Share this page
zata kawai dan ina sonki sai nayi laifi? Anum" Durkusawa tayi a gaban shi, tana kallon yadda yake numfashi. "Wallahi ban tab'a Niman wata Y'a mace ba, Anum" ya kira sunanta a gajiye bayan ya daura hannun ta a kirjin shi. "Ina sonki" Cikin tsannanin damuwa ta riko shi, ya mike dakyar ta fitar da shi, daga wurin ta isa inda keken dokin su yake, rike ta yayi yana kallon yadda take kokarin rabuwa da shi. Janyota yayi tare da rungume ta ya saka kan shi a kafadarta. "Don Allah sake ni" ta faɗa Muryan ta yana rawa. "Ina sonki" ya janye daga jikin ta, Sannan ya dafa keken. "Ina sonki." Sororo ta tsaya tana kallon shi. Murmushi ya mata sannan ya ce mata. "Ki zauna da shirin zan zo daukar ki" "Baka da lafiya" ta fada tana barin wurin, baki daya yau tausayin shi yasa ta kasa tuna tsanar shi, a daddafe ta gama kiwo ta nufi gida, zuciyar ta babu dad'i. Kusan kwana tayi tun da taci abinci bata kuma bin ta kai kowa ba, sai ka gyara kwanciyar ta da tayi a gadon ta. Lokacin da ya koma masarautan, ya samu Bingel tana tsaye, Fulani Haima tana kuka a gefen ta. A rikice ya isa wurin Haima. " Waye ya saka ki kuka? Gaya min meye ya faru da ke?" Duk lokaci guda yake mata tambayar, "Ina ka tafi?" "Wurin Anumullah!" "Kai baka san niman rayuwar ka ake ba?" "Ban damu ba, ina sonta" "Zaka mutu idan kace zaka tsaya akan yarinyar domin ba zan tab'a amince ka aure ta ba" "Fulani kawai ki ce na mutu, wallahi na rantse da Allah matukar na rasa Anum mutuwa xan yi! Haima ki wuce gida share hawayen ki, kin ji" "Toh" ya fada tana jan hancin ta, Juyawa yayi a fusace, bai yi dogon tafiya ba, aka ga ya yanki jiki ta faɗi. "Barkindo!!!" Suka kira sunan shi da ƙarfi, ** Yau ake saka ran zuwan su, dan haka bangaren su Fulani Aminatu hidima ake sosai, domin shirin zuwan zaratan yaran ta, wurin magariba kuwa suka ji ana ta buga tambura, sun iso. Kwalla ne ta cika mata Idanu. Musamman isowar Gidado. Zama yayi bayan ya fisgo kalmar sallama da kyar, yana kallon su. Goge kwallar tayi tana murmushin farin ciki. Yau ina da zata ga Baffa'm yau ga ajiyar shi da yaki amsa, riko hannunta yayi yana kallon ta. Da hannu ya mika mata yana mata magana. "Ammyn bani abinci na ci" "Ina dan uwanka?" Alama yayi mata sannan ya ce mata. "Yana wurin mai martaba" Haka ta zuba mishi fura, Innayoh ta shigo da manyan tassa, sai akushe zama tayi tana tambayar shi lamido,ya gaya mata yana can wurin mai martaba. Sai da ya ci ya koshi sannan ya nufi dakin su wanda aka gyara, sannan ya shiga wanka. Kamar an ce ta d'ago kai, ta zuba mishi ido, fuskar shi ma'abociyar nutsuwa da kamala, ta fito rass kwarjini tare da wata irin sirrintacciyar iko irin ta sarakaunan daular Gobir wanda ta ga irin n shi a saman kamilalliyar fuskar Baffa'm yau take hangowa a bisa fuskar shi, haiba cikar halitta. Nutsuwa da kunya wanda ya samo asali daga gare ta, take hangowa a kwayar idanun shi. Uwa Uba hakuri da kawaici irin Mahaifin su, ta gani b'aro-b'aro akan fuskar shi, abin ya matukar tab'a zuciyar ta wani irin wayo baffa'm ya mata ne haka da yaran suka dauke kome nashi, aikuwa wata zuciya ta ce mata. Ribar soyayyar ku ce, sunkuyar da kai tayi kamar yadda shima yayi kasa da idanun shi, yana takowa cikin kuzari