Share this page
babu wani wanda ya isa d'aga musu murya ko musa musu idan suka ce suna son abu, a haka a cikin masarautan zaluncin da ake ya fi kome dagawa bayin Allah hankali, gashi dai babu Sarki Bello babu Aminatu sai da suka yi danasanin hada kai domin cutar da Bello, ana cikin wannan yanayin aka nemi Baffa'm aka rasa, babu Sarkin Gida babu labarin shi, Da wannan aka shafe tarihin shi dama Aminatu ta gaya mishi soyayyar su, tarihin su watan wata rana zasu zama tarihi toh kuwa sun zama, domin babu ma wanda yake iya tunawa da shi. Shi kan shi Waziri Zakaria sai da yayi da gaske domin an so a mishi tawaye, Allah ya taimaka shima ba sakarai bane.. A bangaren Bingel, itama tana tsoma musu baki a sha'anin shugabanci masarautan, duk da sun fahimci so take mulkin ya dawo wurin danta, amma basu yi yunkurin mata kome ba, domin ko sun so haka, dole suke hakura dan a shirye suke ita da danta dan shekara biyu, dan haka ita ce macen da ta rage na Baffa'm, waziri Zakaria bai yi kasa a gwiwa ba, idan aka fara magana yana tuna musu ita ce take da ikon akan mulkin masarautan dan haka su gama abinda xa su yi dan ta shi zai maye gurbin Sarki nan gaba, tunda shima Yakubu ai rikon kwarya ne, da wannan dayawan mutanen fadar suka bazama niman Sa'a. A cikin wadanda suke faffutukar mulkin ya dawo hannun su, har da Chiroma dan haka zama yayi a gaban wata yar bori.. bayan ta gama haukata da faduwa a kasa ta kalle shi sannan ta ce mishi. "Dukkan ku ba zaku iya ba, kuma ba zaku tab'a cimma matsaya ba, Aminatu da Bello sune kawai zasu iya, toh kun Kore su. Mulki kuwa tana tafe ne d zuciyar mutum Yakubu mutum ne a badili a zahirin shi kuwa fitanannen kuke gani ba, Gara shi dan haka ko ka hau mutuwa ce zaka samu madadin mulki magadan masarautan suna nan tafe. Lokacin kukan ku ya fara kayi fatan mutuwar ka kafin isowar Zakin fama, an haife su ne domin tabbatar da adalci, a dare mafi girma da albarka, dan haka kamar yadda kuka saka iyayen su kuka haka zasu saka ku kuka, ganin su kawai sai ya haifar muku da hargitsewar hantar cikin ku. Sautin takun su, kawai abin a gudu ne, iya su kawai gayya ne a filin yaki dan haka kuyi ta kanku." "Ban gane me kike nufi ba?" Ya tambaye ta, kallon shi tayi tare da kallon tukunyar sidabbarun ta, sannan ta girgiza kai kome ya shafe bayanan da ta samu sun B'aci, kafin ta tattaro wasu bayanan sai shake mata wuya aka yi. Ta shiga kakari da kyar Allah ya kwace ta, cikin masifa ta ce mishi. "Fita min a bukka, ka tafi ka nimo. Aminatu ita ce zata iya taya ka samun mulkin ba kowa ba" zaro idanu yayi taya haka zai faru, bayan shi ya kitsa yadda kome zai tafi domin cimma manufar su ta son mulki duk da shima yana da na gaba da shi. Baya shi ya kitsa kome ba, shima haka aka turo mishi ya aiwatar, toh ya gaji da yiwa wani bauta ne, yake son ya ci gashi kansa. Haka ba zai samu ba sai ya zama sarkin gobir.. * Borno Bayan shekara daya. Innayoh ce ta tallafo, Gidado da jikin shi yayi laushi. Lamido yana kwance shima amma jikin shi bai kai na gidado laushi ba. Wanka tayi mishi da ruwan magani, sai kuka yake. Sannan ta mika