kowa. Shi yasa ya zama sussu akan ta, sannan idan kun duba zaku ga duk wulakancin da tai mishi ba zai taba ba shi haushi ba, har ila yau da suke tafiya kafada da kafada. Kawai abinda zuciyar shi da tunani yake bashi zai iyaa bin Anum ko ina ma.
Barin su kofar Sarki Yakubu ya iso, tare da tawagar dakarun shi..
"Waye ya fita yanzu?"
"Yarima Yazidu da wata mace suka fita"
"Maza abi bayan su" ya bada umarnin da a tafi, suna gaba yana bin bayan su.
-
Basu yi wani dogon tafiya ba, amma sun bar da'iran Masarautar, dan haka masu dawakai suka musu kawanya. Mutanen da Bingel ta turo, rike hannun Anum yayi yana kallon ta ina zasu tsere musu.
Ganin babu hanya yasa shi bude baki ya ce.
"Me muka muku?"
"Yarima Yazidu babu abinda kayi, asalima ita yarinyar zaka bamu kayi tafiyar ka, idan kuma ka ki zamu hada har da kai umarni aka bamu"
Sake k'amk'ame juna suka yi bakin shi na rawa,
"Ke yarinya kawo kan ki"
"Idan na kawo kaina zaku kyale shi?"
Ta fada lokacin da ta cire hannun ta cikin nashi.
"Anum!" Ya kra sunan ta cikin sassanyar murya.
Juyawa tayi tana kallon shi.
"Tsoron mutuwa kake ko tsoron Allah?"
"Dukka anum" ya fada yana hàdiye yawun tashin hankali, har makwalontan shi yana motsawa.
Murmushi tayi sannan ta ce mishi.
"Ni kuwa bana jin haka domin jikina yana bani jarumina yana dab da shigowa duniya ta."
Juyawa tayi tana kallon su.
"Toh shi kenan gani" ta fada daidai lokacin da sarki Yakubu da jama'ar shi suka iso wurin, wani irin fisga zoben yayi yaja dokin shi zuwa gaban Anum.
"Lafiya?"
"Kai ku kama mana yarinyar shi kuma ku kai shi inda yafi wayo"
D'aga hannu Sarki Yakubu yayi, a take aka sakewa mutanen bingel kwari da baka. Duk suka zube dawakan su, suka shige daji.
Sauka yayi kan dokin ya iso gaban Anum. Sake matsawa yayi yana kallon fuskar ta.
"Au dama kece sarauniya ta?" Ya fada yana fashewa da dariya.
Ja da baya tayi tana kallon shi hannun ta cikin na Barkindo.
"Ka bamu hanya mu wuce"
"Dakaru ku mai da Lusari wurin Uwar shi, ita kuma ku kai min ita gidan hutawa na"
Ya fada tare da hawa dokin shi, ai kuwa cikin cika umarni suka nufi Anum, da wani irin kara da ya fasa sai da dajin ya dauka me matuƙar firgice, hatta tsuntsaye tashi suka yi tayi suna kada fuffuken su. Masu kwanciyar kasa dabbobin suka shiga gudu domin ceton rayuwar su, wani irin guguwa me karfi hade da iska ta shiga kadawa a sararin samaniya, bishiyoyin nan suka shiga rangaji kamar an shiga tsakiyar watan ruwan sama, ko ina sai tashin kar'ar ta.
Surarrta Baffa'm wanda yaji karan ta, tun daga inda yake, dama yafito nimanta ne, sakamakon labarin da aka basu an zo an dauke ta, mayafin shi ya lullube ta da shi, suka B'ace baki daya. Sai da suka B'ace iskar ta tsaya cak.
Kurawa wurin da take idanu suka yi babu ita babu daliln ta.
Juyawa yayi ya kalli Barkindo. Wanda akan idanun shi yaga lokacin da aka dauke ta, amma tsabar karfin iska da yashin da yake shiga musu idanu ba zai fadi ga asalin abinda ya faru ba.
Marin shi Yakubu yayi yana faɗin.
