suka bashi, madadin haka sai murmushi ya sake yana kallon baki daya dake matsorata ne gudawa suka yi da Barkindo, komawa yayi cikin majen ya watsa mata harara, babu shiri ta fito tana sunnne kanta kasa.
Yana kallon ta daga nesa ta shiga cikin gidan komawa yayi yana nazarin abinda yake gaban shi.
*
FADA
Tsawon kwanaki uku ana kai ruwa Rana da Waziri Zakaria akan lallai sai dai ayi wani abu akan Yakubu, abinda ya saka aka fara zargin ko zai sayi mutanen fadar ne yayi juyin mulkin tunda kowa yasan ana haka, shi yasa basu bashi goyon baya ba, suke ganin kamar ya kawo musu wata hanyar da zai ruguza musu zaman lafiya z da tattalin arziki, wanda shi a tunanin shi so yake a kara karfin tsaro ta yadda zasu kare masarautan. Amma suka mishi caa,
Ba dan kome ba sai dan idan aka ce za ayi yaki duk wani arzikin masarautan zai kare ne a niman zaratan maza da kuma kera makaman yaki, wanda haka zai shafi tattalin arzikin kasa baki daya, sannan uwa Uba basu sa goyan bayan wasu masarautun balle su basu goyan bayan da aron dakarun da zasu taimaka musu, wannan yanayin yasa suka gwammace Gara kar su shiga yakin kar su tankawa Waziri, da ya ishe su ne ma suka saka shi a gaba.
"
Haka zamu zuba mishi ido babu wanda ya isa da shi? Karku manta a masarautun nan aka sace Baffan Bello, har yau babu labarin shi, sannan aka shigo cikin masarautar nan aka ɓalle kofar birnin aka shigo har sashin Fulani bingel aka daki mutanen ta, gaskiya akwai matsala ba zan iya hakuri na Zubawa Yakubu ido ba, na tsawon shekaru nayi yanzun kan sai inda karfina ya kare."
Caaa suka mishi tare da kare Yakubu karshe haka ya rasa wanda zai yarda da shi dan dole ya fito da adawar shi akan lallai sai an fita yaƙi, sosai ran Yakubu yake b'aci akan fita yaƙi dan haka ba tare da wani sabon abu ba ya sauke mishi rawan shi.
A hankali sai alamarin ya zama fadar cikin gidan, domin Zakaria yaki yarda a sauke mishi rawanin shi.
Kiri-kiri Chiroma ya gaya mishi abinda bai sani ba inda ua gargade shi ya fita a harkan Yakubu girma da arziki ko kuma su wulaqanta rayuwar shi kamar yadda suka wulakanta Bello.
"Ni nan na shirya kome, tare da goyan bayan yan majalisar Bello, ni na saka aka kullawa Aaminatu sharri, sannan na koma na juya kamar bani ba, kau Yaro ne Zakaria. Dan haka ka koma gefe kayi kallon duniya idan ba haka ba, zan saka a dauko min Yarka Haimah na bawa Yakubu izinin lalata kome da ka shirya domin ita. Idan naso sai na hada uwar da yar na bawa Yakubun yayi yadda yake so da su, dan haka shawara a gare ka shine ka tattara naka ya naka,.ka bar mana fada."
Wani irin mugun tsoro ne ya shiga cikin zuciyar waziri Zakaria, ya kasa aiwatar da kome, dan haka ya nufi gidan shi da zimmar ya haɗa kan matar shi da Yar shi su bar masarautan idan kome yayi kyau sai su dawo, amma sai me? Labarin da aka gaya mishi ya kusan zautar da shi domin yana zuwa aka ce mishi bingel ta zo ta saka an tafi da Haimah da Mamar. Cikin tashin hankalin mara iyaka ya nufi bangaren bingel. Ya samu ana rirrike Mahaifiyar Haimah, ita kuma Haimah Bingel ta saka a lalata fuskar ta.
Domin tayi irin kwalliyar Bingel alƙawari ne babu wanda ya isa yayi kwatankwacin irin kwalliyar Bingel. Sai gashi hatta alkyabbar iri daya ne, wannan abin ya masifar bata mata rai shi yasa take son wulakanta yarinyar da uwar ta.