irin ta lafiyayyun maza da suka amsa sunan su maza, irin mazan da jarumar mace kawai zata iya fahimtar da cewa shi din Sadauki ne, kwalla ne ya gangaro daga cikin idanun ta. Zama yayi a kan gwiwar shi a gabanta yana me daura hannun shi dukkan biyu akan gwiwar shi, irin zamana sarakunan asali da mulki take kewaye da su, shigowa Innayoh tayi da kayan abinci ta fara jera mishi ta a cewa. "Barka da zuwa namijin duniya namijin gaske, sannun Jarumin maza me dakawa maza gumba a hannu, Barka da zuwa Sarkin sarakan Gobir na gaida gatan gobir, na gaida magayakin Gobir, kowani Sadauki ana haihuwar shi da al'ajabi kai naka domin kare ahalin ka kazo, shi yaushe Jarumin maza zai wanke Uwar Magajin Gobir.... 🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️🚶🏾‍♀️ _Muna fama da rashin wuta gaskiya posting zai zama sau daya a rana kuma sai dare wallahi a takure nake bani da ikon walwala fa sai tunanin typing din ku nake kar a manta Saura kwanaki 29 Insha Allah na fara posting din ZAYN MALIK ₦300 BABU YAWA IYA SHI KAWAI NA SAKA NASAN BA ZAI GAGARE KU BA DA YARDAN ALLAH INA MARABA DAKU MASOYANA HAR DA MAKIYA DOLE SAI DA KU XAN YI TAFIYAR🥰😍🤌🏽_ #Mai_Dambu [6/2, 10:35 AM] Empress Anum: KALLABI...! A Tsakanin Rawuna EWF *Yau naga duniya waye ya gaya muku Barkindo hege ne?😥🤔 mutane sai yad'a labari mara tushe kuke salon Bingel ta juyo kaina gaskiya bana son rashin tsoron Allah😟🥸* BABI NA ARBA'IN DA HUƊU Cikin wani irin yanayi ya ke kallon ta, a hankali take kallon shi itama, cikin kauna da tattalin shi, ya zuba idanun ta kan shi, tana karantar yanayin shi. "Barka da hanya" murmushi yayi tare da boye damuwar shi, sannan ya gyada mata kai. "Ya karatun?" Sai lokacin ya iya bude bakin shi kamar me ciwon hakori ya ce mata. "Alhamdulillahi" murmushi tayi sannan ta ce mishi. "Kun sha hanya ko? Na zuba maka abinci ne, ko sai kayi wanka wancan bawan cikin ya kasa hakuri sai da ya ci" "Sai na yi wanka" ya fada kamar me koyan magana, Ya jima zaune yana wasa da dardumar da yake kai kafin ya samu damar mikewa yana cewa. "Zan shiga ciki" "Toh jarumi" A hankali yake takawa cikin kuzari da alaman lafiyar shi a bayyane take, nufar dakin su yayi ya samu Gidado ya mike, wato barci yake, sai da yayi wanka sannan ya shirya cikin kaya masu kyau irin na mutanen Sudan, ya nad'e kan shi da rawani, zama yayi yana kallon gidado da yake barci abin shi cikin jin dadi da nutsuwa babu abinda ya da me shi. Kallon kasa yayi kalaman mai Martaba yana yawo a kunnen shi. _Ka shirya nan da kwana biyu na tafi masarautan Kano ana bukatar ganin ka, kafin nan kq fara kokarin ganin ka isa Gombe. Muna son mu hada karfi da karfe ku koma mahaifar ku, amma dole sai ka samu dangantakar aure da Masarautan Kano domin ta haka ne zamu iya tsaya maka ke xama sarki_ Shiru yayi yana kallon kasa kafin ya kuma tuna abinda ya fadawa me Martaba. *Allah ya baka nasara ni bana sha'awar mulki Husain yake da burin zama sarki nayi alƙawarin tsayawa a gefen shi, matukar zai zama sarki ni zan zame masa jagaba, Allah ya kara nisan kwana bani da buri ko mafarkin zama sarki amma ina da burin wanke Mahaifiyar mu a idanun al'ummar Gobir don Allah karku tirsassani domin bani da ilimin mulki, ilimin yaki gare ni, ba musu