"Shege mara amfani, Meye ka kurawa wuri ɗaya ido."
Cikin fushi shima ya kai mishi duka, sosai suka kaure da dambe wanda shi kan shi barkindo bai san yana da wannan karfin ba, kawai Yakubu dai nuna mishi kwarin kashi ne, amma akan Anum ya gwammace a kashe shi da ya bari a isa ga Anum, dan haka suka yiwa juna jina jina,
Ganin yadda Barkindo ya makale mishi da Naci da dambe yasa shi kiran Dakaru.
"Kai ku balla min shi"
Babu musu suka shiga dukan shi, motsin da suka ji ne daga bayan su, yasa su juyawa, Duk da basu gane waye ba, amma kuma sun yi kuskuren dukan Barkindo, domin idanun mutumin har yana cika da kwalla, kamar mahaukaci ya far musu da azababben yaki, kuma kashe su yake kamar ya samu kwari, zai da ya girbe, Yakubu ya tsaye tsoro ya gama cika shi.
Mutumin bai kula shi ba ya dauki Barkindo ya daura shi akan doki, ya nufi masarautan da shi.
*
A can kuwa toshe mata baki Baffa'm yayi da hannun shi, wanda yayi sanadiyyar sumarta a jikin shi. A hankali ya isa da ita rugar su, ya isa da sallama.
"Gata nan na same ta an kawo musu hari tare da mutanen da suka taso rakata"
Ya mika musu ita, sannan ya wuce abin shi. Jin suna mishi godiya bai saka shi ya ce musu cikanku ba.
Koda ya isa gidan kallon Galadima yayi da suka zuba mishi ido.
"An fara farga da yarinyar nan ya zamu yi?"
"Insha Allah babu abinda zai faru, ina jin haka"
Zama yayi yana kallon su, baki daya ya rasa yadda zai yi domin duk wanda zai zo jikin shi yana da muhimmanci, shi yasa yake kaf-kaf da su.
--
Sai da ya kusan suma lokacin sa yaga mutumin ya wuce, sannan ya samu ya sake numfashin sa, tare da zabura ya haye doki,koda wasa bai yarda ya nufi masarautar ba,domin wani mugun tsoro da ya kama shi, kamar zai mutu bai tab'a fadawa irin wannan yanayin ba sai yau, kuwa ta bayan masarautan ya shiga cikin masarautan tare da nufar Hanyar sashin sa, kicibis suka yi da mutumin rike da takobi tsirara.
Cikin rashin Imani mutumin ya shiga saran shi,cikin fushi da fusata. Kafin ya ce mishi.
"Kar na kuma ganin ka kuskuri Barkindo! Idanu na yana kan ka" ya mishi alama da yatsu biyu.
Sannan yayi tafiyar shi, ya bar shi a cikin jini malala.
*
Lokacin da aka shigar da Barkindo, bingel ta razana domin bata kawo zasu mishi irin wannan dukar ba, a rude ta shiga kiran mandiya aka fara bashi taimaka mishi..aka kai shi dakin shi duk da yana cikin wannan yanayin bai fasa kiran sunan Anum ba.
"Anum!!" A hankali yake kiran sunan ta.
Hankalin kowa ya tashi gashi ita tasa a mishi toh gashi nan dai a halin wani yanayi.
**
Borno
Kwana suka yi akan ta, washi gari ya haɗa kayan shi kamar yadda ya shirya tafiyar shi, domin haka kawai yake jin wani irin yanayi akan tafiyar kamar wanda ake azzalashi, lokacin da ta farka wurin goshin asuba, zuba mishi ido tayi.
Hannun ta, ta kai kan shi tana girgiza mishi kai tare da cewa.
