wannan daren da lokacin Gidado ya amsa sunan magidanci da yasan me yake yi, ya amsa sunan abinda ya dace. Ya mai da Bintun shi cikakkiyar mace kamar sauran mata masu aure, sai da ya gama kome sannan ya sauka ya shiga ban daki ya haɗa mata ruwa sai da yayi sannan ya fita ya kaita da kan shi yayi mata kome sai kunya take ji, yana dariya.
"Yan mata bude fuska kawai ki gaya min gaskiya"
Dakyar ya gama mata sannan ya fito.
Jin ana buga mishi kofa yasa shi fita, bayan ya saka kaya.
"Lafiya?"
"Waziri yana niman ka"
"Toh gani nan zuwa" ya koma ya duba matar shi ya taimaka Mata, sannan ya shiga cikin ban daki da zanin gadon ya wanke tass, sannan ya fito ya samu bata nan, shimfida yayi ya tafi dakin ta, ya samu tana sake gyara jikin ta zata kwanta.
"Ki jirani gani nan zuwa" gyada mishi kai tayi, sumbatar goshinta yayi sannan ya fita..ko babu kome ta wanke mishi zuciya sannan ya nufi gidan Waziri...
🤌🏽Sorry....
[6/24, 11:29 AM] Zahrah Maman Khausar: KALLABI..!
A Tsakanin Rawuna
EWF
https://www.wattpad.com/1239564115?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=BcmARJ1IRXCXlo4PZvhqWXRMt%2F6qCcA5aUcaHqX59UQolhqkTeaFsrPkDfNylRAH5jo0wA4euOBLpL4x9lS4Lio9N3oEkn%2FXM2GeWhp6XrZnAA3gYL3GAw2RrtgWT9m5
BABI NA SABA'IN DA UKU
Bai kai zauren farko ba, yaji an yi sama da shi tare da rufe mishi kai, akayi wani hanya da shi, a yadda ake tafiyar bai nuna musu wani abu ba, haka suka wuce da shi har gidan Chiroma.
Suna kai shi aka ajiye shi a kujera sannan suka cire abin kan shi. Hango Chiroma yayi a hankali ya zube akan gwiwar shi,
"Na tuba na bi Allah na bika, wallahi duk abinda kace shi zan bi"
Dariya yayi yana kallon shi tare da cewa.
"Don Allah dube shi sabida hakuri da biyayyar shi, Matashin da ya dace ya zama Sarki yau shine a gaba na, tashi d'anan,ka saka a ranka ni nan zan dawo maka da mukamin ka"
Girgiza kai yayi cikin kwantar da hankali ya ce.
"Gadon hari sau fanna ramin kura sai y'ay'an ta, bige sai bige babban goro sai magogin karfe, Daka yau adaka gobe dai mai gaskiya, Kainuwa dashen Allah, Giwa me tafiyar kasaita, birnin da babu kai ba birni bane hankaka me da dan wani naka. Me zance? Ai wannan wurin na jarumai ne, ni da takobin ma tsoron shi nake ji, Baba Chiroma wurin can bana Yara bane ya zaka ji idan aka ce kai ne a wurin mulki sai jarumi masani wanda yaga jiya ya ga yau, aka jima ana bugawa da shi. Amma ka gafarce ni idan nayi wauta"
Kallon juna suka yi su uku, wato tun cire mishi abin fuskar shi ya gane akwai Sarkin gida a cikin su, sai Yakubu.
"Kun ji me yace?" Chiroma ya tambaye su.
"Eh Chiroma amma kai Husaini me yasa baka son mulki?"
"Tun ina Yaro marubuci ne ni, idan nace zan yi mulkin ba zan iya ba, sannan shi kuma Hassan mayaki ne" Yakubu ya tambaye shi.
"Toh yanzu ta wani hanya zaka taimake.mu?"
"Baba Chiroma ina tare da ku, kuma zan tsaya muku a kowani fuska, sai dai ina tsoron cin amana domin Yaya waziri ya kira ni yanzu "
"Jeka zamu yi nazari babu wanda ya isa cin amanar ka, yadda kake da hankalin nan"
"Nagode "sannan ya bar su nan suna musu,akan abinda ya gaya shawaran da ya gaya musu, sannan ya. Nufi gidan Waziri. Cikin kunya da girmamawa ya zauna tare da cewa.