shi ga Mahaifiyar shi. "Innayoh bakin shi ya feso da wasu kuraje fa" "Eh haka bakon dauro yake, gashi kin ga Lamido kamar bayi ciwon ba, ta Gidado ce tayi yawa." Saka mishi mama tayi a baki ya dawo da maman yana kuka, Jakadiya Baabaghana ce ta shigo ta zauna tana faɗin. "Fulani bani shi na wanke mishi bakin nan da yake darewa, haka kawai yaro ya koma wani iri." "Toh ni kan ba zan iya ganin yadda zaku dauki alhakin Uban ɗakina ba" inji Innayoh ta dauki Lamido suka fita, haka Baabaghana ta wanke bakin Yaron nan tass, har yana jini. Dake a shekaran an samu yawaitar cutar bakon dauro, shine fa Yaran suka kamu da shi, Lamido Hassan ya fara yi amma bai wani jima ba, sai ga shi Gidado Husaini ya kama, shima. Haka aka yi ta jinyar su, har tsawon wata guda, kafin suka warke sai dai baya magana, baya hum baya uhum. Aikuwa Aminatu tayi kuka a lokacin. Mai Martaba da kan shi ya tura su, har Chadi, aka duba shi anan aka fahimci zai yi magana kawai cutar da yayi ne, ya taba wuyar shi dama bakon dauro yana wannan illar wa yara. Haka suka dawo. Idan Aminatu ta kalle shi kuka take baki daya sai Tausayin shi da kaunar shi ya danne soyayyar Lamido Hassan. Shima ganin yadda Mahaifiyar su, bata ta shi yasa ya koma jikin Innayoh abin shi, karshe shi kan bai wani sha mama har aka iyaye su ba, shekara daya da wata biyu ya daina amsar mama, dan wani lokaci idan yazo shan Maman, yana kamawa Gidado zai taso, ya kama shima, shi kuma Allah ya daura mishi son aba shi abu shi daya, duk abinda suke Innayoh tana lura da su, shi Gidado son dan uwan ne yake saka shi Yana ganin zai yi sha sai shima ya taso ya ce zai sha wani lokaci ba shan yake ba, kallon dan uwan yake yana mishi wasa, amma dan baten da buje, sai ya bata rai kamar ba shi ba, da wannan yanayin ya barwa Gidado nonon baki daya, har Aminatun tana kai karan shi wurin Innayoh aikuwa ranar ta sha mita a wurin Innayoh ta ce mata. "Tunda Yarima Gidado ya samu matsala kika manta da biyu kika haifa ba daya ba, soyayyar ki ta uwa da kulawa kin daura akan Gidado, shi kuma ko oho, ba dole ya hakura ba, lokacin da xai sha shi kuma dan nime me kama da Bororoji ya taso yace zai sha, ya bar muku kayan ku ya kama hatsi sai kuyi ta dama da shi" "Ayya ayya Innayoh" "Ba wani Ayya ayya" da haka suka bar zancen. A hankali Yaran suna tasowa so da kaunar junar su, yana kara bayyana domin tun daga ranar ta hade kan Yaranta, a hankali suke kara girma kamar su da mahaifin su yana kara bayyana, har ma sun so zarce shi kyau sabida hasken fata da kuma siririn hancin irin na Mahaifiyar su. Duk da haka sai da Lamido yayi dan duhu kaɗan. Ba kamar Gidado da yake da hasken fata sosai ba. Rashin maganar Gidado shi ya haifar da rashin maganar Lamido, dukkan su suka taso ba su magana, sai tsabar rashin jin. Musamman Lamido, duk inda ya zauna sai ya takalo fada. Yayin da shi kuma Gidado idan ya zauna zaka samu ko yana cikin matsanancin farin ciki, ko kuma ya ga abu yana burge shi. Suna da shekara bakwai a duniya, wani abin mamaki ya faru bayan sun dawo daga karatu a wurin mai Martaba, sun zo zasu wuce aka samu labarin