"Kace ina jiran shi, tawo kafin lokaci ya kure ina jiran shi, iya shi nake jira yazo mu gana"
A hankali ta mike tare da nufar gaban wani akwati wanda akala ya kai sama da shekaru ashirin bata bude ba, zama tayi ta kalli cikin akwatin tana me budewa, tari take me hade da jini goge bakin ta tayi da damshin jini ta a hannu ta binciko akwatin, jelar dan dalago ta dauko, tana kallon shi hawaye na suka daga kyakyawar fuskar ta, wanda har kwanan gobe ba zaka ce ita ta haifi zakuna biyun nan, nutsuwar da takr samu yasa jikin ta da yanayin ta bai sauya ba, a hankali ta ciro wani katon kundi wanda aka daure da igiyar fatar barewa, a hankali ta juya tana me isa wurin su, kamar zata fadi. Gidado ya rike hannun ta. Yana girgiza mata kai yayi hawaye na zuba daga idanun shi.
Motsa bakin shi yake al'ama magana yake mata. Sannan ya taimaka mata ta zauna.
Zama yayi shima a ƙasa, sannan ya kalli yadda take kallon su. Wani irin tausayin yaran take ji, gani take kamar masarautar Gobir bata mata adalci ba, gani take kamar dukkan su kashe mata su za ayi, kaunar Yaran yana kara ninka idanun ta, kuka take kamar karamar yarinya, bude musu hannu tare da musu alama su tawo jikin ta.
Da sauri suka shige jikin ta, kallon su innayo take domin yau ta tabbatar da cewa dagaske Aaminatu zakanya ce da take boye yaran ta sabida masu farauta, ita kanta kuka take domin suna jikin Aminatu amma ta kasa sake su, gani take kamar zata iya rasa su kamar yadda ta rasa Uban su, shi take kuka tun daga kasar zuciyar ta, irin kuka mara dadin nan take tana kara rike su.
"Hassan don Allah karka juyawa dan uwanka baya, karka tsane shi, karka taba rabuwa da shi, kayi hankali da shi. Don Allah na roke ka. Kar wani abu na rayuwa yasa ka juya mishi baya, ka tuna bai da kowa sama da kai
Hussain ka tuna baka da kowa sama da Hassan don Allah ku had'e kan ku. Idan kan ku ya hadu babu wanda zai iya shiga tsakanin ku, don Allah don Allah kar ku raba min kan ku, iya shi zaku min naji farin ciki."
Hada ya cire su a jikin ta, ta hade hannu su. Tana kuka kamar ranta zai fita, gani take kamar zata rasa su cikin tarin kaunar su, da wani irin begen yaran take kara rike su.
"Uwar ɗakina ki bar shi ya tafi,domin cimma burin da aka jima ana tanadar shi"
A hankali ta dauko kundin ta mika mishi.
"Ka kai mishi! Kace yarinayr nan tana nan tana jiran masoyinta, yarinyar nan dai tana jiran shi, gashi ka kai mishi kace mishi ko duniya ta manta da Waye Bello Aaminatu bata manta fa shi ba, bata manta da malamin ta ba, bata manta da waye shi ba" daga nan ta kuma sunkuyar da kai tana faɗin.
"Allah ya haɗa ka da rahama da nasara, ya baka abinda baka zata ba, ya cika maka alkhairin da yake tattare da nasarar da ka samu, Allah ya maka jagora ya rabaka da sharrin abin halitta. Allah ya ƙaddara ganawar mu/ tashi ka tafi"
Kallon ta yayi yana hàdiye yawun shi, ta bashi tausayi baki daya ya rasa yadda zai yi dan haka ya mike tare da riko hannun Gidado suka fita daga cikin gidan, suka tafi gidan dawakai ya dauki farin dokin shi me suna Hari, ya saka kome da kome jikin dokin akwai wani irin sirdi da aka kawowa Sarkin yaki daga can ƙasar larabawa, masu Aljuhun.
Kallon juna suka yi kafin suka rungume juna. Sake juna suka yi Gidado ya rike hannun shi ya saka a saman Kirjin shi.
"Yarinyar tana nan don Allah kar ka manta ka nima min ita, kace ina son ta ka bata wannan mayafin"
Ya mika mishi mayafin shi, kurawa juna idanu sukayi, zuciyoyin su yana wani irin bugawa kamar zai tsage ya fito daga kirjin su. Kowannen su yana jin wani irin yanayi akan tafiyar, komawa cikin gidan suka yi bayan sun dauko kayan Lamido, suka fito a tare.