"Don Allah Fulani Bingel kiyi hakuri tayi laifi masarautan ma zamu bar shi balle tayi irin shigar ki don Allah ba a matsayin waxiri nake rokan ki ba, a matsayin Uban Haimah" ya fada gwiwar shi a kasa yake rokon ta.
"Ka ɗauke ta ku bar masarautan nan" ta fada bayan ta mike, tare sa barin wurin.
Baki daya zuciyar ta rawa take, shi kuwa waziri bayan sun bar bangaren Bingel kayan su, suka dauka amma sai da aka kwace kayan jin dadin su, aka Kore su a garin idan akwai abinda yake mishi dad'i karya ne, dan haka Haimah da mahaifiyar ta kuka suke kamar me.
Bayan fitar su ne Bingel ta koma dakin Barkindo ta same shi shame-shame an buge kayan aikin shi ina yaga kuzarin wani abu.
"Kace min wannan dai da ya taimaka mata shi ne ya maka wannan dukar?"
Gyada kai yayi tare da cewa.
"Innah idan na warke don Allah ki nima min auren Anum"
"Da karfin tsiya zan nima maka auren ta"
--
Sarki yakubu na dakin hutawar shi aka ce Sarkin yaki yana sallama da shi.
"Kuce ya shigo"
Fita sallama yayi ya gaya mishi ya shigo, cikin ladabi da biyayya tare sa uban tirsassawa ya sunkuyar da kan shi yana faɗin.
"Allah ya baka nasara an sami yarinyar tana nan rugar gona ce"
Zubur ya mike yana sake murmushin jin dadi kafin ya ce mishi.
"Maza a shirya kome akai gidan su"
"Allah ya baka nasara, yarinyar mareniya ce amma an ce an ganta da wani bako"
Gyada kai yayi sannan ya ce mishi.
"A sayi mutanen gidan"
"Toh Allah ya baka nasara ka samu Ajuji da batun"
"Toh an gama"
Ya fita, dariya Yakubu ya fara yi yana hango yadda zai yi watandar arziki da yarinyar da yaga K'ugunta kamar na uwar mata, wannan duk namijin da ya samu nasarar daukar ta sai ya kusan gigicewa. Balle shi da ya gama sanin waye mace.
--
A hanyar su ta tafi ne suka hadu da Sarkin Gida, wanda shi yayi kokarin boye kan shi, ganin yadda suke tafiya a wulaqance yasa shi rudani ya koma ya gayawa su Baffa'm, kasa hakuri Baffa'm yayi ya fito hanyar da suka bi.
"Zakaria!" Ya kwala mishi kira, juyawa yayi ya hango baffan shi, wanda masarautan ta ci amanar shi, kuka ya fashe da shi kamar karamin Yaro, ya juyo suka dawo, bude mishi hannu Baffa'm yayi a hankali abubuwan da ya rasa yana dawo mishi.
"Ka gafarce ni Baffana, wallahi abubuwan masarautan nan yafi karfina daga ni har Iyalina bamu tsira ba, tashin hankalin yau daban na gobe daban, na gaji sun cire kome Dakyar muka tsira da Iyalina"
"Allah yana nan baya barci"
Kallon Haimah yayi tare da cewa.
"Muje gida ko amarya ta!" Haka suka nufi gidan su, aka gyara musu daya dakin, dake Galadima da Lamido basu nan, aikuwa nan suka shiga hiran yaushe gamo, suna cikin haka Galadima da Lamido suka dawo, cikin farin ciki suka rungume juna, galadima da waziri, nan aka barke da hira, kallo daya Lamido yayiwa Haimah ya hango yanayin da Gidado ya mishi misali,. Cikin farin ciki ya ajiye kome idan har ta sake jiki zai bata sakon dan uwan shi.
Ganin waziri da halin da yake ciki yasa sukara yarda Chiroma shi yake buga mulkin shi a cikin masarautan.