nayi da kai ba. Duba al'amarin* Shiru ne ya gifta a tsakanin su, kafin shi mai martaba ya ce mishi. _Mun yanke shawarar haka ko Mahaifiyar ka bata sani ba, dan haka wajibi ne ka tafi izuwa Kano domin cika mana umarnin mu. Mulki tana bukatar wanda zai daka tsawa ne. Mulki tana bukatar wanda takun sa daya faduwar gaban makiya ne,. mulki yana nufin adalci da sassauci! Mulki yana nufin daidaito tsakanin talaka da Mai Kudi! Adalci zaka nimawa mahaifiyar da ta bar gidan da ake jiran dawowar ta domin jifarta! Idan har jinin Gobir ne ta dauka ya zame mata inuwar gajimare me zai hana? Yau da kimata naje nima maka aure an ce ana ƙyamar ku! Jeka ka huta Yarima Hassan_ Tabbas al'amarin ba karamin al'amari bane, kimar Mahaifiyar su zai kare ko muradin dan uwan shi. Yasan tun tasowar su Hussain yake da burin zama sarki amma bai san lokacin zata juya har yau bai da bakin magana ba, mulkin yana bukatar tsawa? Wato mulkin tana bukatar me magana! Ba yau ya fara kokarin ganin haka ba, amma yana yawan ganin kwarin gwiwar zai iya abu a idanun Ammyn su, sai dai haka kawai yaji bacin rai da aka ce ba a bashi aure ba sai an gan shi, haka ya fita ya nufi Zauren da Ammyn take ya zauna, suna hira da Innayoh. Zama yayi yana kallon su, abinci Innayoh ta fara zuwa mishi, ya fara ci yana kallon kasa, sai da ya gama sannan ya ce musu. "Nan da kwana uku zan tafi Kano" "Uban ɗakina Da fatan dai lafiya?" Lashe bakin shi yayi, sannan ya sunkuyar da kai, bai ce kome ba. Kawai dai ya ce musu. "Aika na aka yi" "Daga dawowar ka?" A karon farko da ya d'ago bacin rai akan rashin zaman shi a tare da Ammyn su, domin bata iya hakuri ba fada ta shiga yi. "Shi kenan ban isa nayi iko da yarana ba? Innayoh kwana uku yaushe yaji dumin Uwar? Kawai daga dawowa Sai wata tafiya, fisabilillahi idanun wani abu ya same shi fa? Gaskiya ba A min adalci" *Ammyn kenan ashe nima kina sona.* Ya fada a ran shi, "Toh uwar ɗakina ai aikan muhimmanci ne idan ba haka ba, ai ba za a ce yaje ba. Uban ɗakina tashi ka tafi sai da safe, yau rikici take ji a ranta idan ka biye mata ma zata yi ta kunco ma kura ne" Sai da safe yayi musu, sannan ya wuce dakin su, kamar ta aro baki tayi masifa har da karamin kukan ta. Washi gari kin fitowa tayi ta cigaba da jin fushinta. Jin Muryan Fulani Bintu da Gidado, suna ta hiran su. Haka suka yi kwana uku tana jin fushi da bacin rai, shi kuwa gogan ko a jikin shi, yana gama shiri ya nime Gidado ya raka shi, yayi tsalle yace bai zuwa yana da nashi tafiyar, dan haka yana barin garin shima ya shirya tare da cewa Ammyn su ai zai bi Lamido ne bata kawo kome a ran ta ba, ta musu addu'ar nasara. A yayinda Lamido ya nufi Gombe ya gana da kakan shi, sannan ya wuce Kano, shi kuma Gidado wucewa masarautar Gobir yayi cikin shigar larabawa da suka fito daga yankin gabas yana tafe da faran dokin, yayin da Lamido yayi shigar yaki yana tare da bakin doki, duk Alkaryar da ya gota sai an razana domin ya shirya tsaf ne domin tunkarar kudirin kakan.shi da burin fansa. Yayinda Gidado ya shiriya tsaf domin cika burin shi na binciken Meye ya faru bayan barin mahaifiyar su, masarautar Gobir, duk inda ya gifta duk alkaryar da ya ratsa cikin girmamawa ake karrama shi domin basu saba ganin