo tana hutun ta ba, amma kuma tayi kewar baffa'm. Har Innayoh ta mata magana.
"Ki rage yawan daukin da kike kar ya fahimci haka"
Shiru tayi sannan ta ce mata.
"Toh" a lokacin Innayoh ta shiga koya mata abubuwa da akanta, tana nuna mata yadda zata rike miji.
Ana cikin wannan yanayin watan azumi ya maka, har zuwa lokacin babu abinda ya nima daga Fulani Aminatu, a cikin gida kuwa kiri kiri Ajuji take jin daci akan Aminatu. Tun tana boyewa har ta fitar da kiyayyar ta.
Innayoh da wasu bayi da ita Fulani Aminatu, duk shirya abubuwan kyaututtuka suka shiga cikin gida da shi, dakin Gambo suka fara zuwa. Jakadiya na gaya mata ga Fulani Aminatu, ta mike da sauri ta faɗin.
"Lalle maraba da fara me farar Aniya" ajiye mata tiren bayi suka yi, sannan Fulani Aminatu ta zauna tana murmushi.
"Ayi hakuri ban samu zuwa da wuri ba, ga wannan na tarban azumi ne" ta fada tana Murmushi akan fuskar ta.
Murmushi Gambo tayi sannan ta ce mata.
"Idan akwai wata toh ba makawa taurarin da suke zagaye da shi masu haske ne." Ta fada tana kallon Innayoh.
Bude baki Innayoh tayi zata yi magana suka ji muryan Fulani Aminatu.
"Hmm! Daidaiton hasken shi karfin kusancin shi, mun barki lafiya"
"Haka ne, sai dai kar kusancin hasken ya rage karfin wani shaashi. Koda yake kwanaki naji labarin Fulani Aminatu ta girma har yanzu bata yi daidai da tsarin mulkin Sarki Bello bane? Idan yau ban cire ba a gobe akwai masu cirewa!" Kallon Innayoh Fulani Aminatu tayi tana kuma kallon Gambo.
"Laa karki damu, da alamu baki tab'a haduwa da shi bane? Tambaya da kyau. Waye Sarki? Baffa'm da kike gani shine Sarkin" kallon Innayoh ta kuma sannan ta kalli Gambo, da take dariya.
"Ta Yaro kyau take bata karko, da alamu abinda nake ji ma da gaske haka ne, Fulani Aminatu bata san me ya kawo ta masarautar Gobir ba, auren sarki kike Innayoh wannan ba kauna bace boye abinda yake daidai,Kanwata Nagode ayi azumi lafiya sai dai ki sani baki dayan mu, mun auri sarakuna ne a shekaru irin naki, idan kika sake lokaci ya karu baki same shi ba, kwarkwarah itace zata hanaki rawan gaban hatsin kamar yadda Kwarkwarah Ajuji ta min."
Idanun Fulani Aminatu ya cika da kwalla, amma sai ta mai da kwallar ta kwantar da hankalinta sannan ta kalli Gambo tace mata.
"Fulani Gambo, Nagode da tunatarwan ki. Ai na jima da sanin me nake a cikin masarautan, ni Mace ce kuma soyayyar sarki nake nima, ba baiwa bace ni, sannan ba karfin mulki nake nima ba, balle nayi tunanin bin shimfidar shi. Na barki lafiya"
Sannan suka fita tayi matukar kokarin boye tashin hankalin ta, har suka shiga shashin Ajuji.
"Ina ruwan maraba da gasashe, kura yaga bakin jaki, karku dauka da ku nake nufi."
Cikin wani irin dakewa fuskar ta a had'e Fulani Aminatu ta ce.
"Innayoh ku ajiye kayan. Gashi nan na tarban azumi ne" tana me juyawa,
"Fulani Aminatu! Ana niman mazaunai ne ko ana niman kafa hujja ne?"
Juyawa tayi tana kallon Ajuji, sannan ta sake murmushi ta ce.