"Barka da hutawa Yaya Waziri."
"Ni ba zaka ce min Baba Waziri bane kamar yadda dan uwanka yake gaya min" hàdiye yawu yayi sannan ya ce mishi.
"Allah ya huci zuciyar ka Baba Waziri"
Murmushi yayi sannan ya ce mishi.
"Dama na kiraka ne muci abinci da kuma tsarin mulkin zamu tattauna akai."
"Toh gashi ni a koshe nake,yanzun naci abinci a wurin Haimah " d'ago kai yayi tare da murmusa mishi.
"Ya take?"
"Tana lafiya "
"Da fatan bata maka zancen shirme ba?" Ya tambayi Gidado,
"A'a Baba Waziri"
"Toh muci mana, ban tab'a ganin mutumin da bai da mu da mulki irin ka ba, naso kwarai da Lamido yayi dogon zamani, muga irin tashi mulkin, ga wasu abubuwan da nake son a ce da ya ciki-cika."
"Allah sarki dan uwana, haka Allah ya nufa, me kake so ya ciki-cika?"
Jim yayi sannan ya ce mishi.
"Manta kawai, mu ci mana " babu musu ya fara tab'awa yana gyada kai, kallon juna suka yi kafin Waziri ya ce mishi.
"Sam baka sha'awan mulki ne?"
"Haba ina me zan yi da shi a matsayina na Galadima ya iso ma, sai dai Baba Waziri ina ganin daga amsar damar aiki naga kamar ana yawan tab'a kayan Baitul Mali amma kayi hakuri kar haka ya zama babban damuwa xan gayawa mai Martaba a shawo kan abin"
"Ikon Allah kaji kwazo, har ka gane haka? Toh yanzu ya za ayi domin bana son ka gayawa Mai Martaba ni na dace da sanin kome "
"Idan da hali duk wani abinda yake shigowa ta hannun mutane ya koma hannun ka, sannan zai zama karfin da kake samu ya zarce na kowa daga lokacin da dukiyar Baitul Mali ya shiga hannunka, ni ina gefenka ga sarki a gefen ka kana tsammani masarautar da mulkin ba zata koma taka Ba ce?"
Cikin tsannanin mamaki yake kallon Gidado, tunda yake bin bokaye da malamai babu wanda y gaya mishi zai iya mallakar kowa sai Gidado.
Dariya yayi sannan.ya ce mishi.
"Anya wannan shawara ne?"
"Ka zuba idanu xaka ga dalilina na cewa haka "
Sun jima suna hira bai yarda ya kawo mishi hiran Chiroma ba, har suka gama ya tafi.
Sai da ya shiga cikin gida ya samu Baffa'm,.yana dakin nazarin Lamido.
Suna nazarin wasu abubuwan.
"Ya kome yake tafiya?"Baffa'm ya tambaye shi.
"Alhamdulillahi kome na tafiya dai-dai"
"Kana cusa kanka cikin hatsari fa!" Baffa'm ya gaya mishi.
"Baffa'm babu hatsari ku taya ni da addu'a kawai Allah ya cika min burina ranar da lamido zai cika kwana arba'in ranar kowa zai biya zunubin shi"
"Meye shirin ka?"
"Yana dayawa tsare tsare na!"
"Shi kenan ka duba Anum taki cin Abinci sai Saraki yazo" tsigar jikin shine ya mike, ya tashi a hankali ya nufi hanyar cikin gidan, bin shi da Idanu Baffa'm yayi sam yanayin shi tafyyar shi.maganar shi bata tab'a nuna zallar bacin ran shi, kullum fuskar a sake take, amma shi din ruwan sanyi ne dafa mod'a.
A hankali ya shiga babban zauren inda suka sakata a gaba ta ci abinci, tana musu bori, zama yayi a gaban ta. Sannan ya wanke hannun shi da ruwan da yake cikin akushi.
"Ahaam" ya fada mata, bude baki tayi tana son yi kuka.
Sake cewa yayi Ahaam,
Ammyn ta mike zuwa ɗakinta, kuka take son yi amma ta kasa sai salati, wannan abun da yake yi lamido ne yake mishi lokacin suna yara idan yaki cin abinci.