Balarabe a cikin yankin kasar hausa ba. Kalaman Sarkin yaki yana kara tabbatar mishi lallai tafiyar nan dole yayi ta domin jagorantar babbar damar wanke mahaifiyar shi, har yake kawo mishi wata irin magana me ɗauke da wasu abubuwan na daure kai. Ratar da ke tsakanin So da Kiyayya ba daya yake da tazarar da ke tsakanin Mutuwa da Rayuwa ba...Amma a kashe shi ko a ci nasara abu daya ne... ba komai ba ne.. wajen Zane Kaddara. dole ne a raba rayuwa akan abubuwa guda biyu... Soyayya da Kaddara... kar a zargi alqalamin kaddara Murmushi yayi lokacin da ya zaburi dokin shi, tare da cillata a guje. "Meye damuwata da wata soyayya? Ina ruwana da wata soyayya? Hanyar da soyayya yabi ban gan shi ba, kuma ban bi ba" Haka Lamido Hassan Kenan ita soyayya babu ruwan ta da kasanta ko baka santa ba. Ita din tamkar maciji take, hadiyar duk wanda ya tsaya mata a hanya take. A bangaren Gidado kuwa abin da ya daukawa kan shi tafiyar ƙaddara ce Imma yayi sa'ar tafiya Imma ya fadi ba zai tab'a danasanin tafiyar ba. Kowanensu ya kudiri Aniyar sa kuma burin shi na son isa inda yake so yana kara cika zukatan su. ** M. Gobir Kwance yake rigis kamar wanda aka yiwa mugun duka, ya gaji sosai. "Yarima Barkindo ga Fulani Haima tana shigowa" "Barta ta shigo" Da sallama ta shigo dakin, tana kallon shi yadda baki daya ya kuma sukurkucewa. Dan gaishe shi tayi tare da tambayar shi. "Ya jikin ka?" "Da sauki, ya Umma?" "Tana lafiya" "Kin san me yasa na tura kizo?" Girgiza kai tayi. "Don Allah Alfarma daya zaki min, ki tafi rugar gidan gona ki dauko min Anum, don Allah ki dauko ta da soyayya ba da takurawa ba" D'ago kai tayi tana kallon shi idanun ta yana cika da kwalla. "Idan Fulani ta sani zata iya sakawa a min bulala" "Ni zan amshi bulalar Alfarma zaki min" ya fada idanun shi cikin nata, "Toh zan dauko ta" Juyawa tayi zata fita ya ce mata. "Kiyi hakuri da abinda take miki" "Ba damuwa" Ta fada sannan ta bar dakin, kwanciyar shi yayi yana jin kamar ana yanka duk wani tsoka na jikin shi tsabar asiri da yake samu daga mutane mabanbanta kawai. --- Tun da ta kado shanu take jin wani irin yanayi, akwai ayarin wasu matasa da suka shigo rugar da wasu irin jajjayen shanu, matasan basu da kunya, domin basu da kamun kai, yan mata da matan aure basu isa zuwa rafi ba, sai da rakiyan mazan gidan su, domin matasan tare su, suke su afkawa mace. Babu wanda ya gayawa Anum labarin kawai dai taga sauyi a yanayin zirga-zirgan mutane dan haka sai ta kad'a shanun suka nausa da shi, ashe suna halkance da ita, kuma wani abin mamaki suma mutanen ashirye suke dan ba kananun shaidanun bane. Tunda suka ga wucewar ta, suka yi ta zaran jiki suka bin bayan ta, kasance hantsi ya dubi ludayi, suka nausa da dajin, tana cikin kiwo taji an yi sama da ita bayan an toshe mata bakin ta, ayi ta hanyar har cikin wani sunkurun me cukurkude da bishiyoyin masu mugun duhuwa da firgitawa, baki daya suka danneta, Sani da Rabi'u ne suka fito suna dariya. "Yar iska har kina da bakin gayawa iyayen mu, su tambaye mu me muka yi yunkurin miki? Toh bari muyi sai mu gaya musu yadda muka yi miki kome dalla-dalla, tare da taimakon Mahaifiyar Yarima Yazidu Barkindo ta biya domin ɗan ta ya rabu dake" suka fada suna janye zanin ta