"Wasu lokutan ban cika gane banbancin me hankali da mara hankali ba, sunan su daya nake musu lakabi. Idan har akwai tafiyar Ƙaddara toh ba makawa sai ba fuskanci ire-iren ku masu tarawa da ragewa. Na barki lafiya"
"Ke Fulani Aminatu" bata juya ba har ta isa bakin kofa.
"Ajuji bana amsa kiran tababbu" sannan suka fita, sai da suka fara kokarin barin cikin gidan, kawai wasu daga cikin bayin cikin gidan. Suka fara dariya. Dama idanun ta ya gama rufewa da jin haushin kowa tsayawa tayi sannan ta kalli kande a cikin.
"Ki kira min Sarkin gida kuma ya tawo min da wadannan dabbobin" sannan ta wuce ta bar wurin. Aikuwa basu yarda hakan zai faru ba, dan haka suka kuma sake dariyar su. Tun da ta shiga shashinta, ta zauna idan akwai abinda ya tab'a mata ciwo bai kai yadda Baffa'm ya boye mata waye shi. Daga bakin kofar Sarkin gida ya ce mata.
"Allah ya taimaki Fulani Aminatu, gasu can a waje" shiru tayi bata yi magana ba, kallon ta Innayoh tayi.
"Koyi sarrafa fushinki kamar yadda kika yi a cikin gidan, wannan dalilin yasa nake nuna miki wasu abubuwan."
"Ka cire musu hakoran dariya" zubewa Innayoh tayi tana me rarrafawa gaban Fulani Aminatu.
"Don Allah karki ce zaki yi haka baki yi kama da haka ba, ki musu afuwa"
"Sarkin gida nace ka cire musu hakoran su" ta fada da ƙarfi.
"Don Allah Fulani Aminatu hukuncin yayi tsauri" cikin fushi ta mike zata bar zauren ta yanki jiki ta faɗi.
"Sarkin gida maza ka kira Mai Martaba ka gaya mishi"
Yana barin wurin tana, gyara mata kwanciya ko daukar lokaci basu yi ba, sai gasu nan a tare, domin kai tsaye daga fada yake, kusan rabon shi da ita wata biyu kenan, sai dai ya aika mata da maganin ta, haka ya faru ne sakamakon kokarin kawo musu hari da ake. Yasa bai da lokacin kansa sai na amsar korafe-korafe, ga yan gudun hijira suna dawowa cikin masarautar da zama. Yana isa zauren ta ya dauke ta cak ya wuce shashin sa da ita, su kan su bayin bai bi ta kan su ba. Yana shiga da ita ya kwantar da ita. Sannan ta shiga shafa mata maganin yana kallon yadda take juyar da kanta.
Haka ya zauna tana ta fama da abu daya, har ya samu labarin zuwan galadima, cewa yayi ya shigo. Haka ba karamin al'amari bane da zai bari a shigo har cikin tukakar su, yana shiga ya mika mishi wani karamin kwarya, ya umarce shi da ya saka mata a tafin kafarta.
"Ka samu labarin abinda ya faru?" Galadima ya tambaye shi.
"A'a ya kamata ka girmama al'amarin ta, domin ta kai an fara mata dariya."
"Su waye haka? Su waye masu bakin dariya? A kama min su a cire musu hakoran su" ya fada a fusace.
"Idan aka ce haka za ayi kiyayyar ba zata kare ba, amma idan aka rangad'a gud'a tare da fitar da shaidar ita din macen da sarki ya ke so ce me kake tunanin zai faru?kimar ta da mutuncin ta sai ya fi haka karuwa. Sai ya kai duk inda ta shiga kowa yana ja da baya "
"Shekarun ta baki daya sha uku ne bata kai hudu ba, kawai bana jin haka ma mafita ne, kawai a bar abin a hukunta masu laifin." Ya fada yana shafa fuskar ta.