Shima hawa dokin shi yayi me suna Sare, ya kada linzamin suka bar masarautan a guje, girgiza kai Lamido yayi....
_WANNAN SHAFIN NA YAN WATTPAD NE MUSAMMAN WAD'ANDA SUKA YI TA SITIRIN DUBA UPDATE NAGODE DA KULAWA ITA SHA'ANIN RUBUTU YANA DA GUNDIRA DA HAWA KAI NE, SHI YASA JIYA NA WATSAR DA SHI NA KAMA DAHIR much love masoyan Sarauniya Bingel 🥰😍🔥❤️_
#Mai_Dambu
[6/12, 8:06 PM] Black Girl: KALLABI...
A Tsakanin Rawuna
EWF
BABI NA HAMSIN DA SHIDA
Cikin wani irin azababben zafin nama yake yakar su, kamar ba bako ba. Irin yakin nan da ake yi dan kare kai wato (self defense) haka yakar su, tsabar tsoro ko bude idanu bata yi ba, sauran mayakan gani yana kokarin kar su, yasa suka juya a guje, taka dutse yayi ya murza tare da cillata da kafa, ai kuwa ta samu keyar dayan su, faduwa yayi yana rike kan shi. A hankali ya sake takobin ya kunce ta daga jikin shi fincikota yayi har zuwa lokacin bata bude ido ba, ai kuwa ya damke rigar ta gaba sannan ta cillata, kamar wata bushashen ganye haka ta gibgu da kasa ji kake timmm.
"Wayyo Allah na katarya ta!" Ta rike kugun ta, tana me bude idanun ta. Ganin shi tsaye yana nad'e fuskar shi , kallon yadda yayi mugun barna yasa yasa ta ce.
"Amma kai daga duniya makasa kazo ko? Da yanzun na mutu waye zai biya Ni mutuwa ta? Kawai ayi mutum bai da burbushi imani, salon na mutu a saka shanuna kuka."
Rike baki tayi tana kallon yadda wurin ya b'aci da jini, bata san lokacin da ta fara kwara amai ba, sabida karnin jinin da ya kaure a wurin.
Aikuwa shanun suma munafukai suka ce "muaaaaah!"
A wahale ta ce musu
"Ai na sani bayan ku babu me min kuka ko na mutu"
Bai damu da zanttukar ta ba da kuma halin da take ciki ba, dan yasan dole haka ta faru, kawai abinda yayi shine zuwa wurin mutumin ya riko wuyar shi, ya D'aga shi cak. Rike bakin ta tayi tana kallon rashin imani irin nashi.
"Waye ya aiko ka?"
"Anum aka turo mu kashe don Allah ka min rai wallahi ina da iyali don Allah kayi hakuri"
"Waye ya aiko ku?"
"Mahaifiyar Yarima Barkindo!" A hankali ya ke juya sunab barkindo kafin ya juya ya kalle ta, sai wani cika take ita nan an nime kashe ta.
Mikewa yayi ya fara nad'e kayan shi yana daurawa akan dokin shi, sannan ya haura saman dokin zai wuce.
"Kai barawo kazo nan wallahi baka isa ba, idan na yarda wutar lahira ta ci ni, ba zaka tafi ka bar ni anan inda yake cike da dangin ka makasa ba"
Dan ita har yanzun gani take satotta yayi shi yasa take kiran shi barawo. Janye mayafin fuskar shi tayi ya watsa mata harara.
"Sai idanun sun fado ƙasa zan fahimci kana harara ta, malam saukowa zaka yi ka mai dani inda ka dauko ni" ta tsaya a gaban dokin shi.
Sauka yayi ya riko linzamin dokin ya fara tafiya a hankali, itama ta kad'o shanun ta, suka fara tafiya.