sama. "Kasan mayya ce kafin maitar ta motsa bari mu isar mata da sakon" inji Rabi'u. "Ai muryan ta, shi ne karfin maitar ta, shi yasa muka toshe bakin ta. Matukar tayi kara ko ihu zata iya kome" baki daya suka danne ta, tsayuwa akanta Sani yayi tare da janye wandon shi kasa, sannan ya fara kokarin durkusawa domin biyan buƙatar shi, yayinda Rabiu yake matse madaidaitan nonuwar ta, kwalla ne me zafi ya shiga ƙoƙarin sauka mata. *Allah kaga abinda zasu min Ya Allah ka agaje Ni" Ta fashe da kuka, tana mutsu-mutsu tare da kokarin kwacewa, karan gudun doki da kukan shi, ya sa suka fara kokarin Sani yayi,.kafin ya fara daga can nesa kaɗan ya ja kwari da bakar shi ya sakewa Sani a kadadar shi. Faduwa yayi tare da fasa kara, wanda yasa suka firgita, itama ta fasa ihu, abu biyu na farko tsoron abinda yake shirin faruwa da ita, na biyu faduwar da Sani yayi akanta jini yana watsuwa a jikin ta, haka yayi ta bin su yana harbin su da kifiya, kafin ya dawo gare ta, ganin yadda take kokarin juya baya tana kare jikin ta yasa shi sauka ya cire babban rigar shi, ya ya.wurga mata. "Wuuuuuuuuuuuu!" Zuma suka bi kan Yan iska suna harbin su. Gurnanin zaki yaji a bayan shi. A hankali ya juya yana kallon Zakin da yake kokarin komawa cikin duhuwa, yana kad'a mishi jela. "Me ya kawo tagwai nan?" Duba zoben sa yayi ga gashi nan, sake kallon wurin yayi yaga babu al'amar Zakin. Koda ya juya ya samu ta gudu, kamar wacce aka dauke ta. Abin sai ya bashi mamaki da al'ajabi. Dan haka yayi ta bin su yana cire kibiyar shi, sannan ya bar su a wurin, har ya kama hanyar shiga gari. Yana jan dokin shi. Har ya kawo rugar. A lokacin labari ya karade gari wani Maharbi ya kawo hari, kasancewar basu san shine ba ya wuce abin shi. A hankali yake tafiya yana kara hango katangar masarautan, wani murmushi ya sake tare da cigaba da tafiya ba tare da ya damu da inda yake jefa kafar shi ba, bangaje juna suka yi da Sarkin Gida da ya ya tafi niman labari. Wani irin yarrrrrr Sarkin gida yaji, da sauri ya juya tare da kallon yadda yake tafiya wallahi ban da yasan sarki Bello yana can ba, zai iya rantse wa da Allah Sarki Bello ne a gaban shi kafin ya samu damar tare shi, ya shiga cikin mutane ya b'ata, da sauri ya nufi gidan, ya samu Anum a firgice tana kuka ta makale a jikin Galadima, ilahirin jikin ta rawa yaƙe bakin ta yana faɗin..... *Yaushe zan gama labarin nan ne?😏😒 Allah yasa mu samu wuta an jima na kara muku ko haf page ne ina son na rage tsawon labarin domin wallahi ba ayi kome ba ayi hakuri da rashin Editing nasan kuna ganin kura-kurai* #Mai_Dambu [6/3, 7:49 AM] Empress Anum: KALLABI..! A Tsakanin Rawuna *EWF* https://www.wattpad.com/1232110481?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=qdPF257mAlL4SscuWviHyQ7CE5dgZi01jL8C2l6BFzEf%2BA9Mo%2BPWeo2qUEYYSuJLMHyyyYEUw0VhW4qalgEh%2B1ejYATd5aEoORqseCPYDNa1R4qCFgA%2Fh%2BXzfCil2NEg BABI NA ARBA'IN DA BIYAR Yadda jikin ta yake rawa, yasa baki daya hankalin su ya kasu gida biyu. Aka rasa yadda za su yi da Anum, dan dole Baffa'm ya kira sunan ta, sannan ya mika mata hannu, zuwa yayi gaban shi ta durkusa. "Gaya min me ya faru?" Cikin tsananin tashin hankali ta ma rasa da wani yare zata mishi bayani dan haka ta shiga kuka riris,tana