"Ban san me nayi ba, sai dai hatta shawara ba ayi dani, tunda bayan batar ka na fahimci kai ne kawai kayi mulkinka da adalci ba tare da an zubar jinin kowa ba, a yanzun haka an zubda jinin wadanda basu ji ba basu gani ba, nayi kokarin dakatar da haka Baffa abin ya ci tura.
Akwai mugaye a cikin masarautar masu fuska biyu wadanda basu son zaman lafiya amma haka ba zaka iya cewa kai tsaye wane ne, abinda na sani Chiroma shine me kaso me girma a cikin Masarautan"
Haka suka tattauna, har inda Baffa'm ya gabatar mishi da lamido, sai da ya zubda kwalla, ya cewa Baffa'm.
"Dole ya shiga Masarautan dole ya zama sabon sarkin mu Insha Allah"
**
Washi gari
Da safe baki daga masarautan suka kawo kayan na gani ina so na Anum. Sake baki suka yi aka rasa me Magana, sai Inono ce ta fito tana kallon su ta ce musu.
"Tunda mai martaba yace yana so mu ai ba zamu hana shi ba, waye zai ki amincewa da wannan haɗin? Kace idan ya shirya ya tawo a daura auren."
"Lallai ma kuwa wallahi ba zan aure shi ba, ko kashe ni za ayi." Ta fadi haka tana me fita daga cikin gidan da gudu,
"Kunga Ku kyale ta aure babu fashi ranar sati" inji Inono, ba kome ya haddasa haka ba sai tulin dukiyar da aka kawo, me shegen yawan gaske.
Haka suka tafi aka bari, kowa ya shiga barin bakin shi, masu hassada suna yi masu bakin ciki suna yi.
Amma ga Inono tafi nono fari jikar ta zata auri sarkin gari sarkin daular da babu irin ta, ba yarima ba sarki takanas ta kano ya kawo kayan na gani ina so na jikarta me farin jini shi yasa mana bata da samari ashe kwarjini ne da ita. Duk jikokin ta babu irin ta wannan wacce irin sa'a yarinyar take da shi ne haka?
Cikin wakar fulatanci ta fara yada habaici tana fada musu.
_Yarinya jinin Larabawa jikar Fulani haihuwar Sa'a farin jinin manyan mutane alfaharin manyan sakaruna, waye ya iya haihuwa irin ta D'anta Salihu?_
Sam ta manta tana da sauran Yara a cikin gidan, ta manta akwai jikokin da ta fi so, sai gashi ta bad'a toka a idanun ta tana wake Anum, baki daya tsohuwar nan ta hana kowa sakat, ga bakar magana tare da cewa duk wani ya daure fuska tabbas dan bakin ciki ne da hassada, wannan dalilin yasa surukanta suka sake amma tabbas suna cin wuta a ran su, haka akayi ta zuwa gani daga makotan gidajen da suke kewayen rugar gona,
Daadah kan turawa Bingel labarin kawo kayan na gani ina so na Sarki Yakubu tayi, bata bari dan aikin ya dawo ba suka taso tare da kayan da ya ci uban na Yakubu,da kwarin gwiwa tazo nimawa Barkindo auren Anum,dan ta lura baki daya Anum itace hasken ta matukar tana son cigaban su ita da D'anta.
Ai kuwa Inono ta rude ga sarki ga Yarima, wannan abun yayi matukar gigita mata lissafi,
"Yanzu duk wannan duk na auren Anum ake Anum nima? Ikon Allah ashe ina da rabon ganin Masarautar Gobir? Toh gaskiya ki bari sai mun yi shawara da ita domin mu san waye take so" ta fadi haka ne domin har ga Allah tafi son Sarki Yakubu, domin nan ne zata kira Jikarta matar sarki ba matar Yarima ba,waye zai sake ya rasa wannan babbar daman matar sarki ba wasa ba fa, yarima kuwa sai an gadama zaa bashi mulkin indai Sarkin da yake kai yana da yara ita kan tana fatar Anum ta samu ciki da Sarkin itama ta zama uwar sarki.