wani mahaukacin doki ya tsinke a cikin barga, kowa gudu yaƙe dan har an je kiran Madawaki, wato sarkin dawakai, ga Sarkin gida da Sarkin yaki, da wasu dakaru a tsaye aba tattauna yadda zasu kama shi, kutsa kai yayi cikin su ya tsaya yana sauraron yadda xa a tare dokin, aikuwa ya wuce ta cikin mutane har wurin bargan, ya tsaya kamar wanda aka tura shi, hawa yan itaccen da aka yi bargan da su yayi, sai lokacin Jama'a suka hango shi, kafin su dakatar da shi Lamido ya daka tsalle akan dokin nan, tare da fisgar linzamin dokin, suka ficce daga cikin masarautan, sai yakuwa Mutane suke. Sai da ya nufi can bayan katangar masarautan, kafin ya ja linzamin dokin suka fadi baki dayan, lokacin labari Ya same su ita da Innayoh. Shi kan Gidado bai san yadda zai bata labari ba, tunda ya samu damar fisgar sunan Lamido da doki bai kuma cewa kome ba, sai kwatance yake mata da hannu, dake sun saba da bayanin shi sosai musamman Innayoh da Lamido. Idan ranta yayi dubu sai da ya B'aci, koda aka tafi wurin su, tashi yayi yana karkade jikin shi, sannan ya ratsa tsakanin mutane ya wuce kamar ba shi ba, idan ka ga yadda yake turnike fuska sai ka rantse da Allah ba shi yayi wannan takadarirrancin ba, a hanya suka hadu da Sarkin yaki ya ce mishi. "Yarimar Gobir zaka iya bani damar baka horon yaki?" Kallon gefe da gefe yayi, sannan ya sadda kan shi kasa. Shima kuma Sarkin yaki cikin girmamawa ya zube a gaban shi yana faɗin. "Ina farin cikin bawa Jinin Gobirawa horon yaki, ka Amshi haka a matsayin kyautar abin da ka min" kallon shi yayi sai kuma ya samu kan shi da gyada kai. Dan haka Sarkin yaki yana baya, Lamido ka gaba suka isa bangaren su, sannan ya juya, shi kuma ya shiga cikin gidan, kamar bai yi kome ba. Kallon fuskar Innayoh yayi ya fahimci ran Ammyn shi a bace yake, da gudu Gidado ya so wurin shi. Cikin maganar shi ta kurame ya ce mishi. "Lamido ya aka yi ina dokin?" Saka hannun shi yayi a kan daya sannan ya juya hannun ya ɗan yarfe, wato yana nufin. "Ai ya mutu na fitar da shi daga cikin bargan" Cikin zakuwa Gidado ya kuma watsa hannayen shi dukkan biyu yana cewa. "Kai da gaske ya mutu?" Wani hade fuska yayi ciki ciki, kamar ba shi ba, take Gidado ya sake murmushi yana girgiza kai tare da saka hannun shi a kunne yana motsa bakin shi. "Tuba nake Yayana, tuba nake Hassan dina, Tuba nake Lamidona" sai a lokacin ya ɗan sake murmushin gefen baki iya, ai kuwa Gidado ya fashe da dariya, yana murna tare da dannewa bayan Lamido aukuwa ya dauke shi, har zasu shiga sai ya sauka. "Karka shiga ran Ammyn ya b'aci" ya fada mishi da hannu, sunkuyar da kai yayi kafin ya cire takalmin shi, ya shiga cikin dakin, tana nan inda ya saba ganin ta rike da wani farin gashi bai san na meye bane amma yana da yakinin abu yana da daraja a wurin ta, a wayo da yayi duk lokacin da ya ganta ta kebe shi yake jan hannun Gidado su fita bayan son Gidado yaga kukan ta. Shiga yayi ya zauna a gaban ta, har lokacin kuka take sosai. Bai ce kome ba dan dama bai cika sakewa da ita yayi magana ba, abokiyar maganar shi ce kawai take iya isar da sakon shi wurin ta, wato