yarfe hannu ta. "Gaya min" "Sune suka zo suka ka mani shine ya zo yayi ta harbin su." "Zaki gane shi idan kika gan shi?" Cikin shashekar kuka ta ce mishi. "Fuskar shi a rufe yake" "Toh shiga ki wanke jikin ki" "Toh" ta ce mishi, ta mike tana me barin wurin su. Kurawa Sarkin gida idanu suka yi,, zama yayi ya labarta musu abinda ya gani. "Ka tabbatar da abinda ka gani kar a samu matsala?" Inji Galadima, Zufa ne kawai yake karyo mishi, kan shi na wani irin sarawa. "Baka ce kome ba Bello?" Galadima ta tambaye shi. "Shekaru ashirin da bakwai na gaya maka karka yanke hukunci cikin fushi ai? Sannan na gaya maka cewa ka mata magana yadda zata fahimce na? Me yasa baka yi ba?" "Ban san yadda zan gaya mata bane, amma nayi haka ne domin kare rayuwarta da na abin cikin,bayan nasan Ni na fara koya mata abubuwa" "Yanzun babu lokaci komawa masarautar zamu yi domin fito da Yaron kuskure ƙalilan idan muka yi zasu iya samun damar daukar shi." Kusan fita suka yi aka bar Anum da ta gama razana da abinda ya faru, dan haka a gurguje ta wanke jikinta, sannan ta kalli alkyabbar shi ta nad'e, jikin ta yayi mugun sanyi dan tsoro take, faruwar al'amarin ta kad'o shanun bar su a kofar rugar su, dan haka mutanen gidan suka kai su garken su. -- Badd'a kama suka yi, dukkan su uku suka nufi cikin gari, suka yi ta niman shi, dakyar suka same shi a wani gidan saukar baki, shima din kasancewar Sarkin gida ne ya fara ganin shi a farko kuma shi ya gane shi, kawai suna ganin shi babu wani b'ata lokaci, kawai suka saka mishi wuka a baya, bai yi musu ba suka bar masaukin wanda haka ba karamin al'amari bane domin suna barin wurin dogarai suka dira a gidan saukar bakin, suka gama niman shi basu gan shi ba. Basu bari ya dauki dokin shi ba, sai jan shi a hannu suka yi, suna fita daga masarautan suka dauki dawakan su, suka nausa dajin. Sai da suka isa gidan suka samu Anum bata nan, dan haka suka umartar shi da ya warware mayafin fuskar shi. "Cire mayafin ka?" "Toh amma me yasa kuka kama ni?" Ya tambaye shi, yana cire mayafin, jikin Baffa'm ne yayi sanyi wannan bai kama da shi ba, kuma bai kama da Aminatu ba. "Baku bani amsar tambaya ta ba?" Ya kuma tambayar su. "Kayi hakuri daga ina kake?" Murmushi yayi tare da kallon su, sannan ya ce musu. "Suna na Yarima Hamza daga masarautan Fika can Yobe, nazo ganin Fulani Haima ce" Jinjina kai Baffa'm yayi sannan ya ce. "Koda zaka shiga cikin masarautar don Allah ka saka idanu akan bakuwar fuska" "Shi kenan Insha Allah zan yi haka" daga nan ya musu alama su bar shi ya tafi, sai da yarima Hamza ya bar gidan sannan Baffa'm ya zuba musu ido, yana niman karin bayani akan masarautan. "Yar waziri ce, Haima sai dai yarinyar daga ita har iyayen su, suna cikin tashin hankali fitinar Bingel" Murmushi Baffa'm yayi sannan ya kalli hanyar waje, --- Malam Gidado kan ai garin shi giji, domin kuwa abinda ya jima yana mafarki ne, yayi ya bin unguwa unguwa yana kallon tsarin gidajen masarautar, babu tsoro a ran shi sai ma farin cikin da yake shekaru talatin baya anan Ammyn da Baffa'm suka yi soyayya, zama yayi yana rubuta duk abinda ya gani a ranar yau har cikin masarautan. Yamma likis ya bar wurin sannan ya juya zuwa wajen gari, kasancewar babu wani alamar