Haka ce ta faru domin kuwa an hukunta su sosai, bayan ta farka bata mishi magana ba, sai dai bin shi da ido idan yayi mata magana sai ta fashe da kuka, ita a tunanin ta ya ci amanar ta. Har tsawon kwanaki uku, anan ne hankalin shi ya tashi yana kallon yadda take mishi kuka.
"Aminatu gaya min meye aka miki?" Ya tambaye ta, yana rarrashin ta. Wani sabon kukan ta saka mishi tana kallon shi kamar taga sabon halitta. Ya rasa yadda zai yi da ita kawai sai ya janyo ya ta rungume ta, tare da lallubar bakinta ya tushe da nashi, kamar yadda ya sabar mata haka yayi ta bin ta, sai gata tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya.
"Gaya min meye aka miki?"
"Dama kai ne Sarki?" Ta tambaye shi. Goga hancin shi yayi a kafadar ta, yana kara jin wani irin nutsuwa akanta.
"Shine kike kuka? Eh ni sarki ne" janye jikin ta tayi daga na shi.
"Baffa'm" janyo fuskarta yayi a hankali kai hannun shi wuyarta, yana shafawa.
"Zamowana sarki ba wai na har na karshen rayuwa ta bane, akwai lokacin da zan rabu da shi. Kinji kwantar da hankalin ki ba zan jima ba zan rabu da shi"
Shigewa jikin shi tayi tana faɗin.
"Baffa'm karka rabu da ni, don Allah kar ka min abinda Baffana yayi min"
Murmushi yayi yana kara matse ta a kirjin shi,
A cikin wannan yanayin aka yi azumi bayan an sha ruwa, ya tafi har garuruwan da ake kawo hari, ya duba su sannan ya kai musu agaji. A kan hanyar shi ta dawowa ne haka kawo musu hari. Bai tab'a yaki ba sai a lokacin dan haka duk yadda yaso kare kan shi, haka ya shiga yakinin sannan aka kama maharan, kallon su yayi sannan ya ce musu.
"Waye ya turo ku?"
"Ba zamu fada ba koda zaka kashe ku ne." Lumshe idanu yayi sannan ya kalli Yarimar Gobir ya ce mishi.
"A matsayin ka na yarima ya zamu da su?"
"Me zamu yi kuwa wanda ya wuce a tafi da su masarautar ayi ta gana musu azaba sai sun fadi waye ya turo su."
"Toh a daure su" duk da ba wani jin ciwo yayi ba, sai a damtsen shi. Tun kafin su isa labari ya karade gari an farmaki Mai martaba a hanyar shi ra dawowa gida. Fulani Aminatu tana shiri taji wasu bayi suna faɗa. A bayan tagar dakin ta, da gudu ta fito ta haura katangar shashinsa, tana kallon hanyar waje. Tun da ta fito bata koma ba, tana tsaye a wurin har garin ya dauki wani masifaffen hadiri bakikirin. Daga nesa ta hango keken dokin shi dan haka bata yi wani yunkuri ba, sai da ya kusan shigowa ta sauka da gudu, ta nufi hanyar da zai sadasu, ruwa na zuba a kanta. Tsayawa tayi a bakin kofar da xai shigo tana jiran shi. Fitowa yayi hannun rigar shi a yanke ga inda ya daure. Da gudu ta nufe shi tare da fadawa a kirjin shi. Rungume ta yayi yana jin kamar kar ya rabu da ita. Shashekar kuka take tana kallon raunin. Har cikin turakar shi suka shiga ko nace ya dauke ta. Sai da ya cire kayan shi ya wuce ban daki, dan ta juya mishi baya. Yana gama abinda zai yi ya fito ya saka wasu kayan sannan aka gaya mishi ga me maganin masarautan yazo.
"Sarkin gida kace ya je raunin bata da muni, zan kula da shi" yana fita ya koma dakin ya same ta saka wani mayafin shi zata fita. Tsayawa yayi a gaban ta.
"Ina zaki" kallon farfadan kirjin shi tai sannan ta sunkuyar da kai tana faɗin.