"Allah sai ya saka min cinye abincin da kayi baka bani ba, kuma su wadancan da ka sare su waye zai mai da su gida, kana bako kazo zaka jangwalo mana damuwa, gaskiya ban yafe ba wallahi dole ka nima min abinda xan ci"
Juyawa yayi a fusace, tona aika-aikan da yayi yasa ta, kasa da murya tana faɗin.
"Allah ya baka hakuri" bai kulata ba yayi gaba abin shi, aikuwa ta bi bayan shi da harara. Juyawa yayi ya kamata tana hararan shi bai bi takan ta ba, sai dai yanayin garin da haka kawai ya soma hada hadari yasa shi. Niman irin manyan duwatsun nan da suke a wajen gari(wato mountain) ya shiga zaga cikin shi. Kaf ya duba babu kome sannan ya koma ya dauko dokin shi suka shiga kokon dutsen, ita da shanun ta suka ki Shiga, gani take kamar tana shiga zai mata wani abu shi yasa taki shiga, aikuwa aka fara ruwa kamar da bakin kwarya, fitowa yayi yana kallon ta a tsugune duk sanyi ya dame ta, fita yayi a cikin ruwan can sai gashi da ƙaruwar gada, da kirare ya shiga abin shi ko ta kanta bai bi ba, ya haɗa wuta ya turara kokon sanan ya fede gadar ya shafe ta da gishiri da garin citta da Innayoh ta hado mishi da dan barkono kaɗan, sai yar man shanu shi da ya shafe gadar da shi, ya bankare fadar ya haɗa kome ya hura mata wuta sosai, kallon bakin kokon yayi yaga tana leko kai, bai wani kuma damuwa ba, shi kan ma mamaki yake yar yarinya karama irin ta aka turo a kashe toh me tayi musu?
A hankali kamshin gashin ya fara daukar hankalin na kusa, tun tana iya jure kamshin har ta kasa sai wani sosa soshe take, kai karshe sai gata a cikin kokon ta zauna a gaban wutar tana hàdiye yawun, warware mayafin fuskar shi yayi yana kallon yadda gashin yake daukar kamshi, hàdiye yawun tayi tana kallon lokacin da ya ciro wukar shi ya yanki suka ya duba yaga babu ruwa da jini, sakawa yayi a baki yana taunawa a nutse cikin wani miskilin yanayi yake lumshe idanun shi, yana jin wani dadi da dandano har yana saka kunnen shi rawa,
Sake hàdiye yawun tayi tana motsa bakin ta, tare da gyara zama tana marairaice fuskar ta.
"Allah yana son masu kyauta da bada abinda bai..."
"Kurrrrrrr!" Cikin ta ya bada sauti, kallon shi tayi ta kara marairaice fuska.
Yankar naman yayi sosai ya koma gefe ya zauna yana ci a hankali, ganin yadda yake ci hawaye ya shiga zuba mata cikin shashekar kuka ta ce mishi.
"Don Allah yunwa nake ji" d'ago kai yayi ya zuba mata ido, kafin ya mai da idanun shi kan wukar, itama wukar ta kalla ta mike da sauri ta fara yankar namar jikin ta yana rawa, da wutsiyar ido yake kallon ta, har ta gama ta koma gefe ta fara cin namar, d'ago kai tayi tana kallon shi yadda yake cin namar, kamar bashi ba. Har ya gama ita kan sake karawa tayi yana kallon ta bai hana ta ba, sai da ta gama ta koma gefe jikin ta ta mutu. A hankali ta shiga barci.
Shima kwanciyar yayi yana jin barci, sabida sanyin da ake ga ruwan da ake kwararawa, har barcin shi ya fara nisa. Yaji shashekar kukan ta, bude idanun yayi zuba mata,kafin ya tashi zaune ya ciwo mayafin shi ya lullube ta, sannan ya koma ya kara hada wutar sosai. Sannan ya fita yana duba dabbobin ta. Duk suna nan lafiya lafiya, sannan ya koma yayi alola kafin ya gabatar da sallah azahar, yana kallon har lokacin barci take yi.