damu ya gama abinda zai yi akan gobe zai kuma shiga masarautan, ya fita wajen masarautan tare da tuna ai ya wuce wani rugar Fulani ba mamaki ya samu masauki, sai da yayi tafiya sosai sannan ya isa garin. " "Allah ya baka nasara, kashe mutanen da aka a dajin sai kara, da kibiya ne sai kuma zuma da suka musu kawanya, ga kibiyar mun samu ɗaya" Labari ya iso masarautan cewa wani mahari ya harbe mutane bakwai hudu sun mutu uku sun jikkata. Dan haka koda ya gayawa malamin shi, cewa yai maza a kama mishi maharin domin dan leken asiri ne. Kallon Waziri da su Chiroma yayi yana tab'e baki ya ce musu. "Ban san kome akan haka ba, waye ya san wani abu akan kibiya?" Mikewa Sarkin yaki yayi ya tako ya amshi kibiyar, yana kallon shi. "Ina zan samu gawarwakin mutanen?" "Ba mamaki zuwa yanzu an binne su!" Kallon Waziri Zakaria yayi. Shima ya kalle shi. Kafin suka kalli Yakubu. "Ku bani baka?" Bashi aka yi ya ja mayafi ya rufe idanun shi, a hankali ya haɗa bakar, tare da jan zaren ta da kibiyar! "Alfadari me kashin kudi, Giwa me tafiyar kasaita, wuji wujji namijin guguwa, wani kaya sai amale, hadisin k'ak'a b'ata kayan rago, rumfa sha shirgi, ruwan sama maganin daud'a cinnaka, baki kake ga yan gida baki kake ga baki, a dawa sarki kake a waje sarki kake, shugaba ya dawo!" Ya cire kyallen fuskar shi yana kallon yadda kowa na fadar ya mike hatta sarki Yakubu. "Sarki Bello ne ya koya mana wannan harbin duk wanda yayi harbin nan Imma sarki Bello da kan shi ko kuma Abinda Aminatu ta tafi da shi ne" "Karya kake!" Yakubu ya daka mishi tsawa. Rufe baki yayi yana kallon kasa sam a manta da cewa ai a fadar yakubu yake. "Ku nimo min shi, a yanke min kan shi a kawo min babu shegen da ya isa raba ni da mulki na" da sauri suka juya suna kallon shi. "Allah ya huci zuciyar ka, Yarima Yazidu fa?" "Idan ta kama a kashe shi, shima" ganin haka yasa kowa ya shiga hankalin shi tunda suka ji batun kisa. "Maza dakaru su bazama su nimoemi. Shi" Haka suka fita aka fara ƙoƙarin niman Gidado. Koda ya koma garin, ya rasa Inda zai kwana. Ga dare ya fara yi, tagwai ne ya bayyana a gefen shi, ya shiga gaba shi kuma ya sauka akan doki, a hankali suke tafiya cikin sand'a kamar marasa gaskiya, ya shi har cikin dakin Anum, da take ta kokarin barci, sidif ya shige cikin dakin. A hankali yake takawa, har ya isa bakin gadon ta, dake akwai fitilar mai a dakin, tana ganin inuwar mutun ta takarkare ta kwamutsa ihu, da sauri ya toshe bakin ta, ilahirin jikin ta rawa yaƙe, hawaye na zuba mata. Mai da ita yayi yana girgiza mata kai. A hankali ya saka hannu shi a bakin shi. "Shiiii" ya ce mata. Gyada kai tayi, a hankali ya mike ya fara rage kayan shi, wannan shine karon farko da ya kwanta a dakin daya da mace, toh bai da zabi yasan tunda tagwai ya kawo shi nan babu inda zai dace da shi sama da nan, dan haka ya fita a hankali ya bar gidan bakin tafi ya tafi yayi wanka shi da tagwai. Tagwai shine baiwar su na yan biyu, kamar yadda ake haifar yan biyu da maciji da kunama su an haife su ne da zakuna biyu, tagwai shine zakin Lamido, Zakin gidado suna kiran shi da biyuna, shi bai cika zama a cikin su ba, kasancewar Gidado bai damu da shi ba, shi yana tare da Lamido ne, amma kowannen

Chapter 23 of 39