"Zamu kawo abinci ne"
Tallafo hannun ta yayi ya saka a kirjin shi yayi.
"Kin ji yadda yake bugawa"
"Eh"
"Kece sanadi" ya fada bayan ya sumbaci goshinta, sannan ya gangaro wuyarta. Zuwa habb'atar lumshe idanun ta tayi tana jin shi. Kafaffuwar ta ne ya fara rawa, murmushi yayi ya zungure goshinta.
"Raguwa kawai" da sauri ta fita, basu dauki lokaci ba sai gasu da manyan tire na abinci da ruwan zafi, ita dasu kande da yahanasu. Haka suka jera sannan suka fita. Yar karamar wasika ya rubuta ya tura ga fadar shi zai yi Hutu na kwanaki sabida ciwon shi. Aikuwa ganin haka ta barwa Innayoh kome itama ta tare a shashinsa, basu da wani aiki sai na soyayyar da yake koya mata, idan suna daukin baka jin kome sai muryan shi yana bata labarin da ya rubuta. Itama kuma bude kunne take tana jin labarai.
A gefen Innayoh itama bata bar su a baya ba wurin basu abincin da zai kara musu lafiya cikin yan kwanakin dakyar yake dakatar da kan shi, amma tabbas yana gab da amsar hakkin auren shi..
**
Bayan shekara biyu......
Akwai kayan mata masu kyau serious buy a min magana ta wannan number: 0813269641
[3/28, 11:49 AM] UmmuHabibah🥰🌹❤️: KALLABI...!
A tsakanin Rawuna
Na
Mai_Dambu
EWF
https://www.wattpad.com/1207713931?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
**
Bayan shekara biyu.
Wanke mata kai Innayoh take, tayi shiru zaka dauka kawai tayi shiru ne dan wanke kan, a'a a zahiri ba haka bane maganar da taji a bakin Balaraba ne yake dawowa ranta. Bude idanun ta tayi akan Innayoh kafin ta dan matsa kadan kasancewa kanta aka yi baya da shi, tana kwance an saka mata matashi a keyarta. Duk da ta fahimci kamar akwai abinda Innayoh take boyewa amma bata da wani damar da zata kasa magana.
"Innayoh da gaske za a bawa mai martaba auren Yar Sarkin sokoto" ta tambaye ta.
"Eh gara yayi tunda ita wacce yake tare da ita bata san yadda zata girma ba" inji Innayoh, shiru Fulani tayi bata kuma magana ba, domin Innayoh tana ganin a halin yanzu ya ci ace ta samu kan mai Martaba ba wai ayi ya ta kananun magana babu abinda ya kasance a tsakanin su, tun va a gane ba har an gano cewa babu kusancin aure a zaman su.
Babban amawali innayoh ta dauka ta nad'e mata gashin kanta, tana goge mata. Sannan ya tashi kwana lalle tai da danyen kwai ta shafa mata a fuskarta da wuyar ta, sai lalle da lemun tsamin da ta shafa mata a hammatarta, tana kuma komawa gwiwar ta tana shafa mata dankon zuma, tana fisgewa da dan ƙarfi tana cire gashin dake jikin Fulani Aminatu.
"Toh me zan yi?" Ta tambaya tana tura bakin ta.
"Me kuwa zaki yi? Bayan tun bara nake kokarin ki fahimci haka, Fulani kefa ba Yarinya karama bace, ke matar aure ce kuma a yanzun shekaru uku kenan da auren ki, idan lissafina yayi daidai kina da shekaru goma sha biyar a rayuwar ki. Ki zama mace mana"
Shiru tayi tana kallon ta, bata ce kome ba tana nazarin maganar ne, shiga cikin ban dakin Innayoh tayi tana fatar wannan gyaran da take mata karya tashi a iska, kasancewar gobe Laraba kuma zata shiga turakar shi, tana fatar idan ta shiga da kafar dama. Shi yasa take ta gyara mata jiki, yadda shi kansa mai Martaba sai ya gigice da Yar ficikar shi.