Innayoh idan kuma ta shiga irin wannan yanayin shi yake koran su ya ce a barta tayi kuka, Allah yayi mishi kaifin basirar da yasa yake gane yawan kukanta ba wai yana ta'alaka bane akan su, akwai ciwon da yake damun ta, shi yasa idan zata yi kukan shi daya yake zama a kusa da ita, idan ya ga taki shiru sai ya fita ya nufi bayan tagarta ya zauna, tare da ɗaukar wani sarewan da Mai Martaba Sarki Muhammad Omar, ya kawo musu daga Saudiya yayi ta busawa. Har sai ta tura a kira shi. Yau ma haka ce yake shirin faruwa. Dan haka ya mike zai fita sai lokacin ta ce mishi. "Lamido!" Cak ya tsaya, "Karka sake shiga cikin gidan sarautar nan da sunan wani taimako idan ba so kake na mutu ba" kamar wanda ta zuba mishi ruwan sanyi haka ya juya yana kallon ta. Lumshe idanun ta hawaye suka zubo mata, tare da gyada mishi kai. Lashe bakin shi yayi sannan ya gyada mata alamar yaji. #Mai_Dambu [5/25, 7:52 AM] Mai_Dambu: BABI NA TALATIN DA HUDU Sannan ya saka kai ya bar dakin, ta kuma fashewa da kuka. Shigowar Innayoh bai hanata kukan ta ba, sai da ta zauna a gefen ta tana faɗin. "Karki illata idanun ki da kuka mana" "Innayoh Lamido tsoro yake bani, kowani lokaci sauyawa yake, tsoron kar ya tambaye ni waye shi nake ji shi yasa bana son yana shigewa cikin gidan sarautar nan" "Taya jini ba zai bayyana kan shi ba? Taya kike tunanin zai zauna shiru haka, matukar jinin Gobir ne, kiyi hakuri amma fa dole sai sun bayyana kan su." Ta gaya mata haka bayan ta bar mata dakin tana jin ta, haka kawai dan tana da taguwar zuciya sai ta hana yaro sakat. Dan haka Innayoh ta dauki aniyar lallai sai Yaran sun dan asalin su sai tayi kuma, Dan haka ta zuba ido ta ga yadda zaa boye asalin su, kwatsam ana cikin kokarin ganin ya daina shiga masarautan borno, sai ga shi ya fada fita da yan farauta, abin ya samo asali ne lokacin da suka fita sallah Jumma'a, ya ga shugaban yan farauta ya kai gaisuwa wurin sarki a lokacin, yaji suna bisa kukumo, da kirari kawai sai ganin shi aka yi a tsakiyar su tsugul, ayin juyin Duniyar nan ya dawo Yaron nan yaki fir karshe ma farautar aka fita da shi, Allah da ikon shi bai dawo gida ba, sai da yar barewar shi a kadadar shi, ranar bakin ciki kamar ya kashe Aminatu, kura Mishi ido tayi gashi bata iya duka ba, sam ta rasa ya zata yi da shi. "Gaya min me kake son kayi? Ka gaya min zan Barka kayi" "Ki bar ni a bani horon yaki toh" ya fada kan shi a sunkuye. "Shi kenan Lamido na amince, amma ban da farauta" kallon ta yayi tare da cewa. "Kiyi hakuri ko banje ba, zasu dauke ni" a matukar firgice ta ce. "Su waye?" Tashi yayi ya bar ta cikin tashin hankali, kawai tayi imani ne da Allah amma zuciyar ta, ta kusan bugawa baki daya Lamido sai jangwalo damuwa yake a kan shi.. A gefen Gidado kuwa, bai da aiki sai na idan ya zauna yayi ta rubutun da babu kai babu gindi, idan yaga abu yayi mishi zai dauki alakami da yar battar tawadar shi yana rubutu, Yana son mulki amma yasan ba zai tab'a zama sarki ba, shi yasa duk ranar juma'a idan ya tafi masallaci, bai da aiki sai na rubuta shigar da Sarkin Borno yayi kayan da dokin sa ya saka daban abubuwa