A hankali kome yake dawo mata sabo, ta'aziyar da kuma abubuwan da tayi ta gani a mafarki,. Bata fasa kiran sunan Allah ba sai da taji zuciyar ta yayi sanyi sannan ta kwanta.
A waje kuwa abinci ya bata yana gamawa, ya kalli Innayoh sannan ya ce mata.
"Ki kula da ita zan tafi na kwanta" ya mike tare da barin sashin, ai kuwa ta saka kuka zata bi saraki ne. Dakyar suka rarrasheta amma kamar wacce ake kara mata kuka, har Innayoh ta kaita dakin tare da taimakon iyayen ta.
Yana shiga sashinsa wanka yayi sannan ya nufi dakin Bintu da take barci, hawa gadon yayi ya janyota jikin shi.
Ajiyar zuciya ta sauke ajiyar zuciya, juyata yayi suna kallon juna,gyara mata kwanciya yayi a jikin shi barci yayi gaba da ita.
**
Washi gari bayan sun fito sallah asuba, suna tafiya da Barkindo.
"Yaya Barkindo! Ina son ka saka idanu da mutanen da sune zagaye da kai,"
Cike da mamaki yake kallon shi domin kusan abinda ya gayawa Lamido kenan wancan lokacin, bai kula shi ba.
"Ban gane ba?" Ya kuma tambayar shi.
"A'a kawai dai ka saka idanu akan kowa"
Daga haka yayi tafiyar shi, bai kuma bin ta kan Barkindo ba, a hankali Allah da ikon shi ya toshe musu basirar su, sannan ya kuma bawa Gidado damar shiga cikin su a cikin kwanaki biyar kacal, kamar yadda suka cutar da su, sai gashi yadda ya shiga jikin su da barnan da yake musu Allah kadai ya sani.
Ya cika zuciyar Waziri da son abin duniya, sannan ya haɗa shi manyan mutanen fada, rikici a hankali suka fara darewa a jikin Waziri suna komawa jikin Chiroma, a nan jikin Wazirin kuma ya cigaba da zama yadda yake abun shi ba zaka tab'a kawowa zaka iya saka mishi hannu a baki har ya ciza ba, sai dai kawai da ya tashi ya haɗa Waxiri da BARKINDO. Inda yayi tawa BARKINDO hannunka me sanda a yadda yake tare da waziri yayi a hankali da shi, ranar wata Laraba ana fadanci dama tun jiya talata Gidado ya gaya mishi abinda waziri yayi na rubda ciki akan dukiyar masarautar.
"Don Allah ka rufa min asiri kar ka cutar dani idan na gaya maka gaskiya yanzu haka ana shirya kashe ka, Chiroma da sauran mutanen fada idan baka sauke rawanin Waziri ba, don Allah kar ka gayawa kowa"
"Insha Allah ba zan fada ba"
Ana zaman fadan kuwa barkindo ya kalli waziri ya ce mishi.
"Ma'aji ya gaya min ka amshi kome na Baitul Mali ka dawo da shi,"
"Eh na amsa domin barnan dukiyar ake haka kawai tunda bikin yar shima sa dukiya al'umma yayi hidimar".
"Waye ya baka izinin amsa?"
"Ya kake min magana kamar dan ka ko sa'anka?" Waziri ya tambayi Barkindo. Cikin fushi Barkindo ya daka mishi tsawa.
"Gaya min waye ya baka izinin taɓa dukiyar Al'umma? Ku cire rawanin shi daga an Kore shi na dakatar da shi ba, kuma dawo da kome da ya tab'a idan ba haka ba ku wulakanta shi "
"Ka san waye Ni kake tozartawa? Ka san waye yake tsaye a gefen ka ba dan ni ba waye zai yarda da Lusari irin ka"
Ran Barkindo ya gama ɓaci san haka yasa aka fitar da shi daga cikin fadar, murmushi Gidado yayi, sannan ya shiga bawa Barkindo hakuri tare da cewa ya kula domin xa a iya kashe shi.
Bayan an tashi fada, ya fita Inda Sarkin gida yake ya Kalle shi.
"Kace zaka iua bada rayuwar ka domin fadar gaskiya? " Gidado ya tambayi Sarkin gida.