*
Kasancewar fada tana da wani daki na musamman wanda yake kawace da litattafai da sauran su, zaune yake shi da galadima.
"Kana min kama da sabon ango da yake shirin fara sabon rayuwa." Inji galadima.
Murmushi yayi sannan ya cigaba da diban tawadar shi a jikin alkalamin shi yana me cigaba da aikin shi.
"Baka da aiki sai na maganar amarci" mai Martaba ya fada yana murmushi, kallon shi Galadima yayi dan ya fahimci mai Martaba yana son ayi mishi maganar kenan, gyara zama yayi ya duba wata kyakyawar kwarya da yake cike dam da fura da nono, man shanu ya kwanta a kai, ya mika hannu zai dauka, ya ce mishi.
"Ajiye min Fulani Aminatu ce ta dama min."
Kasa Galadima yayi da murya yana faɗin.
"Kana iya shanye damunta amma ba zaka iya bata naka damun ba" ya fada yana wata shu'umar Murmushi, girgiza kai Mai Martaba yayi yana kallon Galadima, a hankali ya cire rawanin shi da alkyabbar ya ajiye a gefe sannan ya sauka kasa sosai ya zauna bayan ya tankwashe kafar shi ya zubawa Galadima idanu.
"Sam ka manta sarki ne ni guda" ya fada yana muzurai cikin zolaya.
"A'a karaga ne ba sarki ba, malam ga wannan Kyakkyawar hadi, amma gobe zaka yi amfani da shi."
Ture hannun Galadima yayi yana daukar ƙwaryan fura da nono yana motsawa, sannan ya kalli galadima.
"Kana tsammanin sai nasha wani abu zan iya ratsa Fulani?"
"A'a shi yana kara kuzari ne" ya fada mishi yana murmushi.
"Ba sai nasha ba, ina da lafiyar da zan take bata hudu a dare daya ban gaji ba" ya fada yana kallon furan.
"Kai haba na zata irin mu ne da sai mun had'a da magani"
"Kai ma rashin godiyar Ubangiji ne irin naka amma bana tunanin sai ka haɗa da wani abu, maganin basir kawai xaka nima shima ya isa."
"Kace mutumin nan kallon ka muke ashe kai, ba haka kake ba toh wallahi yar mutane." Inji galadima yana dariya.
"Hmm" shima yayi dariya yana me cigaba da shan furan.
"Allah ya baka nasara, kayi kokarin ganin ka daidaita tsakanin ku bana son ka auri wata mace bayan Aminatu, sabida ita Aminatu renon kace, ba yau nake gaya maka ba Aminatu a hannun ka ta girma kai ka fara koya mata abubuwa dayawa, idan har zaka mata adalci toh tabbas bata bukatar zama da kowa sama da kai. Duk da nasan zai yi yiwa idan baka auri wata ba, ko a Kwarkwarah"
Ajiye furan yayi yana kallon Galadima.
"Ban san yadda zan maka bayani ba, amma ina tausayin Aminatu ne, shi yasa bana iya niman ta, amma insha Allah zan ga abinda ya dace" ya fada bayan ya mike, ya daura rawanin shi, sannan ya dauki alkyabar shi, yana me nufar hanyar waje.
"Yaushe zaka tafi daurin auren Yar Sarkin Rano?" Galadima ya tambaye shi.
"Kome yana hannun ka."
"Amma zaka tafi da Fulani Aminatu ne?" Juyawa yayi yana kallon galadima.
"Tafiyar zata bada ma'ana. Ka duba zancen da idanun basira" Galadima ta fada bayan ya fita daga dakin karatun.
"Kuma!"
Tsayawa Galadima yayi, sannan ya juya yana faɗin.