dai gasu nan, Allah ya daura mishi shiririta, gason saka kowa farin ciki, baya magana amma duk abinda masu magana suke zaka samu yana yi. Bayan shekara goma, cikin wani irin zafin nama ya kaiwa sarkin Yaki sara, ya tare, ya kuma kai mishi wani saran ya tare. "A yayin da zaka fuskanci gaskiya dole kwakwalwar ka,.tafi zuciyar ka sauri dan haka idan jinin Gobirawa ne ke yawo a jinin ka gwada min kai sadauki ne" Wani irin sara ya kai mishi sai da takobin Sarkin yaki ya rab'e gida biyu, sannan ya saka mishi takobin a wuyar shi. "Tabbas zaka jagoranci rundunar da zata kasar Chadi domin taimakawa kana domin yakar Sahil" a hankali ya sake takobin yana me sunkuyar da kan shi. Ji yayi an danne bayan shi, fisgo shi yayi, kamar zai buga shi da kasa. Yana kallon idanun shi. Da yake hango iyakar bashi hakuri da kuma farin cikin. Zama suka yi Sarkin yaki ta kawo musu ruwa, zama shima yayi sannan ya ce musu. "Mahaifin ku sarki ne, a masarautan Gobir,.mikewa Lamidi yayi ko ba a gaya mishi ba yasan shi din dan sarki ne a bakin Innayoh, amma ganin kukan da Ammyn take yasa shi jin tsanar masarautar su, kuma yasha jin haka a wurin mai martaba sarkin Borno idan yayi baki yana gabatar da shi, Rike hannun shi Gidado yayi a kan ya zauna su ji labarin baban su, wani irin duba yayi mishi dan dole ya kyale shi. Sannan shi ya zauna yana kallon sarkin yaki, da yayi ta bashi labarin su, dauko littafi yayi ya fara rubuta labarin iyayen su, A yanzun yaran aminatu suna neman shekaru goma sha takwas ne, domin suna cikin na sha bakwai ne, dan sun fara mallakar hankalin su, ba kamar Lamido wanda tsabar aikin yaki da horo, fita farauta da sauran su, ya saka shi ya bude har ya fi Gidado budewa. Shi kan Gidado cewa yake ba zai iya aikin wahala ba, dan Lamido ya saba da wahala sai yayi ta yi. Bayan ya gama rubutawa, ya mike yana dariya sannan ya bar wurin yana godiya. Allah cikin ikon shi ya raba musu halayyar su, yayin da shi Lamido ya gado jinin gidan su, sai gashi Gidado ya dauki halin baffa'm baya son rigima babu ruwan shi da hayaniya asalima dai idan har tafiya ta tafi ba mamaki baffa'm ne domin yana son abinda zai saka shi farin ciki, ko sau daya bai taba rike takobi ba, kai Gidado tsabar bai kaunar rike takobi ko kaza wannan bai saka kan shi ya yanka ba, domin kiri kiri ya ce musu da hannu shi ya auri alkalami,.kamar yadda Lamido ya auri takobi, haka Allah ya rabawa kowa abinda yake ganin shi ne ra'ayin shi. * Masarautar Sokkoto. Inna Marwa wacce shekaru suka haura mata ce zaune tana kallon Baffa'm da yake ta rubutu yana ajiyewa. "Bello jiya Galadima ya zo kana barci" "Inna" ya fada yana sake alkalamin hannun shi. "Eh yana nan shi da Sarkin Gida zasu zo an jima" a hankali yayi kamar zai tashi sai ya koma ya zauna sai ga hawaye sharrr. Da wani ido zai kalli galadima? Me zai cewa galadima? Me zai ce musu, ya ce musu shima dan yana da sauran shan ruwa ne yake raye ko me? Bai san halin da Waziri Zakaria yake ciki ba, tunda shi yaro ne, ya so kwarai da ya gaya mishi ya bar masarautar domin zasu iya kashe shi. "Kuka kuma? A'a ai ba naka bane, shi