"Eh na fadi haka "
"Yau ku kaiwa barkindo hari bayan sallah isha, sannan ku tabbatar da Waziri ne ya aiko ku"
"An gama ranka shi dade, ya batun Chiroma?"
"Kowa zai biya abin ya shuka jeka kawai "
A hankali ya juya abin shi, kowani me hannu a cikin masarautar sai ya biya zunubin da yayi da hannun shi, kowani me ruwa da tsaki sai ya fanshe abinda ya biya da hannun shi, ranar da Lamido zai cika kwana arba'in su kuma zasu biyo shi da zunubin su.
Shi yasa ya zama wawa a tsakanin su,ya hana kan shi magana akan mulki ya hana kan shi fushi akan.kome ya ke mu'amalar su kamar ya yafe musu kamar ya manta da jinin biyun shi.
Shi yasa yake ganin Anum a cikin laluran xaucewar tunanji,yake dauke kai kamar bai damu ba, shi yasa ya jingine Haimah kamar bai damu da abinda uban ta yayi mishi ba, yaki gayawa Baffa'm kome ne, kamar yadda galadima ya ce yabi kadin kome a sannu yana bin su, tsarin kome yana ajiye a kan shi tun ranar da Lamido yace idan ya samu lokaci su tsara yadda zasu karkabe. mugun iri, shi da kan shi ya rubutawa Lamido yadda za ayi kome amma bai kawo a ran shi lamidon ne zai tafi ya bar shi ba,
A ranar da Sarkin Gida ya dawo abinda ya gaya mishi cewa yayi zaka yi aiki domin fadar gaskiya amma da sharadi, sai ka gaya min me yasa ja tsani Baffa'm?
Sunkuyar da kai yayi cikin takaici da kunya ya ce mishi.
"Sabida Amunatu! Ina son Aminatu, ina son matar Abokina, ni na hanata daukar cikin Mahaifin ku, domin duk lokacin da zai kasance da ita Ni nake zuwa na amso abincin shi anan nake zuba musu garin maganin da zai hana ciki zama a jikin ta. Ni na kawo mutumin da aka ce kwarton ta ne, sannan na tsira da rayuwar shi ga shi nan, na ce ya kafe akan cikin na shi ne, ban san da wani ido zan kalli Bello ba, a farkon ganin ka da nayi jikina ya bani kai ne zaka iya kawo karshen mu, daga baya sai muka fahimci baka da amfani, koda akazo kashe ku ni nace kar su har ba maka kifiya me guba. Domin mulkin aka baka ba zaka iya ba, Tun farko naso kashe Baffa'm amma Allah bai nufa ba, muka bar shi a araye! Naso kwarai hakan sai ga lamido shi yaki yasani da ɗaukar fansa, bai san yadda zai shiga jikin kowa ba domin yasan za a iya cin amanar shi.
Shi yasa sai muka kara shiga jikin shi sannan muka kashe shi, Gidado ka yanke min hukuncin da ya dace..
*Yau kam daya zaku samu bamu da wuta wallahi idan kuma mun samu wuta zaku ji ni! Wadanda suka biya Zayn Malik kuyi hakuri an kusan rufe Kallabi sai mu daura ko kafin kwanakin Zulhajj Insha Allah 😍❤️🥰🔥*
#Mai_Dambu
[6/24, 9:35 PM] Zahrah Maman Khausar: KALLABI..!
A Tsakanin Rawuna
EWF
BABI NA SABA'IN DA HUDU
ko zan samu sassauci a wurin Ubangijin mu na ci amana matuka gaya'
"Ba zan maka kome ba, ka je an yafe amma zaka biya laifin ka da wanke hannunka" inji Gidado,
A ranar da kyar yayi barci domin koran Bintu yayi a dakin shi baya son takura, kawai kan shi zafi yake mishi, me yasa ma bai mutu ba, ya bar Lamido da wannan tashin hankalin, zama yayi a tsakiyar gadon shi bayan sallah asuba, shigowa Bintu tayi, mika mata hannu yayi domin tun daren shi da ita na farko yau sati Daya kenan vai kuma niman ta ba,sai shiga dakin ya hargitsa mata lissafi amma baya niman wuce haka,
Hawa gadon tayi tana kallon shi, kafin ta ce mishi.