Mamaki da barcin ta yake, wuni guda tana barci yayi kokarin tashin ta, amma bata farka ba, ai dole kodan wannan yawon da tayi tayi babu barci, shi yasa bai kuma D'aga ta ba, sai wurin tsakiyar dare ta farka, ta hango shi zaune akan buzu yana karatun Alqur'ani. Kama mayafin tayi tana kallon shi.
Kamar zata ci babu haka ta farka da mugun yunwa, ganin ruwa a gefen ta a cikin goran ruwan shi tayi alola tare da fita waje yaga garin yayi duhu ga sanyi, dan haka ta dawo kokon ta gabatar da sallah tana idarwa ta juya wurin naman da ya saura ta dan kalle shi aikin hankali tayi ta yanki kadan ta bar mishi sauran. Dan haka taci ta koma ta kwanta. Barci me nauyi yayi gaba da ita, sai da ya kara dumama kokon ya kwanta.
**
"Ki min rai! Wallahi wani mutum ne ya taimaka mata, ya kashe kowa da kowa don Allah kar ki kashe ni ina da iyali"
"Ku fitar min da shi" bingel ta bada umarnin a fitar da shi, juyawa tayi tana kallon Mandiya.
"Ta ina zan samu damar kashe ta? Na tsani yarinyar nan"
"Ni kuma ina son ta! Ina kaunar ta innah idan wani abu ya same wallahi ba zan yafe ba, ashe dama kece sanadin b'atar ta?"
Ya tambaye ta yana ihu, bata kula shi ba, amma kuma ranta ya b'aci.
"Zan tafi niman ta" ya fada bayan ya juya dan yasan tunda ta mishi shiru ba zata tab'a kula shi ba. Dan haka ya bar gidan cikin fishi.
Hana shi fita aka yi dan dole ya hakura.
-
A can kuwa suna barci, a hankali yake jin kukan dokin shi bude ido yayi yq dauki takobin shi da bakin wuta ya fita, hango shanu yayi suna guje guje kura ta saka su a gaba,
"Keee!!!" Ya daka mata tsawa, da gudu suka bar wurin ya manta ne bai daure dajin daga dabobbi ba, dan haka ya kama ganye da sauwar shi, ya daure dajin tsaf sannan ya shiga ya ga yadda take barci, juyawa yayi ya kwanta akan buzun shi, har asuba tana barci sallah yayi ya fita farauta.
Koda ya dawo ta hanyar ya gane wasu sun shiga cikin kokon dan haka yana shiga ya hango irin arnan dajin nan, sun rufa akan ta sai dambe suke. Bai kula inda suke ba sai ma aikin da ya tsiro yi, ganin haka suka juya gare shi da sun san ma'anar shirun shi da basu fara wannan kuskuren ba, kawanya suka mishi, kura mishi Idanu suka yi tare da kai hannu suka Safar kadadar shi....
*Lalaci nake ji😿💔🔥*
#Mai_Dambu
[6/12, 8:45 PM] Black Girl: KALLABI..!
A Tsakanin Rawuna
EWF
BABI NA HAMSIN DA BIYAR
Wani irin zaburar dokin yayi, tare da kaiwa Gidado cafka ya sha gaban shi.
"Insha Allah zan nima maka, amma da sharadin zaka kula Fulani Bintu domin ta cancanci zama wata alkaryar agefen ka"
Dariya yayi ya kara a guje, yana me kallon Lamido har suka bar masarautar, sai da ya raka shi wajen gari lokacin an fara sallah asuba suka tsaya suka yi,sannan yana kallon Lamido ya bar kasar borno,cike da kewar juna. A hankali ya juya baya, yana jin kamar ya bi dan uwan shi.
Shi kuwa Lamido ko juyawa bai yi ba, domin yana jin yadda dan uwan shi yake kallon shi yasan kewar shi yake ji, dan haka yaki juyawa shima ai kewar Gidadon yake ji.
Haka yayi ta tafiya sallah da cin abinci yake tsayar d shi, sai da yayi tafiyar wuni guda. Kafin ya yada zango ya kwanta.