yasa muke addu'ar Allah ya haɗa mu da mutanen arziki. Gashi Allah ya haɗa ka da Nafi'u kuma yana tare da kai ba dare ba rana, duk abinda ya faru baka da laifi, haka Allah ya ƙaddara sai haka ya faru kafin ka iya gane dama can kai ma da laifin ka, ni da kaina na gaya maka soyayyar ka da Aminatu itace hanyar da za'a iya farraka ku amma ka yi kunnen uwar shegu, Allah na tuba gidan sarautar da tun daga haihuwar ka ake binka da Idanun balle kuma an san ta yadda za'a yake ka, fir kaki ji toh gashi nan dai kana ki kana gani sun shiga kyakkyawan alakar dake tsakanin ku" tana gama fadar haka ta mike tana me barin dakin, shafa gefen wurin kwanciyar shi yayi yana me dauko wani jakar fata, a hankali ya juye yayan jigidar ta, yana kallon hawaye na zuba mata. Ranar da ta fara shiga turakar shi ya tuna, da lokacin da ya kwashe jigidar ya ajiye yana kallon su da idanun basira, kafin ya cigaba da goge fuskar shi, "Ina sonki Aminatu sai dai lokaci ya kure da zan kuma samun damar da na samu, duk inda kike Allah ya jibanci al'amarin ki" ya fada yana sake wani irin kuka me ban tausayi, shine gaskiyar abinda yake ji, shine gaskiyar abinda zai iya faɗa yana ji a kanta. * A can wajen masarautar kuwa, Galadima ne da Sarkin Gida, bayan sun gama gaisawa da Yaran Inna Marwa, suka nufi dakin da yake. Da sauri ya shiga tattara kayan shi, da ya ciwo. "Assalamu alaikum!" Suka shiga mishi. "Wa'alaikumunsalam!" Ya fada a raunane, suna shiga ya ga galadima wani sunkuyar da kai yayi, sam yaki d'ago kai ya kalli waziri. "Sarkin gida yaushe na zama Surukin wannan bawan Allah?" "Ba mamaki tunda akwai aure a tsakanin su da Maimunari" kallon juna suka yi kafin ya ce mishi. "Kuma wallahi sai yanzun na tuna zan iya bashi auren Maimunari, toh ka zama shaida kafin Aminatu ta bayyana, na bashi auren Maimunari" da sauri ya d'ago kan shi. Murmushi Galadima ya sake mishi. "A'a galadima, ita ɗaya na mallakawa kaina don Allah karka kawo min wani tashin hankali" "Toh kunyar uwar me kake ji? Kunyar me kake ji a kaina? Sauke min rawanin da na gada tun iyaye da kakanni da kayi ban haushi ba, mara mutunci kawai" "Kayi hakuri" " Da ban yi hakuri ba, ba mamaki da takaicin ka ya tsiro a gadon bayana, Ina Zakaria?" Ya tambaye Baffa'm, Girgiza mishi kai yayi yana kallon kasa. "Ban san halin da yake ciki ba, nima Sarkin gida ne ya dauko Ni" kallon sarkin gida yayi sannan ya ce mishi. "Ban gane ba, ya aka yi?" Zama suka yi suna kallon sarkin gida. "Allah ya baka nasara, galadima al'amarin da ban mamaki a ce matar da ta haifi d'a da kai ita take yunkurin ganin bayan ka." Waiwaye adon tafiya. Lokacin da Waziri Zakaria yayi aure toh gaskiya baya samun damar zuwa duba Baffa'm sai Bingel ta maye gurbin shi, tana saka Sarkin gida ya daga mata shi ta bashi abinci da magani, ana cikin haka ne ya fara gano jikin Baffa'm ya fara nauyi sama da ace kunyar ta fi haka, dan haka ya dauki abincin da take bashi ya kaiwa wani me magani anan ne yana samu har da gubar maciji ake saka wa kadan a cikin abincin, wanda yana ci a hankali yana shiga jikin shi, tare da kassara duk wani laka