"Kwarai da gaske, kwarai ka nunawa duniya ita din matar so ce, ba zaka iya tafiya me nisa babu ita ba"
"Toh Babu damuwa ka shirya haka ma" ya fada yana murmushin jin dadi, sannan ya nufi shashin Fulani Aminatu, tana zaune bayan ta fito wanka wata yar yaloluwar riga ce ba shan iska a jikinta, dan kirjin ta me ɗauke da dukiyar Fulani ya cika daidai na matashiyar budurwa. Fatar ta sai wani mugu sheki yake, rigar tana da tsantsi da wasu irin tsagu. Ya kwanta a jikin ta luff, ga ruwan gashin kanta da yake sauka a dokin wuyarta. saka mata lalle Innayoh tayi a hannu da kafa, shine take zaune a wurin duk da ranta a jagule yake bai hanata kallon kofar ba shigowa ba dan tasan yau zai shigo rabon ta da saka shi a idanun tun ranar Lahadi da daddare da ya rakota. har yau bata saka shi a idanun ba, taje shashin sa aka ce baya nan. Tabar sako bai biyo sawu ba. Ana cikin haka kuma Balaraba take bata labarin ai sarkin Sokoto zai bashi auren Yar shi. Wani irin kunci taji.
"Assalamu alaikum!" Ya mata sallama, d'ago kai yayi yana kallon ta, yadda tayi wani shar da ita, gwanin ban sha'awa sai wani fitanannen kamshi dakin yake badawa, kallon hannunta yayi da yake dauke da lalle sai kafarta shima yana dauke da lallen. Cire rawanin shi yayi ya ajiye, sannan ya cire alkyabbar shi ya ajiye ya gama sabawa kan shi da matseta, da ya ganta a wurin wani irin hàdiye yawu yake. A hankali ya taka har inda take, ya zauna yana kallon ta. Kafin ya kai hannun shi baki daya ya dauke ta cak ya daura akan cinyar shi. Tun can baya tana tsoron haka da yake mata, zuwa yanzun tasaba da shi sai dai kunyar da take da ita baya barin ta, tayi kome sai yadda yayi da ita. Rungume ta yayi yana me cusa kan shi tsakanin wuyar ta da kafadarta. Yana goga mata hancin shi.
"Ayi min kowani hukunci amma shiru da shariyar zata iya saka baffa'm ya sussuce"
D'ago kai yayi yaga har zuwa lokacin bata kalle shi ba.
Dan baya yayi da ita a hankali yake shafa cinyoyin ta zuwa saman cikin ta, wani zaro idanu tayi, tana jin yadda bugun zuciyar ta yake kara sauri-da- sauri kamar ana wasan tseren dawakai.
Hancin shi ya kai bakinta ya sumbata sannan ya ce mata.
"Naga sakon ki a wurin Sarkin kofa" har lokacin bata amsa mishi ba.
"Fulani" ya kira sunan ta,
"Baffa'm! Aure zaka yi?"
"Waye ya gaya miki?" Ya tambaye ta yana kallon yadda take kokarin kauda kanta rike fuskar ta yayi yana faɗin.
"Waye ya gaya miki labari mara daɗi?"
"Taya za ayi abu a cikin gidan nan ta boya? Ka manta ina kake ne. A gafarce ni idan nayi shirme" ta fada tana kokarin tashi daga jikin shi.
"Nasani mantawa nayi, tayi aka min ba auren xan yi ba. Kuma ba gaya musu ina da yar kwailata wace kirjinnta bai gama budewa ba" sumkuyar dai kai tayi tana kallon lallen hannunta da yake kokarin burbushewa a jikin shi.
"Ina b'ata maka jiki da lalle" ta fada tana lumshe idanun ta.
"Toh ai nasan domina aka yi ko?" Goga hancin shi yayi a kumatun ta, yana shaƙar kamshin jikinta.
" Ki cewa Innayoh, na kara mata matsayi zuwa uwar bayin cikin gidan nan baki daya" a matukar mamaki ta kalle shi kafin kuma ta sake murmushi tana kara rungume shi.
"Nagode sosai" ta fada, ai kuwa mutumin ku ganin yadda take farin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 39