Ba tare da ta nuna Bingel bata son danta, ta amshi kayan akan sai sun yi shawara da yan uwan Baban Anum, sannan akan lokaci zata gayawa Daadah.
*
Yana tsaye yana goge jikin Hari, ji alamar tsayuwar a bayan shi, juyawa yayi yana kallon ta, tab'e baki yayi yana cigaba da aiki.
"Sarkin Gobir ya turo kayan na gani ina so na!"
Kamar ba da shi take ba, ya cigaba da aikin shi, kuka ta fashe da shi tana cewa.
"Kayi min shiru?"
Wallahi ko a jikin shi ya cigaba da aikin shi.
"Subhanallahi Anum! Me ya faru?"
Cikin wani irin kuka ta ce.
"Baffa'm sun amshi kayan auren Sarkin Gobir wai yana niman aurena, ranar sati zasu aura min shi"
"Baki son shi ne? Ko baki son zama matar sarki ne? Anum wannan damar da kika samu ba kowa ke samu ba, ki xaka matar sarki ba karamin al'amari bane ya kika gani, akwai kayan k'awa kayan kwalliya. Akwai kayan jin dadi da abubuwan more rayuwa" inji Baffa'm, a hankali ta juya ta kalli inda yake kafin hawaye Masu zafi suka shiga zuba mata, sannan ta juya zata bar wurin domin ta rasa inda zata fadi halin da take ciki.
Suna ganin take tafiya tana share kwalla da yake zuba mata.
"Hassan!"
Juyowa yayi ya zuba masa idanu,
"Kana son ta?"
Daidai fitowar jama'ar gidan baki ɗaya, suna jiran amsar shi.....
__________
Tare da masu karantawa suma suna jiran Abinda zai fada...🤣😂😿
#Mai_Dambu
[6/16, 7:22 PM] Black Girl: KALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
EWF
BABI NA SITTIN DA DAYA
Shiru yayi yana kallon su kafin ya mai da hankalin shi kan hanyar da Anum ta bi, lashe bushashen fatar bakin shi yayi yana me kallon kasa sam baya da.muradin aure nan kusa sai ya share tare da kakkabe duk wani wanda yake da hannu a cutar da Ammyn. Kai tsaye kuma ba zai iya cewa Mahaifin shi da ya bashi damar haka ba. Baki daya zuciyar shi ta rabu gida biyu.
"Idan baka bukatar ta shi kenan zan nimawa Gidado! Na fahimci rashin maganar shi ba zai hana shi ya amshi abinda na ba shi ba, ai na manta ne kai may..."
"An haife ni ne domin na bautawa Allah na kuma so Annabin Allah, sannan nayiwa iyyena biyayya, bana fatan ranar da zan juyawa umarnin ku baya, Allah yasa mutuwata ta zama itace farko kafin na bijire muku, ina maraba da duk abinda ka bani nasan me kyau ne da inganci"
"Galadima kaga irin Aminatu, ka ga abinda bakar saniya me farar madara ta bani, akwai wanda ya fini dacen samun Y'ay'a haka? Insha Allah yau ba sai gobe ba, Anum zata zama mallakar ka, galadima a shirya kome!"
"Alhamdulillahi" kowa yake fada domin basu yi tsammanin haka ba, ita kan Haimah bata zata yana iya zaro magana har haka ba.
Dan haka take ta mamakin halin shi, Cikin tsananin farin ciki Waziri Zakaria ya ce musu.
"Na bawa Gidado Husaini auren Haimah a daura auren su lokaci guda"
"Ikon Allah, Allah me kyauta da kari. Toh idan aka daura Sarkin gida ka ɗauke su da Anum a kai su Borno ka gayawa Aaminatu gani nan tafe bari ba tallafawa dan Albarka aikin shi"
Murmushi Lamido yayi domin bai kai ga isar da sakon Gidado ba, an tabbatar da haka. A yammacin ranar Galadima da waziri, Baffa'm da Sarkin Gida suka nufi rugar su Anum,
Cikin dattako da sanin ya kamata, aka karbe su, dake dattawan rugar maza sun san Sarki Bello da labarin shi, da kan shi ya nimawa Lamido Hassan auren Anum, wanda ya bada sadakin da wani sarkan da ya ajiyewa Aaminatu, sai galadima da ya nimawa Gidado auren Haimah shima da nashi sadakin.