da wani kuzari a jikin shi, dan haka me maganin ya yi tsam da ran shi ya ce mishi. " Ka ɗauke shi daga cikin gidan, ba iya gubar bace matsala idan ya fadi ya mutu kai ne abin zargi, ga shi wannan guru ne, wannan layya ne ka saka ka kudiri inda kake son kai shi, ku bar gidan" Wannan dalilin yasa yana komawa gida, bai tsaya ba, ya je yayi sallama da matar shi, sannan ya shiga cikin gidan sarautar ya dauke mai martaba suka yi layyar zana. "Sannan ba iya yau ya fahimci Bingel tana bibiyar lamarin ka ba, na sha kamata tana makalewa tana jin abinda kuke da Aminatu, na sha kamata tana niman hanyar da za zo gare ka. Allah ya huci zuciyar ka, Bingel ita ce ta bawa Makiya damar cimma maka" Lumshe Idanun yayi tare da bude shi akan galadima. "Ku mai dani masarautar" wani kallon da suka mishi kafin suka kwashe da dariya, sannan suka ce mishi. "Da kafarka zaka koma ba yau ba, ba gobe ba. Akwai lokacin da saka koma a yanzun ma balaiin da suke ciki ya ishe su, muna kai ka kuwa kwaɗo zasu yi da kai wallahi, ka bari dai ka jira lokacin sai mu koma ai ba damu koma ba, sau abinda Aminatu ta dauka ya dawo" *Zan tafi amma ka zuba ido ka ga abinda zai hanaka gani* Kalaman ta da alwashin ta, ke yawo a jinin ta, kura mishi ido suka yi. "Yarima Yazidu ya girma" "Dole zan koma, amma ba zan zauna a cikin masarautan ba, ina bukatar mahaifata" "Duk mun sani amma dole mu jira ko, domin yakin da yake gaba yafi wanda ya tsallake, ina yawan bincike akan abinda Aminatu ta haifa, kamar yadda na gaya maka tun farko zakuna biyu ne zagaye da ita, ban san me haka yake nufi ba, ina fatar Allah ya gajarce mana wahalar jira" Haka suka yi ta tattaunawa har dare yayi abinda ke fidda su sallah da cin abincin. ** M. Gobir Tsaye yake rike da takobi, ya juya ya ya kuma juyawa, kafin ya cillar da shi. Yana b'ata rai. "Ni fa ba zan iya yaki ba, wallahi ba zai kashe kaina a banza ba" Aikuwa da sauri sarkin yaki ya taso yana faɗin. "Kai min rai Barkindo, wannan umarnin Fulani Bingel ne" "Kai na ce ba zan iya dole ne sai na yi yaki ji min fa ba zan iya ba" *ZAN YI AMFANI DA WANNAN DAMAR NA TALLATA MUKU SABON LABARI NA ZAYN MALIK PAID BOOK ONE♡300₦* #Mai_Dambu [5/25, 6:31 PM] Mai_Dambu: https://www.wattpad.com/1229064726?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=V%2BtqNmVxWKMWP%2BVLqvIEo9xllqhzq4rS6FN927LtJnDd9KBJtEtZwxGDVVUWLeZWzPmaj%2FkfxAQgcBI0ary%2B%2B7YcfMLySyt5tKYzwwx5JP3i2F77SaTsVUs59bbRZDEw KALLABI..! A Tsakanin Rawuna Mai_Dambu EWF BABI NA TALATIN DA BIYAR Barkindo Yazidu, Allah bai daura mishi kaunar wani hidima na mulki ba, asalima shi irin sakarkarun Yaran nan ne, gashi Allah ya daura mishi tsoron tsiya bai da karfi irin na maza, bar shi da son yawo ya shiga nan ya fita nan. Kaf masarautan babu wanda bai san halin shi ba, gashi da son zama cikin yan matan masarautan, musamman bayi, amma koda wasa bai tab'a musu wani abu na rashin da'a. Bar shi da keta idan abu na mugun ta ne toh wallahi Barkindo karshe ne, shi yasa kowa ke bashi kulawa na musamman. Tawowar Jakadiya mandiya ya dauki kwari da baka ya nunata da shi. "Ke me

Chapter 18 of 39