"Kayi hakuri na dame ka ko? Bana jin dadin yadda kake shiru shiru nan" janyo ta yayi tare da cire mayafin ta, kanshi ya kifa a kirjin ta, sannan ya shiga ya motsa ta kamar zai cinye ta.
Sai da ya birkita mata lissafin sannan ya samu nutsuwa, rungume ta yayi a kirjin shi yana shafa bayanta.
"Idan aka yi addu'ar arba'in zamu tafi borno ki ga iyayen ki zan barki anan na raka su Anum zuwa Somaliam"
Gyara kwanciyar ta tayi a jikin shi.
Kallon shi tayi sannan tace mishi.
"Amma Anum ba zata kuma dawowa ba ko?"
"Eh zata dawo kodan abin cikin ta" kasa tayi da kai bata kuma magana ba, haka kawai gaban ta yake yawan faduwa, tunda taji batun cikin Anum sai baki daya ta kasa samun nutsuwar,
Haka ya zare jikin shi yaje yayi wanka ya nufi fada, bai isa can ba aka ce mishi Baba waziri na kiran shi..
Nufar gidan waziri yayi, ya same shi kamar zai yi hauka, dan haka ya nufe shi.
"Me yasa kake haka?"
"Gidado ya ba zan yi ba, Chiroma ya juya min hankalin Barkindo, ban isa kome ba yanzun, tsoro nake ji karsu kashe shi "
"A ina zasu kashe shi? Idan kuwa haka ne ya kamata ka dakatar da su, daren yau, Wayyo don Allah kar ka yi amfani da abinda na gaya maka wallahi hankalina ne ya tashi shi yasa na sake baki "
"Ba sake baki bane shawara ne me kyau dole na kashe su da hannuna, jeka don Allah ka saka idanun ka akan shi kar wani abu ya same shi "
"An gama ranka shi dade," sannan ga fita hana jin kwalla na cika idanun shi. Su da aka tab'a su babu wanda yayi magana, sai shi da yake wurin kar a taba shi. A hanyar shi na wucewa ya hadu da Mandiya yasan ta da mugun son abin duniya, san haka ta cire silallar zinari ya mika mata a jaka, cikin murna ta zube sannan ya wuce itama zata yi nata aikin yau.
Yana shiga fada ya samu ana fadanci, zama yayi yana kallon dogaran fadar, ranar Litinin Lamido xai yi arba'in kafin wannan ranar yana son ta karkabe ko ina, dan haka ya gama karantar kowa a fadar matukar zaka bashi abin duniya zaka saye shi.
Bayan an tashi fada, da kan shi tayi ta turawa ana kiran dogarai yana basu kyaututtukan abubuwa masu kyau sannan ya ce musu.
"Marigayi lamido Hassan saura kwana uku ya cika kwanaki arba'in shine na raba sadaka daga cikin abinda na mallaka, nasan bai muku kome ba bai zalince ku ba don Allah ku mishi addu'a Allah ya gafarta mishi". Sunkuyar da kai suka yi sannan suna amsa da Insha Allah.
*
Bayan tafiyar su da Gidado ta turawa Chiroma boyayyen sako ta hanyar gaya mishi Waziri zai zo daukar fansa. Dan haka shiga shirin ko ta kwana, ya haɗa kansu fada sannan ya koma gefe yana kallon su,haka ce ta faru ranar a daren Waziri ya kai hari gidan Chiroma, sannan Sarkin gida suka kai hari gidan Barkindo. A hankali yake Bin tsarin, da idanun shi yana jin yadda masarautan ya kaure sannan ya zuba dakarun da suka yi mishi mubaya'a, kafin ya koma ya zauna yana jinjina kome da ya tsara.
Sai da aka kusan ritsa Barkindo sannan ya shiga bangaren su ta kofar baya yayi kokarin ceton su, sai da aka yanke shi a damtse suka samu guduwa, kafin dakarun shi suka kama su Sarkin gida.
A gaban Barkindo aka gurfanar da su.
"Waye ya aiko ku?"
"Waziri Zakaria, yana gidan Chiroma ya tafi kashe su"
"Gidado zaka iya zuwa?"
"Allah ya baka nasara me zai hana?"
A tare da wasu dakaru suka tafi gidan Chiroma, suna zuwa suka samu an cinnawa gidan wuta, waziri Zakaria da wasu dakarun shi.