Auren da ya samu halartar mutanen rugar, dake ba a fada a cikin gidan ba sai da aka gama daura auren, sannan aka fadawa Inono, kan kututturen bala'i, da tayi ya masifa sai da aka rasa yadda za ayi da ita, bayan an gama daurin auren suka bar rugar, sannan suka zauna ka fara tsara yadda za a shiga cikin dan haka suka fara niman Sarkin yaki, shi kan cikin daren aka kamo shi, wanda aikin Lanido ne,
Da daddare mata kanen Baban Anum suka kawo ta, dakin su Haimah aka kaita domin gobe Insha Allah sai sun bar yankin baki daya za a fara gumurzu.
Haka ce ta faru da sassafe aka raka su har iyakar kasar sai da suka kusan shiga wata yakar Lamido da Galadima suke tattaunawa, wanda kus-kus suke ba zaka gane abinda suke fada ba.
Suna isowa bakin mayaka daga sokkoto da kano suka iso, dan haka aka gama shirya kome, da alkawarin ba za'a taba kowa ba, kawai za'a kifar da mulkin Yakubu ne.
Tun a wunin ranar ake bushe bushe da algaitu ana farin ciki da murna, sai da dare yayi sannan aka samu damar shiga cikin masarautar ta kofar baya, ba tare da an taba kowa ba, sai dai duk wanda ya nime kawo farmaki sai dai babbar shi ta haifi wani da wannan yanayin suka isa cikin masarautan aka kewaye gidan manyan yan majalisar sarki, sannan aka fara sanarwar an yi sabon Sarki an cire Yakubu daman rikon kwarya ne, haka suka kafa sabon Sarki babu sanin kowa da gari ya waye manyan Yan majalisar da aka kama, sun hada da Chiroma dan Isa, Turaki, talba, Makama, Barade, Magayaki, Wadannan sune manyan fitinannun mutanen da suka dami kowa dan Haka,aka shigar da su Fada, Baffa'm yana tsaye da shigar yaki, lamido na zaune a ƙasa.
"Bello!" Suka kira sunan shi a tsorace, dafe kirji Chiroma yayi kafin ya fadi a kasa yana tari da aman jini, dukkan su durkuwa suka yi a gaban Baffa'm.
"Galadima wadannan mutanen sun ci Amanata, me zamu musu?"
"Hukunci daidai da laifin su mana, idan aka bar su zasu iya kawo mana tsaiko a yanke musu hukuncin kisa dan sunci amana" inji Waziri.
"Galadima baka ce kome ba?"
"Abinda Zakaria ya fada haka za ayi, amma ina ga me zai hana a musu sassauci, domin bincikar su ne waye ya aikata kullawa Aminatun sharri ko Lamidon mu?"
Gyada kai Lamido yayi, sannan ya zuba musu ido.
"Koran su A fada shine abinda ya da ce, idan aka kashe su gabar ba zata mutu ba, ruruwa zata cigaba da yi. Baffa'm ka duba magana ta abar su a ka koma kan kujeran ka ka cigaba da mulkin ka"
"Ina sarkin Fada? Ina liman, Alkali? Ku shaida ni na ajiye mulkina da na dawo na sauke Yakubu na barwa Lamido Hassan Muhammadu Bello, cikin da Amunatu ta tafi da shi Husainin yana borno zasu tawo idan naje, sannan akwai auren lamido da aka daura ayi hakuri nan da sati biyu za a hada ayi bikin bayan an maida aurena da Aminatu, Waziri Zakaria ya bawa Gidado Husaini auren Yar shi Haimah dan haka a cigaba da shagali."
A gigice Lamido yake kallon Baffa'm, bashi mulki ba shine matsalar ba, Ya zai yi da dan uwan shi? Da shima mafarkin shi kenan.