**
Wannan abin da ya faru sai da yasa Anum ciwo sosai, domin ko magana bata yi, muryan ta ya dishe ainun bata ko iya wani motsin kirki jikin ta kamar an kareraye ta, idan ka ganta akwance kamar danyen nama, ga masifar Inono, ga fitinar matan gidan su.
A hankali tayi ta ja da ciki domin yunwa take ji, tura kofar karanta tayi ta hango Dadah tana ta kokarin sauke dafaffen madara, sako kai tayi tana kallon ta. Hawaye na zuba daga idanun ta, yunwa take ji kamar tayi ihu, amma ba a jin me zata ce. Dan haka ta daura kanta a dokin kofar, tana kuka a hankali, wani irin Haushin Mamanta take ji akan me bazata tafi da ita ba, ina ma take yanzun,gashi Abbanta ya rasu bata da kowa sai Allah.
Kamar ance Dadah ta juya, idanun ta ya sauka kan Anum da take kwance. Komawa daki tayi ta dauko fura ta dama sannan ta zuba zuma a kai, sannan ta zuba dafaffen madara, ta kawo mata. D'aga ta tayi sannan ta yi ta bata da bakin ƙwaryan anan ta fahimci ciwon Anum har da yunwa, dan tana bata,ta shiga sharbe zufa.
"Me yasa wannan ranar kika fita cikin dare?"
Kurawa Dadah idanu tayi sannan ta ce mata.
"Nima Gwaggo Bingel ce ta saka aka tafi da ni" sanin halin Anum bata yarda da kowa ba, balle har tayi magama da kai, sannan yarinya ce da tun tafiyar Mahaifiyarta duk abin da zata fada gaskiya ne, bawai ta yarda anum ba zata mata karya bane, amma bata san lokacin da zuciyar ta ya amince da abin da Anum din ta fada mata ba.
"Kiyi hakuri kin ji, haka Allah ya halicci wasu da son zuciya, nasan Barkindo baya cikin masu irin wannan yanayin don Allah ki kaunace shi"
Hawaye ne ya zubo mata, ta kauda kan ta sannan ta ce mata.
"Daadah ina niman wanda zai kare rayuwa ta ne ba wanda ni zan bashi rayuwa ta ba, Daadah hawai na rena tayin bane Wallahi sam bai min ba, ina son shi amma ba zumunci, ban da son soyayya da za a gina rayuwar aure akan su ba."
Cike da mamaki take kallon Anum gashi dai gaskiya ta gaya mata, amma ya zata yi da Bingel da ta matsa lallai ta nima mata yardan Anum.
"Baki ganin shi din sarki ne gaba" goge bakin ta tayi tana kallon Daadah sannan ta tattaro hankalin ta baki daya ta Zubawa Daadah.
"Daadah shi mulki jarumi ake nima, wanda zai gyaran murya jikin kowa ya dauki rawa ba Lusari ba wanda da shi da babu ɗaya ne"
Murmushi Daadah tayi tana faɗin.
"Mulkin baya gabanin kenan?"
"Eh Daadah" ta fada lokacin da ta hada karfi da karfe ta mike, ta fita waje.
"Toh yar iska kin samu lafiya daga yau ba zaki kuma fita domin aikin wasu ba, su shanun da Ubanki ya bar Miki mune zamu miki kiwon su?" Tura baki tayi tana faɗin.
"Idan aka ce na tafi da su kiwo ai ba zan ki tafiya da su ba, da sai an hada da Ubana da yake kabarin shi bai ji ba bai gani ba, Insha Allah yau babu me shan ruwa cikin salama" ta fada kasa kasa,tana nufar waje bayan ta dauki tulun diban ruwa, tun da tafiya ta tafi bakin rafi ta zauna tana kallon ruwa, a hankali ruwan ya shiga rinewa zuwa jajjur kamar ruwan jini, ita kanta idanun ta wani irin rinewa yayi kamar yana ci da wuta, Murmushin keta tayi tana faɗin babu me shan ruwa cikin salama sai kun ji a jikin ku.
Sannan ta dauki tulunta ta tafi bakin rafin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 28 Chapter of 39