"Ku kashe su, shi kuma ku kama shi"
"A'a Barkindo, karka min haka sabida kai nayi haka."
"Kuje a kai shi haramtacciyar sashi a daure shi, sannan nan da gobe zamu gurfanar da shi a cikin fada "
Sannan ya wuce. Koda suka koma gida Bingel da bata da wadataccen lafiya, tana ganin shi ta ce mishi.
"Basu maka kome ba?"
"Eh muje" kallon ta Gidado tana karantar razanar ta, tun farko haka baffa'm shima yaso yayi amfani da Barkindo, amma ganin Lamido sai yayi tunanin zai iya nasarar akan su, da salon yaki lumshe idanun Gidado yayi cikin tsannanin tsana ya kalli Waziri ya girgiza mishi kai lokacin da aka tafi dashi.
Luuuu Gidado yayi zai fadi suka tare shi suka nufi masarautan da shi.
Zaka dauka da gaske ciwon ne nan kuwa duk cikin salon aikin ne, haka suka shiga da shi, hankalin Baffa'm ya tashi, dakyar ya raka Barkindo sashin su da aka gyara ko ina, shi kuma ya dawo ya samu abin mamaki.
"Na wanke masarautar daga daud'a gobe Insha Allah akan idanun Zakaria zai amshi hukuncin shi, Baffa'm mutum Mugu ne" nan ya labarta mishi abinda ya faru,zama yayi ya fashe da kuka, kamar ran shi zai fita. Dakyar ya rarrashe shi.
Haka suka kwana a wurin qashin gari ana sallah asuba, aka nufi fada musamman wadanda basu san kome ba, haka suka tattauna har gari ya waye, aka koma sai da hantsi aka taru a fadar nan anan aka shigo da Sarkin gida da Waziri, Lumshe idanun Gidado yayi yana jin wani irin tsanar su kamar ya saka takobi ya sare yan banza, dauke kai yayi sannan ya cigaba da sauraron kafin ya mike tare da kawo wasu bayanai da suka kusan girgiza fadar har shi kan shi barkindo ya mike na kome bane ya faru sai shigowar wasu mutane uku maza biyu mace daya, suka zube a gaba kowa.
"Allah ya baka nasara, shekaru talatin da biyu lokacin da aka gyara dakin da zaa saka Fulani Aminatu, wadanna bayin Allah sune suka yi aikin, ko Baffa'm, sarkin gida, Galadima marigayi waziri Zakaria! Galadima baya raye ko ha haka aka yi ba bayin Allah?"
"Haka ne yarima Hussain!" Mutanen.suka bada amsa.
Damke hannun shi yayi yana jin wani irin daci a ran shi.
"Malam barau gaya min me ya faru?"
"Allah ya baka nasara, bayan an mu gama kome ne aka sarkin gida ya fita damu daga masarautar har mun fita sai aka tare mu, a cikin mu shida da muka yi aiki aka kashe uku sannan suka ce inji Sarki Bello tare da waziri"
Wani boyayyen murmushi Gidado yayi sannan ya ce.
"Ina jin ka ai ba a nan ya kare ba!"
"Sai suka ce zasu taimaka mana mu dauki fansa, amma sai mun bar garin, anan muka bar garin na tsawon shekaru uku, muka dawo a lokacin an kawo farmaki za a tafi da Aminatu muka dawo amma sarki Bello ya kare ta daga sharrin waziri da Sarkin Gida, domin a lokacin me gaskiyar da yake tare da shi Galadima, kuma Alhamdulillahi ya kare shi "
Lumshe idanun Baffa'm yayi hawaye na zuba a idanun shi.
"Malam Sani ina jinka?" Inji Gidado,
"Wato duk wani sharrin da ake kullawa a masarautar nan Waziri ne, shi ya hada kai da mutanen Sahil su dauke Amunatu sannan ya kashe Jakadiya rama, ya kashe sankira da Sanda, abu me ciwo shine kashe mahaifin shi da yayi, domin shi ya kashe mahaifin shi sannan ba zan iya fadar kome na wannan matar zata fada "
"Muna jinki tabawa!"