Bingel da ta samu aka bata hanya ta shigo, kallon Baffa'm tayi tare da fashewa da kuka.
"Ka yafe min ni ban san da wani baki zan baka hakuri ba."
Kallon Lamido tayi bakin ta yana rawa ta ja da baya, tana kallon yadda aka fara nadin sarautar da ta gama cin alwashin danta ne, wani irin kuka ta sake tana kallon ikon Allah, ana gama nadin aka sanar tare da bude kofar fadan.
A take aka fara mubaya'a ga sabon Sarki sam lamido bai son wannan al'amarin amma ya zai yi, a ranar da aka tabbatar da shi dakarun Kano da sokkoto suna masarautan har tsawon kwanaki uku, su Chiroma kuwa kai su aka yi gidan yari, aka ajiye su.
**
Cikin farin ciki da nutsuwa suka isa Masarautan Borno, tarba na karamci aka musu, sannan Sarkin gida ya isar da sakon shi ga Sarkin Borno, shima yaji dadi sannan ya saka aka musu iso har sashin Fulani Aminatu, tana zaune Lamido yana bata labarin yanayin da ya ga Anum, murmushinn farin ciki take tana kuma karfafa mishi gwiwa aka shigo da sallama.
Ganin mata uku namiji daya yasa ta kallon Innayo alamar daga ina?
"Ranki shi dade Uwar sarkin Gobir matar sarkin Gobir ga bakin ki daga masarautar Gobir"
"Sannun ku da zuwa" inji Innayoh,
"Ku shigo" da sallama suka shiga cikin ga shi dama dabi'ar barebari ya aure ta kamshi take ta ko ina.
"Eh Sarkin Gida! Kaine?"
"Allah ya baki nasara ya kara miki daraja ya baki lafiya da nisan kwana,Uwar dirken Gobir, Ga matan Zakuna nan na kawo miki, ita me farin alkyabbar ita ce matar Lamido me jar alkyabbar itace matar Gidado? Sannan an bawa Mai Martaba Sarkin Gobir auren Fulani Hadizah yar Sarkin Kano,.shima Baffa'm yana nan bisa hanya"
Sunkuyar da kai kowa yayi, kafin aka kai su cikin dakunan da suke gidan daga cikin gidan kuwa abinci akayi ta shigo da shi, lokacin da labarin auren Gidado yazo kunnen Bintu murmushi kawai tayi amma bata jin haka zai karya mata zuciya,
Basu samu nutsuwa ba sai washi gari, fitowa Anum tayi tana me Niman wanda zai taimaka mata ta cire kayan ta a cikin sundukinta.
"Kece matat Gidado?" Inji Innayoh,
"A'a" ta faɗa a kunyace.
Shigowar shi dauke da wata kwando, ya sake fuskar shi dauke da farin ciki, ya nufe ta.
"Dakata Gidado! Matar Lamido ce"
Wani irin sake kwandon yayi kome ya watse jikin shiga yana rawa, riko hannun shi Innayoh tayi zasu fita Fulani Aminatu ta ce.
"Lafiya?"
Da sauri ya nufe ta, suka shige daki, jikin shi sai rawa yake, tashin hankali da ya shiga baki ba zai iya faɗa ba, idanun shi sun yi jajjur, ya daki kirjin shi ya daki bakin shi, sannan ya kifa fuskar shi a tafin hannun shi, ya sauke wata irin sirrintacciyar kuka tare da jin Hassan ya ci amanar shi. Kuka yake domin ya gama ajiye burin shi akan Anum, yana kuka yana dukar kirjin shi.
"Itace wacce kake so?" Innayoh ta tambaye shi, gyada kai yayi ya rike hannun ta ya shiga mata bayanin yadda suka yi da Lamido.
"Idan haka ne kuwa Lamido bai san ita bace wallahi ba zai tab'a wulakanta alkawarin ka ba."
"Ya isa Innayoh idan har lamido da gayya ya mishi haka wallahi sai ya sake ta, bana son abinda zai raba min kan Yarana na gaji sannan akan me zai aura mishi wata mace bayan ga Bintu nan"
Nan Amunatu tayi ta faɗa, kallon ta yayi tare da rike hannun ta ya ce mata.
"Sabida bana magana,. Sabida bani da jarumta? Bani da wani baiwa shi kuma dan baiwa ne ko? Ya zama sarki ya kwace yarinyar da nake so ba kome nima zan fita duniya zan nimo shahara da baiwar da na rasa har ya min fintinkau"
Ran Amunatu ya barci dan haka tana son dakatar da shi sai da ta falla mishi mari.
"Kai ne ka faro me ya kai ka Gobir? Idan ka sake hassada da kyashi ya shiga tsakanin ka da dan uwanka ban yafe maka ba, wallahi ko kallon Yarinyar kayi ban yafe maka ba, matar dan uwanka ne idan har ya san kana son ta ba zai tab'a yarda ya aure ta ba, Meye ne Lamido bai bar maka ba? Mace da mulki sune Damuwar ka? Na sani tun yarantaka kake burin shi idan Allah ya nufa baya cikin kaddaran ka fa? Kayi hakuri Allah zai baka lafiya, mulki kuwa ka yarda Allah yake badawa ba wani ba, shi ya zaɓi Lamido, ba lamido ne ya zaɓi mulki ba, nasan shi baya kaunar shugabancin komi kashin sa, kayi hakuri nasan an fi karfin shi ne, dan ran shi ba zai amshi mulki haka ba"
Rarrashi hakuri nasiha wanda yasa shi jin ya hakura amma idan ya tuna sai ya kara hawa dokin zuciya, abin ka da kurma abin dai hakuri akan abinda yake ganin an zalunce shi, Innayoh sun yi magana da Sarkin Gida baya gaya musu gaskiya abinda ha faru, da yadda suka yi da Lamido, da wannan yanayin Fulani Aminatu ta tura shi ya tawo da Baffa'm ya nime auren Bintu da Gidado, domin sosai tayi fushi. Ai ba a haka kawai dan yaga Lamidon ba me yawan magana bane za a kama a bashi mata tunda ba son ta yake ba Gara a raba kowa ya kama ganin shi.
_Insha Allah idan na kai page 70 zan dakatar da rubutun nan zan fara typing ZAYN MALIK Insha Allah dan hakan ku sha karatu lafiya_
#Mai_Dambu
[6/17, 10:09 AM] Black Girl: KALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
EWF
BABI NA SITTIN DA BIYU
Sosai ran Aminatun ya b'aci akan Anum kuma taki yarda ta ga Anum wai cewar ta ai ta sanadin ta ne yaranta suke shirin samun matsala, dan haka ta dauki fushi akan Anum ko D'aga kai ta kalle bata yi, haka yayi mugun batawa Innayoh rai, dan basu tab'a samun rashin fahimta da yar rikon ta ba, dan haka Innayoh da kanta ta kai Anum cikin gidan sarautar wurin Fulani Babba, ta gaya musu halin da ake ciki, suma basu ji dadi ba amma sun dauki haka a matsayin zanen ƙaddara, dan haka a cikin gidan dakin su daya da Bintu, sannan kasancewar masarautan akwai masu gara na musamman haka aka hada Anum da wata Hajja Yalwa, ita ke gyara jikin matan sarki da surukan su, haka aka yi ta gyara mata jiki ana tsumata, domin sun yi ittifakin matan sarakuna basu cika zama su daya ba dole sai da abokiyar zama.
Tsawon kwana huɗu bata ga giftawar Anum din ba, suna cin Abinci ta kalli Innayoh.
"Innayo naga Haimah ina Anum?" Cikin harshen fulatanci tace mata.
"Na kaita inda zata fi samun kulawa" d'ago kai tayi ta kalli Fuskar Innayoh,
"Allah ya baki hakuri na san nayi laifi amma da ciwo ne, kuma a yanzun kallon da yakewa kan shi na daban ne gani zai yi kamar dan nakasar shi yasa aka bawa Lamido kome"
Rike hannun juna suka yi, idanun Innayoh cike da kwalla.
"Kome Lamido ya samu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 39