"Wato Allah ya kiyashe mu da aikin danasani Ubangiji ya kare zuciyar mu daga aikin asha ko shi sarkin Bello yasan kome shi da Fulani Aminatu, amma saboda rashin haihuwa yasa suka dauki haka a matsayin kyautar da ba zasu iya mai dawa ba, Amma abin da tashin hankali na iya fadin Sarki Barkindo Yazidu shege ne domin ba jinin Bello ba ne dan Waziri...
KUYI HAKURI MUNA BIKI NE INSHA ALLAH ZAMU KARASA
[6/25, 10:01 PM] Zahrah Maman Khausar: https://www.wattpad.com/1240027018?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=EiVGEzJCSWf2H5IEMX3Qn%2BeChpdOdlLP8gFqMkf4Rjn%2BcXW7keWrewgR4kFfhDlfIjiLRygHkn7BYMyqzSXKWjY9dBvTN8WWWNdlPVRoaO%2BlrgCbUuhfSY3V5mm2cPaz
KALLABI...!
A Tsakanin Rawuna
EWF
BABI NA SABA'IN DA BIYAR
"Innalillahi wa'inna illahi raju'un!" Abinda fadar ya dauka kenan, Waziri yana kallon Gidado cike da al'ajabi, yadda yaro karami ya yaudara shi tare da mishi kwanton bauna.
Cike da mamaki yake kallon Gidado.
Sannan ya zubawa Tabawa idanun, yana jin yadda take kokarin tona mishi asiri a idanun duniya.
"Lokacin da Bingel ta shigo masarautar nan, shi ta fara gani ta ce mishi tana son ganin sarki don Allah yayi mata hanyar da zata gan shi,anan take ba shi labarin yadda akayi tasan shi, ita kaunar shi take. Shine ya dauke ta ya kawo ta sashin su har ake zargin marigayi Yakubu da shiga kan bayi ba shine Waziri ne. Shine yake shiga rigar Yakubu a zata tsohon sarki ne, lokacin da yasa ka aka mai da bingel gidan Chiroma daga baya yasa Chiroma ya bawa Sarki Bello ita a matsayin kwarkwarah, kafin tazo wurin Sarki Bello yayi ta mu'amalar ta har ta samu ciki a lokacin sai aka danne cikin yadda lokacin da zaa bayyana shi kowa zai gamsu na Bello ne, koda aka kawo ta sarki Bello yaki mu'amalar ta sai da ta kai ga tayiwa Innayoh barazanar cutar da Aminatu ta hanyar d'aga mata hankali ta hanyar saka ciwon Aminatu ya tashi tayi ta barna bayan Baffa'm ya rufe mata yadda zai tashi,.da wannan innayo ta amince aka sakawa Sarki Bello maganin da zai saka shi bukatar ta, ita kuma tayi amfani da hakan tarar Sarki Bello har wani abu ta shiga tsakanin su, tun daga ranar bai kuma bin ta kanta ba, sai ranar da ta haihu, daga d'aga Yaron ya fahimci bana shi bane ni da kaina na ga haka a kwayar idanun shi, amma babu wanda ha fahimta, ganin idan na cigaba da zama da su kome zai warware shine ta saka aka tafi a kashe Ni, Yallabai Galadima wannan shine abinda na sani!"
Kallon Barkindo yayi da yake kuka wiwi, yana karawa kallon waziri yayi kafin ya ce.
"Laifin me na muku? Me yasa suka saka na biya bashin da ban ci ba? Me na muku a duniyar nan? Ku je a dauki Innar " ya fada a fusace.
A hankali ya warware igiyar alkyabbar jikin shi, yana kallon yadda kowa yake gyada, takawa Gidado yayi gaban Waziri.
"Kayi mamakin yadda na shammace ka ne? Ko kayi mamakin yadda na tafiyar da kome kamar ban san me nake yi ba ko? Kamar yadda ka kashe kowa haka wancan sakaran zai idda nufin shi akan ka zan yi amfani da iyawa ta na ga ya saka an kashe ka, s cikin kwanaki biyu masu zuwa idan ka isa ka tserewa ƙaddarar mutuwar ka"
Sannan ya koma ya tsaya a gefen Barkindo.
"Kayi hakuri kukan da kake bai kai wanda aka saka ni ba, a cikin masu sakani kukan har da kai! Me yasa ks cewa Anum ni na kashe Lamido? Me yasa ka lalata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 37 Chapter of 39